Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karbar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ.

Dedicated to
YUSUF KING__SKEEBOY👑🎧🎶🎤
🎧🎤🎶🎼🎸🎹🎙️🥁🎻
Shatan rapper reagea rb rap da kuma hausa hip hop brother of Zainab kalar camera and Na'im❤️.
I know everything about u is so good but one thing is wrong that you are not mind.

✍️📚Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë

Paid book #500👉2410673902
#YUSRAHMS#
Page 0️⃣5️⃣&0️⃣6️⃣
_________Da dare Fadilah tana zaune a bedroom ita kad'ai tayi tagumi idanuwanta a kumbure jin wayarta tayi qara yasa ta kalli wurin ganin sunan wanda yake kiran saida taji gabanta ya fad'i d'an tsaki tai tana kawar dakai bata d'auka ba har Kiran ya katse wani ya kuma shigowa nan ma bata d'aga ba da kamar minti biyu taji qarar message shima kamar bazata duba ba sai kuma tunani yazo mata tadau wayar tana budewa taga ya rubuta mata.

"Why not answer my call"?.

Wani tsakin ta kuma ja cikin takaici zatai cilli da wayar sabon sa'ko ya sake shigowa.

"I call u ad u're wasting my time, it is good".

Tana gama karantawa ta jefa wayar kan gado tana nufar window ta d'aga labule tana kallon wajen Mahat yadda ta haskaku da fitilu🌃 na qawa tai kyau balle dare ya rufa kusan tara da rabi...........

Jin motsin an bud'o kofa yasa da sauri ta juyo ganin wanda bata ta'ba zaton ganinsa a wannan lokacin ba ya shigo ga wani yanayi na 6acin rai da take hangowa a tare dashi yasa a firgice ta qame jikinta guri a tashiga uku meya kawo shi part d'insu har cikin bedroom d'inta a wannan daren Momy tasan da zuwan san......

Ganin ya nufo gurin ta yasa a gigice take neman bi ta gefensa ta fice a bedroom d'in fisgota yayi da qarfi yana dawo da ita baya zatai ihu yasa hannu ya rufe Mata baki fuska ba walwala yace.

"Fadilah ni sa'an wasanki ne dazan kiraki a waya ki'ki d'aga min nayi message d'inki ki duba ki share ni ko anfada miki yanzu irin dane!¿ Ki kama kanki kina qarqashi nane kin gane¿ sai abinda naga dama dake yanzu baki da iko da kanki koda da 'kiftawar idone".

Hawaye ne ya fara xuba Mata shar shar jin abinda yake fad'a innalillahi gaskiya rayuwarta ta fad'a cikin gagari yanzu tsakani da Allah ba amincewarta Abba ya d'aura mata aure da Al'ameen? Al'ameen Mahat fa?............

"Keee".

Jin saukar muryarsa yasa da sauri ta dawo cikin hankalin ta tana qoqarin qwace kanta daga ri'kon dayai mata cikin kuka tace "ka rabu dani ka sake ya Al'ameen meyasa zaka shigo min cikin rayuwata anaso dole ne"?..

Kaiya jinjina mata yana sakinta hanyar kofa ta nufa zata fita cikin tsawa yace "come back here Fadilah".

Tsawar dayai mata yasa ta a gigice ta qara gaba da gudu tana qoqarin bud'e kofa ta fita ya damketa yana sanyawa kofar lock ya zare key d'in ransa a 6ace ganin irin taurin kan da take nuna masa yace "Fadilah ki fad'a min me nayi miki a rayuwa da bakya sona"? Bata bashi amsa ba sai kokarin qwace kanta daga ri'kon dayai mata takeyi tana cewa "ya Al'ameen Mahat ka sake ni please ka rabu dani" bai sassauta mata ri'kon ba saima qara matseta yske a jikin shi har tana runtse ido yace "idan kinga na sake ki to kin fad'a min dalilin ki idan baki fad'a ba wallahi idan zamu kwana a haka bazan sake ki ba" jin abinda yace yasa cikin kuka Fadilah tace "ka sake min hannu na fita anan ya Al'ameen" ''bazan saki ba sai kin fad'a min"? Fadilah na shashshe'ka tace "wai ana so dole ne pls leave me alone nayi rayuwa ta ni kad'ai ce mace a cikin Mahat da dole saini pls ka sakeni?" Zuba mata ido yayi ransa na tafasa da irin qiyayyar da take nuna masa fili qarara wanda shi kuma kaf duniya babu wacce yake so sama da ita hum aiko zai bata mamak,,......,.....,..,.qwanqwasa kofar da akai ne ya katse masa tunanin da yake jin muryar Momy tana Kiran sunan Fadilan yasa ya saketa yaga iya gudun ruwanta zata bud'e ne ko a'a, tabdijan ga mamakinsa yana saketa yaga da gudu taje ta bud'e kofar kafin Momy tayi magana ta qara gaba aguje ko hijab babu balle takalmi haka ta nufi gidansu Al'ameen Mahat dad'in abun ma dare ne suna zaune sai ganinta sukai ta fad'o tana haki da kuka kamar ranta zai fita taje gaban Alhaji Musa tana durkusawa ta zuba gwiwoyinta a qasa tare da sake fashewa da kuka me ban tausayi tana cewa.

"Dan girman Allah Daddy ka rufa min asiri ka taimake ni kasa ya Al'ameen Mahat ya sake ni wallahi bana sonsa bazan iya zama dashi Daddy dan Allah kaje ka baiwa Abban mu ha'kuri bana son auren".

Kai Alhaji Musa ya d'aga Mata da serious face yace "Fadilah bakya son auren shine matsalarki akan haka kiketa 6ata hawayen ki hum Alhaji Aliyu ya'ki ya fahimce ni amma batare da saninsa ba zan dau doka a hannu na yanzu Ina Al'ameen d'in yake"?.

Cikin jin sassaucin abinda Alhaji Musan yace tasan koba komai dole zaisa Al'ameen ya saketa tace "yana part d'in mu gurin Momy".

''Ok tashi ki koma gida ki kwantar da hankalinki Ina nan zuwa yanzu zan taho miki da takardar sakin ki bari na nemi Al'ameen d'in tashi ki tafi".

Mi'kewa Fadilah fuskarta fal da tsananin murna da ganin girma da darajar Alhaji Musa tace "na gode sosai Daddy Allah ya saka da alkhairi".

"Ba komai Fadilah jeki".

Da sauri Fadilah ta fita dan ta koma bayan fitarta Ummi dake kallon Alhaji Musa daya mi'ke yana shirin fita tace "amma Alhaji baka ganin wannan abun da zakai cutarwa ne ga Al'ameen yana son yarinyar nan fa kamar ransa taya a yau ya aureta sannan ace ya saketa a yau gaskiya tsarin baiyi ba inaga kayi hakuri ka kyale idan ya tafi Barcelona ya dawo maybe lokacin ta sau'ko zata amince ta zauna dashi".

Kai Alhaji Musa ya girgiza yana cewa "kinga da Allah me d'a wato a matsayin ki na uwa kina tausayawa d'anki amma ita da yake ba kece kika haifeta ba kina maganar tayi hakuri saboda farantawa 6angarenki to ki sani bazai wannan dani ba nima ubane me adalci kuma zan tabbatar dashi a nan dole Al'ameen ya saki Fadilah koda hakan zai zamo sanadin rayuwarsa ne".

A damuwance Ummi tace "haba dan Allah Alhaji ya kake irin wannan maganar mara dad'in ji dan Allah kayi hakuri kar ka yanke hukunci cikin fushi ka tsaya ka sauka daga dokin xuciyar daka hau".

"No kefa ki barma 6ata bakin ki sakine saiya sake ta idan har bazaki taya ni muyi wa Fadilah adalci mu nema Mata yancinta ba to ki min shiru kin gane? bari naje gidan Alhaji Aliyun ai nasan Al'ameen din yana can" yana gama fad'in haka yayi waje tagumi Ummi tai cike da tausayin Al'ameen Mahat gaskiya idan Alhaji Musa ya matsa dole sai Al'ameen Mahat ya saki Fadilah Mahat akwai gagarumar matsala tasan wanne irin so yake Mata tasan damuwa da ita da Al'ameen yayi ta riga ta zama itace bugun numfashin sa sau tari yana cewa itace zuciyarsa akwai wani lokaci da Al'ameen yake waya da abokinsa taji abokin na cewa Ina zuciyarka Al'ameen Mahat? Al'ameen yayi dariya yana cewa tana lafiya Buddy nagode da kula bama iya shiba abokan Al'ameen Mahat da yawa haka suke kiran Fadilah a gurinsa suce zuciyar Al'ameen Mahat,,, sauke ajiyar zuciya tayi tana addu'a a ranta Allah yasa kada Alhaji Musa ya had'u da Al'ameen Mahat ko kuma Allah yasa Alhaji Aliyu yana nan ai tasan bazai bari ba.

Al'ameen kam tun lokacin da Fadilah ta fito da gudu baicewa Momy komai ba shima ya fito sakamakon ganin gidansu ta nufa abun ya bashi mamaki kuma yaji hankalinsa ya tashi dan yasan mahaifin sa yana nan shiyasa bai karasa gidan ba yana tsaye a jikin motarsa da xai je airport da ita da kayansa a ciki da komai sallama yaje Mata ta tashi masa wannan borin yana cikin duhu inda babu hasken fitilun da suka haske Mahat sosai yaga Fadilah ta fito daga part d'insu taga waigen bayanta ko Alhaji Musa ya fito su tafi tare domin tana masifar tsoron komawa Saboda tasan idan Abba ya samu labari batasan irin hukuncin dazai d'auka me zafi ba a kanta dan haka taja ta tsaya tana jiran fitowar Alhaji Musan, fahimtar da Al'ameen Mahat yayi ta samu mahaifin sa tunda gashi ta dawo cikin nutsuwar ta tadaina kukan ya fahimci yanzu shine a kwana takowa ya farayi ta bayanta batare da saninta ba har yazo daf da ita kafin ya tsaya yana cewa.

"Fadilah meyasa kika fiya taurin kaine"?.

Jin muryar Al'ameen Mahat a bayanta yasa a zabure ta juyo tana kallon sa tare da had'iye wani yawu ganin irin kallon da yake watso Mata mai nuna tsantsan fushin dake fitowa tun daga qarqashin zuciyarsa ja da baya ta somayi batare data bashi amsa ba tana shirin gudu cikin zafin nama ya rikota zatai masa ihu ya rufe mata baki yana d'aukarta ya soma tafiya da ita hankalin ta inyayi dubu ya tashi amma babu yadda za'ai ta iya ceton kanta sai idan shine yaga damar rabuwa da ita, har gaban motarsa yaje yana bud'ewa yasaka zai rufe kofa tasa hannu da qarfi tana kuka tsawa me tsananin qarfi ya buga mata wacce ba arziki ta matse jikinta guri d'aya tana kifa kanta akan cinyarta ta soma kuka bai damu ba ya koma d'ayan site d'in ya bud'e ya shiga yanaiwa motar key ya nufi gate d'in Mahat na qarshe inda babu me gadi sakamakon a kulle yake ba fita aka cika yi ta gurin ba, tsantsan tashin hankali daya sameta batasan lokacin data shid'e ba ganin ta inda yake son fita da ita daga Mahat to Ina zai kaita a wannan daren kusan qarfe goma da ra'bi innalillahi wa Inna ilaihi raji'un😭, bai damu ba bai kuma nuna kukan ta wani abu bane tu'kinsa kawai yake yi har sukaje airport tanajin sanda motar ta tsaya amma bata d'ago kaiba saida taji saukar muryarsa.

"Zaki iya fitowa"?.

Da sauri ta d'ago tana qarewa gurin kallo tabbas airport ya kawota ta shiga uku badai qasar zai bari da ita ba................

"Fadilah nace ki fito ko anan d'in ma taurin kan zaki nuna min? Wallahi tallahi kinji na rantse ko? Idan kika kuskura wani ya fahimci abinda yake faruwa tsakanin mu saina d'au mummunan mataki a kanki muje".

Cike da tsoro Fadilah ta wuce suka nufi inda wani mutum yake tsaye wanda already dashi Al'ameen Mahat yayi magana Fadilah ya bashi yace ya sata a jirgin shi yana dawowa tunda sai qarfe sha biyu na dare zai tashi shi kuma ya dawo Mahat ya qarasa shirinsa yayi sallama da mahaifansa.

Ummi tasha mamakin ganinsa har ta kasa hakuri tace "Al'ameen daga Ina baka had'u da Daddynka bane"?.

Kaiya ya d'aga mata da fuska ba walwala yace "eh ban ganshi ba Ummi sallama zamuyi ni na tafi saina dawo".

A yadda yayi Mata maganar saida taji kamar hawaye ya zuba mata sake kallonsa tai tana cewa "amma Al'ameen baka tsaya kun gama magana da mahaifinka zaka tafi ya d'au zafi fa sosai yanxu ma yana can maybe a part d'in su Fadilan".

Numfashi Al'ameen Mahat ya sauke tare da d'an rufe ido kafin yace "ba komai Ummi zan kar'bi kaddara ta duk yadda taxo mini idan babu alkairi tsakani na da Fadilah Allah ya yaye min sonta na huta idan da alkairi Allah ya shafe qiyayyata a zuciyarta ya musaya da Sona shine fatana".

Kai Ummi ta d'aga zatai magana Alhaji Musa ya shigo yana kallon Al'ameen dake a shirye cikin shirin tafiya yace "idan ka dawo zamuyi magana domin yanxu naje neman Alhaji Aliyun baya nan na Kira wayarsa bai daga ba amma ba damuwa idan ka dawo sai ayi komai".

Jakarsa Al'ameen Mahat ya d'auka yana rataya ta a kafad'a yace "shikenan Daddy na tafi saina dawo".

"Ok safe journey".

Gurin Ummi dake binsa da kallo ya juya itama yana ce mata "na tafi Ummi saima dawo"? Kaita d'aga masa tana cewa "Allah ya tsare hanya Al'ameen yadda ka fita lafiya Allah ya dawo dakai lafiya" "amin Ummi na gode saina dawo" ya fad'a yana fita bai koma airport da motarsa ba yayi kiran Ahmad Mahat ya fito ya kaishi sukai sallama ya dawo gida shi kuma lokaci dama ya cika jirgin su ya d'aga🛫.

Babu wanda yasan Al'ameen Mahat ya tafi tare da Fadilah Mahat tunda babu wanda yaga fitarsu sannan ko Momy saboda takaicin haukan da Fadilan take yi yasa ko damuwa da inda ta fita da gudu ta tafi batai ba tayi kwanciyar ta koda Abba ya dawo ma bata fad'a masa ga abinda Fadilan taiwa Al'ameen Mahat ba tasan zai iya mata duka kawai tayi shiru da bakinta zuwa safiya taga mezai faru saita fad'a masa komai ya takawa Fadilah burki kafin tayi fushi da ita.

RUSSIA🌆
Ganin irin banzar rayuwar da Siyama take yi da samarin iska tabar abinda ya kawo ta kawai sharholiyarta take yi yasa Taj yayi tunanin zai bar qasar zai dawo Nigeria domin maganar gaskiya bazai iya cigaba da zama acan ba ya fasa qarin karatun wanda yake dashi ma ya ishesa doctor babu abinda daya gagareshi batare da sanin Siyama ya bar qasar ya dawo Nigeria domin dama ba tafiyarsu daya ba bashi aka baiwa amanarta ba bata da wani hakki a kansa idan taga dama ta dawo idan taga dama taci gaba da rayuwar ta acan bai damu ba wannan matsalarta ce ita da mahaifiyar ta.

Iya Abba ya sanarwa dawowarsa amma ko Momy bata sani sai a ranar dazai taho ya kirata ya fad'a Mata aiko ta cika da murna sosai dole tasa akai Mata Kiran Samrah Mahat da da Nabilah Mahat suka zo suka taya Mai aikinta abincin saukar Taj d'in balle yace in ya dawo a main parlor za'a zauna tare dasu Aunty Hauwa, hum su Samrah tunda suka shiga kitchen suka fara aiki suke aikawa juna harara kowacce tana kishi suna furta baka'ken maganganu a tsakanin su kowa akan Taj Mahat har suka gama qin tafiya sukai saidai me ba wacce tayi wanka a cikinsu ganin Hafizah ta shigo d'agwas ta tsara make-up yasa a gigice suma suka mi'ke ko sallama basu yiwa Momy ba suka fita domin suyo wankan ala tsine uwar me qarya😁.

✍️ YÚSRÃH MÛSÃ ABUBAKAR
Mrs Äl'ämëëñ Ahmed ce😘.

💓💓💓
Ayi haku bani da caji shiyasa nayi kadan amma insha Allahu zaku samu dogon page kullum.

We will meet again nagode.
Ngd

✍️ Yusrah Musa Abubakar
Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd ce😘.

YMA DUTSE NEW WORLD🌎
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment