Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu Mai jinki har suma saina tura ki saina tabbatar na baki hukuncin ki kuma zaki gani" yana gama fad'in haka ya mi'ke yana fita a parlon.

Hannu Zainab ta d'ora aka tana fashewa da kuka ta shiga uku ta lalace meya kawo wannan maganar harta kaisu ga haka da sauri ta mi'ke tana hasa upstairs da gudu taci gaba da kuka tana qara volume tun kafin ranar tazo.

Mohan kam yana fita direct gida ya koma baibi ta falo ba dan kadar mum ta tareshi da tambaya ya shiga ta garden ya wuce part d'insa a falor ya kwanta akan three seater tare da rufe idonsa yana tunanin Zainab wacce irin yarinya ce duk abinda yazo ranta shi zata fad'a.......

Tunanin sane ta katse jin wayarsa tana qara ganin me Kiran yasa yaja tsuka yana shigewa bedroom yabar wayar a gurin,,yana shiga Beenafah ta shigo tana kwankwasa masa tace.

''yaya kazo inji mum".

Bud'e kofar yayi yana fitowa tare da kallonta yace "beenah Ina zakije naga kinyi kwalliya"? Kallon jikinta Beenafah tai tana cewa "babu ko'ina muna gida".

"Ok jeki".

Ya fad'a yana komawa bedroom ya canzo kayan shan iska sannan ya fito jin magana a parlon yasa ya dakata yana le'kawa zaro ido yai kafin ya juya yana komawa ya canza manyan kaya yadawo dasallama ya shigo yana zama a qasan carpet suka gaisa da maman Zainab dan shi baima san tazo ba gurin mum ya juya yana cewa.

"Mummy gani".

Kallonsa mum tai tana cewa "a'a Kiran kenan dama naga baku had'u bane kuma ta Kira Zainab bata daga ba shine nace beenah ta duba ko ka dawo".

"Ok" kawai yace yana mi'kewa ya fita shiga motarsa yayi yana son fita daga Mahat yaje wani wuri amma shi bai kunnata ba yana dai zaune jin an qwanqwasa masa glass yasa ya d'ago ganin wacce take tsaye yasa kawai yaji ransa ya 6aci dan indai tazo saita dagula masa lissafi itakuma dama gidan tazo saboda shi ta shigo kenan taga shigarsa mota amma badan hakaba bazatace yana ciki ba saboda ba'kin glass ne na ciki zaiga na waje na waje bazaiga na cikiba.

Fitowar maman Zainab yasa ga mum tayo Mata rakiya yasa a wayance Salma Mahat ta matsa daga jikin motar tana danna kiran wayar qarya har saida sukai sallama mum ta koma ciki da sauri Salma ta bita zatai kamun kafa.

Da sallama ta shiga mun dake zaune ta amsa Mata tana cewa "yau Salma ce a gidan namu"?.

Zama Salam Mahat tai tana cewa "eh wallahi mum nice dama nazo ne mu gaisa na jima ban shigo miki ba" ta karasa maganar tana kar'bar yankan alayyahun da mum keyi".

Cikin jin dad'i mumu tace "ayya Salma na gode da ziyara ai kinfi Auntynki Samrah zumunci itakam bata zuwa min sam".

Kai Salam ta d'aga. "qwarai mum ai indai Aunty Samrah ce zata aikata dama haka bata zuwa gidan kowa a Mahat sai gidan maman Aryam da gurin Momyn Tajuddeen in banda su kaf girman Mahat bata zuwa gurin kowa".

''Ai saiki fahimtar da ita ta ri'ka zuwa saboda girman zumunci"?.

"Uhm mum Aunty Samrah fa lamarin ta sai ita kona fahimtar da ita a banza ba zuwa zatai ba".

"To ai shikenan niki turo min ita xanyi Mata fad'a ta ri'ka zumunci".

Dariya Salma tai tana cewa "tan zan fad'a Mata Allah yasa tazo dan idan na fad'a gani zatai kamar qarya nake" Salma ta qasara maganar daidai ta gama yanka sauran alayyahun tana ajewa mum wasu kaya a leda tace "gashi mum idan Muhammad Mahat ya dawo ki bashi naji Ahmad Mahat yace ya kusa tafiya"?.

Kar'ba mum tai tana cewa "an gode da hidima Salma duk lokacin da yazo inzai koma sai kin kawo masa arziki¿ dan Allah ki ri'ka hutawa".

Mi'kewa Salma tai tana cewa "babu komai mum ai yiwa Kaine kinsan yayanmu Sudais baya nan shiyasa yake maye min gurbinsa (humm ji Salma da zubit ga Aliyu Mahat ga Ahmad Mahat cabdi).

Kai mum ta jinjina da murmushi tace "Allah sarki to muna godiya Salma sannunki da kokari".

Hanyar fita Salma ta nufa tana cewa ''Mum bari na tafi gida sai anjima".

"Ok Salma dakata Ina zuwa" mum ta fad'a tana shiga part din Moh dan tasan ba'a rasa nono a riga kamar me mace indai anzo part d'insa sai an samu kayan kwalliyar mata tana bud'e wata drawer kuwa ta gansu turus dauko Mata tayi wani package wanda babu abinda babu na kwalliya ta dawo parlon mi'ka Mata tai tana cewa.

"To Salma na gode ki gaishe min da Hajiya Barakan idan kin koma gida".

Kar'ba Salma tai da godiya tana cewa '"insha Allahu mum zan fad'a Mata sai anjima" da farin ciki fal ranta Salma ta fita duk Mohan baya bata lokacin sa amma tunda uwarsa tana sonta an wuce gurin.

Muhammad Mahat kuwa baya cikin Mahat sai dare ya dawo saboda yasan ba lallai Salma ta tafi ba shikuma ya tsani yawan magana yana shigowa parlon da mum suka ci karo kallonsa tai tana cewa "sarkin yawo daga Ina ko fira kaje"?.

Kau dakai yai yana cewa "mum sannu da gida".

Zai wuce ta fisgoshi tana cewa "wai kai lafiyar ka kuwa kamar me aljanu sam baka son maganar aure kodai ba'kar aljana ce ta aureka"?.

Baiyi magana ba sai cin magani yake jansa mum tai tana yin wajen dinning dashi tace "okay zo muje kayi dinner wai idan ba takura maka nayi ba saika kwanta bakaci abinci ba kamar wani yaro wannan idan baka samu mace mai kula dakai ba ai lalacewa zakai".

Kayan cinye cinyen da Salma ta kawo mum ta nuna masa tana cewa "me zaka ci a ciki"?.

Humm dama yasan za'a rina tunda yaga tazo maybe taji labari zai koma shine tayo d'abi'arta ta toye-toye data saba zama sukai mum na cewa "kona bari ka tafi dashi goben"? Kaiya girgiza zaiyi magana mahaifinsa ya karaso gurin da ladabi yace.

"Sannu Dad barka da dare".

Zama Dad yay yana kallon sa da murmushi yace "yauwa Muhammad sannu gobe za'a koma ko? Allah ya kaimu darai Allah ya tsare hanya".

"Amin" Mohan ya fad'a a narke yana kallon mum dake masa dariya, duk zama sukai akan dinning harda su beenafah mum tai serving kowa kafin ta zauna suka fara cin abinci tana cewa "karfa ka manta wannan kayan idan zaka tashi".

B'ata rai yai yana qin d'agowa da mamaki Dad yace "me ya hadoki da d'an naki ne naga sai cin magani yake"?.

Dariya mum tai tana sake duba yanayin sa tace "babu komai d'azu ne Salma ta kawo masa kayan cinye2 saboda taji zai tafi akan haka yake wannan hade ran".

Kallon sa Dad yai yana jinjina kai yace "gaskiya kana da farin jini kowacce budurwa sonka take kodai hud'u zaka aura rana d'aya domin yanxu dad'ewar danayi ban dawo ba Abdul-kharim ya tare ni akan maganar 'yarsa wai ita tunda kaje gidansu ta ganka saikai ta'ki cin abinci kullum sai kuka ni na rasa ma wacce irin amsa zan bashi wallahi saboda kunya amini na guda".

Murmushi mum da yar tsokana tace "dazai auri mata hudun ma rana d'ayan zaifi tunda zai iya rikesu, koba haka ba"?.

Kai Mohan ya girgiza da yar shagwa'ba yace "nifa mum ko Zainab ma dan babu yadda zanyi ne amma babu tsarin aure kwana kusa a guna da za'a fasa zanfi kowa farin ciki".

Dad yace "ok to shikenan tunda baka so na Zainab d'in ma anfasa sai ranar daka shirya dan duk abinda baka so Nima bana so".

Cike da murna yace "Dad da gaske an gasa? Kai gaskiya na gode ka taimake ni yanzu bani da wani sauran damuwa".

Cike da mamaki mum tace "haba Alhaji ya zakai haka yanzu me kake son mu fadawa iyayen Zainab ka tuna hargitsin Mahat ya yawan maganganu........

Da ido Dad yaiwa mum magana ta hanyar yimata wani irin secret looks dayasa dariya ta kusa qwace Mata da sauri ta rufe baki dan kada Moh ya ganta Shima Dad cikin son faranta masa yace "eh an fasa da kaina zanje gidan na musu bayani" kamar gaske cikin mazewa mum tace "shikenan tunda kaja mana abun kunya a Mahat yau saikai dinner d'in da kanka dan bani da hannun baka yau nayi fushi" langwa6ar dakai yayi irin saidai ta bashi ko ya ha'kura ganin yadda yai tasan baci zaiyi ba zai iya tafiya ya kwanta a haka indai bata bashi saida taja kunnensa sannan tad'au spoon ta soma bashi kadan yaci ya karbi juice na pineapple Mai sanyi yasha yana mi'kewa yayi nusu saida safe ya shiga part d'insa Abedah da beenah kam tuni sunbar wurin tun bayan gama dinner su.

Kallon Dad mum tai tana cewa "nifa ban gane ba me kake nufi da anfasa".

"Ki rabu dashi kawai yanzu ba zai tafi da tunanin an fasa auren ba? Yana can saidai yaji an d'aura masa a bazata zaifi".

Zaro ido mum tai tana sakin dariyar da bata shirya ba tace ''tabdijam da aiki fa wannan shi ake Kira da auren rashin sani Muhammad uhm" mi'kewa Dad yai yana cewa '"share lamarin yaron ki d'in nan muje ki had'a min ruwan wanka" mi'kewa tai suna shiga part d'in Dad tare.

Washe gari qarfe bakwai daidai Moh ya fito cikin shirin tafiya Bangalore ko breakfast bai tsaya yi yana sauri da'kyar mum ta tareshi yayi a gaggauce a lokacin Dad ya fito sukai sallama ya tafi, daga daya fita kai tsaye gidan su Zainab ya tafi bai shiga ba a harabar gidan ya tsaya yana amsa kiran daya shigo wayarsa.

Zainab tana kwance a bedroom d'inta da waya a hannunta tana chat taji kamar alamun muryarsa mi'kewa tai da sauri tana d'aga labulen window taga kuwa da gaske shine "kenan tafiya zaiyi yau" ta fad'a a ranta tana kallon sa masifa yake zazzagawa a wayar kamar ya ari baki d'an ta'be baki tai tana cewa.

"Kai kowa ma saika nuna masa halinka gaskiya ya Muhammad Mahat akwai masifa anya zan iya zaman aure tare dashi kuwa wannan da nayi lefi ubana zai ri'ka ci hankalin sa kwatanc..,............

Tsawar dayai yasa batasan lokacin data saki wayar hannunta ta fad'i qasa ba secreen d'in ya fashe da mamaki ta d'ago tana kallon shi taga sai zage zage yake yana maganganu mayar da labulen tayi tana barin bakin windown ta dawo bakin gado ta zauna shiru tai jin yadda zuciyarta take harbawa kamar da ita yakewa tsawar tsoronsa ne ya sake rufeta tana cikin tunani taji an turo kofar bedroom d'in an shigo ta d'auka ummanta ce ko qaninta sai kuma taga sa'banin haka boss ne ya shigo mi'kewa tai cike da fargaba tana kallon sa ganin yadda idonsa yayi ja saboda fad'an dayai jikinta har rawa yake da sauri ta soma jada baya tana neman hanyar guduwa saidata qure bango bai daina binta ba ya qarasa daf da ita runtse ido tayi da qarfi dan gani take kamar wani abu zai mata muryarta na rawa tace.

"Wayyo Allah ya Muhammad kayi hakuri dan Allah".

Hannunsa ya fitar daga aljihu kafin ya ri'ko hannunta zatai ihu ya girgiza Mata kai shiru tai ya fara tafiya da ita ya dawo da ita bakin gadon ta zauna knee down yai a gabanta yana ri'ke hannunwanta sakamakon muhimmancin maganar dazai fad'a Mata yana kallon fuskarta cikin nutsuwa yace.

"Hakurin me kike bani? Kin ta'ba ganin an bayar da ha'kuri batare da sanin laifi ba¿ Nine ya cancanta na baki saboda ni nayi Miki ba daidai ba kiyi hakuri da abinda zai fito daga bakina ki d'auka haka Allah ya qaddara miki Zainab duk da kece kika ce kina sona tun farko hakan baisa naga aibun ki ba domin nima a yanzu haka ina sonki saidai son bazai amfani ba domin dole haka zaki rabu dani magana d'aya ce ta gaskiya Zainab na fasa auren ki dama can mum da Dad ne suka matsa min sai nayi ba ra'ayi nabane saidai kada hakan yasa kiji ba dad'i nina fad'a miki zaki samu wanda ya fini komai domin kedin kyakkyawa ce I love you fatan kin fahimce ni zaki min afuwa"?..

Jin tayi shiru yasa ya kasa kallonta cikin tsumewa dan bayaso zuciyarsa tayi rauni jin abu me d'umi yana diga a hannunsa yasa da sauri ya d'ago yana kallon fuskarta hawaye ne yaci karo fasu shakab sun dame mata fuskarta cikin azama ya d'auke kai yana mi'kewa ya nufi hanyar fita a lokacin ta fara shashshe'ka saida ya bud'e kofa zai fita sannan ya juyo yana kallon ta, mi'kewa tai tana qarasowa inda yake ta tsaya so take tayi magana ta qasa bakinta yayi nauyi sai wani azababban qaqqarfan kuka da yaci qarfinta da gudu ta toshe bakinta tana yin hanyar toilet tabbas rayuwata taxo qarshe tunda Moh yayi Mata iyaka dashi bata tunanin zata rayu dawani mutum dabam wanda bashi bane.

Kallon kofar bathroom d'in yayi kamar zai bi bayanta sai kuma ya juya ya fice daga bedroom din yabar gidan ma gabadaya koda ummanta bai tsaya sun gaisa ba tare da driver sukaje airport motar da yaje da ita driven ya kar'bo ya dawo da ita gida babu wanda yasan abinda ya faru tsakanin Zainab da Muhammad Mahat daga ita sai shi.

💓💓💓💓
____Kamar yadda Abba yacewa Al'ameen Mahat ya d'aga tafiyar sa zuwa sati daya yayi wa kowa bazata ciki harda Al'ameen din domin dayai masa magana duk hankalinsa bai kawo wajen ba sai juma'a kawai Abba ya nemi da ya bada sadaki hunm yayi mamaki matukar bai sake shiga yanayi ba Saida yaji da gaske Abba ya d'aura masa aure da Fadilah, Fadilah tabd'i Alhaji Musa yayi tunanin harda had'in bakin Äl'ämëëñ Mahat Saboda ganin yadda ya qwallafa ransa akan Fadilan dan haka bai bari anje gida ba tun a gurin ya rufe Äl'ämëëñ Mahat da fad'a.

"Äl'ämëëñ me kake yi haka kayi hauka ne wato abun har yakai kayi aure batare da sani naba saboda kaji Ina cewa saika rabu da ita akan me zakai mata haka ka nemi amincewarta ne ko ana so dole"?.

Shiru Al'ameen yayi domin baisan me zaice mahaifin nasa ya fahimta cewa Shima baisan da zancen auren ba...........a zafafe alhaji Musa yace "Al'ameen ba dakai nake magana ba karka fusata nifa"?.

Kai Al'ameen Mahat ya girgiza yana cewa "kayi hakuri Daddy wallahi Nima bansan da maganar auren ba".

Wani kallo Alhaji Musa ya watsa masa yana cewa "bakasan da maganar auren ba inji ubanwa? Wannan qarya ce Al'ameen".

"Wallahi tallahi Daddy ka yarda dani bansan komai ba idan baka yarda ka tambayi Daddyn Fadilah d'in kaji"?.

"Bazan tambaye shiba matsa can kaban guri..........

Karasowa Abba yai ganin yadda Alhaji Musa ke zazzaga fad'a dama yasan za'ai haka yana sane yayi maganin abun domin shi Daddy hankalin Al'ameen Mahat ne ya burgeshi tsarinsa mai kyau yana da matukar nutsuwa ga kyakkyawar tarbiyya ta bangaren Alhaji Musa bawai bane.

"Musa meyake faruwa ne anan naga sai fad'a kake ba laifin Al'ameen bane nawa ne domin nine na yanke hukuncin daya dace akan Fadilah bata ita ta watsa min qasa a ido ba".

Huci Alhaji Musa ya fita yana cewa "amma Alhaji Aliyu meyasa zakai haka koba komai Fadilah tana da 'yancin da za'bi mijin da take son rayuwa dashi taya za'ai mata haka sannan bakasan meyasa take gudun Al'ameen ba maybe akwai abinda take hangowa a tare da ita idan sojan daya zama ne bata so fa shikuma yace shida aikin soja sai mutuwa ko ritaya".

Murmushi Abba yai yana cewa "eh ta godewa Allah idan aikin sojan ya tsaya iya shi idan kuma akwai me gadonsa a cikin 'ya'yan dazai haifa kaga itama ta samu ba batun qi Ina ruwanta da sojansa hum ka rabu da lamarin Fadilah yarinyar nan rigimammiya ce".

Kallon Al'ameen Alhaji Musa yai yana cewa "ok kaji dad'i an yabeka sannan an baiwa Fadilah laifi a gabanka shikenan bari mu koma gidan da kaina zansa a kirata indai tace batayi saika rubuta Mata takarda saki a take wallahi kaji na rantse da wanda ya halicce ni ko? Kada ma kace fad'a nake domin bazan bari ta cutu ba dan ranka ya faranta".

Jin maganar da Alhaji Musa yake yi Mai kama da saukar qaqqarfar tsawa yasa zuciyar Al'ameen Mahat tayi mugun bugawa a firgice ya d'ago yana kallon mahaifinsa wanda ya juya yana barin gurin qamewa yayi ya kasa motsin kirki domin maganar Allah indai ya rabashi da Fadilah bayajin zai iya rayuwa inko ya rayu ya tabbata bazai amfani ba zai zama yana tsakatsakin gawa darai bai mutu ba kuma baya tare da mutune............

Katse masa tunani Abba yai da cewa "kaga Al'ameen share batun rabaku da yake wallahi ko Fadilah bata son auren bata isa ba bazaka saketa babu Mai rabaku sai mutuwa indai nine na haifi Fadilah na isa da ita kuma abinda ya dace nayi Mata nasan bazaka ta'ba cutar da ita ba karka wani dama tunaninka muje wallahi ko bata son auren saita zauna dakai fad'a tace".

Sauke wani irin numfashi Al'ameen Mahat yayi wanda yake qoqarin tafiya masa da ransa tun lokacin da Alhaji Musa yace indai Fadilah bata so saiya saketa kuma harda rantsuwa kafin ya rufe ido da qarfi yana godewa Allah ya tabbata insha Allahu Abba zai tari maganar kafin ace mahaifin sa ya kira Fadilah, har suka dawo gida Al'ameen Mahat yana tunani kawai tafiya yake amma hankalinsa baya tare dashi burinsa yaje ya had'a kayansa domin yau bazai kwanan Mahat ba Bercelona zai tafi kamar yadda ya alkawrta.

Abba yana komawa gida ya Kira Momy parlor tare da Fadilah ya fad'a musu komai daya faru yau sannan yadau sadaki dubu d'ari biyar kamar yadda Al'ameen Mahat ya bayar ya mi'kawa Mommy wacce sai hamdala take a ranta dama ta gaji da wulakancin da Fadilan take yiwa Al'ameen d'in gara da Abban yayi maganinta ya mata bazata qarshen qarya da zille zille ya qare.

A 6angare Fadilah kam kuka take cikin tsananin tashin hankali a gaban Abba kamar ranta zai fita tanai masa magiya yana zaune akan kujera ta dur'kusa a gabansa tana rike da qafafunsa muryarta har ya daina fita sosai tsabar kuka tace.

"Dan girman Allah Abba ka rufa min asiri Abba ka yafe ni na shiga uku nalalace".

Kai Abba ya jinjina yana kallon ta yace "Fadilah ban ta'ba sanin ke shashashar yarinya bace sai yau dama rashin hankalin naki har yakai haka dazan miki magana ki'ki saurarona are you out of your sense" ya qarasa maganar da qarfi cikin tsawa wanda yasa Fadilah qara volume din kukanta tana juyawa 6angaren da Momy take zaune ganin bata kulaba tace.

"Momy dan Allah ki fad'awa Abba yayi min rai ki bashi ha'kuri".

Kai Momy ta girgiza tana cewa ''no Fadilah bana goyon bayanki kin gane abinda Alhaji yayi shine daidai wallahi Fadilah yau kin bani kunya yadda kika nuna bamu isa dake ba dan anyi miki abinda ya dace kika fito kina nunawa duniya ba'ai miki daidai ba yayi miki kyau".

Ganin da Fadilah tai bata samu karbuwa a gurin Momy ba yasa a susuce ta mayar da hankalinta kan Abba tana cewa "Abba ka dubeni dan rahma Abba kayi min rai wallahi bana son ya Al'ameen Mahat bana qaunarsa ko ganinsa bana so na tsanesh............bata iya qarasawa ba sakamakon zazzafan marin daya sauka a fuskarta daga Abba cikin 6arai rai yake kallonta Lokacin data kifa tana sake ri'ke da kunci ga wani azababban kuka daya taso mata na tsantsan damuwa duk abinda akeyi hajiya Jamila bata sani ba fitowar ta kenan ganin yadda Fadilan ke kuka tana kuma dur'kushe a gaban Abba yasa ta kalli Momy cikin alamar tambaya da son sanin meke going da alamar tambaya tace.

"Tofa wannan kuma lafiya kukan me takeyi haka kamar anyi mutuwa? Ai ko mutuwa bazatai wa irin haka ba meya faru"? Shiru Momy taibata bata amsa ba cike dajin haushi hajiya Jamila ta sakarwa Momy harara a kaikaice kafin ta mayar da hankalin ta kan Abba wanda ya tsume ya had'e rai sosai tace.

"Alhaji lafiya naga haka meya samu Fadilah take irin wannan kukan kamar anyi mata kai Kuma ka had'e rai?.

Fuskarsa babu alamun wasa ko wargi yace "eh lafiya na aurar da ita ne saura Zarah".

Zaro ido waje hajiya Jamila tai cikin firgici tace "ka d'aura Mata aure da wa! Amma dai ba yaron nan Al'ameen Mahat ba"?.

"Eh da shi".

Jin amsar daya bata yasa a susuce tace "amma gaskiya Alhaji kana da abun mamaki yanzu tsakani da Allah yarinyar nan bata sonsa saida kayi mata dole............

Hannu Abba ya d'aga mata yana cewa "Kinga Jamila saurara min ki kama bakin ki akan abinda na yanke hukunci babu ruwan ki kin gane"?.

Shiru Hajiya Jamila tai zuciyarta na turiri ganin shikenan ba damar faridah ta auri Al'ameen Mahat Amma itakam ta shiga uku ta lalace anya burin ta zai cika kuwa? Tun daga yanzu ta fara hango fad'uwa a tattare da ita......... .

Jin Abba yayi tsawa yasa ta dawo cikin hankalin ta da sauri daidai Fadilah ta mi'ke da gudu ta shiga part d'in su zubawa Abba ido hajiya Jamila tai kawai tana kallon sa tana son tace wani abu amma kuma yace ta iya bakin ta dole tai shiru bakin ciki goma da ashirin ya isheta ji take kamar ta zubar da hawaye da'kyar tace.

"Gaskiya Alhaji ba'a haka kasan fa babu kyau auren dole amma kai kayi mata".

A fusace Abba yace "Kinga Jamila idan bazaki taya ni nayi abinda ya dace ba ki rufe min baki anan bana son wannan maganar taki domin bata da wani amfani a guna fatan kin gane"? .

Cizon lips hajiya Jamila tai ranta a 'bace amma ta danne tace "shikenan ai tunda haka kace baka son gaskiya Allah ya bada zaman lafiya".

"Amin in da gaske kike"? Abba ya fad'a batare daya kalli inda take ba balle ya fahimci halin ba'kin ciki da hassadar dake ciciyarta.

Cike da takaici Hajiya Jamila tace "da gaske man nake yi kodan na fad'a maka gaskiya shine ta 6ata maka rai? To kayi hakuri Allah ya huci zuciyarka".

Wani kallo Abba yai mata a harzu'ke yace "bazan yi ha'kurin ba nace bazan yi ha'kurin ba zancen banza zancen wofi kenan ni bana son munafirci da kika ganni nan komai nawa gaskiya nake nunawa kuma bance ki sake min magana akan Fadilah ba domin babu ruwanki get of my sight mtww" Abba ya karasa maganar babu wasa yana nuna mata kofa, cikin 6acin rai hajiya Jamila ta juya fuuu kamar ana hankad'ata ta shige part d'inta, mi'kewa Abba yai bai sake cewa Momy komai ba shima ya shiga part d'insa aka bar iya Momy a gurin tana tunanin wacce irin yarinya ce Fadilah da batasan me qaunarta ba ta biyewa yan matan Mahat tana neman lalata rayuwar ta da shashanci taqi ta tsaya ta gane me sonta da gaskiya.

____A 6angaren Al'ameen Mahat ma hake ne yana shiga part d'in mahaifiyar shi ta rufeshi da fad'a "Wato Al'ameen ka kyauta yanzu saida ka takura ka auri yarinyar nan hankalin ka ya kwanta ana aure dole ne Al'ameen meye ya rud'e ka da Fadilah ne meye tafi sauran yan matan Mahat dashi fad'a min Ina jinka yanxu daka matsa ka aureta ya zakai da ita kaida ba mazauni ba"?.

"Ai Ummi anan zan barta na tafi ni dama damuwa ta naga ta zama matata wannan shine kuma burina ya cika zata zauna a part d'ina kafin na dawo...............

Kaita jinjina tana cewa "shikenan Al'ameen na kasa gane kanka kawai saidai nace Allah yasa haka shine mafi alkairi".

''Amin Ummi insha Allahu shine alkairin dama saida na roki Allah idan babu alkairi ya cire min sonta amma sai naji son nata yana sake ruruwa a zuciya ta Kinga ko ai alkairi".

"Amma Al'ameen baka ganin ka shiga hakkin yarinyar nan ka duba fa"?.

Had'e rai yai yana cewa "to Ummi dan ubanta ni sa'an wasanta ne? Ta godewa Allah na daina duka ma yanzu saboda nayi hankali wallahi da dane take min irin wannan haukan da jikinta yayi tsami saina koya mata hankali".

Rufe baki Ummi tai tana kallon shi tace "Allah ko? Humm to Allah ya shiryeka bari Alhaji ya shigo zamu qarasa maganar".

Wucewa Al'ameen Mahat yai yana cewa "ai Daddy tun acan muka gama magana dashi babu wata matsala bari naje na qarasa had'a kayana" yana kaiwa nan yai gaba yana murmushin nasara da kuma wata shawara da zuciyarsa ta yanke masa wanda kowa zaisha mamaki idan hakan ta faru..............
YÚSRÃH MUSA ABUBAKAR CE.

See you tomorrow morning 😁.

Fatima Elham
Little Zaran Aunty💃🏿💃🏻.

TYPING 📲 SUN, SEP29/24 10:18AM YUSRAH MUSA ABUBAKAR💋🤟💔.

💓Täjüddëëñ Äryäm💓

💫ÀÑÑÙRÌ WRITER'S ASS💫
Home of hospitality and harmony 🤙 gidan

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment