Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

8:30"
"Akwai inda zakaje ne ana tsuga ruwa?"
"Hajiya wallahi Sajida ce tace tanason tuwon shinkafa miyar wake shine nakeson zuwa in sanarwa da y'ar aiki"
"Yo y'ar aikin dana koreta jiya Kuna tafiya?"
Hajiya ta fad'a tana ke6e baki,
Matsalar dai d'aya ce gashi mun Sami k'aruwa dole a nemo y'ar aiki a gidanan kodan Sajida ya'r albarka mai juna biyu".
Hajiya ta mik'e tana cewa "barinje kitchen d'in in dora mata ahincin"
Da sauri Alhj Kabir ya mik'e shima kana yace "no Hajiya bazakije girki ba zanje in siyo mata"
"Ina babu inda zakaje, jikan nawa zai zo duniya kacemin ba hakaba, kai Kabiru inaga nafika farinciki samun wannan rabo"
Tawuceshi, kai tsaye ya fito tare da shiga d'akin Nafisa, samunta yayi tana waya, yana shiga ta a iye wayar da sauri kamar mara gaskiya, "Nafisa kizo ki taya Hajiya d'ora abinci a kitchen"
Nafisa ta yamutsa fuska kana tace "bacin an kammala breakfast yana dining?"
"Eh nasan da haka kinsan Sajida na d'auke da juna biyu, to shine batason cin komai sai tuwon shinkafa miyar wake shine Hajiya ta shiga kitchen dorawa, kuma ai yakamata kije ki tayata"
"To naji"
Nafisa ta fad'a a tak'aice.
Yana fita ta d'auko wayarta ta danna number Safiya, ring d'aya ta d'aga "Safiya muna cikin waya dake Alhj ya shigo, shin baki kirasa bane ?"
Safiya tayi dariya kana tace "wannan alhjin naku sai ku hmm, yanzu dai me kikeso ?"
"Hmm"
Safiya tace, in inda tayi hakan Safiya ta jiyowa tace kiyi magana kinyi shiru kinsanni bana barin ta kwana,
"Safiya bana son cikin dake jikin Sajida yakai labari bana son d'an data Haifa yazo duniya, saboda zai zamemin ciwo a zuciyata kina sane da bana aihuwa,
Amma na 6oye masa saboda masifaffiyar mahaifiyarsa"
"Nafisa abinda nakeso dake shine, kibar d'an dazata Haifa yazo duniya inyaso sai mubi dare mu kasheshi ba tare da kowa ya sani ba"
Safiya ta fad'a tana tafi alamun duniyar zatayi musu dad'i.
"Nafisa tace "to sis shikenan amma kinsan dole zan ga wulakanci dan har wani rawar k'afa yake a kanta"
Daga nan sukayi sallama.
Har Hajiya mama ta kammala girki Nafisa bata fito ba,
Sai wajen 10:11am, sanye da dogon hijab tayi d'akin Hajiya mama da sallama,
"Antashi daga baccin asarar kenan?"
Hajiya mama ta fad'a tana kai lomar tuwo bakinta,
"Ina kwana Hajiya"
Nafisa ta fad'a batare da koda ruwan fara'a a fuskarta ba,
"Lafiya lau wani abunne ya faru naga kina fushi"
Mik'ewa Nafisa tayi, har tazo bakin k'ofa tajuyo tace "yau zanje gidanmu"
Hajiya mama na sud'e hannu tace "to zuwa yaushe zaki sai in shirya"
"Babu buk'atar kije"
Nafisa ta fad'a tare dayin gaba.
'Dakinta ta koma ta shiga toilet tayi wanka, tana fitowa ta shafa mai, kai dakaga fuskarta zaka tabbatar yau babu lafiya, don ko fara'a batayi, bayan ta gama kwalliya ta bud'e drowa ta ciro leshi mai ruwan k'asa anyi masa aikin wuta a wuyan rigar, kasancewarta fara, sai leshin yayi mata kyau, a yanayin inda akayi d'inkin ma ya zauna a jikinta sosai.
Humra ta d'auka ta goga a jikinta kana taje gurin mayafai ta d'auki fari mai duwatsu da takalmi fari mai tsini ta d'auki wayarta ta fito parlo, Sajida da Hajiya mama ne zaune a kan doguwar kujera, sai da Nafisa ta ke6e baki sannan ta k'arasa tace "sannu anty Sajida ya jikin"
Fuskar Sajida d'auke da far's tace "youwa Nafesa anguwa zakije ne?"
Hajiya mama tace "ni naga tijara wai Nafisa ni take cewa bazan bita ba?"
Sajida tayi murmishi sbda ada inda wacce Hajiya mama ta tsana bai wuce ita ba yanzu Kuma tana ganinsu a rana tunda batada hak'k'insu,
"Sai na dawo"
Nafesa tace tare da ficewa batajira amsaba.
Tana fita Hajiya mama tace "shegiya juya"
"Innalilahi, haba Hajiya mama wannan aihuwar da aketa magana a kanta fa Allah mai bayarwa, bawai dan baya son bawansa bane take hanashi, sai Dan gwada imaninsa, wasu zasu d'auki tsawon lokaci basu aihu ba, wasu kuma zakiga kamar a bakin k'ofa suke tuntu6e dashi, akwai wanda sam harsu koma ga mahaliccinsu bazasu aihu ba, to mezasuce?"
Hajiya mama tace "wato kina nufin ni inayiwa Allah butulci kenan?"
Sajida tace "a'a Hajiya mama inhar maganar ta 6ata miki kiyi hak'uri"
GIDANSU Nafisa.
Horn driver yake a bakin wani tangamemen get, ga dukkan alamu gidan yafi na Alhj Kabir, sbda shima d'in an narka dukiya babu laifi, ana bud'e get drivern ya shiga da mota, kai tsaye parking space ya tsaya, fitowa tayi mayafinta ninke a kafad'arta hannun hagunta Kuma ta rik'e hand bag, kai tsaye taje bakin k'ofar da zata sadaka da sashen mahaifiyarta, part-part ne a gidan har guda uku, k'ofar farko itace ta mahaifiyarta, ta biyu kuma itace ta kishiyar mahaifiyarta, ta uku, wato amaryarsu, mahaifiyar Nafisa zatakai shekaru 74yrs kishiyarta kuwa batafi 40yrs ba, amaryarsu kuma 20yrs dan yarinya ce,
Hajiya Sakina, shine sunan mahaifiyar Nafisa, tanada yara uku, namiji mai suna Kalil zekai shekaru 35yrs, dagashi sai Nafisa, sai kuma k'anwarsu mai suna Salma wato autarsu shekararta 18yrs.
Kishiyarta kuwa sunanta Hajiya Hauwa, yaranta hud'u itama na farkon namiji ne mai suna Bashir Yanada shekaru Ashirin da biyar 25yrs yayi irin saurin girman nan ne, Wanda idan ka gansa sai ka rantse yayi 30yrs, Dan har yafi Kalil girman jiki, sai k'aninsa mai suna Usman yanada shekaru 15,sai k'anwarsu mai suna Juwairiyya, shekararta 13yrs me binta Husna, itace mai shekaru 9yrs.
Amaryarsu sunanta Hajiya Amina sbda taje Makkah, bata ta6a aihuwa ba, amman yarinyar Hajiya Hauwa Husna tana gurinta.
Kai tsaye Nafisa tashiga part d'in mahaifiyarta, samunsu tayi suna hira sai dariya suke, da alamu duniyar tayi musu dad'i, ko sallama bata tsaya yiba ta fad'a jikin momynta tana kuka, cike da damuwa suka matso kusa da ita, Kalil yace "haba sister menene haka daga zuwa sai kuka?"
Yana idda magana Salma tace "anty Nafisat keda waye?"
Momyn ma takasa cewa komai sai binta da kallo take, daga k'arshe tace "daughter meke faruwa?"
A shagwa6e Nafisa tace "momy ciki ne da Sajida harya fara girma, ni bansan ya zanyi ba, d'an tarairayata da Kabir yakeyi duk ya dena soyayyar ta koma gurin Sajida akan cikin data samu" ta k'arashe maganar tana kuka.
"Eeeeh" ciki fa kikace ?, kice bokanta yayi nasara to inhar tasan wata batasan wata ba, narantse da Allah baza'a haifi wannan yaron a gidan ba, inhar an Haifa to lahira ce makomarsa"
Momy ta fad'a tana jinjina kai.
Cikin natsuwa da sigar kwantar da hankali Khalil yace "haba momy sai kace ba musulmai ba, ke da girmanki kike wannan maganar, kinsan iya adadin zunuban da zaki kwasa kuwa?"
"Kai Ibrahim.! inhar bazaka kawo taka gudunmawar ba to kayimin shiru, wato harda Hajiyar tasa ake sakarcin ko?"
Nafisa ta gyd'a kai da sauri,
"Za suci ubansu basai an had'a da malamai ba wallahi sai sun gane kuransu"
Sai da suka lafa da zancen sannan Salam tayi magana,
"A ganina momy abata maganin da cikinta zai zube wallahi sbda anty Nafisa ta samu kawanciyar hankali"
"Yauwa y'ar gari, kekam halinki abin a duba ne, baza'a bata maganin komai ba amman dai zasu d'an d'ana kud'arsu wallahi"
Sum-sum Khalil ya mik'e a zuciyarsa yana binsu da adu'ar shiriya,
Wuni sukayi hirar Sajida da Hajiya mama da Alhji Kabir,
Sai yamma taje part d'in Hajiya Hauwa, da sallama ta shiga ta zauna akan kujera tana jiran fitowarta, Juwairiyya da Husna suna jinta suka rugo da gudu suka rungumeta suna cewa "anty Nafesa ashe kinzo"
Fuska ba yabo ba fallasa tace "eh mana ai nayi fushi ko kud'an lek'o gidan nawa"
"Anty Nafisa dad ne ya hanamu wai makaranta"
Juwairiyya ta fad'a, tana dariya.
Suna cikin hira Hajiya Hauwa ta shigo, fuskarta d'auke da fara'a,
"Ah Nafisat ashe kinzo amma dai ba yanzu kikazo ba ko?"
"Eh Hajiya na sauka da ciwon kai ne shine nasha magani na kwanta, sai d'azu na tashi"
Nafisa ta fad'a tana rik'e kanta, alamun dai bata da lafiyar,
"Ayya ubangiji ya baki lafiya mai d'orewa ya su Sajida da Hajiyar?"
"Suna lafiya tace tana mik'ewa,
Hajiya Hauwa tace "harzaki wuce be?"
"Eh Hajiya wlh yamma tayi Kuma nice da girki"
'Daki Hajiyar ta koma ta d'auko wata leda mai d'auke da turaruka masu tsada da kamashi ta mik'a mata tare da cewa "ki gaishe da mutan gidan,
Godiya Nafisa tayi mata tace bari taje part d'in Hajiya amarya, haka suke kiran amaryar baban nasu,
Da isarta tayi sallama ta k'arasa, Hajiya Amina na ganinta ta kwa6e baki kana tace "walkslm sannunki da zuwa yau kece a gidan namu?"
Nafisa ta d'an yi Jim sai Kuma tace "nice"
Mik'ewa tayi kana tace "zan wuce sai anjima"
Batare data jira amsarta ba ta fice sbda basa jituwa, Nafisa na ganin dad ya auro musu sa'arsu, ita kuma tana ganin bazata d'auki raininsu ba.
Part d'in momynta ta dawo a gurguje tayi musu sallama, tare da ce mata duk halin da ake ciki zata Kira a waya,
Tafe suke suna hira ita da Salma har suka isa parking space, motar gidansu ta shiga ta koma gida, kasancewar drivern nasu ya koma can gida.
Sun isa gidan k'arfe 6:40pm lokacin anata kiraye-kirayen sallah,
Da sallama ta bud'e k'ofar parlon ta shiga, turuss tayi ganin Alhj Kabir da Sajida suna zaune a parlo su biyu, yana zaune akan kujera mai zaman mutum uku, ya mik'e k'afafuwansa ita kuma ta kwanta akan cinyarsa hannunta nakan gemunsa, suna dariya,
Wani masifaffen kishi ne ya taso tare da tokare mata wuya, cikin masifa tace "to dai sallah ake masoyan asali sai a tashi ayi ibada"
Tana kaiwa nan ta shige,
Tana zuwq d'akinta ta cillar da wayarta da handbag d'inta a kan gado, ta ajiye mayafin a gefe ta zame d'ankwalin kanta, cikin yanayin damuwa da tashin hankali tace "wai sosuke su haukatani?, dama haka abun yake? meyasa Kabir ya koma kamar wani Wanda bazai iya control d'in kansa ba?"
Ta fad'a tana juyi a tsakar d'akin, "kodai asiri tayi masa?"
Ganin wankin hula yana neman kaita dare yasa ta d'aga waya ta Kira k'awarta, layin a kashe dole ta hak'ura, ta shiga toilet ta d'auro alwalah tazo ta shimfid'a sallahya ta kabbara sallah,
Bayan tayi sallama ta dinga kwararo adu'a akan itama Allah ya azurtata da juna biyu ko hankalin Alhji Kabir zai Kuma dawowa kanta kamar da sai abinda tace,
Sai da akayi isha'i sannan ya shigo, hannunsa rik'e da babbar leda,
Kasancewar a d'akin Nafisa yake ya sashi zuwa d'akinta kai tsaye, da sallama ya shiga ya sameta zaune akan gado tana latsa waya, mamaki ne ya kamashi sbda ba haka suka saba yiba,
Ganin bata da niyyar tasowa yasa ya k'araso tare da zama kusa da ita cikin muryar lallashi yace "haba Feenat d'ina mekuma yw faru?"
Sai da tad'au lokaci sannan tace "komai ma"
"Kinje anguwa kin dad'e gashi Hajiya bata nan taje gidan,Mama Mero, da ita da Hajiya mama, uwarsu d'aya Ubansu d'aya, tana zaune a tudun wada batada miji shima ya rasu, tanada yaro guda d'aya Hashim yana da super market babba, wanda take a mazaunin mallakinsa,
Dama abinda take jira kenan tace "kenan babu hali inje in gaishe da iyayena?, ita anty Sajidan a kwance take bata motsi?"
Kamar Wanda aka tunzuro, kamar bashine ya fara lallashinta ba yace "kotanada lafiya fa?, Doctor ya hanata aikin K'arfi, kinsani Hajiya Kuma ta kori y'ar aiki shine kikaje kikayi shiru sai dare zaki dawo ko?"
"Duk cin amanata da kayi bai isheka ba? zakazo kana damuna da fad'a"
Alhj Kabir yace "wato Nafisa wuyanki ya isa yanka, zargina ma kika farayi kenan?, A ina kika kamani dacin amanar taki?"
"Amman dai kasan k'arfe shida nayi ka dawo d'akina ko?"
Alhji Kabir daya fara gajiya da surutu yace "ni na hanaki dawowa?"
Daga haka yaje kan loka ya bud'e flaks na ruwan zafi ya d'auki cup d'in dake gurin ya had'a tea ya d'auki bredi ya koma gefe kan kujerar roba ya zauna yana shan tea,
Da kallon mamaki ta bishi, a zuciyarta kuwa cewa take "a haka zamuci gaba da zama yana gasamin aya a hannu dole in samo mafitar abinyi tunda dai wayar K'awata Salma a kashe.
Kwanci tashi asarar mai rai cikin Sajida yanata girma, ga wani kyau da k'iba data sakeyi, Hajiya mama kuwa kamar zata cinyeta, kullum cikin yi mata hidima take,
Nafisa kuwa, kowanne hali ta tsinci kanta a gidan Sai ta sanarwa da mahaifarta.
Bayan zuwanta gidansu da sati biyu, momy ta kirata a waya, da sauri ta d'aga tare da cewa "aslamu alaikum"
Daga can 6angaren momy tace "Nafisa kina ina ne? idan kina kusada mutane ki kauce akwai important thing da zamu aiwatar, da sauri ta mik'e, kasancewar tana parlo suna kallo, tana zuwa d'akinta ta danna key kafin ta kara wayar a kunnenta tace "momy ina jinki"
Cikin k'asa da murya kamar ta marasa gaskiya, momy tace "Nafisa kinada 50k a gurinki?"
Nafisa ta waro ido tare da dafe k'irji tace "momy ina zanga wanan kud'i, yanzu duk k'arshen watan ma da yake bamu 10k yadena bansan dalili ba"
"To nidai na gaya miki duk inda zakiyi ki samo koda 30k ne kizo muje gidan Hajiya Lami"
Da sauri Nafisa tace "ita kuma wacece?"
"Wallahi mai magani ce daga Niger duk taurin kan namiji da jiji da kansa Tasha gabansa, zata dawo miki dashi kamar k'aramin yaro sai inda kikayi dashi"
Murna ce ta kamata sbda taji cikakken bayanin da momy tayi mata, cikin k'arfafa guwaiwa tace "momy zanyi masa magana koda aro ya bani...?

# Love
# Romantic
# Funny

Madarar soyayya tare da cakwakiya

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿
*🫦TSAUTSAYIN TAUNA🫦*

✨GAWURTATTU BIYAR✨

*Zainab Habib (Mom Islam*

Page ,9-10
Gabanta na tsananta fad'uwa ta ajiye wayar tare da tunanin kud'in da momy ta fad'a mata, da Kuma mallakar da sukayi magana.
Komowa parlon tayi ta samu iya Hajiya mama ne Sajida ta koma d'aki, Hajiya mama na ganinta tace "yau dai y'ar aiki zata zo, inata zuba ido ma na jita shiru"
Nafisa tace "wow Masha Allah"
Hajiya mama ta ke6e baki had'i da cewa "dama abinda kukeso kenan kuci ku kwanta ai kinga kwayi d'uwaiwaka, dama gakinan dasu hardana siyarwa"
Waro ido Nafisa tayi kafin tace "Hajiya mama cin fuska fa bashi da dad'i".
Sallahr magrib ne yasa kowa ya koma sashen sa, bayan anyi magrib da isha'i, ta fito Dan cin abinci,
Samun Sajida ta fito tayi, ta zauna akan kafet ta mik'e k'afafu, cikinta yad'anyi girma, plet ta d'auko da kular abincin ta zuba musu shinkafa da miya da nama ta d'auko musu ruwa a fridge ta ajiye tare da saka cokali,
Suna cikin cin abincin Sajida tace "Nafisa.."
"Na'am anty Sajida"
Nafisa ta fad'a tana mayar da hankali ga Kiran da tayi mata sbda tana ganin kamar akwai magana mai muhimmanci da zata gaya mata,
"Gobe idan zanje hospital zaki rakani? Wlhi wancan satin danaje nasha wuya gashi cikin yayimin nauyi"
Cikin tausayawar da a iya fuska ta nuna tace "ayya anty Sajida dama inason rakaki kodan taimaka miki da wasu abubuwan Alhj ne yake cewa a'a"
Sajida tace "kibari zamuje gobe insha Allah"
Daga haka sukaci gaba dacin abinci suna kallo, har k'arfe 8:30pm tayi, yink'urin mik'ewa Sajida tayi, kana tace "Wai kinji abun mai ciki wallahi wainar fulawa nakeso "Nafisa ta yak'e baki kana tace "bari ayiwa y'ar aiki magana saitayi miki"
Ta taimakawa Sajida zuwa d'aki ta dawo,
Kitchen ta wuce tare da sanarwa y'ar aiki tayi wainar fulawa tace "ta kaiwa anty Sajida ta wuce d'akinta,
Hajiya mama kuwa na daga d'aki tana cewa "abin mamaki, Nafisa tayi sanyi da masifarta gashi tanabin Sajida sau da k'afa Allah ya k'ara had'a kansu dama shine fatanmu".
Nafisa na shiga d'aki tayi wanka, tana fitowa ta shafa lotion d'inta mai k'amshi tare da turaruka, harda shu'umar humra,
K'ananun kaya ta saka riga da skirt rigar pink color rigar ko rufe mata cibiya batayi ba, skirt d'in kuwa iya cinyarta yake black color, ta kuma feshe jikinta da turare mai sanyin k'amshi, zama  tayi kan bed kana ta janyo wayarta, number Alhji Kabir ta danna ring d'aya zuwa biyu ya d'aga,
"Hello"
Nafisa ta shagwa6e fuska tare da sauya murya kamar ta mai shirin yin kuka tace "uhm Alhji shine ko ka kirani, ko har yanzu fushi kake dani?"
A inda tayi muryar sai jikinsa yayi wani yarr, kasancewarsa mutum mai son shagwa6a ba k'aramin rikita masa kwanya shagwa6a take ba,
Da sauri yace "haba Hajiya Feenat ni bakiyi min laifi ba, yanzu ma ina hanya ne nakusa gida"
"Allah ya dawo min dakai lafiya mijina"
Alhj Kabir na washe baki yace "amin Hajiya Feenat"
Sake gyara jikinta tayi ta jere masa abincinsa akan table dake bedroom d'in ta ajiye su jug na zo6o da ruwan sanyi a gora ta ajiye plet da spoon ta koma ta zauna,
Driving yake amma hankalinsa gabaki d'aya hankalinsa yana kanta, sbda muryar datayi masa ta haifar masa da feeling, Allah-Allah yake ya isa gida,
Tana zaune taji horn d'in mota da alamu ya iso, 6oyewa tayi a cikin labulen daya rufe k'ofar toilet, yayi sallama shiru, ya nemi guri  ya zauna a doguwar kujerar data kasance ita kad'ai ce a bedroom d'in, mai zaman mutum biyu, wayarsa ya ciro a aljihu har zai danna numberta, yaji an rungumeshi, da sauri ya k'amk'ameta a jikinsa yana cewa "haba Feenat kinason tsoratani ko?"
Bin ta yake da wani irin kallo mai d'auke da soyayya, sam yak'i d'auke ido daga kallon shigar jikinta.
"Wanka zaka farayi ko abincin zakaci?"
Cikin cold voice wacce baima san yanada ita ba yace "inda na dawo da zazzafar soyayyarki ai kya bari in nuna miki ko?"
"Uhm ai nafison ka sami nutsuwa ta hanyar cin abinci ko yin wanka"
"Kece nutsuwata pls zo gareni matata"
Bata zod'in ba kamar inda ya buk'ata, ta bud'e kular abincin ta zuba masa shinkafa da miya da nama, ta bud'e wani d'an k'aramin bowl mai murfi ta zuba masa salad, zama tayi gefensa tare da d'aukar spoon ta fara bashi a baki, duk da hakan nutsuwarsa bata tare dashi sosai,
Bai yarda ta bashi shikadai ba, sai da yasata ta d'auko wani spoon d'in sannan yana bata tana bashi.
Bayan sun gama ta rufe kayan abincin ta ajiyeshi a gefe taje toilet ta had'a masa ruwan wanka sannan ta dawo ta taimaka masa ya cire kayansa, ya shiga wanka, bud'e drowa tayi ta ciro masa farar jallabiya mai hula ta ajiye tare da fesheta da turare mai k'amshi, ta d'auko boxes shima ta fesa turare,
Alhji Kabir kuwa, yana toilet baima fara wankan ba, yana tunanin sabuwar soyayyar da Nafisa take nuna masa, sbda rabonsu da hakan tun tana amarya, kawar da tunin yayi ta hanyar yin wankan yanajin wutar sonta a zuciyarsa, yana gamawa ya goge jikinsa da d'an k'aramin towel, ya d'aura wani fari a kugunsa ya fito,
Samunta yayi tana dane² a wayarta, yana zuwa yayi huge d'inta had'i da manna mats kiss, k'amshi sabulun da yayi wanka ya ziyarci hancinta, lumshe ido tayi kana tace "lokaci yayi nisa har k'arfe 10:11pm na dare"
Bai ce mata komai ba, sai iya boxes d'in daya saka ya rage hasken d'akin ya kasance hasken pink color bamai haske sosai ba.
Tsam ya rungumeta a k'irjinsa jikinsa na karkarwa,kamar sabon ango, ita kanta tasan da hakan,sbda turaren da momynta ta bata wato humra Wanda akayi had'e² a ciki, sosai ta rikita masa kwanya Dan har wani mimik'ewa yake, gadon bayansa take shafawa a hankali cikin salo na k'warewa da lallausan hannunta, tana hura kunnensa, daga nan salo da labari ya sauya, zuwa nasu na masoya suka lula duniyar da suka mance da mai ciki can a d'aki.
Sai wajen 11:pm ya sarara mata, ta tashi a gajiye taje toilet ta tsarkake jikinta, tana fitowa d'aure da towel ta zauna a bakin gado kana tace "Alhj wanka fa"
Kuma rarumota yake shirinyi, ta kauce da sauri tare da cewa "uhm ni katashi kayi wanka kokuma muje inyi maka"
Rik'e da hannun juna suka shiga toilet ta taimaka masa yayi wanka,
Bayan sun fito farar jallabiya yasa da new boxes, itama ta sanya sleeping dress suka kwanta rungume da juna, asuba ta gari.
Washe gari, d'akin Sajida zai koma kasancewar yayi kwana biyu  d'akin Nafisa, kafin yayi wanka ya wuce gurin aiki sai da aka sakeyin zazzafar soyayya sanan ta barshi ya wuce,
Yana fitowa cikin shirnsa na zuwa aiki ya wuce d'akin Sajida, kwance ya sameta akan sallaya lokacin 7:30am, "Maman twins" sunan dayake kiranta dashi kenan,
Bud'e ido tayi tare da rik'e k'afar gado ta yink'ura tana ce masa "barka da safiya"
Fuskarsa wasai yace "barka mom twins ya kika tashi ya Kuma k'arfin jikin?"
"Da sauk'i" tace tana yamutsa fuska, har zai fice tace "yaune komawarmu asibiti fa"
"Okay akwai kud'i a gurin kayana ki d'auki abinda zai isheki"
A karo na biyu tace "tare da Nafisa zamuje Dan ta tayani wasu abubuwan ina Shan wahala idan naje"
"Okay baby damuwa saikun dawo"
Ya fad'a yana fita, tayi masa Allah ya kiyaye hanya"
Daga nan ya wuce d'akin Hajiya mama, da sallama ya shiga ya sameta ta kwanta, durk'usawa yayi kafin yace "barka da safiya Hajiya"
Hajiya ta tashi zaune kana tace "yauwa barka ya aikin, amman dai ka karya ko?" A'a Hajiya idan naje gurin aiki zan karya"
"Nifa bana son sakarci haka zaka tafi da yunwa? me amfanin matan naka a gidan?"
"Alhji Kabir yace "haba Hajiya suna aikatuwa ba, bawai dan ba'a d'ora bane kawai yau bazanyi breakfast da wuri bane"
"To ai shikenan idan yunwa ta cinyeka zaka nemi maganinta"
Hajiya ta fad'a tana yi masa sababi,
"Na tafi adu'arki nake buk'ata Hajiya"
"Allah ya dawo dakai lafiya Allah ya kareka daga dukkan sharri Allah ya kareka daga sharrin mutum da aljan"
"Amin ya rabbi nagode hajiy nagode"
Ya fad'a, tare da ficewa.
Koda ya shiga mota yana tafiya, mamaki darensu na jiya ya dingayi.
K'arfe 9:11am Nafisa ta farka daga bacci, ta dad'e a kwance bata motsa daga inda take ba, tuno makirci da kissar da tayi masa jiya tayi,
"Hmm inyasan wata ai besan wata ba, zan bari sai ya sake dawowa d'akina sai in kuma janye hankalinsa tare da cusa neman buk'ata ta a zuciyarsa Dan sai ya bada 50k d'innan "
Tana gama fad'ar haka ta sakko daga kan gadon, tare da shiga toilet ta cire kayanta tayi brush kafin tayi wanka, tana fitowa ta goge jikinta taje gaban mirror ta shafa mai  da powder tasa man baki,
Drowa ta bud'e ta d'auko doguwar rigar shadda milk color anyi mata aiki da jan zare, sosai tayi mata kyau Kuma ta zauna a jikinta, parlo ta fito hannunta rik'e da d'ankwali, Hajiya mama ta samu zaune a dinning tana breakfast ita kad'ai, karasawa tayi, kana ta durk'usa tace "barka da safiya Hajiya" Hajiya mama tace "barka dai ya gajiya" Nafisa tace "lafiya lau naga anty Sajida bata fito ba lafiya?"
"Tadai sha shayi ta koma d'aki naji tace yau zakuje asibiti ko?"
"Eh yaune barin duba ko ta shirya"
Nafisa ta wuce d'akin Sajida, sallama tayi kana ta k'arasa ciki, murmishi Sajida tayi kana tace "anty harkin shirya?" Sajida  tace "eh dama ke nake jira"
Tana zaune har ta gama shiryawa ta mik'a mata wata y'ar jaka suka fito parlo, Sajida na sanye da riga da skirt na atamfa, super Holland tana d'auke da manyan flawoyi purple da bak'i sai adon fari, mayafin jikinta fari, hakama takalmanta.
Komawa d'akinta Nafisa tayi ta d'auko d'in mayafi da takalmi milk color da hand bag d'inta sukayiwa Hajiya sallama suka wuce,
Driver na ganinsu ya taso yana gaishesu, bayan sun amsa ya bud'e musu suka shiga, ya tambayesu inda zasu, asibitin GIWA hospital,
Suna tafe suna hira jefi-jefi, Nafisa kuwa burinta shine, suna zuwa asibitin ta aiwatar da abinda zuciyarta take raya mata,
Suna isowa yayi parking a harabar asibitin, suka fito tare da ce masa ba dad'ewa zasuyi ba,
Zama Nafisa tayi a gurin da mutane suke zama, ita kuma Sajida ta shiga jerin layin masu ciki lol,
Layi na zuwa kanta ta shiga d'akin awon,
Nafisa ta mik'e da sauri tare da aron pen a hannun wani security, ta sashi ya samo mata paper, yana kawo mata tayi wani d'an rubutu ta buk'aci jami'in tsaron ya nuna mata ofishin babban likitan, yana nuna mata ta shiga tana shiga ta sameshi hakimce akan kujera yana juyi lokaci-lokaci, sallama tayi kafin ta shiga, bayan ya amsa yayi mata umarni data zauna, tana zama tace "likita nazo maka da wata buk'ata ce, inhar ka amince zaka huta nayi maka alk'awari,
Ina cikin talauci ne? kokuma ance miki ni talaka ne?"
Kalmar data

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment