Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wannan Al'qur'anin da ke hannunka baka tab'a kusantar Fadila ba , sannan ba kai bane mahaifin Ahmad da cikin jikinta , idan kuma kai ne ka b'oye Allah ya sa wannan Al'qur'anin ya cika , Allah ya hanaka abun da kake nema duniya da lahira , Allah ya nisanta ka da duk rahamominsa " Haka MD ya nanata kamar yadda mai karanto mai ya karanto , inda MD ya idasa maganar jikinshi ko ina yana rawa ga zufa da ke keto mai kota ina, wadda hakan ya ba kowa mamaki .


MD na kai rantsuwar Alk'alin ya kalli Fadila wadda ke kuka ya ce " Fadila , babu zargi yanzu kan MD saboda ya yi rantsuwa da Al'qur'ani mai girma , dan haka ya wanke kanshi daga zargi "

Alk'alin na fad'in haka ya tashi .



Fadila kuka take sosai , inda Aisha ma kukan take , sannan ita ta lafa da nata ta kamo hanun Fadila ta ce " Ki tashi mu tafi " Fadila tashi ta yi , sun zo k'ofar da za su fita ne su ka ci karo da MD , MD kallan Fadila ya yi ranshi b'ace ya ce " Fadila , da ace kin ji maganata biki kawoni nan ba da na rufamiki asiri , amma yanzu ki sani natsame hannuna akan duk abin da ya shafeki dake da Ahmad har da ma wanda zaki haifa " Fadila kai ta d'aga tana kallan MD sannan ta ce " Ka ji tsoran Allah MD , ka amshi cikin jikina ko ba zaka amshi Ahmad ba , ni nasan cikin jikina naka ne koda ko zaka had'iyi Al'qur'ani ne , saidai da ya ke ka kasance cikin marasa tsoran Allah masu rantsuwa akan k'arya ka ji tsoran Allah" MD kallan Fadila ya yi cikin tausasa zancesa dan sai kuma ya ji tausayinta ya ce " Fadila , bani da jib'i akan cikin jikinki shi ne gaskiyar lamari , na so in ci gaba da taimakonki saidai gudin zargin zama'a akaina ba zan iya ba , ina miki fatan alkairi sai watarana duk da nasan akwai ranar da zaki sake naimana " MD na fad'in haka ya yi tafiyarshi da sauri "


Aisha hannun Fadila ta ja suka tafi .


Mahaifiyar Fadila a gida ko ta k'osa su Fadila su dawo ta ji yadda suka k'arke . Tana nan zaune su Fadila suka shigo . Mahaifiyarsu Fadila tashi ta yi da sauri tana kallan Aisha ta ce " Aisha , ku tsaya daga nan kusanar dani yadda ake ciki ? " Aisha cikin kuka ta zayyana ma mahaifiyarsu duk yadda aka yi.


Mahaifiyar Fadila kallan Fadila ta yi ta ce " Fadila , zan miki wata alfarma guda d'aya, zan ci gaba da zama dake badan ina so ba dan kin fira raina , amma ba zan zauna dake da Ahmad ba da kuma cikin jikinki ki je duk inda zaki idan kika haihu sai ki dawo amma da su ba ki naimi ubansu ki ba shi su , ba zan zauna da yaran shegu har biyu ba, ki fita kije ki naimi ubansu dan wallahi ba zaki kwana gidan nan ba yau "


Aisha cikin marairaicewa ta ce " Mama , dan Allah ki yi hak'uri idan kika koresu ina za su ? " Mahaifiyarsu Aisha cikin d'aga murya ta ce "Aisha , Wallahi in duniya zata taru akaina ba zan zauna ina kallan Fadila da shegeba tana raino ga kuma wani aciki yana shirin zuwa duniya , amma ta je duk inda zata ta haihu , k'ila in ta haihu ta dawo min ba da su ba in yafe mata "


Aisha zata k'ara magana mahaifiyar Fadila ta ce " Wallahi , indai Fadila bata bar gidan nan ba na bar ganinta zan mata baki "


Fadila sanin halin mahaifiyarta da ta yi na indai ta yi zuciya babu mai iya lankwasata ya sa ta shiga d'akinsu ta d'akko wasu daga cikin kayanta da na Ahmad , tana rungume da Ahmad ta je wajan mahaifiyarta tana kuka ta ce " Mama , zan tafi in sha Allah kuma ba zan dawo da Ahmad da abin da ke cikina ba , amma dan Allah mamana ki bar fushi dani ki samin albarka ko zan samu sukunun zuciya dan Allah kar ki yi fushi dani "


Allah sarki mahaifiyar Fadila ma kuka take cikin kunan ne ta ce " Fadila , ki tabi zuciyata ta kasa jure ganin Ahmad da abin da ke cikinki dan Allah ki tafi bana son ganinku baki d'aya ! "


Fadila tana kuka ta juya ta fita gidan har tana sake juyowa .


Fadila na fita Aisha ta durkushe awajan tana kuka sosai .


Fadila ko koda da ta fita rasa inda za tabi ma ta yi , hakan ya sa ta mik'e hanya tana tafiya tana kuka ga Ahmad rik'e ahannunta . Fadila sai da ta yi tafiya sosai tabar unguwarsu baki d'aya sannan ta samu wani waje ta zauna tana tunanin inda zata . Tunanin Kiran Jamilu ta yi sai kuma taga shi ma yanzu d'auke mata kai yake hakan ya sa ta fasa .


Fadila na nan zaune , Muhammad Sagir mai shadda ya fad'o mata arai , charting d'insu ta tino da yake ce mata zata bar mai Ahmad ,ta ce shi da bai da mata wa zai rik'e mai , ya ce ga mommynshi nan .


Fadila shiru ta yi tana tunani ta ce " Tom kodai da gaske yake , kai koma bada gaske yake ba yana da kirkin da zai iya taimakamin "


Fadila da keneman ceto da kuma tunanin kamar zaitaimaka mata ya sa ta Kira number shi .


Sai dai ta Kira bai d'aga ba, sai da ta yi mai kira uku amma bai d'auka ba .


Fadila ganin bai tauka ba ta fara tunanin ko gidan marayu zata ta kai Ahmad ita ma ta zauna in ta haifu ta bar abin da ta haifa acan ta dawo gida , in da mahaifiyarta ta ce zata amsheta in dai babu su Ahmad .


Fadila tashi ta yi ta samu Napep ta ce ya kaita gidan maru dan Allah da ke nan kusa .


Fadila koda suka isa gidan marun ce mata akai sai ta zo da wani nata sannan a amshi Ahmad .



Fadila bacin ta biya mai Keke - Napep d'in , tafiya ta fara yi ak'asa batare da ta san inda zata ba. Fadila jin ta gaji ta fara ganin jiri ga Ahmad har ya fara kuka , hakan ya sa ta samu waje ta zauna , ta na zama ta sake tunanin k'ara kiran Muhammad , nan ma sai da ta yi kira uku amma bai d'aga ba .



Wani tunani ne ya zo ma Fadila a zuciyarta ta ce " Tabbas , Muhammad Sagir ya na da kirki kuma ina ji ajikina zaitaimakamin dan haka Adamawa zani kafin in isa zanta kiran numbersa har Allah ya taimakeni ya d'aga "


Fadila na gama wannan tunanin ta tashi ta hau Napep ta nufi tasha , tana zuwa ko ta samu motar Adamawa ta cika saura mutum d'aya ta hau suka tafi ✍🏻



FADEELAH free page ya k'are ga mai muk'ata # 300 kacal 👌🏻


Kud'in littafin FADEELAH d'ari uku ne dan Allah idan ba siya zaki ba karmu b'ata ma juna lokaci 🙏🏻



My Number 08063830828

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment