Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba...
Amma kuma hakan baya nufin
mun rabu da ke...zan neme ki
idan kin karasa karatunki, duk
inda kike sai na nemeki dan a
duniya bani da kamarki Tani.... Na
san ke kadai kike kaunata a
duniya....kin ga dai kowa ya
tsaneni saboda halina, amma ke
kike sona...''.
.
Ya danyi shiru, sannan sai yace.
''Tani Darling, sai wata rana!''.

Ya juya zai fice daga dakin
karatun. Sai Tani tayi caraf! ta
rike hannunsa tana kuka, tace.
''Jabir....ka yi min rai dan girman
mahaliccinka...wallahi idan ka
gujeni Jabir bazan taba yin aure
ba a duniya....dan kai kadai ka
dace da ni....''
Ta fara kuka wi!wi!!.
''Cool down Tani. Ba gudunki zan
yi ba alkawari ne duk inda nake
ina tare da ke...kin ga Tani
auranki ina kaunarsa a raina,
amma komai yanzu sai da
kudi...to ni bani da su, dama
wannan karatun kadai na
dogara sai gashi yau an koreni....
Ni namiji ne Tani, zan shiga
duniya kafin ki kammala
karatunki, duk inda kudin
auranki yake doron 'kasa sai na
nemoshi...''
Tani ta sake fashewa da kuka. Ta
dago kai da niyyar ta sake
lallashin Jabir, to amma abin da
ta gani a idanunsa shi ya
gargadeta da cewa babu wani
abu da zata ce da Jabir wanda
zai sa yaki barin makarantar.
Dan haka cikin kuka sai ta zare
zoben azurfar da ke hannunta
wanda itama mahaifiyarta ce ta
bata ta kama hannun Jabir tasa
masa zoben.
''Ga..zobe na nan..Jabir..Ka tuna
da ni dan Allah..kullum ina tare
da kai..Ka rike alkawari
Jabir..ni matarka ce in Allah yaso
Ina Nan Ina Jiranka.
INZAMIN SHAIDAN-04
.
Ga....zobena nan....Jabir....Ka tuna
da ni dan Allah.....kullum ina tare
da kai....Ka rike alkawari
Jabir....ni matarka ce in Allah
yaso.... Ina nan ina jiranka Jabir,
komai tsawon lokaci ba zan gaza
ba, har sai ka dawo gareni''.
.
Ta kara fashewa da kuka.
Jabir ya dubeta cikin takaici,
sannan sai yace hawaye na

'kokarin subucewa daga
'kwayar idanunsa.... Bai bari ta
gani ba sai kawai ya juya yana
cewa.
'lNa rike alkawari matata''.
Itace kalma mafi dadi da faranta
zuciya da ta taba ji a rayuwar ta.
A haka suka rabu tana kuka
kamar ranta zai fita.
.
'Ga goro!!''
Wata yarinya ta 'kwalla talla a
zauren gidan.
Sidi mai Jaka ya dubeni. Nayi
mamaki sa'ar da na ga har yanzu
idanunsa da kwalla.
''Nas, kullum yaran nan sai sun
kawo talla gidan nan, sun dauka
ina da mata, basu san ni kadai
nake zaune ba''.
''Basu da tunani ne''. Na ce da shi
ba tare da ni kaina na fahimci
ma'anar abin da nake nufi ba,
domin na matsu ya ci gaba.
''Nas, in dai kana biye da ni a
cikin wannan labari, to ka san ko
ban fada maka ba, tabbas Tani
dole ta shiga matsanancin hali?''.
''Har bayan da ta gama karatu
bata sake kula wani mutum ba
da sunan soyayya. Ga shi dai
kullum sai matsin lamba take
samu daga wurin iyayenta na
'kauye akan ta samo miji, ta
samo miji, abin ya ci tura. Domin
sam a kullum Tani gani take
kamar Jabir zai dawo ma ta,
amma gashi wasa-wasa yau
shekara biyu babu shi babu
alamarsa.
A wannan yammaci ne to da
nake baka labari Tani ta tashi
daga aiki, tana 'kokarin tsallaka
titi domin zuwa kasuwa sayen
wasu kayan masarufi katsam! Sai
taji ance.
''Tani na dawo''.
Ta juya firgigit! Zuciyarta kamar
zata fasa 'kirjinta, domin ko kafin
ta juya ma tasan duk duniya
babu mai wannan muryar sai JABIR. !
.

''Jabir ruhina!'' ''Jabir....wayyo!
Allah, ban gaskata idanuwa na
ba''.
Tani tace a rikice, ''Nine Tani.... Ai
nace miki alkawari ne sai na
dawo gareki...''.
''Masoyan biyu suka yi shiru na
dan lokaci suna duban juna
kowa na kokarin ganin sauyin
fuskar dan uwansa bayan
rabuwa. Jabir dai yayi matukar
kaduwa da ganin irin yadda Tani
ta dada kyau da kwarjini, gashi
kuma ta mulmule ta dada kiba
sai 'kyalli take.
A bangaran Tani kuwa, tana
duban Jabir sai taji zuciyarta ta
rubza, domin kai da ganin
kodaddiyar kwat dinsa mai
kamar dasta kasan yana cikin
mawuyacin hali. Haka nan kuma
takalmin dake 'kafarsa a yanzu
tun zamanin zamansu a
makaranta ta san shi da takalmin.
A da takalmin na cinyewane
gurin 'yan matan jami'a, amma a
yanzu da Tani ta dubi takalmin
sai taji cikinta ya murda, domin
yaso yayi kama da rubabben
danyen nama.
.
''Ai sai mu shiga ciki ko.... Gida na
yana ciki...'' Tani ta nuna 'kofar
asibitin da hannunta.
''A nan kike aiki ne?''. Tani tayi
murmushi tana duban
kodaddan takalminsa mai
kamar kwale-kwale. ''A nan nake
aiki, gidana kuma yana ciki... Ni
kadai ce aciki'. Jabir ya dubi
agogon hannunsa. ''To kije zan
shigo na same ki nan da awa daya... Yanzu ina sauri akwai
wani (meeting) da zamu yi,
amma ki jira ni zan shigo nan da
'karfe biyar...''
Murmushin dake fuskarta ya
subuce. ''Haba Tani, ba guduwa
zanyi ba....ki tuna fa ni na fara yi
miki magana baki ganni ba''.
Tani ta sake jifansa da irin
murmushin nan da rabon daya
ga irinsa tun suna jami'a. ''To

shikkenan Jabir, idan kazo sai ka
zagaya can bayan asibitin,
gidajen suna daga can ciki. Nawa
shine mai lamba (28)''
''To sai na zo''. Jabir yace da ita.
.
Tana nan tsaye ya hau dan acaba. Haka nan bata motsa ba
har sai daya bace, sannan tayi
ajiyar zuciya ta juya a hankali ta
koma asibitin zaman jira, domin
tuni ta manta ma da cewa
kasuwa zata sayayya. A kwai
wani yanayi a fuskarta wanda
rabon da aga irinsa a fuskar tun
farkon haduwarsu da Jabir....''.
.
Sidi mai Jaka yai atishawa gami
da hamdala. ''Idan baka manta
ba Nas dazu na baro ka ne a inda
Tani take zaune a lambun
gidanta, inda har nake cewa me ma?''
Ya tambaye ni.
''In babu ji to akwai jimami''. Na
bashi amsa. ''Da kyau Nas, ashe
dai duk kana fahimtar
zarurrukan labarina ba bata
lokaci nake ba...''
''To zaman da take yi yanzu cikin
wannan dan madaidaicin lambu
dake gidan, Jabir take jira. Tuni
har ta fara tsammanin ma bazai
zo ba, dan haka ga mamakinta
sai taji hawaye ya fara zuba.
''Hello Darling''. Akace da ita daga baya.
Tani ta juya firgigit!.
'Oh! Jabir na dauka baza ka zo
ba''. Jabir ya dubi adon data caba
bayan rabuwarsu dazun nan.
''Lallai har yanzu tana sonsa''.
Yace a cikin zuciyarsa.
''Gani kuwa na zo''.
Ya janyo wata farar kujera dake
gindin bishiyar goba zai zauna.
Sai Tani tace. Haba Jabir zo kusa da ni ka
zauna mana'' Ta matsa masa kan
bencin ya zauna Duk da yake
jikin Jabir har wari yake yi....
Amma Tani ji take yi warin kamar wani
turare ne mai sabon salo na kamshi
Suka yi shiru na tsawon lokaci
suna duban juna sannan kuma
hadari yana kallon rana tuni har

ya fara dakushe hasken ranar
yammacin Tani ta kama
hannunsa ta dora akan cinyarta
cikin farin ciki tace
''Jabir a yau zuciyata tafi nono
fari Tunda ka cika alkawari ka
dawo gareni gashi kuma ga
dukkan alamu har yanzu ina
ranka dan ga zobena har yanzu
a dan yatsanka..duk kuwa da
cewa yau shekara biyu ke nan
rabona da kai''
Jabir ya dubeta cikin farin ciki
yace
''Tani a kullum kwanan duniya
bani da wani buri da ya wuce
auranki..'' Tani ta katse shi
''Daman maganar da nake son ji
ke nan daga bakinka Jabir
domin wallahi iyayena dake gida
sun takuramin (last week) ma da
naje kauyen gaishe da su baka
ga irin fadan da suka yi min ba
to amma ni ban ga laifinsu ba
domin kasan gulmace-gulmacen
kauye wai har cewa akeyi sun daure min gindi na dawo birni
ina zaman karuwanci na ki yin
aure zan tsufa a haka. Wai dan
kudin da nake kai musu idan
naje ganin gida duk a karuwanci
nake samu. To kaji fa wannan
abu Jabir, amma duk da haka na
dake, domin a kullum ina ji a
jikina cewa Jabir sai ka dawo
gareni, to gashi ka dawo... Ya
maganar auren mu?''. Jabir yaji
kamar an kwara masa ruwan
sanyi a baya sa'ar da Tani tayi
shiru tana dubansa. Hannunta
ri'ke da dan yatsansa mai
zobenta. A dan takin dakika
sai zuciyarsa ta dawo masa da
hoton sa'ar da take sa masa
zoben alkawarin a dakin karatu
a zamanin zamansu na jami'a.
''Tani masoyiyata....'' Jabir yace a
sanyaye.
Akwai wani irin yanayi dake
fuskarsa da ya fara bata tsoro,
dan ta fahimci tun zuwansa
lambun kamar in tana magana
ba saurarenta yake yi ba haka dai

yanayinsa kamar wanda ke
yawan tunanin wani abu.
''Tani... Sanin kanki ne ina
'kaunarki, matukar 'kauna, tun
da nake ban taba soyayya ba
akan wata 'ya mace sai ke.... Ina
son nayi miki albishir da cewa na
sha wuya bayan rabuwarmu
dake duk akan neman yadda zan
sami damar da zan aureki a
mutunce ba a tsiyace ba, amma
ban samu ba.... To amma nan da
awa ashirin da hudu zan samo
wannan damar...''
Tani ta dubeshi cikin damuwa
tace a sanyaye. ''Haba Jabir, kada
ka takurawa rayuwarka a
kaina.....daga yau wahalarka ta kare, kayi farin ciki ya mallakina,
domin a yanzu haka ina da kudi
masu yawan gaske dana ajje
maka a banki, tunda na fara aiki
nake tarawa, kuma kasan
albashinmu na likitoci yana da
tsoka, dan haka in kana so yanzu
ma mu shiga cikin daki na baka
cek din kaje ka karbo duk naka
ne masoyina...''
Ta danyi shiru tana dubansa
cikin farin ciki, sannan sai ta
dada cewa.
''Kayi amfani da kudin gurin
al'amarin aurenmu''.
Jabir ya dubeta cikin mamaki,
idanunsa cike da dumbin kauna
yace.
''Nagode Tani sahibata, na yaba
da kokarinki... Amma kudinki
naki ne, ki ajje kayanki dan ba
zan karba ba, nafi son na aureki
da gumi na, idan na karbi
kudinki na zama mata maza kenan''
''Haba Jabir ai ba haka bane...''
Jabir ya girgiza kansa, sannan ya
rankwafa kusa da ita yace.
''Irin yadda nake sonki Tani, so
nake ayi bikin da ba a taba irinsa
ba a duk 'kasar nan.... Kuma ina
tabbatar miki da cewa gobe war
haka ina da kudin da zan maida
wannan mafarki naki gaskiya, shi
yasa nace dake ki ajje kudinki,
domin duk da dai ban san

adadinsu ba ni nasan basu fi na
shan askirin ba a ranar bikinmu
da ke...''
.
A dai-dai lokacin ne hadarin
yammacin ya taso. Nan da nan
lambun ya game da iska kamar
zai dauke su sama.
Zuciyar Tani cike take da tunani
da fargaban rashin fahimtar
bayaninsa, ta kankameshi
lokacin da taji iskar ta fara
kadawa kamar zata dauketa.
''Hadari Jabir mu shiga daga
ciki''.
Numfashin Jabir ya dauke sa'ar
da yaji tattausan jikin Tani a
jikinsa, don haka maimakon ya
saketa sai ya 'kara matseta gam a
jikinsa. Da haka suka ratsa a
hankali ta cikin iskar da shukeshuken furannin dake ta rangaji
suka shige dakin.
.
''Nas wannan shine kuskure na farko..... Allah ya rabamu da
sharrin shaidan...''
Sidi mai Jaka yace da ni. Nace
''Amin''
Sannan yaci gaba.
''Lokacin da suka shiga dakin
Tani bata tsayar da su a falon ba
sai ta wuce da su zuwa dakin
kwananta suna zuwa sai suka
fada kan gado har yanzu
rungume suke da juna..''
''Allah raba mu da sharrin shaidan''
Sidi mai Jaka yace
Ni kuma na sake cewa ''Ameen''
''Hankulansu suka gushe
shaidan yayi amfani da tsantsar kaunar dake tsakaninsu ya
shagaltar da su suka manta da
Ubangiji musamman ma ita Tani
wacce har ta.
INZAMIN SHAIDAN-05
.
Shaidan yayi amfani da tsantsar
kaunar dake tsakaninsu ya
shagaltar da su suka manta da
Ubangiji musamman ma ita Tani
wacce har ta gama jami'a bata
taba taba namiji ba balantana
wani abu ya shiga tsakani amma

a wannan ranar sai shedan ya
shammacesu yasa su akan
mummunar hanyar da daga
karshe ta barsu cikin nadama.
.
Karfe shida na yammar suka
dawo cikin hankulansu Tani ta
fashe da kuka tana cewa.
''Jabir.....na...shiga uku....ya ya
muka yi haka...?''
Jabir ya gyara rigarsa bai iya
hada idanu da ita ba sai yace
''Sai goben''
A haka ya fice daga dakin ana
iskar
Tani ta sake fashewa da kuka
tana cewa ''Yau ya zanyi da
kaina? na tsani kaina na shiga
uku
Bata gushe ba tana cikin wannan
hali har aka fara tsuga uban
ruwan saman kamar da bakin
kwarya Feshin ruwa ya fara
zubowa akan fuskarta ta tagar
dakin shi yasa ta tashi zaune
gaban rigarta ya jike sharkaf da
hawaye da kuma feshin ruwa
Zuciyarta na bugawa ta dubi
agogon dake manne a jikin
bangon dakin karfe goma
saura kadan. Ita kanta bata san
abin da ya rudesu suka yi
wannan masha'a ba. Shin
Kauna ce ?
Yaudarar kai ce ?
Sha'awa ce ?
Sakaci ne ?
Ko kuwa rabon
wahala ne ?
Tambayar ke nan
data dorawa kanta. Bata sami
amsar ko daya ba sai ta sake
fashewa da kuka. A dai-dai
lokacin ne taji talfon din dake
kan dan karamin teburin da ke
fuskantar gadon daga arewa ya
dauki ruri.
''Wanene kuma wannan?''
Ta tambayi kanta. Da farko ta
dauka Jabir ne ya bugo mata
wayar daga wani wurin. Nan da
nan ta mike zumbur! daga kan

gadon ta nufi teburin a hankali
kamar mai zaben danyan kwai,
sai ta dauki talfon din tace.
''Hello....Jab....''
Aka katseta daga can bangaren
da cewa. ''Tani, ni ce Asabe...''.
.
Sidi mai Jaka ya dubi fuskata
yace. ''Yanzu kam na san ka fara
yadda da cewa lallai da na iya
rubutu to da ba 'karamin
marubuci za a yi ba ko?''
Nace da shi ''Tabbas haka ne''.
''Nas kaga fa yadda sannu a
hankali nake harhada maka
zarurrukan labarina ina kulla
maka su guri guda kamar gizogizo to bari na karasa kulla
maka wannan zaren''.
Na ce da shi ''To''.
Yaci gaba ina saurrare.
.
''Nas, Allah ya halicci Tani da zafin
nama, dan a cikin 'yan mintuna
ta gama shiryawa ta suturta kan
ta cikin kayan ruwa bakake na
leda, sannan ta fito cikin
gaggawa, domin in har ana sabo
to ta saba da irin wannan
gaggawa na dare... Tunanin abin
da ya afku tsakaninsu da Jabir
shi ya mantar da ita cewa zafa a
iya bugo mata waya daga asibiti.
Lokacin da ta shigo cikin ruwan
da kyar take tafiya saboda
karfin ruwan da kuma iska,
amma bata damu ba domin abin
da suka aikata da Jabir ya gama
busar da zuciyar ta. To amma
duk da haka sanda aka buga
wata uwar aradu gami da
walkiya sai taji tana mai ina ma
ace Jabir na nan kusa da ita ya
dan tallafeta. Lokacin da ta
karaso cikin (Emergency room)
din tayi mamaki domin ga al'ada
tun daga 'kofa zata jiyo surutun
Asabe da Peter suna ta musu, to
amma yau taji tsit!.
Tani ta shigo dogon falon ruwa
na diga a jikinta, sannan ne to
itama Allah ya nuna mata masu

fuskar katakon.
.
''Shigo daga ciki likita... Kada ki
bata mana lokaci, so muke ki ceci
dan uwanmu cikin daren nan.....
Alburusan bindiga ne a cinyarsa
zaki cire.... Ki kuma tabbata bai
mutu ba, domin yana da matukar
muhimmanci a
garemu''.
Tani tayi turus! Cikin kaduwa
tana kallon yanayin da ake ciki.
Mutanen hudu suka zira mata
idanu kamar mayu.
Tani ta dada matsawa cikin dakin
jikinta na rawa. Kallo daya ta
yiwa fuskar Asabe wacce ke
tsaye kan marar lafiya ita da
Peter ta tabbata ba lafiya. Haka
nan kana kallon fuskar mutanen
tafi kama da fuskar abin tsoro a
cikin mummunan mafarki.
''Malama matsa mana ko so kike
ya mutu!?''. Farin saurayin dake
cikinsu ya buga mata tsawa.
''Amma fa kun san fa bamu
karbar mutum sai an zo da 'yan
sanda....Kuma....''
Tayi shiru lokacin da taga
dukkaninsu sun zaro bindigogi
kamar budar ido.
''Kiyi masa aiki muka ce! In kuma
kika sake ya mutu kina wannan
yangar to kwanakinki sun
kare....''.
Cikin rawar jiki Tani ta matsa
zuwa kan gadon. Asabe da Peter
suka dare suka bata guri ba tare
da dukkaninsu sun dubi juna ba.
Tani ta dubi mutumin dake
lullube da farin mayafi yana
gurnani.
''Kun tsaida jinin?''.
Tani ta tambaye su, kafin Asabe
ta bada amsa sai mutumin ya
motsa da jikinsa kadan sai
hannunsa na hagu ya fito.
Sannan ne to Tani taji kamar an
caka mata wuka a 'kirji. Tani tayi
lau zata fadi, daya daga cikin
mutanen yayi sauri ya riketa
gami da girgizata, sannan sai ya

kwada mata mari tas!.
''Dan ubanki baki taba ganin
marar ladiya ba ne?! Idan fa ya
mutu wallahi kashe ki zamu yi''.
Tani ta hadiye ihun dake
makogwaronta Marin da yayi
mata shi ya hanata sumewa
Hawaye na zuba ta kama hannun
mutumin dake kwance ta sake
dubawa domin ta dada
tabbatarwa abin da ta gani a
hannun
''Na shiga uku''
Tani tace a sanyaye idanunta
kamar zasu fado Ko shakka ba
ta yi a makale a dan yatsan
hannun dake rike da shi zoben
da ta bai JABIR NE!
Hannunta na rawa ta yaye farin
kyallen da ke fuskar mutumin
Duk da yake yayi badda bami da
gashin baki haka nan bai hanata
gane fuskar JABIR abin begenta
ba
A karo na farko tun sa'ar da Sidi
mai Jaka ya fara labarin sai ya
dubeni ya bushe da dariya yace
''Na bada kai ko? Ka ce da baza
ka saurareni ba sauri kake yi
Nayi wa tsohon murmushi
sannan nace Kai gaskiya an
bada ni dan ban ta6a tsammanin
Jabir ne mutumin da aka kawo
asibiti ba
Sidi mai Jaka ya sake fashewa da
dariya ''To Nas in banda abinka
da ka san Jabir din ne? Ba sai da
aka koma daga baya aka sako
maka zaren labarin ka san shi
ba?''
''Haka ne Baba'' nace da shi.
''Yaya kuma Tani tayi?''.
Sidi mai Jaka ya dubeni ya ce.
''Nan inda na tsaya shine
'karshen wannan zaren labarin,
dan haka dole mu ajje shi gefe
guda har sai shima mun sa'ka
masa wani zaren sannan mu
had'asu guri guda mu 'kulla, sai
kaga mun ci gaba da tafiya a
kai''.
''To amma Baba ai da zan so in ji

yadda Tani tayi da ta fahimci
cewa Jafar d'inta ne''.
''Da sannu a hankali zaka ji,
amma dole ne yanzu ka bini mu
sa'ko wani sabon zaren kamar
yadda nace ma baya kafin mu
'kullasu..... In ban da abin ka da
ba raina ni ma kayi ba''.
''To ina saurarenka''.
''Yauwa Nas, haka nake so da
kai... Ga wani sabon zaren nan
to.... Ina son yanzu ka manta da
zancen Tani ka bani aron
zuciyarka na mai da ita can
tsakiyar birni shekara daya da
rabi bayan an kori Jabir daga
makaranta....''.
''Na baka aron zuciyar''. Nace da
shi.
.
YACI GABA
Liyafa ake yi a wani tangamemen
gida 'kerarre. Gidan 'katon gaske
ne, domin farfajiyar gidan idan
ka dubeta da kyau zaka ga ako
da yaushe a shirye take ta
had'iye taron ido guda.... To
amma sa6anin hakan a wannan
yammacin misalin shida da rabi
dai-dai. Wasu 'yan tsurarun
mutane ne a ciki suna watayawa
abin su, domin su kad'ai suka
cancanci gaiyata a wannan
asirtacciyar liyafa ta bogi.
Zaka yi mamakin jin duk da
wannan kururuwar dana yiwa
wannan liyafa na kirata bogi, to
ba wani abu bane yasa na kirata
haka ba sai dan duk kusan
wad'anda aka gaiyata a gurin
duk 'yan bogin ne.
Wannan 'kerarran gida sabo fil
ne ba a ko ta6a shiga cikinsa ba
sai yau. A ha'ki'kanin gaskiya
wani baban 6arawo ne ko kuma
idan har zan saye maka zancen
in ce da kai wani maciyin
kasuwar dare ne ya ci riba mai
yawan gaske, dan haka sai ya
'kera wannan gida, sannan ya
nemi wata zu'ke'kiyar budurwa
ya aura. To wannan liyafar da ake

yi tsuntsu biyu aka jefa da dutse
guda. Wato liyafar shagalin
bikinsa ce gami da kuma bikin
bud'e wannan 'kerarren gida,
wanda rabon da ganinsa me
yiwuwa sai ko a cikin fina-finan
mutanan 'kasar Sin.
Duk inda ka duba a tsakar gidan
fulawoyi ne da furanni birjik
suna 'kamshi, farfajiyar an
lullu6eta tsaf da irin koriyar
ciyawwar alfarmar nan mai
taushi da a turai ake kira da
(Grass Carpet) banda wannan
kuma an fitar da hanyoyi sirara
wad'anda aka da6e su da dutsen
alfarma mai she'kin d'auke idanu
da sa ka manta cewa a cikin
'kasarka kake.
Wad'annan siraran hanyoyi su
zaka yi ta bi su kuwa suna yawo
da kai ko ina a cikin farfajiyar
gidan domin kawai ka kashe
'kwar'kwatar idanun ka.
Gwanayen ginin wannan gida
basu bar gefen wannan 'yar
siririyar hanya ba har sai da suka
tabbatar da sun 'kawata gefenta
da wasu irin fitilu na alfarma
masu hasken tsiya kamar rana,
haka nan 'karafunan da aka yi
wannan fitilu da su duk na gwal
ne da narkakkiyar azurfa, sauran
ginin gidan kuwa ko makaho ya
laluba ya san ginin dutse da
dutse ne, ba na bulo ba. Ha'ki'ka
gidan kam sai dai ko mahadi ka
ture.
Mafi yawa daga wad'anda suka
halarci wannan liyafa duk 'yan
kasuwar dare ne, sai 'yan d'aid'aikun mutane da aka gaiyata
wad'anda a ya yin da suka ga
tsaruwar gidan sai suka fara
tunanin kai lallai wane
kasuwanci ya yi kyau.
Liyafa tayi liyafa, tuni har an fara
tand'e-tand'e da lashe-lashe, duk
inda ka duba sai kaga mutane
akan tattausar koriyar ciyawar
sun shinfid'a dadduma, gabansu
kuma kayan sha da ci ne iri

daban-daban suna ta cusawa
bakunansu suna santi.
.
To amma duk da wannan
sharholiya da ake yi, a can wani
6angare daga cikin ginin gidan,
wasu mutane ne guda hud'u tare
da mai gidan suna tattaunawa.
Mutanen a cikin wani 'katon falo
suke wanda ke dauke da
tagwayen kofofi na gilashi
wannan shi ya basu damar ganin
duk abubuwan da ke faruwa a
farfajiyar gidan domin kofar
daman farfajiyar gidan take kallo.
Mai gidan ya mi'ke tsaye a
hankali ya dubi mutanen biyar da
ke lullume a cikin kujerun
alfarmar da suka yiwa d'akin
kawanya...
July 13 at 8
INZAMIN SHAIDAN-06
.
Mai gidan ya mike tsaye a
hankali ya dubi mutanen biyar da
ke lullume a cikin kujerun
alfarmar da suka yiwa dakin
kawanya ya nuna daya daga
cikinsu yace
''Wannan fa? Mutumin da ya
nuna a cikinsu ba wani bako
bane a gareka Nas Jabir ne!
.
''Jabir?'' Na maimaita sunan ina
duban Sidi mai Jaka
''kwarai kuwa.. Ai labarin da na
ke baka in zaka iya tunawa a
baya na ce da kai shekara daya
da rabi ne bayan an koreshi daga
makaranata ka ga wata shida ke
nan kafin su sake haduwa da
Tani a wancan tsohon zaren
labarin da muka ajiye''
''Haka ne'' Nace da shi
''To sa'ar da Jabir ya dawo gida
da zummar tun da yanzu an kore
shi daga makaranta bari ya koma
harkarsa wacce ya saba don
haka sai ya dada kutsawa
neman abota da manya-manyan
miyagun abokai Amma duk da
haka dai babu wani abin zo ku

gani da ya tara domin daman
yan sace-sacen unguwa ne da
ire-iren 'kananun damfara domin
har izuwa wannan lokaci babu
wani daga cikin mutanensa da ya
ta6a bada kwarin gwiwar a
shiga fashi. A haka suka yi ta
zama har zuwa shekara daya da
rabi, asara goma da shirin ga
Jabir domin gashi dai ya bar
makaranta a shekararsa ta
'karshe. Haka nan da yake
mafarkin mallaka ma kanshi
auren wacce yace tafi kowa a
duniya shi ne ya gagara, dan
haka adai-dai lokacin da ya fara
tunanin lokacin fa ya 'kare masa,
domin yasan tuni TANI ta dade
da gama karatu, don haka dole
ne ya san nayi.
A ranar da wannan tunani ya zo
kansa ne to aka gaiyaci abokansa
guda hudu zuwa liyafar.
.
''Wani tsohon abokin mu ne
wallahi..... Amma kaji kuwa yadda
ya yi bala'in (hitting)... Kai wallahi
ya dace, ka shirya mu tafi Jabir
duk da yake dai bai gaiyata da
kai ba, amma zan so ace ka
ganshi, domin sa'ar da muka
had'u da shi kai kana can
makaranta kana 6atawa kanka
lokaci a banza''.
'Daya daga cikin abokan Jabir
d'in ne ke cewa da shi haka.
.
''Wannan wane ne?''.
Sai d'aya daga cikinsu yace.
''Abokin mu ne wannan... Mun
dade da shima duk da joni ne...''.
Mutumin ya saki fuskarsa sannan
yace da su. ''To ku fita mu zagaya
in nuna muku fasalin gidan''.
Kusan mintuna arba'in da biyar
suka yi yana ta zazzagawa da su.
Zuciyar Jabir cike da tunanetunane barkatai, domin duk inda
aka zo a cikin gidan idan ya ga ya
birgeshi sai ya fara tunanin
inama ace wannan nasa ne shi
da abar 'kaunarsa TANI, domin

shi a tunaninsa wannan
'kayataccen gida da aka nuna
musu duk duniya babu wanda ya
dace da shi sai masoyiyarsa TANI.
Bayan an tashi daga liyafar ne
Maigidan ya tara dukkan
wad'anda suka halarta yai musu
godiya, sannan sai ya rako
manyan abokansa har zuwa
'kofar gida. Suna zuwa sai
abokanansa hud'u gami da Jabir
suka ga wata mota bakikirin
tana sheki 'kirar ''HONDA'' ta
tsaya gaban mai gidan yayi
'kasa-'kasa da muryarsa yace.
''Ku shiga a kaiku gida....na gode,
kuma daga yanzu duk sa'ar da
kuke neman taimako to kuna iya
samuna.... Ni kam na tsallake
saura ku.... Sai ku dage''. Mutanan
hud'u suka shiga gidan gaba,
wani direba fari fat da shi mai
siffar buzaye yaja motar suka tafi
suna dagawa juna hannu har
suka bar farfajiyar gidan. Lokacin
da direban motar ya ajjesu a
majalisarsu, sai ya bud'e bayan
hondar ya d'auko 'yar
madaidaiciyar akwati, ya dubi
babban cikinsu sai ya mi'ka masa
akwatin ya ce. ''Alhaji ne ya ce a
baku''. A haka yaja motarsa ya
barsu baki bud'e cikin mamaki.
To amma sa'ar da suka kad'aice
a d'akin d'aya daga cikinsu sai
suka tarar akwatin cike take da
'yar murtala-murtala sababbi
kakar! Har naira dubu
hamsim.
.
Zancen banza ke nan!
Wai zaki ya taka wuka.... Wannan
matsiyacin ya rasa abin da zai
bamu sai dubu hamsin? Uban
dubu hamsin!''.
Mutanen uku gami da Jabir suka
yi shiru na d'an lokaci suna
sauraron mai bambamin fad'an.
Me yiwuwa su baza su iya surutu
bane....babu mamaki kuma
kad'uwar ganin 'kan'kantar
kud'in ce ta sa su yin shiru kamar

ruwa ya cinye su.
Jabir ya dubi kud'in da ke
gabansu, sannan ya dubi d'akin
da suke zaune, 'katon d'aki ne
wanda rashin kayan al'ada na
d'akin ya da d'a sa shi fad'i,
domin in ka d'auke gado d'aya
jal d'in dake d'akin, gami da
tsofaffin kujerun katakon da
suke zaune akai d'akin ba komai
sai tarin yanar gizo-gizo daga
can saman rufin d'akin. A can
gefe guda kuma tarin tsofaffin
kwalayen taba ne tsibi guda.
Domin a kullum kwanan duniya
ba a sha ba a shanye sama da
kwali biyar.
.
''Kai wallahi.... wannan d'an
banzan ya yi bala'in raina mana
hankali ma....!''. Jabir ya muskuta,
sannan ya dubi abokan nasa uku
da ke zaune, biyu sunyi tagumi
d'aya na bambamin fad'a, ya yi
murmushi sannan ya ce.
'Kai Gambo, kada kasa jininka
hauhawa a banza gado in ba na
uwarka ba ne idan aka baka
allura ai sai ka gode Allah... In
banda abinka ina kai ina fada
dan an bamu dubu hamsin?
Karenmu ne ya kama? Shekarar
mu nawa yau muna shirye amma
har yanzu bamu tana samun
dubu hamsin a dunkule ba''
Jabir yayi shiru haka nan sauran
mutanen uku suka yi shiru kowa
na nazarin abin da Jabir ya ce
domin sun san duk abin da Jabir
ya fada gaskiya ne.. Haka nan
maganar tasa tamkar zagi ne a
garesu gami da Allah wadai da
lalaci irin na su'
Sidi mai Jaka yayi shiru yana
dubana
''Nas lallai gaskiya ne wato ko a
cikin mutane akwai shaidani''
''Gaskiya ne'' Nace da shi
Cikin rudewa, domin har yanzu
labarin da yake yi ni a fahimtata
bashi da wata alaka da wancan
labarin da ya baro a baya domin

wan can duk ya fi wannan dadi
Sidi mai Jaka ya yi murmushin
yake yace ''Na san daman nan
gurin (Nas) dole ne labarin ya
gundure ka domin duk cikin
labarin nan ya fi ko ina
gundurarwa da rashin dadi to
amma in har za ka bini a hankali
Nas da sannu zan harhada maka
shi guri guda na dauki bakin
zaren labarin mu hada da
wancan da muka baro a baya mu
'kulle''
''Haka ne'' Na ce da shi
Sidi mai Jaka yaci gaba.
.
''Tsawon lokaci samarin hudu na zaune
suna duban kudin duk ransu a
bace kai ka ce kullin kashi suke
kallo
Gambo ne ya fara bata shirun
''To kunji abin da Jabir ya ce dole
ne mu nemo inda matattun
zuciyoyinmu suke mu farkar da
su domin ni irin wadannan 'yan
sace-sacen sun isheni lokaci yayi
da ya kamata mu huta''
Aka sake yin shiru a dakin.
A wannan karon Jabir ne ya dubi
Gambo yace ''To ai mu kai muke
sauraro.. Kawo mana mafita tun
da dai na fuskanci yau duk kafi
kowa kumfar baki'' Jabir yayi
shiru yana murmushi. Gambo ya
yi kamar bai ji abin da ya ce ba.
Amma can sai ya nisa ya ce.
''Hanya daya ce mafita''.
Mutanen uku suka dubi juna
lokaci guda cikin mamaki.
''Mene ne mafitar?'' Biyu daga
cikinsu suka tambaya. Gambo ya
sunkuyar da kai kasa tsawon
lokaci yana duban 'kasa, sannan
sai ya dago kansa ya ce. ''Muma
sai mun bi hanyar da ya bi''.
Sauran suka fashe da dariya jin
abin da yace, domin duk sun
dauki abin shirme.
Gambo ya dubesu a fusace.
''Menene kuma na dariya? Uban
wa kuka tambaya mafita? Bani
ku ka...'' Jabir ya katse shi.

''Zubawa ranka ruwa ka kwantar
da hankalinka, ko ma fahimci
juna. Gayu ne

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment