Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uwansa yana bashi hakuri amman ina tuni yafice yadawo tsakar gidan yayi duru duru cike da tashim hankali saiyafada dakin dasauri yatadda lami zaune tayi wuki wuki tana zare ido yana shiga tafara magana ka kwantar da hankalinka malam indai akan gidane muje mukama haya tunda ai....... Rufemin baki munafuka sau nawa nake cemiki kicire hannunki daga kan maganar yaran nan yaji koshi waye aduniya amman saida kika fadamasa to tsaya kiji banida wani gata dayawuce na Allah da dan uwana daya daukoni daga cikin wahala yanemo mini aurenki yaci gaba da dawainiya dani kisani idan na bar nan banida wurin zuwa don haka kedai da kika janyowa kanki kece zakibar gidan dolenki kuwa takalleshi damamaki matuka tana fadin malam akanfadin gaskiya kake wannan furucin kinga banja dagon zance dakeba kiwuce kawai nasakeki yana kaiwa nan ya fice daga dakin .......4⃣0⃣ Lami tafashe da kuka tana fadin na shiga ukku yanzu akan dan shege har akasane natsani wannan yaro daman nasan zuwanshi gidannan Annoba ce kuma harzuwa yanzu banyi nadamar fadin cewar shi shege neba dawannan tadinga sambatu tana kuka Sunwayi gari cikin tashin hankali kam tun Asuba tabar gidan saboda yanda jibril ketayimata kwakwazo hankalin yayanta yatashi matuka musamman Raliya da Amina musa kam yanajin ciwo sakin mahaifiyar tasa Amman yanajin takaicin Abinda ta.aikata gaba daya gidan angaza karyawa kowa yanacikin damuwa ma'u kam kuka takeyi tana fadin danasani dabangayawa yaya Ahmad abinda raliya keyiba duk da deeje tana cikin tashin hankali hakan baihanata rarrashin diyar tata ba tunda suka dawo daga masallaci jibril yatare malam yana kara bashi hkr dasanar dashi hukunci daya yanke tun dare jiya malam sulaiman yakalli dan uwansa cike da tashin hankali yace subhanallahi meya sanya ka.aikata haka nima bacin raine yasanya fadin abinda nafada kayi hakuri da abinda nayimaka dankai dan uwa nane jinina daban isa nasakakaba Dejee kam bataji ko dar da mutuwar auren lamiba tunda tarasa danta komaima yafaru wajen misalin karfe goma sai Hajiya Amina ta iso akidime don yan dubo Ahmad sun iso hargidanta duk yanda deeje kekorin taddanne zuciyarta saida ta fashe dakuka ganin hjy Amina tana fadin yagudu hjy bamusa inda yashigaba danasani munbakishi ina zankai hakkin yaron nan tadafa kafadarta cikin kwantar da murya take fadin kidaina wannan maganar deeje ko ina yake aibazaiwuce kaddararshi ba Nakuma tabbata duk inda Ahmad yake zaidawo inda kuke muyi Addu.a kalaman hjy ne suka dan kwantar mata da hankali tace kuma adaina zuwa nemansa zaidawo dakanshi tasoyin maganin lami saidai tasamu lbr sakin da.akayimata kwanaki ukku suka cika cikin tashin hankali abincin kirki babu maici agidan Ranar kwana na hudu datafiyar tasa ma.u tadawo daga kai markaden gero na kokon da yamma sakaliya tana tafe tarera wakokinta tahangoshi tafe da kayansa tunna ranar dayatafi yarame yayi duhu dakyar yake tafiya kamar me ciwon kafa batasan sanda ta watsar da robar markadan ta falla gida dagudu tana fadin Umma gayaya Ahmad umman dake tukin tuwo tafito da.azama jikinta sai kyarma yake harzaninta yana neman faduwa darawar baki tace A ina kikanshi gashinan zaishigo gidannan yashigo gidan dasallama
4⃣1⃣ yatsaya turus cikeda farin ciki ganin ummansa itama tsayawa tayi turus tana kallonshi kuma kome tatuna saita nufeshi da sauri ta wanka masa mari sai kuma tafashe dakuka tajuya gida da sauri ma.u dake tsaye ta zuba masa ido wanda ya ciko da kwalla shima idon ya zubamata yana hawaye shida kansa yasan abin da yayi bai kyauta ba cikin kuka tace yaya Ahmad mai yasanya ka gudu ka barmu Umma ta daina bacci tadaina cin Abinci baba yadaina fita kasuwa yaya Auwalu yadaina zama a chemist sani yadaina zuwa kasuwa ni idan akaturani makaranta bana zuwa sai intafi nemanka ranar har gwammaja naje dakafuna nemanka memukayimaka kagudu kabarmu yakamo yarinyar maicike dawayo ya rungume yana kuka yafadin ba gudowa nayiba tafiya nayi nasamu natsuwar zuciya ta saidai bansamuba zama daku shine nutsuwar zuciyata yamike hannunta suka nufi cikin gida saidai duk yanda yaso yayi wa Umma magana taki sauraronsa tayi fishi dashi maitsanani wanda yakara tada masa hankali Malam sulaiman yagyara zama yana fadin tabbas hjy Amina tayi gaskiya tace mini Ahmad bazai iyabarinmuba munyi masa rikon dako mahaifiyarsa ce tadawo duniya bazatayimasa irinsa ba saidai nayi mamaki dakabarmu Ahmad shinkanaganin kayimana adalci yadukar dakai cikin kuka yake fadin kuyafemin baba tabbas nasan na.aikata muku laifi mai girma wani irin tausayi yakama malam mai tsanani shikadai yasan Abinda yakeji Azuciyar sa game da yaron
4⃣2⃣ kwanaki sunja ga Lami tun tana ganin abin kamar wasa har karamar magana tazama babba domin sam mlm jibril yaki zuwa biko sai abin yazamomasa kamar gaba takaishi domin daga gidan yayansa yayansa akefitomasa da girki maidadi wanda yafi namatar sa Su raliya kam kullum saita saci jiki ta tafi gurin uwarta suyita ta kitsa mugunta dadai lami ta kula abin bana wasa baneba hankalinta yafara tashi ga wahalar gidan tafara damunta da yunwa don haka tafara bin kan mahaifinta
ABDULLAHI YUSUF MAITAMA
09034598552
@whatsapp

11 April 2015 at 06:49 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like61
Write a comment...

·
Dauda Yahaya Masanawa
MADALLAH
Like · React · Reply · More · 11 Apr 2015
Mukhtar Umar Daura
Muna gdy
Like · React · Reply · More · 12 Apr 2015
Bakoji Lamara Misau
Gud
Like · React · Reply · More · 11 Apr 2015
Halima Ibrahim
Tanks
Like · React · Reply · More · 11 Apr 2015
Halima Abdullahi
tnx
Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015
Zainab Muh'd Zakariyya
Wldn
Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015
Ahmad Sabo
Sannu da kokari
Like · React · Reply · More · 12 Apr 2015
Yusuf Mamman Nadaji
Godiya muke, babu admin kamar ka a cikin wannan zauren!
Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015
Sardaunan Telolin BG
Wannan lbrn har sai da ya sanya ni hawayee
Like · React · Reply · More · 12 Apr 2015
Yahuxa Kabir
tnx
Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015
View more comments… Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO PART 4

Saidai mlm jibril yace bashi za.aba hankuriba yayansa za.aje abaiwa idan yahakura shikenan dan bawan Allah baiyi kasa agwiwaba yanufi gurin mlm sulaiman din darajar tsohon tasanya yace shikenan komai yawuce amman sujawa Lami kunne matuka domin bazasu kuma yadda da irin wannan rashin tarbiya ba haka tsohon yatafi yana godiya haka aka tarkato Lami aka dawo da ita su Raliya tamkar sallah shi kuwa mlm jibril sai cika yake domin wahala takuma dawo masa sabuwa dal yanayin Rayuwar Ahmad tasanya gaba daya yadukufa kan karatunsa bashida lokacin komai sai karatu idan kaga yana dariya yana cikin gidan donka da Ummansa ta damu ahaka har suka shiga aji hudu Ummi sada itace yariyar data dafe masa tun farkon shigowar su take bibbiyarsa dafarko dasigar koyon karatu tashige shi har shakuwa tashiga tsakaninsu ahankali tajuya soyayya kusan kowa yasan halin da ake ciki cikin dakinsa ma katon hoton tane kyakykyawa ce fara da ita duk da bata cika tsayiba Ummi ce kadai kesanyashi farinciki idan yana cikin damuwa yana son Ummi matuka musamman yanda iyayanta suka daukeshi kamar su suka haifeshi yana tsaye adaki yana kallon hotonshi na ranar dasuka kammala karatu yana sanye da kaya wadanda digiri yan uwansa sun baibayeshi cike da farin ciki ga hajiya Amina agefe dakuma babansa ga ma'u nan anyimata kwalliya yana matukar son hoton arayuwarsa domin yasanshi dangata ne lokuta dadama kalmar shege tafado masa yatuna wannan matsayin dayake kai yakuma tuno yanda yan uwansa da iyayensa kesonshi sai yaji zuciyarsa tayi wasai baitaba kukan rashin dangiba sakamakonsa yayi kyau matuka har an turashi jahar taraba bautar kasa hankalin Ummi gabadaya yatashi domin batason yayi nisa da ita aganinta shekara tayi yawa saida yadinga tausarta dasu ishak sannan tahakura itakam tayi sa.a batayi nisa ba jigawa akaturata amman bakincikin rabuwa damasoyinta yaraunana farincikinta kwanci tashi kamar yaune shekara guda sai gashi haryadawo umma tayi murna matuka hajiya Amina kamar itace tayo sabon digiri sai murna take yi da Alfari ta amshi takardunsa daniyar tanemasa aiki saidai abin yaci tura domin samun aiki agarin saika shirya daga karshe dai tasamomishi aiki n gidan wani mai dasuke mutunci da maigidanta da maigidan man kwarai dagaske Alhaji nura kwangila yayi murna kwarai da samu don babu abinda yake buri illah yafara cin gashin kansa yataimakawa iyayensa kamar yanda suka yimasa duk sanda yatuno iri dawainiyar dasukayi dashi saiyaji son su yakuma cika ranshi Lami tayi tagama tsakaninta dashi saikallo sai harara domin tunbayan dawowarta gidan tashiga taitayinta saidai samun aikin nasa yatsaya aranta matuka domin cikin kankani lokaci komai nasa yasauya yakuma yama dan gayu cikin lokaci kankani yasayi babur dinsa irin wanda samarin zamani ke yayi tsutsun soyayya ...
4⃣4⃣ ba umma ba hatta mlm yadaina kukan babu domin Auwalu da sani da Ahmad sun isheshi kowa akwai abinda yaware yake siya awata don ma dai Auwalu yatattago Aure amman duk da haka yana iyakacin kokarinsa ko kishin yanda rayuwar gidan ke gudana Lami batayi nata sanya yayanta suzama mutane nagari idan kafidda musa saishegen kishin tsiya da kyashi Raliya kam likkafa taci gaba tazama gogaggiyar yarduniya domin duk tayi billicin tayi fari tas kamar gauta ga tara samari kala kala akofar gidan tun yayyen suna fada har sun gaji sun watsar domin lami ke dauremata gindi tace anayiwa hassada dakyashi cikin wannan sati aka kai kayan Auren Ahmad gidansu ummi saidai mahaifinta yatsaida lokacin biki gabadaya wata hudu wannan abin yafi yiwa Ahmad da ummi dadi domin sunkagu sumallaki junansu Abba da umma kuwa sunyi farinciki da hakan Ahmad kam yadage hada kayan Aure sai Alokacin yagano kokarin da Auwalu yayi dominshi har gini mayayi koda yake tuni yazama cikakken ma.aikaci yana da albashi me kyau shi kam haya zaikama dole amman gaskiya ba zai kama hayar karamin gida ba domin yasan Umminsa yar gayuce gwara ya kama gidan da zaiburgeta saura wata daya biki yagama hada kayan lefensa yayi kokari matuka domin saida yayi akwatuna hudu sanda yakawowa su umma kaya sun cika mamakin kokarinsa daganan yafara kokarin nemo gida da kudin haya dama babansa ya sauke masa sadaki domin tun sanda za.akai kayan lefe yabada dubu ashirin na sadaki biki yarage sauran sati biyu yasami gidan sa makyau acan Unguwar gaida mai dakuna madaidata guda ukku da kichen da bandaki dangin Ummi harsunzo sun gani sunyaba komai gabadaya gidan ansanya masa wuta yaimasa fenti maikyau saidai abinda yafi damunsa da za.ayi bikinsa ma.u bataman domin suna gab dafara jarabawa tunsauran kwana goma biki yafara rabao iv nabiki yabaiwa Ummi nata anshirya shagali daidai na takala ma'u kam harkuka tayi amakaranta domin tana lissafin bikin yayanta yazo saura sati guda biki da magriba Umma tana tsakar gida tana ta aikace aikace mata suka fara shigowa gidan da sallama dauke da akwatuna riki riki mamaki yacikata ta mike tsaye tana tambayar lafiya daga inakuma? Domin tasan basuda wata budurwa daza.akawo kayan aure saida suka gama ajiye kayan babu ko gaisuwa daya daga cikinsu ta kalli umma tace daga gidansu Ummi aka aiko mu mudawomuku dakayan aurenku domin ajiya mukasamu labarin ashe yaron dake neman diyarmu ba danku bane ba shege ne daba.asan asalinsa ba Umma tadafe kirji cike da fargaba daidai lokacin Ahmad yashigo gida inyajikomai akunnensa don haka yatsaya turus a bakin kofa cike da tsananin damuwa datashin hankali MUHADU AKASHI NA BIYU

BOOK 2

1⃣ DAME AKE ADO 2 Uban waye yagaya muku wane munafuki ne yasanar daku wannan magana Umma tafadi ahasale batabar sunce komai ba tadora da masifa to duk wanda yagayamuku karya yake yi hassada ce kawai nice nahaifi Ahmad nice uwarsa Afusace take maganar Daya daga cikinsu takuma amshewa haba baiwar Allah kiyi hakuri munriga munji komai zance duniya fa baya buya Idan har danki ne mai yasanya aka cireshi daga lissafin sunan yayan gidan kinada Auwalu da sani da rabi'u yaya akayi shi yafita daban? Mu kinga yansako ne kiyi hakuri sai anjima tadire kudin sadaki akan kayan suka juya suka nufi kofar fita Umma tabisu dasauri tana fadin don Allah kudawo nayi muku cikakken bayani don Allah kudawo Basu saurareta ba suka nifi kofa suna ficewa suna ganin Ahmad suka kalleshi suka wuce kawai Umma data biyosu da sauri arude taci karo da Ahmad tsaye ta yi turus cike da tsanani tashin hankali tana kallonsa Ahmad yana tsaye idonsa yana zubda hawaye cikin muryan kuka yake fadin kirabudasu Umma ki kyalesu gaskiya suka fada munyi laifi dabamu gayamusu gaskiya tun farkoba wannan wace irin masifa ce wane irin cin mutunci ne wannan don cuta sai da muka gama komai harmun raba katin biki zasuzo mana dawannan maganar wane irin Abin kunyane wannan shikam tsananin tausayin Umma yafi komai yawa aransa wane irin so ne wannan baiwar Allah take yimasa ina ma itace tazo a matsayin mahaifiyarsa inama ana komawa baya asauya Uwa daya koma yafita daga cikin mahaukaciya yakoma cikin Ummansa mlm sulaiman dake sallama yashigo da hanzari jin kuka matarsa a rude yake yakalli deeje dake kuka yakalli Ahmad cikin tsananin damuwa yace lfy deeje meke faruwa haka kike kuka subhanallahi Dahannu ta nuna masa tulin kayan lefe dake jibge yakallesu yadawo da kallon kanta yakuma shiga rudu kansa ya kulle yace banfahimta ba deeje ? Cikin kuka tace daga gidnsu Ummi wacce Ahmad zai aura waisun fasa auren ...... Takuma fashewa dakuka yawaro ido waje da wata irin kidima mara fasaltuwa gabadaya jijiyoyin jikinsa sun janye saiji tamkar yadaskare dakyar ya iya karfin halin kakalo wani zancen bangane sunfasa Auren ba wani abu akayimusu tadansausata kukan tana goge hawaye
2⃣ tace ba.ayimusu kome ba mlm saidai munafukai sun shiga ciki lamarin anje angayamusu Ahmad wai shege ne ba shida uba banda wulakacin mai yasanya tunfarko basu ce haka ba saida aka kammala komai malam yayi shiru yama rasa abinda zaice domin iliminsa da tunaninsa suntsaya gabadaya na wucin gadin Lami dake labe tana jinsu tadaka tsalle cike da tsananin murna har da daga hannu sama ta fadi Alhamdulillahi da.anayimin wata fuffuka kullum yaro yana shiga manyan riguna shiga masu gida daman nafadamasa ba da riga ake ado ba da uba ake ado ehe! Takuma zuro kanta tana jiran jin abin da mlm din zaice tasami nadorawa sai jiyo shi yana fadin kunga kuwuce ciki muyi maganar kantabarma suka zauzzauna mlm yadubesu da damuwa yace duk Abinda Allah yakaddara babu makawa sai ya sami bawa daman can Allah baikaddaro ummi matarka bace Ahmad don haka babu yanda za.ayi ka aureta Umma tace Amman mlm baka ganin anbata masa suna kana ganin ko wata diyar yaje aure zata yadda ta aureshi malam ? Ahmad yadafe kai yana kallon umma tausayinta yana kuma karuwa aransa da kyar ya iya bude baki saboda nauyinda yayi masa yace Umma kiyi hakuri kiyi hakuri .......kuka yaci karfinsa malam yadube shi da tausayawa wato Umman yake baiwa hakuri Umma tace Ahmadu kai ya dace mu baiwa hakuri tunda mun kasa kareka daga wannan suna mummuna mun kasa cire kalmar shege daga jikinka Balaifinku bane ba Umma bakuda laifi kunyi duk wani yunkuri na boye wannan mummunan suna daga gareni Amman Allah yakaddara sai najishi Umma idan wanka ba.aboye cibifa malam yakalleshi da hanzari yace kaga tashi kawuce dakinka zansan yanda za.ayi idan takama aje a sulhunta nema zanyi zannemeka yamike dasauri yana tangadi iska naneman kayardashi saboda juwa akarshen kwanar gidan yaci karo da Lami tana lekensu takalle shi da hanzari saita juya tayi cikin gidanta yabita ka llo cike da mamaki mai tsanani bai san abinda yayima matar nan ba tasanyashi agaba yanufi gidansu Ummi yayi shiru yana tunanin idan yacemata shine zata iyakin fitowa kokuma iyayenta suhanata don haka yace da yaro kace Abdul ne bayan tafiyar yaron da kamar sakan talatin saigasu tare da Ummi fuskarta dauke da tsananin mamaki waye kuma Abdul yake sallama da ita mamakin ta yadada karuwa sanda takula bakowa bane sai Ahmad tsaye ya hade hannuwa akirji gabanta ya yanke yafadi tayi dan dum dum kamar zata koma sai kuma ta dake ta bata rai tace gani yaya akayine ? Tana magana babu ko fara.a
3⃣ tsananin mamaki yacika Ahmad yau Ummi ke masa haka yadaure da kyar yace Ummi babu gaisuwa kenanko? Takara hade rai tana fadin baikamata nagaida mayaudari ba kacuceni matuka Ahmad kasanya nabata lokacina daduk wani tunanina akanka Ashe kai shege ne bakada Asali maganar tadakin kirjin kwarai dagaske idonshi yakuma cikowa da kwalla kamar zaifashe da kuka yakwantar da murya cikin lallashi yana fadin
Ummi yanda muka gina soyayyarmu cikin aminci banyi zantan dan Abu kalilan irin haka zai iya mana itaba...... Takalleshe afusace tana fadin Au kai agurinka wannan yar karamar matsalace kenan amman ka bani mamaki matuka to idan kai ta zama karamar matsala a gurinka kana ganin doka kasance shege bawani abu bane to nikam Allah yasani babbar matsala ce bazanso nahaifi ya ya adinga cewar Ubansu shege ne mara asali ba maganar mungina soyayyarmu kuwa daman can akan tubalin toka da karya muka ginata don laillai dana san kai shege ne da banta lokacina akanka ba na soka Ahmad ashe kai mara asali ne ka boyemini kacuceni wlh kayaudaran .... Saita fashe dakuka 4⃣ DAME AKE ADO ....... Ahmad yaji duk yatsani kansa da rayuwarsa tabbas Ummi tayi gaskiya waye zaiso hada zuri.a da shege mara.asali hawaye dayake ta hadiyewa suka ci gaba da biyo kuncinsa yakasa cewa komai domin bashida sauran abinda fada din Ummi ta kalleshi afusace tace idan abinda ya kawoka kenan nizan koma domin inada abinyi a gida yayi dum yana kallonta da tsananin mamaki da damuwa jiyake kamar ya bita yakamota shikenan Ummi tayimasa nisa haka yajuya yanufi gida baisan yanda akayi yajeba yasandai Allah ne yakaishi Acikin gidama duk wanda akasanar da shi abinda yafaru cikin yan uwansa sai hankalinsa yatashi abinda suke tambaya shin Uban waye yaje yafada duk yanda sukaso ganin Ahmad sulallasheshi abin yatura don ya kargame kansa acikin daki Malam sulaiman kam yajima yayi shiru akan dakali yana tunanin mafita har zuwa lokacin da ya cimma burin tunanin nasa yasanya yaro yakira masa dan uwansa mlm jibril bada jimawa ba ya fito ya zauna kusa da yayansa yace malam gani naji ance kana kira na yakalle shi tsahon lokaci sannan yace kaji abinda yafaru da Ahmad kuwa? Dasauri yace naji wlh dazu na shiga gida Lami take sanar dani Abin kam baiyi dadi ba mlm sulaiman yanisa yace tunda abin nan yafaru nake tunanin mafita har Allah yasanya tunanina yafado kan diyarka Raliya da hanzari yadubeshi yace Raliya kuma mlm yagyada kai yana fadin ita kuwa kamar yanda kasani nima nasani Raliya tazama gagararriya wacce duk wani kokari namu dana yan uwanta yagagara gyara ta saidai addu.a gashi tayi girman daya dace ace tafidda miji amman anrasa wanda zaifito dagaske yace yana sonta saboda sanya shashanci datayi agabanta hakan nakeganin abune mawuyaci Raliya tasamu miji nutsattse don haka tunani yasanarda ni mezai hana tunda anyi haka amaida ranar auren Ahmad kanta kada acanza komai ayinan da wata gudan amman kai yakagani domin ka fini hakki akanta yayi shiru tsawoh lokaci yana nazari can yadaga kai yakalli yayanasa yace yaya duk abinda kayanke yayi saidai kana gana ganin Ahmadu bashida wata illah da zata iyayiwa rayuwar Raliya illah ? 5⃣ mlm sulaiman yaduberhe da sauri yace kada kace mini kacikin mutane masu jahilci dakama wani da laifin wasu wlh bagori zanyiwa kaina ba Ahmadu yafi duk yayanda muka haifa nagarta balle Raliya da kai kanka kasan irin abubuwan kunyar da ta daukowa gidan nan auren nasu shi zai zama rufin Asirinsu baki daya jibril ya girgiza kai yana fadin wannan haka yake to Allah yasanya Alkhairi mlm sulaiman yayi murmushi cike dajin dadi yace Amincewarka tafi komai agareni kuma koda hakan batafaruba kayan dakin raliya daman akaina suke tunda dai nine waliyinta dahaka suka rabu ran malam yahaskake yasan yana da damar kara kyautatawa Ahmad da mai dakinsa Adaki yatta Umma tana lazimi da alama addu.a take yiwa danta yasami guri yazauna yana murmurshi yace Allah dai ya.amsa Addu.arki saiki kwanta ki soma bacci Umma tadubeshi damamaki
Fuskarta babu yabo ba fallasa tace malam kenan kana zaton hankulanmu zasu kwanta cikin sauki kuma wannan kankanin lokaci ? Yakuramata ido yana karantar yanayinta yace Amman ai tunda abin nan yafaru Allah muke gayawa ba kyazato zai kawo mana mafita cikin gaggawa tayi saurin yadda da batunsa har daga fuskarta yafimci hakan ta hanyar yin murmushinta tana fadin duk abinda da akace Allah magana takare Amman taimakeni sanar dani wannan Abin dadin yayi dariya yana kokarin tattaro farin cikinsa suyi rabonshi tare yace danki dai yasami matar aure kuma awannan rana za.ayi bada fashi takalleshi datsananin murna da mamaki wacce tagaza boyuwa akan fuskarta tace najima banji labari mai dadin wannan ba dan Allah mlm wacece dan Uwanane ya.amince da baiwa Ahmad auren diyarsa Raliya kinga Asiri yarufu ko ?
7⃣ DAME AKE ADO Anacigaba dagudanarda sha anin biki Abba duk yaraba iv ga dangi da abokansa abin mamaki har sanarwa yasa agidan radio itama Umma tadauki dukanin burinta tasanya akan bikinnan hakanne yasanya yadanne zuciyarsa da damuwarshi ake gudanarda komai cikin farinciki duk da bahakanne akasan ranshiba Abinda yabashi mamaki da tsoro ya kuma sanya Raliya tafita daga ranshi baiwuce rashin mutunci datayi mashi cikin soron gidanba malam yayi matukar kokarinsa domin shine yayi duk wasu kayan daki na Raliya akaje akayi jere hatta kayan daya dace ace uwa tayi shine yayi domin lami cewa tayi Auren da akayiwa diyarta na dole ne donhaka ko tsinke bazatayi ba wadanda suka haka suzasuyi komai saidai mutane dayawa sungane borin kunyane domin babu tsiyar dataaje domin Auren diyarta tuncan baya kudinta wurin bin malamai yake karewa balle yanzu datake iyakacin kokarinta na wannan Auren baitabbataba domin acewarta diyarta kalar masu kudice da Asali ba kamar Ahmad fakiri ba Ranar kamu amarya ba yabo ba fallasa tayi kwalliya kamar gaske koda yake yayyanta sunyi mata fada harda mahaifinta da Abban duk da Ahmad duk da Ahmad bahalarta wurin kamun ba yayi farinciki kwarai dagaske da lbr dayaji gurin yara na yadda Amarya ta cashe rawa

13 April 2015 at 09:38 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
LikeSadAngry78
Write a comment...

·
Halima Ibrahim
Allah yabiya
Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015
Zuhra Maigari
TANX,amma dan Allah adinga mana posting kullm.
1 · Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015
Bernges Kanu
duk maisan group din hausa novel na whatsap to yamin magana ta account dina dan samun shiga group din
Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015
Ya'aqub M Sabo
Hm daman can ummey bason ahmad din take b . Da tanasonsh jin cewa shi shege ne bazai sauya ra'ayinta ko taji cewa za ta iya wulakantashi b. Kawai tanunamasa halinsu na mata wato yaudara hakan na nuni da cewa koda ya aureta taji shi shege ne cewa zatai yasaketa. Kugyara halinku mata. Daga SULEIMAN MUSA SABO COPING.
Like · React · Reply · More · 14 Apr 2015
Musa Yusuf Shariff
Thanks
Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015
Khadija Haruna
Thnks
Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015
Jabeeru Inuwa
thanks alot
Like · React · Reply · More · 14 Apr 2015
Adama Adam Maidala
kash na so ace an hadashi aure da Asma'u
Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015
Nabanje Samaila Saidu
Allah abin godiya
Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015
Bala Sani Hafsat
Tnxxx
1 · Like · React · Reply · More · 13 Apr 2015
View more comments…

Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
------>DAME AKE ADO part 5.
8⣠DAME AKE ADO Karfe biyar daidai motonci daukar Amarya suka iso Raliya tayi wanka duk da batayi wata kwalliyaba amman tayi fes domin wata yayar Lami takama fada tanafadin tunda akadaura ya kamata su watsarda makaman yakinsu surungumi kaddara yaushe za ace akai amarya haka wannan yasanya tadan kimtsa idonta kemadagas babu alamun kunya itakadai tasan tanadin datayiwa Angon nata narashin mutunci buhu buhu haka akawuce gidan mijinta da ita saiwajen karfe 9 nadare Ahmad yagama kammala shirya kayansa tsaf cikin jakarsa don haka rataya kawai yayi yanufi gurin Ummansa tana zaune arumfa dasauran yan biki basu watseba yadurkusa yanagadin Umma zanwuce inabukatar Adduarku idan nayimuku wani abu kuyafemin don Allah yasunkuyarda kansa jin muryansa tana rawa tamkar zaifashe dakuka idanuwan Ummansa sunciko da kwallah tanajin kamar zata rabu da dantane har Abada Allah yajarabeta da tsananin

Please Login or Register in order to submit comment