Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai yayi sha'awar musulunci bayan ba ranar ya fara jin karatun qur'anin ba, kai koma dai menene to wannan wata babbar rahama ce daga Allah,

Goodness hakika ubangiji yasoki da rahama kuma yasoki da samun babban rabo acikin rayuwarki, yanzu abinda nake so dake shine kar ki yarda ki sanar da mahaifiyarki sannan kije gidan mahaifin jabir mijinki ki karbi musulunci agurin mahaifinsa, bana son mamanku tazo ta tarar dake agidan nan,ubangiji Allah yayi miki albarka yasake baki *Wani haske* acikin rayuwarki"

Mahaifinta yafada yana kwallar farin ciki, ita kanta goodness itama hawayen take yi, tashi tayi tafita ta koma gidanta, katoton dogon hijabin da Ummu al'amin ta bata ta dauko ta dorashi asaman doguwar rigarta ta tafi gidansu jabir,

A soro ta tarar da Malam mahaifin jabir, Malam yayi mamakin ganinta amma lokacin da yaji kudirinta sai mamakinsa ya sake karuwa gamida farin ciki, wanda har sai da hakoransa suka bayyana,

"Dafarko dai ina fata ba wani ra'ayine yasaki sha'awar karbar musulunci ba? Ina fatan zaki yi hakanne domin Allah saboda dukkan aiki sai da niyya shiyasa acikin hadisin da aka karbo daga Umar Allah ya kara masa yarda yace annabi Muhammad yace dukkan aiki sai da niyya sannan kowanne mutum akwai abinda yayi niyya, duk wanda yayi hijira domin Allah da manzonsa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da son manzonsa,wanda yayi hijira kuwa domin duniya ko wata k'awa, ko dan wata mace da zai aura to sakamakon hijirarsa tana ga abinda yayi hijira dominsa, shugaban masu rawaito hadisai ne ya rawaito wannan hadisin _(imamul muhaddasina)_"

Kanta ta daga "ba wani ne ya tilastani ba, kuma ba dan wani nayi hakan ba face dan Allah"

"To alhamdulillah, da farko dai ina son kisani shi musulunci yana nufin mika wuya ga Allah, da jawuwa agareshi da biyayya,da kuma tsarkakewa daga shirka,

Sannan shi musulunci yana da ginshikai guda biyar kamar yadda annabi Muhammad yafada acikin ingantaccen hadisi cewar angina musulunci akan abubuwa guda biyar, nafarko shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah sannan annabi Muhammad manzon Allahne, sai tsayar da salla, salla itace aiki nafarko da zafara bincikawa ranar tashin alqiyama, idan ta gyaru dukkan ayyuka sun gyaru idan kuma an samu sabanin haka to abin sai dai ace Allah ya kyauta,abu na uku shine azumin watan ramadan,

Amma babu tilas akan marar lafiya, ko kuma tsoho wanda shekarunsa suka ja ko kuma karamin yaro, ko matafiyi duk an samu rangwame akan wadannan mutanen,

Abu na hudu kuma shine bayar da zakka ga wanda ya kasance mai arziki, sai abu na karshe, ziyartar dakin Allah ga wanda ya samu dama, dalilin haka saboda hadisin da aka karbo daga Umar Allah ya kara masa yarda yace: wata rana muna zaune da annabi Muhammad sai wani mutum ya bullo mana, mai tsananin farin tufafi, mai tsananin bakin gashi, babu alamun tafiya agareshi kuma babu daya daga cikinmu wanda ya sanshi har ya zauna akusa da annabi Muhammad, ya jingina gwiwowinsa ajikin gwiwoyinsa ya dora tafukan hannunsa akan tafukan hannunsa yace ya Muhammad bani labarin musulunci, sai annabi yace,

Musulunci shine shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ni manzon Allah ne, da tsayar da salla da bada zakka da azumin watan ramadana da ziyarta dakin Allah ga wanda ya samu iko, sai yace kayi gaskiya, sai muka yi mamakinsa yana tambayarsa kuma yana gasgata shi,

To wannan shine musulunci sannan kuma duk musulmi ana son ya zama mai imani, rukunan imani guda shida ne, imani da Allah, imani da mala'ikunsa,littattafansa,manzanninsa da ranar karshe, da yin imani da kaddara mai kyau da marar kyau,

Dalilin wadannan rukunai guda shida shine fadin Allah madaukakin sarki "'Ba aikin alkairi bane kadai ku juyar da fuskokinku gabas da yamma ba, sai dai aikin alkairi ya hadar da yin imani da Allah, da ranar karshe, da mala'iku, da littafi da manzanni"' _(Qur'an chapter 2)_,

Dalilin kaddara kuma fadin Allah madaukakin sarki "'hakika mun halicci dukkan komai cikin kaddara"'

Gyada kai goodness tayi "Malam nagode madalla Allah ya saka maka da alkairi"

"Babu komai malama domin yanzu kema kin zamo malama, sai dai akwai abubuwan da nake so ki kiyaye,

Abu nafarko shine kowanne aiki akwai sharuddan karbar aikin, sharrudan sune nafarko sai anyi aikin domin Allah, na biyu kuma sai anyishi irin yadda annabi Muhammad ya koyar dashi, baya halatta ga mutum domin yana son ya samu lada ya kirkiri wani aiki dakansa acikin addini, anfi son komai zaka yi kayi shi kan koyarwar annabi shiyasa awani hadisi annabi sallallahu alaihi wasallam yace:

"'Duk wanda ya kirkiro da sabon al'amari acikin wannan addinin, wanda baya daga cikinsa, to anmayar masa dashi"' _(muttafakun Alaih)_

Ko wanne aiki mutum idan zaiyi to yayishi akan sunnah, sannan yayishi yanda sahabai suka yi domin acikin addini bai halatta mutum ya kafa hujja da iyayensa ba ko kuma malamansa, acikin musulunci mutum dayane aka yarda ya kafa hujja da mahaifinsa shine wanda ya kasance babansa annabine to wannan an yarda yayi koyi dashi amma bayan wannan to haramun ne mutum ya tashi yana bin addinin iyaye da kakanni, mutukar ba akan daidai suke ba,

Shiyasa sharadin karbar aiki sai anyi aikin kamar yadda annabi ya koyar ko kuma yadda sahhabansa suka koyar ko yadda salihan bayi suka yi,

Son manzon Allah wani yanki ne daga cikin yanki na imani, domin acikin hadisin da aka karbo daga Anas dan malik Allah ya kara masa yarda yace annabi Muhammad sallallahu alaihi wassalam yace:

_"'Imanin dayanku bazai cika ba har sai nafi soyuwa agareshi fiyeda yayansa, da iyayensa, da sauran mutane baki daya"'_

Son annabi shine kiyaye dukkan abinda yayi hani dashi da kuma yi masa da'a da yarda da dukkan abinda ya fada, mutum baya zama mumuni na kwarai har sai yayiwa annabi da'a, fadin Allah madaukakin sarki:

_"'kuma abinda manzo ya baku to ku karbeshi, kuma abinda ya haneku dashi to ku barshi. Kuma kubi Allah da takawa, lallai Allah mai tsananin ukuba ne"'_ _(Qur'an, chapter 59,verse no 7)_,

Ya zama wajibi ga dukkan mai imani yaso annabi kuma yayi koyi dashi sannan yayi koyi da sahabbansa ya sosu ya kaunace sannan ya nisanci dukkan kirkirarren abu wanda annabi bai yishi ba kuma sahabbansa ma basu yi shi ba, bayan mutum yaso annabi da iyalan gidansa ana so yaso sahabbansa ya kaunace su domin babu wasu wanda suka fi kusanci dashi sama dasu, sunada daraja da matsayi har awurin Allah, sune mutanen da suka rayu dashi suka taimakeshi suka bashi kwarin gwiwa suka yi masa biyayya alokacin da kowa yayi masa tawaye, matsayin sahabbai awurin annabi Allah ne kadai yasan yawanshi shiyasa ahadisin da aka karbo wurin Abi sa'idil kudri manzon Allah (S.A.W) yace:

_"'Kada Ku zagi sahabbai na, na rantse da wanda raina yake hannunsa da ace dayanku zai ciyar da zinare (sadaka) kwatankwacin girman dutsin uhudu to bazai kai matsayin dayansu ba adaraja,koda rabin dayansu bazai kai ba"'_ Bukhari ne ya rawaito,

Sannan dukkan abinda zakiyi wanda ya shafi ibada to kiyi bisa sunnar annabi Muhammad koda kuwa ace salla ce domin ita kanta sallar annabi yace: _"'kuyi salla kamar yadda kuka ga ina salla"'_ amma sam sallar ma yanzu ba ma yinta cikin kushu'i da nutsuwa, sannan na horeki da nisantar duk wani Sabon abu domin bidi'a batace haka annabi ya fada kai asalima annabi cewa yayi _"'Duk wanda yayi min karya da gangan to ya tanadi wurin zamansa agidan wutar jahannama"'_
Nasan dukkan wadannan abubuwan mijinki zai sanar dake idan ya dawo, amma yanzu bayan na baki Kalmar shahada kin karba zakije kiyi wankan shiga musulunci sannan kuma zaki shiga cikin gida domin zasu koyar dake abubuwan da zaki gabatar"

Anan take Malam ya bawa goodness Kalmar shahada ta karba, sannan yace wanne suna take sha'awar komawa tace A'isha sai Malam yace mata,

"Hakika sunan A'isha sunane mai girma domin sunane na daya daga cikin matan fiyayyen halitta wacce yafi so yafi kauna domin an tambayeshi aduniya waya fi so yace A'isha, akace amaza fa yace babanta Abubukar, to amma ni anawa ganin ki karbi suna *BAHIJJA* domin sunane mai daraja awurin jabir mijinki, sunan mahaifiyarsa ne wacce ta rasu tun yana jariri dan wata takwas shiyasa yayi burin inama ace al'amin mace ne da ya mayar da wannan sunan"

"Malam asamin bahijjan domin yanzu nima naji ina kaunar sunan" tafada idanuwanta dauke da kwallar tausayin jabir mijinta domin ita bata taba sanin shi maraya bane, Allah mai yadda yaso hakika Allah baya barin wani dan wani, ita dai yanzu ta yarda addinin musulunci akwai tarin *Wani haske* mai yawa acikinsa wanda ta shaida hakan.

Cikin gidan suka shiga tare da Malam yayi musu bayani, nan suka shiga gwada mata yanda ake yin wankan musulunci da dukkan sauran wankan da ya wajaba akanta, dama alwala ta iya domin akwaita acikin bible,

Har dare takai agidan ana koya mata abubuwan da suka shafi addini, littattafan addini wadanda aka rubuta da turanci Malam ya bata irinsu, _40 Rabbana_, _Good Muslim_, _40 hadiths_ da sauransu,

Gida ta koma ta zauna tafara tsefe tulin gashin kantin dake kanta, yau jinta take cikin wani farin ciki gashi wata iska mai dadi tana shigarta ta ko ina lallai musulunci shine addini na gaskiya, hakika musulunci shine addinin Allah .


Anty Bilkisu ta kira tayi mata albishir sannan ta roketa kan tazo gobe domin sake koyar da ita wasu abubuwan masu muhimmaci, washe gari kuwa sai gata nan ta wunar mata sai yamma ta tafi amma fa mahaifiyarta har yau bata san abinda ke faruwa ba haka shima jabir bata sanar dashi ba har lokacin tafi so tayi masa bazata sai ya dawo zata sanar dashi.

***

Jabir kuwa yana can madina tare da ummu al'amin da al'amin din, in banda soyayya babu abinda suke yi shida ummu, yauma kwance yake agefenta yana rungume da ita ta baya, yana shafa gashin kanta, jin tayi shiru ya tabbatar da cewar tayi bacci, ahankali ya tashi ya fita,

Zama yayi yafara kiran wayar goodness,lokacin da ya kirata tana zaune afalonshi tana karanta abinda aka dora mata agidan malam saboda kullum sai taje an doro mata karatu wani lokacin ma can take wuni,

"Hello abbu" tafada acan Kasan makoshinta,

"Kidaina kirana da sunan nan fa" yafada cikin sanyayyiyar muryarshi,

"Saboda me?" Ta fada tana murmushi,

"Saboda ban haifi kamarki ba, iya al'amin na haifa" ya bata amsa,

"Inji wa? Nima fa ka haifi kamata" ta fada cike da son ta zunguroshi,

"Kar ki kashe min kasuwa, yanzu idan naje neman auren ta uku taji kina cemin abbu sai taki aurena tace nayi mata tsufa tunda na haifi katuwa kamar ki"

Ba karamin mamakin abinda ya fada tayi ba wato ashe shima ya iya bayar da amsa, wani abu taji ya soki ranta wanda tafi zaton kishine, zuruf ta tashi zaune tana sake makale wayar acikin kunnenta,sannan abinda yafi bata mamaki shine kiranta da katuwa da yayi,

"Abbu me kace?" Ta sake tambayarsa,

"Abinda kunnenki yaji, ni kidaina kirana da abbu" ya mayar mata da martani amma aranshi yana tuna girmanta, tabbas yarinyar katuwa ce ta wasu wurin,

Shiru tayi ta kasa yin magana gaba daya kishi ya gama lullube zuciyarta,

"Hello goodness are you there?" ya kira sunanta

"Nima kadaina cemin goodness" tafada tana zumburo baki kamar yana kallonta,domin yanzu ji take ta tsani wannan sunan,

"Why?"

"Saboda na sauya suna"

Dariya ya danyi amma sai bai dauki maganar tata dagaske ba,

"Yaushe kika canja suna ban sani ba, sannan wanne sunan kika koma?"

Shiru tayi masa domin tasan idan ta fadi sunan zaiji babu dadi saboda sunan mahaifiyar sa ne,

"Bana fadar sunan?"

"Meyasa?" Ya tambayeta wanda shi kansa ya rasa gane kansa da kansa, dadin hirar da suke yi yake ji,gashi yau tunda yaji muryarta sai ya ke jin wani irin yanayi atare dashi wanda bai san menene ba, amma jin abin yake tun daga babban dan yatsansa har zuwa tsakiyar kansa,

"Saboda bana fadar sunan" ta bashi amsa,

"Oya fada min kawai tunda baki son waccan sunan kinga idan kika fada min sai in daina kiranki dashi"

"Bazan iya fada ba" tasake bashi amsa tana lankwashe murya,

"To kashe wayar ki yimin text sai in kiraki"

Wayar ta kashe ta tura masa text din sunan, lokacin da ya ga text din,mamaki ne ya kamashi gamida al'ajabi, to a ina tasan wannan sunan yana da muhimmanci awurinsa, murmushi yayi ya sake kiranta,

"Hello binti, waye ya fada miki sunan nan?"

"Menene binti?" Ta tambayeshi,

"Yarinya, ke ai yarinya ce tunda kina kirana da abbu"

"Abbu a ina ta ukun take?" Ta tambayeshi cikeda shagwaba, shi yama manta da maganar budurwar da yayi ashe ita abin yana ranta bata manta ba,

"Wacece?" Ya tambayeta shima,

"Agaida al'amin" tana gama fadin haka ta kashe wayar gabaki daya cikeda kishi, abin dariya ya bawa jabir,

Motsin da yaji abayansa ne yasashi juyawa nan yaga Ummu tsaye tana rikeda labulen dakin, tana kallonshi da alama duk taji hirar da suka yi da binti.


_Masu karatu sai mun hadu ashafi nagaba (shafin soyayya)._




_*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ»
[10/24, 5:26 PM] Manshat: [9/29, 9:02 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE..!*


_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_


_86-90_




~~~Jiyowa yayi yana kallon ummu al'amin,

"Har kin tashi daga baccin?"

"Wallahi kuwa amma yanzu zan koma, naji kana waya da antyn al'amin"

"Ehhh nida itane, yau rikici take ji, da alama yarintar ta motsa" ya fada yana murmushi,

"Yarinta?" Ta tambayeshi,

"Ehh mana, ai dan bakiga shirmen da tai tayi bane itada al'amin lokacin da yana can"

Murmushi tayi ta juya ta koma cikin dakin, tashi shima yayi yabi bayanta.

Kishi fal dankare acikin kirjin goodness tunanin jabir kawai take yi da tuno kyakkyawar surarsa mai daukar hankali, gaba daya hankalinta ya gama tashi gani take kamar dagaske auren zai sake yi,

Wayarta ta sake kunnawa ta fara kiransa, yana kwance ajikin ummu ya daga wayar,

"Binti" shine kawai abinda yace,

Cikeda shagwaba tafara magana "abbu dagaske kake yi?" Ta tambayeshi wanda ita kanta bata san lokacin data yi tambayar ba,

"Wai me?" Shima ya tambayeta, tashi yayi daga kusa da Ummu ya koma falo,

"Abbu wai meyasa kake cemin katuwa ne?" Tafada ashagwabance, jin shagwabar da take yi masa yake har cikin ransa,

"Ke katuwa ce mana,ko baki sani ba?"

"Abbu nidai ka fada min idan dagaske kake yi"

"Wai menene dagaske"

"Ta ukun da kace zaka yi"

Dariya ce taso subuce masa jin maganarta, gashi duk tabi ta damu bata san shi da wasa yake yi mata ba,

"Dagaske mana, bayan itama zan sake aurar wata kinga hudu kenan"

Kirji ta dafe da karfi, sai kuma ta kashe wayar kit ta ajiyeta agefe, tunani tafara tana dafe kuncinta, kishine tsababa acikin ranta,

Wayar ta sake dauka ta kirashi,

"Yau ba zaki barni inyi bacci bane?" Ya fada lokacin da ya daga wayar,

"Abbu yanzu nida Anty bamu isheka ba har sai ka sake wani auren?"

Tafada tamkar zata fashe da kuka, har sai da yaji mamakinta aranshi yana tunanin kishi irin nata,amma burgeshi shagwabarta take yi,

"Ehhh" yafada kansa tsaye yana dan nazarinta,

"To a ina take?"

"Tana Nigeria ki bari idan nadawo zaki rakani wurinta"

Ranta taji yayi bakikkirin amma ta daure tace,

"Yaushe zaka dawon?"

"Acikin next week zan dawo"

"Allah ya kaimu, agaida ummu al'amin"

Wayar ta katse bata jira amsarshi ba, ruf da ciki tayi akan doguwar kujerar shi, kishine kawai ke dawainiya da ita,

"Mtsssss me za ayi da auren mai mata yanzun ma tasan yana can tare da matarsa ita kuma gashi tun zuwanta gidan babu abinda ya taba hadasu"

Tafada acikin ranta, haka ta zauna ta bata lokaci da yawa tana cikin yanayi na bacin rai,

Lokacin da taje bacci ma ta dade bata yi baccin ba juyi kawai take tana tunanin jabir, pillow taja ta rungume tana tuno mijinta abin sonta.

*

Tunda satin da jabir zai dawo ya kama tafara shirin tarbarsa, kullum sai ta shirya masa kayan dadi amma shiru sai taji babu alamunsa, yauma sai da tayi masa girki tayi kwalliya sosai amma har 9 shiru,

Wayarshi ta kira yana dauka ta fara kukan shagwaba,

"Abbu bazan sake yi maka girki ba har sai ka dawo, kullum sai nayi sai kaki dawowa"

Sai da tsikar jikin jabir ta tashi saboda yanda take masa wannan kukan shagwabar,

"Binti dama ai cemiki nayi acikin satin nan ban fada miki date dinba, kidaina wahalar da kanki, ki bari kawai duk ranar da nadawo sai kiyi min girkin ina gidan, kinji?"

"Nidai abbu ban yarda ba ka fada min" ta sake fada cikin shagwaba,

"To ai kinga saura 3 days week din ya kare, dan haka may be gobe zan dawo ko jibi ko...."

"No abbu nidai ban yarda ba ka fadamin Allah"

Lumshe idanunshi yayi acikin ranshi yana cewa "yarinyar nan tana son tayar min da hankali fa" amma afili sai yace,

"Kwana uku ne fa kawai binti ai kinga nabaki satar amsa"

"Ok to nadauki jibin, gobe bazan yi maka girkin ba, sai jibi, idan ranar ma baka dawowa shikenan ko ranar da zaka dawo bazan yi maka ba"

Duk wadannan maganganun cikin kukan shagwaba tayi su,

"Haka kika tsara?"

"Ehh abbu" tasake fada cikin sigar farko, ita kanta wani iri takeji ajikinta bare kuma jabir wanda ko kwakkwaran motsi ya kasa,

"Ohhhhh abbu my cooking, girkina ya fara konewa, bye bye" wayar ta katse ta ruga kitchen da gudu inda take dafa indomie guda daya tal dan shegen kwadayi,

Bin wayar jabir yayi da kallo yana murmushi tareda tuno shiririta irin ta goodness.

Aranar da zai dawo wani boutique ya shiga ya kwaso mata english wears hadaddu _(sexy dress)_ masu kyau da aji domin yasan bata saka atamfa ko shadda kullum cikin kananan kaya take,

Wasu kyawawan braziers yagani amma yana tantamar ko zasu yi mata daidai kuwa saboda yaga ita din bata wasa bace, braziers din sunyi masa kyau sosai domin masu daukar hankaline, diba kawai yayi aranshi yana tunanin idan sunyi mata kadan tasan yadda zata yi dasu,

Akwati guda ya ciko mata da kananan kaya bayan shima ya lodi nashi, gida ya koma inda ummu ke jiranshi ita da al'amin duk tabi ta damu saboda tafiyar da zaiyi ya barta,

Hannunta ya kama ya kwantar da kanta agefen kafadarshi al'amin kuma yana kan cinyarshi,

"Haba Ummu menene abin damuwa ne?"

"Abu al'amin dan Allah kadawo hajji, zamu yi kewarka nida al'amin"

Murmushi jabir yayi "ummu ba lallai ne nazo aikin hajji ba saboda wasu dalilai masu yawa, kiyi hakuri idan sabuwar shekara ta kama zan turo muku kudi sai kuzo gida"

"Yawwa abu al'amin Allah ya saka da alkairi, Allah ya kaika lfy"

Ya dade tare dasu yana rarrashinsu kafin yayi wanka Ya shirya suka rakashi har airport, wani kwalin chocolate al'amin ya bashi wai ya kaiwa goodness, murmushi jabir yayi,

"Ohh Al'amin ka rasa abinda zaka bawa antyn naka sai chocolate?"

"Abbu anty mayyar chocolate ce wani lokacin ko abinci bata ci sai dai tai ta shan chocolate"

"To shikenan al'amin zan kai mata"

Sallama yayi musu ya shige cikin jirgi, Ummu harda yar kwallar ta yayinda al'amin keta daga masa hannu, suna nan tsaye har jirginsu ya tashi,sai da suka ga tafiyarsa sannan suka koma Gida.


K'arfe uku na yamma jirginsu ya sauka yayiwa driver waya yaje ya daukoshi,

Tana falonshi ta baje akasan carpet tana bacci daga ita sai yar body hug dinta baka da short trouser milk colour, dama tana hutun salla,

Yana saka kansa cikin falon ya hangota, idonsa ya sauke akan lukuta lukutan cinyoyinta wadanda suke afili domin wandon data saka iya rabin cinyoyinta ya iya rufewa,

"Masha Allah"shine kawai abinda ya iya fada bayan ya lashi lips dinsa,

Ciki ya karasa ya tsaya akanta yana karewa halittarta kallo kamar yau ya soma ganinta,

Babu zato tayi wani juyi tare da wata mika nan rigar jikinta tayi sama cikinta ya bayyana,

"La ilaha ilallah, muhammadur rasulillah"

Shine abinda yaji ta fada, ahankali ta soma bude idonta, shidai jabir mutuwar tsaye yayi saboda jin abinda ta fada,

"Lahh abbu yaushe ka dawo?" Tafada tana kokarin tashi zaune,

Kan kujera ya karasa ya zauna yana kallonta,

"Yanzu shigowata kenan yar lukuta"

Bakinshi ta kalla ta hadiyi yawu ita dai aduniya tana son bakin nan na jabir, duk ranar data kamashi babu sauki ta ayyana hakan acikin ranta,

"Sannu da zuwa, bari naje nayi maka girki abbu" tashi tayi tana sake yin wata mikar ta fita, kitchen ta shiga duk tana cike da murnar ganinsa jinta take kamar anyi mata albishir da gidan aljanna,

Kasancewar tanada kayan amfaninta wanda zata bukata yasata dora jalop din shinkafa da kayan lambu, sai murna take har ta yanke hannunta wurin yanka cabbage,

Tana kokarin yanda zata yiwa yatsan nata jabir ya shigo cikin kitchen din,

"Yankewa kika yi?"

Boye hannun tayi ta bayanta ta jiyo tana kallonshi, bata son ya gani saboda kar yace sai ya saka mata hydrogen,

"No abbu" tafada tana raurau da idanuwanta,

"Ya salam" yafada acikin ranshi,

"Bani to ingani, bazan saka miki hydrogen ba Allah"

Fito da hannun tayi ta mika masa, rike hannun yayi ya fito da ita zuwa falonta, dan kyalle ya samu ya daure mata wurin ita dai tana daga tsaye tana kallonshi yana sanye da jallabiya ruwan kasa kansa babu hula amma ba karamin kyau yayi mata ba ahakan,

Kitchen ta koma ta ci gaba da girkin da take yi shikuma jabir ya fita zuwa masallaci domin lokacin sallar la'asar yayi,

Bayan ta sauke girkin sai da ta hada lemon kwakwarta kamar yadda ta saba amma na yau harda jabir tayi shi,

Wanka ta shiga tayi ta fito daure da towel sai ga jabir ya shigo sashen nata,

Dan doddoka kafafunta akasa tafara yi tana rike towel din jikinta,

"Abbu bana salla kabani pad"

Dama can ai ba sallar kike yi ba ya fadi hakan aranshi amma afili cewa yayi,

"Ke wai kullum acikin jini kike ne? Koda yaushe jini,koda yaushe jini sai kace wata marar lafiya"

Farr tayi da idanuwanta tana matse cinyoyinta gudun kar tayi staining,

"Abbu lafiyata k'alau, ni sau biyu nake yi awata"

Tab nashiga uku kenan, yafada aranshi danma shi ba mai yawan bukata bane, sai yayi wata bai bukaci mace ba wani lokacin ma zai iya yin fiyeda haka,

Kallonta yayi sai ya hango jinin yana bin cinyoyinta,

"Ina zuwa bari na kawo miki" juyawa yayi ya fita, yana fita ta fashe da dariya dama tana sane tayi masa haka saboda tun lokacin da yayi mata maganar wannan ta ukun da yace zai aura ta daura aniyar haukatashi da salonta kala kala wadanda anty Bilkisu ta koyar da ita,

Tana nan a inda yabarta har ya dawo yana rike da pad din guda biyu,

"Gashi,amma haka wannan abin yake yi miki rushing?"

"Ehhh abbu amma zuwa kwana ukune, yana yin kwana uku zai daina"

Juyawa yayi ya fita baice da ita komai ba, nan tasake komawa toilet tayi wani wankan ta fito, shiryawa tayi cikin riga da wando na jeans baki rigar kuma light green mai gajeren hannu,

Abincin da ta shirya ta dauka ta nufi sashen jabir, yana zaune yana waya dasu al'amin da ummu, abincin ta ajiye ta tasashi agaba kamar zata shige cikin cikinsa, abin har dariya yaso bashi gashi ta wani kafeshi da ido duk motsin da bakinsa yake yi akan idonta ne,

Wayar ya mika mata yaja abincin ya zuba ya fara ci yana sauraren hirarta itada al'amin wanda gaba daya yarintace aciki,

Har yagama cin abincin bata gama wayar da al'amin din ba, lemon kwakwar da tayi yasha madara dan haka ba karamin dadi yayiwa jabir ba, sai da ya shanye rabin jug amma abincin kadan yaci,

Kan doguwar kujera ya koma ya zauna ya kamo huda tv yafara kallon wani program da suke yi alokacin mai taken _Da'awah workshop_,

Yana jin lokacin da goodness tagama wayar ta ajiye,guntun abincin da ya rage acikin filet tasa hannunta zata ci sam ta manta da yankewar da tayi dazu a yatsanta, tana saka hannunta taji yaji ya ratsa wurin, babu shiri ta zubar abincin ta zabura tayi inda jabir ke zaune,

Tana zuwa tasaka kuka tare da zama akan cinyarsa,

"Abbu yaji..."

Hannun ta mika masa tana kuka,

Rike hannun nata yayi baiyi wata wata ba yasa dan yatsan abakinsa ya fara tsotse mata shi,

Kanta ta kwantar acikin kirjinshi tana jin wani sanyi har cikin ranta,

Tsotsar dan yatsan nata yaci gaba dayi yanayi yana hura mata iskar bakinshi a wurin, acikin zuciyarsa kuma yana tuna rak'i irin na mata su mata babu wuya sun yiwa abu kuka komai kankantarsa.


In banda haka menene abin kuka dan yaji yashiga wurin da ta yanke,

Cusa kanta cikin jikinshi take tayi tana shakar kamshin turarensa na _beautiful touch_ wanda ya cakudu da kamshin _special oud_ ita dai arayuwarta tana tsananin son jabir domin jin sonshi take har acikin jinin jikinta yana yawo,

Mak'aleshi tai tayi shikuma sai tsotsar yatsan nata yake yana hura mata iska awurin, gaba daya ta gama shagala sai kamshinsa take shaka mai mutukar dadi, hakika babu abinda yafi kamshi dadi ajikin mutum musamman ma Ma'aurata amma wasu mazan sam tsafta bata damesu ba harma wasu matan suma

Please Login or Register in order to submit comment