Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan nacr zanyi abu sai nayi, tana so tayi magana amman ta kasa mai naped na tarar mana muka shiga muka tafi, shiru nayi ina sauraran kukan Dejja wanda nikeji kamar mai dan bansan kukanta ko ya yake, kallonta nayi nace....



*ina kan bakata wallahi mudun bakuyin ruwan comment kamar yanda kukeyi a da ni kuma ba zan kara maku yawan typing ba, kuma next stage bansan abunda zanyi ba😂*

*Yauwa duk wanda take son karanta Izzah ko mulki tayi ma wannan number magana ta private 08160508316 zan tura mata document dinshi dan maganar gsky ban iya posting din shi page page daman sayan maku akayi duk mai ra'ayin karantawa sai tayi magana bye*

Share
Comment
And
Vote




*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 39⏩40

"Ni banga amfanin kukan naki ba Dejja, zakiyi ciwon kai ne a banza a wofi kuma kinsan banson abunda zai samaiki ko ya yake a rayuwa." Murmushi tayi tana goge hawaye sannan tace "baki son abunda zai samaini ko Aunty Auta? Sannan kuma baki san kiga ɓacin rai na ko Aunty Auta."? Nima Murmushin nayi sannann na ɗaga mata kai alamun eh, bata ce komai ba har muka iso hostel, muka biya mai naped kudinshi sannna muka shiga ciki, bayan mun gama ajiye kaya na tashi na shiga wanka ina fitowa itama ta shiga wankan bayan mun gama shiryawa tazo ta zauna kusa dani, kallona tayi sannan naji ta dafani tace "da gaske Aunty Auta baki san kiganni cikin ɓacin rai? Sannan kuma baki san damuwa ta ko ya take."?

Tsayawa nayi ina kallonta sosai, dan ta bani mamaki ai nasa mungama wanann maganar kuma, dan nasan dai maganar gizo bata wuce ta ƙoki inji hausawa, Murmushi nayi sannan nace "Dejja kenan, a shirye nike na sadaukar da farincikina saboda naga ke kina cikin farinciki Dejja, sannan kuma ko ɗaya bani son naganki cikin damuwa hakan ya kan sa nima na shigeta Dejja, Dejja keɗin ɗiyatace kuma ƙawata ce ke sannan kuma aminiyata wanda banda kamarta, keɗin haske ce mai haskaka sararin samaniya keɗin kin wuce komai da kike tunanin zan faɗi Dejja kina taka rawar gani a rayuwata kina kula da duk wani al'amarina taya za'ayi ace ni kuma naso naganki cikin damuwa ko kuma ɓacin rai? Ko ɗaya bani fatan hakan ke ni Dejja kullun addu'a nike Allah yasa na rigaki mutuwa ba ki ragani ba, dan ban iya jure rashinki yar'uwata."


Murmushi tayi tana share hawaye sannan tace. "Tabbas hakane Aunty Auta, amman ina da saurin alfarma a wajenki kuwa."? Kama hannunwata nayi ina murzawa sannan nace. "Kece ko keda alfarma a wajena, ki nemi ko wace irin alfarma ce ni kuma zanyi maki idan har bata fi karfi na ba Dejja." itama ƙara kama hannuna tayi sannan tace. "Alfarmar ɗaya ce Auntyna ina son dan Allah ki fidda wannan mumunan kudirin a zuciyarki na kashe Nurandeen, ba ruwanki da shi ki maida hankalin ki wajen karatu sannan kuma ki maida hankalinki wajen masoyanki guda biyu uncle Aminu da Dr Umar sannan kuma ki maida al'amarinki wajen Allah ina ganin hakan zaifi da ki tsaya cewa zaki kashe wani Nurandeen ɗin banza."


Miƙewa tsaye nayi zan barmata ɗakin, dan banyi tunanin abunda Dejja zata tambayeni kenan ba, ji nayi ta kamo hannuna tana cewa. "Daman nasan banda wata alfarma a wajenki Aunty Auta, amman bakomai hakan ma nagode dan hakan ya nuna man matsayina a wajenki sosai, ina ma rayuwarki fatan alkhairi."


Murmushi nayi mai ciwo sannan nace. "Naji na dauki alkwari ba zan kashe shi ba, shikenan ko Dejja."? Na faɗi ina goge mata hawayen fuskarta Murmushi itama tayi sannan ta rungumeni tana cewa. "Eh shikenan Aunty Auta, Allah ya barni da ƙanwar Babana." lakutar mata hanci nayi sannan nace. "Allah ba zai bar maki ki ni ba Auta, mutuwa dole ce kuma tana bisa wuyan kowa da komai na duniya harta dutse da kuma bishiyoyi." Murmushi kawai tayi sannan tace. "Hakane Allah yasa mu cika da imani kuma muyi kyawkyawan karshe."
"Amin ya Allah."



Zaunawa nayi na dauko handout dina na cigaba da karatun da Dejja ta hanani na ida ta jani kasuwa har nayi baƙin gani, sosai nike karatun kuma inajin dadinshi dan yana shiga sosai ji nayi wayata tana ringing Murmushi nayi dan nasan ba mai kirana indan ba yangidanmu ba ko kuma Aminu, amman ni raina Aminu ya bani ya kirani daukar wayar nayi sai naga bakuwar number, ajiyewa nayi na cigaba da karatuna sake kira akayi naki dauka sai da aka kira kusan sau ukku sannan nayi picking.


Jinayi an sauka wata naunauyar ajiyar zuciya sannan aka ce. "Alhmdulillahi, wallahi bakiji yanda na shiga damuwa ba, da baki dauki wayata ba Khadija." nidai ba muryar Aminu naji ba sauke wayar nayi daga kunnena sannan na kalli wayar na maimaita maganar a zuciyata, maida wayar nayi a kunne ji nayi yana cewa. "Hello Khadija, baki ce komai ba amman koda yake nasan ba zaki ce komai ba tunda baki san da wa kake magana ba, sunana Dr Umar Garba Ali, Khadija Allah ya jarabaini da ciwon sonki tunda na daura idona a kanki na faɗa tarkon sonki ba tare da nasani ba Khadija, naso na ba zuciyata hakuri ta hakura amman na kasa dole tasa na amayar da abunda ke cikin raina a kanki shine ina sonki kuma ina kaunarki aurenki zanyi."

Zufa ce ta keto man na kasa cewa komai cewa ya sakeyi. "Please Khadija ki sani a cikin jeran masoyinki nima na nuna maki yanda nikejinki a cikin raina wata kila idan da rabo ni sai nayi dace na zamo na ɗaya a cikin su." nidai shiru nayi na kasa magana dan bansan abunda zan ce mashi ba, kuma ina mamakin yanda mutun kamar Dr Umar yake gayaman kalaman soyayya har haka mutumin da bai shiga sabgar kowa bai damu da kowa ba, a depertment kowa tsoranshi yake dan yanda yake ba wasa gareshi ba, amman shi yake man wannan kalamai tsunkulin kaina nayi naji zafi nan na tabbatar da idona biyu ba mafarki nike ba katsaman tunani yayi wajen cewa. "Kinyi shiru bakice komai ba Khadija."


"Khadija." ya kira sunana a sanyaye kamar mai jin bacci, cikin in-ena nace. "Na..am Dr." sake sauke wata ajiyar zuciya yayi sannan yace. "Ina saurarenki matata." kirjina ya buga sosai da naji ya kirani da matarshi, dan ni yanzun saurin tsorata gareni kuma ina tsoran dadin bakin namiji, daurewa nayi sannan nace. "Daman ni tsakani da Allah Dr ni b... "Karki damu da abunda ya faru dake Khadija ni na ɗaukeshi a matsayin kaddara ni Umar ina sonki a haka koda kuwa yaro kika haifa a duniya kuma ba na sunna bane naji na yarda zan aureki a yanda kike." ya ida maganar, bayan ni ba haka naso gaya mashi ba take ya kulleman duk wata hanya da zan bi naga na yaki ceshi a rayuwa nidai ban sake yarda nace mashi komai ba, cewa yayi. "Ina sauraren ansa ɗinki Khadija, amman ki sani ina sonki."


Shiru nayi na wani dan lokaci sanann nace.....




*afuwan jiya banyi maku posting ba, naje ganin doctor kunsan masu asthma wannan lokacin nasune dan haka kuyi man Addu'a Allah ya bani sauki da duk wani marar lafiya ngd.*

Share
Comment
And
Vote






*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 41⏩42




Shiru nayi na wani dan lokaci sannan nace. "Dr ina bukatar ka bani dan lokaci nayi tunani gami da shawara please." cewa yayi. "Haba Matata har zuwa wani lokaci zan baki? Kinsan yanda zuciya take azubtaka a kanki kuwa? Kinsan yanda nikeji gami da sonki da ke ɗawainiya da ni Khadija? Khadija wallahi ina sonki sona gaskiya so na tsakani ga Allah, ni idan so samune ki bani dama cikin satin nan ayi bikinmu bcox ilove you more and more, wallahi ina iya rasa numfashina idan na rasaki Khadija dan Allah ki taimaka man ki anshi soyayyata, wallahi zan saki farinciki ba zan taɓa saki kuka ba Matata ya dace ki tausayaman Matata."



Sosai na kasa motsi mai karfi dan maganganun Dr Umar sun shiga jikina sosai,amman sai nayi Murmushi nace. "Naji Dr Umar karka damu, amman duk da haka ka bani lokaci nayi tunani dai." ji nayi yayi shiru duba wayar nayi naga ya kashe wayar, Murmushi kawai nayi na ajiye nima na cigaba da karatuna hankali kwance Dejja ce ta shigo tana waya, zaunawa tayi kusa dani naji tana cewa. "Haba Uncle Aminu wallahi ka yarda muda komai ba abunda bamu dashi fa." bansan abunda yace mata a bangarenshi ba naga dai ta kalleni sannan tace. "Gata nan zaune tana ta karatu, kuma lafiyarta lau ka kwantar da hankalinka ba abunda ke samunta fa." dariya naga tayi sannan ta miƙa man waya, ma'ana nayi magana da shi, ansa nayi cewa yayi. "Myluv fatan kina lafiya? Wallahi zuciyata ke bani kina cikin damuwa fatan ba abinda yake damunki ko."!? Cikin tsoro yayi tambayar dan duk ya shiga damuwa yanayin maganar kawai ya nunaman haka, Murmushi nayi sannan nace "wallahi ba abunda ke damuna ina cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali." ji nayi ya sauke ajiyar zuciya sannan yace."sure."? Ɗaga mashi kai nayi kamar yana gani na sannan nace "yes, ya kake kaima."?


Murmushi yayi sannan yace. "Gani nan dai Myluv, kinsan ban taɓa samun natsuwa da kuma jindadi har sai randa na mallakeki ki zama tawa, wallahi Khady jikina yana bani kamar har yanzun baki sona dan Allah Khadija ki daure ki soni ko ya yake koda kwatan yanda nike sonki ne, ni hakan ma yayi mani nasan watarana kema zaki soni kamar yanda nike sonki, kice rayuwata Khadija wallahi rasaki ni nasan a ranar zan bakunci lahira inasonki ina kaunarki inason komai naki, kina burgeni Khadija, nidai fatana da addu'a ta Allah ya bani ke a matsayin mata kuma uwar ƴa'ƴana."


Murmushi nayi sannan nace. "Allah dai ya tabbatar mana da alkhari, amman karka damu nima ai ina sonka kabar sama ranka baka samu karbuwa a wajen Khadija Bello ba, sai dai indan na tuna da wani abu sai naji ban dace da nayi aure ba Aminu, koda ya dace nayi auren bai dace da na aureka ba Aminu, dan na kasa manta abunda nayi maka Aminu na kasa manta kazamar ra... "Enough please Myluv, karki sama ranki damuwa akan haka, wallahi Khadija har abada ba zan taɓa yi maki gori ba, Khadija haka kika zano qaddararki wallahi ba wanda ya isa ya chanza maki qaddara kuma mu dukanmu mu yarda da qaddara fatana dai Allah ya bani ke, sannan dan Allah idan kika dawo ki bani dama ayi maganar aurenmu dan na kosa naganni dake a matsayin mata da miji Myluv."


Murmushi nayi sannan nace. "Allah yasa.".... "Amin ya Allah." nan muka kara gaisawa naba Dejja wayarta sannan na tashi na dauko mana abinci muka fara ci, ji nayi wayata tana ringing dauka nayi sai naga number din Dr Umar ce, ƙin dauka nayi na cigaba da cin abincina, shi kuma bai fasa kira ba, kallona Dejja tayi sannan tace. "Wa yake kiranki haka kuma Aunty."? Taɓe baki nayi sannan nace. "Dr ne wallahi ." murmushi tayi sannan tace. "Bawan Allah, wallahi shima yana sonki sosai Aunty Auta, karki so kiji yanda Baby yake gayaman son da yake maki, ni kuma naga kinfi dacewa da Uncle Aminu wallahi saboda shi Uncle Aminu baya da mata shi kuwa Dr Umar yana da mata duka duka basuyi two years da aure ba fa, amman ki dauka kiji abunda zaice maki pls."


Dauka nayi kafin nayi magana naji yace. "Matata fito gani nan a bakin gate dinku pls." kallon Dejja nayi sannan nace mashi. "Amman kuma Dr... "Please ineed to see you pls, kuma Seriou magana nike son yi dake Mywife." cewa nayi." ok gani nan zuwa." na kashe wayar, kallona Dejja tayi sannan tace. "Wai zuwa yayi ba tare da ya tambayi izininki ba."? Ɗaga mata kai nayi sannan nace. "Aikuwa kinga muna cikin waya naji yayi rejecting ashe zuwa zaiyi bari na gama cin abincin sai naje ko."? Ɗaga man kai kawai tayi sannan muka cigaba da cin abincinmu muna gama wa na shiga wanka na shirya sannan na tafi wajenshi.



Ina fitowa na kirashi dan naji yana ina, dan bansan motarshi ba balle na tafi wajen, wani waje ya gaya man yana can cikin black mota, gaka naje ina zuwa ya fito da yake wajen ba mutane sosai dan mutanan wajen basu wace ukku ba, shiyasa ya fito dan bai zama dole ace sun sanshi ba, tunda ya fito ya zubaman ido yana kallana sai kace bai sanni ba, dauke kaina kasa nayi sannan nace. "Ina wuni."? Iska ya furzar a bakinshi sannan yace. "Lafiya lau Matata, kinyi kyau sosai kamar na saceki na gudu fa." Murmushi nayi sannan nace. "Ina godiya sosai." shiru mukayi na wani dan lokaci sannan yace. "Na kasa hakuri Khadija, sannan kunnena basu iya daukar maganarki ta waya idan ba kallon idonki nayi ba, nasan nafi fahimta ta haka ma, Khadija inasonki sosai bai kamata ace ba zaki anshi tayin soyayya ta ba har sai kinyi tunani ba, nasa zuciyarki zata baki result a kan soyayyata kuma nasan ta baki ansarce kawai ta gagari a gaya man ita why Khadija."?


Murmushi nayi dan mamaki ma ya bani dan ni zuciya ta bata bani wani result ba akanshi, kallonshi nayi sannan na dauke kai nace. "Dr please kayi hakuri na... ''Nayi hakuri fa kakace Khadija? Kina nufin ban samu waje a zuciyarki ba? Khadija kinsan ko mai ake kira da so? Kinsan irin son da nike maki kuwa Khadija."!? Yayi man questions din cikin wani yanayi dan idanuwanshi cike suke da hawaye gani nayi hawaye sunabin fuskarshi, da sauri na girgiza mashi kai nayi sannann nace.





"Ba haka nike nufi ba Dr, ina nufin da ka daure ka barni dai nayi tunanin sai naga kamar haka zaifi."





Murmushi yayi sannan yace. "Khadija ina jin tsoro, na fahimci baki sona Khadija kuma ni ina sonki Khadija dan Allah ki daure ki aureni koda kuwa baki sona Khadija zanyi hakuri na zauna dake a haka, amman wallahi kika aure wani ba ni ba ina iya mutuwa Khadija, wallahi baki dace da kowa ba sai ni Khadija, please Khadija karki gujeni ki soni dan Allah." ya ida maganar yana hawaye kamar wani karamin yaro, kallonshi nayi sannan nace....




Share
Comment
And
Vote





*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 43⏩44


"Dan Allah Dr kabar kukan nan, naji Allah ya tabbatar mana da alkhari." Share hawaye yayi, yana murmushi yace "hakan na nufin kin yarda da soyayyata kenan Matata."? Murmushi nima nayi sannan nace "eh Dr na yarda da soyayyarka, amman ba hakan na nufin zan aureka ba, dan ba kai ɗaya kake neman aurena ba maganar gaskiya sai dai ina fatan Allah ya zaɓaman wanda yake alkhari garani."


Murmushi yayi sannan yace "insha Allah nine alkhari ma a gareki sannan kuma nine mijinki Khadija." nima murmushi nayi sannan nace "Allah yasa, ni zan koma ciki idan ka bani dama." murmushi yayi sanann yace "ba dan naso ba, sai dai ina kishi a ganki a nan wajen ana kalle man kai, dan haka ki koma ciki zamuyi waya."




''Ok." kawai nace sannan na dawo hostel, kwanciya nayi dan na gaji sosai yau din nan.


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya soyayya muke yi da mutane biyu Aminu da Dr kuma ko wannan yana nuna man irin nashi salon so, ko wane soyayya yake nuna man iyakar iyawarshi, haka har muka fara exams, kuma Allhmdulh dan karatu muke ba kama hannun yaro kuma muna ganin cigaba a wajen karatun dan ina cikin masu kokarin depertment dinmu ba laifi.



Yau bamu da exams na samu interval, amman Dejja tanayi ita bata kai da samu ba, zaune nike ina karatu ji nayi karatun baki ɗaya baya shiga, kallon Dejja nayi sannan nace "kinga bari na dan fita nayi yawo cikin school na dan miƙe kafafuna hakan, dan karatun ji nike baya shiga ko kadan."



Murmushi tayi sannan tace "shikenan Aunty Auta ai jiki da jini yana bukatar hutu, kuma kinga baki da exams sai tuesday dan haka kin dan huta yau sai ki cigaba da karatunki saturday kinga ai kinyi refreshing din brain dinki ko."?




Ɗaga mata kai nayi sannan na shirya na dauko kudi ko da ina bukatar cin wani abu sai na siya, tunda na fito nike tafiyata cikin natsuwa da kwanciyar hankali dan yanzun ba abunda yake damuna na manta da duk wata damuwata, kullun addu'a ta Allah ya zaɓaaman wanda yafi zama alkhari a tsakanin Aminu da Dr, dan kuwa su duka ina son kowa, kuma ina bukatar kasancewa da duk wanda Allah ya zaɓaman a matsayin miji.




Ina cikin tafiya naga wani wajen cin abinci, shiga nayi dan na saya chips sai kuma chocolate, shiga nayi nasa a kawo man sannan na samu sit din da ba kowa na zauna ina kallo, dan Arewa24 suna wani film mai bala'in kyau dan film din ya tafi da imani na sosai yayi man dadi, ji nayi anzauna gudun sit din da nike ban damu da wanda ta zauna ba, dan nasan wajen cin abinci ne ba dan ni ɗaya akayi shi ba, cigaba da latsa wayata nayi dan ban ɗago naga mai zama a bisa wanann kujera ba, nan aka kawoman abunda na bukata, ji nayi ance. "Nima a kawo man abunda aka kawo mata, sannan ka hado mana da samosa sai kuma pizza please kayi sauri karkayi late."



Take naji gabana ya faɗi dan ko a mafarki ba zan manta da wannan muryar ba, daure fuska nayi na cigaba da cin abunda na bukata a kawo man,amman inajin ciwo ƙasa zuciyata hakuri kawai nike ina nuna juriya dan bansan ya gane halin da nike ciki kan jin muryarshi da naji duk da ban kalle fuskarshi ba, dan bani son ganin ɓakar fuskar nan tashi saboda na tsaneshi kuma bani kaunarshi, take nayi nadamar fitowata da na sani kwanciya nayi bacci da zaifi man dadi, akan jinwannan muryar da naji, tusa abincin kawai nike a baki ba dan dadi ba ji nayi ance "sannu My life, yanzun ni zaki gani ki nuna kamar baki sanni ba? Ashe daman soyayyar karya kake man ban sani ba? Daman duk soyayar da kike cewa kina man karya ce Khadija? Kha.... Tas! Na wanke shi da mari baki ɗaya hankali kowa ya dawo wajenmu, ban damu ba dan raina ya ɓaci kallonshi nayi cikin nuna tsana nace "wallahi kaci darajar nayi ma Dejja alkwarin idan na sake ganinka ba zan maka komai ba, wallahi Nurandeen da yau sai ka baƙunci lahira a matsayin sabuwar gawa, na tsaneka ban kaunarka na tsani duk wani mai sonka wallahi ko Nurandeen, kuma bari kaji daga yau karka sake gigin yi man magana idan ka ganni fatan ka gane ko Malam."?



Murmushi yayi yana sosa wajen da na mareshi, kallona yayi ido cikin ido sannan yace. "Wallahi ni kuma yanzun na fara sonki, kuma ba zan daina sonki ba wallahi Khadija sannan kuma kisa a ranki wallahi nine mijinki ba wani ba, duk abinda kike ciki ina sane dake da duk wani makaryacin masoyinki duk akan idona kuke komai, sai dai ki sani duk cikinsu baki da wani miji bayan ni Nurandeen Abubakar dan haka tun wuri ki dawo cikin hankalinki wallahi Mylife baki da miji bayan ni, na barki lafiya."



Yana gama fadin haka ya tafiyarshi ya barni tsaye da tunanin maganarshi, daukar wayata nayi nima na taho , ina shigowa naga Dejja tana karatu zama nayi na buga abun tagumi dan na rasa abunda yake man dadi, kallona tayi sannan tace "lafiya naganki haka."!? Cikin tsoro tayi man tambayar, ban boye mata ba na gaya mata duk abunda ya faru a wajen cin abincin, Murmushi tayi sannan tace. "Rabu dashi Aunty Auta, ta Allah ba tashi ba ki kwantar da hankalinki karkisa wannan a rai har ya kawo maki matsala a karatunki."



Murmushi nayi kawai, nan ta samu har hankalina ya kwanta sannan na cigaba da hidimata haka har muka gama exams muka koma gida, anyi murnar ganinmu haka muka kwana muna labari da Aunty Asiya.


Muna zaune naji wayata ta ringing bakuwar number ce nagani, kallon su Dejja nayi suka yi man alama da na dauka naji ko waye, haka na dauka ji nayi ance...




Share
Comment
And
Vote





*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 45⏩46

*Jinjina gareku yan'uwana yan'kungiyata wato manazarta writers association ban san da wani irin baki zan yi maku godiya ba da kuka nuna man kauna sannan kuma kuka nunaman mahimmancina a cikin kungiyarmu hakan yayi man dadi sosai, ku sani ina sonku son fissabilillah Allah ya bar kauna da kuma zuminci Allah ya kara haɗa kaimu Amin ya Allah💘💓*


*ki sani da bazarki nike taka rawa a faɗin social media, kece kike haskaman gabana, sannn kum kike fidda ni a duhu, Auty Binta Umar Abbale ni bansan da wani baki zan maki jinjina ba sai dai nace Allah ya kara maki daukaka Amin🙏💘*


Kallon number din na tsaya yi, dan bansan number din ba amman sai na dauka na kauga a kunne nayi shiru bance komai ba, ji nayi ance "My life fatan kinje gida lafiya."?

Tsaki nayi sannan nayi rejecting din wayar, kallona Aunty Asiya tayi sannan tace “Khady lafiya naga kin chanza lokaci guda? Kuma an kiraki waya kiyi tsaki ka kashe, ko wani abu ya haɗaku da Aminu ne."?



Girgiza mata kai nayi sannan nace "Aa lafiya lau Aunty, kawai dai wayar bata amfani ne shiyasa kikaga na kashe." sai a lokacin Dejja ta dauko ta kalleni sannan kuma ta maida hankalinta wajen karatum novel din da takeyi a waya, matsowa Aunty Asiya tayi ta dafa ni sannan tace "gaya man waye ya kiraki waya a yanzun kika kashe bayan kin hadashi da tsaki? Shin kodai a akawai matsala baku gaya man ba? Dejja ajiye wayar nan ku gaya man abunda ke faruwa dan na lura Khady bata cikin natsuwarta sosai fa."


Murmushi Dejja tayi sannan tace "Aunty Asiya ba dole kiga bata cikin natsuwarta ba, Aunty Auta tasama kanta damuwa tunda wannan wawan Nurandeen ya dawo cikin rayuwa ta." dafe kirji Aunty Asiya tayi sannam tace. "Kamar ya Nurandeen ya dawo cikin rayuwa ta Dejja."!? Tayi question din cikin tsoro, dariya Dejja tayi sosai sannan tace "Aunty Asiya Nurandeen ya dawo wai yana son Aunty Auta kuma aurenta zaiyi, wai amman inji karyar shi ni na tabbata duniya bai maison Aunty Auta da aure sai mutun biyu, kuma cikinsu ni yanzun Dejja na kasa gane waye gwani dan ko wane yana iyakar bakin kokarinshi wajen nuna mata irin soyayar da yake yi mata"




Harararta Aunty tayi sannan tace "Daughter ban gane mutum biyu ba? Kina nufin akwai wanda yake neman yayi ma Aminu shiga sauri."? Ɗaga mata kai Dejja tayi sannan tace "tabbs Aunty Dr Umar yana nan ya matsa shima yana son Aunty Auta, kuma mun gaya mashi abunda ya faru da ita yace yaji kuma yana so a haka, kuma sosai yake nuna mata soyayya kamar ba gobe ni wallahi har tausayi yake bani watarana Aunty idan kikaji yanda yake sonta sai dai matsala ɗaya."


Iska Aunty Asiya ta furzar a bakin ta sannan tace. "Maiye matsalar Daughter."? Gyara zama Dejja tayi sannan tace. "Yana da mata fa Aunty kuma abun taƙaicin ko shekara uku baiyi da yin aure ba, sai dai har yanzun matarshi bata haihu ba ina tunanin bata haihuwa ko kuma lokacin haihuwar ne bai kai da yi ba."


Numfashi Aunty Asiya tayi sannan tace "dole Khady ki shiga damuwa, kuma dole kiji tausayin Dr Umar sai dai ni a gani na baki dace da ko wane miji ba inba Aminu ba, dan Aminu yafi sonki da gaske tsakani ga Allah kuma badan wata suhura ta jikinki ba yake sonki kawai Allah ya

Please Login or Register in order to submit comment