Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Indo ke kallonsu har sukayi nisa suka 6acewq ganinta,mabaratan gurin sukace wannan mata anyi y'ar bala'i yasin, anbamu kud'i su  rik'e saboda cuta da son zuciya, Baaaba Indo dai bata nunar da tasan mama ba sbda shiru tayi, dan suka gano ita tayi mata hanyar zuwa gurin masifa ta auku.
Suna isa gida suka tarar da malam Haladu a zaune ya zabga tagumi, maman Aisha tayi sallama har sau uku shiru ko waigowa  beyi ba,
Sai da tace "maa...laam!!" sannan ya d'ago fuska irin ta yanayin cikin damuwa ya sauke ajiyar zuciya kana yace "ina kukaje tun d'azu nake nemanku har can k'asa naje amma ko d'uriyarku babu"
"Nifa bance kayimin tambayar k'wa-k'wa ba, dan haka ka k'yalemu"
Shiru malam Haladu yayi tare da mik'ewa ya shige d'aki ya nemi guri akan kujera ya zauna,
Murya k'asa-k'asa yace "wannan wace irin damuwa ce, sai kace ni kad'ai Allah ya jabarta da talauci, ina zansa kaina, yau na nifa aiki mashin ta 6allomin gyaran dubu uku, gashi ko cinikin dubu d'aya banyi ba" sai ya fashe da matsanancin kuka,
Daga can tsakar gida, maman Aisha tacewa Aisha jeki siyo mana shinkafa mudu d'aya da rabi, ki siyo mangyad'a gwangwani d'aya ki siyo mana kifi na d'ari biyu ki had'o da Maggi da onga kiyi sauri tunda munada itace barin had'a wuta in d'ora sanwa"
Tana bawa Aisha kud'in ta fice da gudu tana murna yau abinci harda kifi shikenan suma sun zamo y'an gayu,
Jiki a sanyaye malam Haladu ya fito, ya tsaya a bakin k'ofa kana yace "maman Aisha a ina kika Sami kud'in cefane?"
"Nifa sa idone bana so, tunda dai kaga an d'ora ai saikayi shiru da bakinka ko? amma zaka wani cikawa mutane kunne da surutu"
Maman Aisha ta fad'a tana gyara wuta,
"Allah ya baki hak'uri"
Kalmar daya furta kenan ya k'ara gaba.
Tsaki taja had'i da buga k'afa tace "wallahi gobe ma saina koma maula ai naga gurin zuwa"
Aisha na dawowa aka gyara kayan miya takai nik'a, zuwa dare ana kiran magrib shinkafa da miya ta kammala danma kafin mai awara ta kawo sunci,
Sai da mama tayi sallah sannan ta raba abinci, yaukam ansawa malam Haladu abincin da yawa, bayan ya dawo daga sallahar isha'i ya shiga da sallama,  ga mamakinsa sai yaji tana cewa "oyoyo da mai gida,Aisha mik'a masa abinci"
"Sannunku" kawai yace dan a inda tayi fara'ar sai abin ya bashi mamaki Dan ba kasafai ake ganin fara'arta ba.
Washe gari asubar fari ta mik'e yau babu dogon bacci, kasancewar ta riga kowa tashi hakan yasa ta share gida ta d'umama abinci, taje tayi alwalah sai da tayi nafila sannan ta tashi malam Haladu, yana tashi yayi alwalah ya wuce masallaci, sai da gari ya waye sannan ya dawo, mamaki ne ya kamashi, ragowar shinkafa da miyar jiya harda ragowa kuma cikin kwana, batare da yayi magana ba bare akuma dank'ara masa bak'ar magana, yasa cokali ya fara cin abincin.
Yana gamawa yayi hamdala tare da tura hannu cikin aljihunsa ya ciro wata kod'ad'iyar d'ari biyar ya mik'a mata kana yace "cefanenku na dare da rana wallahi daga fara aiki da mashin d'innan jiya harta 6allomin gyara"
Ko tanka masa batayi ba ta kar6i kud'in tayi d'aki.
Yana fita suka fara shirye-shiryen barin gidan, kamar jiya shigar da sukayi yauma ita suka mai-maita, wato had'in bauta Aisha kuma da yagaggun kaya haka suka haye mashin suka wuce,
Suna sauka ta mik'awa mai mashin kud'i ta kamo hannun Aisha da d'an buhunsu a hannu ta gaishe da matan gurin, suka amsa mata cikin d'agun kai, Baaaba Indo dataga maman Aisha bata hangots ba, ta sunkuyar da kai,
Juyowar da maman Aisha zatayi sukayi ido biyu da Baaaba Indo, maman Aisha ta washe baki kana tace "Baaaba Indo ashe kinzo"
Bayan sun gaisa ko wacce tasa ido a titi, ita kuma Aisha na tsalle tana cewa "a taimakemu babanmu ya gudu yabar mamanmu da yunwa,
Yau dai kamar anyiwa garin shara Dan masu manyan motocin ma basu wani wuce ba bare susa ran samu, har k'arfe ukun rana su maman Aisha ko sisi basu rik'e ba, malam Haladu ya dawo daga gareji yana daga tsallaken titi, ya hango maman Aisha zaune ita da Aishar a layin mabarata, mamaki ne ya kamashi had'i da takaicin, abinda bai ta6a tunanin zata aikatashi ba, ya taho da gudu zai tsallaka titi mota tayi gaba dashi, da gudu mutane sukayo kansa cikin harda mabaratan gurin dasu maman Aisha, wani mai mashin cewa yake "malam Haladu nefa yanzu na ganshi a tsaye, lallai tsautsayi ba'a samasa rana"
Daga jin  mai mashin yace malam Haladu maman Aisha ta rugo da uban gudu tana ihu ta watsar da buhun da sandar hannunta tana cewa "mijina ne, indai Haladu ne wallahi mijina ne"
Kaff mutanen gurin mamaki ya kamasu kowanne sai kallonta yake, wai ashema tanada miji mijinma mai K'arfi Wanda ba musaki ba,
Kasancewar motar data bigeshi ta tsaya aka sanyashi a ciki suka wuce Giwa hospital harda maman Aisha da itama Aishar,suna  isa  aka shiga dashi, likitoci furr sukak'i kar6arsa, sai sun kawo jami'an tsaro,
Duk da ba wani ciwo yaji ba sai kujewa da yayi a goshinsa amman da alamu yana jin ciwon gurin sosai, Wanda ya bige malam Haladu ya d'aga waya tare da matsawa gefe, ba'a jima ba sai ga abokinsa nan yazo aka shiga dashi emergency room, abu d'aya yake ambato wato kansa, idan ka gansa lokacin da akayi hatsarin bazaka ta6a cewa ya bugu sosai ba, sbda kujewa ne kawai, Amma asalin ciwon yana cikin jikinsa,
Sai da akayi masa allurar bacci sannan suka sami lafiya, doctor daya gama y'an gwaje-gwajensa ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, kana yace "ku biyoni zuwa office, 
Da maman Aisha da mai motar wanda a k'alla zaiyi shekaru 35yrs a duniya, suka shiga office d'in, nuni yayi musu da su zauna kafin ya cire gilashin idonsa yace "wato a gwaje-gwajen da mukayi mun gano zuciyarsa na daf da kamuwa da ciwo, gaskiya yana cikin damuwa, ke iyalinsa ce?"
"Eh"
Maman Aisha tace tana gyad'a kai,
Ya rubuta musu magunguna yace suje su siya a cikin asibitin,
Jikin maman Aisha na rawa tace "likita maganin zekai nawa?"
"Dubu goma"
Likita ya bata amsa a tak'aice,
"Ina zuwa"
Mutumin yace tare da ficewa,
Itama maman Aisha fitowa tayi ta koma kan dogon bencin dake k'ofar d'akin da aka kwantar da malam Haladu,
Cikin yanayin damuwa "Aisha tace "mama baban ya mutu ne?"
Muryar mama a dashe tsabar kuka dataci tace "ciwon zuciya ya kusa kamashi"
Aisha ta toshe baki had'i da cewa "mama mu dena zuwa yawon maula kinga baba zai mutu"
Buff ta bige mata baki kana tace "yawon maulan ba taimakonsa mukeyi ba ki gayamin?"
Aisha tayi shiru kamar mai tunanin wani abun,
Wanda ya bige babanta ne suka taho shida abokinsa, mama ta mik'e da sauri, tare da cewa "bawan Allah ansami maganin?"
"Eh zankoma office d'nne"
Ya fad'a a tak'aice,
Suna tafe abokin nasa yace "Alhaji Kabir meka fahimta game da wannan baiwar Allahn?"
Wanda aka Kira da Alhj Kabir yace "Jamil abinda na lura dasu, suna cikin matsanancin talauci, dan a inda na lura talauci yana damunsu,
Isarsu office ne yasa sukayi shiru da maganar da sukeyi,
Doctor yace "Masha Allah amma bawan Allah na jinjina maka, irin namijin k'ok'arin da kayi gurin tsayawa ceto ran bawan Allah, sa6anin wasu mutanen babu tsoron Allah saisu gudu".
Murmishi Alhaji Kabir yayi kafin yace "inaso ka tsoratar da wannan matar.."
"Ina jinka"
Doctor yace, yana kallon Alhaji Kabir.
"Inaso kasanar mata da cewar zuciyar mijinta tana daf da bugawa muddin bata dena yawon maula ba"
"Ai wannan mai sauk'i ne, karka damu Alhji temakonta zamuyi sai dai ta yi gaggawa gurin kashe zuciyarta a yawon maula"
Likita ya fad'a yana mik'ewa,
A tare suka shiga room d'in da malam Haladu yake, sun sameshi ya farka yana ta d'aga hannu,
Da sauri likitan ya k'arasa tare da zuwa kusa dashi yace "baba jikinne sannu Allah zai baka lafiya"
Malam Haladu yafara magana a sark'e yana cewa "ka..ki..ra..min matata"
Da sauri likita ya lek'a ta window yace "baiwar Allah mijinki na magana"
Maman Aisha ta rugo da uban gudu ta bud'e k'ofar ta shigo tana cewa baban Aisha yadai jikinne ko kanason wani abu ne?"
Duk jerin tambayoyin data dinga yi masa d'aya ya sami damar amsawa yace "banason komai ki mayar da Aisha gurin iyayenta sai kici gaba da yawon maula!! Yawon maula kawai Aisha taji, kasancewar yanzu ta shigo, ganin mama a yanyin damuwa yasata matsa kusa da ita ta kalli Malam Haladu kana tace "baba ya jikin?"
Hannu ya d'aga mata yaci gaba da cewa "ki mayar da ita gurin iyayenta inhar kika barta a gurinki ita kanta yarinyar ba yafemiki zatayi ba"
Dama ba kune iyayena ba? dama baku kuka haifeni ba?!"
Kukane ya kubce mata ta fice da gudu,
Alhj Kabir da Jamil da doctor ta wuce suna ta tattunawa akan inda zasu taimaki maman Aisha da malam  Haladu, ganinta kawai sukayi tana kuka,
"Baiwar Allah jikin baban naki ne?"
Kasancewar ta toshe bakinta da hannu yasa d'aga musu kai kawai tayi sbda kukan dake taho mata.
Alhj Kabir ne ya taso yazo inda take kafin yace "baiwar Allah meya faru?"
"Babu komai"
Aisha ta fad'a a tak'aice.
'Bangaren Malam Haladu kuwa tari ya sark'eshi hannun maman Aisha a nashi tana rok'on gafara, kalma uku ce ta kuma had'ashi da ita wato, "ki mayar da Aisha gurin iyayenta inyaso kije kici gaba da yawon maula! kamar inda ya fad'a d'azu, sai kuma da yace "ana bina bashin d'ari biyar, sai kuma kalimatu shahada da yayi tare da ambaton lahaula wala k'uwawata illah billah" a gigice maman Aisha tayi waje tana hango doctor dasu Alhaji Kabir tace "ka kasheshi ka huta shikenan dama kaso kasheshi ne shiyasa ka bigeshi, ashe duk maganar da malam Haladu yakeyi suna recording, Jamil ya mayar da waya cikin aljihunsa kafin yace "baiwar Allah inda yayi niyar kashe megidanki wallahi ko saurararki bazaiyi ba, ke bama zai tsaya ku gansa ba Dan haka ki iya kalamanki,
"Wallahi sai ofishin jami'an tsaro ya Bimini hakkina"
Jamil yayi murmishi kafin ya fito da I'd card d'insa yace "shari'a daga nan har kotun Allah ya isa inhar akwai muje tunda ke bakisan tauhidi ba, doctor yaja hannun Jamil tare da cewa "just forget muje"
Kai tsaye suka wuce room d'in suka sami likitoci a kansa, suna zuwa aka rufe masa fuska da farin k'yalle...!
# Love
# Romantic
# Funny

Domin magana da marubuciyar 08141799224

       MOM ISLAM

Akwai cakwakiya a cikin labarin, nasan yanzu ba lallai ku fahimci inda muka Dosa ba.

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿
*🫦TSAUTSAYIN TAUNA🫦*

_✨GAWURTATTU BIYAR✨_

*Zainab Babib(Mom Islam*

Page 5-6
Wata Norse ta fito da sauri hannunta rik'e da wayar malam Haladu, mama taje da sauri ta k'ar6a tare da karawa a kunne, "ina Haladun"
Akayi magana daga cikin wayar, cikin kuka mama tace "Allah yayi masa rasuwa" ta kuma fashewa da kuka,
Sai da aka kuma magana a cikin wayar tad'au murya tace "Yaya Tanimu ne?"
"Eh nine kuna wane asibitin?"
"Asibitin giwa" ta bashi amsa.
Ba'a jima sosai ba asibitin ya cika da y'an uwa da abokan arziki, duk wani abu da ake bukata Alhj Kabir da Jamil suke gudanarwa har akayi masa sutura aka sallaceshi, sannan aka kaishi gidansa na gaskiya, Baaaba Indo kuwa tariga da tazo ta kasa shiga cikin asibitin, dataga  an fito da gawar ne ta bisu aka wuce gida.
Aisha kuwa ta riga kowa dawowa  dan anan aka sameta,
Gida ya cika sosai da y'an uwa da abokan arziki, a ranar abinci har  neman gurin zubawa sukeyi, Alhj Kabir kuwa dashi ake komai,
Bayan kwana uku an watse daga zaman makoki Aisha ta rame sosai duk da ba wata babba bace Amma tanada zurfin tunani sosai,
Ranar da malam Haladu ya cika sati d'aya, maman Aisha na zaune a d'aki ita da mak'ociyarta, Aisha ta shigo tana sanye da hijabi har k'asa tace "mama dama baku kuka haifeni ba?"
A razane maman ta d'ago, cikin tsawa tace "seme idan bamu muka haifeki ba, idan kika kuma yimin magana mai kama da wannan wallahi saina sa6amiki".
Sallamar da wasu mata sukayi ne yasa mama yin shiru suka kar6i gaisuwa,
Baaba Indo kullum sai tazo zuwa yamma ta tafi, Alhji Kabir kuwa har iyayensa sai da sukazo sukayi gaisuwa tare da kawo musu kayan abinci.
Rasuwar Malam Haladu da kwana arba'in wato lokacin mama ta fita daga takaba, saura idda, duk da kwanakin da suka kwashe har yanzu abinci bai yanke musu ba,
Wata ranar Juma'a da misalin k'arfe 1:30pm, Zaune Aisha take a cikin d'aki ita kuma maman tana parlo, kamar kullum taci kukanta ta gaji, duk wata tsiwa yanzu babu wani lokacin ma tayi ta rok'on Allah mutuwarta tunda dai batada iyaye meye amfanin zamanta a duniya.
'DAN 'DANO💞
Gidane had'adde wanda tsayawa misalta kyawunsa sai mu cika pegi bamu gama ba, zaune suke a babban parlonsu wanda yake da girma sosai, shi kansa parlon abin tsayawa a kalla ne sbda ya tsaru iya tsaruwa, wasu mata ne  zaune a kujera guda su biyu, daga can gefe kuma wata tsohuwace wacce a k'alla zatayi shekaru 70 a duniya, sanye take da riga da zani na atamfa ta kwafa d'aurin d'ankwali abindai gunin ban dariya, kallon matan tayi kana ta Kira sunan d'aya daga ciki tace "Sajida kin wani zauna kin zubawa talabijin ido sai kace yau kika fara kallo ga aiki can a kicin kamar zai kashe uwani me aiki" wacce aka kira da Sajida ta yamutsa fuska tare da cewa "Hajiya mama damafa an kawo uwani ne dan mu huta da wasu aiyukan"
"Ah lallai bari kabiru ya shigo zanyi masa magana idan ya koreta sai ku huta"
Takuma cewa "kekuma Nafisa kitashi ki d'orawa Kabiru abin bud'a baki kinsan dai yau ya kammala azuminsa"
Wacce aka kira da Nafisa ta mik'e da sauri tabar gurin tana gunguni.
Alhaji Kabir babban d'an kasuwane, sana'arsa itace siyarda atamfofi da shaddoji, a Kano yanada manyan shaguna har guda biyu, haka ma a jos yanada shago d'aya, a nan Kaduna yanada shaguna biyu, inda Allah ya yalwata masa arzik'insa, bayan rasuwar mahaifinsa ya d'auko Hajiya mama ta dawo gidansa, wato mahaifitarsa, shi kad'ai Allah yaba Hajiya mama, gashi bata son taga ansami koda nera biyar ne a gurinsa, Allah ya zubawa Hajiya mama k'ananun magana ga gori da sa ido uwa uba wataran ta fasa ihu tace baka bata abinci ba, wannan kenan. Sajida itace babba a halin yanzu bata da d'a ko d'aya, Hajiya mama tasa Alhji Kabir k'aro aure akan Sajida bata aihuwa, shine ya auro Nafisa y'ar k'awarta, wani lokacin ta nuna tafison Nafisa wani lokacin kuwa tayi mata tatass, watan Nafisa bakwai tayi 6ari tun daga nan Allah bai sake bata ciki ba.
"Au eyye, harkinyi samun gurin da zaki dinga yimin k'ananun magana kenan nagode babu komai, kuna yaran mata bakusan inda zaku kula da mijinku ba, wani sa'in ina fad'ar gaskiya ana ganin laifina"
Dole suka watse dukkansu suka bar mata parlon taci gaba da surutunta ita kad'ai,
K'arfe 8:pm bayan Alhji Kabir ya shigo, sai da ya fara shiga d'akin Hajiya mama sannan ya mik'e zai fita ta tsayar dashi, dawowa yayi ya zauna kafin yace "Hajiya kinsani na dawo?"
Eh dama dalilin dayasa na dawo dakai shine, gara ka zauna musha hira tunda dai ba wani abun suke tsinana maka ba, aihuwar ma basuga dama ba, yo banga amfanin shiga d'akunansu ba, sai dai suci suyi Kashi su juya d'uwaiwaka dan iskanci"
Kan Alhji Kabir a k'asa yace "Hajiya dole fa aba kowacce hak'k'inta wanda Allah ya ratayamin"
"Kabiru kacemin wa'azi ka koma yi aibansan wa'azi ka koma ba sai yanzu, ni zaka gayawa hak'k'i? to nace yau ka huta maza jeka, d'akinka ka kwanta"
Har ga Allah wani sa'in yanajin haushi idan tana yi masa haka, dayake mahaifiyarsa ce koda yayi fushi dole yake sakkowa.
Yana fita ya shiga d'akin Sajida, sanye take da sleeping dress pink color rigar mai shara-shara, ana iya hango komai na jikinta, da sauri ya k'arasa tare da rungumeta kasancewar tana tsaye tana jifansa da murmishi, yana rungume da ita ta dinga matsawa a hankali suna tafiya har suka zube kan bed, takai bakinda dai-dai saitin kunnensa ta rad'a masa "ina alfahari da samunka, hasken idaniyata  anurin raina, tabbas samun miji irinka shine abunda mata da yawa suke fata na sameka hakan ya sanya nakejin kamar nafi ko wacce mace sa'a a duniya, ina alfahari dakai mijina ilove you"
Kiss ya bata tare da cewa "love you too my sweet heart"
Suna rungume da juna wayarsa tayi ring, gyara ruk'on da yayiwa Sajida yayi da hannunsa na hagu ya d'aga wayar da hannunsa na dama, kafin ya d'aga sai da ya duba number yaga babu suna, yana d'agawa, daga can 6angaren akace "hubbil khairi nayi kewarka fa"
Da sauri ya sake Sajida tare da kallon number ya kara wayar a kunnensa ya kuma mayarwa kunnensa a karo na biyu kana  yaci gaba da cewa "ban gane dawaye nake magana ba"
Daga can 6angaren wacce ta kirashin tace "kana magana da Safiya, nasan bazaka ganeni ba, amma inaso kasani soyayyarka tana neman hallakani sbda kar in cutar da kaina da yawa yasa nanemi numberka na kiraka pls ka yarjemin"
Ta k'arashe maganar tana jan numfashi.
"Mtsw karki sake Kiran wannan layin ban sanki ba"
Yafad'a ransa a 6ace.
Tare da cilla wayar gefe,
Tashi d'aya mood d'in Sajida ya sauya, sosai kishi ya cika mata zuciya, ta juya baya alamar tayi fushi, a hankali ya isa gareta yana bubbuga mata baya, kana yace "haba sweetheart akwai wani albishir da nakeson yi miki?" 
"Ina jinka" ta fad'a batare da ta juyoba,
"Mezai hana muje gidan marayu mu d'auko yarinya koya kika gani?"
Da sauri ta juyo kana tace "ina rok'on Allah ya bani nawa basai munje can ba"
Dole ya hak'ura da shawarar tunda dai batayi na'am da zancen ba.
Sai da yaci abinci ya k'oshi sannan yayi brush yazo ya rungumeta suka kwanta, tayi nisa da bacci sai ta dinga mafarkin wani mutumi na binta da wuk'a, sosai ta firgita ta tsala uban ihu wanda yaja hankalin Hajiya mama da dama rabi bacci rabi sa'a ido takeyi.
Washe gari da asbha bayan sunyi sallah Alhji Kabir ya dawo daga masallaci, dama al'adarsa idan ya dawo daga masallaci sai yaje ya gaisheda Hajiya mama da Nafisa sannan ya koma d'akin Sajida kuma duk wanda yake d'akinta ba itace da breakfast ba, yana shiga ya sami Sajida kwance tanata juyi akan kafet, da sauri ya k'arasa gurinta jikinsa na rawa ya fara tambayarta, "Sajida meke faruwa?"
Toshe bakinta tayi sbda amai daya taso mata, tayi toilet da gudu, amai ta dinga kwarawa kamar zata amayar da y'ay'an hanjinta, sai data d'auraye bakinta ta juyo ta ganshi jingine a bango kamar zaiyi kuka, " Sajida kifad'amin abinda ke damunki" yayi maganar ne cikin wani irin yanayi"
Ya rungumeta suka dawo bedroom, hijab d'inta ya d'auka kana ya taimaka mata tasa suka fito parlo, samun Hajiya mama sukayi tana zaune tana sana'ar tata wato kallo, "ina kuma zuwa da sassafe?"
Ta tambayesu tana mik'ewa tsaye,
"Hajiya sai amai take zamuje asibiti ne a dubata"
"Ashsha! koda kunje ya wuce suce shawara"
Ita dai Sajida datagaji da tsayuwa ta zauna tana dafe da kanta,
"Honey ina kuma zakaje da sassafe?"
Nafisa ta tambaya tana kallon Sajida,
"Zamuje asibiti Sajida batajin dad'in jikinta"
"Oh Allah sarki barin d'auko hijab sai in taimaka mata" ta k'arashe maganar tana yatsina baki, kafin tace "sannu anty"
Cikin k'arfin hali Sajida tace "yauwa"
"To bazakije ba, nace bazaki ba taje ita da mijin nata taji da kiti fifin munafurcinta"
Nafisa ta sosa kai Dan ba haka taso jiba.
"Allah ya kiyaye hanya"
Hajiya mama tace tana ke6e baki.
Kai tsaye suka wuce parking space, d'aya daga cikin motoci biyun dake jere ya d'auka, suka tafi a ita, kai tsaye suka wuce GIWA hospital, wato asibitin da Malam Haladu ya rasu, kasancewar a iya zirga zirgar da sukayi ya sama da doctor d'in,
Bayan yayi parking ya dinga jerawa Sajida sannu, gyad'a masa kai kawai take har suka isa office d'in doctor,
Bayan sun gaisa ya sanar masa da matarsa ce babu lpy, file aka bud'e musu sannan yace suje test, bayan anyi mata abubuwan daya kamata, Norse d'in tace musu su nemi guri su zauna, bayan wasu lokuta results ya fito ta kai can office d'in kana tace "suje can akwai bayanin da za'ayi musu,
Hanunta ya kama suka shiga office d'in, doctor yayi musu nuni da gurin zama,
"Congrats madam tana d'auke da juna biyu"
Alhj Kabir ya juya yaga babu kowa, a tunaninsa ko da wani doctor yake magana, ganin shi yake mik'awa hannu yasa shi, mik'a nashi hannun da rawar jiki,
Doctor ya kuma nanata "congrats ina tayaka murna ya mik'a masa results kafin yace "mahaifarta bata da k'wari, akwai buk'atar ta dinga samun hutu tare da yawan bacci, da kuma cin y'a yan itace, karta dinga d'aukar abu mai nauyi"
Jikin Alhji Kabir na rawa fuskarsa cike da farinciki yace "insha Allah wannan ai duk mai sauk'i ne, mungode doctor, kuje pharmacy ku kar6i magani ga  card, suna zuwa aka basu maganin tare da jaddada mata ta yawaita shan ruwan gishiri da sugar, daganan suka fito, kana suka shiga mota, suna cikin tafiya ta hango mai yalo, "uhm honey yalo zanci" mamaki ne ya kamashi sbda bata cinsa kwata-kwata, tunowa da juna biyun dake cikinta yasashi saurin parking ya lek'a ta k'ofa yace "mai yalo..!" mai yalo ya rugo da gudu yana gaishe da Alhj Kabir,
"Duka na nawa ne?"
"Na dubu d'aya ne"
"Ok juye mana a leda"
Alhj Kabir ya mik'a masa 1500, mai yalo yace "na dubu d'aya nefa"
"Eh nasani wannan na baka ne"
Mai yalo yayi godiya tare da sanya musu a leda yayi musu fatan sauka lafiya.
Suna cikin tafiya Sajida ta kwantar da kanta jikin kujera, har suka iso bata saji ba.
Bayan ya shigo gidan yayi parking, ya dad'e yana k'arewa fuskarta  kallo, hankali ya shafi gefen fuskarta tare da manna mats kiss a kumatu, a hankali ta bud'e ido da fuskarta datayi fayau tace "harmun iso"
"Eh barin bud'e miki"
Dariya tasa kafin tace "haba sai kace jinjira?"
"Uhm ai kinfi jinjira babyna"
A inda yayi maganar sai ya bata dariya, suka fito a tare, babu kowa a parlon,
Zama tayi tare da jingina da kujerar, "Hajiya..!"
"Nafisa..!"
"Kufito kuji abin farinciki"
Alhj Kabir ya fad'a muryarsa cike da nishad'i,
Har suna rige-rigen fitowa tsabar son jin k'wa-k'waf,
Hajiya mama tana fitowa tace "to muna jinka"
Nafisa ma haka, fuska ba yabo ba fallasa tace "muna jinka"
"Sajida na d'auke da juna biyu"
Ya mik'awa Nafisa results d'in, mood d'inta ne ya sauya tashi d'aya, ita kanta batasan yanayin natan ya sauya ba, sai kuma ta k'ak'alo fara'ar dole tace "wayo dad'i anty Sajida zata haifo mana baby"
Kasancewar babu wanda ya lura da yanayin data sauya suna can suna firarsu da Alhj Kabir da Hajiya mama, ta kalli Nafisa tace "cikin haryakai wata nawa? Wata d'aya ne Hajiya"
Nafisa ta fad'a tana kuma k'ak'alo murmishi, it's kam Sajida har bacci ya Kuma gaba da ita,
Wata muhimmiyar fara'a Hajiya take ga wani rawar k'afa da take, bini-bini tana d'akin Sajida tana tayata hira, zaman parlo ma tayi masa k'aura.
Washe gari ta kama, lahadi, tun dare aka fara ruwa har asbha tayi ba'a d'auke ba, kasancewar muna watan ogusta, ruwa ake bana wasa ba, Alhji Kabir bai sami zuwa masallaci ba, tare sukayi sallahr shida Sajida, bayan sun idar sunyi adu'oi sun gaisa, yayi mata ya jiki, "da sauk'i" tace masa, har ya murd'a handle d'in k'ofa zai fita tace "honey inason cin tuwon shinkafa miyar wake" angama my baby" kijira zuwansa insha Allah"
Alhji Kabir ya fad'a jiki na rawa ya fice..!

# Love
# Romantic
# Funny

Domin magana da marubuciyar 08141799124


_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

*🫦TSAUTSAYIN TAUNA🫦*

✨GAWURTATTU BIYAR✨

*Zainab Habib (Mom Islam*

Page 7-8
Yana fita kai tsaye d'akin Hajiya mama ya shiga, bakinsa d'auke da sallama, bayan ta amsa ya k'arasa kana ya durk'usa ya gaisheta, gyara zama yayi kana ya kalli agogon wayarsa, "k'arfe

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment