Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hana shi fita da
akwatin.
''Ka kula da kyau!''. Itace kalma ta

'karshe da Gambo ya fada masa.
Daga nan sai ya juya a guje,
sauran suka bishi a baya kamar
tunkiya da 'ya'yanta, cikinsu ya
gama durar ruwa.
.
Tsawon mintuna biyu Jabir na
tsaye cikin duhun dakin yana
sauraren guje-guje da harbeharben iska na jami'an tsaron da
suka shigo gidan. Daga inda Jabir
ke tsaye yana iya hangen
farfajiyar da ke bayan gidan ta
cikin gilashin tagar dakin. Ya
kuwa yi imanin babu wanda ya
isa ya hango shi, wannan shi
yasa ya kashe kwan lantarkin da
ke dakin.
Tun a karon farko da Jabir yaji
'karar harbin bindigar ya gama
tunanin hanyar da zai bi ya tsere.
Jabir ya riga ya gama fahimtar
gidan, ya san cewa yana fita ta
cikin tagar dakin tafiya kadan
zai yi a farfajiyar gidan ya riski
inda rumfar injin bada wutar
lantarkin gidan take, ya san cewa
rumfar injin bada wutar a jingine
take da katangar gidan, wanda
hakan ya dada kara masa
'kwarin gwiwa domin yasan
rumfar zata taimaka masa
matuka wajen haura katangar.
To amma abin da yafi damunsa a
yanzu shi ne dan tattakin da zai
yi a farfajiyar gidan kafin ya kai
ga katangar.
Jabir yasan abu ne mai sauki
'yan sanda su hange shi, domin
duk ilahirin farfajiyar gidan a
haske take da 'kwayayen lantarki
kamar rana. To amma dole ne
yayi kasadar wucewa domin
itace kawai mafita. Sai dai kuma
kafin ya haura katangar dakin
zuwa waje yana bukatar lekawa
ya tabbatar babu wani jami'in
tsaron da ke labe yana jiransa.
Jabir yaci gaba da leken waje ta
tagar dakin, lokaci guda kuma
yana tunanin hanyar da su
Gambo za su bi su tsere''. ''Su

suka jiyo!''. Jabir yace a ransa.
Sannan ga mamakinsa sai ya
nemi kansa yana mai addu'ar
Allah sa ma a kamasu shi kuwa
ya tsere.
''Ta6! Da yau ya baiwa
masoyiyarsa Tani mamaki. Har
yanzu tana 'kaunata''. Yaci gaba
da tunani. ''Gaskiya duk abin da
zan yiwa Tani ban biyata ba''.
Jabir yaji gabansa ya fadi sa'ar
da ya tuna alfashar da ta shiga
tsakaninsa da masoyiyarsa Tani a
yammacin ranar. ''Tsautsayi ne!.
Yace da kansa. ''Hakika tsautsayi
ne...da kuma shaidan.... To amma
dai daga wannan ba za su 'kara
ba har sai idan sunyi aure. Yau
dai zata faru ta kare. Kudi dai ga
su an sami na auren Tani....saura
fita da kudin. Hakika fita da
kudin nan shi ne rayuwata....''.
.
Wadannan guntattakin tunani
masu kama da kururuwar
shaidan su suka yi tasiri a
zuciyar Jabir, suka kuma karfafa
masa gwiwa. Jabir ya jingina
jakar da ke hannunsa, a nan sai
wani murmushin bazata ya
subuce masa, sannan sai ya ce da
kansa.
''...LALLAI RANAR AURENA DA TANI ZA'A YI TA'BARA!!''.
.
Jabir ya sake lekawa. Hakika a
yanzu ya tabbata babu kowa a
bayan gidan.
''Me yiwuwa jami'an tsaron can
farfajiyar kofar gidan suka tsare,
wasu kuma su shigo su binciki
abin da ke faruwa.
Domin karfin gwiwar da Jabir ke
samu a ransa shi neLINZAMIN SHAIDAN-10
.
Domin 'karfin gwiwar da Jabir ke
samu a ransa shi ne, ya tabbata
jami'an tsaron lalube kawai suke
a cikin duhu tun da dai harbin
bindiga kawai suka ji a gidan ba
su da yakinin abin da ke faruwa.
Jabir ya bude katuwar tagar
gilashin ta alfarma wacce tuni

daman ya san yadda ake budeta
ba tare da ta bada wani
'kwakkwaran sauti ba, wannan
kuwa tun sa'ar da attajirin ya
gaiyace su liyafar bude gidan ne
Jabir ya koyi hakan.
Sai da ya shafe minti guda tsaye
yana sauraro kamar ungulu,
sannan zuciyarsa na bugawa sai
ya yi shahada ya zura 'kafarsa ta
hagu, sannan ta dama. Akwatin
rike kam-kam a hannunsa ya
haura katangar ya dirga a
farfajiyar da ke bayan gidan ba
tare da yayi wani 'kwakkwaran
motsi ba. Jabir na dirga sai ya
nufi saitin inda injin bada wutar
yake. Ba gudu yake yi ba, haka
nan shi kuma ba a hankali yake
tafiya ba, zuciyarsa na bugawa ya
nufi gindin injin domin a
kowanne lokaci tsammani yake
zai ji harbi ko kuma kuwwa a
bayansa. To amma sa'ar da ya kai
ga gindin injin bai ji komai ba a
bayansa, Jabir yaji wata
sassanyar iska mai dauke da
'kamshin turbaya ta daki
fuskarsa, ya daga kansa sama
sai yaga ashe hadari ne
bakikkirin a sararin samaniya.
.
Tunanin Tani ya sake mamayar
zuciyarsa. Yanzu haka tana can
tana barci, domin ya san abin da
suka aikata a yammacin ranar bai
barin zuciyarta da wuri.
Jabir yaji numfashinsa ya dauke
saboda abin da ya gani. A jingine
a jikin rumfar injin wani dogon
tsani ne. Jikinsa na bari ya ajje
akwatin a jikin katangar, sannan
ya dauko tsanin ya jingina a jikin
bangon. Cikin sauri ya dauki
akwatin sannan ya juya ya yiwa
farfajiyar kallo daya. Sannan ya
hau tsanin cikin sauri ya nufi
saman katangar.
Jabir yayi tsaye na 'yan dakiku
yana nazarin bayan gidan. Kamar
yadda yayi tsammani babu kowa
a bayan gidan domin gidan da ke

fuskantar bayan wannan gida
wani 'katon kango ne an zagaye
shi da katanga, sai kuma wata
'katuwar kwata mai fadin gaske
wacce duk kusan ko ina a rufe
yake da tubalin siminti.
Jabir yayi ajiyar zuciya, sannan
har zai dirga sai ya ga kuma ai
bai dace ba ya bar tsanin jingine
a jikin bango, domin duk dan
sandan da ya kawo ga gindin
katangar na iya fahimtar abin da
ke faruwa cikin sauri, wanda
hakan na iya sa dandazon 'yan
sanda su tuso shi a gaba.
Jabir bai shiryawa hakan ba dan
haka sai ya zura 'kafarsa ta dama
da niyyar wai ya ture tsanin ya
fadi kasa. Ashe tsautsayi ne ke
jiransa. Abu biyu suka faru ga
Jabir kusan lokaci guda. Na farko
yaji kamar kwarankwatsa ta
fado masa a kan cinya, yayin da
alburushin bindiga sama da
guda biyar suka farfasa cinyarsa,
sannan kuma sai sautin harbin
bindigar da ya gauraye daren.
''Ah.... Tani....!''. Jabir ya 'kwalla
'kara gami da kiran sunan
masoyiyarsa Tani, sa'ar da yaji
wani irin ciwo da bai taba jin
irinsa ba ya soki cinyarsa. Nan da
nan ya rikito daga katangar ya
fado bayan gidan. Jabir bai fado
kasa ba sai da ya wuce kai tsaye
cikin katuwar kwatar ta cikin
wani gurbin tubali da ma'aikatan
share muhalli suka cire a
yammacin ranar domin share
kwatar.
Jabir ya fada akan tarin takardu
da ciyayi na shekara da shekaru
dake cikin kwatar babu shara.
Haka nan sun hana ruwa bi ta
ciki, wannan shi ya rage 'karfin
faduwar da Jabir yayi. Ya daga
kansa cikin firgici ya duba saman
katangar, ya san da wuya, 'yan
sanda suyi tsammanin sun same
shi. Har yanzu akwatin na nan
makale a hannunsa daraf kamar
mayen 'karfe!.

Jabir ya shafi cinyarsa yaji tuni
har ta jike da jini. ''Na shiga
uku... Tani sabo da....ke na ke
wannan....'' Jabir ya ce muryarsa
a shake. A dai-dai lokacin ne to
Jabir ya fahimci ashe in ka dauke
dai-dai inda ya fado duk kwatar
a rufe take da tubalin siminti.
Nan da nan yayi ta 'yan maza ya
fara jan ciki, ya nufi cikin kwatar.
Jabir ya san in dai har sa'a tana
tare da shi in da rabon ya sake
ganin masoyiyarsa Tani babu
abin da zai hana shi bullewa a
dai-dai inda suka baro direbansu
yana jiransu.
Loakcin da Jabir yayi tafiya mai
nisa a cikin kwatar, sai yaji
numfashinsa ya fara daukewa
kamar zai suma. Abin da ya fi
damunsa shine jinin da ke zuba a
jikinsa, ga kuma nauyin akwatin
Sa'ilin ne dabarar boye akwatin a
magudanar ruwan ta fado
masa....
.
A can cikin duhun dare a jikin
wata 'katuwar katangar waya da
ta zagaye wani lalataccen lambu,
su Gambo ne zazzaune a cikin
jibgegiyar motar 'kirar
Landiroba. Zai yi wuya wani mai
wucewa a 'kasa ko a cikin mota
ya iya ganewa cewa akwai
mutane a cikin motar. Duk kusan
gine-ginen da ke gurin
kangwaye ne ba'a 'karasa
gininsu ba. Hakan shi ya basu
damar boye motar a bayan wani
tsohon kango, wanda daga inda
suke suna iya hangen bakin titi.
Wannan dabarar Gambo ne ya
kawo ta ya ce da su su bar
mutum daya a cikin motar
domin koda za ta baci dasun zo
sai tafiya.
To sai dai a halin da ake ciki a
yanzu basa bukatar waccan
tsohuwar shawarar ta gudu,
domin akwai abin da suke jira.
Gambo ya muskuta a bayan
motar, ya dubi sauran mutanen

uku, biyu a kusa da shi, sai kuma
direbansu a gaban mota. Gambo
ya lura da cewa duk sun yi
mutuwar tsohuwa, numfashi ma
da 'kyar suke shaka, sun yi
zugum kamar gumaka. Hannun
direbansu akan dan mukullin
motar. Gambo ya dada
musgutawa ya ce da sauran a
tsorace.
''Ina jin harbin da suka yi sun
sami Jabir''.
Mutanen uku suka dubeshi
kamar kurame. Basu ce da shi
komai ba sai hadiyar yawu suke
yi suna huci kamar macizai. ''Mu
bashi 'karin mintuna biyar idan
bamu ganshi ba sai mu wuce''.
Hakan da ya ce ya sa daya daga
cikin mutanen magana a karo na
farko. ''Amma kuwa da mun yi
aikin banza..... Ya babu kudi, ga
asarar ran dan uwanmu Jabir,
ga kuma laifi....?''.
''Ka cika shirmen banza....!
Gambo ya ce da shi a fusace. ''In
banda shirmen ka wa ya san
cewa mu muka yi fashin?''. A ka
sake yin shiru a cikin motar,
kowa na sakar zuci. Wani na
tunanin me yiyuwa fa rayuwarsu
ta zo 'karshe ke nan, domin da
zarar an kama su to kwanansu
ya 'kare ke nan. Wani kuwa
tunani yake yi da bakin cikin
asarar da suka yi, domin yana
kyautata tsammanin Jabir ya
shiga hannu idan kuwa haka ta
tabbata sun yi sallama da samun
kudi ke nan. Ya zargi kansa da
wautar da ya yi, domin a dai-dai
lokacin da suke 'kokarin tserewa
daga gidan ya so ya cika
aljihunsa kafin su fita, amma
tsoro ya hana shi.
Mintuna hudu suka wuce kamar
wasa. Mutanen hudu zaune cikin
duhun motar suna ta ta sukusuku kamar kaji a akurki.
Wani 'kwa'k'kwaran motsi a daf
da su ya sa su zabura lokaci guda
kowa hannunsa ya kai kan

bindigarsa. ''Kamar motsi nake
ji''. Wani daga cikinsu mai suna
LANTO ya ce a tsorace yana
jujjuya bindigarsa da ke
hannunsa kamar yar tsana.
''Ba kai kadai kaji ba...!''. Gambo
ya ce da shi a fusace, amma cikin
rada.
.
Gambo ya lura da fuskar Lanto ya
ga a bala'in tsure ya ke. Ya yi
mamaki in har Lanto zai iya harbi
da bindigar da ke hannunsa idan
bukatar hakan ta tashi. Direban
ya kai hannu zai tashi motar
jikinsa na rawa. Gambo ya
yunkuro daga bayan motar cikin
zafin nama ya buge hannunsa.
''Ka da kayi gaggawar tashin
motar ka tona mana asiri. Wa ya
sani ma ko Jabir din ne?''.
.
''Motsin daga cikin 'katuwar
kwatar can ne....''. Lanto ya ce
bakinsa na rawa. Tsawon
da'ki'ku babu wanda ke iya koda
numfashi a cikin motar
ballantana wani 'kwa'k'kwaran
motsi. Idanunsu na 'kokarin
hango abin da ke motsi a cikin
'katon kwatamin ta cikin duhun
daren ne. Sannu a hankali sai
suka hango kan mutum ya dago,
sannan sai gangar jiki da 'kyarda-'kyar mutumin da ke cikin
kwatamin ya janyo ciki ya fito
bakin ramin yayi 'ko'karin ci
gaba da jan ciki, amma hakan ya
gagara. Nan da nan ya kife rub
da ciki baya ko motsi kamar ya
mutu.
.
''Jabir ne!''. Gambo ya ce da su
cikin doki. Nan da nan ya bude
bayan motar a hankali bindigarsa
a hannunsa, sannan ya nufi inda
Jabir yake kwance. lanto ya biyo
shi a baya. Suna zuwa basu bata
lokaci ba sai suka ciccibeshi suka
tafi da shi cikin motar.
.
''Wayyo 'kafata!''

Jabir ya ce
muryarsa cikin rada, domin in ba
dan Gambo ya tallabi kansa ba da
ba zai taba jin abin da yake fadi
ba. Tun kafin su isa ga motar
suka kwantar da Jabir a bayan
motar. ''Anyi ba a yi ba!''. Gambo
ya ce yana duban Lanto. ''Me
kenan?''. Lanto ya tambaya.
''Babu jakar kudin....''. Gambo ya
ce lokaci guda kuma ya yi shiru
yana duban 'katon kwatamin da
suka dauko Jabir. ''Zo muje mu
gani''. Lanto ya bishi a baya babu
kalma, domin ya fahimci abin da
Gambo ya ke nufi. Sun dade
suna birkita takardun da ke
kwatamin amma ba su ga komai
ba sai guma guman duwatsu.
Cikin sauri suka koma gindin
motar. Jabir na kwance a bayan
motar yana faman kakari.
Mutanen uku suka yi tsaye a
kansa suna jiran su ji abin da
shugabansu Gambo zai zartar.
''ina mafita ke nan?''. Gambo ya
tambayesu. ''Mu 'karasa shi
kawai mu bar gurin nan! Domin
duk da'ki'ka daya cikin hadari
muke.LINZAMIN SHAIDAN-11
.
''Ina mafita ke nan?''
Gambo ya
tambayesu ''Mu 'karasa shi
kawai mu bar gurin nan Domin
duk dakika daya cikin hadari
muke kara shiga'' Lanto ne ke
bada shawarar
Gambo ya yi kamar bai ji abin da
Lanto ke fadi ba Maimakon ya
dubeshi sai ya rankwafa ya kara
bakinsa kusa da kan Jabir ya ce
''A ina ka baro kudin ?''
Shiru Jabir bai motsa ba Gambo
ya sake maimaita tambayar har
sau uku shiru! A fusace sai ya
kama kwalar rigar Jabir ya
girgiza shi da karfi ''Ah! kafata!!'' Jabir ya 'kwalla kara...
Amma kuwwar ihun ta ratsa
shirun da ke dare ne... Lokaci
guda kuma aka saki wata
'kwakkwarar aradu, sararin

samaniya ya haske da walkiya,
''A ina kudin suke?'' Gambo ya
tambaya a fusace yana kara
girgiza Jabir''.
''Na....bo....ye....su''. Da 'kyar da
kara kunnensa a bakin Jabir
Gambo ya fahimci abin da yake
cewa. ''A ina ka boye su...'' Ya
tambaye shi gami da dada
girgiza shi
Amma ina! Jabir bai sake motsi
ba, ya suma. Gambo ya ja da
baya sauran suka ja da baya
sannan Gambo ya rufe bayan
motar ya ce. ''Ku mu bar gurin...
Ina tsammanin 'yan sandan can
sun jiyo ihun'' Da gudu-gudu
suka shige cikin motar. Tun kafin
su gama zaunawa sosai har
direban ya fisgi motar a guje.
Koda suka fara tafiya sai Lanto ya
dubi Gambo ya ce ''Yanzu mene
ne mafita?''. Gambo ya dubi
fuskar Lanto tayi sharkaf da gumi
ya ce. ''Asibiti zamu nema...a
duba mana shi...a dawo da shi
hankalinsa, in ba haka ba munyi
sallama da kudin ke nan.... Dole
ne ko ta ya ya, ko ta halin kaka
sai ya fada mana inda ya boye
kudin...''. Gambo ya yi shiru yana
sauraren sautin 'kananan
'kwayoyin ruwan da ya fara
wanke saman motar. Nan da nan
sai wani murmushi ya subuce masa.
''Wannan ruwan saman alamun
nasara ne.. Fatan mu daya shi ne
Allah ya sa kada dan iskan nan
ya mace ba tare da ya fada mana
inda ya boye kudin nan ba...''.
''Rabon Gambo da addu'a NAS,
tun yana 'karami dan shekara uku''. Sidi mai Jaka ya ce da
ni.
Sidi mai Jaka ya yi shiru a karo na
farko tun sa'ar da ya fara zuraro
min labari kamar saukar ruwan
sama. Kusan mintunansa ashirin
yana zuba baya ko
'kwakkwaran numfashi.
''Nas, wannan shine 'karshen
wannan zaren labari mai tsayin
tsiya. Gashi ba wani ma dadi ne

da shi ba, domin kusan kowa ne
ke son zaren labari mai tsayi da
kuma yawan harbe-harbe da
doke-doke ba''. Sidi mai Jaka ya
yi gyatsa 'kyat! Kamar an shake kwad'o.
''Ka gafarce ni Nas''. Sidi mai Jaka
ya ce yana gwaggwale idanu
kamar kuturu.
''Wani lokaci haka nake fama da
irin wannan doguwar gyatsa
idan na ci TUBANI!''.
Allah ya sauwake''. Na ce da shi
cikin kaguwa da ya ci gaba da labarin.
''Na so a ce ka ci Tubanin nan
Nas, dan ba ka san irin dadinsa
ba ne shi ya sa ka barni na cinye...''.
''Wata rana ai zan ci..''. Na ce da
shi, ina tunanin yadda za'a yi na
iya hadiyar Tubanin nan. To ya
ya aka yi kuma bayan sun tafi da
Jabir d'in?''
Sidi mai Jaka ya dubeni cikin
mamaki sa'ar da yaji tambayar.
''A'ah, kada kace da ni ba ka
fahimci labarin ba... Ai 'karshen
zaren labarin ke nan.... Inban da
abinka a wancan tsohon zaren
labarin da muka bari sai da na
baka labarin zuwansu asibiti da
kuma duk abin da ya faru har
zuwa sa'ar da Tani ta gane masoyinta...''
''Haka ne na ce da shi ina murmushin fahimta.
Yauwa Nas,
ko kai fa? To irin wannan
zarurrukan labari su ake kullawa
guri guda su baka labari... In ka
fahimci zaren labari to shi ke nan
in kuwa ka sake daya daga cikin
zarurrukan ya subuce maka to
rikicewa zakayi''.
''Wannan gaskiya ne''. Na ce da
shi. To ya ya akayi da Tani ta
gane cewa masoyinta ne Jabir?''.
Sidi mai Jaka ya yi tari sa'annan
ya daga kai sama yana duban
dan saurayin farin watan da ya
fara haske sararin samaniyar Subhana.
''Wannan ka yi babbar tambaya
Nas.... Domin wannan zarurrukan
labarin guda biyu da zan 'kulla
maka a yanzu sune bangare na
takaici da kuma karyar da zuciya

a duk cikin labarin da na baka a
baya''.
''Ai kuwa takaici ya gama faruwa
tun da dai a inda muka tsaya a
wancan zaren labarin da wuya
idan masoyin Tani Jabir zai kai
labari''.
Sidi mai Jaka ya fashe da wata
busashiyar dariya. ''Kai kuwa ka
cika azarbabi Nas, in banda
abinka wane irin takaici ma ta
gani a yanzu ai labarin da saura
ka dai bari in jona maka wannan
zarurrukan guda biyu daga nan
sai mu ajiye su guri guda mu
dauki sabon zare''
''Zarurruka nawa suka rage
mana a yanzu?'' Na tambayi Sidi
mai Jaka
''Baza su wuce uku ko hudu
ba... Ina tsammanin kafin nan da
'karfe tara na dare zan sake
maka su na hade su duk su
zama daya'' Sidi mai Jaka na
gama fadin haka sai ya gyara
zama ya ci gaba
''Nas ina son ka dauki zuciyarka can-cak!
Ka maida ita can
'karshen wancan tsohon zaren
labarin da muka saka kafin wannan..
In zaka tuna mun tsaya
ne a inda Tani ta gane Jabir da
zoben da ke hannunsa..?''
''Haka ne''. Na ce da shi cikin gaggawa.
''Da kyau Nas"
''Sa'ar da Tani ta gane cewar
lallai marar lafiyar da ke kwance
yana ihu a gabanta ba wani bane
sai Jabir, sai duk 'kwakwalwarta
ta rikice.
''Na shiga uku na lalace! Jabir!!!....''
Mutanen hudu suka dubi juna.
Gambo ya dubi Lanto, sannan
Lanto kuma ya dubi Gambo cikin
kaduwa. Gambo ya matsa kusa
da Tani a gaban gadon asibitin
da Jabir ke kwance ya cakumi
gashin kanta da karfi ya girgizata ya ce.
''Dan ubanki wa ya ce da ke
sunansa Jabir?''. Tani ta fara
shesshekar kuka a firgice.
Sauran Malaman asibitin na can

gefe duk a kidime. Peter sai
zazzaro idanu yake yi kamar ta
matar kwado. Ya yin da Asabe
kuma ke jin kamar zata yi aman
kayan cikinta saboda tsabar
tsurewa.
''A...ina kika san shi.... Eye!!?''.
Gambo ya sake maimaita
tambayar cikin ihu, domin sautin
zubar ruwa sama bai barin aji
abin da wani ke cewa sosai a
dakin sai an daga murya domin
ruwan ya dada tsugewa da
'karfin gaske
''Tani ta hadiyi yawu da 'kyar
sabo da mummunan rikon da
Gambo ya yiwa gashin kanta.
''Ma...soyi..nane... Dan Allah kar ku
kashe min shi...''.
Gambo ya saketa jikinsa na rawa.
Bayanin ya yi matukar sa shi
kaduwa, domin bai taba
tsammanin haka ba.
''Ta san Jabir?''. Ya ce a ransa.
''Gawa biyu ke nan''. Ya sake
maimaitawa a ransa.
''Dole ne ita ma ta bakunci
lahira''.
Gambo ya juyo ya dubi abokan
barnarsa su uku. Duk sun yi
cirko-cirko kamar zakaru kowa
da bindigarsa a hannu. Jira suke
su ji 'kwakkwaran sauti ko da
na bugun agogo ne su fara
harbi.
.
''Likita...! ban san haka abin ya ke
ba....''. Gambo ya ce da Tani a
tausashe kamar gaske. Tani ta
dago kai idanuwanta na zubar
da hawaye ta dubeshi domin ta ji
alamun rahama a kalamansa.
''Ku taimaken kada ku kashe min
shi dan Allah... wallahi idan ku ka
kashe Jabir nima mutuwa zan
yi....!''. Ta fara kuka, lokaci guda
kuma ta durkusa a gaban
Gambo tana rokonsa. Gambo ya
kama hannunta a nutse ya dago
ta sama ya ce.
''Bari kuka 'kanwata....zancen mu
kashe Jabir bai taso ba.... Jabir

abokin mu ne ke kuma
masoyinki ne, mu muna son ya
rayu sabo da wasu dalilai namu...
Ke kuma kina son ya rayu saboda
masoyinki ne, tun da haka ne mai
zai hana ki cece mu baki
dayanmu ki hanzarta ceton
rayuwarsa cikin gaggawa? Kin
ga raunin da ke 'kafarsa ya sa ya
yi asarar jini mai yawa''.
.
Sidi mai Jaka ya yi shiru yana
dubana. ''Nas, Allah ya horewa
Gambo iya kera 'karya da
gamsar da mutum duk abin da
yake so....''.
''Haka ne''. Na ce da shi.
''Dan haka sa'ar da Tani taji
kalamansa sai nan da nan tayi
ajiyar zuciya domin ta dauka duk
abin da ya fada da gaske ne har
zuciyarsa.
''Tambaya daya kawai muke so
ya amsa mana, in dai kika
magance shi ya amsa mana
tambayarmu to zamu tafi mu bar
miki masoyinki...''.
''Na gode''. Tani ta ce cikin kukan
dadi, domin bata taba
tsammanin wadannan mutane
masu bakaken kaya da bakar
aniya zasu 'kyale ma ta Jabir ba.
Kai hatta ita kanta bata taba
zaton za ta tsira ba.
''Ku kama min nan mu shiga da
shi dakin aiki''. Tani ta ce da su
Peter da Asabe wadanda ke
tsaye gefe guda ba sa ko motsi
kamar an zare musu laka.
Malaman asibitin biyu suka tura
gadon da Jabir ke kwance Tani
na binsu a baya zuciyarta na ta
sake-saken abin da ya hada
masoyinta da wadannan
miyagun mutanen.
Gambo ya 'kiftawa Lanto idanu
ya biyo shi a baya suka bi su Tani
dakin aikin. Ya yin da sauran
mutanen biyu kuma suka yi tsaye
anan suna gadi da bindigarsu a
hannu. Gambo ya dubi dan
tsukakken dakin da suke ciki....

Babu komai a ciki sai wasu
gadaje guda biyu da wasu 'yan
mashina gami da kanta-kanta ta
magunguna iri-iri daban-daban
da kuma sinadarai. Tani ta janyo
wata farar Jaka ta budeta
sannan ta fara zuba tarkacen
aikin da take bukata akan wani
dan felelen faranti launin azurfa
da ke hannun Peter.
Tsawon mintuna hudu Tani ta
yanke 'kafar wandon Jabir,
sannan ta rike numfashi cikin
kaduwa da abin da ta gani a
cinyar Jabir. Gambo ya matso
kusa ya dubi cinyar Jabir, wanda
ke kwance ko motsi baya iya yi
sosai. Abin da Gambo ya gani ya
sa shi kaduwa, domin duk kusan
cinyar Jabir raunika ne kusan
guda tara guri daban-daban na
alburusai.
''Wannan ba karamin aiki
bane...''. Tani ta ce cikin karaya
da abin da ta gani a jikin abin
begenta. Wannan shine kuskure
na biyu, domin tun sa'ar da ta
nunawa Gambo cewa ta san
Jabir ta aikata kuskure na farko.
''Me kike nufi da cewa ba
'karamin aiki bane?''. Gambo ya
tambaya yana duban Tani akwai
alamun zargi a muryarsa ''Aikin
zai dauki kusan sa'o'i biyar kafin
a gama..''Gambo ya ji tsigar
jikinsa ta tashi ''Sa'a biyar? Sai
gari ya waye musu ke nan a asibitin...??
LINZAMIN SHAIDAN-12
.
'Me kike nufi da cewa ba
'karamin aiki bane?'' Gambo ya
tambaya yana duban Tani akwai
alamun zargi a muryarsa. ''Aikin
zai dauki kusan sa'o'i biyar kafin
a gama...'' Gambo ya ji tsigar
jikinsa ta tashi ''Sa'a biyar? Sai
gari ya waye musu ke nan a
asibiti wanda hakan bai taba
yiyuwa. A karo na farko sai
Gambo ya farga ya kuma fara jin
matukar hadarin da suke ciki a
jikinsa wanda a 'yan sa'o'in da

suka wuce dokin Jabir zai fada
masa inda ya boye kudin shi ya
hana shi gano hadarin a fili.
Amma a yanzu da ya fahimci
cewa sai an dauki sa'o'i kafin
Jabir ya iya magana da shi sai ya
ga lallai akwai sake. A wannan
dakika ne to mahaukacin tunani
ya zo masa!
''Sai kuma....an 'kara masa jini''
Tani ta ce cikin sauri saboda
ganin sauyin yanayin da ke
fuskar Gambo ita a tunaninta
hakan da ta ce burge Gambo ta
ke yi tun da dai 'kokarin ceton
ran abokin su take yi Gambo bai
ko ji abin da take fadi ba Wata
zuciya na cewa da shi ''Wani
ma'aikacin asibitin na iya baro
bangaren aikinsa ya shigo
wannan bangaren a bazata duk
da yake dai ruwa ake yi to amma
tsautsayi bashi da kadan..
Jami'an tsaron da suka yi artabu
da su na iya biyo sawunsu har
zuwa asibitin.. Kai abin na da
hadari''
Wannan tunane-tunane da wasiwasin zuciyar su suka sa Gambo
ya sake tunani lokaci guda kuma
tunanin abin da ya kamata ya yi
ya darsu a zuciyarsa
''Daure masa 'kafar!'' Gambo ya
ce kusan a fusace. Tani ta rike
numfashi a tsorace.
''Ba...aiki za'a...''
''Ki daure masa 'kafar na ce!''
Gambo ya ce lokaci guda kuma
ya zaro bindigar sa fili. Lanto da
ke tsaye a bayansa shima ya yi
abin da ya ga shugabansa ya yi.
Jikinta na bari idanun Tani a kan
bindigogin ta yi saurin saka
bandeji ta daure 'kafar cikin
hikima yadda jini ba zai ci gaba
da zuba sosai ba.
''Dauki duk kayan aikin da kike
bukata''. Gambo ya umarce ta.
Tani ta dube shi a rude cikin
rashin fahimta. Gambo ya kama
kwalar rigarta ya fisgota kusa da
shi ya ce cikin kakkausar murya.

''Dauki duk kayan aikin da kike
bukata, wadanda zasu iya
tsaida jinin da ke zuba... Kada ki
manta kuma ki dauki har da
jinin da za ki 'kara masa.... Idan
kika sake muka je kika ce dani
kin manta wani abu sai na kashe
shi a gabanki... Kema ki bishi a
baya''. Gambo na gama fadin
haka sai ya hankada Tani da
'karfi ta tafi taga-taga ta daki
wata katuwar kanta ta magunguna.
Nan da nan sama
da kwalabe goma suka fara yiwa
kamsu rotse a 'kasa. Gambo ya
dubi Peter da Asabe ya ce. ''Ku bi
wannan ku koma can ciki inda
sauran suke kuyi jirana''. Jiki na
rawa Lanto da Peter da Asabe a
gaba suka fice daga dakin.''Ku
daure min su kafin na zo''.
Gambo ya ce da Lanto cikin karaji.
.
Sidi mai Jaka ya sake yin shiru a
karo na biyu tun sa'ar da ya fara
'kulla wannan zaren labarin.
''Nas, na yarda kudi na iya sa
mutum ya haukace lokaci guda.
Yanzu ka duba ka ga yadda son
abin duniya ya gama haukata
Gambo cikin dan 'karamin
lokaci''.
''Wannan gaskiya ne''. Na ce da
shi.
''Ya ya to aka yi?''.
Sidi mai Jaka ya ci gaba.
.
''Bayan kamar mintuna biyar
Gambo ya sako Tani a gaba
fuskarta babu kyawun gani,
domin babu mafi munin gani a
fuskar kyakkyawar mace a
lokacin da take cikin janhuru.
Tani dauke take da 'katuwar
jaka ta magungunuka da sauran
tarkace da Gambo ya sata ta
dauka duk ta watsa su cikin
jakar, Gambo na biye da ita a
baya yana tura gadon da Jabir ke
kwance a kai.
Gambo ya yi tsaye yana nazarin
jama'arsa guda uku. ''Me....me za

ku yi musu?''. Tani ta tambaya
cikin shesshekar kuka sa'ar da
ta ga su Peter da Asabe kwance a
tsakar dakin an hada
hannayensu da 'kafafunsu guri
guda an daure tamajau kamar
damin goro. ''A nan zamu tafi mu
barsu Tani''. Gambo ya ce da ita.
Ga mamakin Tani gambo ya sake
tausasa muryarsa a karo na biyu.
''Ko...kashe shi za ku yi?''. Tani ta
tambayesu cikin karayar zuciya
tana duban gadon da Jabir ke
kwance a kai.
''Ba lallai bane...indai kika yi abin
da muka saki..''. Sannan sai ya
dubi sauran mutanen uku ya ce.
''Ku taho min da shi cikin mota''.
Ya nuna Jabir da hannu lokaci
guda kuma ya dada cakumar
Tani ya ce, ''Mu tafi cikin mota''.
Akwai wani abu a muryarsa da
ya hana Tani 'kokarin yi masa turjiya.
Har yanzu ruwan ake tafkawa
kamar da bakin 'kwarya, a
wannan karon har da iska mai karfi.
.
Motar ta fice daga asibitin a guje,
ta doshi hanyar da za ta fitar da
su daga birnin. Mutum uku ne a
gaban motar har direba, ya yin
da Gambo, Lanto da kuma Tani
suke zaune a bayan motar bata
ko motsi ga dai ruwan saman da
ya jika mata gashi sa'ar da suke
fitowa daga dakin yana 'kokarin
shigar mata idanu. Amma ba ta
damu da ta goge fuskarta ba.
''In dai kashe Jabir za su yi, to
nima gara su kashe ni''. Abin da
Tani ke cewa ke nan a zuciyarta
.
Lanto ya kara bakinsa a kunnen
Gambo ya ce da shi cikin rada
''Ina muka nufa kuma?''
''Maboyarmu mana.. Kafin
al'amura su yi sanyi gurin nan ya
yi mana zafi yanzu'' ''Kana da
maboya ne?'' Lanto ya sake
tambaya. Gambo ya saki
murmushim yake ya ce ''Na
gama tunanin komai tun kafin

mu fara komai Tabbas ina da
maboya...maboyar da babu wani
jami'in tsaro da ke 'kasar nan da
ya isa ya gano mu a can!''.
.
KASHI NABIYU
Sidi mai Jaka ya yaye bakinsa
gaba daya kamar zai fashe da
kuka Ashe wai duk hamma ce
yake yi
Sidi mai Jaka ya shafi fuskarsa
sa'ar da ya gama doguwar
hamma ya dubeni ya ce
''Wani lokaci Nas

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment