Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba gashi sai kamshine ke tashi, koda ya shiga cikin toilet dinma abin haka yake komai fes fes tsaf tsaf, cikin nishadi yayi wankanshi ya fito ya shirya ya fita lokacin an kira sallar magrib, hannunsa rikeda dabino yana ci ya sameta a falon har lokacin gugar take yi,

"Sir sannu" ta fada ahankali,

"Yawwa" shima ya fada ahankali tare da fita, bai dade da fita masallaci ba ta gama gugar kayan ta koma sashenta.


Sallar magrib kawai yayi ya dawo gida yasha ruwa, lokacin isha nayi ya koma masallaci, bashi ya dawo gidan ba sai wurin karfe 9,

Sashensa ya shiga ya yi wanka bayan ya dawo daga mosque, kayan bacci yasa maroon colour masu taushi, kamar kullum laptop dinshi ya bud'e ya shiga net ya fara amsa tambayoyin jama'a, yana nan zaune agefen gadonshi laptop din na ajiye akan cinyarshi goodness ta bude kofar dakin ta shigo, daga kai yayi ya kalleta tana sanye da kayan bacci doguwar riga mai rubi biyu iya gwiwarta light purple kanta sanye da hular roba baka, tana rike da karamin tea flask wanda ta zubo masa dafaffen shayin na'a na'a aciki,

"Weldon sir" tace dashi tareda karasawa gaban gadon ta ajiye masa tea flask din akan dan karamin stool dake ajiye agaban gadon,

Da mamakinsa sai yaga ta haye kan gadon tana cewa "sir aikin office ne kake yi har agida"

"Ba aikin office bane" ya bata amsa a takaice, pillow taja ta kwanta ta dora kanta akai tana mai fuskantar jabir wanda ya tsaida idonsa akan laptop din dake gabanshi lokaci lokaci kuma yana dan kurbar shayin dake ajiye agefenshi,

Fuskar nan tashi mai kyau ta zubawa ido tana kallo ko kiftawa bata yi, kamarsu daya sak da al'amin danshi sai dai shi al'amin din yafi shi hasken fata domin ummunshi ya dauko a haske amma baya ga haka komai na al'amin irin nashine,

"Oh my al'amin am missing you" tafada ahankali,

"Abbu bani aron wayarka" ta fada tana daga kwance, ahankali ya jiyo ya kalleta tareda maimaita sunan aranshi "abbu" yafada acikin zuciyarshi,

"Me zaki yi da wayata?" Ya tambayeta, "pls abbu i want to hear the voice of my lovely son al'amin" ta fada cikin shagwaba, daga kai yayi ya kalli agogo karfe _10_ saura yan mintuna,

"Yanzu al'amin yayi bacci amma gashi ki kira kiji" mika mata wayar yayi ta mika hannunta ta karba ta fara neman layin ummu al'amin din amma wayar akashe, ta dade tana kiran wayar amma bata samu ba dole ta hakura ta mika mishi,

Kallonsa tayi tace "abbu kayi min addu'a ina son zanyi bacci"

Dago kanshi yayi ya kalleta,

"Wacce irin addu'a?" Ya tambayeta tare da mayar da hankalinsa kan laptop dinshi,

"Irin wacce kayi min jiya, ban taba yin bacci cikin nutsuwa kamar wanda nayi jiya ba"

"Kawo hannuwanki inyi miki" ya fada ahankali, zaune ta tashi ta matsa kusa dashi ta hada hannuwanta wuri daya ta mika masa tafin hannuwan nata, addu'o'in kwanciya bacci ya karanto yana tofa mata acikin tafin hannunta har ya kammala ya dubeta,

"Ki shafe jikinki"

"Thank you abu al'amin" ta fada tana shafe jikinta kamar yadda yace, hakan data fada sai ta tuno masa da matarshi Salma wato ummu al'amin.

Kwanciya ta koma tayi tana kallon kyakkyawar fuskarshi har bacci ya dauketa, sai da ya kammala abinda yake yi sannan ya tashi yaje toilet ya dauro alwala yakoma inda ya keb'e domin gudanar da ibadarsa ya fara sallar nafila.

Can tsakar dare goodness ta farka daga bacci tafara dube dube domin taga gadon wayam babu jabir, acan gefe ta hangoshi yana salla, jijjiga kai tayi ta koma ta kwanta tana mai jinjina rikon addinin da jabir yake dashi, sai wurin _3_ ya hawo gadon ya kwanta har lokacin goodness idonta biyu tana kallonshi, addu'o'in kwanciya bacci yayi kafin ya kashe wutar dakin,

Minti 10 atsakani taja jikinta taje ta shiga jikin jabir kamar yadda tayi jiya, cikin barci ya rungumeta tareda k'ankameta ba tare da ya sani ba, tamkar zasu mayar da junansu cikin cikinsu haka suka yi.

K'arfe _5:30_ ya samu ya farka bakinsa dauke da salati,mamaki ne ya kamashi jin yadda shi da goodness suka makalkale junansu kamar wasu tif da taya, hannuwanshi yasa masu mutukar taushi ya janyeta daga jikinsa ya tashi ya shiga toilet, bin bayansa da kallo goodness tayi aranta tana mai burin inama zasu dawwama ahaka ita da jabir.


Tun kafin ya dawo daga masallaci ta koma sashenta tayi wanka ta shirya ta shiga kitchen ta hada abin karyawa ta dauka ta kaiwa jabir nashi sashensa sannan ta dawo dakinta tafara gyara kayan sawarta tana shisshiryasu cikin sif,

Stool din madubi ta dauko ta taka tahau dan ta dora wani akwatin kayanta asama, cikin tsautsaye ta goce ta fad'o, gefen kunkuminta sai da ya bugu da gadonta, tashi tayi kokarin yi amma ta kasa dan haka ta ci gaba da zama awurin har jabir yashigo yace mata ya tafi office.

Tunda ta buge agefen kunkumimta ta baya take tafiya dakyar tana dingishi, da haka ta samu tayi duk wasu ayyukanta har yamma tayi jabir ya dawo, ganinta tana yin dingishi ya sashi tambayarta abinda ya sameta, bata boye ba ta sanar dashi,

"Ok dauko Robb acikin dakina sai ki shafa awurin bayan kin gasa gun da ruwan zafi" ya fada yana kallonta,

"No abbu" ta fada tana mak'e kafadarta,

Bai sake cewa komai ba ya tashi yafita ya tafi salla sai da ya dawo yana zaune akan gado hannunsa kuma rikeda littafin _sahihul bukhari_ ta shigo tasha kayan baccinta doguwar riga fara sai faman kamshi take zubawa,

Kan gadon ta hau ta kwanta tana gyara hular kanta, mikewa jabir yayi ya ajiye littafin hannunsa akan drewar din gadon ya shiga toilet, ruwan zafi tafasasshe ya taro acikin karamin baho ya dauko towel karami wanda yake goge jikinshi dashi idan yayi wanka,

Tana kwance ta yi rub da ciki tana fuskantar bango yazo inda take,

"Oya tashi" yafada ahankali,

Tashi tayi babu musu ta juyo tana kallonsa ganinshi da kayan gashi ya sanyata mikewa da sauri domin guduwa, robar ruwan zafin ya ajiye ya yi sauron rikota babu zato ta fado jikinsa ta baya nan ya rungumeta baiyi wata wata ba ya dage rigar dake jikinta nan take farin pant din dake jikinta ya bayyana, da saninsa ya sake dage rigar domin yana son ganin kalar bra din da ta saka, itama fara ce sol,

"Hmmmm to match akayi kenan, komai white, that's good" ya fada acikin zuciyarshi, jin tana kokarin kwacewa daga rikon da yayi mata ne ya sanyashi dawowa daga duniyar tunanin da ya lula, towel din ya tsoma cikin ruwan zafi ya dauko shi yana tiriri gashi harda ruwan ajiki ya manna mata akan kunkuminta,

"Abbu, pls da zafi ka bari" ta fada arude, bai kulata ba ya sake tsoma towel din ya ciroshi ya dora mata akan wurin gashi idan ya dora baya daukewa har sai ya huce, haka yayi ta mata har sai da ya tabbatar gurin ya gasu sannan ya kyaleta,tashi tayi tana goge gumin da ya feso mata agoshinta dan azaba idonta kuma yayi rau rau tana son yin kwalla,

"Ungo Robb shafa awurin, ko ba zaki iya ba na shafa miki?" Ya fada yana bin lukuta lukutan cinyoyinta da kallo,

"No abbu zan iya" tafada cikin sauri tareda amsar Robb din, toilet ta shiga ta shafe wurin da Robb amma ba karamin dadi taji ba saboda har taji saukin ciwon da wurin yake yi mata,bude kofar toilet din tayi ta fita aranta tana jin dadin yadda jabir wani lokacin yake sakin jiki da ita har yayi mata wasu abubuwan masu kama da na masoya gashi yanzu ya sake shiga ranta sosai dalilin kwana da ta fara yi dashi a gado daya,

Yana zaune yana jona laptop dinshi a charge ta fito tana kawar da fuskarta, ta gefen ido ya dan kalleta yayi murmushi wanda shi kadai yasan yayishi, ya gane nufinta na shiga toilet wato dan kar yaga jikinta ne ya sanyata yin haka, bakinshi ya tabe aranshi yana cewa,

"Na nawa kuma? Jiki kam ai nagama gani yarinya sai dai ki kiyayi gaba kuma" idonshi ya lumshe ya tuno manyan cinyoyinta da ya gani dazu, juyawa yayi ya kalleta lokacin da take kokarin hawa kan gadon,

Gyara zamanshi yayi ya dauki laptop dinshi ya kunna ya dorata akan gadon ya fara lallatsawa,

"Abbu addu'a" ya jiyo muryar goodness tana fada masa cikin wani salo na daban,

Kamar yadda yayi mata jiya yau ma haka yayi mata ta shafa ta kwanta, amma kuma bacci yaki daukarta son jabir ne kawai ke azalzalar ruhinta, tana son amon muryarshi domin idan yana yin magana har ji take kamar dodon kunnenta zai suma da dadin muryarshi.

Fiyeda minti talatin ta shafe tana kallonshi yanata rubuce rubucenshi acikin laptop gashi ita kuma baccin yaki zuwar mata, tashi tayi zaune ta saisaita muryarta tace,

"Abbu kayi min labari, bacci yaki daukata yau" ta fada tareda jan wani dan guntun tsaki, kallonta ya dago yayi,

"Ni ban iya labaran duniya ba sai dai labarin da alqur'ani yazo dashi idan kina so sai in baki" ya bata amsa,

"Yes ina so" ta fada tana gyara pillow dinta domin kwanciya, laptop dinshi ya rufe ya ajiyeta agefe ya juyo yana kallonta.



_*Ummi A'isha*_πŸ‘ŒπŸ»


[9/21, 8:45 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE...!*



_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_


_71-75_


_*Wannan babin nakune kyauta wad'anda suka yi mafarkin wani haske adaren shekaran jiya da daren jiya, ina fata daren yau babu mafarkin wani haske,ina sonku fiye da yanda kuke son wani haske, masu mafarkin wani haske nagaisheku kyauta gashi kunada yawa balle na zayyano sunayenku,asha karatu lafiya.*_




~~~Laptop dinshi ya rufe ya ajiyeta agefe ya juyo yana kallonta, "kika ce kina so?"

Kai ta d'aga sannan ahankali tace "yes i like it"

Dan kishingida yayi yana mai fuskantarta, "zan fara da baki k'issar d'aya daga cikin annabawan da Allah ya aiko zuwa ga al'umma, yanzu ki zabi guda acikinsu sai na baki labarinsa ina nufin kissarshi"

"To ai ban sansu ba" ta fada tana shafa fuskarta da hannunta,

"Eh nasani amma zaki sansu yau, ki zaba acikin guda ukun nan, annabi Adam, annabi musa, annabi Yusuf,wanne kike son na baki k'issarsa aciki yanzu?"

Kallon fuskarsa tayi tana murmushi, "annabi Adam"

Gyara zama yayi ya fuskanceta sosai ya fara bata kissar annabi Adam tun daga halittarsa har zuwa kan halittar matarsa hauwa'u da zaman da suka yi a aljanna har zuwa kan lokacin da suka ci ganyen itaciyar da Allah ya hanesu,

Idanuwan goodness a lumshe suke ta nutsu tana sauraren sautin muryar jabir yana bata labari, yanda take jin labarin gani take kamar a tv take kallo gashi tamkar jabir zabo kalmomin da yake fada mata yake yi, labarin gaba daya ya tafi da ita, musamman ma daddadar muryar jabir da take sauraro,

"Zan barki haka sai gobe zan k'arasa miki" ya fada yana kallonta,

"No abbu kar kayi min haka, pls ina son jin abinda ya faru dasu bayan sunci ganyen itaciyar, pls abbu"

Dan murmushi yayi da dukkan alamu bukatarsa zata biya tunda gashi tana da interest akan k'issar da ya fara bata,

"Sanadiyyar cin wannan itaciyar da nana hauwa'u tayi shine mata suke yin jinin al'ada domin lokacin da ta hadiyi ganyen take jini ya fara fita daga jikinta, shine sauran mata suka yi gadonta suma suke zubar da wannan jinin lokaci zuwa lokaci, shi kuma annabi Adam bai hadiye ba, nan gaba daya sutturar dake jikinsu ta bar jikinsu, Allah ya sauko dasu daga cikin aljannah"

"Oh God" ta fada tareda dafa goshinta tana runtse idonta,

"Sun koma kuma?" Ta tambayeshi,

"Sun koma domin Allah mai yawan yafiya ne ga bayinsa"

Murmushin farin ciki tayi, "gaskiya abbu labarin nan da dadi, kai da waye ya baka shi?"

Kansa ya girgiza yana murmushi "Allah ne ya sanar damu acikin littafinsa mai tsarki, duk wannan labarin da na baki ba wani bane ya zauna ya shiryashi ko ya kirkireshi ba, no, abunda ya farune Allah ya sanar damu ta harshen annabinsa"

Kallonsa kawai take yi yanda yake furta maganganun daya bayan daya da dan mitsitsin bakinshi,

"Duk wani abu da kika sani na rayuwar duniya da rayuwar da za ayi bayan anbar duniya to duk alqur'ani ya sanar damu"


"Tunda hakane kullum zaka rinka bani labarin nima ina ji, sannan nima zan fada maka irin namu labarin wanda Bible yazo mana dashi"

Murmushi ya danyi mai kayatarwa wanda har sai da fararen hakoransa masu mutukar haske kamar farar takarda suka bayyana,

"Ashe kema kina da labari?"

Ya tambayeta,

"Yes, i have it, indai zaka ji zan baka"

Murmusawa ya sake yi yana kallonta, tana kwance ta rungume pillow sannan duk wadannan maganganun da suke yi idanuwanta a lumshe suke, amma aranta tunani take yi lallai tunda aka samu labari irin wannan acikin littafin musulmai to za asamu wasu labaran masu kayatarwa wadanda suka fi wannan.

"Nima ina so indai zaki fada min" ya bata amsa yana kallonta,

"Zan baka sai bayan ka bani wani gobe"

"Allah ya kaimu, yanzu dare yayi ki kwanta kiyi bacci nima bacci zanyi tunda yau kin rikeni kin hanani sallar dare"

Murmushi tayi bata ce komai ba ta juya ta gyara kwanciyarta, toilet ya tashi ya shiga ya dauro alwala ya fito yazo ya kwanta agefen gadon bayan ya gabatar da addu'o'insa, tana jinsa har ya gama ya kashe wutar dakin, kasa bacci tayi sai tunanin labarin da jabir ya bata take yi amma wannan abin mamaki da yawa yake yanzu wannan labarin dagaske ya faru? Ta tambayi kanta, tana nan kwance tana ta sharhin wannan labarin har bacci ya dauketa.

Asubar fari jabir ya tashi kamar jiya yau ma ganinta yayi kwance ajikinsa ta rungumeshi tana ta bacci, janyeta daga jikinshi yayi ya tashi ta shiga _bathroom_,masallaci ya tafi bashi ya dawo ba sai wurin 6:30,lokacin da ya dawo yana shiga bedroom dinshi ya hangota acikin kitchen tana aiki, kwanciya yayi ya dan mike domin jiya bai samu bacci da yawa ba.

Wunin ranar goodness ta yishi ne cikin doki domin alla alla take yi dare yayi su zauna da jabir domin ya bata labari, tunda wuwwuri tayi wanka ta shirya tasaka _sleeping dress_ dinta light brown colour, ta kinkimi abincin jabir ta nufi sashensa amma har lokacin bai dawo ba gashi wurin karfe 9,cike da damuwa ta ajiye kwanukan abincin ta juya ta koma sashenta, kallo ta kunna ta fara kallon wani american film mai suna _the chronicles of narniar_ tana kwance tana kallon har ta fara dan bacci sama sama daga karshe ma baccin ya dauketa gaba daya.

Karfe _10_ jabir ya dawo, sashensa yaje ya ci abinci yayi wanka ya sake sabon shiri cikin gajeren wando baki da yar t shirt fara mai gajeren hannu (su mal jabir an dawo samari), net ya shiga na wasu yan mintuna, baifi 30 minutes ba ya fita ya rufe laptop dinshi,

Sashen goodness ya shiga ta baya, tana falo tana bacci ga tv tana yi ita kadai,

Sunkuyawa yayi ya fara kiranta ahankali "goodness" sai da ya kirata wurin sau uku sannan tayi firgigit ta tashi,

"Abbu yaushe ka dawo?" Ta tambayeshi tana murtsuke idanuwanta,

"Yau ba kya son labarin ne kika kwanta kike bacci?"

"No, ina so na kwantane kafin ka dawo"

Tv din ta kashe tabi bayanshi zuwa sashensa, ba karamin kyau yayi mata ba domin ya zama dan saurayi sak,

Acan inda ta saba kwanciya yauma ta kwanta, shi kuma yana daga farkon gadon azaune,

"Yau wanne labari zan baki? Ko kece zaki bani?"

"Ka fara bani, nima zan baka idan ka gama"


K'issar annabi musa da dan uwansa annabi harun ya fara bata da irin gwagwarmayar da suka yi da fir'auna da hamana da dan karuna,

Bakinshi kawai take bi da kallo tana mai jin wani irin sanyi acikin zuciyarta wai yau itace jabir yake yiwa dogon labari irin wannan duk da tasan sa'a kawai take ci domin surutu ba sabonsa bane,a bangare daya kuma na zuciyarta tana jinjina labarin domin labarin yakai inda duk wata hikima takai domin ba karamar hikima bace acikin rayuwar annabi musa,

Zumbur ta tashi zaune tana kallon jabir,

"Abbu kar ka cemin basuyi nasara ba a gasar da aka shirya ta matsafan nahiyar"

Kallonta ya daga kai yayi "sunyi nasara ai sandar annabi musa micijiya ta zama ta rinka hadiye duk wasu abubuwa wanda suke ba kanana ba, anan sauran mutane suka yi imani dasu"


Komawa tayi ta kwanta tana murmushi domin labarin da yake bata har wani imagining din abin take acikin kwakwalwarta.

Lokacin da ya kammala fada mata k'issar ba karamin mamaki tayi ba jin wai har yanzu fir'auna yana nan aduniya agidan tarihi a kasar misra,

"Abbu wannan labarin da ka fada min dagaske ya faru?"

Daga mata kai yayi "its true life story, ni har fir'aunan nagani lokacin da naje gidan tarihin, ai Allah ne ya fada cewar zai tseratar da gawar fir'auna daga lalacewa domin ta zama aya ga mutane"

Mikewa tayi daga kwanciyar da take "gaskiya sunsha gwagwarmaya daga shi har dan uwanshi, sannan abinda yafi bani tausayi agame dashi shine irin yanda dan uwansa d'an karuna ya juya masa baya yakoma ya hada kai da fir'auna bayan ya zama mai arziki, ya manta da cewar shine yayi masa addu'a har Allah ya bashi arzikin"

"Ba mantawa yayi ba tsabar shak'iyanci ne kawai,amma duk wannan tawayen dasu fir'auna suka yi hakan bai hana annabi musa samun nasara ba domin yanada yawan al'umma shiyasa afilin alk'iyama za ahango wasu al'umma masu yawan gaske har annabi Muhammad (s.a.w) zai taso domin ya zata al'ummarsa ce sai ace wannan al'ummar annabi Musa ne (A.S)"

Shiru tayi zuciyarta cikeda mamakin yadda aka yi har teku ya daskare ya rabe gida biyu mutane suka wuce ta cikinsa,

"Tunda nagama baki labarin to nima ki bani wani inji" yace da ita yana gyara kwanciyarsa,

Dan murmushi tayi tace "ni labarin ruhu zan baka domin labarinsa yazo mana acikin Bible, shi ruhu ba mutum bane kuma ba aljan bane sannan bashi da farko kuma bashida karshe....!"

Katseta yayi "shima kenan ubangijinku ne?"

Kai ta girgiza "no, he's not our lord but...!"

"But what? Goodness don't deceive your self,indai wannan ruhun da kike fada ba ubangijinku bane to babu hujjar da zai sa ki kira annabi Isah a matsayin ubangijinki domin shi wannan ruhun da kikace Bible yazo muku da labarinsa ai yafi annabi Isah abin mamaki, dalili shine shi annabi Isah baku bashi wannan siffofin ba amma shi ruhu gashi kun bashi"

Kallo ta bishi dashi tana dan nazari akanshi, "Kaine fa kace in baka labari kuma shine daga fara fada maka zaka yi interrupting dina" ta fada fuskarta ta kwakkwabe kamar zata yi kuka,

"Ba katse ki nayi ba, ki bari gobe zan baki k'issar shi kanshi annabi Isah din da ta mahaifiyarshi Nana maryam, labarin nakine bana son jinshi saboda na rigada na sanshi tun dadewa, ko baki san nima na karanta bible ba?"

Kallonshi tayi da sauri "are you serious?" Ta tambayeshi,

"Am serious goodness, duk wani abu wanda ke cikin Bible na sanshi na karantashi"

Jingina tayi da jikin _pillow_ tana kallonsa, "ki bari sai gobe zan fada miki waye yesu, almasihu, zan sanar dake k'issarsa tun zuwanshi duniya da kuma dawowar da zai yi nan gaba"

"Dawowa? Zai dawo nan gaba?" Tafada cikeda mamaki,

"Yes zai dawo nan gaba haka Allah ya sanar damu" ya bata amsa yana kokarin tashi,

Batare da tace masa komai ba ta koma ta kwanta tana binsa da kallo har ya shige cikin _bathroom_. Tana nan kwance har ya fito ya tsaya agaban gadon ta taso tazo inda yake ta mika masa hannuwanta ya karanto mata addu'o'in kwanciya bacci ta koma ta kwanta tana shasshafe jikinta da tafukan hannayenta.

Ido ta tsura mishi lokacin da ya tada kabbarar sallar nafilar da zaiyi, tana nan kwance tana kallonsa har bacci ya dauketa bata san lokacin da jabir ya dawo kan gadon ya kwanta ba.

Washe gari da safe da ciwon cibiya ta tashi amma bata sanar da jabir ba har ya shirya ya tafi office aranar mamanta tazo gidan domin ganin lafiyarta duk da cewa suna haduwa a church duk ranar lahadi, huduba iri iri ma tayi mata kafin tabar gidan, a irin kudin da wani lokacin jabir yake bata ta dauko ta bawa ma _2000_ haka ma ta karba babu wani farin ciki domin jikinta ya gama yin sanyi da lamarin goodness gani take kamar goodness din zata karbi addinin musulunci.

K'arfe 8:30 jabir yana zaune a falonsa yana kallon huda tv inda ake gudanar da wani program _(Qur'an and the science)_ gefenshi kuma wasu littattafai ne a ajiye wadanda ya gama dubasu,

Kallonsa goodness tayi lokacin da ta shiga cikin falon acikin ranta tana cewa "kullum baka gajiya da karance karance da kallon wannan channel din"

"Sannu abbu" ta fada tareda zama a k'asa can nesa dashi kadan,

"Yawwa" yace ba tare da ya jiyo ya kalleta ba,

"Abbu ina son zuwa hospital gobe, zan ga dr"

Sai a lokacin ya juyo da hankalinsa zuwa gareta,

"Meya faru?"

"Cikina ne yake ciwo" tafada kanta a sunkuye,

"Cikinki ko mararki?"

"No,cikina ne"

"Ba period pain bane?"

"Abbu ba shi bane, cibiyata ce ke yin jini"

"Jini? Tun yaushe?"

"Abbu dama ya jima yana yi to yanzu ne yayi yawa yau da safe naga jinin yana fita da yawa"

"Let me see"

D'agowa tayi ta kalleshi amma ta kasa motsawa daga inda take,

"Ba kiji abinda na fada bane? Zo nagani"

Hada ido suka yi amma har lokacin bata da niyyar tashi,

"Abbu ba sai ka gani ba"

"Ok ni ba sai Nagani ba amma zaki iya nunawa dr shi yagani ko? You are not serious"

Wayarshi ya dauka ya fara kiran dr din da yake dubashi idan ba shida lfy, nan ya fara fada masa matsalar goodness, tambayarshi dr din yayi cewar yaya cibiyar tayi, tayi rami ne ko kuma daga can ciki jinin ke fitowa,

Goodness ya kalla ya dan janye wayar daga jikin kunnenshi,

"Come here"

Ahankali ta tashi ta matsa inda yake, bai jirata ba ya daga rigarta, ya fara duba cibiyar ta,dan yatsanshi ya saka akan cibiyar cikin sauri ta rike yatsan nashi "ohh wash abbu da zafi",

Wayar ya mayar jikin kunnenshi yana yiwa dr bayani, ido ta zuba masa aranta tana tunanin to me kenan? Meye dalilinshi na kin barinta taje taga dr Kodai kishi yake?? Hhhh masu karatu nikaina ummi A'isha tambayar da nake son inyi muku kenan kodai kodai??? Anya kuwa mal jabir ba a kamu ba?? Hmmm muje zuwa zamu gane ai.

Sai da ya gama wayar sannan ta saki dan yatsan nashi tana kallonshi shikuma fuskarshi na kallon wayarsa,

"Bari zai turo da sunayen magungunan da za asai miki kisha yanzu, idan ya turo sai nabayar a siyo miki",

"Thank you abbu"

Tashi tayi ta koma part dinta tayi wanka tayi shirin bacci ta fito ta shiga kitchen ta dafawa jabir shayin na'a na'a ta dauka ta nufi part dinsa.

Yana falo azaune jikinsa sanye da kayan bacci _lemon green_ yana dudduba magungunata wanda ya bayar aka siyo mata,

"Zo ga maganinki"

Karasawa tayi ta zauna tana kallon maganin itama harda wani mai kamar hydrogen amma ba shi bane sai nasha kala daban daban,

"Ki dauka kisha yanzu, shi kuma wannan goge wurin zaki rinka yi dashi"

"Toh" ta karba tana kallonshi, dakyar ta iya daurewa ta goge cibiyarta da spirid domin yanada zafi dan dai kawai tana tsoron jabir ne kar yayi mata irin na rannan.

Kallonta yayi lokacin da take shan maganin tasha kayan baccinta riga fara mai digon pink ajiki sai wando pink colour, mikewa yayi ya shiga _bedroom_ dinshi nan ta tashi tabi bayanshi, agefen gado ta sameshi zaune yana waya da ummu al'amin, bata iya jiyo abinda yake fada hakan ya sata kwanciya acan karshen gadon ta juya masa baya tayi ruf da ciki.


Sun jima suna yin waya da matarshi tana jinsu har ya gama wayar, jin shiru yasata juyawa tana kallonshi,

"Abbu labarin da kace zaka bani jiya"

Juyowa yayi gareta "labarin wa nace zan baki"

"Jesus" tafada tana kokarin gyara kwanciyarta,

"Kamar yadda nafada miki yesu ba Allah bane kuma ba dan Allah bane, asalima idan aka ambaci wannan kalmar sama da kasa sai sunyi kamar zasu hade domin Allah bai cancanci wannan siffar ba, annabi Isah annabin Allah ne wanda mahaifiyarshi ta haifeshi ba tare da uba ba kuma itama Qur'ani ya sanar damu cewar mutuniyar kirki ce tagari mai yawan ibada, amma da Allah ya tashi nuna hikimarsa da ikonsa sai ya nufeta da haihuwar annabinsa ba tareda ta taba saduwa da wani d'a namiji ba, kawai mala'ika ne ya hura mata iska take ta dauki cikin

Please Login or Register in order to submit comment