Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai tayi da kanta"

Lebenshi ya sawa babyn abaki ya fara jijjigata yana rarrashinta har tayi shiru, shidai tunda babyn nan tazo duniya yake kallonta domin komai nata irin nashine, yanzun ma anyi mata ado cikin blue din kaya riga da wando harda safa da hula tana nade cikin farin towel,

"Zo muje malam ne ya zo ganinku"

Hijab bahijja ta dauka suka fita zuwa sashen jabir inda malam yake, daukar yarinyar yayi yaita yi mata addu'a yana sakawa bahijja albarka.

Ana saura daya suna mai lalle tazo tayiwa bahijja hadadden kunshi baki da ja sannan aka yi mata kitso kananu three step mai 7,7,shi kam jabir lokacin yana can yana yi musu shirye shiryen walimar da za agudanar ranar sunan, al'amin kam koda wanne lokaci yana nanuke da yar jaririyar kamar zai hadiyeta.

Sai dare sannan jabir ya samu ya shigo gidan, part dinshi yaje ya kira ummu ta hada mishi ruwan wanka ta gabatar mishi da abinci yaci sannan ya kira bahijja,

Yana bakin gadonshi azaune lokacin ummu ta tafi bahijja ta shigo tana sanye da blue din t shirt da bakin skirt na jeans, hannunta dauke da jaririyar,

Kallonta jabir ya tsaya yi ganin yadda tayi kyau, gashi tasha kunshi da kitso, babyn ya karba yana shafar hannun bahijja,

"Kunshin nan yayi kyau binti"

"Nagode abbu" tafada cikin fara'a,

Jikinshi ya jata yahada ta da nashi yaci gaba da shafar kitson kanta da kunshin dake hannunta,

"Binti har yau baki tambayi sunan babynki ba"

"To ai abbu kai nake jira ka fada min"

Murmushi yayi yakama jelar kitsonta guda daya, "sunanta _Bahijja_ mai sunanki kika haifa"

Ya rada mata acikin kunnenta, dago da kanta tayi ta kalleshi "dagaske abbu?"

Sai da yayi kissing din hannunta sannan yabata amsa "dagaske binti, yanzu me zaki kirata dashi?"

"Abbu ni dama imtisal zan nace mata"

"Imtisal? Binti kin san ma'anar imtisal din?"

Girgiza kai tayi alamun a'a,

"To imtisal yana nufin kwatance kwatance ko misalce misalce, kina son arinka kwatanta abubuwa akan yarki?"

Nanma kai ta girgiza "indai hakane to ki hakura da kiranta da wannan sunan, nidama a niyyata mu kirata da *_TASLEEM_* sunan tasleem sunane mai kyau domin yana nufin wanda ya mika wuya, kinga idan kin sake haihuwa idan namiji ne sai mu kirashi da aslam ko?"

Murmushi tayi batare da tayi magana ba,yan yatsunta ya kama yafara ja yana murzasu ahankali,

"Binti kisani yanzu wani nauyi yahau kanki, wannan yarinyar da kika haifa wata amana ce Allah ya baki dan haka ki kula mutuka wurin ganin rayuwarta ta inganta, yanzu lokaci yayi wanda zaki san irin abubuwan da zaki runka yi agaban yarki domin idan ta tashi dake zata yi koyi, duk wata dabi'a taki to ita yarki zata dauka dan haka sai kinyi takatsan tsan sosai wurin sanin irin maganganun da zaki rinka furtawa idan ranki ya baci da kuma idan kina cikin halin farin ciki, sannan ki yawaita yi mata addu'a kan Allah ya shiryar da ita yasa mata imani acikin zuciyarta domin hakkin iyaye ne yiwa yayansu addu'a, yanzu gobe za ayi mata aski da safe"

Baki bahijja ta zumbura "nidai ba za ayi mata aski ba abbu"

Kanta ya shafa yana murmushi "binti yin hakan sauke wani hakkine da ya rataya awuyanmu, annabi yace hakkin yaya akan iyayensu sun hadar da yi musu addu'a tun suna ciki, idan aka haifesu kuma to hakki nafarko shine yi musu kiran salla a kunnensu sannan ayi musu huduba da suna mai kyau domin suna yana da tasiri sosai akan mutum amma ku matan yanzu kowanne suna kiran yaranku kuke dashi indai yayi muku dadi,

to tsaya kiji wani mutum yazo ya samu manzon Allah duk kayan mutumin a yayyage da alamun wahala da tsanani atare dashi, sai annabi ya tambayeshi sunanshi sai ya fada sai annabi yace dole ne kasha wahala arayuwa domin fassarar sunanka tana nufin matalauci, marar arzuki mai shan wahala, dan haka yanzu zaka canja suna ka koma wani domin suna yana da mutukar tasiri ga mutum, to kinga indai hakane to dole ku rinka sanin ma'anar suna kafin ku sakawa yaro, sai abu nagaba shine bawa yaro zam zam da dabino ko zuma lokacin da aka haifeshi wannan ma sunna ce,

sannan ranar suna ana son ayiwa jariri ko jaririya aski idan angama za abayar da sadaka kwatankwacin nauyin gashin da aka aske, hakika yin aski itama wata sunnarce amma mata dayawa bakwa son ayi wa yaranku wannan askin indai matane to wannan gashin datti ne, daudar mahaifa ce asketa shine mafi a'ala,

sai hakki nagaba shine yankawa jariri rago idan namiji ne rago biyu idan kuma macece rago daya wannan shine yazo abisa koyarwar manzon Allah amma babu laifi ga wadanda suke da wadata su yanka fiyeda haka, abu nagaba acikin hakkin yara akan iyayensu shine basu tarbiya da kula da tarbiyarsu tun suna cikin tsumma har kawo lokacin da zasu girma su mallaki hankalin kansu, ya kamata iyaye su rinka koyar da yaransu saukakan kalmomi tun suna kanana irinsu alhamdulillah, bisimillahir rahamanur rahim, masha Allah, astagfurullah,

sannan ki sani duk abinda kike yi to yaronki yana lura dake kuma dake zaiyi koyi a dukkan al'amuransa idan ya tashi zai tashine da dabi'unki yanda kike reacting idan ranki ya baci, yanda kike reacting idan abin farin ciki ya sameki da dukkan abubuwan da kikeyi agaban idonshi shiyasa idan ranki ya baci to anfi son kiyi addu'a idan abin farin cikine ya samu nanma kiyi addu'a sai yaronki yataso cikin tarbiya mai kyau.

Sannan alokacin da yaro ya fara tasowa to yana dakyau iyaye su jashi ajiki su bashi kulawa su sakar masa fuska su rinka zama tare dashi suna tattaunawa suna sanar dashi hakkin Allah akanshi da kuma tsoratar dashi da azabar Allah to irin hakane zakiga ko yaro yataso to zai tasone da shakuwa mai karfi tsakaninsa da iyayensa sannan baya iya sanar da kowa damuwarsa sai iyayensa amma indai bamu ja yayanmu ajiki ba to maimakon su sanar damu sai dai suje su sanar da wasu awaje ko su sanar da kawayensu saboda mu suna jin kunyar fada mana bayan kuma iyaye su suka fi cancanta da zama aminan yayansu na kut da kut domin babu mai rufawa da asirinsa sama da iyaye, ke kanki shaidace akaina nida al'amin nadaukeshi tamkar wani abokina shiyasa ya taso bashida wasu abokai sai ni tun yana yaro nakan zaunar dashi nayi wasa dashi muci abinci tare muje salla tare shiyasa ya taso da dukkanin irin halayena da dabi'una sannan baya iya boyemin damuwarsa ko sirrinsa, ko mafarki al'amin yayi sai ya fada min har takai akwai lokacin da nasanar dashi cewa zaiyi mafarki, mafarkin balaga nafada masa cewar duk lokacin da yayi wannan mafarkin to ya girma ya zama cikakken namiji wanda zai iya yiwa mace abinda zata haihu kuma yanzu anbude masa littafin rubuta ayyukansa na alkairi da sharri nayi masa nasihohi masu ratsa jiki, to haka ake son iyaye su zama domin su kansu yayan suna samun sassaukar rayuwa"

Gaba daya jikin bahijja yagama yin sanyi, "nagode abbu Allah yasaka maka da alkairi yayi maka sakamako da gidan aljanna"

Jaririyar ta karba ta tashi zata fita idonta taf da kwalla, bin bayanta jabir yayi ya rakata har kofar falonta sannan ya juya ya koma sashensa,

Koda bahijja ta kwanta bacci sai takasa tanata tunanin maganganun da jabir ya sanar da ita lallai indai hakane to tarbiyar yara is not easy sai dai ahada da addu'a.

Washe gari aka radawa yarinya suna bahijja tasleem, tuni mai jego da baby sun shirya cikin kaya na alfarma, anyi girke girke da toye toye danma jabir ya hana taron suna yace walima kawai za aje ayi a central mosque nacikin garin,

Karfe uku nidai ummi A'isha muka bazama nida aminiyata *Cwt Kausar Luv* muka nufi inda za agudanar da walimar abakin gate muka ci karo da bestynah *Phertymah Xarah* itada kawayenta Sadiya berry da Miss Aysha, nan muka rankaya zuwa ciki, yanda wurin ya cika dam da al'umma yasa bana iya hango kowa ganin haka nai ta maza nakutsa ciki nan nayi arangama da kawata *Khadija Sidi* gilashinta na ara nasa a idanuna take nafara hango mutane radau nan naga marubuta kamar dansu aka shirya walimar, gefena nadama nafara dubawa nan na hango Lubabatu mai Tafsiri itada Benaxir Omar sai handamar dambu suke, gefensu kuma Maman Shakur ce itada bestynta kuma kawata Humaira sukuma sunata shan kunun aya kowaccensu ta rike roba hurhudu, jan hannun Kausar da pherty nayi muka kara gaba tsayawa nayi ina kallon ikon Allah domin Jidda Aliyu na hango itada Rash Kardam sai wawar alala da dambu suke gasu Anka da Ummu abrar agefensu sukuma suna shan zobo can bayansu kuma S A Aziz ce da stylish bch da zeebeels, da ummu adnan da Aneeluv, ga Anisa didi da Ummu sabreena da baby Lilmeerahcute da khadija chafe sai faman daukar selfie suke ana son asamu na dorawa akan dp,

Bayana na waiwaya nan na hango kannena su Mimi bee da Autar hajiya da Afra mai yar bincike da Futhahatul khair da Kdeey yan matan junior sunsha jar atamfa iri daya mai hoton jaririyar ajiki "ohh wadannan yara da shisshigi kuke ko a ina kuka samo wannan atamfar" nafada azuciyata na kara gaba domin nan nabar su cwt Kausar da besty pherty domin su samar mana take away saboda kar mu koma gida a zero,

Wurin da nahango kawayena na nufa Fiddausi Sodangi itace agaba sai kwasar dambu take duk ta bata fuskarta da maiko ga takwarorina zagaye da ita suna hanbadar jalop A'isha Dansabo da A'isha A Gambo da A'isha Munay da Aisha chuchun gaye ko waccensu ta ajiye mayafinta agefe, daga bayansu kuma Xarah BB ce da takwararta Pherty BB da Teemah Cool sai Hafsa Bunza su dinma ba abarsu abaya ba wurin wawason dambu da lemon kwalba, "yaufa an samu na bati dole ayi cin keta" nafada nawucesu domin basu ganni ba kasancewar idonsu yana kan kwanon da suke wawaso,gaba dasu kadan na hango dotar ubbe da Jidda samusa,da E'eeshmal da amrah ga billy a giro sai wawaso suke yi adaron shinkafa duk kayansu ya baci da maiko,karawa gaba nayi ina dariya har nazo kujerar karshe nan naga ummi adnan da Qurratul ayn da basma erlele sun zage sun takarkace sai zukar kunun gyada suke dukkaninsu hankalinsu yana kan kular kunun dake gabansu gashi duk sun diddisa kunun ajikin kayansu, "masha Allah" nace na nemi wuri na zauna ina zare idanu.

Bayan anci ansha anyi kat ne mai jego bahijja ta shigo taci gayu cikin wani orange colour din leshi tasha katon mayafi tana rikeda jaririyarta tasleem wacce tasha ado cikin riga da skirt yan kanti jajaye masha Allah jaririya kam katuwa ce,

Malamar da zatayi wa'azi ce ta shigo wato malama safiyya Ummu Abdoul, anan ta gabatarwa da mata lecture mai taken *Tarbiyyar yara a musulunci* malamar tayi namijin kokari mutuka wurin fadakar da mata yanda ya kamata su kula da tarbiyar yaransu tun daga haihuwa har zuwa girmansu da lokacin da ya kamata afara raba musu makwanci,

Walimar ta kayatar mutuka amma duk nacin masu naci basu samu ganin jabir ba domin baizo wurin ba yana can shima yana tasa hidimar.

Karfe 6 daidai aka tashi daga walimar kowa ya kama gabansa, su bahijja na komawa gida tayi wanka da ruwa mai zafi ta fito daure da towel yayinda anty Bilkisu tana zaune tana yiwa tasleem wanka, ko jabir bata nema ba tasaka rigar baccinta ta kwanta nan bacci ya dauketa,

Jinta shiru da jabir yayi yasashi binta dakinta bacci ya sameta tanayi ga tasleem agefenta ta kunna musu air condition,

"Binti angaji kenan" yafada ahankali bayan yayi musu kiss ita da babyn akumatu, a.c din ya kashe musu ya fita zuwa part dinshi.

Haka bahijja taci gaba da rainon jaririyarta gashi anty Bilkisu ta dage wurin shiryata domin gabaruwa ta samo mata take tafasa mata tana zama aciki ga wani hadadden tsumi na sassaken baure wanda ake dafashi da kayan kamshi irinsu citta da kanumfari da zuma da ta dage wurin hada mata, daga bahijjan har babyn duk sunyi bulbul dasu sunyi kyau gwanin sha'awa, ranar da suka yi 40 aranar anty Bilkisu tatafi bayan jabir ya hada mata goma ta arziki.

Nan fa jabir da bahijja aka bude sabon babin soyayya domin tattarasu yayi ita da tasleem zuwa dakinshi inda ya basu kulawa ta musamman, har tafita daga girki kullum jabir cikin tattalinsu yake dama kuma da rana tasleem din hannun al'amin da ummunshi take wuni.

Haka rayuwa taci gaba taci gaba da gudana agaresu cikin jin dadi, yanzu watan tasleem biyu, misalin karfe 2 nadare tasleem sai kuka take tsalawa bahijja domin yan kwanakin kukan dare take yi,

Tana zaune ta rasa yadda zata yi mata gashi ba ranar girkinta bane domin idan ranar girkinta ne baccinta takesha tabar jabir da raino, jabir ne ya shigo yana sanye da kayan bacci,

"Meya sameta" ya tambayeta yana kokarin daukar tasleem,

"Abbu haka kawai rigima dai" tafada kamar tayi kuka,

Daukar tasleem yayi yafara jijjigata yana lallashinta sanin yagama da hidimar ummu al'amin ya sashi fita da tasleem din zuwa bedroom dinsa, kwanciya yayi ya dorata asaman kirjinsa yana jijjigata ahaka suka yi bacci shi da ita, ita kam bahijja dama tun kafin jabir yafita daga dakinta ma tayi kwanciyarta amma tana jin soyayyarshi tana karuwa acikin jinin jikinta domin tasan jabir nadaban ne acikin maza saboda samun namiji wanda zai yi irin abinda jabir yake yi ba abune mai sauki ba.

Washe gari kuwa tunda jabir ya fita tasleem take yi mata kuka gashi jikinta yayi zafi dau, zama bahijja tayi tai tagumi tana kuka takasa aikata komai har la'asar tayi,

Dawowar jabir kenan ya shiga sashenta nan ya samesu suna kuka itada tasleem,

"Binti menene"

Tasleem din ta mika masa tana hawaye,

"Ina jin bata da lafiya tunda katafi take min kuka gashi babu abinda nayi agidan"

Jin jikin tasleem da zafi yasashi fita domin kaita asibiti sai alokacin bahijja tasamu tayi ayyukanta tashiga wanka tafito tayi kwalliya,

Tana daura dan kwalinta jabir ya shigo dauke da tasleem akafadarshi tana bacci,kwantar da ita yayi ya nufi bahijja,

"Binti zazzabi ke damunta da ciwon ciki amma dr ya dubata ya bata magani"

Tasowa tayi ta shiga jikinsa tana murmushi "sannu abbu mun gode"

Fuskarta ya lukuce "ba godiyarki nake bukata ba kulawarki nake bukata"

Kanta ta cusa akirjinsa "abbu ina jin tsoro"

"Name?"

"Ciki" tafada ahankali,

"Ai bazan baki yanzu ba sai kin yaye tasleem"

Bude baki tayi tana kallonshi da niyyar yin magana, bakinshi ya hada da nata ya dauketa zuwa dayan bedroom dinta yana cewa, "kin kusa ki dauki dawainiyata ma ke daya domin su al'amin nanda 3 weeks zasu koma.

Tana kwance ajikinshi tana ta faman zuba masa shagwaba,

"Abbu nidai ka samo min yar aiki wacce zata rinka yimin rainon tasleem, akwai wata Xarah ta iya raino sosai"

Sake rungumeta yayi sosai ajikinshi, "kiyi hakuri binti kiyi dukkan ayyukan gidanki da kanki sai Allah ya baki sakamako mai kyau"

Sake kankame juna suka yi suna dariya.



BAYAN SHEKARA 20

*

Wata mata na hango tana sanye da katon hijabi har kasa awani wawakeken fili wanda mata suka cikashi tana yi musu wa'azi, ta kwashe fiyeda awanni 3 tana yi musu wa'azin kafin ta kammala ta rufe da addu'a,

Wurin motarta ta nufa ta bude ta shiga tana murmushi akusa da wani saurayi ta zauna wanda kallo daya zaka yi masa ka gane jabir ne sak "dan autan abbu yau kai kadai ka taho"

Murmushi shima saurayin yayi "ammun yau ban samu yan rakiya ba duk sunki
rakoni sunce awurin abbu zasu zauna"

"Kace yau gidan namu acike yake da yan jikoki" tafada tana dariya,

"Ai kuwa dai ammun"

"Allah dai yayi muku albarka abdul halim" tace dashi tana murmushi, tafiya kadan ta sadasu da gidansu, nan suka shiga tun kafin tafito wasu kyawawan kananan yara kimanin su 10 suka taho suka rungumeta suna "jaddati oyoyo"

Rungumesu tayi suka shiga cikin falonta inda jabir ke zaune da wasu yaran yana koya musu alifun ba'un,

"Abbu yau haka gidan namu ya zama?"

Dagowa yayi ya kalleta "ga masu gyara gida nan sun zo yau"

Cikin dakinta ta wuce ta zauna tana hamdala acikin ranta domin hakika jabir ya zama *_WANI HASKE_* acikin rayuwarta domin ta sanadinshi duk danginta dake okene sunzo sun musulunta awurin jabir gashi yara 9 Allah ya azurtasu da samu ita dashi tun daga kan tasleem, abdullah, abdulrahman, abdulrahim, abdul hamid,abdul rashid, abdul gani, abdul malik sai dan autansu abdul halim,gashi yanzu harda jikoki suke dasu wurin su goma sha biyar,

Shigowar jabir ce ta katse mata tunanin da take yi,

"Yanmatan abbu ki shirya danki al'amin ya biya mana umarah"

Yafada yana zama akusa da ita,

"Allah saka masa da alkairi, shima Allah ya bashi masu yi masa" tafada idonta narai narai,

"Kar kiyi min kuka, nidai yanzu kulawa nake son kibani domin nakada wadancan jikokin naki zuwa gidan zoo suda uncle dinsu abdul halim"

Murmushi tayi ta kwantar da kanta ajikinshi "abbu baka gajiya dani, ban taba ganin sauyin fuska atattare dakai ba"

Hannunta ya kama ya rike cikin nasa,

"Binti duk auran da aka ginashi akarkashin koyarwar ma'aiki to haka yake kasancewa, shiyasa annabi yace maza su auri mace mai addini domin itace matar da kullum tana tsufa tana sake rike addininta, maimakon kaji tana fita daga ranka sai dai kaji tana sake shiga cikin ranka, sannan duk soyayyar da aka yita saboda Allah to tana dorewa"

Hannunshi ta matsa "nidai nayi sa'a, ina addu'a Allah yabarni dakai har lokacin da zan koma gareshi"

"Kizo muje mu kula da junanmu kidaina yi min maganar rabuwa"

Yace da ita gamida daukarta zuwa special room.


*ALHAMDULILLAH*

Anan nakawo karshen littafin wani haske ina addu'ar Allah yatara mu acikin ladan ya yafe mana kuskuren dake ciki, duk wacce ta karanta wani haske taji dadinshi to ta taimaka tayiwa ummi A'isha addu'a akan Allah ya biya mata bukatarta.


*SADAUKARWA*

Na sadaukar da wani haske gareki kawata *BAHIJJA BEBEELO* (marubuciyar D'a na kowane) dake da dukkan masoyan littafin wani haske, Allah ya raya miki yarinyarki iman, nagode kwarai da kaunarki agareni.


*TUKWICI NE*
agareki bestyna *PHERTYMAH XARAH* (marubuciyar littafin matar sadiq),Allah yakara dankon zumunci agaremu.

*DOMINKU NE*
Masoyana masu yi min fatan alkairi akoda yaushe.


*JINJINA GAREKI*

Uwar dakina *HAUWA M JABO* nagode da kulawarki.

*KINA RAINA*
Aminiyata mai share min kukana *CWT KAUSAR LUV*, hakika kinfi karfin kawa agareni, ke ta dabance awurina ina kaunarki kawata, Allah yabarmu tare,tabbas banda kamarki.


*FATAN ALKHAIRI*
Gareki tawan kawata *KHADIJA SIDI* nayaba miki sosai hakika ke ta musamman ce agareni.

Gaisuwa ta musamman gareku masoya yan uwana marubuta, ina addu'ar Allah ya kara muku basira da hazaka, yaci gaba da taimakonku acikin al'amuranku, ya kara muku baiwa mai amfani,ya baku lada aduk inda kuka yi daidai, ya yafe muku a inda kuka yi kuskure.

Gaisuwa mai dunbin yawa gareku masoya wadanda suke karanta rubutuna suna yimin fatan alkairi akoda yaushe, nagode muku sosai ina kaunarku mutuka kuma ina addu'ar Allah yabar zumuncin dake tsakaninmu, duk wanda yake kaunar ummi A'isha ko kuma yake kaunar rubutunta ko yaji tana burgeshi ko yaji yana sonta to UMMI A'ISHA loves you too, sai mun hadu acikin labari nagaba da yardar mai sama Rabbi Azimu.








DOCUMENT MADE BY SALMARH



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment