Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da mamaki da fargaba don tun dayamma yaga ranta abace nakula tunda maraice akwai wani Abu dakike boyemin to kinshiya fada kenan yanzu tafashe da kuka tana fadin aidazun mabakin gaya maka haka kawai ba sai don gudun kada yaransu ji Abinda zamu tattaunawa to wallah nagaji dazaman gidan nan na.amince kakamini haya da masifar da ake shirin kunno mini saita kara fashewa da kuka batunyau ba nake sanarda kai irin azabar da matar nan takeyiwa yaron nan Ahmad ba har Abin yakai nadaina sanarda kai toyau takai har Lami kenunuwa Ahmad shi shege ne bazan yadda ba Allah wannan neman masifa ne dason tozartani Hankalin mlm sulaiman yatashi yadinga fadin subhanallahi garin yaya hakan tafaru tasan kuma doka ce nasanya agidan nan tunba yauba ko mijinta nace yafadi wannan maganar zamuraba gari dashi
2⃣9⃣ DAME AKE ADO ....... ........... Dasassafe yatura yaran makanrata safe kamar yanda suka saba duk Ranar Assabar da lahadi da babu boko saisu tafi daukar darasi amasallacin Unguwar kaitsaye suka shiga gidan jibiril sunyi sa.a kuwa yaran gidan suma sunfice sai matar gidan zaune akan tabarma suna ta hira suna jin sallamar su mlm suka daga kaida mamaki dominsunsan baya shiga gidansu saita baci jibril yamike yana fadin A.a yayane sannu dazuwa zauna mana yadaga hannu yana fadin ba wannan takawoni ba gargadi nashigo yiwa matarka duk da nasan kasan duk abinda take aikatawa to wlh ahir dinta hawainiyarta takiyayi ramata Lami ta dafe kirji tana fadin nikam nashiga ukku nazama shara komai aka kwaso sai ayaba mini yanzu kuma nayi..... Rufemin baki marar kunya banza aikinfi kowa sani Abinda kikayi waike danbakida mutunci harkike tsare yaron nan Ahmadu kina masa habaici dole duk saiyasan shiba mune iyayensaba ko? Lailaha ilallahu nidin wlh sharri akemin yaushe nataba tareshi nagayamasa wannan maganar kuma? Yakalli deeje yana cigaba dafadin gayamata duk abinda tafadi tasan ya dawo kunnenmu deeje tamaimaita duk Abinda Ahmad yasanar da ita har shegen datake cemasa sai lami tayi wuki wuki babu kuma bakin magana dontasan tafada yanda kuma suka tsara sai take tunanin ko deejen taji nema


ABDULLAHI YUSUF MAITAMA
09034598552

9 April 2015 at 07:24 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like55
Write a comment...

·
Saihanatu Umar Umar
mungode sosai
Like · React · Reply · More · 28 Feb 2019
Fatima Bintu Mohammed
thanks allah yasaka
Like · React · Reply · More · 21 Mar 2018
Sadam Yusuf
Ana wata gawata
Like · React · Reply · More · 9 Apr 2015
Muhammad Layya Misau
Ina gai suwa yusuf maitama
Like · React · Reply · More · 9 Apr 2015
El-aliyu Hudu Mairafi
Tnkx
Like · React · Reply · More · 9 Apr 2015
Usman Mustapha
Muna Godiya
Like · React · Reply · More · 9 Apr 2015
Dauda Yahaya Masanawa
MADALLAH
Like · React · Reply · More · 9 Apr 2015
Ayshee Mohammed
8
Like · React · Reply · More · 14 Apr 2015
Abubakar Ibrahim
Godiya ba adadi
Like · React · Reply · More · 9 Apr 2015
Ukashat A Abbakar
thnks alot
1 · Like · React · Reply · More · 9 Apr 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
-------> DAME AKE ADO part 3.

3⃣0⃣ Malam sulaiman yace to yaya koharyanzu sharri ake miki eye? Mijinta ya amshe don Allah yaya kayi hakuri kuskurene akasamu kuskuren gidanku nace kuskuren gidanku tun yaro nan yana wata guda matarka ke cutar dashi yanzu kuma abin yanzu kuma abinda zata koma yi kenan idan kinkwantar da hankalinki watarana zan sanarwa Ahmad wacece mahaifiyarsa kodon yadinga yimata Addu.a ma amma sai sanda ya mallaki hankalin kanshi yatara iyali yasami wadanda zasu debemasa kewar danginsa amman ayanzu banshirya sanardashiba don banason hargitsa masa rayuwa yakasa karatu da.anfanar rayuwarsa idan kuma bazaki daina ba zan saida gidan mukoma haya kowa ma yahuta don daki salwantarda rayuwa Ahmad gwara na kare rayuwata ahaya har Abada kana jina yanuna jibirilu kaine mijinta banason jin makamanciyar wannan magana a gidan don Allah yaya kayi hakuri wallahi tadaina insha Allah baisaurareshiba yakalli deeje yace maza wuce mutafi duk sanda yakuma sanardake irin wannan maganar datafito daga bakin Lami kisanar dani nikuma za.aga hukunci dazanyi wlh suka wuce suka fice Lami tabisuda harara tanafadin aikin banza ko kunya bayaji mace tasakoshi agaba yazo yana jaraba kaikuma takalli mijinta awulakance saiwani rawar jiki kake kana bashi hkr yana kara kumbura to idan ancemasa shege shin karya akayi? Yanada uban tsinanne dan mahaukaciya insha Allahu sainayi Ajalinsu aitsintacciyar mage bata mage yau tundasafe gidan babu dadi gurin samarin gidan dasuka fara mallakar hankalinsu domin tunsafe Ummansu batada lfy
A Iyakacin shekarun Ahmad sha ukku da sani shabiyar da Auwalu shabakwai rabi.u shabiyu sunfahimci nakuda ce takeyi tunsafe yan uwan maman nasu mata keshige da fice anyi su tafi makarntar boko sunkasa zuwa alokacin Auwalu yanada shekar karshe sani yana aji hudu Ahmad yana aji daya hakama Rabi.u dayake kusan tard akemusu komai donsun tashi kamar yanbiyu cankamar daga sama suka farajin kukan jariri suka mimmike a rude suna lekawa amman sun kasa fita sunajiran Abasu izini saida aka kammala gyara uwar dajaririyata sannan akwala musu kira har rige rigen fita sukeyi ganin Umman tasu tana zaune akan filo afalo kamar ba ita ce tahaihu ba tayi kyau sai kamshin turaren wuta ketashi suna shiga ta washe baki cike da farinciki tana dariya inna balkisu kanwar tace tace Albishirinku samarin umma Atare sukace goro inna tayi dariya tanafadin yara saikunbani tunda nayi muku albishir yar budurwa da.aka haifa muku wacce kuke marmari amakota sasuka saka ihu atare saida umma ta kwabesu sannan suka natsu suka dinga amsar yarinyar suna kallo duk wanda ya.amsheta baison baiwa dan uwansa saboda kyan yarinyar Ahmad kam kamar jira yake su fito yakwasa dagudu yayi gurin Abokinsa musa yama manta shaf yana makaranta domin yanaimasa gorin kanne mata shi guda biyu yake dasu Raliya yarsheka shidda da Amina yar shekara ukku kofada suke saiyayi masa gori don haka yaga yashiga da ihunsa ko sallama babu yana fadin musa musa zokaga kanwata nima yau Ummanmu tahaifa mana mace mekyau datafi yan gidanku..... Yatsaya turus cike da tsoro sanda lami tafito daga daki tana muzurai kamar zata cinyeshi danye cikin tace shege meyakawoka gidanmu tsinanne yatsaya jikinsa yana kyarma bakinsa yana rawa yace daman..... Daman um Ummarmu ce tahaifi diya mace shine nazo nagayamasa takara dokamasa tsawa kaitafican banza shege ummanku ko ko ummansu kana murna anhaifi mace agidan wasu ko shashasha da baisan ko shi waye ba shege
3⃣2⃣ fice kabani guri kuma kaje kasanar da uwar rikon naka inci ubanka shege yajuya yafice dasauri jikinsa yana rawa yana jujjuya maganganunta aransa yakasa fahimtar abinda take nufi sukaci karo da musa azaure yakalleshh yana fadin Ashe ummanku tahaifi mace yanzu rabi.u yake gayamin Awaje yadaure yayi yar dariya ainashiga nagayama banganka ba dokin yarbudurwa yamantardashi Abinda innar musa tayi masa Ranar da hjy Amina tazo barka ranar kwana biyar da haihuwa sanda zata tafi mlm sulaiman yashigo dakayan lambu masu yawan gaske dayake sana.arshi kenan suyake saidawa kasuwar yankaba shagone dashi babba yasamya akadibarmata mai yawa tace yabarshi yace saita tafi dashi saidai motar haya tazo gidan domin motarta tana wurin gyara Ahmad yadaukar mata kayan yakaimata bakin titi suna tafe suna hirar makarantarsu dasauran Abubuwa saiyace mata Anti daman inason Intambayeki wani abu tatattara hankalinta agurinsa tace masa Uhum inajinka yagyara kayan dake kansa yace wai meye shege da Uwar riko kuma? Hjy Amina taja wani wawan birki tatsaya cike datashin hankali tace kai waye yake gayama wannan maganar badai ummar kaba ko ganin tarude yanda ummansa tayi idan yasanar mata yasanya gabanshi faduwa dan Allah kada kigayawa ummana zatamini fada daman Innarsu musa ce take gayamini kuma canake wani abune mai Amfani shine nake tambaya tayi ajiyar zuciya don zatonta deeje kefada masa haka tace lallai ta cika munafuka tunda take nuna batason kowa yanuna masa ba itace tahaifeshi ba amman duk da haka har lokacin ranta abace yake ta daure tace Agaban ummarka take gayamaka haka kuma yagirgiza kai yana fadin a.a saidai idan nashiga gidanta kuma ummana ma tahanani shiga ranar suna yarinya taci suna Asma.u sunan da deeje kenacin idantahaifi mace asanya mata saboda kaunarta ga mahaukaciya babar Ahmad tun washe garin suna tafara kiranta da ma'u kwanakinsu goma da haihuwa Hjy Amina tayomusu Asubanci sundan tsorata daganinta dasassafe amman ganin tanata wasa da dariya dayara yasanya suka fahimci ba wani abu ne yafaruba saida yaran suka wuce makaranta sannan suka kule adaki aka kara gaisawa suka nutsu sunajiran abinda ketafe da ita tagyara zama tace tabbas kunzama iyaye nagari masu rikon Amana kuma kuncancanci kuyi rainon kowane irin da banzo amatsayin shugabar gidan rainon yara ba domin nayi ritaya saidai nazo amatsayin inakaunarku dason danku Ahmad inafatar idan nafadamuku dalilin dayasa nakeson amsarsa bazaku bata rankuba tunda tafara magana suke kallonta jintazo wannan gaba yasanya deeje mikewa tana fadin tafdi jam ai wlh bazai yiwu ba koshugaban kasa bai isa ya.amshi Ahmad ahannunaba clkin matukar tashin hankali da kuka take maganar shikanshi malam din yakadu dayake namijine yasanya yadanyi karfin hali
Yakwantar da kai yanafadin Adokar daukar yara agidan daman tanuna akwai wani lokaci da ake karbar yaro daga iyayen rainonsa ba.asanar damuba ko kuma rainonmu kikaraina kinaganin kinfimu iya raino hajiya takula dayanda suka shiga Rudu daman kuma tayi tunani haka zata faru dantasan yanda suke matukar son yaron takwantarda murya tana fadin kufahimci kamar yadda nasar da ku banzo da sunanan ma.aikaciya ba saidai yar uwa agurinku Ahmad bashida iyayen dasuka fiku saidai inason na rikeshi nawani lokacine har zuwa sanda zai iya daukar kowacce irin magana akwakwalwasa nasan kun san halin matar can Lami kumasha jin irin rigimar da kuke yi da ita akan yaron to abinnata yakiyin sauki donhaka mezaihana kubani aronsa haryagama Karatunsa na University insha Allah sannan nadawomuku dashi gabadaya suka sauka daga kan fushin nasu dansunsan inda maganarta tasanya gaba donhaka sungano magana tafimtar juna takawota mlm yace shin wani abune yafaru takwashe duk yanda sukayi da Ahmad tasanar dasu sanda zai rakata tahau mota sai deeje tasanya kuka tana fadin Ahaf ainasha gayawa mlm maganar nan matarnan batada mutunci wlh bazan yadda ba Hajiya kiyi hakuri wlh bazan iya rabuwa da Ahmad ba sai inmutuwa ce tarabamu kifahimci Abinda nake nufi Deeje bawai zankwacemiki Ahmad bane dawata manufa hjy Amina tafada da lallashi ganin yanda duk Deejan tabirkice mata mlm ne ya raba gardamar dafadin ke hajiya kiyi hakuri dan wlh rabamu da Ahmad babbar matsalane sannan hakan ma zai iya tona Asirin dakike son Rufewa indai lami ce matsala to zanyi maganinta ayau ba sai gobe ba dakyar suka shawo kanta ta amince zata barshi amman dole tace taza yiwa Lami kashedi da barazana don haka tare suka shiga gidan Lami da ita lami tamike jiki yana rawa tashimfida musu tabarma dan Allah yayita datsoron Hukuma tasan tsaf za.a iya daureta hajiya ce tafara magana cikin bacin rai kinfi kowa sanin laifinki bawai rarrashinki nazo yi ko rokon kiba a.a umurni ne nake baki abinda kikayiwa yaron nan yasarnar damu cikin rawar murya tace wai menayi mlm sulaiman ya yunkura da bacin rai zaiyi magana hajiya Amina datakatar dashi takalli lami tana fadin Kinmance sanda yashigo gayawa abonkinsa musa haihuwa abinda kikace to zakiyi bayani agaban hukuma tunda tunaninki rashin mutunci saita mike tsaye Hankali jibirilu yatashi yamike dasauri yana fadin a.ah hajiya baza.ayi hakaba tabbas tayi kuskure ayimata afuwa dan Allah yaya kasanya baki Lami kuwa tuni tafashe dakuka tagigice mlm sulaiman yayi dariya aransa yana fadin fitsarar riyar banza saida suka wanasu sannan tayadda tajanye sanarda hukumar yansanda wannan tasanya tadaina kiran Ahmad da shege koda sunhadu ahanya bata kyarar sa saidan harara kawai gabaki daya yaran sundauki soyayyar su sundora kan ma.u shekarunta biyar akasanxata aprimary saidai kullum sai dai kullum sai anyi dambe da ita kamar dage yawanfadan dasukeyi da raliya yasanya ummansu tayimasa kashedi akanta don kullum
Dan kullum Lami ahanyar kawo kara take tayita zage zage da gore gore kalala dole tasanya yadaina kulasu Rayuwa yin Allah ayanzu haka Ahmad yana BUK takano inda yake karatunsa akan computar science Sani kam diploma yayi anan FCE sai yayi sa.a yasamu yasamu aiki awani kamfani maizaman kansa shikuwa Auwalu makarantar aiki tsafta yayi HND yabude chemist anan jikin gidansu yakuma samu aiki a temprary rabi u kam yanbokone nahakika ma.u kam ana aji daya a secondary school saikara firirita ake da iyayi da gwalli tafi kowa kokari a ajinsu gaba daya kai harma acikin tsaran ajinta itace kedaukar na daya wannan yake karamata soyuwa awurin yayyanta kafin ummansu ko babanta yayimata abu daya sunmata goma dominshi idan yatashi saiya hada dasu Raliya danhaka tafisu komai Raliya datake ganin itace budurwa dayadace tayi kwalliya sai taga ma.u tafita dawani yammaci lokacin ma.u tadawo hutu domin makarantar kwana take tataso daga islamiyya tana rike da kur.ani tahango lariya taci kwalliya tanufi shagon sisko wani dangayene a Unguwartasu da inmace kekulasu ake ganinta mara kamunkai dan haka tanaganin Raliya tashiga shagon sisko jikinta yadauki rawa hankalinta baikara tashiba saida taga saida ta hango sisko yadan leko yakalli gabas da yamma sannan yaja kofar shagon nasa dasauri ya kulle tayi dum dum cike da tsoro da fargaba tayi hanyar gidansu dasauri tasanarwa da yayyanta tayi sa.a ta tadda Ahmad da musa akofar gida zaune suna hira jikinta yana rawa idonta nazubda hawaye tanufesu Ahmad ne ya farga da ita yakalleta da mamaki yana fadin yadai ma.un baba lfy cikin rawar murya tace Raliya Raliya ce tashiga dakin sisko suka mike atare arude suna fadin Raliya zomuje saidai wani Abin bakinciki sanda suka isa kofar shagon suka hango cincirindon mutane ashe wani saurayi yaga sanda tashiga darufe kofar da akayi ya gayyato wasu matasa aka balle kofar dakyar suka barta tadaura zani suna mata ihu suka fito da ita tanufi hanyar gida tana kuka shikuwa sisko rufeshi sukayi da duka Ahmad da musa suka isowurin cike da bacinrai tundaga nan suka zare belt dinsu suka fara narkarta tana ihu tanufi gida da gudu Ahmad yarufamata baya shiko musa takaici ya isheshi yaga garayaje yakoyawa sisko hankali tashiga gidansu dagudu tana ihu daga itasai daurin kirji yankayanta data dauko duk tawatsar dan zafi duka yabita hargidan nasu yana dukanta tana ihu lami tafito daga daki arude tana fadin meyene yake faruwa tatsaya turus ganin Ahmad nadukan Raliya har cikin gida wata zuciya ta ciyota ta isa dasauri
3⃣5⃣ ta angajeshi tana fadin shege dan iska mediyata tayimaka dazaka biyota kana dukanta tamike cike damamakin ganin diyar tata daga ita sai daurin kirjg Ahmad yamike yataso daga cikin kwanikan wanke wanke data hankadashi yana karkade jikinsa ya isa kusa da ita yana fadin inna wannan yarinyar yau ta tona asirin gidannan ta tozartamu ashagon sisko aka kamata yara suka rakota suna mata ihu meyafi wannan takaici da tozarta sunan gidannan yakarasa maganar da kunan rai Lami takalleshi cike da wani irin bakin ciki data kasa rikewa tace Ahayye yaufa karin maganar hausawa tafito SHEGE YANA YI DAMAI ZINA don ankama Raliya ashagon sisko zaka biyota kana mata wannan dukan kaine kafi cancanta da adaka ba Raliya ba Shege irinka ne zaitonawa maiyin zina asiri cikin tada jijiyar wuya take magana musa dayashigo bakomai ahannunsa ya isa cike da bacin rai dadamuwa ganin yanda Ahmad ya tsaya sororo yana kallonta cike da madaukakin mamaki donshi sam baifahimci tana daurewa diyarta gindi ne akan abin da ta.aikata musa ne yace haba inna baidace kidaurewa yarinyar nan gindiba har kidinga ciwa Ahmad mutunci ba kai rufemin baki da.ace kai ko Auwalu ko sani suka kamo yarimyar nan dawani banzan damuba tunda ku kowa yasan "ya"yan halak ne ba shegu ba amman wannan yaron shege ne zai aibata diyar da akahaifa tahanyar Auren sunna ta Nuna Ahmad gaba daya suka tsaya suna kallonta cike da fargaba tashin Hankali musa yafara magana cikin kaduwa da gigita inna kazafi baida kyau kada tunanin nemawa Raliya kariya yasanya kifita daga haiyyacinki harkije ki fadi abinda baidaceba ninasan Ahmad dan gidan baffa sulaiman ne kuma...... Kai tafi can toyau zanfasa kwan da.akajima ana kiwonsa yau zansanarda kai abinda bakusaniba saunawa nake gayamuku kudaina damuwa dan Ahmad yafiku wani abu kasha damuwa danyafika kokari kasha damuwa danyafika kaya nasha gayamaka duk dayafika aikin banza ne tunda ku kunada abin ado wato uba shikuwa shege ne dan mahaukaciya wacce ba.asan daga inda ta fitoba ........ Innalillahiwainna ilaihi rajuun lahaula walakuwati illah billah muryan Ummansu Deeje ta ankardasu wacce ta shigon gidan gigice jiyo hayaniyar da akeyi taleko taga abinda ke faruwa Ahmad kam mutuwar tsaye yayi yakasa motsawa daga inda yake tabbas yasha tunanin maganganu Lami dake fada akansa Ummansa da Hjy Amina suna tauye masa tunaninsa wannan ne yasanya hankalinsa ketashi aduk sanda sukaji ance masa shege faduwar da Ummansa tayi jib dafasa ihun ma.u ne yadawo dashi cikin hayyacinsa
Yanufeta da gudu kamar yanda yaga musa yayi idonta yabirkice yajuye da alama banumfashi a tattare da ita cikin karaji ma.u kefadin umma kada kimutu kibarmu dan Allah Umma kitashi shikam gaba daya tunaninsa da basirar sa suntushe yakasa cewa komai sai hawaye da idonsa keyi musa ne yamike dagudu yadebo ruwa abuta ya yayyafa mata amman abanza bata ko motsi sai asannan ya iya bude baki yana fadin Umma kada kimutu kece Uwata maisona idan kika mutu zankasance banida kowa kitashi Umma kici gaba darikeni a matsayanin danki na cikinki kada ki mutu Umma na yana kuka da majina yake wannan magana musa ne yayi dabara fita dagudu yanufi gurin Auwalu dake chemist wanda bai san wainar da ake toyawaba Lami kam tayi tsuru tsuru tsaye da fargabar da tashin hankalin abinda zaije yazo Raliya kam sai sharbar kuka take yi cike da takaici da dana sani Auwalu yashigo aguje hannunsa rike da fanfon auna jini ya isa gurin mahaifiyar tasa yahada bakinsa danata yafara bata taimakon gaggawa da ake kira da mouth to mouth yatallafo kanta cikin ikon Allah saiga numfashin nata yadawo tabude idonta dasauri saita mike zaune kamar ba itace tasuma ba yanzu takamo Ahmad tana fadin karya take nice nahaifeka ba mahaukaciya ba ranar dana haifeka ne tazo nan gidan katambayi malam kaji ainasha gayamaka Lami makaryaciyace tana kuka take maganar shima Ahmad kuka yakeyi Auwalu da baisan abinda ke faruwa ba yamike cike da mamaki yana fadin wai meye yafaru me yasameki Umma? Arude yake maganar saita mike cikin karfin hali tana fadin babu komai kuzo muje gida banason kara kallon fuskar Azzalumar matarnan tanuna Lami da hannunta Ahmad yarirriketa dakafarsa suka nufi gidansu harlokacin musa Ahmad da ma.u kuka suke Lami ji take yi kamar maganar tadawo tamaidata cikin ta donbatasan abinda zaibiyo baya ba amman saboda tsabar taurin rai saida taga sunfice eh gaskiya ce nafada sai dai Akasheni wallahi haka kawai shege zaitonawa diyata Asiri yanda yatona m
ini asiri nima natona masa
3⃣7⃣ koda suka iso gidan abin datake maimaitawa kenan Auwalu yace Umma mema tacene? Meyafaru ne? Cikin kuka tace Azzalumace Lami waicewa tayi Ahmad shege ne bayan nice nahaifeshi da cikina cewa tayi dan mahaukaciyane bayan gashi dana ne ranar dana haifeshi ranar mahaukaciya tazo nan gidan bari kuganima na dauko muku takaddar dazaku san danane saita mike jiki yana rawa takama lalube saidai abinda batasaniba shaidar datake son kare ta itace zata kara sanyawa abin yafito fili tunda duk mutumin dayakasance danka dakahaifa aibabu bukatar wata shaidar takarda arubuce gashi ita batasan abinda akarubuta na yarjejeniya bace baiwar Allah saida tafito dakayan wata tsohuwar adaka sannan takwakulo wata takarda acan kasan jikinta yana rawa tamikama Ahmad tana fadin karanta kagani karya takeyi nice babarka ya.amsa yafara karantawa bawani abu Acikiba illah yarjejeni sun amsheshi zasu rikeshi kuma duma duplicate ce aka basu da.alamu original din tana can inda suka basu shi kukansa yakuma karuwa hankalinsa yakuma tashi tabbas ba sune iyayensa ba Auwalu ya warce takardar yafara karantowa yakalli mahaifiyar tasu datausayi datashin hankali rashin ilimi datayine yasanya batasan Abinda takardar takunsa ba data sani data kara boye takardar cikin sheshshekar kuka yake fadin Umma wannan takardar tana nuna yarjejeniya dakukayi ne asanda zaku amshi wani yaro nasan ba Ahmad bane mantawa kikayi kika fito da ita sai asannan tagano wautar datayi amman taji dadin yanda Auwalu din yakawo mata mafita dasauri tace ahaf namanta wannan ajiya ce akabani bari nazakulo wancan bani na adana wannan din kafin masu ita suzo nema ta.amsa dasauri tanufi akwatin tana cigaba dalalube tsanananin tausayin dasoyaryar Ummansu tashigeshi yakula da idan baiyi wani abuba zata iya rasa hankalinta ko wani yashigeta yanufeta inda take tazakulo kaya daga cikin tsohuwar adakar yadafa bayanta yana kokarin kwantar mata da hankali yace Umma kidaina lalube nifa nasan kece mahaifiyata bakece kikasha gayamin innarsu musa karya ne da ita ba tayaya zanyadda damaganarta dake ba uwataba ce ba saikin nunamini watarana dakuma saiwani yayi mini gori acikin layin nan kishare maganarta ki kwanta ki huta tana son bata miki raine don ankamo diyarta dakin sisko suna iskanci tadago cike da matsananci farinciki tana fadin haba ainasan saboda mugunta take son rabani dakai tahadda samaka wani ciwon dazan rasaka bakayadda da abinda taceba kenan? Yadaga mata kai yana kokarin kakalo murmushi wannan yasanya tadan sami sassauci aranta daga wannan karon anyita takare ko ita ko lami dole dayan yabar gidan dakyar ta iya kyalesu suka tafi masallaci bada farali gani take yi kamar daga can bazata koma ganin Ahmad dinta ba saidai shi yana sallah yana kuka ransa yayi baki ashe shi yanata barankadama da homa ashe shi shege ne bashida kowa aduniya shin wacece mahaifiyarsa datayi shegensa koda yake ance mahaukaciya ce to waye mara imani dayayi mata ciki har kawo shi duniya
3⃣8⃣ tana ina ita mahaukaciyar ta warkene kohar yanzu tana cikin haukan? Yakasa natsuwa daga masallaci yalallaba yafice yayi gabas yana ta tafiya baisan inda zaidosaba Anshirya cin abinci yanda aka saba amman babu Ahmad tun Ummansu nasanya rai zaishigo har tafara karaya bacin rai datake kokarin boyewa yafara yabaiyana tadinga sanyawa ana nemansa sam tahana kowa cin Abinci nan malam yashigo cike da taikaci yana fadin wai Ahmad yaro ne dazaki sanya ayi ta wani nemansa saika ce wanda zaibata kinsa dai bazai wuce yana gidan yaron Abokinsa Abdullahi ba cikin sheshshekar kuka basan abinda nasaniba tabbas idan Ahmad bai bata ba to zaigudu kuwa saita fashe dakuka cikin mamaki yakd kallonta hasken wutar lantarki da.aka kawo yanafadin wace irin magana kike yi khadijatu kamar wacce tayi gamo memukayi masa da zai gujemu cikin kuka tace yau Lami tasanar da Ahmad shi shege ne tasanar da shi banice nahaifeshi ba tagayamasa shidan mahaukaciyane baniba... Kuka take yi sosai kamar wata karamar yarinya malam yamike cikin tashin hankali yana fadin mekikeson sanar dani khadija inanilillahi wainna ilaihi rajuun yanzu ina Ahmadu bari nanemoshi... Baijira yi jin abinda zatace ba ya fice sani da salisu da rabi.u ne agurin sunkuma riga sun fahimci abinda ake anufi saidai harkarfen dayan dare babu Ahmad babu labarinsa hankalin kowa yatashi sanda malam sulaiman yashigo gidan Umma Deeje tamike tana fadin yaya dai malam kungan shi yagirgiza kai cike da damuwa mai tsanani takuma wurga masa tambaya hargidansu Abdullahi mlm kunje munje taredashi muke ta nemansa ma yanzu haka nabarsu shida Auwalu suna ta bin gidajen Abokanansu Akanme zaku wahalarda kanku wanda yabata ake nema bawanda yagudu ba Ahmad bazaije inda zaku ganshi ba abinda najima ina nusar da kai kenan wlh Lami bamasoyiyar mu bace ko Ahmadu yadawo ko baidawoba nagama zama a gidannan yanda Ahmad yatafi haka nima zatasalwantar min yarana tana magana tana kuka ya hasala matuka gaya yama rasa hukunci dazaiyanke sai kawai yamike cikin fushi yanufi gidansu Lami
Yanashiga yakama kwada sallama kamar zaitsaga gidan dafarko sunyi shuru adaki don lami tagayamasa tabargazar dayayi duk da lika abin asharri yayiwa diyarta ammam duk da haka mijin nata yabata rashin gaskiya don yana tsoron abin da zaije yazo can dai sai ga mlm jibiril yabayyana cike da tsoro mlm sulaiman yagalla masu harara yana fadin Barkanku Ahmad yagudu yabace mana yarabu da mu saidai kusani jibril yanda Ahmad yarabu damu tokaima karabu da komai nawa kashirya kayanka agobe zansanya gidan kasuwa tunda dai zamanmu tare baida Amfani sai haddasa masifa nima nahakura dazaman gidan gabadaya hankalin jibril yatashi idan yarabu dan uwansa inazaisoma rayuwarsa waye zai iyaciga dabashi taimakon dayake bashi tabbas shikansa yanzu lami ta isheshi yabi dan

Please Login or Register in order to submit comment