Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya daurewa tace wacece ma,un? Ya jingina da kujera yana murmushi tamkar ta masa albishir da gidan aljanna. Yace ma,u ita ce matata, mai sona mai darajani fiye da yanda yakamata ta mini, ban hadata da kowa cikin raina da al,amuran rayuwata ba. Cikin gaggawa da rashin sanin abinda ta fada tace Har ni ma? Shirun da yayi yana kallonta ne yasa ta gano ta fadi wani abun daya jima aranta tana nuku nuku dashi. Sai ta dauke kanta daga kallonsa da sauri ta kalli gefe gabanta na faduwa dakin yayi shiru sai karar A.C da ta bugawar zuciyoyinsu. Ahmad kam addu,a yake cikin ransa Allah ya sanya abinda ta fada bashi take nufin fada ba, amma sai ya jiyo sautin muryarta ya cigaba da fadin. Maza da dama sun soni masu kudi da masu mulki da sarauta, amman bantaba kallon kowa da mutunci ba tunda bansan meye so ba, sai kwatsam watarana naci karo da wani tsageran matashi a gidan mai wanda ya tsaya cikin raina har ya karya tarihin zuciyata, tun ina yaudarar kaina da zuciyata karya takeyi bazan taba son mutum irin haka ba har daga karshe na yarda na sallama ina sonka Ahmad. Ta waigo ta kalleshi yayi mutuwar zaune. Ta cigaba da magana idonta na zubda hawaye Nasan ka jima da gano ina sonka domin na gwada maka abubuwa da dama irin na masoya amman kana basarwa nasan badon komai bane sai don ma,unka! Sai dai ina fatan zanci albarkacin ma,un ka sammin kadan daga cikin son da kakeyi mata
Like· Report·Jun 14
Nusaybarh Mustapha Ibraheem
123. Tana kaiwa nan ta mike tsam da sauri ta nufi kofar fita Ahmad yana zaune kamar an dasashi ya kasa motsawa daga inda yake yana jin kamar bashi bane ba. Ya bi nana da kallo wacce ta kama kofa zata bude har saida ta bude sannan ta kuma yin magana ba tare data waigo ba. Ahmad ka sanya aranka ba karamin abu ne zai sanya mace kamata mai cika da daraja da kyau da arziki ta fuskanci namiji kamarka ta sanar dashi tana sonshi ba. Tana fadin hakan ta fice. Ahmad ya doki tebur ya dafe kansa dake juya masa yana fadin Ya subahanallah! Lallai lokacin barina cikin wannan

So naga kuna korafi dayawa, bari na wakilci@maitama nakarasa muku.

Surayya

10 October 2015 at 11:27 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like26
Write a comment...

·
Jamila Umar Tanko Books
thañk you sury
1 · Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Sarauta Ta
Tnx
Like · React · Reply · More · Yesterday at 23:21
Amina Abdullahi
Good
Like · React · Reply · More · 30 Nov 2018
Mubeenat Muhammad
Muna godiya
Like · React · Reply · More · 30 Nov 2018
Kamaluddeen Sulaiman
Agaida suryy
1 · Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Tahir M. Kaumi
No, pls continue this.
Like · React · Reply · More · 10 Oct 2015
Abubakar Ibrahim
tnx alot
Like · React · Reply · More · 10 Oct 2015
Salisu M. Mu'azu Dankado
Him
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Ibrahim M-Gani Yariman Fcbk
Tanx surry
Like · React · Reply · More · 10 Oct 2015
Usman Aliyu Taller
Mungode
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO....4**8

Haka ranar ya koma gida sukuku ba walwala har sai da ma,u ta fahimci yana cikin wani hali, bata matsa masa da tambaya ba don ya sanar da ita tuntuni akwai matsala a ofis dinsu, don haka addu,a kawai takeyiwa mijin nata. Duk yadda taso faranta masa ta sanyashi cikin farin ciki ta kasayi dole ta barshi shi daya cikin daki don ta kula abinda yafi bukata kenan.
Nana kam da kyar takai kanta gida domin kanta wani irin ciwo yake yi da juyawa. Tana yin parking ta nufi gidan da gaggawa, amma bata kai ga ainihin sashinta ba ta yanke jiki ta fadi kasa. A dai dai lokacin hajiya batula mahaifiyarta ta fito daga sashinta ta hangota. Hajiya batula ta fasa kara ta nufeta da gudu tana salati, ta kamata ta dagota sai taga idonta ya juye alamar ta suma. Ta fasa ihu tana kwallawa masu aikin gidan kira. Da gudu suka iso kowa a rude jin kiran da hajiya batulun ke musu, ganin halin da nana ke ciki ya kara daga musu hankali suma. Hajiya batulu cikin kuka take cewa kubani ruwa na yayyafa mata, daga daga cikin matan ta kwasa da gudu sakwanni kadan ta dawo dauke da ruwan robar swan mai sanyi.. Hajiya batulu ta karba saboda tsabar gigicewa ma kurzawa nana shi tayi ajikinta gaba daya. Nana tayi wata doguwar ajiyar zuciya ta bude idonta a hankali. Hajiya batula tayi doguwar hamdala sannan ta kalli yan aikin tana cewa ku taimaka mini ku kamata mu kwantar da ita akan kujera. Suka ciccibi nana aka kwantar da ita ta dauko wayoyinta ta fara neman layin wayar mijinta wanda yake abuja. Bugu daya ya dauka, cikin tashin hankali hajiya batulu tace masa Alhaji nana bata da lafiya, yanzu ta fadi har da suma. Alhaji nura kwangila ya gigice yace, suma kuma me ya sameta? Ta kalli nana dake kwance akan kujera tana kallonta tace bansani ba, dama cikin kwanakin nan na kula bata jin dadi, amma danayi mata magana sai tace babu komai..........Kinga bar bayanin nan haka zanyiwa likita waya yanzu yazo ni kuma zan hayo jirgi na taho yanzu, ki kula da ita kafin nazo. Ya kashe wayar da damuwa a take a lokacin yayi waya a tanadar masa ticket mai zuwa kano.
Like· Report·Jun 14
Nusaybarh Mustapha Ibraheem
127. Hajiya batula ta isa ga nana ta zauna ta dora kanta bisa cinyarta tana shafa kanta. Sannu nana, meke damunki? Nana ta rintse ido hawaye ya zubo mata , batason tunawa amma bazata taba mantawa ba domin soyayyar Ahmad ta zame mata masifa, bazata iya rayuwa ba Ahmad ba. Ganin tana hawaye ya kara tayar da hankalin mahaifiyarta ta tace shikenan ya isa daina kukan. Mintuna goma baya sai ga likita ya iso gidan masu hidima sukayi masa jagora har cikin gidan da yake kowa ya sanshi a gidan. Hajiya batula na ganinsa ta mike da sauri tana fadin yauwa karaso doctor ka dubamin ita. Likitan ya isa da sauri ya sauke jakarsa da yake rataye da ita ya fara fiddo kayan awo kala kala. Cikin yan mintuna kadan ya kammala auna nana yayi mata wasu yan tambayoyi ta bashi amsa, daga karshe yace da hajiya batula dole sai sunje can asibitinshi anyi mata wasu gwaje gwajen. Hankalin hajiya batula ya kara tashi sosai ta dubi likita tace likita gaya min meke damun diyata? Cikin kwantar da murya likitan yace kwantar da hankalinki hajiya ba wani abu bane ba, ina dai so nasami sakamakon da nake bukata ne. Babu musu ta fara shiryawa aka dunguma zuwa asibiti.

11 October 2015 at 16:52 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like26
Write a comment...

·
Salisu M. Mu'azu Dankado
Gud
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Ummu Khadijah Ummu Adnan
Weldon
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Asabe Ali
10x
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Abubakar Ibrahim
pls continue
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Usman Aliyu Taller
Nice
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Dauda Yahaya Masanawa
Madalla
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Adamu Safeeyarh
tnx
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Tahir M. Kaumi
Next pls
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Azinatu Umar
TNX
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Muhd Dawud Rano
Muna tare
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO 4**9

daga karshe yace da hajiya batula dole sai sunje can asibitinshi anyi mata wasu gwaje gwajen. Hankalin hajiya batula ya kara tashi sosai ta dubi likita tace likita gaya min meke damun diyata? Cikin kwantar da murya likitan yace kwantar da hankalinki hajiya ba wani abu bane ba, ina dai so nasami sakamakon da nake bukata ne. Babu musu ta fara shiryawa aka dunguma zuwa asibiti, Acikin mota tayiwa Alhaji nura kwangila bayanin sun wuce asibiti, alokacin shi kuma yana cikin airport hankalinsa ya kara tashi kwarai da gaske amma ya dake. Dukkan gwaje gwajen daya kamata anyiwa nana, sai dai sakamakon ya dan girgiza likitan don haka yaja bakinsa yayi shiru don bai kamata ya sanar da mace wannan labarin ba. Ana kiran sallahr isha,i alh nura kwangila ya iso garin, kai tsaye asibitin dr musa ya wuce har dakin da nana take ciki lokacin anyi mata wata allurar barci idonta yana rufe, hajiya kuma tanayin sallah. Alh nura ya isa gadon da nana ke kwance ya tsaya yana kallonta sai kuma ya fara lalubar wayar Dr. musa daya tabbatar masa yana cikin asibitin sai ya fita ya nufi ofis dinsa. Yana shiga Dr. musa ya mike cikin girmamawa yana gaisheshi amma bai kula da wannan ba cewa kawai yakeyi Dr meke damun diyata me ya faru da ita? Dr. musa ya jinjina kai yace kwantar da hankalinka alh zauna na maka bayani.
Alh nura kwangila kamar bazai zauna ba amman dai ya hakura ya zauna yana kallon likitan. Dr. musa ya zauna ya dakko masa envelop a rufe kamar guda uku ya fara dubawa yana kallon alhaji nura wanda ya kagu yaji abinda zaice. Dr. musa ya fara bayani. Da farko na fara yiwa nana gwajin jini ne na tadda jininta ya hau........... Nanar me zai sanya jininta hawa kuma? Alh nura kwangila ya tambaya a gigice. Dr. musa yace wannan shine abinda ke bani mamaki. Sannan yanayin bugun zuciyarta ya sauya yana dudu fiye da yanda ka,idarsa take wannan dalilin ya sanya nace mu taho asibiti don ayi mata sauran gwaje gwajen, ga mamaki na sai naga zuciyarta ta dan sami matsala don ta buga fiye da yanda ya kamata ta buga musamman lokacin da ta fadi, Allah ya taimaka anyi gaggawar kawota asibiti da wani mummunan abu ya faru da ita. Hankalin alh nura kwangila ya kuma tashi yace. Abin mamaki meye zai sanya zuciyar diyata bugawa har akusa rasa rayuwarta? Kwantar da hankalinka alh, wannan ba wata matsala bace insha Allahu komai zai zama dai dai zata dawo dai dai musamman idan anyi gaggawar gano abinda ke damunta an kuma magance mata shi da wuri. Alh nura kwangila ya gyada kai yana fadin, na gode Dr. bari naje wajen mahaifiyarta. Ya tsare hajiya batula da tambayoyi, abinda ta fada masa yana can kafin yazo shi ta kara fada masa yanzu ma, dole dai su bari diyar tasu ta sami lafiya. Washe gari tunda safe Ahmad ya sami labarin abinda ya faru, hankalinsa yayi matukar tashi, don haka da wuri ya wuce asibitin ya tadda mutane anyi dandazo kama daga kan yan fadanci zuwa dangin hajiya batula dana alhajin, amma ba,a barin kowa ya shiga sai dai ko su gaisa da mahaifan nata ka juya ka tafi. Shima Ahmad din sun gaisa sai dai bai samu ganin hajiya batula ba tana ciki da yake dakin irin na masu kudine har da wani katon falo. Nana tana barci kamar cikin mafarki ta dinga jin muryar Ahmad. Nana tana bacci kamar cikin mafarki ta dinga jin muryar Ahmad lokacin da yake sallama da alh nura kwangila. Da sauri ta bude idonta ta kalli mahaifiyar ta da ke zaune a kusa da ita tayi tagumi cikin sanyin murya tace mummy ba Ahmad ne yazo ba? Hajiya batula tace bansani ba ko kinason ganinsa ne? ta gyada kai alamar eh da sauri hajiya batula ta mike ta nufi falon. Alh nura ya kalleta da sauri ganin ta fito arude yace yaya dai lafiya hajiya? Cikin karewa mutanen wajen kallo tace nana ce tace taji kamar muryar Ahmad wai. Ba wai bane shine yanzun nan ya fita bari na kirashi idon tana son ganinsa ne. Ya dauko wayarshi ya fara neman layin Ahmad bugu daya ya daga har ya tayar da motarsa, amma yace masa ya dawo maza maza nana nason ganinsa. Gaban Ahmad ya fadi yaji kamar kada ya koma din, amma bazai iya kin zuwa ba, don haka dole ya fita daga motar ya nufi dakin gabansa na faduwa yana ta addu,a a cikin ransa. Kai tsaye Alh nura ya shige dashi cikin dakin da nana ke kwance , mutanen dake zaune agurin suka dinga mamakin irin matsayin da Ahmad yake dashi a gurin Alh nura kwangila din daya samu shiga gurin nana. Nana ta kurawa kofar dakin ido dai dai lokacin da Ahmad ya shigo sukayi ido hudu, tayi doguwar ajiyar zuciya murmushi ya bayyana akan fuskarta. Ahmad ya matsa kusa da gadon nata ya tsaya da damuwa akan fuskarshi yace sannu hajiya nana, yaya jikin? Tayi murmushi da sauki nagode da kazo dubani ka kula da komai kafin na koma. Azahiri kowa zai zaci tana magana ne ko taso ganinshi don kamfani da gaske sai dai kasan zuciyarta tayi hakane don ta ganshi kawai. Alhaji nura kwangila da hajiya batula suka kalli juna da mamakin abinda tace.

Surayya

11 October 2015 at 18:02 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like26
Write a comment...

·
Son Guy Bin Abdallah
Ana ahaka
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Salisu M. Mu'azu Dankado
Him
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Son Guy Bin Abdallah
Ana haja
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Tahir M. Kaumi
Next pls.
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Amirah Muh'd
Tnx
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Umar Dahiru
Tnx Alot
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Ummu Khadijah Ummu Adnan
Tnxxx
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Ahmad Sabo
Good. Sury
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Azinatu Umar
TNX
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Firdaus Feedy Paradise
Dan Allah aci gaba
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO....4**10

Ahmad yayi tsaye kamar bazai tafi ba sai da ya dan jima sannan ya musu sallama ya wuce idonsa ya ciko da kwalla saboda ganin irin halin da nana ta shiga, idonta yayi jawur hawaye ne kawai ke zuba daga cikinsa.
Ko da ya isa ofis kasa komai yayi sai tunanin halin da nana ke ciki da ace zai iya taimakonta da yayi, amman bazai iya bari rayuwar nana ta lalace ba dole zai san abin yi. Kwanaki hudu tana cikin asibitin amma babu sauki sai abinda ke karuwa, musamman hawan jininta gashi anyi anyi ta fadi abinda ke damunta ta ki sai kuka. Shi kansa Ahmad tun zuwansa na farko ya kasa kara komawa, don bai son ganin nana cikin halin da ya san bazai iya taimakonta ba. Bayan kwana uku Abangaren nana dai hankalin iyayenta atashe yake kullum yau kam Alhaji nura kwangila ya tabbatarwa kansa da sai yasan abinda ke haddasawa diyarsa wannan halin da take ciki, don suna jin kukan da take kusan kwana tanayi indai ba,ayi mata allurar barci ba. Tana zaune atsakiyar gado tana shan ice-cream ya taso daga inda yake ya dawo kusa da ita ya zauna agefen hadadden gadon dake kama dana gidan wani hamshakin sarki don ya sha gyara. Cikin sanyin murya Alh nura ya kirawo sunanta ta dago kai ta kalleshi gabanta yana faduwa ta amsa. Ya sake kwantar da murya yace nana ki taimakeni ki sanar dani gaskiyar abinda ke damun ranki? Nana ki tuna bani da kowacce diya a duniya sai ke, ke kadai Allah ya bani dan uwana guda daya ne yana kwance cikin jinya ke kadai nake kallo adangina kuma yata, idan kika bari na rasaki bazan yafe miki ba, don babu makawa nima karshen rayuwata yazo...... Yayi dan shiru yana kare mata kallo sannan ya cigaba Nana ki taimaka ki sanar dani abinda ke damunki, ina da kudin da zan siyo miki dukkan abinda kike bukata awannan duniyar, idan kuma ya fi karfin siya zan tayaki da addu,a Allah ya baki shi ko kuma ya sanya sanyi da salama azuciyarki ki fadamin abinda ke damunki nana.. Nana ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na zubowa daga idonta tace. Daddy idan na gaya muku abinda ke damun zuciyata zakuji haushina da abin watakila hakan ma ya sanya ku daina tausayamin. Injiwa yagamiki? Dukkan abin da zai sanya ki cuta irin wannan ya wuce mu d'aukeshi k'arami. Ki gaya min Nana ko kin manta nine Daddy d'inki da kike gayawa dukkan damuwarki?" Ta d'ago kai ta kalleshi kamar ba za ta fad'a ba, sai ta ce, "Daddy tun randa na yiwa Ahmad wulak'anci a Gidan mai na fara kamuwa da sonsa, nayi zoto wasa ne ko zan rabu da son a hankali, amma sai abin ya cigaba da hauhawa, cikin raina har ta kai na zamto bani da buri bayan ganinsa kullum, don haka kullum sai naje Gidan Man su, daga baya nayi hanyar da ya sami aiki kusa dani, wannan ya sanya na sami sanyi cikin raina, ban ta6a zaton idan na bayyanawa Ahmad buk'atata zai juya mini baya ba, sai dai na gano halin Ahmad bai sanya akan komai don na gwada masa dukkan abin da zai sanya ya gane ina k'aunarsa amma ya kauda kansa, daga k'arshe da naga sonsa yana neman hallakani ya sanya na sanar da shi amma sai ya gaya mini bai sona bai kuma ta6a sona ba....." Ta fashe da kuka maganar ta kasa ciga da fitowa. Hajiya batula da Alhaji nura kwangila suka bita da kallo da tausayawa basu taba zaton abinda ke damun yarsu kenan ba. Wato hakan na nuna musu ta warke daga cutar dake damunta tun tana da kuruciyarta, wacce suka kashe makuden kudade gurin ganin sun samar mata lafiya. Alhaji nura kwangila ya riko hannunta ya dora kanta akan kafadarsa yace. kwantar da hankalinki diyata nasan illar da soyayya ke yiwa zuciyar dan adam dan ta taba illata rayuwata amma indai akan Ahmad ne kukan ki ya kare da damuwa zan samar miki shi da ikon Allah. Ya mike da sauri yanzu zanje gareshi insha Allahu damuwarki sun kare. Idon nana na zubar da hawaye tana kallon baban nata daya nufi kofa kai tsaye zai fita cikin sanyin murya tace. Daddy don Allah idan yaki yarda kada kace zaka koreshi daga aiki, ganinshi kadai abin jin dadi ne agurina kada ayi masa dole akan sai ya soni. Alhaji nura kwangila yayi shiru bai juyo ba amma tabbas maganar diyar tashi ta shigeshi tausayinta ya kara kamashi ashe akwai wani abu da diyarsa zata iya rasawa awannan duniyar yana raye? Lallai iko yana gurin ubangiji ya kada kansa ya fice. Hajiya batula ta matsa kusa da nana don rarrashinta. Ahmad yana zaune a ofis wayarsa ta fara kira ya dago da sauri ya na kallon screen din wayar lambar Alhaji nura kwangila ya gani gabansa ya fadi amma dai dole ya daga, yana shirin gaida Alh nura sai ya katseshi da cewa kana ofis ne Ahmad? Da hanzari Ahmad yace ina nan Alh. Alhaji nura kwangila, ok to ganinan zuwa. Gaba daya hankalin Ahmad ya gama tashi ji yake kamar ya gudu kada Alhajin ya sameshi amma babu halin yin hakan dole ya zauna ya jira zuwanshi. Lokacin da Alh nura kwangila ya turo kofa ya shigo Ahmad ji yayi kamar akan kirjinsa aka mako kofar saboda wani bugu da yaji kijinsa nayi. Da sauri Ahmad ya mike tsaye yana wa.

12 October 2015 at 13:56 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like27
Write a comment...

·
Hauwa Muhammad
Friends y Kke d ftn kowa Lfy dn Allah angama tattalin so ne wlh baba na ne y rasu bana Hawa online ngde
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Jamila Umar Tanko BooksJamila Umar Tanko Books
Allah ya jikansa da rahama, mu kuma intamu tazo... More
Al-Rayyan... replied · See all 4 replies
Sumayya Nasir Abdullahi
mungode acigaba
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Dahir Uthman
Tend
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Khadijah Aliyu
Tnx
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Al'amin Khalid Sulaiman
Mungode, Dan Allah acigaba Dakyau,
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Usman Aliyu Taller
Muna godiya
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Nafisa Danladi Danladi
Allah jikan sa.ya.jikan iyaye mu ,ya jikan alumar musulmi
Like · React · Reply · More · 17 Oct 2015
Abban Husnat replied · 1 reply
Bakoji Lamara Misau
Gud
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Ahmad Sabo
Dai dai kenan!
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Hauwa Muhammad
Ameen nagode sosai
Like · React · Reply · More · 13 Oct 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO...4**11

Gaba daya hankalin Ahmad ya gama tashi ji yake kamar ya gudu kada Alhajin ya sameshi amma babu halin yin hakan dole ya zauna ya jira zuwanshi. Lokacin da Alh nura kwangila ya turo kofa ya shigo Ahmad ji yayi kamar akan kirjinsa aka mako kofar saboda wani bugu da yaji kijinsa nayi. Da sauri Ahmad ya mike tsaye yana wa Alhaji sannu da zuwa. Alhaji Nura ya dubeshi yana murmushin yak'e yace, Zauna Ahmad inason yin magana dakai ne, kuma magana ce mai mutuk'ar muhimmanci a garemu. Ahmad ya koma ya zauna cikin sanuyin jiki, gabansa na dukan d'ari- d'ari. Alhaji Nura ya janyo Kujera dake fuskantar wandda Ahmad ke kai azaune shima ya zauna ya tsare Ahmad da ido yana fad'in, Ba sai naji komai daga bakinka ba na san Nana ba ta yin k'arya, ko yaudara, abinda na ke fata daga gareka kawai shi ne ka amince Ahmad, bani da Kud'i ko ikon da zaniya siyan soyayya, domin da zan iya da tuntuni na siyuwa wani soyayyar Nana na aurar daita. Tunda Nana ta taso ta k'i jinin kula Saurayi har zuwa girmanta, hakan ya jagoranci tunaninmu da kuma fad'hn wasu Malamai cewar wai aljani bak'i ne ya aureta, yanzu kuma sai gashi allah ya kawo mana maganin abin rana d'aya, nana ta furta da bakinta cewa tana sonka Ahmad. Ahmad kayi duba da kyau ga wannan lamari, nana yarinya ce mai kyau da tsari kamar nana ace ta tunkari namiji tace masa tana sonshi ka san ba k'aramin abu bane,
Kamar nana ace ta tunkari namiji tace tana sonshi ba karamin abu bane, ka taimakeni Ahmad ka auri nana don Allah. Ahmad kansa yana kasa tunda alh nura kwangila ya fara magana, da ace akwai mutumin da zai iya yiwa wani abu ko da ranshi bai so ba to bai wuce Alh nura ba, amma bazai iya yiwa ma,un shi kishiya ba dan yiwa ma,u kishiya kamar yiwa ummansa ne, mutanen da suka raineshi suka bashi mace yaya zai iya yi musu haka? Bashi da amsar da zai iya baiwa Alh nura kwangila dan haka ya dukar da kansa kawai. Alh nura kwangila ya zuba masa ido da mamaki sannan yace. Ahmad ko akwai wani abu da nana take wanda ranka bai bukata ko kuma tana da wata illah ne gaya mini don banyi zaton wani namiji zaiki diyata ba a wannan lokacin. Ahmad ya girgiza kai yana fadin, ko daya babu wani abinki dana gano a wajen nana amman..........Sai kuma yayi shiru ya sara ma mai zaice. Lallai Ahmad ka nunamin kai namijin duniya ne, hakan kuma ya sanya na kara yarda nana tayi zabi, don nayi imanin wani zai so nana ko don arzikinta ko kyanta ko dan nasabarta amma ko daya bai burgeka ba daga cikin wadannan abubuwan. Ahmad ya kada kai tunda nake ban taba sanya kwadayin abun kowa araina ba na wadata da abinda nake samu, amma kayi hakuri Alhaji ina cikin halin da ba zan iya aurar wata ba. Alhaji nura kwangila ya sake kallon Ahmad da tsananin mamakin karfin halinsa amma hakan kara birgeshi yake da kuma nuna masa shine mijin daya dace da diyarsa nana.Cikin kwantar da murya yanzu Alh nura kwangila ya cigaba da magana. Yanzu kam alfarma nake nema ka dubi halin da nana take ciki, bani da kowacce diya sai ita kadai zan iya rasata saboda sonka ka ceci rai Ahmad, ka ceci rayuwarta daga cikin bakin cikin dake damunta. Jikin Ahmad yayi sanyi lallai yakamata yayi wani abun akai, amma

Please Login or Register in order to submit comment