Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son Ahmad bata son Abinda zainisantasu saigashi yau Aure zairabasu tayi shiru tsawon lokaci sannan tadaga kai ta kalleshi yana tsugunne kan kafafuwansa Kansa yana kasa Tunda nake dakai banta ganin wani abu na ashsha kona kaico agarekaba nasan Raliya zata iyayin komai domin ta tunziraka ta kuma hasalaka banason jin komai daga gareka sai alkhairi kada kayadda wani abu nabacin rai yafito daga wurinka kayi komai domin kafarantawa" babanka rai kiyayyar mace takaitacciya ce wata rana zata daina ranar daza awayi gari kunfara tara zuria shikenan komai yazama tarihi Allah yayimaka Albarka idanuwansa suka dinga zubdaí ½í¸­ inama yanda yake da iyaye nagari sukai masa fada yaji Raliya ma tanada su da Aurensu yazauna lfy daga can saman kansa yaji umma nafadin tashi kaje kada dare yayi Allah yayi maka Albarka yamike sumu sumi yana fadin Amin yawuce shikenan kyau zai bar gidansu zai bar cin abinci Ummansa ya isa kofar gidan nashi da babur dinsa yasauka yatura kofar ga mamakinsa sai yaga kofar abude take donhaka yatura babur dinsa yashiga tundaga tsakar gida yafara jiyo kugin radio ankure wakokin turawan zamani mamaki yacika shi domin dai daga dakin dake kulle wakokin suke fitowa yasan wannan dakin baccin Raliya ne yakada kai yanufi dakinda aka jera kujeru aciki domin yasan dakin da raliya take bazaisamu damar kwana acikiba ko bata rufo kofarba balle dakin abame yake ma har ya kwanta akan kujera yaga dacewar yakoma shagon gidansa kawai da kayansa ya zauna nanne dakinsa da asuba yatashi ya nufi masallaci tayi sallah yadawo yafara lazimi kamar yanda yasaba daman baisanya ran raliya zata tashi tayi sallah ba domin yasan batada wannan tarbiyar sai wajen 10 nasafe take tashi ai kuwa yau dinma hakane saida rana tatake sannan tatashi lokacin tuni yadade da karyawa domin flask yadauka yaje yasiyo musu shayi dayasha yabar mata nata aflask duk da yanacan daki yana hangota ta windo yaga tafito amman abinda yabashi mamaki har karfe goma raliya bata fitoba kuma gidan ba irin na yangun nan bane mai bandaki aciki balle yace tayi Alwala aciki can saiyajiyo sautin radio ansa kidan jiya naturawan zamani yaso yashareta amman sai yatuna yanzu hakkin raliya da tarbiyar ta duk suna kanshi dole yatunatar da ita gaskiya don haka yamike yanufi dakin nata yatura kofa dasallama tadaga kai cike da tsananin mamaki tana dubansa shikam yanayin daya taddata ne yasanyashi tsananin firgita da rudewa domin wata yar figigiyar rigar bacci ce ajikinta dukkan surarta tana waje jikinnan nata yayi jajur tasha man kanti gashi tana kan kurciyarta saiwani sheki da sulbi fatarta keyi 9⣠DAME AKE ADO Wani abu yadinga jin yanaimasa yawo cikin kanshi saboda baitaba baitaba ganin wata mace cikin irin wannan yanayiba yayi masa wani kallon banza sama dakasa tana yatsina fuska tace inazaton kayi batan kaine ko malam yanayin yanda tayimasa maganar yayi gaggawar dawo dashi cikin haiyacinsa yayi kokarin tattaro jarumtakarsa da nutsuwarsa yasanya akan fuskarsa duk da zuciyarsa tayi kokarin bijirema hakan sannan yayi kokarin zakulo abinda yakawoshi inatasau raren ganin kinfito kinyi sallah asuba saikuna naji kin kunna radio ma alamar bakida niyyar gaida ubangijinki Tayi dariya tayi shewa tayi masa irin kallon da akeyiwa yantasha Au ashe fa Ustazu aka kakaba mini ko? Wai kayi zaton zuwa nayi zama agidanka dan Allah dubeni kadubi fatata aikasan banyi kalar dazan iya zama acikin wannan gidan kirar talakawaba talauci yahaifeni nakuma yadda nazauna natayu acikinsa amman bazan yadda na dauwama har nakare rayuwata acikin saba batun sallah kuwa kada ka matsamini domin ba kabarinmu dayaba bakuma bazo zama bane jira nake kashigo kabani red card dina Ransa yabaci ainun banda kaddara me ye hadinsa da Raliya komai jahila bata iya komaiba sai wauta amman ace itace matarsa takuma zage tana zaginsa haka yayi kamar yakara magana saiyaga rashin dacewar hakan danhaka yajuya da zummar ficewa saiya jiyota daga bayansa tana fadin malam fitafa bata kama kaba gwara kasallameni tunban yagama rigar mutuncinkaba baikulataba yafice domin tunaninta irin na dabbobine idan yaci gaba dajinta komai na iya faruwa kawai sai yafice daga gidan yaukam abin yafi najiya domin tundaga kofar gida akejin sautin kida yashiga da sallama badon yasan zatajiba sai domin mutanen boye abin mamaki saiya hango takalmi barkatai na mata dakuma hayaniyarsu anata shewa ga tukwane da kwanuka Nan anyi girki anbata gidan yayi faca faca harda garar abban

See translation
18 April 2015 at 11:18 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like50
Write a comment...

·
Yahuxa Kabir
hmm raliya abi duniya a sannu
Like · React · Reply · More · 18 Apr 2015
Babangida Lawan Miko
Da kyau
Like · React · Reply · More · 18 Apr 2015
Hassan S Saddiq
ttnx
Like · React · Reply · More · 18 Apr 2015
Shafiu Shanabash
DAME AKE ADO...?
Like · React · Reply · More · 18 Apr 2015
Maman Ihsan
mungode
Like · React · Reply · More · 18 Apr 2015
Rukayya Abba
nice
Like · React · Reply · More · 18 Apr 2015
Kabiru D Shagari
Tnks.
Like · React · Reply · More · 18 Apr 2015
Jameeylarh Dalhart
sannu da kokari
Like · React · Reply · More · 18 Apr 2015
Muazz Alawo
Weldone
Like · React · Reply · More · 18 Apr 2015
Abubakar Ibrahim
Pls my friend be patient, everything will be normal soon
Like · React · Reply · More · 18 Apr 2015
View more comments… Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO part 7.
duniya tayi mata yanda takeso kenan tsawon sati guda kenan anazaman yan marina agidan babu wani da Raliya dakeyi na zaman Aure hatta shara shiyakeyinta wanke wanke kawai take yi shima dan ita take bata kwanikan da kawayenta dake wuni kullum agidan dayafita aiki sukuma zasu dira basu barin gidan sai dare zuwan Lami nafarko kuma nakarshe shiyakara dagula komai suna daki ita da diyarta sunata kulle kullensu ya iso gidan agajiye yake tubus domin yau bai tsaya hutawa ba kamar yanda yasaba yana rashi daga aiki yayo gida kawai kai tsaye yashigo da babur dinsa gidan Dai dai lokacin da yaji Lami tafito daga dakin Raliya nabiye da ita furucinta nakarshe ne ya doki dodon kunnensa 1⃣2⃣ DAME AKE ADO 2 Yayi tsai yana jiyo ta tana ta habaici da zage zage dukkan kalamanta bakomai bane illa tunin kalaman da mahaifiyarta kegaya masa sanda yana yaro har ya girma bashida abinyi bayan neman tsari daga shaidan dan kada yatunzurashi ya aikata abinda zaisanyashi dana sani agaba yana jin kiran sallah magriba yayi sauri yafice dan bada farali acan masallaci ya zauna yana lazimi har akayi sallar isha I yayi sannan yanufi wani gidan Abinci namasu karamin karfi yaci yakoshi ya jima agurin yana tunane tunane domin yarage dare fatanshi sanda zai isa gidan Raliya matar jaraba tayi bacci don haka sai wajen karfe shadaya yanufi gidansa ya tura kofar a hankali ya shiga yamaida kofar yarufe cikin gida yawuce yadauro Alwala domin dai yau daren jumua ne waton ranar Alhamis daren da Allah kanyi saurin amsar Addua bayinsa don haka yayi Alkawarin kaima Allah kukansa shima yau yazabamasa Abinda yafi Alkhairi yana sallah yajiyo bugun kofar raliya kamar zata balle masa kofar abinda yabashi mamaki biyu ne na farko kofar abude take amman taketa dukanta nabiyu kuma me yakawota dakinsa saidai yakula bazata barshi yayi sallah nan idan har baikulataba dan da karfi take bugun kofar tayi kokarin yin sallam yanufo kofar yadubeta sanda take kallon sa tadaina dukan kofar cikin tsananin mamaki yace lfy takalleshi araine tayi wani tsaki zuwa nayi Amsar sallamata domin nagaji dazama wannan akurkin naka nakula bakada zuciya domin kare yacinye dazai iya dayanzu zaiyiwa Raliya saki dubu sai dai bazai iya baiwa iyayensa kunya ba amman yau yakamata ya nunawa raliya shima fa baya kaunarta ko sau daya cikin kallon isgilanci yace waikina zaton ina zaune dakene dan kyawon fuskarki ko kyawon jikinki kiwata dabia maikyau dana gani agareki kiyi sani kamar yanda kika tsaneni kika kuma tsani aure na kodon inasonki a a kodaya nima haka nakeji harnawa ya linka naki tayi shewa da dariya tana kallonsa cikin tsakiyar idonsa da tsananin raini da wulakanci Ahayye wannan shi akecewa shege yi da maizina kaiko rayiwarka kayace nikam zan iya duk abinda naga dama nadawo natuba nakuma Auru sabanin kai da anriga anrubuto kai shege ne babu kankara shut up stupid yadakamata wata irin gigitacciyar tsawa data sanyaya firgita yaci gaba damagana cikin bacin rai koda nakasance shege wlh nafiki Albarka damutunci a idanuwan kowa dabba shashasha kiyita gorin naki dafadar abinda kikaga dama domin halinki irin na wawaye ne jahilai amman kisani idan har ga hannuna saki yake bazan taba sakinki ba sokuwa kawai yajuya dazummar komawa cikin shagon saidai riko wuyan rigarsa datayi tabaya ne yasanya yakasa cigaba datafiyar tarikeshi katamau tana fadin wlh ba indazaka saika sakeni meye kawai banda naci banason aurenka dolene wlh yawon karuwanci yafimin wannan kalgaggen auren naka zuciyarsa yadinga zillo datafasa afusace ya banbare hannuta cikin zafinrai ya hanbareta tayi taga taga tafadi warwas akasa tayi karo dabango tafasa wata kara domin hannunta yabugu da alama tayi targadema tafashe dakukan azaba ya kalleta dajan ido yana fadin sokuwa kinyadda duka guda zai iya maganinki kisani bawannan rayuwa ce agabanaba tadabbobi inada hankali da tunani idan har kinason rabuwa dani kije can kisami can wadanda suka daura kisanar dasu yamaida kofar yarufe raliya kam dakyar
tatshi daga faduwar datayi tanakuka sakale da hannuta saidai bakinta bai mutuba taci gaba datijara ta Allah ya isa shege tsinanne dan mahaukaciyar kan bola daba asan aslinsaba duk abinda yazo bakinta fadi takeyi afatanta nata tunzirashi yafadi kalmar saki agareta kamar yanda Lami tabata umurni tagayamasa kalaman dazasu tunzirashi amman baice uffanba saidai hawaye

See translation
20 April 2015 at 07:54 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like52
Write a comment...

·
Murtala Ibrahim
Dan halak kayi
Like · React · Reply · More · 13 Sep 2018
Mukhtar Moh'd Mopol
good
Like · React · Reply · More · 20 Apr 2015
Hussaina Umar
tnx
Like · React · Reply · More · 20 Apr 2015
Abdullahi Mai Nasara Abdullahi
Mdk
Like · React · Reply · More · 20 Apr 2015
Abdulrahaman Shuaibu
Tnx
Like · React · Reply · More · 20 Apr 2015
Azinatu Umar
MUNGODE
Like · React · Reply · More · 20 Apr 2015
Ahmad Sabo
Kwana 2 ko saceku akai ne?
Like · React · Reply · More · 20 Apr 2015
Khadijat Ahmad Mashi
Ammafa yayi hakuri sosai
Like · React · Reply · More · 20 Apr 2015
Ayshee Mohammed
5
Like · React · Reply · More · 20 Apr 2015
Isah Shaaibu
Anayi munajin dadi
Like · React · Reply · More · 4 May 2015
View more comments… Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO part 8.
baice uffanba saidai hawayeí ½í¸­í ½í¸­ dayake zubdawa yana tasbihi ga Allah afili dazuci harzuwa lokcin datagaji datijarar takama hanya tawuce dakinta tana kukan bakinciki kukan nata kashi biyu ne nafarko narashin cikar burinta nasakinta dayakiyi nabiyu kuma nabugewar datayi hartayi targade dayadaina jinmuryarta saiyamike yaci gaba da sallarsa yana kuka yana sanarda Allah halin dayake ciki
..........DAME AKE ADO 2 .................Saiwajen karfe 3 dawani abu nadare yaji gwiwoinsa sunyi sanyi idanuwansa sunyi nauyi babu abinda yake bukata illah yakwanta yahuta don haka yayi addua yakwanta bisa tabarmarsa cikin kankani lokaci kuwa bacci yadauke shi saboda rashin bacci daibaiyi da wuriba yasashi yamakara baitashi da asuba yayi sallah ba saida hasken rana yashigo dakin ta wundo ya haskemasa ido sannan yafarka afirgice ya duba agogon dake jikin wayarsa saiyaga yanuna karfe 7 nasafe yamike dasauri yana istigfari yanufi kofa yabude kaitsaye cikin gidan yanufa don daura Alwala abinda yabashi mamaki yau baiwuce rashin jiyo sautin kidan raliya ba wanda kullaum dashi take farkawa kamar shedaniya yashiga yakama ruwa yadawo yatsuguna gundi rariya yana daura Alwala yana satar kallon dakin nata yana adduar Allah yasanya harya gama Raliya batafitoba domin bayason ko kallon fuskarta cikin ikon Allah kuwa har yakammala din bata fitoba yanufi shagonsa yayi tusur cike datsananin tsoro domin ganin kofar gidan abude abinda yabashi tsoro kuwa tunda suke agidan raliya bata taba bude kofar gidaba yawaiga cikin gida saiyaga babu takalman Raliya akofar dakinta dasauri yadaga labule gamamakinsa saiyaga duk anwatsar da kaya acikin sif dakin yayi kaca kaca da alamar andibi wasu kayan gabansa ya kuma faduwa badai gudowa raliya tayiba dagacan kan gado yahango wata takarda ayashe ya isa dasauri yadauka yabude cikin wani cukurkudadden Rubutu yaga sakon nata yafara karantawa BAKA BUKATAR SALLAMA DOMIN BATA DACE DA SHEGE IRINKABA DUK WASU HANYOYI DA NASAN ZAN IYABI DON GANIN KASAUWAKEMIN WANNAN KALGAGGEN AUREN NAKA NABI AMMAN KAKI SAUWAKEMIN DON HAKA NABI HANYAR DATAFI DACEWA WATON NAGUDU NABARKA DA AURENKA IDAN KAGA DAMA YANZU KA IYA AIKAMA IYAYENA DATAKARDAR SAKINA DOMIN SANDA ZAKACI KARO DAWANNAN TAKARDA TUNI NAYIMAKA NISA KAIDA RAYUWARKA SAIKUMA ACIGABA DAZAMAN GAURANTAKA DONNASAN HARKA KOMA GA ALLAH BABU MACEN DAZATA YARDA TA AURI SHEGE BA .SAIWATA RANA RALIYA yaruntse idanuwansa sanda yakai karshen takardar sako mafi muni dazafi da idanuwansa suka tabacin karo dashi yajima tsaye yana tunanin meyadace yayi farincikin rabuwa da Raliya ko kuma bakin cikin gudunshi datayi
1â£5⣠DAME AKE ADO2 Mlm jibrilu ne yafara tambayar yaya akayi yaya Allah dai yasanya lfy domin naganku cikin damuwa malam sulaiman yamika masa takarda yana fadin karanra kagani malam jibril yakalli takarda batare da ya amsaba yace yaya aikasan ban iya karatun boko sosai ba danhaka bana gane kowane rubutu balle wannan danake ganinsa kamar zane tsutsotsi mlm sulaiman ya gyara tsayuwa yanuna masa takardar yace kaga wannan takardace da raliya ta rubuta kafin tatafi yawon karuwanci mlm jibrilu yadafe girji dadamuwa yaya wane irin yawon karuwanci kuma A iya sanina Raliya tana gidan mijinta naji dadi dakace a iya saninka alama bakasan gaibuba kenan to kabuda kunnuwanka dakyau kaji Raliya tabar gidan amadu yau da asuba bayan duk tayi wani cinmutunci dazagi baikulataba tabar wasika takuma ce dazaman auren Ahmadu gara taje tayi karuwanci yafiyemata kaga abunda nake nusar dakai tun abaya ko? Mlm jibril yayishiru cike da tsananin damuwa yamarasa mezaice dan idanuwansa sunkada suyi jajir gwanin bantausayi itakuwa Lami babu wata damuwa ko kyas atare da ita saiwani fici fici take da idanu irin namarasa gaskiya tana kara tsare gida mlm jibril yace yanzu to yaza ayi kenan kobin sahunta za ayine? Abita ina Raliya bayarinya bace tunda har taiya hada kayanta tagudu takuma furta kalmar tafiya karuwanci abin yakai intaha saidai Abinda tace Ayau zankaryatashi da tace sai dai Ahmadu yamutu babu Aure to tayi karya itace zata mutu babu Aure ba Ahmadu yaron kirki ba taje duniya fadine da ita wanda baizobama jiransa take yakada kai yashige dakinsa yana huci Umma kam saicika take tana batsewa tamkar tashako lami domin tariga tagane dasanya hannun lami takuta tace idan anguji dan wata illah abanza domin shi baida laifin kimai wanda kuma yake aikata irin laifin kumafa ? Karuwanci sana ace babba mai lasisi saidai tanada darussanta muna zuba ido muga karshen butulci darashin tarbiya lami takulu da kalaman umma tayamutsa fuska tana fadin oho kome za afada taba tarago tunda aibamu mukace raliya tatafiba duk kuma inda take Allah ne zaikareta Allah bazaikare Raliyaba lami yarinyar data tafi da hakkin mijinta da Aurenta kike zaton zatasamu kariyar Allah wlh ta barranta daga rahamar Allah bakuma zanyafemata wannan tozarci da cinmutunci dajamini ba Ahmadu dayake namiji yayi hakuri amman ita takasa taje duniyace mlm jibril yakarasa maganar tamkar zairushe dakuka domin yana ganin iyakacin tozarci raliya tayimasa Lami takuma cika afili tace Allah dai shike raba rahama ba mutumba mlm jibril yabita da kallo kamar yashakota amman saiya dake yakyaleta ya gyada kanshi yana kallon kofar dakin yayansa yace malam kafito mukarasa maganar nan kayi hakuri Ahmad dai yana durkushe yana kallonsu.
Abdullahi maitama.
09034598552
@whatsapp

See translation
21 April 2015 at 08:47 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like68
Write a comment...

·
Maryam Muhammad
Abashi ma'u kawai kowa ya huta tunda iyayen bazasui mishi goriba itama ma'un da wuya taimai gori
1 · Like · React · Reply · More · 21 Apr 2015
Maryam Muhammad replied · 2 replies
Aminu Ibrahim
thanks
Like · React · Reply · More · 21 Apr 2015
Isah Shaaibu
Anayi munajin dadi
Like · React · Reply · More · 4 May 2015
Marvin Jonnhy
Dakyau
Like · React · Reply · More · 21 Apr 2015
Abdull Muh'd
Thankx oga kahuta
Like · React · Reply · More · 21 Apr 2015
Isa Sileman
Thank
Like · React · Reply · More · 22 Apr 2015
زينب عبد القادر
Zai aure ta ai ba shiri gashi bata iya ko girki ba shi yake yi
Like · React · Reply · More · 23 Apr 2015
Aminu M Sirajo
Tnx
Like · React · Reply · More · 21 Apr 2015
حفصة أبو بكر
tnx
Like · React · Reply · More · 21 Apr 2015
Umar Bala Muhammad
THANKS
Like · React · Reply · More · 21 Apr 2015
View more comments…

Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO part 9.
1⃣6⃣ DAME AKE ADO 2 Daga masallaci makarantar su Asma u yanufa yadaukota daga can bakin kofa yaji wata sinio tana kwala mata kira Asma'u sulaiman tana ina tamike dasauri jikinta yana rawa tayi zaton wani laifi tayi kokuma dealing dinne yamotsa na sinio hajara domin shegiyar kazamace kayanta har tsami suke dahaka takwace kanta da maryam kemata kalbar da maryam keyimata tanufi wurin sinio hajara tana fadin tanafadin senio hajara gani senio hajara takalleta sama da kasa da alama yarinya uwarki ko ubanki sun mutu domin sir Abdul yace kije kitafi da dukkanin kayanki domin gidanku zaki wuce ma'u tadafe kai cike da fargaba sai tafashe da kuka tana fadin wayyo nashiga ukku Allah yasanya ba umma ko abba bane suka mutu ba wayyo Allah ni ma'u nazama marainiya ihu takeyi iyakacin karfinta gabadaya hostel akayi shuru anakallonta kawayenta tuni sun iso inda take dasauri suna tambayar abinda yafaru senio hajara takama masifa ke sakarya nibance miki wani naki yarasuba cewa nayi kawai inajin kihado kayanki muwuce kusai kutayata debo kayan nata ta kalli sauran kawayen nata dasauri ma'u tanufi gurin kayanta taci gaba da hadawa tana kuka sosai kawayenta suna bata hakuri da rarrashunta sanda suka isa wurin sir Abdul yakalleta damamaki yana fadin ma'u meyasanyaki kuka? Cikin sheshshekar kuka tace senio hajarace tace wai babana ko ummana sunmutu yabata rai matuka yace inji ubanwa? Hajara tanada matsala kawai nace kihado kayanki babanki zaitafi dake shike nan zatace haka barta kawai karya takeyi hankalin ma'u yadan kwanta saidai tana cike da tsananin mamakin abinda zaisanya babanta yazo daukarta bayan anfara jarabawa bukin yayanta kuma ankammala tuni domin alissafinta yau sati biyu kenan da bikin yayanta kokuma dagawa akayine dawanna tunanin tayi sallama dakawayenta sir Abdul yadaukar mata wasu kayan su maryam da jamila suna bata sakon abinda zatasawomusu idan zatadawo tana cewa to batasan wannan ce rana takarashe dazata kara komawa wannan makaranta ba dasunan karatu ba yaune dazata rabu dakawayenta rabuwa tahar abada kuwa ta isa ta tadda abbanta zaune a ofis din principal suna wasu magunguna dabata fahimci komaiba hankalinta yadan kwanta saboda ganin abbanta bakuma cikin wata da muwaba ta durkusa tagaisheda abbanta tagaida principal Abban nata yamike yana fadin to hajiya nagode Allah yataimaka yakuma kara daukaka principal tamike tana fadin Ameen amman munyi missing daliba maikwazo da hazaka Ubangiji yatsareta aduk inda take malam yace Amin dasauri principal tadaga kan ma'u tana fadin Allah kaddara saduwarmu kidage bisa kyawawan halin danasanki kinjiko? Itadai ma'u to kawai take cewa batasan me ake nufiba abbanta yadaukar mata wasu daga cikin kayanta tadauki sauran suka nufi titi sanda suka isa gida anata kiraye kirayen sallah magriba Umma tana kicin tana kokarin hura wuta da alama tayi daren tuwo ne tajiyo sallamarsu ta mike da mamaki tanafadin malam kamar muryan ma'u nakeji mamaki yakoma karuwa ma'u cedai biye da Abbanta yakalli Asma u yace bakama bace deeje itace yanzu na daukota daga makarantarsu mamaki yakoma cikata tace malam amman banji lbr anyi hutuba naji kamar jarabawa suke ma lfy yanufi kofar bandaki ya dauki wata buta da aka ajiye daruwa yana magana lfy kalau kidai kiramin dukkan yaran gidannan awaya kice inason ganinsu idan nadawo daga masallaci zakiji karin bayani yashige cikin bandaki don yakama ruwa Umma tamaida kallonta ga ma'u kamar zata koma tambayarta sai kuma tafasa tace shiga dakayan cikin daki kizo kidaura Alwala ma'u tayi abinda mahaifiyar tata ta umurceta bayan tacire uniform din dake jikinta tasake kaya tafito ta daura Alwala itakuma Umma kokarin fara kiran wayoyin yaran gidan ta isar da sakon da mahaifinsu tasanardasu sannan tadaura Alwala tashiga sallah
1⃣7⃣ DAME AKE ADO 2 Har suka kammala taruwa malam din baishigo ba domin saida ya tsaya yasiyo goro da alawa yataho dasu suna tsakar gida bisa babbar tabarma anata tattaunawa akan maganar gudun Raliya Rabiu yace wlh dani tahadu dashi datuni lbr yasha bamban shegiya kodaddiyar banza kawai taje indai duniya ce wanda baizobama jiransa take shidai Ahmad jinsu yake yana jin tamkar Anrabashi da wata babbar masifa ne arayuwarsa domin kallon raliya bayason yakoma yi yasan Allah ne ya.amshi adduar sa yayi gaggawar rabashi da ita saidai kamar yanda tace din yasan shida aure har abada domin bazai iya kara tunkarar wata mace da sunan yana sonta ba balle haryajawa kansa wulakanci ba zaici gaba dazama ahaka idan yaji zai takura sai yayi azumi Sallamar malam dince ta katse musu hirar su Ahmad yamike da sauri ya amso kayan da malam din yashigo dasu yana fadin sannu abba yakarasa yazauna akan tabarma da yaran ke kai daya bayan daya suka dinga gaisheshi ya .amsa sannan ya kalli Umma yace ina ma'un take kuma? Umma takalli kofa tana cikin daki kasan indai yayanta suna hira bata fitowa cikinsu tazauna wata kilama tayi bacci kotayi bacci atasota yakalli kofar dakin ma'u Asma'u kina inane tafito dasauri tana goge idonta inaciki Abba kadawo sannu dazuwa ya.amsa yauwa samu wuri zauna sannan yaturawa Umma buhun Alewa da goro dake gabansa yana fadin bude kigani deeje Umma taja buhun tafara budawa tadaga kai takalle shi da mamaki goro da alewane kowakilcin Aure zakayi kodaya goron daurin Asma'u da Ahmad ne an daura tundazu a masallacin jumu'a na gidan maimartaba mamaki yakama kowa har akarasa mai iya karfin halin.

See translation
23 April 2015 at 10:45 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like50
Write a comment...

·
Atika A Umar
NICE one
Like · React · Reply · More · 24 Apr 2018
Hureira Suleiman
Tnks
Like · React · Reply · More · 23 Apr 2015
Abubakar Ibrahim
Tnx
Like · React · Reply · More · 23 Apr 2015
Muazz Alawo
gud
Like · React · Reply · More · 23 Apr 2015
Musa Abdullahi
9ce
Like · React · Reply · More · 23 Apr 2015
Shafiu Shanabash
DAME AKE ADO...?
Like · React · Reply · More · 23 Apr 2015
Abashiyyah Umar
waww nyc wlh dame ake ado nake so......bcox akwai nishadi....
Like · React · Reply · More · 23 Apr 2015
Surayyah Abdallah
thanks
Like · React · Reply · More · 23 Apr 2015
Bala Sani Hafsat
Tnxxx
Like · React · Reply · More · 23 Apr 2015
Dauda Gimba
Tnx
Like · React · Reply · More · 23 Apr 2015
View more comments…

Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO part 10.
Umma ce tafara karfin halin yin magana tace malam kaji abinda kace kuwa ? Malam ya gyara zama kwarai da gaske saidai idan kece bakiji ba nasake maimaitamiki goron auren diyata Asma'u da Ahmad ne wanda aka daura dazu a masallacin gidan sarki Ahmad yaji wani abu dim akirjinsa tamkar ancaka masa mashi gabadaya kuzari da tunaninsa ya kwace yama rasa meyada ce yayi Auwalu yayi kokarin yin magana cikin yaran Allah yasanya Alkhari yakuma zaman lfy da zuri'a dayyaba gabadaya suka amsa da Ameen sani yace baba yabatun karatunta kuma wannan yana hannun mijinta dukkan hukunci da yazartar shine daidai daman karatun badole bane ba
1⃣8⃣ DAME AKE ADO 2 Umma ta girgiza kai tace hakane to yanzu yaya za ayi kenan malam Gyalenta zata dauka tayafa suwuce gidan mijinta wannan goron kuma da alawar kirabashi gidan makota domin suma sushaida Ahmad yakalli abbansa Afirgice daidai lokacin da Asmau takalleshi itama saitake ganin abin kamar amafarki anya kuwa dagaskene haka daman ake aure Umma takwantar da kai tace malam da anbari har ashirya ahankali sai akaita yadaga mata hannu babu wani shiri dazaayi kidauko mata hijab dinta suwuce da mijinta duk wanda kika aikawa da goron kice har tatare gidan mijinta fakat akayi shiru babu mai abincewa malam yadubi Ahmad wanda yakasa motsi tamkar anzare masa dukkan lakkar jikinsa yace tashi Ahmad kama matarka kuwuce gidanku Ahmad

Please Login or Register in order to submit comment