Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutane sunyi rad'e rad'insu sun gama, ko an tambayi Ladi Ina kika samo yarinya sai tace "ya yarinyar kanwatace, data rasu ta barta shine na d'aukota, ba y'an uwane da Ladin a garin ba, bare su tambaya suji gaskiyar magana, dole suka bar zancen a hakan.
GIDAN HAJIYA SAKINA.
Tun bayan tafiyar, Ladi daga gidansu, momy da Nafisa suka dawo gida.
Nafisa tace "alhmdulilh momy naji dad'i, gaskiya duk Wanda ya rasa uwa to yayi kuka"
Momy tayi murmishi kafin ta shafa kan Nafisa, dake danneĀ² a waya tace "ke y'arnan akwai ragowar aiki a gabanmu, saboda karfa azo wannan likitan ya tona mana asiri, inaso a sake mallake miki Alhji Kabir, saboda inajin gaba, koda komai zai faru bazai ce uffan ba, sai dai ya zuba miki ido sai inda kikayi da lamarin".
Momy ta k'arashe maganar tana yin makirin murmishi.
"Yauwa momyna haka nakeso wallahi kamar kinsan nafara tunanin hakan, kizo gobe insha Allah muje gurin Saratu mai mallaka"
Nafisa ta tashi zaune, kana tace "momy kinsanfa zai iya cewa fitarnan tayi yawa, ba lallai a satinnan ya barni in sake fitowa ba",
"Okay to duk inda mukayi da ita zan Aiko Salma saita kawo miki",
"Nafisa tasa mayafinta tare da cewa "momy akwai wata humra da kika ta6a bani, wallahi tanada kyau, kinga inda Alhji yake kallonta kuwa?"
Momy tayi dariya, kana tace "wato Nafisa yanzu kin dena jin kunyata ma ko?"
Dariya Nafisa tayi tana cewa "momy dan Allah idan akwai ki bani zan tafi"
Suka shiga bedroom d'in momyn tare, momy ta bud'e mata wani akwati, d'an k'aramin mai d'auke da turaruka iri-iri, Kuma ko wanne da amfaninsa,
"Wanne kikeso?"
Nafisa na dariya tace "ai momy ko wanne tsiyayamin za'ayi"
Dariya momyn tayi mata kana tace "aikuwa sai dai ki za6i guda biyu, saboda wad'anan akwai wanda ban gama biyan kudinsu ba".
Dole badan tasoba ta zabi biyun, momy ta zuba mata a kwalba, sai da tayi sallahar la'asar sanan ta koma gida.
Tana isa ta shiga da sallama, turuss tayi ganin k'awarta Salma a parlo, mamaki da matsanancin tsoro ya kamata, a sukwane ta k'arasa ta lullu6e tsoron dake barazanar karyar mata da zuciya, ta washe hakora tana cewa "oyoyo Salma yaushe kikazo?"
Hajiya mama da Sajida sukayi murmishi, Hajiya mama tace "tun bayan da akayi sallahar Azhar ta shigo, munyita gwada lambarki tak'i shiga",
Nafisa ta zauna tare da cewa "wallahi na mance tun jiya bansa waya a chaji ba, Ina zuwa gidanmu na tuna, shine na kashe wayar saboda tayi saurin cika"
Salma tace "oh Nafisa ko cigiyarmu babu?"
Nafisa nata fakar idonsu, Hajiya mama da Sajida tanayi mata k'ifce, akan tayi shiru, Amma Salma bata ganeba.
Bayan shiru daya biyo baya, Hajiya mama ta fara tashi ta shige d'aki, daga can d'akin Sajida, ita Kuma wayarta tayi ringing, hakan ya basu damar tafiya d'akin Nafisa domin su tattauna, hakan yayiwa Nafisa dad'i sosai.
Bayan shigarsu d'aki, Nafisa tace "mekikeso a dafa miki?"
"No.. Ina sauka aka cikamin gabana da abinci, a halin yanzu na k'oshi".
Ajiyar zuciya Nafisa ta sauke, kana ta yiwa k'ofar key, kafin ta dawo kusa da Salma ta zauna,
"Naje gidanku ancemin kun tashi?"
"Eh hakane, wallahi mugun mutumin Wanda muke hayar gidanne ya matsa mana"
Nafisa tace "to Ina kuka koma?"
"Badarawa"
Salma taba Nafisa amsa.
"Yauwa yanzu dai turomin account number d'inki"
Jikin Salma na rawa ta turawa Nafisa, kana tace "Wai kud'i zaki turamin?"
"Yes"
Nafisa ta bata amsa, wow dama jiya garin kwaki mukaci muka kwanta, gashi yauma sai da Umma taci bashi",
Nafisa tayi murmishi kana tace "karki damu nayi miki transfer na 50k please babu yawa, Amma kafin nan akwai abinda nakeso dake,
Suna cikin magana alert d'in ya shigo, Salma ta daka tsalle tare da cewa "gaskiya kawar arzik'i samun kamarku sai an tona"
A hankali Nafisa tace "Salma koda Alhji ya kiraki yace miki ya mukaji da abinda ya faru, kiyi masa godiya kamar zaki ari baki, kice masa kin gode da taimakonki da yayi, akan in taimaka miki ne yasa na kar6i wannan kudin a hannunsa, ashema kina hanya, kima kirashi yanzu kokuma bari in Kira miki shi a wayata",
Nafisa ta danna number Alhji Kabir, Ring daya zuwa biyu ya d'aga, Hajiya Feenat ya gida ya kike?"
"Lafiya Lau Alhji ga Salma Allah ya fito da ita, zatayi maka godiya akan taimakonta da kayi"
"Laa ai babu komai Hajiya Feenat yiwa Kaine"
Nafisa ta mik'awa Salma wayar,
Bayan sun gaisa Salma tace "Alhji nagode da taimakona da kayi, ubangiji ya tsare gabanka da bayanka, Allah ya kareka daga dukkan sharri mungode, ta k'ara da cewa "Umma ma tanayi maka godiya kafin tazo".
Yaji dad'in adu'ar Sosai shima yace "ya gode" sukayi sallama da Nafisa ta ajiye wayar

*šŸ«¦ TSAUTSAYIN TAUNAšŸ«¦*

*Zainab Habib (Mom Islam*

15-16

Gidansu Baba, Haladu.

Yana iya bakin k'okarinsa, gurin ganin ya ciyar dasu, amma duk da hakan wani sa'in, abun sai ya faskara, wannan shine tak'ai taccen labarin.

Muje zuwašŸ¤™.

Kamar kullum, tun bayan rasuwar Malam Haladu, maman Aisha ta, hana Aishar sak'at, kullum suna hanyar bara.

Washe gari, an tashi da matsanancin sanyi, wanda yasa tun bayan sallahr asbha da sukayi suka koma bacci.
Maman Aisha ce ta fara tashi, ta d'auki man shafawa ta mutsika a k'afafunta, ta d'auko sanda da kwanon bara, tazo kan Aisha dake kwance a kan katifa tafara k'wala mata kira,
"Aisha.. Aisha.., za'a kuma yi miki wani darenne?."

Da sauri Aisha ta tashi zauneĀ  tana mutsike idanu,
"Yi maza sauko muje, ana rabon dukiya a titi, mu mun kwanta baccin asara".

"Mama nikam bacci nakeji wallahi har yanzu bai isheni ba".

"To shikenan, asararriya, ki kwanta ni zan fita, wallahi zakisha mamaki, kindai san yanzu bamu da kowa sai Allah, bamu da mai bamu inhar ba fita mukayi muka samo ba".
Cikin sanyin jiki Aisha ta sauko, ta d'auki man shafawa itama ta shafa, tasa farkakken hijabin daya zame musu jiki, idan zasuje bara yagaggen hijabi sukeĀ  sawa.

Tana gama shafawa, tace "mama muje"

Maman Aisha ta mik'e hannunta rik'e da sanda, tace "Aisha rikemin kwano".

Rik'e kwanon tayi, jikinta har yanzu a sanyaye,
Batare da tunanin yin karin kumallo ba, suka fice, bakin titi suka tari mai mashin.

Da isarsu, mabaratan gurin suka fara gulmarsu,Ā  baba Indo dake zaune tana cin burodi tace "Ladi ashe zakizo?"
Maman Aisha ta ajiye sanda, tace "barkanku, wallahi dole ce ta sani fitowa, in baka fito nema ba, babu mai baka.
Baba Indo ta kira Aisha ta gutsura mata burodi, hannu baka hannu k'warya Aisha keci kamar wacce tayi kwana biyu bataci komai ba.

K'arfe 9:11am wata galleliyar mota tayi parking a gabansu, dukkansu suka mike da gudu, har zanin wata na fad'uwa, Allah yasa akwai sikel din ciki.

Aisha ce dafe da gilashin motar, tana cewa "Alhaji baka bamu ba, kaga har yanzu ko kalaci bamuyi ba".

Dubbanta yayi, kallo na tsanaki kafin yace "ke beauty girl me sunanki?",
Cikin sauri da dariyarta mai kyau tace "Aisha, ga mamana can"
Ta nuna Ladi.
Jinjina kai yayi, yasa hannu a aljihu ya ciro kud'i, wanda shi kansa besan adadinsu ba, ya mik'awa, baba Indo dake cewa "a temaki makauniya",

Da gudu ta koma gurin zamansu, mutumin ya fara tunanin, anya makauniyar ce kuwa? tunda gashi har tasan tayi tafiya mai hade da gudu.

Aisha ta katse masa tunanin ta hanyar cewa "Alhji kaba kowa Ni baka bani ba?",

Hankalinsa yana kan, mamanta, yana yi mata kallon tausayi.

"Kiramin mahaifiyarki",

Aisha taje gurin mamanta da sauri tana tsalle tace "mama kizo inji wancan Alhjin na cikin motar can".

Maman Aisha ta mik'e tare da k'ir-k'iro, yanayi na mugun talauci da wuyatuwa ta isa ga Alhjin dake cikin motar,
"Sannu Alhji barka da safiya",
"Yauwa barka ya gida ya halin rayuwa".

Maman Aisha ta amsa da, alhmdulilh gamunan a cikinsa.
Alhjin ya numfasa kafin yace "idan babu damuwa inaso ki bani Aisha muje gidanmu, wallahi nayi miki alk'awarin bazan cutar da ita ba".
Ya k'arashe maganar yana hade hannayensa biyu.

Maman Aisha ta kalli Aisha da keta dariya tace "to Alhji kasan yanzu duniya babu gaskiya, ina tsoron a batar min da yarinya ko kuma a cutar min da ita, ta hanyar da Allah ya haramta".
Tana kai k'arshen maganar tasa kuka,
"Aisha ita kad'ai ta ragemin a duniya, bani da kowa, Allah ne kad'ai gatana, sai Aisha".
Ta k'arashe maganar tana waigawa taga, sauran mabarata yan uwanta.
Alhjin yayi murmishi, kafin yace "baiwar Allah nasan zafin komai na rayuwa, bazan cutar miki da yarinya ba, kawai inason muje gurin mahaifiyarta ne da ita".

Maman Aisha tace "gobeĀ  kazo sai muyi magana".

Wasu mahaukatan kud'i, ya ciro ya mik'a wa Manan Aisha, tare da cewa "sai goben nagode".

Maman Aisha na komawa gurin zamansu ita da Aisha ta, tattara kayansu suka wuce gida, mabaratan gurin nata gulmarsu, duk da babu wani abun da sukaji.

Suna sauka a mashin, tace Aisha takai kayan barar gida, ita zataje ta dawo,
Kamar inda maman ta gaya mata, hakan tayi ta wuce gida, tana zuwa ta bud'e jakar bakon da kud'in ke ciki, zaro ido tayi had'e da jin tsoro, da sauri ta gyara ledar ta wurgata uwar d'aki.
Maman Aisha kam, wucewa gurin mai siyarda manya-manyan kaji ta siyo manya guda uku, Wanda koda aka gaya mata kudinsu, bata tsaya cewa sunyi tsada ba, ta hado da lemun gora da ruwan leda.
Kai tsaye ta dawo gida.
Aisha na ganinta tahau murna, ta karbi ledar hannunta,
Bayan maman Aisha ta zauna akan kujera doguwa taceĀ Ā  "mik'omin ledar nan"
Tana mik'o mata ta bud'e ta mik'a mata kaza guda daya da lemu kwalba daya tace, yau mun sami duniya, bazamu koma bara ba sai kud'in sun kusa karewa".

JikinĀ  Aisha har rawa yake ta fara ci kamar wacce aka aikota.

Maman Aisha sai fara'a take, tana cewa "arzikinki mukeci aisha, gobe ma wannan Alhjin zaizo ya d'aukeki".
Aisha ta mayar da naman cikin leda kana ta had'e rai.
"Mama, haka kawai, bakisan mutum ba, baki taba ganinsa ba, amma zaki bashi ni, ko dama ba ked'in kika haifeni ba, kamar inda mutane suke fad'a?".
"Aisha ki kiyayeni, wallahi inhar makamanciyar wannan maganar, ta sake fitowa daga bakinki saina sa6a miki".
Maman Aisha ta fad'a,
Kamar wacce ta tuno wani abu, ta janyota jikinta ta rungume, kamar baby, tare da cewa "yafasa tafiya dake, kwantar da hankalinki"
Murmishi Aishan tayi, Wanda ya baiyyanar da lo6awar point d'inta, dake kumatu.

Ranar dai sun wuni cikin tsananin farinciki.

Alhaji Khalil.
Kwance yake akan royel bed d'insa, idanunsa a lumshe kamar mai bacci.

Salma ce ta shigo hannunta rik'e da littafi, cikin shagwa6a tace "yah Khalil assignment zakayimin nakasa"
Bai d'ago ya kalleta ba balle tasa ran amsawarsa,
A karo na biyu ta sake magana.
"Yah Khalil please"
Cikin tsawa yace "get out of my room"
Jikinta har 6ari yake, ta fice da sauri, saboda sauyawar yanayinta ba k'aramin firgita ta yayi ba.
Tana fita, yayiwa k'ofar tasa key, ya dawo ya zauna a parlo tare da jingina da bayan kujera, kansa a sama.
Hoton Aisha keyi masa yawo a fuskarsa, koya yaso cire tunaninta da kamanninta sai abin yayi masa tsauri.

"Wannan yarinya wace iri ce? A kalla nasan dai bazata wuce 12yrs ba, gashi tunaninta yana neman hargitsamin brain"
Duk a cikin zuciyarsa yake wannan maganar,
A fili yace "to idan mahaifiyarta ta bani ita, ina zan kaita?"
Nocking din da akayi ne ya katse masa tunaninsa, ya tashi jiki babu k'wari ya bud'e k'ofar.
Momynsu ya gani a tsaye, tana rik'e da hannun auta Salma,
"Wato bazaka dena wulakancinka ba ko? dan tazo ka tayata rubutu shine zaka koreta ko?"
Khalil ya waro ido, kafin yace "momy banajin dadi ne, please tunda ba gobe bane zuwa makarantar zanyi mata insha Allah".
Momyn bata kuma cewa komai ba ta juya rik'e da hannun Salma.
Suna tafiya, ya kuma danna key, yana tunanin to wai meyasa ma yakeson d'auko ita Aishar.
Da wannan tunanin bacci yayi awon gaba dashi, sai da akayi Azhar sanan ya farka a makare yayi sallah a gida, yana mai rashin jin dad'in makarar da yayi.
Yana idarwa ya ninke sallaya yaje drowarsa ya sauya kaya, zuwa riga da wando na jeans,
Bai shiga part d'in momynsa ba, ya fice daga gidan.

Alhji Kabir House
A wancan lokacin, Nafisa da Sajida suna zaune a gida d'aya ne, yanzu kam ya raba musu gida,
Nafisa tayi wata irin k'iba, wacce daka ganta zakasan duniya ta zauna,
Sajida tana nan da d'anta Namiji Wanda a halin yanzu shekararsa 11yrs a duniya, idan ka gansa sai ka rantse d'an shekaru, 15 ne, a makarantar boko yana primary 5, a islamiya yana izu ashirin, yanada k'wazo Allah yayi masa basirar duk abinda aka gaya masa sau d'aya zai rik'e,
Tun daga lokacin, Sajida bata sake aihuwa ba,
A fannin Nafisa kuwa, tana juya Alhji Kabir kamar waina, tunda ya riga da yazo tafin hannunta, ta zamo itace uwarsa itace ubansa, game da ko meye daya shafi harkar kasuwancinsa da Kuma gidansa.
Ita tasa a raba musu gida, har Hajiya mama, itama gidanta daban, babu inda batayi ba, akan karya raba gidan, indai har yayi gini dominsu ne, to yabar gidan kowa a hannunsa da sunan na matan da nata, Nafisa ta sameshi tace "bata yarda ba, gara kowa ya koma gidansa, inyaso sai ya nemawa Hajiya mama yar aiki".
Hajiya mama, tana takaicin bijire mata, da Alhji Kabir yakeyi, tayi iya yinta ta zubawa sarautar Allah ido.

Maman Aisha.
Washe gari, jikin maman Aisha yayi sanyi, tun bayan sallahar asbha da tayi bata koma bacci ba, tagama juyi a cikin d'akin, sai yau ne take tunanin anya mutumin ma ba d'an Shan jini bane? to idan ya d'auki Aishar ina ze kaita?, jikinta ya gama sanyi, ta fito tsakar gida ta had'a wuta, ta dora musu abinci.
K'arfe 8:30am ta kammala, lokacin Aisha ta fito hannunta rik'e da kwanon bara "ke yau babu inda zamuje"
"Mama ba kince wannan Alhjin yazo ya d'aukeni ba?"
"To na fasa"
Maman Aisha ta fad'a a tak'aice.

Suna zaune suna cin shinkafar data auno a makota dazu, ta dafa musu akayi sallama.
"Waye da safiyarnan"
Aisha ta mik'e tana cewa "waye?"
"Ku tattara yanaku-ya naku kubar min gida, naji labarin ancemin kina zuwa bara, amma kud'in biyan haya ya gagareki, to wallahi na gaji, ai nayi k'ok'ari, dahar na bari kuka cinye wata biyu a gidannan".
Wata mata wacce a k'alla zatayi 57yrs, ta fad'a cike da tsananin masifa.
Maman Aisha ta ajiye cokalin hannunta, kana ta mik'e tsaye tace "insha Allah yau zan biya, tunda dubu goma sha biyar ne"
Wani matsiyacin kallo matar ta bita dashi, kana tace "nifa bawai zamanku nakeso ba, kawai ku tashi kubani gidana za'a kawo amarya k'arshen watannan"
Aisha ma ta mik'e cikin tausayawa rayuwar tasu tace "Baaaba dan Allah kiyi hakuri zamu biya karki tashemu"
Matar tayi fatali da butar dake gabanta tace "ni Wasila nace kutashi ku bani gida tunda ba gadon ubanki bane"
Suna cikin magana, saiga sallamar Baaaba Indo, maman Aisha ta share hawayen da suka sami damar zubowa a kumatunta tace "wa'alaikumussalamu"
Baban Indo ta kalli Wasila mai gida tace "yadai Hajiya har kud'in nasu ya kare ne?"
"Kee tsohuwa babu ruwanki a cikin wannan maganar dan haka, ki kiyayeni kinji"
Baaba Indo tayi shiru, kafin ta kalli maman Aisha tace "Alhjin nanne nace masa ya shigo"
Maman Aisha ta gyara d'aurin d'ankwalinta tana fad'ad'a murmishi.

"Aslamu alaikum"
Sallamar Khalil ta doki dodon kunnen Aisha, tsalle tayi taje da gudu, kamar tun dacan sunsan juna ta rungumeshi tana cewa "oyoyo Alhji, dama gara da Allah ya kawoka"
Yad'an rage tsayi, kafin yace "menene big girl?"
Cikin shagwaba irin ta Aisha tace "kaga wannan matar, tana zagin mama"
Cikin masifa Wasila tace "nifa ba zama nazoyi ba, ki bani kud'in haya kuma ku tattara ku barmin gida".
Khalil ya k'arewa Wasila kallo, irin gogaggun y'an duniyar nanne da babu d'igon mutunci a tare dasu, da muryarsa mai sanyi yayi magana.
"Nawane kud'in da ake binta"
"Dubu Sha biyar, kuma ta tashi ta bani gidana, nasan ko zuwa gaba bazata iya biyana ba.

Khalil yace "kinada account number?"
"Eh akwai"
Wasila ta fad'a tana jefa cingam a bakinta.

Zanyi miki transfer zuwa anjima.

Ta fice ba tare da ta wai wayesu ba,
Baaba Indo, ta kalli Khalil cikin fara'a kana tace "Alhji mun gode ubangiji ya saka da alkairi"
Maman Aisha kam Banda kuka babu abinda takeyi, Aisha taje kusa da ita tana share mata hawaye cikin tausayawa.

Kamar wacce ta tuno wani abu, maman Aisha ta mik'e ta fiddo da tabarma kana tace "zauna"
Khalil ya zauna, fuskarsa nakan Aisha, bayan sun gaisa yace "yazo tafiya da Aisha"

Baaba Indo, tace "to in ban katseka ba, ina zaka kaita...

*šŸ«¦ TSAUTSAYIN TAUNAšŸ«¦*

*Zainab Habib (Mom Islam*
Arewabook Momislam22



17-18

Sai da shiru ya biyo baya, nad'an wani lokaci, kana yace "idan bazaku bani ita ba, kuyimin alfarmar in dinga zuwa ganinta".

Jikin Aisha na rawa, ta dawo gurin Khalil,
"Zan bika in dinga cin kayan dad'i"
Murmishi yayi, wanda yake k'arawa yalwatacciyar fuskarsa kyau da izza,
"Am zan turawa da wannan matar kud'in gidanta, insha Allah a k'arshen watannan zaku koma gidana dake anguwar Katsina road, 3 bedroom flat ne"

Maman Aisha ta zaro ido, cikin raunatacciyar murya, mai kamada ta tsorata, tace "bawan Allah, baka sanmu ba, Amma kake yi mana wannan abin arzik'in?".
Khalil yasake yin murmishi.
Kafin yace "mama ai yiwa Kaine, idan ka taimaki wani sai Allah ya taimakeki, ba a kanku na fara taimako ba, dan haka wannan ba komai bane".
Baban Baaaba Indo dake tsaye ta jingina da bango ta dinga kwararo masa adu'oi had'i dayi masa fatan alkairi, 10k ya k'irga ya mik'a mata, ta kuma yi masa godiya, ta fice tana farinciki.
Khalil ya kalli mama da fuskarta ta jike da hawaye,
"Mama ina baba? meyasa kike zuwa bara?"
Banajin dad'in ganinku a wannan halin, da za'a tattara kaf mabaratan garinnan ayi musu muhalli, idan wani ya zauna wani bazai zauna ba.

Mama ta gyad'a kai tana kallonsa.
"Meyasa kace wani zai zauna wani bazai zauna ba?"
Khalil yayi ajiyar zuciya, kana yace "sau da yawa nakan ware kud'i duk k'arshen wata, domin a rabawa mabarata, amma sunki sauya hali".
Mama tayi shiru, batace k'ala ba, sai hataniyar Aisha data cika gidan, da rigimarta.
"Kansa a k'asa, tashi d'aya fuskarsa ta fara nuna yanayin damuwa, zuciyarsa da ilahirin gangar jikinsa najin nauyin furta kalmar dake yawo a cikin zuciyarsa, a hankali ya d'ago kansa ya kalli Aisha, a kafaice ya kalli mama kana yace "am..am mama dama".
"Yi maganarka Ibrahim, ina jinka"
Maman Aisha ta fad'a kai tsaye.
Lokaci d'aya ya samu k'warin guwaiwar da zai amayo abinda ke damunsa,
"Mama inason Aisha, so na tsakani da Allah, so Wanda babu cuta a cikinsa".
Da saurin kirjin mama ya fara bugawa da K'arfi, sai da tasa hannu ta tare gurin kafin ta iya tattaro kalmomi kamar haka..
"Ibrahim, bazan ce maka eh ba, bazan ce maka a'a ba, hasalima nidai bani da kowa, bugu da k'ari, Aisha guda nawa take?, shekararta 12 fa"
Cikin nutsuwarsa da tazamo masa jiki wacce Allah ya hallicceshi da ita, tun yana yaro yace..
"Mama nasani Aisha karama ce, koda kikace baki da kowa Amma ai a garinku kinada dangi"
Dogon numfashi taja, kafin ta saukeshi cikin tashin hankali,
"Eh bebeji, shine garinmu, mahaifiyata mahaifina dangina kai kowa nawa yana can, nida mijina ne anan, koda mahaifin Aisha ya rasu k'anwata ce tazo, itama din kwananta d'aya ta tafi".
Sunkuyar da kai Khalil yayi kafin yace "to mama amman dai lafiya ko?"
Maman Aisha ta katse masa zancen ta hanyar cewa "eh lafiya, yanzu dai maganar aure da Aisha kayi hak'uri, saboda wani dalili nawa, a tak'aice ma Aisha yarinya ce, kamar inda na gaya maka a baya".
"Mama ki kwantar da hankalinki, tuno a gaban surukarsa yake 6arin zance yasa shi yin shiru, wata sihirtacciyar kunya ta lullu6eshi.
Ya mik'e a hankali tare da cewa "nizan wuce"
Mama tace "gashi ko ruwa baka shaba"
Khalil yayi murmishi,
Aisha ta rik'e masa hannu, wani yarr yaji a jikinsa Wanda ya haifar masa da wani irin yanayi, Wanda shi kansa da za'a tambayesa bai sani ba, dan koda za'a titsiyeshi to an bashi babban aiki.
Da sauri ya janyeta a jikinsa yayi taku daya zuwa biyu, mama tace "mungode da taimakonka a garemu, ubangiji ya saka maka da mafificin alkairi"
Khalil yace "Amin" kana ya fice.
Yana fita mama ta kirawo Aisha, bayan tazo mama ta zaunar da ita, suka dawo kan tabarmar.
"Aisha kinsan so?"
"Eh mana mama, nasani soyayya"
Maman Aisha tasa dariya, tare da kamo hannunta, tace "bazanso cutar dake gurin za6a miki miji ba, saboda a halin yanzu bakisan zafin jikinki ba, ko ciwon wani abun, kar inzo inyi aikin dana sani, kuma ma abin tunani anan shine, inhar na yarda dangina bazasu tsinanamin komai ba, tunda sun tsaneni".
Mama na fadar haka ta share hawaye,
"Mama kidena kuka, amman dai mun dena zuwa bara ko?"
Mama ta zaro ido kana tace "Aisha zuwa bara ai ya zame mana dole, idan bamu jeba babu mai d'aukowa ya bamu, kinga kuwa kodan mu tsira da mutuncinmu maje Amma mu sauya gurin zama".
Aisha ta kar6e zancen da cewa "mama idan Alhjin ya ganmu fa? kuma ai ya baki kud'i"
Zagi ta k'unduma mata, tare da cewa "tashi kije ki sauya kaya, da naso dena zuwa bara, tunowa da nayi Baaaba Indo tacemin k'awarta tasi mota shine naji jikina yana kyarma, kinga muma ya kamata ace mun tsira da wani abun".
Tana gama fad'ar haka tace "mik'omin hijabi na, kema ki d'auko naki mu wuce, ba gurin da Ibrahim zai ganmu zamuje ba".
Kai tsaye suka fito bayan sun gama shirin, da isarsu bakin titi, suka hau napep, mai napep yace "mama ina zamuje?"
Maman Aisha tace "kaimu inda mabarata suke zama"
Mai napep yace "Kano road kenan?"
"A'a inda akwai wani gurin ka kaimu"
Mama ta fad'a tana tararrabin kar suyi ido hud'u da Khalil.

Ba Kano road d'in kuwa ya kaisu ba, wani waje daban ya kaisu, sosai ake samun kud'i a gurin dan yafi wancan gurin.

Kwanci tashi har maman Aisha da Aisha sun saba da mutanen gurin, idan aka mik'o kud'i, maman Aisha ce mai rabo, komi yawansa haka kuma komi k'ank'antarsa, nata yakanfi na kowa yawa.
Tunda ta sami wannan muk'amin, ta dage da bara kullum, safiya suna hanya, gashi ba wani abincin kirki sukeci ba, sometimes ma har yunwar taci ta cinye basuci komai ma, koda sunzo ci zasuji sun k'oshi, Aisha ta rame sosai, kasancewar a halin yanzu babu isashen abinci bare azo fannin wanka ko kitso, kitson kanta yakai wata biyar, rabonta da wanka kuwa idan ance takai sati uku baza'a musa ba, tunda neman kud'in sukasa a gaba.
Bayan komawar Khalil gida, ya zarce d'akin momynsu, bayan yayi sallama ya k'arasa bedroom d'inta dan bai sameta a parlo ba, tura door d'in bedroom d'in yayi, tare da cewa "momy ina kika shiga?".
Turuss yayi ganinsu sunata bud'e k'ullin magani, duk da maganar da yayi Sam daga momyn har Salma babu wanda ya jishi,
"Banaso kiyi aure yanzu, samoda ginin gidan saman da ake yi miki ba'a kammala ba, nafison ki sake farauto mana kud'i a gurin Alhajinki, kinga ana gama ginin sai asa haya kinga munci riba, kici gaba da shafa wannan turaren kamar inda Saratu mai mallaka ta gaya miki"
Juyawar da momy tayi taga Khalil a tsaye, idonsa yayi ja, cikin duburburcewa tace "za...zau...na..na.mana, Khalil, hhh am tahau sosai kai "ashe ka shigo ban sani ba"
Wata kujera yaja, ta katako mai kyau marar nauyi, ya zauna kusa da momyn, Salma ko tuni ta sunkuyar da kai k'asa.
"Haba momy, yarinya takai shekara 27 amma ko tunanin aurar da ita bakyayi? kin zuba mata ido tanata abinda taga dama, wannan ba tarbiya bace momy, kuma gurin wannan bokan da kike zuwa, momy karki mance Allah ya haramta fa".
A hassale Momyn tace "kai ka kiyayeni!! yaushe ka fara wa'azi? da yaushe ka zamo malami bani da labari?"
Ransa na tafasa ya mik'e tare da zuba hannayensa a cikin aljihu, ya fice ransa na k'una.
'Kai tsaye ya wuce d'akinsa, ya zube akan kujera yana mai-maita la haula wala k'uwawata illah billah, innalilahi wa inna ilaihir raji'un, meyasa har yanzu momy bata fahimci abinda takeyi cutarwa bane? meyasa momy bazata Dena wannan sana'ar data d'aukarwa kanta ba?".
Yana gamaĀ  maganar ya bud'e fridge ya d'uki ruwan sanyi ya tsiyaya a kansa har sai da ya k'are, ya cillar da gorar, komawa kan doguwar kujera yayi ya zauna, abubuwan da momy take koyawa Salma suka dinga dawo masa, yama mance da wata Aisha ta kutso cikin rayuwarsa.

Yau rabonsa da zuwa gidansu Aisha sati d'aya kenan, maman Aisha tayi mamakin mamakin tarin kud'in data samu, kama daga ragowar wanda Khalil ya basu har da Wanda ta samu a gurin bara, wasa'wasa ta tara kud'i sunkai 100k da aka lissafa, ta kaisu ajiya a burinta tana neman dubu d'ari bakwai zata siyi mota kota hannu ce babba.
Khalil yazo gidan har sau biyu baya samunsu, gashi baya da number wayar mama, to baima san ko tanada wayar ba.

Wata ranar alhamis, ranar da ta zamewa Aisha ranar bak'in ciki ranar da ta zame mata ranar 6acin rai, Wanda har abada bazata ta6a mancewa ba.
Suna cikin tafiya ita da mamanta, bayan sun sauka a, adai-daita

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment