Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya
boye mana sun wuce yadda kake
tunani''. Uche ya mike tsaye ya
ce, ''Ina zuwa. Nan da minti
ashirin zan dawo, ka san bana
ajje kudi a gida... Idan kana
bukatar abin sha ka bude firji
gashi can''. Uche ya fice daga
dakin cikin sauri.
.
''A OFISHIN JAMI'AN TSARO!''
Suka dubi Uche cikin kaduwa.
''Gambo fa ka ce?'' Wani sajan ya
tambaye shi. Uche ya gyada kai
ya ce. ''Kwarai kuwa...yanzu haka
yana dakina... Ni daman ina
ganinsa na gane hotonsa da ku
ka buga a jarida... Ya zo yana yi
min wasu zantuka wai yana son
ya ranci kudi a gurina... Gashi
nan dai shirme kawai.... Shine na
ce bari in zo na sanar da ku...''
Mintuna goma bayan haka, sama
da 'yan sanda goma suka cafke
Gambo. Abin da ya fi batawa
Gambo rai a lokacin shi ne
amanarsa da Uche ya ci.
Jami'an tsaron suka taru jingim!
A 'kofar gidan Uche. Sa'ar da 'yan

Sandan suka fito da Gambo kowa
da bindigogi. Uche ya juya zai
shige gidansa yana murna sa'ar
da ya ga an sa Gambo a cikin
mota. Sai yaji busasshen hannu
ya ratso ta cikin duhun dare ya
dakumi kafadarsa. Wasu tika-tikan 'Yan sanda ne guda
shida 'Me na yi
muku...lafiya?'' Wani sajan ya yi
masa busasshen murmushi ya ce
Lafiya kalau Muje ka nuna
mana dakunanka muna bukatar
bincike a ciki''
''Don me? Uche ya tambaya
zuciyarsa na harbawa Katon
dan sanda ya daga hannu ya
kwadawa Uche mari fau Ya ce
Kada dauki Jami'an tsaro
mahaukata mana Shekara nawa
muna lura da duk wani motsi na
ka...ka ce baka san Gambo ba
amma ai sau uku ke nan muna
ganinsa a gidanka
Uche yaji kamar katanga ce ta
fado masa a baya.
.
Karfe tara da rabi na safe su
Lanto da sauran mukarrabansa
guda biyu suna zaune a gindin
inuwar wani katon rumbu suna
karta sai suka ji sautin injin
mota Nan da nan suka mike
Tani da ke zaune ita da Gudidi a
can gefe guda itama ta dubi
hanyar cikin mamaki
''Shege Lanto ya ce yana dariya
cikin murna ''Ka ga dan iskan
nan ban da kudi ma har da wata
motar ya sake damfaro
Inyamurin can Cab Lallai yau
wayo ya hadu da wayo
CUTA TA DAU CUTA!
.
Kowa bai san kowa
ne ba'' Tun kafin motar ta gama
tsayawa su Lanto suka tari gaban
Landirobar fara mai duhun
gilashi kofofin motar suka
bude Kafin kiftawa da
bismillah! Su Lanto sun yi ido
biyu da hancin bindigogi sama
da guda goma sha biyar. Lanto

ya daga hannu sama cikin
kaduwa.
Wani dogon 'Dansanda ya lalube
bindigoginsu. A dai-dai lokacin
ne to Lanto ya hango Gambo
dumu-dumu a cikin ankwa 'kafa
da hannu. Gambo ya dube shi ya
yi masa murmushi ya ce.
''Sa'armu ta kare Lanto.... Uche
ya bata ruwa ba dan ya sha ba.....
'Kurunkus!....
TA LEKO TA KOMA!!''
Tani ta shige cikin bukkar da
gudu inda Jabir ya ke kwance ta
rungume shi tana kuka tana
cewa. ''Jabir ga su nan sun zo...za
su rabamu Jabir! Na shiga uku!
Jabir ya ya zanyi da rayuwata....''.
Ta fashe da kuka tana girgiza shi.
''Tashi ka dubeni Jabir....duba na
'karshe Jabir!.... Ga 'Yan sanda
nan a waje''. Tani ta dada jijjiga
shi ta kwalar rigar da ke jikinsa
sai taji nauyi. Ta dafa 'kirjinsa....
BABU NUMFASHI!
.
''Jabir''. Ta fashe da kuka.
A dai-dai lokacin ne 'Yansandan
biyar suka shigo cikin bukkar
dauke da makamai. Tani ta
dago kai fuskarta sharkaf da
hawaye jikinta sai rawa yake yi
kamar mazari ta ce da
'Yansandan. ''Ba kwa
bukatarsa....
YA MUTU!!''. Wani
'katon 'Dansanda mai ciki kamar
tudun ganuwa ya matso kusa da
gawar Jabir ya latsa cikin gawar
da tsinin bakin bindigarsa,
sannan ya juyo ya dubi Tani cikin
murmushi ya ce. ''Mutuwarsa tafi
masa sauki!!''.
Tani bata taba jin mummunar
kalma irin wannan ba a
rayuwarta!''.
*
Sidi mai Jaka ya yi doguwar mika
gami da hamma ya dubi tsohon
agogon sa Omega a cikin hasken
farin watan ya ce. ''Zan shiga
gida Nas, lokacin barci na ya yi....

Ina fatan ka gamsu da wannan
labari.... Ka kuma san cewa baka
bata lokacinka a banza ba ko?''.
Na dubeshi cikin kaduwa na ce.
''A'a ai baka gama labarin ba...
Labarin bai kare ba'' Sidi mai
Jaka ya mike tsaye ya ce ''To me
kake son ji kuma NAS?'' Na dube
shi sa'ar da ya mike tsaye na ce
da shi cikin kaguwa. ''To ya ya
kuma maganar cikin da Tani take
da shi?''
LINZAMIN SHAIDAN-16
.
KARSHE
.
''To ya ya kuma maganar cikin da
Tani take da shi?'
.
Sidi mai Jaka ya ce. ''Kai dai Nas
kafi son sai an kai maka labari
har kurun-Kus! Ai kasan dai
'Yansanda sun kame su... Ai labari
ya 'kare. Tani ta koma gidansu a
can kauye ta tarar da mahaifinta,
amma mahaifiyarta ta rasu
sakamakon ciwon hauhawar jini
da ta yi ta fama da shi tun sa'ar
da aka kawo musu labarin cewa
'yan fashi sun dauketa... Bayan
wata shida Tani ta haifi danta na
miji, amma Allah ya yi mata
rasuwa a ya yin haihuwa''.
.
Sidi mai Jaka ya yi shiru yana
dubana. ''Shike nan ko?'' Ya tambayeni
''Da saura Baba'' Na ce da shi
''Ni duk ka kare min labarin cikin
gaggawa..''
''To me kuma kake son ka
sani..
duk zarurrukan labarin
masu dadi sun kare sauran
koda an baka su gundurarka za
su yi...''
''Ya ya kuma labarin Ja'e da
matarsa?''. Na tambaya.
''A'ah! Anan aka barsu suka ci
gaba da rayuwarsu''. Sidi mai
Jaka ya ce lokaci guda kuma ya
fara 'kokarin nade buzunsa.
''A labarin da ka bayar, na ga tun

da aka fara labarin kake bayanin
'yan fashin su biyar ne, akwai
Gambo, Lanto, da kuma Jabir,
amma har ka 'kare ban ji ka
ambaci sunan sauran guda biyun
ba... Kuma labarin da aka bayar a
ina ka sameshi?''.
Sidi mai Jaka ya rungume
buzunsa. ''Kai dai NAS ka cika
tambaya da bin 'kwakkakkwafi!
Kaidai kawai in za ka ji labari ka ji
kawai... Nima wannan mutane
biyu da kake bayani ban san
sunansu ba a haka naji labarin...
.
In kuwa na sami labarin nima na
manta... Na fada ma tun farko
dattijo kamata bai yin karya sai
dai dan karin gishiri dan labari
ya yi dadi... Amma 'karya dai kam
babu zancenta.. domin KARYA..
LINZAMIN SHAIDAN CE.
.
Nas Allah bamu alheri Sidi mai
Jaka ya juya zai shiga gida Baba
Nayi kiransa cikin sauri Na mike
tsaye sannan na lalubi aljihuna
na dauko takardun kudi masu
yawa na mika masa na ce Ka
manta baka karbi kudin
labarinka ba.. Sidi mai Jaka ya
dubeni cikin murmushi ya ce.
''Nas, wasa na ke yi ma.... In
banda abinka tsoho kamata mai
zai yi da kudi masu yawa haka?
Kada ka damu, wata rana in ka
so jin wani labarin, idan za ka
dawo kada ka manta ka taho min
da TUBANI!...''
.
ALHAMDULILLAHI
.
KARSHE.
.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment