Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba su fahimci abin
da kake son fada sosai ba shi ya
sa ka ji an fashe da dariya''.
Ganbo jikinsa na rawa idanunsa
jajur kamar gauta ya hadiye
zuciyarsa da 'kyar, domin da an
ci gaba a haka to da jikin wani a
cikinsu ya yi tsami. Jimawa
kadan Gambo ya nisa ya ci gaba.
''Dole ne mu bi hanyar da shima ya bi
ya samu, domin in ba haka ba to
sai dai mu mutu a wahale''.
Jabir ya dubeshi ya ce. ''To kai sai
kwana-kwana kake ka 'ki ka
bamu maganar a mike ko ma
gane abin da kake son fadi.
Mece ce hanyar daya bi?''.
''Fashi!...... Fashi mana!!'' Gambo
ya amsa kai tsaye yana dubansu
dai-dai kamar Malami a gaban
dalibansa.
Jabir yace da shi. ''Kazo da
sabuwar bidi'a''.
''Yanzu in ban da shirmenka
yaushe ne wadanda ko dan kin
harbi bamu da shi zamu tafi
fashi...''
Gambo ya girgiza kai cikin sauri.
''Indai dan wannan ne kada ka
damu kanka, ina da aboki
inyamuri a can cikin kasuwar
gwari, na san a dubu hamsin sai
ya bamu hayar bindigogi biyar
da aron mota marar lamba,
wacce koda abin Allah ya kiyaye
rana ta baci ta 'yan sanda ba za
su taba gano daga inda motar ta
fito ba balantana ma har ga
batunmu''.
.
Ya sake yin shiru yana nazarin
fuskokinsu, kowa a cikinsu
wasikar jaki yake karantawa. To
amma akwai wani yanayi a
tattare da fuskokinsu daya 'kara
masa kwarin gwiwa.
''kunga wannan itace damar mu
ta 'karshe, ko dai muyi arziki, ko
kuma mu mace a berayen
masallaci. Ku dubi yadda dan

iskan nan ya kera wannan
makeken gida gari guda, ga
matarsa kyakykyawa kamar
balarabiya, amma mu gamu duk
a bushe kullum ta ci ba ta ci ba''.
Ya danyi shiru yana dubansu.
Abin da ya gani a fuskokinsu ya
gamsar da shi, dan haka ya mike
tsaye yace. ''Nine ja gaba na
wannan tafiya, duk wanda ke iya
yin fashi a cikinku to ya mike
tsaye in ganshi, wanda ko bai
iyawa gara tun da wurwuri ya
kama gabansa domin jin sauran
sirrinmu hadari ne''.
.
''Kyakykyawar mace kamar
balarabiya''. Jabir ya maimaita
kalmar Ganbo a cikin zuciyarsa.
Nan da nan sai wani zazzafan
gumi ya fara barkowa akan
goshinsa, jikinsa ya fara tsuma,
domin kyakykyawar macen da
aka ambata a cikin bayanin sai ta
tuna masa da abar 'kaunarsa
Tani wacce duk wani 'kokari na
buga-bugar rayuwa dan ita yakeyi.
Jabir ya sha jin ciwon korarsa da
aka yi a jami'a. Haka nan kuma
har yanzun nan abin na fado
masa lokaci-lokaci, musamman
ma idan suka yi kicibus ko kuma
idan ya hangi wasu daga cikin...INZAMIN SHAIDAN-07
.
Ko kuma idan ya hangi wasu
daga cikin
abokan karatunsa To amma duk
ta wannan kamar shafar mai ce a
gurin Jabir in har za a kwatanta
da irin zafin ciwon rabuwarsa da
Tani da yake ji a cikin zuciyar ta
sa musamman ma idan ya tuna
da irin rabuwar da suka yi. ''....
Me zaki yi da dan iska irin
Jabir....'' '.... Ke dai kin zubar da
mutuncinki wallahi....''Mutane fa
duk daukar yar
iska suke yi miki saboda kina
yawo da Jabir..
Maganganun cece-kucen da
dalibai sukayi ta yiwa Tani a
kansa ne suka yi ta dawowa

zuciyarsa Wadannan abubuwa
baza su taba rabuwa da
zuciyarsa Jabir ba domin a
kullum idan ya tuna da irin
wulakancin da bakaken
maganganu
da zagi da turanci da duk Tani ta
hakurce tace taji ta gani shi take
so Sai Jabir yaji duk duniya babu
abin da zai iya sakawa Tani da
shi koda kuwa ransa zai bata sai
dai yayi iya 'kokarinsa
Dan haka a yanzu da Gambo ya
ambaci kyakkyawa kamar
balarabiya sai Tani ta fado masa
Ba tare da yayi tunanin
makomarsa ga Ubangiji ba bai
kuma tuna da cewa duk wanda
yayi fashi idan aka kama shi
harbewa za a yi ba abin kawai
dake zuciyarsa a wannan lokaci
shine wannan kawai itace
mafita hanya daya zai sakawa
Tani da ita abin da tayi masa
.. Zan sai ma ta motocin
hawa...na gina ma ta katon gida
mahadi ka ture...in bata duk
abin da take so na jin dadin
rayuwa...''
Ya fara lissafo abubuwan da duk
zai ma ta in har aka sami kudi
Da wannan tunani sai Jabir ya ciri
tuta a cikin sauran mutanen
domin shi ya fara mikewa tsaye
wanda hakan na nufin ya yi
amanna ya kuma amincewa da
shi za a yi FASHIN!
.
Wani tattausan murmushi ya
subuce a gefen bakin Gambo
sa'ar da ya ga Jabir ya mike tsaye.
''Da kyau namiji!'' Ya zuga Jabir.
Sannan ya dubi sauran mutanen
biyu suka mike kusan lokaci
guda ba tare da sun dubi juna
ba. Gambo ya fashe da dariya,
sannan yace cikin 'karaji.
''Shegun duniya! Ashe kowa
yana son kudi''. Abu daya da bai
sani ba shine manufarsu ta sha
bamban da ta Jabir, abin kuma
da bai sani ba shine inda babu

Tani a zuciyar Jabir to ba
'karamar kaduwa zai yi ba,
domin bazai taba mika wuya ya
tashi ba.
.
Sidi mai Jaka yayi shiru lokaci
guda kuma ya dube ni yana
'kokarin ganin irin yadda na ke
bin labarin.
''Nas ka ji yadda sannu a hankali
na ke gangarowa zuwa inda
muka tsaya ko?''.
Na gyada kaina na ce. ''Kwarai
kuwa....yi maza ka 'karasa min
wannan ko ma koma kan
wancan labarin na da, domin duk
ya fi wannan dadi''.
''Haka ne''. Sidi mai Jaka ya ce.
Sannan sai yaci gaba gami da
share gumi akan goshinsa. Nayi
mamakin abin da yasa shi gumi
da goshin magariba.
''karfe uku dai-dai bayan sati
guda da yin alkawarin, cikin
talatainin dare mutanen uku
suka gama hallara cikin dakin
suna jiran zuwan gambo. Ko
wannensu tsaye, sun cakaraicakarai kamar zakaru sai kaiwa
da komowa suke yi kowannensu
rike da karan sigari suna bulbula
hayaki sama abinsu. Wanda ke
hangen tagar dakin ta waje , ba
abin da zai hanashi kawo
gudunmawar bokitin ruwa a
guje, domin zai dauka ko gobara
ake a dakin, to amma duk
hayakin sigari ne. Yau ce ranar
da suka ajje domin shiri na
'karshe, dan a washe garin ranar
ne suke shirin kaiwa gidan
attajirin harin bazata wanda
daga wannan hari ne suke sa ran
cewa kowa a cikinsu ya yi
hannun riga da talauci.
Amma jiranda suke yi yanzu abin
ya fara damunsu, domin tun jiya
da suka rabu da Gambo yace
dasu su zo su jirashi, shi kuma
zai zo musu da dukkanin
bindigogi da sauran abubuwan
da suke bukata. Makon da ya

gabata basu bata shi a banza ba,
domin kullum sai sunyi shawagi
a 'kofar gidan attajirin suna kula
da irin kai kawon da motocin
maziyarta suke yi, sun kuma lura
da cewa kullum Mai gidan baya
dawowa sai 'karfe goma sha
biyu na dare, wannan ita tasa
suka yanke shawarar kai harin
'karfe biyu na dare domin sun
tabbata a lokacin ya shiga barci.
Duk kusan wani shiri dai an
gama shi tun jiya, to amma yanzu
rashin zuwan Gambo ya fara
damunsu. A dai-dai lokacin da
suka fara fargabar ko ba lafiya
ba, sai suka ji tafiya an nufi
dakin sadadaf! Akwai wani abu
a yanayi na tafiyar daya fara basu
tsoro. Kwatsam sai suka ji an
bugo kofar, Gambo ya fado dakin
daga shi sai diras, jikinsa
duk faca-faca da kwata, dauke
da 'kullin tsummokara him! a
kansa kamar wanda ke tafe da
kayan alhaki. Yana zuwa sai ya
jefar da kayan tim! a tsakar
dakin, tun kafin kayan su taba
'kasa mutanen uku suka yi tsalle
gefe guda cikin kaduwa suna
duban ikon Allah, yau ga
Gambonsu a tsaye daga shi sai
diras! Sai warin kwata yake yi
kamar mushe.
Gambo ya dubesu, suma suka
dubeshi, irin duban da yara kan
yi wa macijin wasa na roba,
Gambo bai yi magana ba sai ya
fara matsawa cikin dakin, nan
da nan mutanen uku suka fara
'kokarin samin gurin tserewa
domin ko shakka babu Gambo
haukacewa yayi.
.
Abin da ya fara zuwa zuciyar
Jabir shi ne, yanzu haka yawan
tunane-tunanen zuwa fashin ne
yai wa 'kwakwalwarsa yawa ta
tasamma zauta shi, domin
daman ya fahimci a iya kwana
bakwan nan da suka wuce
Gambo ko rintsawa sosai ba ya

yi, wani lokacin ko da rana idan
ya kwanta ya dan runtsa sai
kaga bakinsa yana motsi.
''Matsoratan banza..... Dan Allah
ku bani wando insa, ku da nake
tsammanin gobe ya war haka
muna can mun ritsa wannan
dan iskan amma kuke tsoron
mahauci''. Su Jabir suka dubeshi
cikin shakka. Jabir ne ya fara
magana bakinsa na rawa.
''Meye ma'anar yawo cikin
wannan uban daren daga kai sai
diras, ga jikinka duk kwata in ba
hauka ba?''. Gambo ya sake
bushewa da dariya a karo na
biyu ya dubesu ya ce. ''In banda
haukanku ta yaya kuke
tsammanin zan iya kawo
bindigogi biyar tun daga
kasuwar Gwari har zuwa nan?....
Ba kwa tunanin 'yan sanda dake
ta sintiri ko ina cikin wannan
dare ko....''.
Mutanen suka bushe
da dariya sa'ar da suka fahimci
hikimarsa. ''Shege Gambo! Lallai
ka isa mayaudari ga fa 'yan
sanda basu damu da su kula
mahaukaci a bakin hanya ba
kuwa''. Jabir ya ce.
Gambo ya zaro bindigogi biyar
cikin 'kullin tsummokaran ya
mikawa kowa sannan ya ce da
su. ''Ina fatan kowa ya rike
yadda abin zai kasance ko?''
Suka gyada kai baki daya.
''Na fada muku....''
Gambo ya ci gaba.
''Wadannan bindigogi duk za ku
rike su kawai don barazana
tawa ce kawai mai alburushi
idan yayi mana taurin kai zan
harbe shi da 'kwaya daya jal....
Kuma ya riga ma ya tsufa, dan
haka ina ganin dan na
dankarawa tsohon 'kokon
kansa alburushi taimakonsa
nayi....
.
.
''Nas'

Sidi mai Jaka yai kirana, sannan
yace da ni. ''Zaka yi mamakin irin
yadda mutanen zamani ke
kafircewa, su zamo marasa
hankali duk saboda rayuwar
duniya...Ka dubi samarin nan dai
ka gani wadanda ko
'kwakkwarar satar ma basu
iyawa duk da yake dai dama
batattu ne, to amma kaji yadda
lokaci guda duk suka rikide suka
canja kamanni duk wai sabo da
kudi suka zama rikakkun
marasa imani..''.
''Haka ne''. Na ce da shi cikin
zakuwa domin naji kamar
labarin ya daina gundurata.
''A can cikin gidan tsohon
barawo attajiri''.
Sidi mai Jaka ya ci gaba.
.
''Attajirin na can kwance shi da
kyakkyawar amaryarsa mai siffar
larabawa, babu abin da ya dame
shi a duniya, bai kuma ta6a ma
kawowa ko da dai-dai da gamin
gafara ba wai sata zata saci sata!
''Kai baka jin barci?''. Laila
matarsa ta ce da shi idonta a
lumshe tana murmushi.
''Yuashe mutum zai iya barci kina
kusa da shi''. Attajirin ya ce da
ita. Sannan sai ya kamata ya
rungumeta a 'kirjinsa yana
sunsunar daddadan turaren da
ke gashin kanta.
''To meye rayuwar duniyar?''. Ya
tambayi kansa. ''Ai ka sami
kudi.....kawaika hole shi ne
rayuwar.... Ni kam daga yau na
daina harkar kasuwar dare.....''.
Ya ci gaba da cewa kansa.
''Nasan dai dan abin da na tara
ya isheni ni da 'yar matata....gara
na hakura na sa matata a gaba''.
Shi kansa yana mamakin irin
masifar 'kaunarta da yake yi,
domin a 'yan kwanaki kadan da
suka gabata shi bai san menene
so ba, to amma yau ya fahimci
ashe ada ba 'karamin rashi ya yi
ba.

''Darling!''. Laila ta 'kirashi a
tsorace. Ya gama shagala cikin
tunani dan haka bai ji kiran da
tayi masa na farko ba, har sai da
ta sakalo wuyansa da kyawawan
hannunta ta girgiza shi sannan
ne to ya dubeta cikin mamaki.
''Dar...lin.....g ni kamar motsi na ke
ji a waje...''. Ya kashe idanu cikin
murmushi ya ce, ''Shuke-shuken
dake gidan nan ne ace mutum ya
gaza jin motsi...? Ke fa wallahi ba
kya rabo da shagwaba....''.Laila ta
sake 'kankameshi cikin tsoro ta
kuma cewa. ''Motsi-motsin takun
sawu na ke ji cikin falo...''. Ya
dada rungumota 'kirjinsa ya ce.
''Kwantar da hankalinki Lailar
duniya....kina nan gabana babu
abin da ya isa ya same ki....Me
yiyuwa ma duk a banza ki ke
damun dan kyakkyawan kanki
da tunane-tunanen wofi.... Yanzu
haka ma 'yar kyanwarki ce ke jin
yunwa ko kuma............
Kalmar ta subuce daga bakinsa
sa'ar da suka ga 'kofar dakin na
budewa da kanta ahankali-ahankali.
''Na Shiga Uku!LINZAMIN SHAIDAN-08
.
''Na shiga uku!!'' Laila ta ce
'kasa-kasa Ta dada 'kankame
shi kamar zata tsaga shi gida
biyu saboda tsoro Sannu a
hankali kofar dakin ta gama
budewa sannan sai suka fara
shigowa daya bayan daya
wannan na bin wannan kamar
'ya'yan carbi Tsawon mintuna
suna dubansa kwance kan
gadon ya yi mutuwar tsohuwa
yana dubansu kowanne fuskarsa
a boye cikin bakin 'kyalle
''Da...wacce...kuma kuka zo.''
Ya tambayesu bakinsa na rawa
Hakan ya bata masa rai domin
bai kamata namiji kamarsa ace
wai bakinsa yana rawa ba tun da
abin ya ke yiwa wadansu ne shi
ma aka yi masa.
''Kudi muke so. Ko ranka da na
matarka Gambo ya ce da shi

cikin tsawa. Nan da nan nadama
ta darsu a zuciyarsu domin jiya
jiyan nan matarsa Laila take cewa
da shi ''Alhaji kudin nan a kaishi
banki mana ai sun yi yawa a
barsu a gida..''
Ita bata san dawan garin ba ke
nan? A bu na farko daya fara
zuwa zuciyarsa shi ne ko zai
mutu ba zai basu kudin ba
Wannan shine kuskurensa na
farko.
.
''Malam ba bata mana lokaci
muke so ba, tashi ka kaimu inda
'karafen suke...''. Tsohon
barawon ya dubi sababbin
barayin kowanne da bindigarsa
a hannunsa..... Ya fara nukunuku....Bai aune ba sai yaji an
kwada masa tafi. ''Wayyo Allah!''.
Laila ta fara ihu. Jabir jiki na rawa
ya kara mata fankwan bindigar a
goshi, domin a lokacin da ta sake
ihu babu abin da zai iya yi dan
bindigar babu komai ciki fanko
ce. Sauran mutanen uku suka
hau attajirin da duka tim! tim!!
da mangari da bindiga, to amma
abin da basu sani ba shi ne ya
saba da duka, abinka da tsohon
barawo. Jini ya fara fita ta
bakinsa ta hancinsa. ''Ko dai sun
kashe ni a banza, domin ba za su
taba samun kudin ba, amma a
'kalla dai Laila ta samu'' abin ke
nan dake cikin zuciyarsa, matarsa
Laila, kamar yadda Tani take a
zuciyar Jabir. ''Ku 'kyale shi
haka!'' Muryar Jabir ta ratsa
dakin. Gambo da sauran
mutanen biyu suka bar dukan
attajirin suka dubi Jabir cikin
mamaki. Jabir ya dubi attajirin
kwance rub da ciki a tsakar
dakin jini na zuba ta baki ta
hanci. Ya durkusa daf da kunnen
attajirin yace.
''In ka so kana iya fada mana
inda kudin suke mu kwasa muyi
tafiyarmu mu barku lafiya....in
kuma baka ma so ba, to zamu

bar ka din dai lafiya muyi
tafiyarmu, amma duba ka gani?''.
Jabir ya mike tsaye cikin hanzari
ya cakumo gashin kan matarsa
Laila ya dora hancin bindiga a
goshinta ya ce. ''Na baka minti
daya, ka zabi daya, ko kudi ko
na fasa ma ta 'kwa'kwalwa.....
Ban san harbin kyawawan mata
ba, amma yanzu zan fara... Zan
'kirga maka goma in baka tashi
ba....''. Ya dada dannan hancin
bindigar a goshin Laila sannan ya
fara lissafi. ''Daya......biyu.....uku.....h
udu.....biyar.....''
''Kayi min rai dan Allah!''.
Atttajirin ya mi'ke tsaye jiri na
d'aukarsa..... ''Ku 'kyale ta ni ku
kashe ni.....''.
''babu ruwanmu da kai.....ita
zamu kashe in baka wuce gaba
ba...'' ''Shida....bakwai....''. ''Ah!
Dan Allah bari muje ku diba''.
Gambo ya dubi Jabir cikin
girmamawa. Suka bishi a baya
mutanen uku rike da shi. Jabir
kuma rike da Laila. Wani dan
'karamin daki suka shiga, suna
zuwa suka yi ido biyu da
'katuwar loka ta katako jingine
jikin bango. ''Gashi nan.... Ku
diba ku bar min Laila....''. Attajirin
ya ce da su cikin takaici, domin
ko shakka babu sun gama
tagaiyara shi....daman an ce wai
garin banza a farau-farau din
banza ya ke 'karewa.... A 'kalla dai
baza su kashe masa LAILA ba!
Mintuna biyu suka balle 'kofar.
Nan da nan numfashinsu ya
dauke baki daya, kudin dake
ciki kamar budar ido. Ga Jabir
ganin kudin tamkar mutumin da
bai taba ganin falki bane, ba zato
ba tsammani kuma sai ya tsinci
kansa a bakin teku. A dai-dai
wannan lokacin da duk wannan
kuma ke faruwa ne Laila ta dubi
Jabir bakinta na rawa ta ce da shi
'kasa-'kasa. ''Zaku bar ni ba za ku
kashe ni ba.....? Tsoron
mutuwa....nake ji?''. Jabir ya

dubeta. Ga mamakinsa sai yaji
tunanin abar 'kaunarsa Tani ya
fado masa cikin zuciya. Nan da
nan sai yaji zuciyarsa ta karaya ya
girgiza kai ya ce. ''Kada ki
damu....babu mai taba.....''
Mummunan sautin bindigar da
ya ratsa dakin shi ya hana shi
'karasa mata maganar da yake
fada ma ta. Jini ya fallatsa akan
fuskarsa. Da farko ya dauka shi
aka harba, amma cikin kaduwa
sai yaga kyakkyawan gangar
jikin Laila ya sulale ya fadi kan
sawunsa. Jabir ya yi tsalle gefe
sa'ar da attajirin ya 'kwalla 'kara
mai tsananin 'karfin gaske. Jabir
ya dubi Gambo a tsorace,
hayakin da ke fita daga bakin
bindigarsa ya ishi Jabir amsa.
.
.
''ME....Yasa....Ka...Kashe Ta....?''
.
Sidi mai Jaka yai shiru yana
dubana. A dai-dai lokacin ne to
aka fara kiran sallar magariba.
.
''Kash! Nas ga shi kuma lokacin
sallah ya yi... Na katse shi cikin
kaguwa bakina na rawa
ME YASA TO YA KASHE TA ?
''Sai ka bari to sai mun dawo
daga
masallaci... Kai da dazun nan
kake cewa labarin ya fara
gundurarka....??.
Na katse shi cikin
'kaguwa bakina na rawa.
''Me yasa to ya kashe ta?''. ''Sai ka
bari
to sai mun dawo daga
masallaci.... Kai da dazun nan
kake cewa labarin ya fara
gundurarka.... To mene ne kuma
yanzu na damuwa....? Ka je kawai,
kada ka damu Nas''
.
Tun kafin na 'karasa gidan Sidi
mai Jaka na hango shi bisa buzu
zaune a 'kofar gidan yana jan
tasbaha kansa babu hula, haka

nan duk da duhun daren da tuni
ya gama shigowa hakan bai
hanani hangen kansa ba fari fat
cike da furfura kamar an yi masa
barin garin alli.
Lokacin dana 'karasa 'kofar
gidan sai na ga ashe har da
kwanon abinci a gabansa.
''Assalamu alaikum''. Na yi masa
sallama Sidi mai Jaka ya shafi
kansa da hannunsa mai carbin,
sannan ya dubeni cikin
murmushi.
''Har ka dawo?''. Ya tambayeni.
Ban amsa masa ba, sai da na
zauna kusa da shi a kan daben
da ke 'kofar gidan, domin buzun
bazai ishe mu ba.
''Dan ma na tsaya sallar isha ne
shi yasa ka ganni a dan
makare.... Ai da tuni na dade da
zuwa''. Sidi mai Jaka ya gyada
kai cikin gamsuwa. ''Wannan
gaskiya ne''. Ya ce da ni, lokaci
guda kuma ya ajje carbin gefe
guda, ya janyo kwanon abincin
gabansa a hankali kamar mai jan
mushe. Kwanon abincin yaji jiki,
Allah ne yasan yawan shekarunsa
a duniya, domin duk kusan
ko'ina a jikin kwanon a farfashe
yake da lambobi ko'ina. Nayi
mamakin abinda ke cikin
kwanon..... Wata zuciyar tace da
ni tuwo ne a cikin kwanon. Ya
yin da kuma cikin gaggawa wata
zuciyar ta 'karyata hakan tana
cewa da ni, me yiwuwa shinkafa
da miya ne tun da dai da tuwo
ne zai yi wuya a hado shi guri
guda da miyarsa.
Ba 'karamin kaduwa nayi ba
sa'ar da ya bude kwanon na yi
ido biyu da dan wake zuka-zuka
yana min signa. 'Dan wake
ne...me yiwuwa kuma idan an
'kirashi tubani duk babu laifi,
domin ban taba ganin curin dan
wake da girman wannan ba. A
had'iye dai bai had'iyuwa lokaci
guda, haka nan ma a taune yafi
'karfin a jefa shi a baki a yi masa

taunar gadara, dolene a gutsura
duk dun'kule guda gida uku
kafin a sami damar tauna shi
cikin zaman lafiya.
.
Na dad'a zubawa cikin kwanon
da Sidi mai Jaka ya bud'e idanu
cikin tsananin shakka, domin har
yanzu ban gama imanin cewa
d'an wake nake kallo ba. To
amma gashi nasha-nasha a cikin
mai, kuma wani abin dad'in
tashin hankali an bad'e abin da
yaji ta ko ina da 'kyar ma ake iya
ganin jikinsa sai yajin.
Sidi mai Jaka ya yi dariya sa'ar da
ya dubi fuskata yaga har na fara
gumi sabo da abin da na gani.
''Wannan tubani ke nan uban
d'an wake'' yace da ni lokaci
guda kuma ya d'auki kwanon ya
fara zunkud'awa ya gauraya
tubanin da yajin.
''Yaran zamani baku san abinci
ba..''. Sidi mai Jaka yaci gaba da
cewa yana zunkud'a tubaninsa.
''Ai abinci in dai ya wuce abu uku
zuwa hud'u....to ana shirga
zaman 'karya ke nan....''. ''Wanne
da wanne ke nan?''. Tambayar ta
su6ucewa bakina tun kafin na yi
shirin furtawa. Sidi mai Jaka ya
ajje kwanon sannan ya d'aga
'yan yatsunsa guda hud'u ya fara
da cewa.
''Kaga na farko shine Tubani.....
Na biyu 'Dan wake.... Na uku
Tuwon tsari, na cikon hud'unsu
kuwa shine Burabusko.... In dai
abinci ya wuce wad'annan NAS,
to al'amarin kuma ya zama ko sai
ace maganin yunwa''.
''Hakane''. Na ce da shi. Ni kaina
sai da kunyar 'karyar da na shara
ta kamani, domin a cikin kalar
abin nan da ya lissafa babu wata
'kwa'k'kwarar cimata ciki,
musamman ma Tubanin domin a
yadda muka yi ido biyu da shi a
yanzu ya fi kama da abin tsoro
fiye da abinci.
.

Barbad'en yajin da
ke saman tubanin shi yafi tayar
da hankalina.
''Bismillah Nas''. Sidi mai Jaka ya
ce lokaci guda kuma ya cakumo
wani sullubeben Tubani kayan
'kato guda ya nufi bakinsa.
''Uhm...uhm! Na gode''. Na ce da
shi cikin gaggawa, domin wata
zuciya na cewa da ni idan na
sake na had'iyi Tubanin babu
abin da zai hanani aman hanjin
cikina.
''A haba, ba za ka ci ba Nas?''.
Na gyad'a kai gami da yi masa
murmushi, domin bana son ya
d'auki abin da wata manufa.
''Cab! amma fa yau zan ci da
rabonka... Wallahi dan baka ji
dad'in daTubanin nan ke da shi
bane... 'Dauki guda d'aya ka
gwada ka ji d'and'ano...''.Sidi mai
Jaka yace lokaci guda kuma ya
jefa dun'kulen Tubanin gaba
d'aya a bakinsa ba tare da ya
gutsura shi ba.
Hakan da yayi shi ya fi sani
kad'uwa fiye da komai, domin a
d'an ta'kin tunani na ke
dun'kulen Tubanin na iya sha'ke
d'an tsohon ya kashe shi a
banza. To amma nayi kuskure....
.
Na zuba masa idanu kamar
macijin da ke son had'iyar 'kwai,
sai dai kuma sa6anin maciji Sidi
mai Jaka bai feso da kwanson
komai waje ba. ''Ka bar dad'i
Nas!''. Sidi mai Jaka yace da ni
yana zazzare idanu har da tande
baki kamar tsohon maye.....
LINZAMIN SHAIDAN-09
.
Ka bar dadi Nas!'' Sidi mai Jaka yace da ni
yana zazzare idanu har da tandar
baki kamar tsohon maye Tuni
har idanunsa sun fara zubar da
hawaye
''Wannan wacce irin masifa ce?''
Na tambayi kaina
Tsawon lokaci mai tsawo kamar
shekara a gurina kafin Sidi mai

Jaka ya gama tande-tande da
lashe-lashensa A lokacin da ya
gama tuni ya hada gumi shakaf
kamar ya hadiyi kunama
''Yauwa ko ni fa?'' Sidi mai Jaka
yace gami da yin ajiyar zuciya Bai
dami da wanke hannunsa ba
dan haka yana gama tande yan
yatsunsa sai ya goge sauran a
jikinsa ''Baka sha ruwa ba''
Nace da shi cikin kaduwa domin
na ga duk uban yajin da ya gama
sha bashi da niyar tashi domin ya
nemo ruwan sha ''Kada ka damu
Nas wani lokaci haka na ke yaji
bai fiye damu na ba kuma ko a
banza ma ai shan yajin maganin
Mura ne a gareni''
''Haka ne..'' Nace da shi bakina
na rawa Sannan sai na dada cewa
''Me yasa to ya kashe ta?'' Sidi
mai Jaka ya zura min idanu yana
tandar baki kamar wanda bai
fahimci abin da nake nufi ba A
dai-dai lokacin da nake kokarin
maimaita tambayata sai ya yi
murmushi yace
''Oho..!
Nas ke nan naci gaba da labarin ka ko? Yanzu kuwa ai tun
da na ci Tubani to babu abin da
zai hanani 'karasa maka
zarurrukan labarin da muka bari
can baya.
''Haka ne''. Nace da shi.
Sidi mai Jaka ya gyara zama,
bayansa a jingine da bangon
'kofar gidan sannan ya fara da cewa....
.
'Nas mutanen duniya sai dai a
barsu akan son duniya...''. ''Don
me kace haka?''.
''Yauwa saboda lokacin da Jabir
ya tambayi Gambo dalilin da ya sa
ya kashe ta, sai Gambo ya
dubeshi shekeke yana cewa....''
Na katse shi da cewa. ''Ka sauya
salon labarin. Baba Sidi...''. 'Dan
tsohon ya dubeni cikin mamaki
ya ce, ''Ban fahimce ka ba Nas?''.
''Abin da na ke nufi shi ne, salon
labarin na ka a yanzu ya koma
kamar salon labarin da, irin na

magabatanmu''.
Sidi mai Jaka yai murmushi,
sannan ya ce, ''Na fahimce ka
Nas, to saurara da kyau na
'karasa maka wannan zaren''.
*** *** ***
.
.
''Amsa kuwwar sautin attajirin ta
cika dakin sa'ar da matarsa Laila
ta fadi akan 'kafar Jabir. Jabir ya
dubi Gambo a karo na biyu,
sannan ya sake maimaita
tambayarsa.
''Me yasa ka kashe ta?''.
Gambo ya dubi hancin bindigarsa na tururi lokaci guda
kuma ya dubi matar da ke kasan
dakin matacciya ya ce. ''Tauna
tsakuwa nayi, wai don Aya taji
tsoro''. ''Tauna tsakuwa?''. Jabir
ya tambaya a sakarce. ''Kwarai
kuwa....kuma har da kariyar
kanmu da kanmu''. Gambo ya ce
yana duban Jabir. A lokacin ne ya
lura ashe sauran mutane biyun
da ke ta kwasar kudin sun
dakata, shi kawai suke kallo cikin
kaduwa, domin basu taba
tsammanin al'amarin zai juye da
kisan kai ba. ''Ku kwasa mana!!''
Gambo ya buga musu tsawa a
fusace.
''Kun tsaya sororo sai kallona
kuke kamar wanda ya aikata
wani mummunan aikin da babu
wani daga cikin ku da zai iya
aikatawa.... Wannan abu nayi ne
dan kare kanmu, domin mace ba
abar yarda ba ce''. Gambo ya ce
gami da nuna gawar Laila da ke
kwance, shi kuma Attajirin
kwance akan gawar sume.
''Shi dai yana iya yin shiru da
bakinsa, domin in ya sake ya
kirawo jami'an tsaro bashi da
mafita dole ne ya yi musu
bayanin inda ya samo kudin. To
amma matarsa ta san komai, duk
ta ga wasu daga cikin
kamanninmu.....
Barinta a raye
hadari ne!''. Ya dan yi shiru

yana mai da numfashi, sannan
shima sai ya sunkuya ya fara
diban kudin yana zubawa a
cikin wata budaddiyar jaka
baka da ke gabansu.
Jabir ya rasa ta cewa, dan haka
shima ya durkusa aka fara
kwasar kudin da shi. Amma fa
duk da haka tuni al'amarin ya
gama ficewa daga cikin
zuciyarsa. Wani mummunan
tunani ya darsu a doron
zuciyarsa sa'ar daya dubi gawar
Laila, yanzu idan wani ya harbe
Tani abar kaunarsa yaya zai yi?
Tunanin hakan kawai shi ya sa
wani zazzafan gumi fara
tsatstsafowa kan goshinsa, to
amma duk wannan kafin su ji
mummunan harbin bindigar a
waje ne.
Mutanen hudu suka mike tsaye
lokaci guda suka yi cirko-cirko da
su kamar zakaru. Cikin 'kokarin
'kin yin imani da abin da suka ji,
sai dai kuma babu ko shakka
sautin bindiga ne domin kafin
ma wani daga cikinsu ya sami ta
cewa wasu 'karin sautin harbe-harben suka sake gauraye
shirun
da ke daren.
Daga can waje suna iya jiyo
sautin sawu ana ta guje-guje.
''Yan sanda!''. Gambo ya ce da
sauri cikin kaduwa yana jujjuya
bindigar da ke hannunsa.
''Kai ka janyo mana. Laifin ka ne
Gambo! Jabir ne yace hakan ba
tare da wata fargaba ko rawar
baki ba. ''Laifi na?''. Ya tambaya a
fusace ''kwarai kuwa inda baka
yi harbi ba wa ya san muna nan?''
Gambo ya kurawa Jabir idanu a
kufule domin ji yake yi kamar ya
sa gindin bindiga ya buge shi
''Ka iya bakinka Jabir...wata rana
bakin ka zai kaika ga halaka!....''
''In bakina bai kai ni ga halaka ba
ai ga shi kai ka kaimu kan
hanyarta'' Jabir ya ce yana
sauraron takun sawun duf! duf!
a zagayen gidan

''Cacar baki ba zai kaimu ba gara
mu sami mafita mu tsere tun
kafin su cimmana muna surutan
banza'' Wani dogo daga cikinsu
ya ce lokaci guda kuma idanunsa
na kallon akwatin da ke kasa a
cike da kudi Jabir ya gyada kai
cikin gamsuwa yana duban
Gambo
''Sai ka fitar da mu'' Jabir ya ce
yana share gumi daga goshinsa
''Ta....ya....ya zan fitar....da ku?
Kowa tasa ta fishsheshi'' ''Kada
ka ce haka Gambo....'' Karar
mummunan sautin da suka ji a
waje shi ya katse Jabir ''Yan
sandan sun shigo...'' Gambo ya
ce cikin kaduwa. Nan da nan ya
nufi kofar dakin a firgice
Sauran mutum biyun suka bishi a
baya amma Jabir na nan tsaye
daf da inda tagar dakin take
''Taho mu fice shashasha'
Gambo ya daka masa tsawa Jabir
yayi banza da shi lokaci guda
kuma ya durkusa cikin gaggawa
ya rufe akwatin kudin da ke
'kasa ya dauketa, sannan ya dubi
fuskar matsoratan ya ce. ''Abin
da ya kawo ni ke nan, dan haka
tsoro ko fargaba basu isa su
hana ni fita da kudin nan ba,
domin in ba dan su ba da babu
abin da zai kawo ni nan''. ''Baka
da hankali..... Ta yi nauyi da yawa
baza ka iya gudu da ita ba''.
''Ku fita mu hadu a inda muka
bar motarmu.... Zan kawo muku
kudin''
.
Mutananen uku sukayi tsaye na
dan lokaci suna kallon Jabir, shi
kuma yana tsaye yana kallonsu
da akwatin a rike a hannunsa.
Abinda suka gani a fuskarsa shi
ya hana su sake yi masa jayayya,
domin akwai wani yanayi da ke
fuskarsa da ke nuni da cewa ko
ta wane hali, ko wuya ko dadi
babu abin da zai

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment