Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shirya ta tafi office, lokacin da taje GM din bai zo ba dan haka ta zauna tafara karanta jaridar sa da aka kawo masa, tana cikin karantawar ne ta jiyo kamshin turare mai mutukar dadi hakan ya sata tsaida idanuwanta akan hanyar shigowa, minti kadan ya bullo yana sanye da farar shadda sai kyalli take dinkin tazarce, kansa dauke da hula ja yana amsa call, cikin sauri ta mike tsaye tana yi masa sannu da zuwa, hannu kawai ya daga mata ya wuce cikin office dinsa.


Mintuna biyu da shigarsa ta dauki jaridunsa guda biyu ta shiga office din,

Good morning sir"

"Morning" yafada ba tare da ya dago ya kalleta ba, jaridun ta ajiye ta juya ta fita, zama tayi tana tunanin to shi wannan wanne irin mutum ne ? Sai dai kuma fa yanayinsa da wannan dabi'un nasa sun burgeta saboda ita mutum marar hayaniya yana mutukar burgeta maganar Massinger ne ya katseta,

"Oga yana kiranki"

Cikin sauri ta mike ta shiga ciki, ta tsaya "gani sir"

Rubutun da yake yi yaci gaba dayi, "yau ba aturo min wani mail daga office din governor ba?"

"Eh ba aturo ba sir"

"To zasu turo,idan an kawo ko bana nan ki turawa director personnel, meeting za muyi da governor zasu bayar da kwangilar gina gidajen ma'aikata guda dari biyar"

Idonta kyam akan bakinsa yanda yake mul mul da baki yana yi mata bayani ita dai wannan bakin nasa yana burgeta, jin shiru bata amsa ba yasa shi dagowa ya kalleta kur yaga ta kura masa idanuwa ko kiftawa ba tayi,

"Kina jina?", yafada tareda dan buga teburin gabansa, firgigit tayi ta fara yan kame kame,

"Yes sir, zasu kawo, eh zan kawo maka"

Girgiza kai yayi yace "you can go" acikin ransa kuma yana cewa "anya kuwa wannan yarinyar kanta daya? Sai ayita yimata magana amma ba zata amsaba sai dai ta zubawa mutum ido"

Tana fita taga wasu baki sunzo su biyu mata nan tafara binsu da kallo daya bayan daya,

"Ya akayi?" Tafada lokacin da take zama akan kujerarta,

"Sannu sakatariya munzo ganin malam jabir ne" daya daga cikin bakin tafada,

"Yasan da zuwanku? Shi ya baku appointment?" Tafada tana yatsina fuska

"Eh shine yace muzo office mu sameshi"

"To yanzu dai bazai samu damar ganinku ba saboda aiki yake yi" tafada tana janyo drawer zata dauko wani file,

"Haba ranki ya dade ki shiga ki sanar masa mana idan yaga zai ganmu sai mu shiga idan kuma bazai ganmu ba ahikenan"

"Bazai ganku ba"

Mikewa sukayi suka fita zukatansu babu dadi, kallo ta bisu dashi "an fada muku ina haukane da zan barku ku shiga wurin wannan zankadeden? Ai wannan nawane" tafada tana murmushi.

Tun daga wannan rana goodness ta bullo da sabon salo domin duk bakuwar da tazo ganin GM bata barinta ta shiga mazan ma sai tayi niyya, yauma tana zaune akan kujerar ta ta hada tea saboda lokacin da ta fito daga gida bata yi breakfast ba, wata mata ta shigo yar madaidaiciya da ita tasha les mai tsada tana ta kamshi tace tazo ganin GM nan goodness tace baya nan, matar tace "munyi waya fa dashi shine yace nazo yau"

Karkacewa goodness tayi tace "to sai ki kirashi ki fada masa ai"

Juyawa matar tayi tafita tana zaro wayarta daga cikin jakarta, ko minti biyar ba ayiba sai gashi ya fito da kansa, kanshi ko hula babu hakan ya kara masa kyau,

"Meyasa idan nayi baki bakya zuwa ki fada min sai dai kice musu bana nan? Wannan aikin nasaki?

"Sorry sir" tafada tana kallon fuskarsa,

"Yanzu kinga meeting zamu yi da S. A ta commerce and industry amma tazo kince mata bana nan alhalin kuma abinda zamu tattauna da ita abune mai muhimmanci"

"Sorry Sir" tafada tana zare ido,

"Bani mail din da aka kawo min daga code of conduct bureau"

Hannu ta mika ta zaro takakardar cikin rashin sa'a kofin shayin data hada ya tuntsire akan takardar tare da sauran files din dake kan tebur din.






_*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ»
[10/28, 9:26 PM] β€ͺ+234 810 100 9022‬: [8/21, 2:52 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_16-20_


~~~Kallonta yayi da manyan dara daran fararen idanuwansa ya juya ya koma office ba tare da yace da ita komai ba, hakan ya sake rudata,

_"ohh God help me pls, pls God"_ tafada arude lokacin da tafara diri diri acikin office din,

"Allah yasa kar oga ya bani query yau"

Hankalinta atashe ta dauki mail din ta bashi cikin office dinshi, lokacin da ta shiga baya kan kujerarsa, yana can kan wata doguwar kujera ta zaman baki, ya dora kafafuwansa akan dan glass table din dake gaban kujerar, yana kallon wata tasha a satellite wacce aka saka karatun alwur'ani mai girma, indai bata manta ba tun lokacin data fara shigowa office dinshi wannan channel din taga yana kunnuwa koda yaushe,

"Am sorry sir" tafada tana rikeda takardar,

"Je ki dorata akan table dina" yafada ba tare da ya kalleta ba domin idonshi yana kan TV,

"Thank you sir" tafada tareda juyawa ta nufi kan table dinshi ta dora mail din ta juya ta fita daga cikin office din zuciyarta cikeda murna.

Karfe biyar ta tashi ta tafi gida tana zuwa ta tarar da sister dinta tazo anty bilkisu sai dai ita musulma ce, suna zaune itada mahaifinsu suna hira goodness ta shiga kunnenta sakale da earphone tana sauraren d banj cikin wakarsa ta _a new day has come_ tana bin wakar ta shiga falon, ganin anty bilkisu yasata dariya, "hey when did you come?"

"Tun safe nazo ashe kin fara zuwa office?"

"Inata so ai nazo gidanki na fada miki ban samu time ba"

"Ayya babu komai Allah ya sanya alkairi" yayar tata tafada tana kare mata kallo yadda ta dame cikin wasu riga da wando,

"Amin, ma taje church ko?"

"Tun dazu ta tafi" inji mahaifinta,

"Oh make i quick because we have weekly prayer today" tana gama fadin haka tayi wurgi da jakarta ta shige daki ta dauko bible dinta ta ajiye akan kujera, ta shiga kitchen ta zubo abinci, sakwara miyar agushi, kusa da anty bilki tazo ta zauna tafara cin abincinta tana cewa "anty ya mijinki? Ranan mun dawo daga church nida promise da ma mun ganshi amma shi bai ganmu ba"

Murmushi anty bilki tayi "ya fada min shima ya ganku" amma acan kasan ranta wani bacin rai takeji marar kwatantuwa, ace mahaifiyarta da yar uwarta basu bawa annabi Muhammad (S.A.W) gaskiya ba,

Mintuna kadan ta cinye abincin ta dauki Bible dinta tafita tana cewa "anty idan nadawo na sameki to, idan kuma kin tafi kigaida mijinki"

Tana fita anty bilki ta dubi mahaifinsu, "yanzu baba haka zamu ci gaba da ganin mama da goodness suna zuwa church? Addininsu daban namu daban yanzu hakan yayi daidai?"

Girgiza kai yayi "Bilkisu halin mahaifiyarku sai ita, da ace tanada rabon musulunta da tuni ta musulunta to bata da rabo, tun kuna yara kanana ni na musulunta amma ita taki saboda macece mai taurin kai da kafiya, ke kuwa lokacin da ta fahimci kina sha'awar musulunci tun daga nan ta tsaneki tamkar ba itace ta haifeki ba, da salla babu abinda take miki haka zata barki kaca kaca dake amma idan Christmas tazo kar kiso kiga irin kwalliyar da take yiwa goodness, nidai ina nan ina yi musu addu'a akan Allah ya shiryar dasu, kema kici gaba da addu'a kinji?"

Kwallar idonta ta share saboda tabbas tasan tasha wahala a hannun mama dalilin bin mahaifinta da tayi ta taso a musulma dama yar gata sai goodness itace shalele saboda halinsu daya da mama wurin kyamar addinin musulunci, su a kafiran ma yan akida ne,

"Babu komai baba, zanje nakoma" tashi tayi tareda ajiye masa wasu yan kudi wanda ba zasu haura dariya shida ba domin yanzu baya aiki ya jima da yin retire.

Lokacin da goodness ta taso daga church tare suka taho da saurayinta promise, wata yar karamar robar giya ya dauko daga cikin aljihunsa ya fara kurba,

Bata rai tayi ta dauke kanta, "promise am tired with your habit, baka da aiki sai shan giya? Gaskiya yana da kyau ka daina shan giya, kazama dan gayu kadaina wadannan halayen"

Kallonta promise yayi da kyau "goodness har lokaci yayi da zaki fara cewa kin gaji halayena? Goodness kece kuwa, nine fa promise dinki masoyinki, ko har kin fara mantawa dani ne?"

"Ni ba wannan maganar nake maka ba kawai dai ina son kadaina wannan shan giyar ne"

Jijjiga kai yayi yace "good kije gida zanzo nasameki agida"

Batare da tace masa komai ba ta wuce tabarshi awurin tana tunanin ita yanzu koda zata auri promise to sai ya koma irin oganta na office wato GM, kai bama ta tunanin zata iya auran promise din.

Lokacin data koma gida kwanciyarta tayi ta kunna irin wake wakensu tana saurara domin akwaita da son kida kullum bata da wani aiki sai sauraren wakoki kusan duk sabuwar wakar data fito tana da ita, shigowar ma da promise ne ya katseta ta tashi zaune, ma tazo kusa da ita ta zauna tana cewa,

"Wake up, meya hadaki da promise?"

Kallonsa tayi sannan ta kalli ma "ma cewa nayi ya daina shan giya"

Wata tsawa ma ta daka mata "shut up, naughty girl,idan baisha giya ba me kike so yasha? Baki san nida har burkutu nake dafawa nake sayarwa ba? Babanki ne da ya musulunta yazama musulmi ya hanani sayar da burkutu, kuma bari kiji tunda yanzu kin samu aiki to bikinku keda promise ya kusa,kin jini?"

Daga kai tayi, tashi ma tayi ta wuce daki, tana ganin haka itama tawuce dakinta ba tareda ta kalli promise ba, tun daga lokacin taji ta tsani promise ta tsani halinsa ko church taje bata kulashi church dinma abinda yasa take zuwa saboda ma na daya daga cikin manya manyan church dinne da daina zuwa zatayi takoma wata.

Yau tunda tazo office take baza idanun ganin GM amma shiru yau bai zo ba, wani file director planning yaturo ta bayar kuma file din yana office din GM shine last wanda tayima sending din file din dan haka ta tashi ta shiga office dinshi,

Office din sai kamshin turarensa na explorer yake yi tamkar yana ciki, kan table dinsa taje ta fara duddubawa amma yawancin abubuwan dake kan table din littattafai ne da suka shafi addini, drawer tafara jawowa tana dubawa nan dinma duk littattafan sane na addini, jijjiga kai tayi ganin yanda har a office ma koman shi na addini ne, dakyar ta iya gano file din karkashin wata drawer dauka tayi ta fita.

Yinin ranar tayi shine cikin rashin jin dadi wanda ita kanta ta kasa gane dalili amma tafi alakanta hakan da rashin ganin GM, nan kuma zuciyarta ta shiga gargadinta gamida tunasar da ita,


"Ke goodness karfa ki jawowa kanki abinda zai dameki saboda mutumin nan tsarinsa da naki ba daya bane, addininsa da naki ba daya bane, al'adarshi da taki akwai banbanci kuma koda ace yana sonki to ba lallaine ma ta yarda kuyi aure ba saboda ita tafi sonki da promise bata son ki auri bahaushe" zuciyarta ta lissafo mata wadannan bayanai alokaci guda,

Tabbas hakane to amma ai shi so babu ruwansa da addini ko al'ada farat daya yake shiga koda ba a shirya masa ba, kasa hakuri tayi ta koma cikin office dinshi anan ta samu visitors cards dinshi birjik, guda daya ta dauka ta koma falo ta kwafi phone number dinshi ajiki tafara kiranshi ba tareda tasan abinda zata fada masa ba gashi gabanta sai faman faduwa yake dum dum,

Kamar baza adauka ba sai kuma taji ya dauka cikin sanyayyiyar muryarsa mai haifar da kasala yace "Assalamu Alaikum warahmatullah,wabrakatuhu"

"Hello sir" tafada a diririce,

"Yes" yafada ahankali,

"Ina yini sir? Yau baka shigo office ba gashi kanata samun visitors sir" ta shararo karya saboda bata da abunda zata fada masa,

"Lfy, ki basu hakuri su dawo next time, nayi tafiyane amma yau zan dawo, gobe zan shigo office"

"Ok sir adawo lafiya" bai bata amsa ba ya yanke kiran, duk da haka taji dadin jin muryarsa sosai, murmushi ta dan saki sai kuma ta bata rai saboda tuno promise da tayi, ita yanzu a duniya babbar matsalarta bata wuce promise ba, bayan shi bata da wata damuwa domin tasan auren Malam jabir kamar tayi ta gama ne.

Washe gari da safe 8:30 ta shiga office lokacin duk sauran ma'aikatan basu zazzo ba hatta shi kanshi ogan bai iso ba hakan yasata shiga office dinshi ta dane kujerarshi tana juyi tana cewa "lallai oga yana shan laushi, ashe ni akan kashi nake zama ga inda laushi yake"

Juyin da zatayi taga ya bude kofa ya shigo, zumbur ta mike jikinta yana rawa,

"Welcome Sir, sorry sir" tafada atare,

Kujerar baki ya nufa yaje ya zauna ita kuma tamkar wata munafuka ta fara takowa tana kallon kasa, daidai lokacin driver dinshi ya turo kofa ya shigo hannunsa rikeda wani kyakkyawan yaro wanda da gani babu tambaya tasan dan oga ne, jarida driver ya ajiye agabanshi ya juya ya fita, kusa dashi yaron yaje yazauna tareda kwanciya ajikinshi,

"Good morning sir? Dama ina duba letter headed ne zan tura mail shine kazo ka sameni" tafada idonta akasa,

"Kin ganta?" Ya tambayeta yana kallon jaridar da yake dubawa,

"No sir ban gani ba"

Tashi yayi hannunsa rike dana yaronshi ya nufi kan kujerarshi,

"Abbu kekena ya karye" yaron ya fada tareda dalewa jikin kujerar dake gaban teburin baban nashi,

"Kabari kar kaji ciwo" yafada ahankali,

"Abbu cikina yana fashewa kaji"

"Menene fashewa" yafada yana jawo drawer din table dinshi,

"Abbu abinci da yawa ne yasa cikina yake fashewa"

Dan murmushi goodness tayi ta karbi letter headed din ta juya zata fita,

"Abu zanje gurin baba idi driver" bai jira amsar uban ba ya ruga da gudu har yana bige goodness, tana fitowa ta ganshi a kasa yana kuka,

"Sorry big boy stop crying" tafada tareda dagashi, daukarshi tayi taje ta zauna akan kujerar ta,

"Kadaina kuka kaji"

Kai ya daga mata yace "dama bana yin kuka, abbu yace ni namijine na rinka abu irin na maza, kuka ba na maza bane na matane",

Fashewa da dariya tayi ta shafa kansa, "ya sunanka?"

"Al'amin jabir m Ahmad" yafada yana goge idonsa da bayan hannunshi,

"Muje na siyo maka chocolate ko?" Girgiza mata kai yayi,

"No thank you, abbu yana siyo min da yawa"

"To muje ka rakani ni in siyo nawa"

Kudi ta Zara a jakarta ta kama hannunshi suka fita aikin da zatayi ma bata bi ta kanshi ba haka ta tafi ta barshi, can bakin titi sukaje ta siyo chocolate packets biyu ta siyo biscuits manya manya guda biyu,acan kuwa sai nemansu ake yi basa nan gashi GM yana son tafiya dama ba zama yazo yi ba unguwa zaije shiyasa ya taho da al'amin din, lokacin da su goodness suka zo yana cikin mota yana jiran al'amin da ma'aikata suka bazu nemanshi office office, sai zubawa goodness labari yake kamar dama can ya santa,

Kayan ta danka masa a hannunsa "ungo kayanka kaji idan kaje gida kasha kai kadai kar kabawa brother dinka"

"Banida brother ni kadai ne" yafada yana dariya irinta ta yara,tareda shigewa cikin mota yana tsalle ajikin abbunshi,

"Abbu kaga chocolate dina"

GM baice komai ba sai kallonshi da yayi yakuma maida kallonshi jikin window nan ya hango goodness tana dagawa al'amin hannu.


Tun daga wannan rana bai dawo office ba saima tafiya da yayi zuwa jihar katsina nan goodness ta shiga cikin damuwa amma kullum cikin yi masa waya take tana fadar karya da gaskiya dan kawai taji muryarsa shi kuwa baima san tana yi ba, ganin irin mutanen da suke zuwa wurinshi yasata tambayar massinger dinshi kodai GM yanada traditional tittle ne? Murmushi yayi yace da ita kawai dai malamin addini ne shiyasa mutane suke zuwa sosai hakan ba karamin dadi yayi mata kuma dama taga alamun hakan sai dai ita ahalin yanzu tana cikin matsala domin ma tafara tasowa da maganar bikinsu da promise wanda ita kuma yanzu bashi take so ba.




_*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ»
[8/22, 9:02 AM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_21-25_


~~~Bayan ta tashi daga aiki tana komawa gida ta samu ma zaune tsakar gida tana tace gasarar koko yau da alama ba taje church ba ko kuma taje da wuri ta dawo,

Agajiye ta zauna tana kallon ma "ma sannu da aiki"

"Yawwa my daughter, daga gani kin gaji"

"Ma nagaji sosai wlhi, ina baba?"

"Bai jima da fita ba, sannan gobe ne birthday din promise dan haka gobe ba zakije office ba church za muje, gobe zaki sawa promise zoben alqawari (promise ring) shima zai sa miki, daga nan kuma sai maganar biki"

Wata uwar faduwar gaba goodness taji saboda jin maganar da ma tafada nan ta bata rai ta kalli ma,

"Ma nifa yanzu bana son promise, akwai wanda nake so, shi promise kwata kwata bai dace dani ba ni bana son mai shan giya"

Ido cikin ido ma take kallonta "waye wanda kike so?"

Cikin faduwar gaba tace "ma oganmu ne a office"

"Musulmi ko? Bahaushe? Kina so ya aureki ya sakeki ko? Hausawa saki suke yi gashi suna yin kishiya saboda su basa yin auren zobe"

Daga kai tayi "ma nayarda indai zai aureni"

Matacin gasarar ma ta saki yafadi a kasa tana tafa hannu "oh chineke, goodness you want to marry hausa man? You want to marry a person that your religion and his religion are not the same, the man that your tribe and his tribe are not the same even your culture are not the same with his own culture, hmmm any where, tunda haka kin zaba, Allah yabaki sa'a amma idan kika auri hausa man duk abinda yayi miki babu ruwana, kar ki zo wurina and lastly koda kin auri hausa ba zakibi addininsu ba, idan kikace zaki bi addininsu sai na kasheki goodness"

Ajiyar zuciya goodness ta saki "ma kin san dai nima ina son wannan addinin namu bazan iya rabuwa dashi ba dan haka ki daina doubting akaina"

"Goodness in kin bar addininmu kin karbi nasu sai na tsine miki albarka, sai nasa Allahnmu yayi fushi dake"

"Ma bazan karbi addininsu ba kidaina fadin haka"

Tashi ma tayi ta kinkimu bokitin gasarar ta tayi kitchen dashi tabar goodness da tagumi tana tunanin yanzu ta ina ya dace tafara tunkarar auren GM? Tambayar da tayita nanatawa zuciyarta kenan.

Daren ranar ba tayi bacci ba, asussubar fari ta dauki bible ta tafi church lokacin ma ta dade acan tana zuwa ta shiga sahun masu bauta ta zuba gwiwoyinta a kasa ta rufe ido ta fara addu'ar samun nasara awurin Malam jabir, sai da rana ta fito sannan ta dauko jakarta ta dawo gida tana kiran _"fire, fire"_ domin su a church dinsu wuta suke bautawa (Allah yayi mana tsari da ita)

Tana zuwa gida wanka tayi ta shirya cikin riga da wando matsattsu ko tea bata sha ba ta nufi office, karfe _9:00_ ta isa lokacin har GM ya dade a office dan haka jakarta kawai ta ajiye ta nufi cikin office dinshi domin ta kagu taga kyakkyawar fuskarshi gashi zuciyarta sai harbawa take yi fat fat,

Kwankwasawa ta danyi kafin ta bude kofar ta shiga, can ta hangoshi zaune kan kujerarsa hannunsa rikeda wani littafi wanda ba zata iya tantancewa ba yana dubawa sannan ya kunna karatun alqur'ani kasa kasa yana saurare, yana sanye cikin farar shadda mai kyau sai kyalli take, kusan duk kayansa farare ne a yanda ta fuskanta domin bata taba ganinshi da wasu kalar ba daga fari sai milk colour,

"Good morning sir" tafada tare da dan durkusawa,

"Morning" yafada a hankali, sanin bazai kara magana ba ya sata juyawa zata fita,

"Am kinga" yafada ahankali, hakan yasa ta dawo tace "na'am sir"

"Kidaina irin wannan shigar idan zaki fito office, ki rinka sako normal kaya saboda nan kinga cikin mazane kuma mu a addininmu hakan bai dace ba, kamar yadda kuma a addininku hakan laifi ne, dan Allah akiyaye"

Kur tayiwa dan karamin bakinsa da idonta lokacin da yake mata magana, dagowa yayi ya kalleta yaga itama shi ta kurawa ido,

"Kinji abinda na fada"

Sai alokacin ta dawo hayyacinta "yes sir, nagode sir"

"Ok kina iya tafiya" yafada tareda mayar da idonsa kan littafin da yake karantawa,

Office dinta ta koma ta zauna tana murmushi amma kuma zuciyarta har yanzu bata daina bugawa ba, tunani tafara yi itafa duk kayanta totally babu atamfa domin bata dinkasu kuma ko ta dinka ba dinkine na cin mutunci domin sai anyiwa atamfar kaca kaca kafin a dinkata, sai anyi mata gutsi gutsi, dan haka kayanta daga riga da skirt sai riga da wando amma duk da haka zata daure ta zabo masu dan dama dan ganin tabi maganar da ya fada mata kuma hakan da yayi ba karamin sake burgeta yayi ba.

Da yamma ta tashi daga aiki ta koma gida, a kofar gida ta hadu da nura cikin murna ta jashi cikin gidan domin dama tana son ganinshi,

"Yanzu kin zama worker kinyi wuyar gani ko?" Nura ya fada ya dariya,

"Sorry nura dama inata son nayi maka waya, nura dan Allah ka taimakeni ka sanar dani wani abu dangane da GM dinmu domin zuciyata ta kasa kyaleni in huta"

Kallonta nura yayi "ban fahimceki ba, wai malam jabir kike nufi? Me ya faru?"

"Nura nothing, i beg ka fada min pls nura, am in bad condition, ina bukatar jin wani abu game dashi domin ina son na aure shi"

Zaro ido nura yayi "aure? Aure fa kikace goodness, taya kike tunanin wannan auren naku zai yiyu kina Christian kina ikirararin Allah ukune, kina mai yarda da cewa Annabi Isah Allah ne, kina cewa Maryam Allah ce, kina cewa Isah dan Allah ne, shikuma mal jabir yaki yake da wannan kalmar, kiran mutane yake akan su daina furta wadannan kalmomin, kira yake abi Allah shi kadai,tayaya wannan hadin naku zai yiyu? Da ace shi ba malami bane mai wa'azi tabbas may be zai iya aurenki, to amma shi mai wa'azi ne malamine wanda yayi suna ba a iya kasar nan ba har da sauran wasu kasashe na musulmai ai kinga abun kunyane agareshi aji yana auren wacce ba musulma ba"

Ajiyar zuciya goodness ta sauke mai nauyi "gaskiya ka fada nura amma kuma ni rashin aurenshi agareni wlhi tamkar rasa rayuwata ne dan Allah nura ka taimakeni" ta fadi hakan lokacin da kwalla tafara bin kumatunta,

"Shikenan goodness babu komai zan taimaka miki domin nasan haduwarki da malam jabir _*Wani Haske*_ ne acikin rayuwarki, zan taimaka miki har kikai ga samun wannan hasken, yanzu kin san ya za ayi? Zanje gidansa anjima da daddare zan halarci majalissinsa inda yake karantarwa bayan sallar magrib anan zan nemi fatawa cewar wata wacce ba musulma ba ta ganni tana sona shin zan iya aurenta? Kinga anan zan gane ko zai yarda ya aureki ba tare da kin musulunta ba"

"Good nura nagode sosai, ina jiranka idan ka dawo"

Tashi nura yayi ya fita a lokacin ma ta shigo tana rikeda bible dinta "hey goodness, meya hanaki zuwa church? Am asking you meyasa ba kije church ba? Kin fara wasa da addinmu ko goodness? Idan kinci gaba da haka pastor will punishe you nikuma ba ruwana ehem"

"Sorry ma dawowana kenan daga office, gashi nagaji shine nabari sai da daddare zanje church din night service"

Fara,a ma tayi cikeda murna tace "i like you my daughter, God bless you, ina babanki fa?"

"Ma babu kowa agidan lokacin da na dawo ina jin ya fita"

Kada kai ma tayi ta wuce cikin daki tabar goodness zaune anan zuciyarta tanata harbawa domin rashin sanin abinda nura zaizo mata dashi.

Kamar yadda nura yace haka yayi bayan an tashi daga karatu ya dubi malam jabir yace "malam ina da tambaya, wata yarinya ce ta yaba da nagarta ta kuma ta yaba da rikon addinina da halayyata tace tana son na aureta to amma fa ita ba musulma bace, mahaifiyarta ma ba musulma bace mahaifinta kuma musulmi ne, to malam ya halarta na aure ta?"

Kallonsa malam jabir yayi yana murmushi "ya halarta ka aureta,addini ya baka dama amma sai ta kasance wacce ba mazinaciya ba, sai ta kasance ya ba baiwa ba wannan shine sharadin, addinin Allah mai saukine, babu haramci a auren ma'abota littafi kwata kwata sai dai idan mutum bashida ra'ayi ne domin ba kowanne mutum ne zai auri wacce ba musulma ba, kaga kamar ni idan ka bani wacce ba musulma ba bazan aureta ba saboda wasu dalilai amma nasan aurenta ba haram bane".

Daga kai nura yayi dama tun farko abinda ya zarga kenan, "to malam amma misali idan kaga yarinyar zata fada cikin wani hali marar kyau ai zaka aureta ko?"

Murmushi malam yayi har sai da hakoransa suka fito "kune yara ku

Please Login or Register in order to submit comment