Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fito daga bakinsa kenan,
"Haba likita abin bana fad'a bane Kuma babu dole a ciki so zaka iya amincewa zaka iya k'in amincewa"
Ta k'ara da cewa "na rubuta komai a cikin pepper d'innan wacce nakeson ayi aikin a kanta zan  shigo da ita ka ganta koda lokacin ya cika" tana kaiwa nan ta ajiye takardar ta fice.
Har ta dawo ta zauna, Sajida bata dawo ba, sai da ta dad'e a zaune sannan ta dawo, tana cewa "wash nagaji wallahi, kiyi hak'uri na zaunar dake ko"
"La anty Sajida babu wani zaunar dani da kikayi, kin kar6o magani ne?"
"A'a yanzu dai zan shiga kar6a gurin likita acan gurinsu ya k'are"
Sajida ta fad'a tana cirar kud'i a Jakarta,
"Muje in rakaki"
Nafisa tace "tana biyota a baya"
Suna shiga office d'in, doctor ya had'a ido da Nafisa, kashe masa ido tayi, kasancewar Itace a baya, hakan yasa Sajida bata fahimci duk abinda ke faruwa ba,
Tana mik'a masa card ya had'a mata magunguna kana yace "taje ta kar6i allura, tariga Nafisa fita, sai Nafisa tayi kamar ta fita sai ta dawo, tana dawowa tace "zan iya samun numberka?" Yes"
Ya fad'a tare da mik'a mata address d'insa da komai da komai, a wani card.
"Tnks sai naji daga gareka"
Ta fad'a tare da ficewa
Lokacin data fito Sajida ma ta fito suka wuce inda motarsu take,
Suna shiga Sajida ta kalli Nafisa kana tace "kinga irin shan wahalar da nake baki labari gashi ko wani abun bamu siya ba"
Nafisa tace "ai gida zamuje anty maci acan".
Da isarsu gida driver yayi parking suka fito a gajiya, Allah ya taimakesu  yanzu akwai y'ar aiki, ta gama komai.
Sai da sukayi Azhar sanan suka fito cin abinci, Hajiya ma ta fito tayi musu sannu da zuwa.
Suna cin abinci suna hirar asibiti, da yamma kuwa bayan anyi la'asar, Nafisa ta shige d'aki, number momynta ta danna, tana shiga momyn ta d'aga, tare da cewa "an sami kud'in?"
"Uhm momy mafita aka samu kinsan dai babu inda za'ayi ya barni in sake fita amman ki turo Salma zan sanar da ita komai dan ko yak'i ko yaso dole yayi min 6arin kud'i wallahi sai nayi rawa da tsalle duk a lokacin da naso"
Momy tayi farinciki tare da cewa "zatazo gobe da Rana insha Allah"
Daganan sukayi sallama...!

# LOVE
# ROMANTIC
# FUNNY

Domin magana da marubuciyar 08141799224
*🫦 TSAUTSAYIN TAUNA🫦*

*Zainab Habib (Mom Islam*

11-12

Washe gari, bayan sunyi breakfast, Alhji Kabir na shirin fita aiki, Nafisa ta tambayeshi zuwa gidansu k'awarta Salma,
Beyi mata musu ba, saboda yasan aminttakar dake tsakaninsu, k'arfe 10:am ya fito tafiya aiki, lokacin ita Kuma ta shirya suka fita tare.
Suna isa anguwar yayi parking a k'ofar gidansu Salma, ya mik'a mata 3k tare da ce mata karta jima ta koma gida.
Godiya tayi masa kana ta shiga gidan da sallama, wata dattijuwar mata ta samu zaune akan kujera tana gyaran shinkafa, bayan Nafisa ta gaisheta tace "Salma na nan kuwa?"
"Ai sun kwana biyu da tashi, babu wanda yasan anguwar da suka koma".
Nafisa tayiwa matar godiya ta fito bakin titi ta tari napep zuwa anguwarsu wato anguwar Dosa, bayan mai napep ya sauketa ta bashi kudinsa,
Nocking tayi a bakin get din gidansu, mai gadi ya bud'e tare dayi mata sannu da zuwa, kai kawai ta gyad'a masa kana ta shige part d'in momynta, zazzaune ta samesu, momy da kanwarta Salma.

"Oyoyo anty Nafisa, dafa yau zanzo"
Nafisa tayi murmishi hadi da cire mayafi ta ajiye gefe, tace "momy wallahi na gaji".
Momy dakeyin waya, sai yanzu ta ajiye wayar tace "ashe kina hanya, gara da Salma batajeba"
Nafisa tace "aikuwa dama na fito ne akan zuwa gidansu K'awata Salm, naje ashe sun tashi".
Momy tace "subanallah ina suka koma?".
"Ai babu labari momy"
Nafisa tace "momy kawo kunnenki"
Ni kaina bansan me ta rad'a mata ba, gani nayi kawai suna dariya,

Momy ta daga waya ta kira dadynsu Nafisa, ring d'aya ya d'aga tare da cewa "uwar gida sarautar gida".
Kai tsaye momyn tace "Alhji inason zuwa anguwa"
Dadyn yace "to Allah ya dawo dake lafiya barinyi miki transfer"
Momy tace "to nagode Alhji Allah ya k'ara bud'i.
Momy ta kalli Nafisa, kana tace "tashi muje gidan Malama Saratu mai mallaka, Nafisa ta ta6e baki kana tace "momy ai ta farkon naji kamar ba wannan sunan bane",
"Kee tashi maza wata aka samu nima tayimin aiki akan dadynku naji dad'i, shine nakeso kema ki gwada"
Salma ta zaro ido
"Momy kenan kin mallake dady kike nufi?"
"Ke dalla can, tunda Allah yayishi namiji meyayi saura, tashi kije kitchen ki Dora abinci mu fita zamuyi".
Daga haka momy tashiga d'akinta ta d'auki ATM da mayafi, sai yar k'aramar Jakarta ta dawo parlo suka fito zuwa parking space.
Drivers suna ganinsu suka fara cewa tafiya ne Hajiya, momy ta daga musu hannu alamar a'a.
A ranta kuwa cewa take, nasan irin munafurci na gidannan wallahi muddin ba fitar mukayi muka shiga motar haya ba, sai anbi didigi.
Suna isa bakin titi suka tari napep zuwa anguwar Mu'azu, ana saukesu Nafisa ta biya kudin, momy tayi musu jagora zuwa gidan.
Da shigarsu sukayi sallama, sun sami mata sama da uku a zaune suna jira, zama sukayi suma har sai da mutanen suka gama shiga sannan su momy suka shiga.
Bayan sunyi sallama suka nemi guri suka zauna.
"Sannunku da zuwa"
Malama Saratu ta fad'a tana kallon Nafisa.
"Yauwa sannu ina kwana"
"Lafiya ya gida"
Nafisa ta amsa da lafiya.
Momy ta koro mata jawabi from A to Z kana ta kara da cewa "yatace dan Allah a taimakemu, wannan muguwar kishiyar tata tana wahalata, gashi ta janye hankalin uwar mijin a kanta, ni kaina kawatace Amma yanzu munsau hannun riga.

Saratu mai mallaka, tayi murmishi kana ta daga kasan wata kwarya ta dibo kullun bak'ar leda guda biyu, ta mikawa Nafisa tace "wannan matsi zaki dingayi dashi, daga lokacin daya kusanceki wallahi saiya yabawa aya zakinta, wannan Kuma shafawa zaki dingayi a fuskarki kullum safiya dazarar kin idar da sallahar asbha".
Nafisa tasa hannu biyu ta karba tana godiya.
Momy tace "ai mutuminki bina yake sau da k'afa, harda yimin kyauta"
Malam Saratu tace "ai na fad'a miki abinda zai baki nan gaba ma zakisha mamaki, kedai kici gaba da gashi".
Momy ta ajiye mata 20k tare da cewa, ki bani account number d'inki zanyi miki transfer kema kici albarkaci".
Sukayi dariya a tare, momy da Salma sukayiwa Saratu sallama suka fito.
A napep wayar Nafisa tayi Kara, tana dubawa taga number Salma kanwarta, Nafisa ta kalli momy kana tace "Salma cefa mai Kira,
Momy tace "to d'aga mana"
Nafisa ta amsa, "anty dan Allah kicewa momy ta kar6ar min maganin farin jinin samari, Amma masu kud'i".
Nafisa tayi tsaki hadi da cewa "dalla rufawa mutane baki taki matsalar karamace".
Tana fadar haka ta kashe wayar.
"Menene naji kina fad'a?"
"Momy wai yarinyar nan saboda batada kunya take iya cemin wai in gaya miki ki kar6o mata maganin samari?".
Nafisa ta k'arasa maganar mamaki ya gama kamata,
Momy tayi tsaki mtsw, wawuya shine wani abu, dame yan matan suke tak'ama yanzu ba sai sun had'a da gurin  malamai ba?".
Shidai mai napep nata dariya yana gaba.
Momy ta wuce gidansu, Nafisa ma ta wuce gidanta.
A gajiye Nafisa ta koma gida.

Washe gari.
Kamar inda malam Saratu mai mallaka ta gaya mata, ta shafa wannan magani bayan tayi sallar asbha, ta fito parlo.
Babu kowa a parlon sai ita kad'ai, abinda bata cikayi ba kenan wato fitowa da wuri,
Motsin bud'e k'ofa taji ta gyara zaman mayafinta, burinta Alhji Kabir na shigowa yayi tozali da idonta.
Cikin sa'a yayi sallama, ta amsa ta murmishi, ya d'auka ta zauna domin tayi masa surprise, sai yaji tace "barka da safiya Alhji"
Ya kasa dauke ido daga kanta, saboda fuskarta tana yi masa wani irin haske gami da kwarjini da dad'in kallo, da kyar yayi kiciniyar janye idonsa daga nata, kafin yace "barin karasa ciki".
Sai daya wuce d'akin Hajiya mama suka gaisa sannan ya wuce d'akin da yake, wato d'akin Sajida.
Yana shiga ya sameta tana shafa powder, tasa doguwar riga irin y'ar kantinnan, ta dameta, cikin ya fito sosai yayi mata kyau, fuskarta ta mugun ramewa, duk Wanda yasan alamun mace ta kusa aihuwa ga yanayin da take kasancewa to a fannin Sajida ma haka ne, saboda fuskarta ta mugun ramewa sosai, hakan bai hana fito da ainihin kyawunta ba.
Hannun Alhji Kabir ta kama, kafin tace "barka da safiya baban twins"
Fuskarsa d'auke da murmishi yace "barka pretty"
"To...an sauyamin suna kenan?"
"Ked'in kyakkyawa ce, kobakiyi kwalliya ba"
Sajida tayi murmishi, kafin tace nagode Alhji".
Sai daya gama kwantar mata da hankali kafin ya shirya cikin lallausan yadi na boyel baki, sai shek'i yakeyi, sanya wayarsa yayi a gaban aljihu kana ya k'arasa gareta ya shafi cikin tare da kai kunnensa gurin cikin yace "Wai banajin suna yimin bye²?" Sajida tayi murmishi, tace "muje kayi breakfast"
Suka fito tare, yana Kara yin arba da fuskar Nafisa, tunaninsa da kwakwalwarsa suka kusa kaucewa daga jikinsa, k'ok'arin control d'in kansa ya farayi, kar Hajiya da Sajida su fahimci wani abu, itako wacce tayi dominshi ta gano tarkonta ya kama.
Suna gama karyawa ya fice, batare daya Kara wasu tsawon lokuta ba.
After 7 days
Ranar Friday, Sajida ta shirya zuwa gidansu, dakyar Alhji Kabir ya amince zai kaita, da yace ta bari saita aihu, sai da Hajiya mama tasa baki sannan ya amince zai kaita inya dawo daga gurin aiki zai wuto gidansu ya dawo da ita gida.

Koda suka shiga mota suka fita daga gidan, a hankali yake tafiya da motar kamar wanda zaiyi parking a gefe, har suka iso gidan.
A tare suka shiga dashi ya gaishe da iyayen Sajida ya bata 3k ko zata buk'aci wani ,
Gidansu Sajida madai-daci ne, mahaifiyarta ita kad'ai ce, sunanta Hajiya Fatima tun auren saurayi da budurwa da sukayi da mahaifin Sajida har yanzu suna tare, yaranta biyar, Samir, Sajida dakuma Zainab da Lirwan
Samir shine babban yayansu, yana aiki a Gombe, yana harkar siyarda motoci da mashina, Sajida ce mai binsa sai Zainab da take karantar likita, sai Lirwan shine karaminsu, shekararsa biyar Zainab kuwa 17, yaran sun taso cikin gata ilimi da tsoron Allah ga taimakon duk wani mabukaci, mahaifinsu mai suna Alhji Halliru, yana kasuwanci ne a Kano yana siyarda kayan kitchen, shagunansa sunkai biyar, mutumne mai mutane ga kyauta uwa uba rikon addini.
Wannan kenan.

Part daya ne a gidan Wanda zamu iya Kiran gidan da muhadu a parlo, a ciki akwai dakuna, na Ammi dana Yaya Samir, dana Zainab dana Lirwan Dana baki, sai kitchen, kasancewar kowanne d'aki yanada toilet.

Babban parlon nasu kuwa, ya cika da kayan alatu na rayuwa, kama daga kan kayan kallo harzuwa kan su kujeru.

Sajida tayi sallama fuskarta d'auke da murmishi,
Ammi fara ce tass idan ka ganta kamar balarabiya, Amma Sajida bata d'auko haskenta ba, komai na mahaifinsu ta d'auko, Yaya Samir da Zainab ne sukayo farinta sai Lirwan da shima yakeda nashi hasken Amma bai kaisu ba.
Cikin fara'a Ammi ta taso tana mata lale, Sajida ta rungume Ammi da tulelen cikinta, tana cewa "Ammi ko nemana bakwayi ina Zainab?"
Ammi dai na fara'a tace "aikuwa muna nemanki, Zainab tana makaranta".
Yakice mayafin jikinta tayi kana ta cire riga ya zamo iya d'aurin k'irji tayi, tace "Ammi zafi nakeji zan watsa ruwa"
Ammi tace "ai dole kiji zafi,shiga ki watsa ruwa".
Tana tafiya, Ammi ta rik'e baki kafin tace "nadai San tanada ciki amma yaushe yayi girman haka?"
Tana tsaka da tunani Sajida ta dawo ta zauna, sai lokacin suka gaisa, Ammi tace "ashe da sai dai muji aihuwa kawai?"
Sajida tayi dariya, sai da Ammi ta tambayeta su Hajiya mama da Nafisa tace "mata duk suna lafiya".
Sajida tace "Ammi albishirinki?"
Ammi na mayar mata da fara'ar tace "goro fari tass"
"Ammi da mukaje asibiti, scanning sukace yan biyu zan haifa"
Wani irin farinciki ne ya lullu6e Ammi abinda suka dade suna roko a gurin Allah, suka dade suna nema gashi har biyu Allah ya basu, Ammi tayi fatan alkairi tare da cewa "Allah ya nuna mana wannan rana",
Sajida ta amsa da "Amin".
Sai wajen yamma yaya Samir ya shigo, haka ma Zainab Lirwan dama yana nan, school d'insu k'arfe 1:pm ake tashi.
Sai da taci abincin dare kasancewar suna gamawa da wuri.
Sannan Alhji Kabir yazo suka tafi.
Suna isa gida anayin sallahar magriba, Hajiya da Nafisa na ganinta suka hau yi mata sannu da dawowa, Sajida na had'a ido da Nafisa taji wani irin sonta da tsoron 6ata mata rai ya shigeta,
Washe gari.
Sajida ta tashi da matsanancin ciwon baya da mara, a ranar cikinta ya cika wata Tara da kwana goma, sosai take rik'e baya da mara, Hajiya mama ta rikice, hatta Nafisan sai abin yaso bata tsoro, saboda bata ta6a ganin mai nakuda ba, a ranta kuwa cewa take "dama haka nakuda take? dama haka zafi da rad'ad'ints yake?"
Tayi saurin cewa "idan na bari tausayi ya shigeni, tabbas bazan aiwatar da abinda nake buri ba".
"Akira driver"
Muryar Hajiya mama ta qwqdoki dodon kunnenta, da sauri Nafisa fice tayiwa driver magana Alhji Kabir na dawowa daga masallaci, bai jira driver ba, a gigice yayiwa motar key suka bar anguwar, kai tsaye asibitin Giwa hospital suka nufa, suna isa aka wuce da ita d'akin aihuwa,
Likitoci biyu ne a kanta, kasancewar dakunan kamar ciki da parlo ne, Kuma duk masu aihuwa ne a ciki, dukkansu babu wacce take cikin haiyyacinta, sakamakon allurar bacci da kowwacce ta samu,
Cikin hukunci da izza ta ubangiji Sajida ta haifi y'ay'anta guda biyu, namiji da mace, tana aihuwa akayi mata allurar bacci mai nauyi sosai, ko kallon yaran batayi ba baccin ya d'auketa.
Doctors na aiki Nafisa ta kira waya,
Rakube take a hanyar toilet na hospital d'in, a zahiri tace wa su Hajiya mama zatayi fitsari ne, nan ko ba haka bane,
"An kammala komai?"
Likitan ya takice zufar data karyo masa kana yace "da saura"
Ta katse kiran itama gumi na sunturi a fuskarta.
Saida suka d'auki tsawon awanni, kafin suka fito, fuskarsu d'auke da takunkumi, kallon Alhji Kabir sukayi cikin yanayi na ban tausayi kana sukace,
"Alhaji sai dai hak'uri, yaran da aka Haifa daya ta koma namijin yana nan"

Hajiya mama tahau yiwa Alhji nasiha tana cewa "ka fauwalawa Allah komai, yafika sonsa dan haka ka gode masa da baiwar da yayi maka"
Ya rigada ya dorawa yaran buri, hawaye ya zubo a fuskarsa ya share tare da cewa Alhmdulilh"
Nafisa tahau borin kunya tana cewa "Ina Wanda yake nan din zamu iya zuwa ganinsa?"
"Yes zaku iya zuwa"

Suka shiga dukkansu, sun samu ankai Sajida d'akin hutu, yaron yasha kayan sanyi sai neman nono take yana tura yatsunsa biyu baki.

Hajiya mama tace "Masha Allah kaga yaro ya d'ibo kamar gidan babanshi"
Ran Nafisa ya fara 6aci, bataso aka rage wannan yaron ba, taso a had'a dashi koma inane a kaishi, sai likitocin suka nunar mata da asirinsu zai tonu,
Alhji Kabir yayiwa yaron adu'a sannan ya tofa masa, Nafisa kuwa sai uban rawar k'afa wanda, su kansu babu wanda ya gane abinda ke faruwa.

Sai wajen k'arfe 12:pm sannan Sajida ta farka, bakinta d'auke da sunan Allah, likitar dake kanta tayi mata sannu tare da turota d'akin da yaron yake, ana kaita idonta yakai kan yaron, "ina dayar?"
Abinda bakinta ya furta kenan a karo na farko data shigo d'akin.

"Tana bacci shi ya tashi ne"
Hajiya mama ta fad'a tana kallon Sajidar,

Sai wajen k'arfe d'aya na rana sukabar asibitin, tare da gawar jaririya wacce ba tasu ba, suna zuwa gida akayi mata wanka da sutura da duk wasu abubuwan da suka wajabta aka binneta.

Tunda suka dawo gida, mutane suketa sintiri, Zainab k'anwar Sajida ma ta dawo gidan, a cewarta kwana uku zatayi, abubuwan data lura dasu da yawa a gidan, komai za'ayi na dangane da mai jego, sai dai Sajida tace a kirawo Nafisa sai abinda tace, idan akaje gurin Hajiya mama itama hakanne, idan Alhjin nema shima sai abinda Nafisa tace shi akeyi.
*🫦 TSAUTSAYIN TAUNA🫦*

*Zainab Habib (Mom Islam*

Page 13-14

Wannan abu ba k'aramin yiwa Nafisa dad'i yakeyi ba, anyi suna na gani na fad'a, inda yaron yaci sunan Mubarak,
Y'an uwan Ammi sun tambayi wankan gida, Hajiya mama tace "meye amfanin zamanta a gidan?", dole suka hak'ura suka bar Sajida.

Bayan suna Nafisa na zaune a d'aki tana latsa waya, da misalin k'arfe 4:pm, kiran doctor ne ya shigo wayarta, da sauri ta sauke numfashi tare da gyara zama, tana nazarin magana ko Kuma amsar da zata bashi, dan zancen tasan baya wuce na kud'i.
Kara wayar tayi a kunnenta da sallama.
"Hajiya mun cika aikinki kamar inda kika buk'ata, zamu turo da account number ne?".
"Eh...eh kuturo zuwa gobe da safe zakaji alert, Amma bakuyimin inda nakeso ba, saboda wannan magajinsa kuka bari",
Ta katse kiran.
Iska ta furzar mai zafi, had'i da buga k'afa,
Zuwa dare, Alhji Kabir yana d'akinta, kasancewar tunda Sajida ta aihu ya dawo d'akinta, k'arfe 8:20pm ya dawo daga gurin aiki, bayan yayi wanka yaci abinci, yana shirin janyo laptop d'insa ya duba, ta ratayo hannunta a wuyansa, muryarsa k'asa-k'asa yace "Hajiya Feenat ya akayi?",
"Uhm Alhji, wata matsala ce ta afku da K'awata Salma, y'an garkuwa da mutane sun kamata, gashi basu da isashen kudi, shine hankalina ya kasa kwanciya", tana kaiwa nan ta manne a jikinsa tare da fashewa da kuka.
"Is okay my wife, don worry, zan taimaka musu insha Allah, ammafa saboda ke"
Yaja kumatunta, kana yace "kamar nawa kikeso a basu?"
"200k ma yayi wallhi sunce zasu kasheta"
Alhji Kabir ya zaro ido, kana yace "sunyi yawa Ina lefin 50k?"
Kuka Nafisa tasa tare da k'ara k'amk'ameshi, tana cewa "kayi taimako inhar kana Sona".
Suna had'a ido da ita, yaga tayi masa wani irin kwarjini, da sauri yace "zan turo gobe bani account number" jikinta na rawa tace "turamin a nawa inyaso sai inyi musu transfer"
"No, banaso kisa kanki cikin matsala"
Kuma marairaice masa tayi, dole ya yarda zeyi mata ta account d'inta.
Washe gari, bayan anyi sallahr asbha, kowa ya koma bacci banda Nafisa da hankalinta ke tashe, saboda a tsorace take, kar doctor ya kirata, tasan inhar ya kira Alhji Kabir saiya tambayi waye?.
Har gari ya waye tana zaune tana karanta wasik'ar jaki.
K'arfe 9:am Alhji Kabir ya tashi daga bacci yayi wanka, ya shirya cikin k'ananun kaya, sai da yayi mata transfer sannan suka fito a tare, ita ko wankan bata samu tayi ba, kamar inda tasabayi kullum, amma duk da hakan babu wani datti a tare da ita.
Suna isowa parlo babu kowa sai breakfast da aka jere a dinning, d'akin Hajiya mama Nafisa taje, ta gaisheta kana ta wuce d'akin Sajida, tana shiga ta sameta a zaune a kan gado tanacin farfesun kaji, hannunta rik'e da jariri, wani uban kishi da tsanar yaron ne ya lullu6e mata zuciya, dakyar ta yakice ta aro murmishi ta yafa a fuskarta kafin ta zauna tace "barka da safiya anty Sajida dafatan big boy ya tashi lafiya"
Sajida ta mik'a mata yaron, tana cewa "aikuwa gashinan lafiya lau sai tsotso da yayi masa yawa",
"Kai karfa ka k'arar min da aunty kaji"
Nafisa ta fad'a tana dariyar da iya kacinta fuskarta.
Fitowa tayi da yaron ta kawoshi d'akin Hajiya mama, tana cewa "gashinan kunyi kama sak Hajiya mama"
Hajiya mama tayi dariya kafin tace "lallai wannan y'a, Ina kamar take?"
Nafisa na dariya ta mik'a mata shi ta fice,
Koda ta isa parlo ta samu Alhji Kabir harya fara Shan tea, ta k'arasa tana jifansa da murmishi mai kyau, Wanda ya lullu6e makircin datake shirin k'ullawa.
"Alhji farfesu za'a zubo maka ko yam balls?"
"Zubomin farfesun sauri nakeyi"
Bayan ya kammala ta rakashi, parking space ya shiga mota ya wuce gurin aiki.
Yana mota yana ganin transfer din da yayiwa Nafisa kamar a mafarki, dan kansa har wani sarawa yakeyi, koda ya k'arasa gurin aikin ba wani abun kirki yayi ba.
Alhji Kabir na ficewa, Nafisa tayiwa doctor transfer hankalinta kwance.
After one week da faruwar hakan.
Gidansu Ammin Sajida.
Tunda Zainab ta dawo ta tayarwa da Ammi hankali, sosai Ammi ta shiga damuwa, saboda ce mata tayi  "an mayar da anty Sajida kamar gunki, bata da zabin kanta sai Wanda anty Nafisa ta za6a mata"
Ammi cikin sanyin jiki tace "da izinin ubangiji, inma sharri take nema, Allah bazai bata ikon yin galaba a gurin Sajida ba, narasa meyasa wasu matan suke kishin jahilci wallahi.
"Hmm Ammi, bakiga wainar da ake toyawa bane a gidan"
Zainab ta fad'a tana kallon Ammi.
Badan Ammin nason cigaba da saurarar zancen nata ba tace "ya isa haka, shiga kitchen ki d'ora mana abinci"
Zainab ta wuce kitchen zuciyarta babu dad'i, cike da tunanin halin da y'ar uwarta take ciki.
Gidan Alhji Kabir.
Washe gari, hankalin Nafisa ya kwanta, sai dai ba anan gizo ke sakar ba, an kashe maciji ba'a sare kansa ba, tana zaune gaban mudubi, lokacin k'arfe 12:3pm, tana duba wasu takardu, tana sanye da atamfa d'inkin riga da skirt, sunyi mata kyau, rurin neman agaji wayarta ta shigayi, a hankali tajanyo wayar tana duba sunan mai kiran "Doctor"
Ta fad'a cikin zaro ido.
"Mekuma yakeso dani?"
Sai da aka kuma Kira a karo na biyu sannan ta d'aga murya k'asa-k'asa tace "barka doctor ya akayi?",
"Am madam, munga sako mun gode, tofa ina tunanin kin mance da babyn ko?, tana raye fa, munbawa mai shayarwa ta dinga shayar da ita, dalilin da yasa na kiraki shine, mai shayarwar yau zatayi tafiya zuwa garinsu Niger, shine nace bari in sanar dake".
"Innalilahi wa inna ilaihir raji'un, meyasa baku kasheta ba? meyasa kuka barta da ranta? sokuke asirina ya tonu?".
Doctor yace "haba madam, kamar kin mance, munyi dake babu maganar kisa, Ina had'a kowanne irin makirci Amma bana kusa!."
Cikin in'ina wacce batasan tanada ita ba tace "to....to..zan...zo asi..asibitin anjima".
Hankale a tashe ta mik'e tare da Zagaye d'akin, tana kaiwa tana komowa, kamar me neman wani abu.
Lokaci d'aya ta tsaya cak, "ina zankai wannan shegiyar yarinyar?"
Ni har na baje k'afa akan komai ya kammala",
Wayarta ta d'aga ta danna number momynta, kamar jira momyn take, ta amsa kiran,
Cikin tashin hankali tace "momy shikenan an yanka ta tashi, momy asirinmu zai tonu, yarinyar dai tana raye, momy kaina ya kulle, momy ki taimakeni momy zan haukace",
Ta k'arasa maganar tana fashewa da kuka.
"Haba Nafisat..,kamar bana numfashi a doron kasa, inhar kikaga kin wulakanta to tabbas na mutu ne, koda na mutu ma bana fata inganki a hakan dan saina tabbatar da kafuwarku ta har abada a gidan mazajenku"
Momy ta fad'a tana lallashinta.
"To momy meye mafita? doctor yace muje mu d'auko yarinya",
"Karki damu, kice masa yayi hak'uri zuwa gobe sai muzo"
Nafisa ta waro ido tare da cewa "momy yau me rainonta zataje garinsu fa"
Momy tace "au kin damu da rayuwarta kenan? idan zataje garinsu saita dawo ki kyaleta wata kila yunwa ma ta kasheta kafin goben".
Cikin amincewa da zancen momy, Nafisa tace "to Allah ya kaimu".
A 6angaren momy kuwa, suna gama waya da Nafisa ta kira wata mata mai suna Ladi, cikin mintuna kalilan matar ta iso, tana zuwa bayan an kawo mata kayan motsa baki, taci momy tace "dalilin da yasa na kiraki shine, wata jaririyace mukeson baki ki riketa inhar kinaso?".
Jikin matar na rawa tace "inaso kai, sanin kanki ne Hajiya Sakina ban ta6a aihuwaba"
Momy tayi murmishi kana tace "to shifa mai gidanku?"
"Shima bashi da matsala ko kad'an"
Matar ta fad'a tana share hawaye,
"Yauwa, wannan ya zamo sirri tsakanina dake, ko zuwa gaba karki alak'anta yarinyar da gidannan,inhar kin amince gobe insha Allah sai muje ki kar6eta".
Ladi tace "haba Hajiya, nemafa mukeyi ruwa a jallo gashi Allah ya bamu".
Washe gari, da Nafisa da momy da ita Ladin, sukaje hospital suka d'auko yarinyar, Ladin ta wuce da ita gida, daganan suka rabu.
Da sallama ta shigo gidan nasu fuskarta d'auke da fara'a, malam Haladu na ganinta ya washe baki, kana yace "kamar goyo naga kinyi?, a ina kika samo yaran mutane da almuru?"
"Ah ai malam damuwa mukayi muje daga d'aki, in fed'e maka biri har wutsiya",
Malam Haladu yace "barinyi magariba tukunna, tunda zancen na zama ne.
Sai da yaje yayi sallah sannan ya dawo, ya shigo d'akin Ladin da sallama, lokacin tana bawa yarinyar ruwan d'umi a kofi, amsawa tayi tare da d'agowa ta kallesa kafin tace "yarinya aka bani, ta kwashe labarin komai ta sanar masa, da yake shima d'in yanason aihuwa amma Allah bai basu ba, yasa ko d'arr beji ba gurin amsar jaririyar, ya kar6eta yayi mata hud'uba da Aisha,
Suna kula da ita iyakar k'arfinsu, duk da ba kullum ake dora tukunya a gidan ba, wataran idan Ladi ta isheshi da masifa, yaje waje yayi kuka ya share, saboda gari babu aiki, dama wani lokacin inya mashinne, kokuma leburanci yakeyi, to yanzu komai ya tsaya cak, y'ar madarar da suke samu su siya mata yanzu ta kara kud'i, da suna siya nera hamsin, yanzu kuwa ta koma saba'in, sosai malam Haladu yake shiga damuwa akan rashin abincin da zasu bawa yarinyar, wani lokacin ya gwammace su zauna da yunwa akan yarinyar tayi ta damunsu da kuka.
Tun daga lokacin

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment