Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan na ci
TUBANI haka yake yi min wannan
tsiyar sai ka ga yana neman sa ni
barci lokacin kwanciyata bai yi
ba''
''Haka ne'' Na ce da shi ina mai
mamakin yadda za'ayi mutum
yaji barci lokacin kwanciyarsa bai
yi ba
''Ina suka nufa da su Jabir ke
nan?'' Na tambayeshi cikin doki
domin na fahimci cewa labarin
ya fara sauya salo
Sidi mai Jaka ya sake jan
doguwar hamma mai barazanar
hadiye duk abin da ke kusa da
shi ya ce
''Haba Nas ai ya kamata yanzu ka
fara gane yadda nake hada
zarurrukan labarina In ka lura da
kyau ai karshen wannan zaren
labarin ke nan dole ne sai na
saka masa dan uwa kafin na
jona shi da wannan mu ci gaba''
''Ina sauraronka'' Na ce da shi
Sidi mai Jaka ya dubeni na dan
tsawon lokaci sannan sai ya fara
da cewa
''Nas dauki zuciyarka da
tunaninka baki daya ka mayar
da su can wata rugar fulani
kimanin kilomita dari da shirin
daga birnin Gongola''
''Gongola kuma?'' Na tambaya
cikin mamaki ''kwarai kuwa ai a
can ne zan sako maka sabon
zaren labarin Kasan kamar gizogizo na ke wajen iya saka
zarurruka... To sai dai ni ban iya

rubutu ba''. Sidi mai Jaka ya yi
shiru na dan lokaci, sannan ya
dora.
.
Wata ruga ce Nas, wacce ke
zaune ita kadai a tsakiyar wani
daji. A daren wani lokaci da ya
wuce ba karamar riga bace,
domin akwai fulani makiyaya
sama da talatin da biyar a rigar.
To amma da zamani ya tsawaita
sai ya zamanto babu kowa a
rigar, daga Malam Ja'e sai
matarsa Gudidi.
Malam Ja'e yana zaune a rigar ne
shi kadai a halin yanzu, domin
sauran 'yan uwansa Fulanin rigar
tun sama da shekara goma suka
bar rigar. Akwai dalilin da ya sa
Malam Ja'e yake zaune a rigar. Na
farko dai tun suna 'kanana shi da
'kannensa, iyayensa suka zo da
su rugar. Iyayensa ne suka fara
zama a gurin tun daga lokacin ne
fulani sukan zo su yada zango na
'yan watanni ko shekara su
wuce. Haka nan wasu kuma su
maye gurbinsu, domin Allah ya
albarkaci gurin da fadamu da
kuma koguna da yalwar abincin
dabbobi sama da shekara ashirin
da wani abu iyayen Malam Ja'e
suna gurin. Ran nan, katsam! Sai
Allah ya yiwa iyayen Ja'e rasuwa,
a lokacin duka-duka bai fi
shekara goma sha biyar ba a
duniya. Haka nan watansa uku
kacal da auren Gudidi diyar wani
sarkin riga da ke kimanin kilo
mita uku daga rigarsu Ja'e.
Mutuwar iyayen nasa ta sauya
masa al'amari, domin sa'ar da
Rani ya kawo kai sai 'yan uwan
ubansa suka nemi da su yi gaba
suga abin da hali zai yi, domin
duk da yawan fadamun da ke
gurin abincin dabbobinsu ya fara
yankewa, saboda yawansu.
Aka kada aka raya, Ja'e ya buka
kasa ya ce sai dai su tafi su
barshi a gurin, domin bai taba
yin nisa da kabarin iyayensa.

Tun daga lokacin Ja'e ya share
gindin zama na din-din-din a
rigar. Duk an watse an barsu
daga shi sai wani takadarin
'kanensa marar jin magana. Tun
wannan 'kanen nasa yana
'karami ake fama da shi domin a
kullum kwanan duniya sai ya
tsokani manoman 'kauyukan da
ke daf da rigar fada. Tun
iyayensa na da rai suke fama da
wannan takadarin yaro, dan
haka sa'ar da iyayensa suka
mutu sai duk Janhurun wannan
'kanen na Ja'e ya dawo kansa,
domin a lokacin yaron ya zama
saurayi, ga shi kuma dogo
'karkarfa, kullum sai sunyi fada
da matar Ja'e. Wani sa'in sai Ja'e
ya dawo daga kiwo sai ya tarar
'kaninsa ya yi mata dukan tsiya
ya daure ta a cikin daki. Wani
sa'in sai ya yi ma ta tsirara
haihuwar uwarta sannan zai
barta a haka Ja'e ya sameta. Idan
Ja'e ya tambayi dalili sai yace.
''Bata da kunya ne shi ya sa.
Kuma kullum sai ta yi min
'kwauron miya idan za ta zuba
min dumame''.
Babu abin da Ja'e zai iya domin
'kanen nasa ya gama tsoratashi,
ya sa masa arwa, gashi dai a
doke bai dakuwa, domin akwai
ranar da Ja'e ya taba 'kokarin
nuna masa cewa shi fa a
gabansa yake amma sai wasan
ya baci domin kanen ya daga
Ja'e ya buga shi da 'kasa ya taka
sannan ya zaro babarbariyar
wuka ya dora a doron wuyan
Ja'e ya ce
''Idan ka sake shiga hanyata sai
na yanka ka na aure matarka
Tun daga ranar Ja'e ya tsorata da
shi. Wata rana katsam! Sai 'kanen
nasa da rana ana hunturun sanyi
sai ya ce da Ja'e ''Ja'e ni zan
shiga duniya, na ga wainar da
ake toyawa'' Ja'e ya dubi fuskar
'kanin nasa a tsorace ya ce.
''Duniya wajen ina?''

Ja'e ya dubi fuskar
'kanin nasa a tsorace ya ce
''Duniya wajen ina?''
''Nima kaina ban san ina zani ba.
Zan shiga birni ne domin naji an
ce mutanen birni na can suna ci
da rabonmu''. Saurayin ya mike
tsaye, sannan ya saba sandarsa a
kafada ya ce. ''Sai abin da hali ya
yi. Me yiyuwa wata rana in na
waiwayeku na taho ma da
burodi na san sau daya ka taba
cin shi''.
Tun daga ranar Ja'e bai 'kara
ganin 'kaninsa ba. Ya yi murna
da hakan, domin kusan shekaru
goma sha biyu da tafiyar 'kanen
nasa ya yi zaman lafiya da
matarsa, su yi kiwon
dabbobinsu, suyi noma. Malam
Ja'e bai damu da duniya ba, sai
dai kuma abu daya ke damunsa,
tun da yake bai taba haihuwa da
matarsa Gudidi ba''.
.
Sidi mai Jaka ya yi shiru sa'ar da
ya kawo nan yana dubana.
''Na gama baka hoton abubuwan
da suka faru a wancan tsawon
zamani. Bari kuma na jona maka
da sabon zamani
.
''A wannan safiya Nas Ja'e ya
tashi tun sassafe ya fara shirin
tafiya gona domin uban ruwan
da aka kwana ana tafkawa an
dade ba a yi irinsa ba
''Gudidi ina kike ne? Gara fa mu
hanzarta tun kafin hantsi ya
hudo''. Gudidi ta fito daga cikin
bukkar dauke da buhun irin
geron da za su shuka, gami da
Akusa guda biyu a kanta na dan
abin da za su jefa a bakin salati
idan sun je gona.
''Mu tafi ko''. Gudidi ta ce cikin
gurbatacciyar Hausa.
Suka kama hanya abinsu tinkistinkis. Malam Ja'e na gaba ya
saba sungumi a kafada, ita kuma
dauke da Akushi da buhun irin
butar duma ta ruwan sha. Duk

kusan inda ka duba a gurin kore
shar yake da ciyayi, hanyar da
suke bi a yanzu tana da dan
fadin gaske, domin hanyar an
saba binta da Amalanken shanu,
amma duk da fadin hanyar sai
ciyawa gambar da ke gefe tayi
sahu-sahu ta fara barazanar rufe
hanyar.
A dai-dai lokacin da da suka
kawo daf da wata mahada
hudu ne to suka ji gurnanin
mota.
''Me ce wannan?''. Gudidi ta
tambayi mijnta Ja'e cikin mamaki.
''Kamar kukan mota''. ja'e ya ce
da ita cikin shakka. Domin sai ya
yi shekara bai ga mota ba...domin
in ba birni yaje ba ba zai taba
ganin mota ba a nan gurin,
domin tun da yake bai taba
ganin mota ba, yana ganin
Amalanke amma ba mota ba. Tun
da Ja'e yake sau biyar kawai ya
taba ganin mota a birni.
Sautin motar ya dada matsowa
inda suke. Nan da nan suka ratse
daga hanyar suka yi cirko-cirko
suna jiran su ga abin da zai bullo.
Suna nan tsaye kuwa sai suka
hango katuwar motar baka ta
nufo inda suke. Ja'e ya dubi
matarsa Gudidi cikin mamaki.
''Me yiyuwa Malaman boko
ne....domin wani abokina a birni
ya gaya min cewa suna bi rigariga suna koyawa fulani karatun
boko''.
Motar ta zo daf da su kamar za ta
wuce. Ja'e ya fara daga wa
motar hannu. Ga mamakinsa sai
ya ga tayi cak! a gabansu ta
tsaya.
''(Hande in boni) na shiga uku..''.
Gudidi ta ce a tsorace, domin ta
sha jin labarin 'yan yankan kan
mutane da ke bin 'kauyika da
rigage. Malam Ja'e ya yi kasake
ciki ya duru ruwa yana duban
motar a rude. Wata zuciyar na
cewa da shi ya ruga ya shiga
cikin daji... Sai dai kuma idan ya

ruga ai ga matarsa Gudidi.
Ja'e ya yi mutuwar tsohuwa a
gurin, gashi kuma wani abin
'karin tsoro ga al'amarin ba ya
iya ganin mutumin da ke cikin
motar sabo da yanayin duhun
gilashin tagar motar. Ga shi dai
ni'imtacciyar iskar damina mai
dauke da kwayoyin ruwa sai
busawa take yi gwanin dadi a
cikin dajin, amma duk da haka
Ja'e gumi yake yi tun daga sama
har zuwa marainansa a jike suke
saboda kaduwa.
Tsawon lokaci suna tsaye, itama
motar na tsaye, sannu a hankali
sai kofofin motar baki daya
suka bude lokaci guda.
Numfashin Ja'e ya dauke sa'ar
da ya ga wasu irin mutane masu
kusan kama daya, suna sauka
daga motar kowannensu sanye
da bakaken kaya. Ja'e ya 'kirga
su a ransa, su hudu ne mutanen.
Ja'e ya gama yanke 'kauna,
mutuwa zai yi, domin ko shakka
ba ya yi 'yan yankan kai ne.
Akushin da ke hannun Gudidi ya
'kwace, abincin ya kife a cikin
ciyayi. Gudidi ta zagaya bayan
Ja'e ta rike kafadarsa jikinta na
rawa. Wani 'kato daga cikin
mutanen hudu ya rabu da
sauran ya matso daf da Ja'e,
sannan ya cire tabaransa suka yi
ido hudu da Ja'e.
''Yaya Ja'e! Har yanzu dai kana
nan da tsoron nan na ka?''. Wata
sassanyar iska ta kada tsirran da
ke dajin. Ja'e yaji gabansa ya fadi
sa'ar da yaji muryar.
.
''Shin baka
gane ni bane Ja'e?''. Nan da nan
Ja'e ya jefar da sungumin da ke
kafadarsa ya dubi fuskar mutumin
Bakinsa na rawa ya ce.
''Ko ina....a ko....ina, indai ina da rai,
idan naji muryar nan sai na gane
mai ita... Na gane ka bawan
Allah kai ne dan uwana na jini
'kani na Gambo !''

''GAMBO kuma?''
*
Sidi mai Jaka ya fashe da dariya
sannan ya ce Da a ina hankalinka
ya ke? Yanzu ashe kai Nas har
abada ba ka iya gane yadda na
ke saka zaren labarina?''
''To amma ai ya kamata tun farko
ka fada mana sunan 'kanin
Ja'en'' Na ce da shi
''In da ban yi hakan ba kuma na
bada kai.. Ai hakan shine labari''
Sidi mai Jaka ya ce Sannan ya ci
gaba
''Kai dai biyoni mu dora da
wannan labari
Wata daya da 'yan kwanaki
da zuwansu rigar ku..''
''A'a ai kuma ka tsallake baka
bani labarin abin da ya faru ba
sa'ar da Ja'e ya gane cewa dan
uwansa Gambo ne ya dawo''
Sidi mai Jaka ya shafi fuskarsa da
busassun hannayensa ya dubeni
ya ce ''Wani lokaci mutane na
ban mamaki Yanzu ace dai ku in
za a baku labari sai an baku
labarin komai da komai har
'kurunkus!? Haba Nas ai idan
aka ce sai an fadi komai da
komai na labari to sai ayi
kwanaki ana yi har wuyan
mutum ya fara ciwo Tsoho
kamata Nas bai kamata ace ya
cika yawan magana ba''
''Hakane'' Na ce da shi lokaci
guda kuma ina mai mamakin
yadda yawan magana zai sa shi
ciwon wuya in har manyamanyan Tubanin da ya hadidiya
ba su sa shi ba''
Nas, ina son ka dauka a zuciyar
ka cewa tuni Gambo da yaransa
sun yi wata guda a maboyarsu''.
Sidi mai Jaka ya ce da ni. ''Na
dauka to''. Na amsa masa.
''Yauwa Nas..... To wata safiya,
wacce ta zamto ita ce safiyar su
ta talatin da uku da zuwa rigar.
Gudidi matar Ja'e na zaune tayi
tagumi a gindin runbu,
daddadar iskar safiyar damina

na bugun fuskarta. Katsam! Sai ta
ga kyakkyawar Malamar asibitin
nan da su Gambo suka zo da ita
ta fito da sauri daga cikin bukkar
da take kula da marar lafiya. Tana
fitowa farfajiyar sai ta fara keta
amai a cikin shuke-shuken duma
da kabewa. Gudidi ta dubi
kyakkyawar matar cikin
tausayawa sabo da kakarin aman
da take yi.
Gudidi ta yi kamar ta tashi taje
kusa da ita, domin ta tallafa mata,
amma tsoro da fargabar
kashedin da Gambo ya yi musu
ita da mijinta Ja'e ya hanata.
Gudidi ba za ta taba mantawa
da ranar ba. Domin sa'ar da
mijinta Ja'e ya gane cewa dan
uwansa Gambo ya dawo, sai aka
zubosu a 'katuwar motar aka
dawo da su riga. Sa'ar da suka
dawo rigar duk sai suka sa su a
gaba kamar za su hadiye su.
Gudidi bata taba jin fargaba a
rayuwarta irin ta ranar ba, domin
duk da cewa ta gane Gambo
amma hankalinta bai kwanta da
shi ba. Ta tuna da wani zamani
da ya wuce a lokacin ma Gambo
ko rabin haka bai kai a girma da
kwarjini ba, dan 'kauye, amma
duk da haka sai ya dankara mata
shegen duka ya yi mata tsirara, in
kuwa haka ne to me za tayi
tsammani daga Gambo wanda ke
tare da wadannan mutane masu
kamar shaidanu a yanzu?
''Bukkoki biyu kawai kuke da su
a rigar nan?''. Ita ce tambayar
farko da Gambo ya yiwa dan
uwansa Ja'e sa'ar da aka dawo
da su rigar.
''Su...ke nan''. Ja'e ya amsa masa
bakinsa na rawa. ''Ina son yanzu
nan duk ku kwashe tarkacen ku
daga ciki....yanzu-yanzun nan ba
sai an jima ba!''. Ja'e ya dubi dan
uwansa a tsorace ya ce. ''Babu
komai a ciki...amfaninta a garemu
daman sai lokacin rani a ciki
muke ajiye korika..''

Gudidi tayi matukar kaduwa
sa'ar da gambo yasa aka dauko
wani mutum daga bayan motar
ranga-ranga kamar matacce.
Haka nan suka dauko wani irin
sangalalin gadon siriri marar
nama. Gudidi bata taba ganin
irinsa ba. Aka shiga da mutanen
da gadon cikin bukkar. Ba'a jima
ba kuma sai Gambo ya sake
sauko da wata kyakkyawar mata
budurwa daga cikin motar
dauke da 'katuwar jaka fara.
Kallo daya gudidi ta yiwa matar
ta tabbata da cewa matar a cikin
takunkumi take. Gudidi tayi
matukar tausaya mata. Bayan an
shigar da matar ne bukka to sai
mutuanen hudu suka zagaye
gudidi da mijnta Malam Ja'e.
Sannan sai dan uwansa Gambo
ya dubeshi ya ce da shi cikin
kakkausar murya.
''Daga yanzu har zuwa lokacin da
zamu bar rigar nan bana son in
sake ganin wani a cikinku ya
leka ko da dai-dai da bayan rigar
nan... Kada kuma wani a cikinku
ya kusanci waccan bukkar da
muka sa mutanen can biyu a
cikinta''. Gambo ya yi dan shiru
yana duban Ja'e. ''Ina fatan ka
fahimta?''
Ja'e ya gyada kai a tsorace,
sannan bakinsa na rawa ya ce.
''Bamu da abinci....gashikuma
muna son muyi shuka...''. Gambo
ya dubeshi na tsawon lokaci,
sannan ya ce.......
LINZAMIN SHAIDAN-14
.
Ja'e ya gyada kai a tsorace,
sannan bakinsa na rawa ya ce.
''Bamu da abinci....gashikuma
muna son muyi shuka...''. Gambo
ya dubeshi na tsawon lokaci,
sannan ya ce. ''Duk abin da kuke
bukata na abinci mai dadi muna
da shi....Zancen noma kuwa ka
manta da shi, babu rabon ku yi
wahala a wannan shekara.
Dabbobinka kuwa na yarje maka

ka fita da su nan bayan rigar nan
tun da dai damuna ce na san
akwai abincin da zai ishe su ba
sai kayi nisa ba''. Gambo ya yi
shiru, sannan sai ya zaro bindiga
daga aljihun kwat d'insa ya dora
ta a daf da fuskar Ja'e ya ce. ''Ina
fatan ka san wannan?''. Ja'e ya
gyada kai jikinsa na rawa, domin
ya sha ganin doguwarta a gurin
maharba. ''Kana iya yin gudu
idan ka so... Amma kar ka zargeni
idan ka sami kanka a kiyama a
cikin dakika guda...
Kada kuma
ka manta duk inda za ka zagaya
kiwo jama'ata suna lura da kai...
Da zarar kayi niyyar gudu to
sunanka matacce''. Gambo ya
numfasa sannan ya dago kai ya
dubi Gudidi ya ce da ita cikin
busasshen murmushi. ''Gudigudi! Ke kuwa daman kin san
halina....!''. Wannan kawai ya isa
ya gama tsorata Gudidi tun daga
ranar suke zaman wakafi, bata
motsawa nan da can. Gara ma
mijinta Ja'e sukan barshi ya dan
zagaya kiwo bayan gida.
.
Bayan kaman wata 3 da gudu
tafito
Malamar Asibitin ta ci gaba da
sheka amai cikin ciyayi. A dai-dai
lokacin da Gudidi ke 'kokarin
tashi domin taimaka ma ta ne sai
ta hangi Gambo ya nufi inda
Malamar asibitin ta ke nan da
nan Gudidi ta sauya niyyarta ta
farko. Amma ga mamakinta sai ta
hango Gambo na ma ta alama da
hannu akan taje yana kiranata.
Nan da nan jikinta na rawa ta
gyara tsumman zaninta ta nufi
inda yake. ''Me ke damunki?''.
Gambo ya tambayi Tani ya yin da
Gudidi ta 'karaso ta tsaya daga
can gefe. Tani ta mumfasa ta ce,
''Ji nake yi cikina shi kadai yana
birkitawa''.
Gambo ya dubeta na dan lokaci...
Bai yi mamaki ba dan cikinta ya

birkita, domin shi kansa ba
kasafai ya fiye son shiga bukkar
da Jabir yake ba, domin 'kafarsa
ta fara doyi, saboda har yanzu
alburushin bindigar na ciki ba a
cire su ba, ga shi kuma har yanzu
ya kasa magana. Gambo ya dubi
Tani ya ce da ita.
''Ki bi Gudidi ku tafi ku dan
zagaya... Kuna iya fita nan baya
ku dan sha iska, zama guri
dayane da kuma iskar da kike
shaka
a cikin bukkar can suka ruda
miki ciki''. Gambo ya dan yi
shiru sa'annan ya harari Gudidi
ya ce. ''Gudidi ga ta nan ku tafi
tare ku dan yawata''. Har suka
fice daga rigar Gambo na kallon
Tani. Wani abu mai kamar tausayi
ya dan yi zarya a zuciyarsa.
.
Wata daya da 'yan kwanaki duk
ta
rame.
Sa'ar da Gambo ya tabbata sun
fice daga rigar sai ya yi fito da
'karfi. Nan da nan su Lanto suka
shigo rugar. Tun kusan asuba
suke zaune a bayan rugar akan
ciyawa suna karta. Gambo ya
dubi mutanen uku ya ce.
''Al'amura fa sun rikice.. Kun ga
dai dan iskan nan har yanzu
yaki ya bude baki balantana ma
ya yi mana magana... Ya ya kuke
gani, kun ga dai 'yan kudin ma
duk sun kare, dan ina kyautata
tsammanin in har muka kara
wata biyu a rigar nan dole ne sai
mun fita daga maboyarmu
domin
mu nemi 'karin kudi'. Gambo ya
yi shiru yana dubansu cikin
damuwa.
Lanto ne ya fara magana a
cikinsu. ''Ni a gani na abin da
zamu yi sai mu dan 'kara hakuri,
domin abin da kawai muke
bukata shi ne ya fada mana
inda ya boye kudin, yana fada
mu gama da shi, sai kawai mu

'karasa shi ya huta da wahala,
mu ma mun huta....''.
Gambo ya
gyada kai cikin gamsuwa ya ce.
''Ka fadi gaskiya Lanto.... Sai dai
kuma abin da nake fargaba shi
ne idan abin nan ya dauke mu
tsawon lokaci a ina zamu sami
kudin da zamu ke sayo
maganunnukan da take bukata
da kuma abinci?''. Lanto ya dubi
shi cikin murmushi ya ce. ''Ina
inyamurinka da ya baka hayar
mota da bindigogi? Ai ina
tsammanin in aka tsara masa
halin da ake ciki zai iya yin
motsi''. Gambo ya fashe da
dariya, ya yi tsalle ya dafe
kafadar Lanto yana cewa. ''Lallai
kanka yana ja dan samari''.
*
A can bayan rigar, a gindin
bishiyar kanta, Gudidi zaune kusa
da kyakkyawar matar, ita tana
kuka Tani ma tana kuka. Tun
sa'ar da suka dan bacewa rigar
Tani ta kwashe duk labarinta ta
fadawa Gudidi. To amma a
yanzu kukan da Tani take yi yana
da wata manufa daban.
''Ki yi hakuri, komai mai wucewa
ne in Allah ya yarda, zai kawo
mana 'karshen wannan masifar''.
''Abin....ya yi min yawa....sun
rabani
da 'yan uwana....sun nakasa
masoyina.....gashi kuma....'' Ta
sake fashewa da kuka kamar
ranta zai fita. Gudidi ta rude,
tausayin wannan mata ya
mamaye ma ta zuciya.
''Baiwar Allah ki bar kukan haka
nan ya isa...ke da ba lafiya ce da
ke ba''. Tani ta dago fuska ta
dubi Gudidi idanunta sharkaf da
hawaye ta dafa kafadar Gudidi
ta ce bakinta na rawa. ''Baki
gane...dalilin kuka na ba Gudidi....
CIKI NE DA NI!
Ban ga al'adata ba.
Cikin Jabir ne a jikina!!!''. Ta sake
fashewa da kuka

*
Sidi mai Jaka ya dada jan
doguwar hamma.
''Matsalar Tubani ke nan Nas
Wani lokacin haka yake yi min
irin wannan lalatar.. muddin na ci
Tubani to barci ya dinga damuna
ke nan'' Ba abin da ya fada na
ke sauraro ba abin da ke raina
shi ne da ya ce da ni..
WAI TANI TANA DA CIKI!..
.
Wane irin ciki kuma?''
Sidi mai Jaka ya matsa idanunsa
da busassun 'yan yatsunsa ya ce
''Ka manta masha'ar da suka
aikata ita da Jabir? Na dauka na
baka labarin dazu kafin sallar
magariba?''
''Oh! Na tuna haka ne...''
''Yauwa Nas.. To yanzu kuma zan
sake katse wannan zaren labarin
mu koma can gaba..'
''Bayan watanni uku da yan
kwanaki...''
Na dubeshi cikin damuwa na ce
''Amma Baba tsallaken naka ya yi
yawa.. Ya ya za ka tsallake ka
koma bayan watanni uku bayan
kuma baka bani labarin abin da
ya faru daga wata daya zuwa na
ukun ba..?''
Sidi mai Jaka ya fara soshe-soshe
''Nas yanzu ashe in za'a baka
labari sai an yi ta fadar komai da
komai? In ban da abin ka ai duk
tsawon wata daya zuwa na uku
ba wani abu da ya faru
muhimmi duk zaman jiran Jabir
suke yi amma a banza domin ya
ki ya bude baki balantana ma ya
yi musu maganar komai.. To sai
dai kuma cikin Tani ya fara
girma''
Sidi mai Jaka ya dan yi shiru..
Sa'annan ya ce. ''Nas, bari na
tsallae da kai zuwa wata uku
domin kaji yadda zata kaya...
Wannan shi ne zaren labarin mu
na biyun 'karshe...''.
Sannan ya ci gaba.
''A wata safiyar Laraba, wacce ta

zo dai-dai da watan su na uku da
kwana goma sha uku a rigar.
Tani na zaune ta sa Jabir a gaba
tana zubar da hawaye, domin ta
san koda Allah ya kubutar da su
daga 'kangin da suke ciki da
wuya idan har 'kafarsa zata sake
amfanuwa, domin 'kafar da aka
harba ta kumbura suntum! sai
doyi take yi tana zubar da
ruwa...abin da ya fi damun Tani
shi ne Jabir ya 'ki koda bude
idanu balantana ma ya yi
magana. A cewar Gambo; da
zarar Jabir ya yi musu magana za
su tafi su barta da abin 'kaunarta
Jabir!
To amma a wannan safiyar
Laraba sai Tani ta sunkuya daf da
fuskar Jabir ta ce. ''Jabir....
Darling....!''.Shiru na dan lokaci
bai ko motsa ba.... To amma yana
numfashi. ''Jabir...''. Ta sake kiran
sunansa muryarta a raunane. Ga
mamakin ta sai Jabir ya bude
idanu ya yi mata murmushin
yake. Tani taji numfashinta ya
dauke. ''Jabir...!'' Ta kara
kunnenta a dai-dai bakinsa
domin taga yana 'kokarin fada
mata wani abu. ''Tani kada ki
daga muryarki sama har su gane
cewa da ni kike magana...''. Jabir
ya yi shiru yana matse idanu
saboda tsananin ciwo. Sannan ya
ci gaba.
''Tani...kiyi hakuri ki fitar da
tunanina daga zuciyarki...domin
bani da wani amfani a gareki,
ban dace da ke ba..... na lallata
rayuwata, na biyewa shaidan da
rudanin zuciya, na yi kuskure....
Tani wadannan mutanen da kike
gani marasa imani ne.... 'Yan
fashi ne, haka nan nima ina daya
daga cikinsu...''. Jabir ya yi shiru.
Tani ta dubeshi tana kuka.
''Magana ta 'karshe Tani ita ce
koda wasa kada kice musu
munyi magana da ke....domin da
zarar kin fada musu to sunanki
matacciya! Duk abin da ake ina

jinku shiru kawai na yi domin
kudin da muka sato ni kadai na
san inda suke, da zarar na fada
musu inda kudin suke bani da
wani amfani a garesu, kashe ni
za su yi su kashe ki. Ina sonki
Tani.....ina 'kaunarki....gara na
mutu a haka da inyi magana da
su, domin ina yi kashe ki za su
yi.... Wannan shine abu na
'karshe da zan yi miki amatsayina
na masoyinki.....!''.
.
A can bayan rigar Gambo da
Lanto suka shiga cikin motarsu,
sannan Lanto ya tuka suka nufi
wani 'kauye inda a nan zai sauke
Gambo shi kuma ya dawo gida.
''Daga 'kauyen babu wuya zan
sami motar da za ta shiga da ni
birni cikin dare''. Gambo ya ce da
Lanto sa'ar da suka fara tafiya a
cikin motar.
''Ina kyautata tsammanin
hakanmu ta kusa cimma
ruwa...domin Tani ta ce da ni jiya
ya fara bude idanu.... Na ce da ita
da zarar ya fara magana tai
kirana....''. Gambo ya yi shiru.
''Kamar nawa kake jin za ka
ranto a gurinsa?''. Lanto ya
tambayeshi. ''Dai-dai misali dai....
Zan ranto kudin da zai iya saya
mana abinci da maganunnuka a
'kalla na wata uku..''. Gambo ya
numfasa lokaci guda kuma ya ci
gaba. Lanto ya ragewa motar
gudu sa'ar da suka kawo daf da
wata mahada-hudu. ''In dai ka
bi da shi a hankali ka nuna masa
romin al'amuran da wuri zai
hadiyi 'kugiyar.... Ka san
Inyamuri da son sata?''. Lanto ya
ce da shi....''.
*
Sidi mai Jaka ya dubeni ya ce,
''Wannan zaren labarin
'karshensa ke nan, dama ba shi
da tsayi. Bari kuma in saka maka
zaren 'karshe na wannan labari''.
''Ya ya na ga duk kamar sauri
kake yi ka gama bada labarin?''.

Na tambaye shi.
Sidi mai Jaka ya amsa kai tsaye.
''Barci na ke ji Nas, Tubanin nan
da na ci duk ya yi min bake-bake
a ciki kamar wanda na
hadiyi kyandira...
Gashi kuma.
LINZAMIN SHAIDAN-15
.
Sidi mai Jaka ya amsa kai tsaye.
''Barci na ke ji Nas, Tubanin nan
da na ci duk ya yi min bake-bake
a ciki kamar wanda na
hadiyi kyandira... Gashi kuma
dadin labarin yana neman ya yi
maka yawa...''
Sidi mai Jaka ya dada jan
doguwar hamma sannan ya ce.
.
''Nas ka mai da zuciyarka can
cikin wata kasuwa ta Gwari a
cikin Kaduna..''.
Me karatu yanxu haka muna A
cikin wani gida wanda ke dauke
da manyan shaguna guda biyu, a
cikinsu ana sai da kayan miya,
kamar su Agushi, Tattasai,
Busasshen Tumatir, da danyan
Attaruhu, Albasa... Kai har da
busasshen kifi da sauran
danginsu.
A cikin wani daki a gidan, wani
'katon inyamuri ya dauki jaridar
cikin damuwa. ''Har yanzu ba a
kama 'yan fashin ba''. Tun ranar
da aka yi fashi Uche ya shiga
cikin damuwa, domin sun yi da
Gambo cewa da zarar fashin ya yi
nasara zai dawo masa da motar
da ya dauka haya a gurinsa da
kuma bindigogin da ya karba.
Ba 'karamar kaduwa ya yi ba
washe gari sa'ar da ya karanta
jarida. A ciki an bada labarin
fashin da aka yiwa attajirin ya ce.
''Duk da yake sun badda
kamanninsu, hakan bai hana shi
gane su ba...''.
Jami'an tsaro sun tabbatar da
cewa shima attajirin mai tsohon
laifi ne, domin ya tabbatar da
hakan da kansa. A cewar

attajirin. ''Tun da aka kashe
matarsa LAILA, to bai damu da
zama a duniya ba... To amma duk
da haka ya bada sunan GAMBO a
cikin 'yan fashin''.
Tun daga ranar Uche ya shiga
cikin tashin hankali, domin ya
san da zarar an kama su Gambo,
to shima kashinsa ya bushe ke
nan. Uche ya zargi kansa da
wauta, domin mafiya yawan
lokuta ya kan dauki matakai da
kulawa kafin ya arawa 'yan fashi
kayan aiki. Shekarunsa ashirin da
biyar yana wannan harka.
Shekaru goma daga cikin
wadannan shekaru shima an
sha yin fashi da makamin da shi,
daga baya kuma da ya ga girma
ya kamashi sai ya yi ritaya, ya
zama turun barayi yana kuma
bada motoci da bindigogi ga
abokan sana'arsa.
Lokacin da ya sami labarin abin
da ya faru ga Gambo, sai ya shiga
damuwa. To amma daga 'karshe
sai dabara ta fado masa. Ya san
abin da ya kamata ya yi, domin ya
tabbata al'amuran Gambo sun
lalace tun da dai har ma an gane
kamaninsa, an kuma buga hoton
Gambo a jikin jaridu an ce duk
wanda ya ganshi ya bugawa 'yan
sanda waya. Attajirin da suka
yiwa fashin shi ya baiwa jami'an
tsaro hoton Gambo wanda suka
dauka tare ranar da aka yi liyafar
bude sabon gidansa.
Uche ya ajje jaridar cikin
damuwa. Hakika in dai har
jami'an tsaro suka cafke su
Gambo kafin su hadu to al'amari
ya baci masa ke nan.
Uche ya juya firgigit! Sa'ar da yaji
'kofar dakin ta bude. Gambo ya
shigo dakin yana murmushi. Sai
da Uche ya yi kusan minti guda
yana kallonsa cikin kaduwa kafin
ya tabbatar da sa'ar sa.
.
''Gambo....!!''. Uche ya ce bakinsa
na rawa. ''Ni ne dai ba wani ba...

Ka dauka ba zan dawo ba?''
Gambo ya ce lokaci guda kuma
ya zauna a kujerar da ke kusa da
Uche.
''Ya ya ake ciki ne...shiru Gambo?
In ce dai lafiya?'' Gambo ya
gyada kai, sannan ya ce da Uche.
''Saurara da kyau kaji''. Kusan
mintuna goma sha biyar Gambo
ya shafe yana tsarawa Uche duk
labarin abubuwan da suka faru.
Sa'ar da ya kawo aya sai Uche ya
gyara murya ya ce, ''Nawa ka ke
so yanzu na 'kara ma?''. Gambo
ya dubeshi cikin mamaki, domin
bai taba tsammanin Uche zai
amsa masa cikin gaggawa ba.
''Dubu dari biyar na ke so!''.
Gambo ya amsa. Uche ya yi fito ya
ce. ''Amma fa ka san da zarar kun
gano inda kudin ya ke za ka
kawo min miliyan biyu?''.
Gambo ya yi dariya. ''Kada ka
damu Uche, kudin da Jabir

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment