Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sahu, zasu tsallaka titi, mota ta kad'e maman Aisha, ikon Allah kenan ita Aishar sai tayi gefe, ko kujewa batayi ba, kan kace me, jini ya wanke maman Aisha, ta hancinta da kanta da idanuwanta, babu inda baya zubar da jini, sosai take kuka, duk da ba wata babba bace amma zata iya cewa tasan zafin mutuwa, tun a rashin babanta takejin duniyar tayi mata sauyi.
Da sauri mai motar ya fito, yana cewa "a kaita asibiti mana, mutane suka taru a gurin kama daga kan mabaratan gurin har wasu da suke zazzaune a shagunansu, kan kace me, sukaga numfashin mama yana kaiwa da kakowa, ta d'aga hannunta sama, cikin murya wacce babu mai iya ganeta, tanason gayawa Aisha magana, Amma ta kasa, ana shirin sakata a mota rai yayi halinsa,
Dole aka wuce da ita gida, Aisha na kuka tana nuna hanyar anguwarsu, tashi d'aya mutanen anguwar suka cika gidan, tunda sukaji labarin abinda ya faru, wasu na tofa albarkacin bakinsu wasu na Allah ya gafarta mata, wata ko cewa tayi, k'arshen tika-tiki ne Allah ya nuna tare da aya (darasi) akan masu zuwa bara, saboda rashin nuna godiya ga Allah,
Aisha kam tasha kuka,
Baba Indo na dawowa taji labarin rasuwar maman Aisha, a gurin ta durk'ushe tana kuka, kamar bazata dena ba, a fili tace "wannan (izna)ne garemu, insha Allah daga yau, na ajiye maganar bara, abinda na samu ya isheni, matan dake zaune sai kallon Baaaba Indo sukeyi, inkaga inda take kuka kamar uwarta ce ta rasu, suna zaune sai ga Khalil ya shigo...


*🫦 TSAUTSAYIN TAUNA🫦*

*Zainab Habib (Mom Islam*



Last free page


19-20



Tun daga nesa, idan ka kali fuskarsa zaka gane yaji labarin mutuwar maman Aisha.
"Aslamu alaikum"
Khalil yayi sallama cikin cold voice d'insa,
"Wa'alaikumussalamu"
Mutanen gurin suka amsa, idonsa bai gane masa kowa ba, sai Aisha daya hango a ra6e tana kuka, a hankali ya isa gareta ya ruk'o hannunta.
Mutane na cewa "to shi waye daya fice da ita?"
Baaba Indo ta katse musu zancen ta hanyar cewa "dan uwanta ne"
Dole sukayi shiru.
Sai wajen k'arfe uku aka kaita gidanta na gaskiya,
Mutane sun ragu ba kamar d'azu ba, su baaba Indo na zaune, sukaga mata su uku, da maza biyu,
Sannu da zuwa sukayi musu, a zahiri babu wacce ta gane ko su waye, bayan sun zauna an kawo musu ruwa da abinci, sunyi gaisuwar rasuwar, babban cikinsu Wanda zeyi shekaru 70 yace 'nine mahaifin Ladi, wata mai kamada maman Aisha, tace "nikuma nice mahaifiyar Ladi, ta nuna d'ayan namijin tace "wannan shine k'aninta matarsa daya da Y'a'ya biyu, ta nuna matan dake zaune a gefenta kana ta Kuma cewa, su Kuma y'an uwana ne".
Anan aka kuma gaisawa, baban Indo na mamakin inda akayi iyayenta sukaji rasuwarta, alhalin tunda sukayi aure da baba Haladu basu ta6a koda waya ba.
Kuka maman marigayiya Ladi ta fashe dashi, tare da Dana sanin fushi da tayi da y'ar tata, shiko mahaifinta kukan zuci yake, wanda yafi na fili ciwo.
Baaba Indo tace "yanzunnan aka fita da Aisha, maman Marigayiya tace "au yaransu nawa?" Baaba Indo, tace "d'aya itace Aishar"
Tunowa da ba sune suka haifeta ba, tasa jikin baban Indo yayi sanyi, a ranta tace "wai nikam ya za'ayi da yarinyar nan oho? gashi babu wanda ta sanarwa , labarin yarinyar, amman nasan Malam Mani yasan labarinsu akan koma meye, wata k'ila shine ya gayawa iyayenta rasuwar, bazai kasa sanin labarin Aisha ba, tunda abokin Haladu ne na gaske, bacci ke rabasu".

Khalil na fita da Aisha ya zarce da ita gidan yarinyar k'anwar momynsa, mai suna  Bahija, shekararta uku da aure, har yanzu Allah bai bata aihuwa ba, da mahaifiyar Bahija da momyn Khalil uwa d'aya Uba d'aya, amma momyn Bahija tana Kano da aure, ita kuma momyn Khalil anan Kaduna take, Bahija na anguwar Badarawa.
Gidane, tafkeke tsararre, Wanda aka narka nerori gurin ginashi, mijin Bahija yana na uku a masu kud'in garin, Bahija fara ce tass gata da dogon hanci, tanada yalwar gashi amman ba doguwa bace, ba Kuma asalin irin guntayenan ba,
Nocking Khalil ya farayi, a hankali, jin shiru yasashi danna door bell, cikin shigarta ta alfarma ta bud'e musu k'ofa fuskarta d'auke da fara'a, tunda suka shigo gidan gaban Aisha ke dukan uku-uku, a tunaninta gidan yankan kai tazo,
Khalil ya kamo hannunta suka k'arasa ciki,
Khalil ya zauna tare da zaunar da ita a gefensa, Bahija ta shiga kitchen ta had'o musu juice mai watermelon da coconut mai sanyi, tana ajiyewa Khalil ya d'auka ya tsiyayawa Aisha ya mik'a mata a glass cup kana yace "me kikeso a dafa miki?"
Har ta bud'e baki zatayi magana, Bahija ta fito hannunta rik'e da trai, wanda yake d'auke da kayan marmari, ajiyewa tayi akan table d'in dake gabansu, kana ta zauna har yanzu fuskarta d'auke da murmishi.
"Ina yini yah Khalil ya aiki ya girma ya Kuma su momy?"
Sai da yaja mata ajin nasa na fama kafin yace "lafiya Ina megidan?"
"ai yayi tafiya tun last week amma next tomorrow yana hanya"
Bahija ta fad'a tana kallon Aisha da kanta ke k'asa tana wasa da y'an yatsunta.
"Allah ya dawo dashi lafiya, daman na kawo miki y'ar taya hira ne, idan kina sonta?"
Jikin Bahija yahau rawa cikin farinciki tace "a ina ka samo beautiful girl haka?"
Khalil yayi murmishi kafin yace "a tak'aice dai mahaifiyarta ta rasu, haka Kuma mahaifinta shima Allah yayi masa rasuwa, ina gudun rayuwar da yarinyar zata shiga, dangin mahaifanta bawai sun damu da yarinyar bane, to nidai bansan dalilin da yasa suka juyawa mahaifiyarta baya ba"
Bahija da batada wuyar kuka ta share hawaye kafin tace "Allah sarki yar albarka zonan"
Aisha ta taso jiki a sanyaye ta isa gurin Bahija,
"Yah Khalil inhar Jawad ya yarda ni zan d'auketa, hatta karatunta zan d'auki nauyinsa insha Allah, dan Allah kar akai kyakkyawar yarinya irin wannan k'auye, haba"
Ta rungume Aisha.
Hankalin Khalil ne ya kwanta sbda ganin jininsu ya had'u, kuma yasan koba haka ba Bahija bazata watsa masa k'asa a ido ba.
Amman yau zamu koma, gobe zamu dawo, idan iyayen sun yarda to, zamu dawo idan kuma kikaji shiru to ki cire rai"
Rau-rau tayi da idanu, kafin tace "haba Yah Khalil kayi fatan su yarda man"
Ta dinga bawa Aisha kankana dasu abarba a baki, da juice har Saida ta ture.
"Ayi miki girki ne?"
Bahija ta tambayi Aisha"
Cikin sanyin murya Aisha tace "na k'oshi"
Ganin lokaci na k'urewa yasa Khalil d'aukar cup ya zuba juice d'in ya kur6a kana ya ajiye, yace "Humaira zomu tafi"
Kallonsa Aisha tayi, ba'a cika gaya mata wannan sunan ba, sam danma tasan duk mai sunan Aisha Humaira ne, yasa ta mik'e ta rik'e masa hannu,
"Idan har sun amince please kafin kuzo kayimin waya, idanma basu amince d'in ba please ka kirani dan Allah"
Bahija ta fad'a zuciyarta babu dad'i.
Ba tare daya ce mata komai ba, suka fice.
Ya tsaya a parking space tare da jingina bayansa a jikin motarsa, kallo ya ke yiwa Aisha, kallon da batama san yanayi ba, kallon da ita kanta ma a k'asa yake, shi kad'ai yasan ma'anar kallon, ya d'agata can suka shiga mota, yayi horn mai gadi ya bud'e masa suka halba titi.
Lokacin da suka isa gidan k'arfe biyar da rabi yamma ta fara yi,
Baaba Indo ce ta hangosu, lokacin da suka shigo gidan, cikin d'aga murya take cewa "sannu Ibrahim Allah yayi albarka" a k'asan zuciyarta kuwa cewa take "Allah yasa dai be lalata y'ar mutane ba"
Khalil ya sake hannun Aisha kaf cikin mutanen dake zaune a gurin, yawanci mutanen anguwarsu ne, sai iyayen Ladi,
Tafi gane baaba Indo, tunda hasali ma tun tasowarta suke tare,
Ta wuce gurin baaba Indo, tana dariya, yaro kenan.
Baaba Indo kallonta takeyi tanason tambayarta amma babu hali,
Sai da ya ajiye musu 10k sannan yayi musu sallama ya fice.
Kafin ya tada mota ya dad'e yana nazarin inda za'ayi dangin mama su bashi Aisha, shi ba kowa nasu ba, balle ace sunsan halinsa ko wani abun.
Da k'yar ya janye k'afafunsa a gurin ya shiga mota, ya fara driving a hankali harya isa gida,
Yana isa bai zarce ko ina ba sai part d'in amaryar babansu wato Hajiya Amina, wacce yarinyar Hajiya  Hauwa take gurinta Husna, yana shiga ya zube kan kujera tare da d'aukan remote ya sauya channel, i' zuwa mbc action, Hajiya Hauwa da suke kiranta da Anty, a zahiri ya bata shekara biyu, amman tunda tazo a matsayin matar babansa yana girmamata fiye da tunani, ba kamar Nafisa da Salma da ko part d'inta basa shiga ba.
Hajiya Hauwa ta fito sanye da doguwar riga baka mai ratsin farin yadi, ta yafa d'an kwalin a kanta, tace "Khalil ka shigo kenan, two days naga ko zama a gida bakayi bayan kacemin ka d'auki hutu?"
"Sai da yayi jim kad'an sannan yace "wlhi anty ina zuwa bitar wani abunne shiyasa".
Suna cikin hira aka kira sallahar magriba.
Ya tashi ya tafi masallci, itama taje yin alwalah.

BAABA INDO.
Jan Aisha zuwa gidanta tayi kana ta kaita d'aki,
"Aisha ina kukaje da Ibrahim kuma meya miki?"
Aisha "Baaba Indo gidan yarinyar k'anwar momynsa ya kaini, wlhi gidan mekyau ga kayan dad'i"
Baaba Indo ta sauke ajiyar zuciya kana tace "beyi miki komai ba daiko?"
"Eh matar ma bata ta6a aihuwa ba injita wai zaku badani tana Sona, nimafa ina sonta"
Aisha ta fad'a tana wasa da hannunta.
Baaba Indo ta jinjina maganar, tare da yin tagumi,
"Uhm Allah gamu gareka, ita dai wannan yarinya bamu san iyayenta ba,bamusan a ina aka d'aukota ba"
Ta sake kallon Aisha taga wasanta kawai takeyi, kawar da zancen tayi ta hanyar cewa "ni da nasa usilinsa d'an arziki ne, da nasa an basu ke, kodan rayuwar da zaki shiga a wannan k'auyen, amma sai dai matsala d'aya, ba lallai kakankinki su yarda ba.

Ranar da akayi sadakar Uku ranar iyayen Maman Aisha suke shirin tafiya gida harda Aisha,
Sun kammala shiri, baban yaje taro musu mashin, sai ga Khalil nan shiga Baaba Indo, kana ganin yanayinsa zaka gane a cikin damuwa yake, ga wani uban numfarfashi da yake saukewa a hankali da alamu yasha gudu a mota,
A babbar tabarmar da aka shimfid'a suka zauna, Baaaba Indo ta fara magana,
"Dan Allah idan babu damuwa, kuma kun yarda da zaman mutunci da amanar da mukayi nida uwar yarinyar nan, kubarmin ita, zanba yarona, saboda matarsa bata ta6a aihuwa ba.
Baba ya kalli Inna wato kakar Aisha yace "tabbas bamu da abinda zamuce muku sai godiya, hak'ik'a kunyi k'ok'ari sosai, baaba Indo ta kafesu da ido tana jira taji hukuncin da zasu yanke.
Baba yace "Maman Ladi ko kinada magana?"
Mahaifiyar Ladi tace "a ganina a bar musu ita, amma ina gudun fad'awa wani halin, ke baba Indo mun damk'a amanarta a hannunki, ki kular mana da ita har zuwa lokacin da ta mallaki hankalin kanta".
Baaba Indo tace "insha Allah zaku sameni mai gaskiya da rikon amana".
Khalil ya sake yi musu godiya, yace "bari yara suzo su shigo da kayan abinci, kwayi tsaraba".
Su baba sukayi godiya, Khalil ya fice, bayan yayi musu Allah ya kiyaye hanya,
Baaba Indo tace "akwai kud'in Marigayiya dubu d'ari a hannun mak'ociyarmu, kuna ganin a kar6o muku ne?"
Jikin baba da maman na rawa sukace a kawo, Aiko ta fice ba'a jimaba sai gata,
Mik'a kusu kud'in tayi suka cigaba da shiri, k'arfe 10:11am suka bar gidan, bayan sun kar6i lambar wayar Baaba Indo itama ta kar6i tasu.

Su biyu ya rage a cikin gidan, daga Aisha sai baaba Indo, a d'akin mamanta kuwa, iya jakar kayanta ne a gurin, sai wata yankakkiyar katifa, duk sun siyar da kayan.

GIDAN ALHJI KABIR.
Sajida ce zaune a main parlo hannunta rik'e da alk'ur ani, suna karanta suratul yusif ita da yaronta Mubarak, shigowar Alhji Kabir ne yasa Sajida tace "Allahu akbar, sukayi adu'a suka ajiye alku'an d'in, Alhji Kabir ya zauna fuskarsa a 6ace ya kalli Sajida "nasan kina sane da zaman hak'uri nakeyi dake a cikin gidannan ko?"
Cikin rashin fahimta Sajida tace "haba Alhji ka fahimtar dani lefin da nayi maka, in yaso sai in baka hak'uri, dan Allah"
Ta kalli Mubarak tace "kai  Qur'an din d'aki".
Da sauri ya mik'e, shima mubarak din zuciyarsa babu dad'i bayajin dad'in wulak'antata da Dadynsa keyi ko kad'an, amma babu inda ya iya, saboda shi kansa ba sonsa dadyn yakeyi ba, shiyasa ma yake tsoronsa ko Kuma bayason dadyn yazo gidansu.
Alhji Kabir ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kana yace "na sakeki saki uku, babu ke babu ni! kuma kikace zaki tafi min da yaro wallahi kotu ce zata rabamu".
K'irjin Sajida yahau dukan uku-uku saboda tsananin firgici da tashin hankali Wanda ba'a samasa rana "wai wane irin gagarumin lefi tayi masa, daya za6i wulak'antata ta wannan hanyar"
Duk wannan maganar a cikin zuciyarta take yinta.
Ta sauko har k'asa tana kuka, kafin tace "Alhji duk da ka sakeni naji zan barmaka gidanka, dama banzo da yaro daga gidanmu ba, a gidanka ns sameshi,ka sani ko nanda shekara goma ne, Mubarak dole zai nemoni duk inda na shiga, Abu na biyu kuma inaso ka gayamin lefin da nayi maka, dahar ka za6i ka sakeni sakin wulakanci da tozarci?"
Dafe kansa yayi, lokaci d'aya ya d'aga mata hannu tare da cewa "kee!! Banason ganinki maza had'a kayanki ki fice oya, yana fadar haka ya mik'e tsaye, Sajida ta d'auko biro da takarda ta mik'a masa kana tace "rubutamin sheda anan"
Ya kar6a jikinsa na rawa ya rubuta ni Alhji Kabir Lawal na saki, Sajida saki uku bani babu ita kuma dana bazai bita ba"
Wasu zafafan hawaye ne suka kuma sauka a fuskarta a karo na biyu, ta share tare da ficewa daga gidan da gudu, saboda tana tsoron kar Mubarak ya fahimci halinda take ciki, zai iya barin gidan shima.
Bayan fitar Alhji Kabir ya dawo gidan Nafisa, zaune ya sameta ita da Saratu mai mallaka sunata hira harda shewa,  fuskarsa a sake, kamar ba shine yaje yaci mutuncin baiwar Allah ba, Saratu mai mallaka ta d'an zamo daga kan kujera ta gaisheshi, amsawa yayi cikin fara'a, Nafisa tace "my honey wannan k'awatace tanasona kamar ranta, jikin Alhji na rawa ya ciro 5k yace "tahau mota ya shige ciki.
Nafisa tace "k'awata in ta6aki da alkairi, a halin yanzu nasaka Alhji ya saki Sajida saki uku kuma nasan ya aikata, aikinki yana kyau".
Saratu mai mallaka ta saka shewa tare da cewa "ai kin wuce hakan K'awata, tunda Allah ya had'amu ai kingama samun komai a duniya da izinin ubangiji"
Nafisa tace "inason a cire masa son Sajida a cikin ransa kwata-kwata"
Mai mallaka tace "angama".
Sajida bata zarce ko inaba sai gidansu, tana isa ta zube a gaban Ammi, cikin tashin hankali Ammi tace "meya faru? gayami menene?"
Sajida na kuka tace "Ammi zan kwanta"
Saboda Sajida tanada wani masifaffen ciwo Wanda yake matuk'ar damunta, ciwon jinnu amman sai ranta ya 6aci, da sauri Ammi ta kama hannunta ta wuce da ita bedroom ta kwantar da ita, gumi babu ta inda baya karyo mata, Ammi ta kunna mata  A.C hade da kullo k'ofar ta fice.
Saratu mai mallaka tana komawa gida ta rataye mayafinta akan igiya ta to yada zango a tsakar gida, kan kujera yar tsuggunno, ta share gumin daya tsatsafo mata, tace "aiki ya sameni, dole inyi aikin da zan farauto zuciyar Alhaji Kabir, dole in shiga ata biyu, kokuma in fitar da Nafisa a gidan, ta inda zan baje inyi darshe-darshe...

#Aisha
#Khalil
#Nafisa
#Saratu mai mallaka
#Sajida

Love and romantic story😘
Cakwakiyar da baku ta6a tunani ba🥰


08141799224




An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment