Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikinta mana." naso nayi gardama amman bani iya yi ma Yaya Jamilu gardama dama Yaya Aisha ce da sai nayi tunda nike bi mata daga ita sai ni, tashi nayi na shiga room din na, ina kallon sanda Yaya Amina ta leko taga mai nike sai akayi sa'a kwance ta tadda ni bisa gado na lumshe ido, ni kuma ina ganin haka nasan magana ta zasuyi amman basu sun naji, tasowa nayi na laɓe jikin kofa yanda zanji komai zasu ce.

Ji nayi Yaya Jamilu yana cewa. "Mama dan Allah muna ƙara baki hakuri akan abunda Auta ta aikata insha Allah ba zata kuma ba, sannan kuma dan Allah karki aura mata Alhaji Salahu ki bata dama ta fiddo wanda take so sai a daura mata, amman aurar da ita ga Salahu da kike niyar yi shine barazanar lalacewar Auta Mama." ji nayi hawaye sun zuboman wai ni za'a daura ma wannan tsohon mutumin wanda ko gaidashi baniyi a unguwa tunda na lura da yanda yake kallona idan na fito zani islamiya ko kuma boko, ina cikin yin hawaye na naji Mama tace. "Duk ki tashi ku bani waje wanda basu da hankali sannan kuma sani wallahi sai na aura mata shi nan da kwana goma dan haka ku fita ku bar man gida kafin raina ya ɓaci." tashi naga sunyi nayi sauri komawa bisa gadona na share hawaye dan ban san na nuna masu naji abunda suke cewa haka suka shigo suka kara dubani suka ce na ringa tsarki da ruwan zafi ina gasa jikina dan naji kwari sannan suka tafi gida, ai suna fita naji tashin motocinsu na tashe da kuka mai cin rai, aiko Mama ta shigo ta fara yi man fada akan nayi shiru na tashi na shiga wanka yau bako zanyi.

Ba yanda zanyi haka nayi duk abunda Mama tace harda bani kayan kwaliya nayi , haka yazo ya gama yi man surutanshi ya tafi, ni kuma na fara shirya kayana cikin wata yar'karamar jikka ina jiran dare yayi na tafi na barma Mama gidan tayi yanda zatayi da shi, idan taga ban nan ai sai ta samu wanda zata aura ma tsoho haka na kama hidimata kamar ba abunda ke damuna ana kiran mangariba Mama ta shiga daki danyi sallah ni kuma na dauki jikka da wayata da komai nawa harda sarƙar zinarina guda biyu wanda Mama da Yaya Jamilu suka saya man sai kudi masu dan yawa na fitowata, ina fitowa naga mai naped nace ya kaini tasar jibia.


👇👇👇👇👇👇👇

*SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!*

💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃


*Matso kiji ƴar uwa* 👂👂


*Shahararriyar marubuciyar nan wadda tayi ƙaurin suna gurin kasheku da dadaɗaɗan litttatafanta wato Aisha Umar Ibrahim (Real eeshow ) yauma gata tazo muku da wani shahararen book ɗinta wanda ta daɗe tana tanada muku shi cikin farashi mafi sauki wato 200 kacal.*


*Ga sunan book ɗin kamar haka*
👇

🌻 *BAR RAINA ALLURA*
*( Itama ƙarfe ce)*


*Domin neman ƙarin bayani kan wannan book zaku iya tuntuɓar mu a kan lambobinmu kamar haka* 👇
*08108362334 or 08135361133*


*Ƴar uwa karki bari a baki labari domin wannan salon na dabanne kamar yadda marubuciyar take ta daban.*😍😍😍😍


*karki bari kiyi missing ɗin wannan book ɗin hajiya.*



Share
Comment
And
Vote



*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________
https://chat.whatsapp.com/BS0N4RFqbe6LFqlXZZ9vxD
*Ga link nan ku shiga, kuma ku tabbatar zakuyi comment idan kun shigo dan gaskiya na daina yin posting a kowane group inba group dina ba zuwa wasu mararsa yawa dan haka duk mai son karanta a sanadin soyayyar minti kan lokaci cikin sauki ya shiga ga link nan, sannan kuma comment dole kuma kiyi dan Allah*

*magana ta biyu naji ana cewa zan maida soyayyar minti na kudi🤔, to ba haka bane soyayyar minti a kyauta nayi niyar baku shi, comment dinku shine bayanku idan kuma kuka daina comment kamar yanda kuke, to ba na kudi zai koma ba sai na na ajiye rubutun kunga sai mu hutu mu dukanmu ko🤗*

*Wannan page din nakine Hajiya Ruƙayya Allah ya kara daukaka da girma gami da lafiya mai amfani Amin*

*Gaisuwa ban girma gareki Fadeelah marubuciyar Rayuwar Husna, my Fadellah ina maki fatan alkhairy ta wajena*


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 11⏩12


Tafiya mai naped yake amman ni ba abunda nike idan ba kuka ba, sai zuciyata ta bani ko naje gidan Yaya Amina sai kuma naga kamar Mama taje ta dauko ni ta daura man aure da Salahu haka na kama saƙesaƙe ina hawaye dan ni yanzun so nike na kurma ihu na kama kuka ko naji saukin abunda nike ji a zuciya ta, amman ba halin yin haka haka muka shiga kofar guga har cikin tashar jibia sannan ya saukeni na bashi kudinshi ya bani chanjin, aiko nan aka fara zuwa aka anshi kayana akasa cikin boot din mota sannan na shiga, ɗari uku na bada kudin mota ba wani daɗewa nayi ba motar ta cika mu tashi zuwa garin jibia, tafiya mukayi mai dan nisa sannan muka iso magamar jibia nan nace zan sauka aiko aka saukeni na dauki kayana, a cikin wani novel na taɓa karanta sunan gari mai sunan HIRJI daga magama ake yanke hanya ake shiga cikin garin Hirji .


Garin Hirji gari na karuwar duk wata karuwa maiji da kanta ita karuwa ce to a garin Hirji take zaune, nima garin Hirji na nufa dan ban iya zama naga Mama tayi man auren dole kwara naje hirji nima na zama karuwa nayi zaman kaina ba kwalkwasin wani ba.


Haka na hau mashin na bashi naira dari ya kaini har hirji, nan fa akeyinta bansan ina zani ba dan bansan kowa ba balle na nufa gida gashi takwas na dare har yayi haka na kama yawo bansan inda zani ba, har tara da rabi ta tayi bansan kowa ba, tsoro ne ya fara kamani ganin yanda mutane suke kallona wasu har dariya suke man, wani kofar gida mai dakali na samu naje na zauna dan ni a niyata idan dare yayi sai na kwanta bisa dakalin kafin gobe tayi na cigaba da tafiya naga yanda Allah zaiyi dani.

~~~~~~~~~~~

A bangaren Mama kuwa bayan tana gama sallah ta fito koda taga bani cikin parlour tasa na shiga ɗakina ne dan ba huta shiyasa bata nemaini ba, sai ma shiga kitchen da tayi ta daman ruwan zafi da magunguna sannan ta dafa man indomie da kwai, kaima ruwan wankan tayi a toilet din dakinta sannan ta fito tana cewa. "Auta maza fito kije ki ƙara watsa ruwa sai ki zo kici abinci na dafa maki abunda kika fi so." jina shiru tayi bance komai ba tashi tayi ta nufo ɗakina tana cewa. "Haba Auta ya kamata ace kin fito kinyi wanann wankan fa, ko kina son indomien ta huce baki ce ba."? Idan shiga cikin ɗakin tayi bata ganni ba, zama tayi bisa gado tasa ko na shiga toilet ne, ganin shirun yayi yawa yasa Mama leƙa toilet din bata ga kowa ba, nan ta dawo ta fara kallon ɗakin nan taga bataga ƙaramar jikka ta ba, da gudu taje ta buɗe dirowata nan taga na kwashe kayana amman ba duka ba, dan karamin box din sakarkokina ta bude nan taga har zinaraina duk na kwashe, ba ta kawo komai a ranta bata, tasa guduwa nayi na tafi gidan Yaya Jamilu, nan ta fito ta kirashi waya bawan Allah yana zaune duk abun duniya yayi mashi yawa lokacin karfe takwas da rabi na dare Mama ta kirashi waya, cikin Mamaki ya dauki wayar Mama cewa yayi. "Hello Sallama Alaikum Mama lafiya kika kirani cikin dare."!? Cikin faɗa Mama ta fara magana. "Wato Jamilu ni zaka nunama iyakata ko? Shine kace ma Auta ta dawo gidanka ko? To komai kake ka tabatar da ka dawo man da ita gida wallahi tun kafin raina ya ɓaci." zufa ce ta keto ma Yaya sannan yace. "Wai Mama kina nufin Auta bata gida a yanzun haka."!? Cikin tsoro yayi tambayar dan hankalinshi bai kwanta ba, cewa Mama tayi. "Wato tambayata ma kake ko Jamilu? Bayan kun zigeta kun hure mata kunne har ta'iyya gudowa wajenku to wallahi ku sani aure ba fashi kuma yanzun nan nace ku dawo gida." cewa yayi. "Wallahi Mama ba gida na tazo ba, amman bari na kira su Fatima ko gidansu taje, taya zamuce ta gudu ta dawo gidanmu Mama? Sa kanta tayi bari na kirasu naji am.... "Yi man shiru Jamilu mudun baku maido man ita ba cikin daren nan ni kaɗai nasan hukuncin da zani yanke maku wallahi." nan ta kashe wayar tana faɗa, shiko Yaya waya ya kama kiran su Yaya yana tambayarsu ko nazo gidansu sai suce ban zo ba.

Lokacin karfe sha ɗaya yayi, haka bawan Allah Yaya Jamilu ya taso ya taho gidanmu yana shigowa Mama ta taso tana cewa. "Ina Autar take? Harni zakuyi ma haka Jamilu? Maiyasa kuke son ja'inja da nine."? Hawaye ne kawai yake yana kallon Mama sannan yace. "Mama Auta gudawa tayi kenan? Nidai bata zo gidana ba haka bataje gidansu Fatima ba Mama." cikin tsoro Mama tace. "Ban yarda ba Jamilu nasan tarbiyar da na Khadija ba guduwa tayi ba, tana gidan Amina ta boye ta wuce kaje gida gobe da safe naje na taho da ita." duk da Yaya ya yarda guduwa nayi dan har rantse mashi Yaya Amina tayi banje gidanta ba, dan kawai hankalin Mama ya kwanta yasa ya juya ya koma gida haka ya kwana zaune.


~~~~~~~~~~~~~~

Haka na zauna ina tunanin mafita dan kuwa nasa a raina ba zan sake komawa gida ba, wata matace tazo wucewa misalin sha biyun dare wajen gidan da nike zaune tazo zata buɗe kallona tayi sanann tace. "Kefa daga ina haka."? Tayi man tambayar tana tauna chigum kallo ɗaya nayi mata na gane karuwa ce dan daga yawonta ta dawo fuskarta tasha bilicin tadai kogu da duniya, shiru nayi ina hawaye murmushi tayi sannan tace. "Na gane matsalarki yan mata,taso shigo gida komai kenan gobe munyi magana, ai baki da gidan da zaki kwana ko."? Cikin sauri nace mata. "Eh wallahi ni bakuwa ce bansan kowa ba anan, dan Allah kiyi hakuri na zauna a gidanki zan ringa yi maki wanke wanke da shara." dariya tayi sannan tace. "Karki damu yanmata zaki yi amfani ne, nagaji sosai dan na kwaso gajiya shigo gobe munyi magana, kema daga gani yunwa kikeji ko."? Ɗaga mata kai kawai nayi sannan na dauki kaya nabi bayanta muka shiga gida, gida ne mai kyau wanda ake kira mu hadu parlour sai manyan kujeruta na zamani gaskiya gidanta ya hadu dan ba abunda babu a cikinshi na more rayuwa dan har mota naga a compound din gida guda biyu mamaki duk ya isheni, kallona tayi sannan tace. "Ba abun mamaki bane dan karuwa kamar ni na tara wannan dukiyar ba, abunda zaki tambaya ana shine taya akayi na zama karuwa shine abun tambayar ba mamakin tara dukiya ba yan'mata." nidai shiru nayi ban ce komai ba, sai ma murmushi da nayi mata kawai, nuna man wani ɗaki tayi tace shine nawa, sannan tace na shiga nayi wanka itama zatayi wanka sannan nazo muci abinci sai mu kwanta dan dare yayi kuma tana jin bacci.


Bayan mun fito kaza ce ta fiddo gasarshiyar kaza sai hollondia mai sanyi sosai, nan muka fara cin muna gama wa tace. "Kije ki kwanta ki huta dan naga alamun kina jin bacci sosai, nima baccin nikeji kuma na kwaso gajiya sosai yau, gobe munyi magana." tashi nayi ina ce mata. "To Aunty nagode sosai." itama tashi tayi tana tafiya tace. "Karki damu yi ma kaine." haka na shiga ɗakin da tace nawane mallakina na haye bisa gado nayi Addu'a na fara bacci hankalina kwance dan ko tunanin gida banyi ba dan na cire gida a rayuwa ta nasa ma raina bani da kowa bansan kowa ba sai ni kaɗa, dan nayi alkwarin yin rayuwar mai dadi wanda tafi ta gidanmu dadi."

*~~~~~~~~~~~~*

Washe gari da safe Yaya Jamilu yaje gidan yaya Amina zaune ya tadda ta bisa dining dinta ta buga uban tagumi dan tunda jiya yace mata ba'asan inda nike ba ta kasa kwanciyar hankali dan ko bacci sai dai ya saceta, tadda mijinta yayi sai lailashe yake yana bata baki, zaunawa Yaya yayi sannan yace. "Amina hakuri zamuyi haka kaddarar Auta take, sannan kuma ki sani komai ya faru laifin Mama ne abunda muke son mu nuna mata kenan amman ta kasa mahimfa." cikin kuka tace. "Yaya ni abun ne ya tsaya man a rai, ace wai Auta tasa ƙafa ta gudu ta barmu bata damu da wani hali zamu shiga ba, kuma wallahi sai nayi ƙarar Mama a court sai dai ta tsine man na gwanma ce amma... "Haba Amina ai idan rai ya ɓaci hankali naya gushewa, maiye ribarki dan kinka mahaifiyar ki a court eh."? Ji sukayi ance. "Wallahi Yaya idan har Amina bata kai Mama court ba to mu sai mun ƙaita court ko ya kika ce Aisha."? Yaya Fatima tayi maganar shigowarsu kenan ita da Yaya Aisha sunzo ne su tafi da Yaya Amina suka tadda suna magana da Yaya.


Tashi Yaya yayi yana cewa. "Idan har na isa da ku, kuma kun daukeni a matsayin ubanku ba Yaya ba to ina son ku kyale Mama ku barta da abunda ya isheta mana, kuna son a dunga zaginmu a unguwa ace mun kai mahaifiyar mu kotu."? Cikin kuka Yaya Fatima tace. "Amman Yaya bakaga abunda Mama tayi ba? Ba yanda bamuyi da ita ba akan ta rabu da Auta karda tayi mata auren dole amman tace sai tayi shikenan tunda ka hanamu amman ku taso muje mu gaya ma Baba Ali halin da ake ciki." tashi Yaya Amina tayi ta dauko gyalenta dan ko motarta kasa dauka tayi a motar Yaya Jamilu ta shiga ita kuma Yaya Fatima ta dauki Yaya Aisha kamar yanda suka zo suka wuce gidan Baba Ali, bayan sun gama gaisawa dashi suka gaya mashi halin da ake ciki, baice masu komai ba har suka gama sannan yace. "Abunda ai Hafsat din tayi kenan ai ko? Shikenan amman ku sani sai na kai ƙararta wajen sarki dan ba zan barta ba." Allah sarki ance ɗa da mahaifi sai Allah nan suka kama bashi hakuri, har Yaya Jamilu yace. "Baba hakuri shine dai dai, kuma nayi alkwarin zan sa a nemo man Khadija duk inda taje a cikin garin katsina, yanzun haka Mama bata yarda da Khadija ta gudu ba tace tana gidan Fatima yanzun zamuje mu gaya mata gaskiya ta gudu." haka suka kama bashi hakuri sannan suka fito sai gida wajen Mama dan su gaya mata gaskiyar magana Auta bata wajensu guduwa tayi...


*Na sake gaya maku ba zan maida litafi na kudi ba, masu biyoni ta private suna gayaman abunda sukaji ance sai dai ku sani kuna daina comment ni kuma zan daina posting din SANADIN SOYAYYAR MINTI wannan maganar a ajiye take babu fashi, sannan magana ta biyu ku daure ku ringa yin share dan wasu su amfana dan Allah ngd*

👇👇👇👇👇👇👇

*SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!*

💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃


*Matso kiji ƴar uwa* 👂👂


*Shahararriyar marubuciyar nan wadda tayi ƙaurin suna gurin kasheku da dadaɗaɗan litttatafanta wato Aisha Umar Ibrahim (Real eeshow ) yauma gata tazo muku da wani shahararen book ɗinta wanda ta daɗe tana tanada muku shi cikin farashi mafi sauki wato 200 kacal.*


*Ga sunan book ɗin kamar haka*
👇

🌻 *BAR RAINA ALLURA*
*( Itama ƙarfe ce)*


*Domin neman ƙarin bayani kan wannan book zaku iya tuntuɓar mu a kan lambobinmu kamar haka* 👇
*08108362334 or 08135361133*


*Ƴar uwa karki bari a baki labari domin wannan salon na dabanne kamar yadda marubuciyar take ta daban.*😍😍😍😍


*karki bari kiyi missing ɗin wannan book ɗin hajiya.*



Share
Comment
And
Vote







*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________
https://chat.whatsapp.com/BS0N4RFqbe6LFqlXZZ9vxD


*Wannan page din nakine Phatermarh kankia Allah ya kara daukaka da girma gami da lafiya mai amfani Amin*

*Gaisuwa ban girma gareki Deey musy, my Dejja, ki sani nayi missing dinki sosai da sosai Allah ya maido man dake duniya social media lafiya sannan ya baki sa'ar karatun da kikeyi, ina maki fatan alkhairy ta wajena*


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 13⏩14

Tunda suka shigo gida suka tadda Mama zaune tayi tagumi ga dukan alamu abun duniya duk ya bi ya isheta, da sauri Yaya Jamilu ya ida isa wajen Mama yana cire mata tagumi da tayi ɗaura kanshi yayi bisa cinyarta yana mata alamun lailashi, suma samun waje sukayi suka zauna duk sunyi shiru sun rasa abunda zakuce ma Mama, Yaya Fatima tayi karfin halin cewa. " Mama kin san dai mutum baya cika cikaken musulmi har sai yayi imani da kaddara mai kyau da marar kyau, itace ake kira da jarabawar rayuwa, Mama Allah kaɗai yasan irin kaddarar da Auta ta zano a rayuwarta kuma ba wanda ya isa ya wannan kaddarar, to mu mai zamuyi ma Auta Mama? Auta a halin yanzun tana bukatar Addu'armu muyi mata fatan faɗawa a hannun na gari." shiru tayi tana sauke numfashi dan halin da ta tadda Mama ta bata tausayi sosai kuma tabbas Mama tana son kula da ban magana mai dadi wanda zai sa hankalinta ya dan kwanta koda ba duka ba.


Kama hannunta Yaya Aisha tayi tana murzawa sannan tace. "Mama dan Allah ki yafe mana sannan ki yafe ma Auta, dan Auta ko tayi kuskure babba da tasa ƙafa ta gudu ta barmu ba tare da tayi wani tunani ba, kuma insha Allah zamu sa a nemo mana ita duk ind... "Aisha na yafe maku itama Khadija na yafe mata, amman ku sani ba wanda zaisa aje neman Khadija tunda ba wanda ya fidda sannan kuma ba'a aiketa ba, tabbas ba zanyi ma Khadija baki ba a halin sa take ciki sai dai nace Allah ya bata sa'a akan abunda tasa gaba nike na fita haƙinta a matsayin ta na marainiyar Allah ni kuma a matsayina na mahaifiyar ta mai son ganin farin cikinta, kuma da ta sani bata gudu ba da yau sai tayi dariya amman yanzun tunda har ta gudu ba baki ba watarana kuka zatayi da idanunta tana da nasani marar iyaka sai dai bani fatan Allah ya barni da rai na har wanann rana tazo, inalillahi wa'inna'alaihijirun Allah kana ganin halin da yarinyar ta samu ciki, ya Allah ka kareta daga sherin duk mai sheri, Allah karka ba wani damar kama ma ɗiya hannu da sunan yin fasiƙanci da ita koda kuwa ita ta kaimai kanta da kanta, ya Allah ka duba rayuwar marainiyarka wanda bata da uba sai uwa da yan'uwanta, Allah.... Kuka Mama ta fashe dashi kuka mai ciwo da ɗaci dan ita kaɗa tasan abunda takeji a zuciyarta.



Yaya Amina ce tayi karfin halin cewa. "Dan girman Allah kuyi hakuri addu'a dai zamu cigaba da yi kuma Mama kinsan jinin ya hau fa inji likita ya dace sausauta wannan damuwar, sannan Mama kika ce da yau zatayi dariya, wace dariya zatayi ko kin fasa aura mata Alhaji ne."? Girgiza kai Mama tayi sannan tace."Aa Amina ina bakata nayi mata aure, bayan Alhaji yazo zun gaisa da Auta sai na tafi nayi mashi rakiya zai koma gida, dan ita Auta suna gama magana ta tashi ta shiga ɗakinta, bayan mun gama ya tafi sai Aminu saurayin Auta yazo ya gaidani yace man ya shigo gari sannan yana ta kiran wayar Khadija a rufe shine yazo Allah yasa lafiya? Nan nace mashi yayi hakuri aure za'ayi mata take ya fara hawaye yana salati yana cewa maiye aibunshi da har Khadija ta fidda miji bata fidda shi ba, ni kuma tausayi ya bani sosai dan naga yana sonta sosai shine na gaya mashi abunda ya faru da ita da auren da zan mata da Alhaji ban boye mashi komai ba, amman abun mamaki maimakon yace bai aurenta sai yace man ai shi yana sonta a yanda take koda kuwa ta haifi cikin to zai aureta bayan ta gama shayar da abunda ta haifa sannan ya rike abunda ta haifa har yayi mashi aure, amman idan har na yarda a fasa auren da Alhaji shi zai aureta, amman sai nace mashi yaje ya dawo yau dan zanyi tunani, sannan ya shiga motarshi ya tafi bayan ya shigo da tsarabar da ya kawo mata, ni kuma ina dawo na tadda ta a parlour zaune, ban kai da yi mata maganar ba aka kira sallah na tashi na shiga dan yin sallah ina fitowa ban tadda ta a parlour ba sai na shiga kitchen na dafa mata abinci na haɗa mata ruwan wanka shigar da zanyi na tadda ta gudu, kuji abunda mukayi da Aminu."


Yaya Fatima ce tace. "Allah sarki nasha gaya ka Auta duk cikin samarinta Aminu yafi sonta amman sai tace ita bata son shi bai'iya soyayya ba, gashi kinga halllacin da yayi niyar yi mana Allah maido ta da hankalinta gida." "Amin ya Allah." suka ansa sannan suka ƙara kwantar ma Mama da hankali kowa ya wuce gida yana tunanin ida na tafi.


*~~~~~~~~~~~~~~*

_HIRJI_

Tun asuba wannan matar tazo ta tadani tace na tashi ankira sallah, sanann ta tafi ɗakinta tashi nayi alwalah nayi sallah da azkar na koma na kwanta sai karfe takwas na tashi nayi wanka na shirya na fito parlour ba kowa a parlourn haka yasa na zauna na kunna kallo dan bansan mai zanyi ba tunda komai na gidan a gyare yake, ban daɗe da zama ba ta shigo taci kwanliya tasa ƙananan kaya matsatso abun dai ba kyaun gani dan duk rabin nononta a waje yake, murmushi tayi man tana zama a kusa dani tace. "Barka da hutawa bakuwa ta." ɗukar da kaina ƙasa nayi nace mata. "Ina kwana Aunty."? Tashi tayi tana cewa."lafiya fatan kin tashi lafiya."? Cewa nayi "lafiya lau" na cigaba da kallona, ita kuma kitchen ta shiga ta dumamana kaza sai flask din ruwan zafi da madara haka muka ci muka koshi sannan na kwanshe kayan na maida kitchen na dawo na zauna, kallona tayi sanann tace. " Yan mata ya sunanki." ce mata nayi. "Khadija." murmushi tayi dan na lura ita mace ce mai yawan murmushi ce man tayi "suna mai dadi, to ni sunan Asiya." murmushi kawai nayi na cigaba da kallona ji nayi tace. "Khady mai ya kawo ki garin Hirji? Ko mamanki ya aikoki wani gida baki gane shi ba." girgiza kai nayi, sannan na share hawayen da suka zuboman nace "Aa kawai nadawo nan ne da zama." ji nayi ta rungumo ni jikinta tana lailashi sannan tace. "Karki damu nima haka naji llokacin da baro gidanmu, amman daga baya kuma sai na dadashe gashi har na yi dukiya, na manta da kowa nawa ina rayuwata yanda nike so, shin ban burgeki ba Khady."? Murmushi nayi na fidda jikina daga jikinta nace "kin burgeni mana."abun mamaki ƙara matsowa tayi a jikina tana cewa. "Kina da kyau kuma kina da abunda akeso a jikinki, amman kinsan mai."?


"Aa" nace mata kawai, dariya tayi sannan tace. "Bakiyi kama da wanda zaki sakarma namiji jiki yana mora sannan ya baki yan-kuɗaɗe wanda bazasu isheki ba, kin ganni nan tunda na fito duniya ban taɓa haɗa kwanciya da wani ƙato ba sai dai mace yar'uwata duk wannan kudin danayi ta haka na samaisu, idan zaki iya sai na koya maki kafin na fara haɗaki da manyan mata yanda zakiyi kudi kema." shiru nayi bance komai ba, ji nayi hannunta na yawo a cikin bireziya ta, da sauri na ɗago kai na kalleta sai naga ta ƙasheman ido tace. "Ki daba kai kawai Khadija zakiji dadi sannan kuma zakiyi kudi sosai. "Ɗaga mata kai kawai nayi sannan nace "ni bansan nayi kudi, sanann bansan ki haɗani da kowa ki barni kawai ina yi maki aiki ni haka ma ya isheni, amman banda niyar sake wani sabon Allah na samu na roki Allah ya yafeman wanda nayi a baya, Auntyna dan Allah karki bani gudumuwa wajen ida lalacewar rayuwata ki tausayaman wallahi zanyi maki aiki ko wani iri idan har na wahala ne."


Murmushi tayi sannan tace. "Ba zan matsa maki ba Khadija, nayi alkwarin ba zan matsama

Please Login or Register in order to submit comment