Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tana cewa "kema bazaki iya ba ko Diana na sani wannan abune me girma amma na shiga uku yanxu mene makomata wanne irin qalubale zan fuskanta a gaba Allah ya gani bazan iya auren kowanne namiji na zauna dashi ba inba Tajuddeen Mahat amma na rasa ta wacce hanya zanbi ko baya sona ya aureni Diana nasan ke zaki iya hango min hanya please kiyi wani abu akai kar ki rasa qawarki"

Kai Diana ta d'aga mata "ok Samrah ya isa haka na fahimta zanyi miki iyaka bakin kokarina kuma insha Allahu zaki auri Taj Mahat kamar yadda kike fata amma dan Allah Samrah ki tsaya ki nutsu tunda baya nan ki daina cutar da zuciyarki ki mayar da hankainki kan karatu tunda shi bazai dawo sai nan da shekara hud'u kinga kuwa ai da lokaci zaki dad'e kina shan wahala idan baki sauke damuwar ranki ba ni nayi miki alkawarin zan karkato miki da hankalin Taj Mahat koda ace zan rasa komai nawa farin ciki na dukiyata walwala karki damu Samrah komai zai zama daidai idan Taj ya dawo kinji zan sadaukar da walwala ta ki samu abinda kike so".

Diana na rufe baki Samrah ta fashe da kuka tana rungume ta tace "nagode Diana tabbas qawa ta garice irinki ake nema a baiwa amana na sani da ace kinada ikon mallaka min Taj Mahat da yanxu ya zama nawa insha Allahu Diana bazan ta'ba barinki ba a rayuwa muna tare".

Murmushi Diana tai kada ki damu Samrah amma zan baki shawara ki tsaya ki duba me Taj Mahat yake so sai ki ri'ka yi tahaka ne zakija hankalinsa amma bada karfi kice saiya soki ba yanxu misali kamar ace wannan yarinyar Aryam take ko? Kai Samrah ta d'aga ''eh haka sunanta yake".

Cigaba Diana tai ''ok kamar yanzu kinga ita yana tsananin son yarinyar kamar ransa haka yake bata gata da kulawa to ki ri'ka janta a jikinki duk abinda takeso kina yi mata kina d'aukota kina yawan bata abubuwa kinace mata idan tayi waya da Uncle d'inta ta fad'a masa wallahi ko Samrah nina fada miki zakisha mamaki kina zaune Taj Mahat zai dawo ya ri'ka kulaki kema yana baki lokacinsa idan kika jawo Aryam jikinki ki gwada kuma ki gani".

Shiru Samrah tai cikin nazari tana jinjina kai kafin ta d'ago tana kallon Diana tace "inko haka Diana indai hasashenki zai tabbata zanyi amfani da shawararki tashi muje gidan Aunty Hauwa yanzun nan aiyau weekend nasan Aryam tana free dama yana yawan sai Mata chocolate da ita zan jata jikina dama mahaifiyar sa na sayeta da ladabi na tana sona wani lokacin har aikowa take lafiya idan taga kwana biyu ban le'ka mata ba tashi kawai muje".

Mi'kewa Diana tai suna fita daga gidansu Samrah kai tsaye gidan Aunty Hauwa suka shiga tana parlor a zaune gefe d'aya Aryam ce zaune a gaban waya suna video call da Uncle d'inta tana masa shagwa'bar yaushe zai dawo ita chocolate take so murmushi kawai yayi Dan tasan rigima kawai take nema amma kullum a zaune take yasa Aliyu Mahat da Al'ameen Mahat suna shigo mata dashi insun fita.

"Uncle yaushe zaka dawo"?.

Murmushi yana kallon ta yace "baby Aryamna na kusa dawowa me kika tanada min"?.

Kallon Aunty Hauwa tai wacce ke magana dasu Samrah duk da hankalin Samran gabadaya yana kan wayar da Aryam d'in keyi so take Taj yasan da ita a gurin ko zaice a bata su gaisa amma taji diff baice komai ba duk da kuwa yasan da zaman nasu tunda Aryam d'in tace masa ga Aunty Samrah ta shigo amma saiya basar data sake cewa.

"Uncle Aunty Samrah ta shigo ita da qawarta".

Cikin za'kuwa Samrah ta kashe kunne tana sauraren taji yace bata wayar sai tace ya sauya zancen da cewa.

"Baby kika ce yau baki sha chocolate ba sai iya ice-cream🍦 da gaske kike fad'a min naji waye ya sayo miki ice-cream d'in"?.

Ya fad'a domin ya bagarar da wancan zancen da take masa kaita d'aga a shagwa'be tace "Daddy ya kawo min kuma ni nace Fab Chocolate🍫 nake so".

"Ok baby kenan baki sha ice cream d'in ba"?.

"Eh ni bana so ka dawo yanzu ka sayo min" ta karasa maganar tana d'an bubbuga kafa kai ya girgiza yana cije lips da murmushi a fuskarsa zaiyi magana jin ana yi masa knocking yasa yace.

"Ok baby Ina zuwa" ya fad'a katse video call d'in.

Had'e rai Aryam tai tana tashi zata bar farlon Samrah ta dakatar da ita "Kinga Aryam rabu da Uncle kinyi fushi yau nice zan sayo miki zo muje".

Juyowa tai tana cewa "da gaske Aunty Samrah"? Kaita d'aga mata "eh da gaske kome kike so idan na sayo miki muka dawo kicewa Uncle bakya son nasa nawa kike so nice zan ri'ka sayo miki" to Aryam tace tana wucewa ta d'auko gyalen doguwar rigar dake jikinta sannan ta fito daidai kiran Taj Mahat ya shigo Aunty Hauwa tace.

"To Aryam ga Uncle ya kira kixo ku karasa maganar" zun6uro baki tai tana cewa "ni bazanyi magana dashi ba nayi fushi tunda ya tafi ya barni gashi yanzu Aunty Samrah tace zata sayo min abinda nake so" takarasa maganar tayin kofar fita kallon juna Samrah da Diana sukai suna murmushi sannan Diana ta mata alama da ido su tafi su tafi mi'kewa Samrah tai tana cewa.

"Aunty Hauwa sai mun dawo".

"Ok Samrah a dawo lafiya" ta fad'a suna fita kafin ta mayar da hankalinta kan Taj dayai shiru yana saurarensu yace.

"Amma Aunty kina kallo kika bari yarinyar nan ta fita yawo da baby baki hanata ba"?.

Kai Aunty Hauwa ta girgiza "no Tajuddeen idan nayi haka Samrah bazataji dad'i ba sai taga kamar wani abu ne shiyasa na barsu".

"Ok shikenan amma daga yau kada ta sake ficewa da ita kice na hana bana so yarinyar nan ta tashi da d'abi'ar yan matan Mahat shiyasa nake kula da ita nake tattalinta miyasa sauran mutane suke ganin zafina akan 'ya'yansu indai zakai rashin tarbiyya a gabana ni kuma zan gyara ka dan hakane yasa ni bana shiri dasu".

"Haka ne Taj Mahat to kayi hakuri bazata sake binta ba daga yau Aryam d'in takace sai a hankali yarinya yar caza kaice kuma duk kaine ka sangarta ta".

Sake knocking akai masa a karo na biyu dan haka yacewa Aunty Hauwa yanzu yana da uzirirrika zasuyi waya idan Aryam ta dawo yana so zai kad'a mata warning kada ta kuskura ta sake bin Samrah su fita waje idan kuma ba haka ba ya dawo saiya zaneta da bulala😳.

A 6angaren Taj Mahat kuwa hakanan yaji ransa ya 'baci da fitar da Samrah tayi da Aryam hankalinsa ya tashi kamar ya hau jirgi a lokacin ya dawo gida domin yazo ya shukawa Samrah rashin mutunci amma ya danne 6acin ran da'kyar yaiwa wanda aka Aiko daga companyn Daddy bayanin cewa insha Allahu jibi zaiyi meeting dasu a fad'awa kowa yau.

Saboda ranar ba school yasa ya kira wayar Siyama yaji inda take a lokacin tana tare da wani gaye ya jata hotel suna hutawa dan haka tayi masa karyar taje anguwa ne bai wani zafafa ba daga haka da tace masa ya share kuma bai kawo komai a ransa ba kawai ya tashi yayi wanka ya shirya tare da wani drivern company yace yana son fita yaje yaga gari yau.

Kyakkyawan guri mai kayatarwa ya Danual ya kaishi wani irin dogon gini ne na glass abin kallo da bud'e ido ko'ina mutane burjik ke zagayawa turawa da baka'ken fata a karkashin wasu kyakkyawan bishiyoyi masu matukar d'aukar hankali ya zauna kan chairs masu kyaun gani farare tass akwai karamin table a tsakiya irin na hutawar nan mai walwali ga swimming pool da mutane a cikinsa sai wanka suke gefe guda wani tsaftaceccan ruwane blue a tsare da kifaye kala kala a ciki suna yawo da wasannin su cikin ruwan gwanin ban sha'awa da iska mai dad'i tana kad'awa a hankali.

"Hi! Barka da hutawa".

Ba zato Tajuddeen yaji muryar mace a kansa da sauri ya d'ago yana kallon ta budurwa ce sosai tayi tsaye da 'kananun kaya a jikinta kanta babu kwali kuma ga dukkan alama ba'kar fata ce, zama tai tana kafeshi da ido tace.

Sunana Zeenat amma anfi kiran zee zee wulakanci zee zee bakki mutunci kuma ni 'yar Nigeria ce nazo nan karatu ne idan kaima acan kake maybe wata rana mu had'u samin numbar ka" ta fad'a tana fito da phone d'inta daga handbag ta mi'ka masa.

Ko kallo bata ishe saba yayi banza kamar ba mutum ke masa magana ba gyara zama tai tana cewa.

"Hey jiman nifa ban ta'ba magana an manna min hauka ba dan haka ka juyo da hankalin ka gareni" ta karasa maganar tana murza yatsunta biyu suka bada qarar qas qas wanda tasa a fusace Taj ya d'ago yana nuna mata hanya cikin tsawa yace.

''get of my sight kafin na 6alla miki qafa nayi miki kama da irin banzayen mazan da kike kulawa ki barnan tun ban tashi a kanki ba ranki zai mugun 'baci".

Murmushi tai cike da bariki ta farfara masa ido tana cewa "oh sorry nifa ba nazo nan dan 6ata maka rai bane ka gane ayya bi a sannu mu fahimci juna domin tunda nake a duniya nayi yawo kasashe dabam dabam Amma ban ta'ba cin karo da saurayi wanda naji ina matukar sonsa ba saikai ya sunanka kuma kaima nasan ka 'kyasa da gani na irin wannan haja babu wanda zai samu ya bari kaima nasan jinkai ne ya hana ka nuna" kallon Danual dake tsaye tai tana cigaba da cewa.

"Idan kuma akan wannan banzan dake tsaye akusa dakai ne yanzu sai nasa a koresh...........................

Bata karasa ba sakamakon mari daya sauka a fuskarta rai 'bace Taj ya mi'ke har shine zata kalla tace ya 'kyasata baisan lokacin daya sake fidda hannu ya d'auketa da wani marin ba yana huci zuciyarsa na tafasa da tsanar dayaiwa yan Mata masu kamun kaima balle ita ballagaza mai rabawa gayu haja.

Da tsananin mamakinsa a fuskarta ta d'ago tana kallon sa dan yauce rana ta farko a rayuwar ta da wani mahalu'ki ya ta'ba marinta tunda take a duniya ganin irin kallon da take masa yasa ya sake buga mata tsawa wacce batasan lokacin data fad'o 'kasa daga kan kujerar da take ba tsabar firgici mikewa tai cike da masifa zatai magana ya sake daka mata tsawa.

"Enough for you!!!".

Hanyar fita daga gurin ya nufa yayin da Danual yabi bayansa da sauri yana dariya ganin yadda ta tsorata da Tajuddeen din.

Cike da mamaki ta bishi kallo harya fice a gurin "who is he"? Dazai mata shouting yasan wacece ita waye ubanta dazai mata haka cikin 'bacin rai tad'au handbag d'inta tana fita daga wajen a ranta kuwa tasa cewa kowa d'an wayeshi saita nemoshi zata bincikoshi saita dau fansa.

Taj Mahat yana komawa gida jin har lokacin bai sauka daga fushin daya hau ba yasa yayi alwala yayi sallah jin kansa ma na masa ciwo yasa bai fita ko'ina ba bayan sallar isha ya kwanta da yaso yaje estate din da Siyama take ya ganota amma saboda ciwon kan ya ha'kura.

Washe gari karfe bakwai da rabi ya shirya ya fito ko tsayawa zancen wani breakfast baiyi ya wuce gurin meeting kamar yadda yace musu sai acan ya dan ci toasted bread da tea kafin lokacin shiga meeting d'in ya karasa.

Gurin meeting d'in a cikin company yake babban hall ne Mai girma an qawata shi da kayan ado da kujeru na Alfarma saboda irin wannan rana ko'ina a cike yake manya mayan mutane zazzaune suna jira.

Lokacin da Tajuddeen Mahat ya shigo duk mi'kewa sukai gabadaya saida yaje ya zauna a gurin da aka tanadar masa sannan suma suka zauna.

Jawabi ya fara da magana cikin harshen turanci na asalin cike da 'kwarewa yana bayani daki daki gurin yayi tsit bata jin komai sai sautin tashin muryarsa cikin nutsuwa daga karshe ya nuna kulawarsa da yabawarsa ga jagororin company ya basu lambar yabo ya kuma jinjina musu irin jajircewar da sukai har sunan company ya d'aukaka yayi suna aka sansa akeyi dashi saboda ingancinsu da hazakarsu.

Lokacin da yazo ga'bar jawabinsa yayi godiya sannan ya koma ya zauna duk hall d'in tafi ya d'auka domin ya burge kamar yadda mahaifin sa yake haka shima yake da sakewar fuska a mutane shugaban companyn ne ya tsaya a gurin jawabin ya karasa maganar data kamata da tsarin abubuwan company ta inda komai zai ri'ka tafiya daidai babu kuskure kamar yadda aka saba.

A ranar ma Taj Mahat bai samu lokaci yaje estate din da Siyaman take ba domin sai bayan sallar isha ya shigo gida a gajiye iya wanka yai ya fito falo yana zama a dinning ganin girkin da Ifeany ya dafa yasa ya ta'be baki domin shifa maganar gaskiya bazai iya cin gagwalgwalon girkin ba gashi baison fita iya fresh eggs yaci yasha ruwa yai kwanciyar sa.

Samrah ta shiga damuwa sosai akan abinda Aryam tace mata wai Uncle Taj Mahat ya hana yace idan ta sake binta suka fita ya dawo humm saiya zane ta jin haka yasa Samrah idan ta fita school saita sayo Mata chocolate din d'aga can nanma yace idan ta sake kar'ba saiya zaneta akan haka har gida ya dawo yayi wa Samrah rashin mutunci yace idan tana hakane dan ta samu ya kalleta to tayi kuskure indai a kansa take 6ata lokacinta yana bata shawarar tayi aure tun kafin ta tsufa babu ita a gabansa ba itaba dukkan mata ma shi basa gabansa babu abinda zaiyi da ita koda a larura ne ta fita hanyarsa kafin ran kowa yai mummunan 'baci Samrah tayi kuka tayi magiya amma ko sauraron ta baiyi ba a ranar daya gama abinda ya kawo shi ya koma Russia domin ko Mahat bai shiga ba school dinsu yaje ya buga mata zazzafan warning sannan ya barta da kuka har idanuwan ta suka kumbura sai glass d'in Diana ta ara tasa da aka tashi saboda kar Umma ko wani ya gani a nemi ba'asi har zancen ya fito fili tasan ta shiga uku Aliyu Mahat saiya mata qaramin rai balle yanxu Fadilah tayi aure a sa'annin ta babu kowa sai ita duk su Umma a 'kule suke da ita sun zuba mata ido na wani lokaci.

RUSSIA
Yau dare Taj yayi dare a school sosai amma sakamakon baiga Siyama taje makarantar a yau ba yasa ya fara bi da gidan data kama ya gani ko lafiya mamaki ne ya kamashi ganin mota a harabar gidan wannan kuma motar waye a ina ta samu sharewa yai ya shiga gidan domin maybe ko motar qawarta ce ko kuma dai oho jin kofa a rufe ya danna doorbell shiru yasa ya zagaya ta d'ayan bangaren gidan domin yana da kofofi da yawa ba mutane ne da yawa a gidan kowa da nasa part din ga Abinda ya tsana ya tarar sai busa haya'ki suke ko'ina ya kaure da wari da'kyar yake jan numfashi wato dama irin wannan wajen tazo ta kama haya tsabar hauka zai fad'a Mata ta canza gida kada wari wannan abar yasa ta kama rashin lafiya inko ta'ki bai dameshi ba dama zai fad'a mata ne matsayin yar uwarsa musulma bawai dan nuna ita d'in wata tasa bace domin Mami bata bashi amanarta ba shiyasa ma bai damu da ita ba.

Bud'e kofar da kowa ke shiga yai ya shiga ta wani dogon hanya gida mai lamba d'ari da d'aya ya tsaya tanan ma kwankwasawar duniya shiru har yayi zaton ko bata nan zai juya yaji karar bud'e kofa waigowa yai yaga samari biyu da budurwa daya sun fito da shigar banza a jikinsu sun fice d'an 'kyabe fuska yai yana bud'e kofar ya shiga shiru babu alamar motsin komai kallon ko'ina yake yana nazari a ransa kafin ya d'aga wayarsa yana danna mata kira sai kuma yaji karar phone d'in nata a palor ta barta caji tsaki yai yana juyawa zai fice yaji surutu an bud'o kofa ana dariya kallon gurin yai Siyama ce ta fito daga bedroom tare da wani gaye da wata iriyar shiga a jikinta d'amammun kaya kuma qanana sosai dan rigar ma kad'an tafi brazia girma kanta a hargitse duk gashinta a barbaje.

"SIYAMA"😳.

Taj ya fad'a da qarfi yana zaro ido waje a firgice Siyama ta kallo inda akai maganar ganin wanda ke tsaye yasa cikin tashin hankali a gigice ta soma kare jikinta muryarta na rawa tace.

"Tajuddeen Mahat kaine yaushe ka shigo dama kasan inda na kama hayane wannan ai friend d'ina ne sunansa Boun muna karatu tare yazo kar'bar abu ne gurina shine shine ummm...............

Kasa karasa maganar tai sai in'kina take zufa na tsattsafo mata ta rasa inda zatasa kanta tsabar tsananin firgici da tashin hankalin data shiga duk ta rud'e wani kallo Taj Mahat yai mata cike da zazzafar tsana da 'kiyayya yana jinjina kai kafin ya juya a fusace yabar parlon d'ora hannu aka Siyama tai tana fashewa da kuka tare da dur'kusawa a gurin kamar kuma an tsikareta ta mi'ke da sauri tana d'aukar wayarta ta kira Mama tana kuka.

Hankali tashe Mama tace "daughter lafiya kukan me kike haka meya faru".

Cikin kuka a burkice Siyama tace "Mama duk abinda Tajuddeen zai fad'a muku kada ku yarda karya ne sharri yayi min saboda ya samu carry over shine nima yake neman a d'ora min".

Cikin rashin fahimta Mama tace "ban gane ba daughter kimin bayani yadda zan fahimta".

Siyama najan ajiyar zuciya tace "Mama Taj Mahat yanzu yabar gidan dana kama akan yazo ya tarar dani tare da wani boyfriend dina shine ya ce wai dama baki iya bada tarbiyya ba abinda nake aikatawa kenan lalata ya zazzage ki ya wulakanta ni yabar gidan".

"Ya wulakanta ki kuma ya zageni Taj d'in"?.

"Eh Mama bakiji irin baka'ken munanan maganganun daya ri'ka fad'a miki ba waike ba uwa ta gari bace gur'batacciyar mahaifiya ce".

A masife Mama tace "Fatima ce gur'batacciyar mahaifiya amma bani ba rashin tarbiyya aka kaishi d'an marasa mutunci au akan haka kike kuka kina wani 'bata hawayenki? Humm daughter share banza Ina nan dake sai nasa shi yayi nadamar abinda dayai miki yanzu ke kuma lokacin ne zaki rika garashi kina wahalar dashi kada ki damu kome ya Kira ya fad'a wa iyayan nasa zan karya idan sun gasgata shi zance ai kedin 'yata ce a barmin ke kome kikai ado ne kinji ki kwantar da hankalinki ba wani shege koma kici gaba da karatunki".

"Ok Mama nagode da kika ce haka har naji dad'i da na d'auka zaki bari Taj yayi nasara a kaina ya fad'awa yan Mahat".

Tsaki Mama taja "wa shi ya isa saidai nasa ya fito fili domin kaf Mahat sai sunsan ya fad'i exam ya samu carry over ke kin haye kin gane"?.

"Shikenan Mama bari naje naci gaba da karatu na kar dare yayi ban karasa ba".

"Ok daughter saida safe ki kula".

Kashe waya Siyama tai tana she'kewa da dariya tace "muje Boun yau anan zaka kwana min domin dama ban gaji dakai ba'' tana rufe baki tai tsalle tana d'afeshi tahau bayansa ya shige dasu bedroom🤪.

A fusace Taj Mahat yaje gida baisan lalacewar da Siyama tai har yakai haka ba ta ri'ka d'iban garadan maza zuwa bedroom d'inta hum shikam babu ruwan sa duk abinda ya faru gaba su kuka da kansu da'kyar yayi barci tsabar damuwa tun a daren yaso kiran Daddy saidai me zai fad'a masa tunda shima bai goyi bayan Siyama tazo Russia ba Mamin ce ta dage saitazo ai ga sakamakon taurin kai ne ta fara gani tun daga yanzu...... YUSRAH MUSA ABUBAKAR.

Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë.
Me tambarin yma dutse Jigawa state new world city of life.

Masha Allah, fans ku kasance tare dani✍️📚 nagode sai kun jini gobe, amma pls ku ri'ka d'aga min qafa domin books biyu nake yi ba lallai ku ri'ka samun update kullum ba saboda wancan ma ana tambayar sa.
Me kamar sarki👍 ya matukar had'uwa kada ku Bari a baku labarin sa book ne had'add'e me zaman kansa yadda sunansa yake haka qasaita take a ciki.
🗣️ MË KÄMÄR SÄRKÏ👑
#500 ne babu tsada akwai darasi🤟.
Acc no: 2410673902
Acc name: Yusrah Musa
Zenith Bank🏦.

We! Will!! Meet!!! Again!!!!
Tnks for loving me 😃.

TYPING📲 Sat, Sep 28/24 12:18PM YUSRAH MUSA ABUBAKAR💋🤟💔.
__________________________________________________________________________
________
________

❤️Tajuddeen Aryam💓

Story written nd editing
Yusrah Musa Abubakar
📝✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë

ANNUR WRITER'S ASSOCIATION💫
Home of hospitality and harmony 🤙 gidan karbar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ.

Dedicated to
YUSUF 👑KING___SKEEBOY🎧🎶👑
Shatan rapper reagea rb rap da kuma hausa hip hop brother of Zainab kalar camera and Na'im❤️ d'an mutan Kanawa Tarauni local government.

💓 NAJA'AT MUSA ABUBAKAR
💓 FATIMA MUSA ABUBAKAR.
My whole life have been deducted to u my sister's.
Salim Musa Abubakar
Aishat Musa Abubakar
Abubakar Musa Abubakar

©️®️YUSEEN AL-AMEEN CE😘.
Wannan book is my own halak🙅🏿‍♀️ sannan na kud'i ne mutum y biya ya karanta batare da hakkina ba akansa ba d'an uwa ka tuna nauyin hakkin wani a gurin ubangiji Allah SWT abune me girma👍.

#YUSRAHMS#
Page 0️⃣3️⃣&0️⃣4️⃣
NIGERIA 🇳🇬
______Da yake yau Abba a part d'in Mama yake suna gama waya da Siyama tad'au hijab d'inta a fusace ta tafi gurinsa tayi sa'a kuwa yana parlor saidai gabanta yayi mugun fad'uwa jin suna waya kuma da tajuddeen hankalin ta ya tashi duk da maganar da suke bai shafi 'bangaren Siyaman ba amma Allah Allah take ya gama kar Taj din yace wani abu lokacin da yace saida safe har wata qaqqarfar ajiyar zuciya ta sau'ke daidai Abba ya dago yana kallon ta itama shi ta qurawa ido cike da rashin gaskiya tana sauraron me zaice mata akan Siyaman ko Taj Mahat ya fad'a masa wani abu......

Katse mata tunani Abba yayi da cewa "Jamila kinyi waya da Siyama ne"?.

A firgice Mama ta sake kallonsa tana girgiza kai tace "a'a bamuyi ba wani abu ne ya faru kota kira kane"?.

"No bata kira niba na tambaye ki kota kiraki tana bukatar wani abu kinsan Tajuddeen aiki yayi masa yawa acan ba lokaci yake samu yana zuwa dubata ba fatan ba wata matsala"?.

Numfashi Hajiya Jamila ta sau'ke tana sakin wani 6oyayyan murmushi a ranta tace "humm anzo wurin Taj Mahat jirani ina zuwa kanka zakai bayani wallahi saina sanya ka ba'kin ciki a rayuwa" amma a fili sai tace.

"Eh ta kirani a waya da kukanta wai Taj Mahat yaje har gidan data kama haya ya mata wulakanci saboda ya samu carry over ita kuma ta haye".

Ba shiri tasa Abba kallonta jin maganar banzar da take masa wacce yasan dagaji qarya ce shiri ne Siyama ce xata wuce Tajuddeen¿ Inaaaa ai daga furucin Mama ya fahimci wannan ba gaskiya bane kai ya jinjina yana cewa "shi Tajuddeen d'in ne ya samu carry over a exam Tajuddeen fa"?

Kai Hajiya Jamila ta d'aga cike da gadara tace "kwarai kuwa shi d'in idan kuma baka yarda ba na kira Siyama ta fad'a maka da kanta".

"No bana bukata zanyi magana da Taj lallai idan gaskiya ne sai nayi mugun 'bata masa da ransa har asarar takai kamarsa ace ya zauna mace ta fishi mayar da hankali Taj Taj hummm".

Ganin da Hajiya Jamila tai ran Abba ya mugun 'baci yasa wani irin dad'i ya rufe ji take kamar ta tashi ta taka rawa sai dariyar mugunta take a ranta tasan Abba mutum ne me zafi ba wuya ya hauro abu kadan ne yake fusata shi, dan ta qara masa 6acin rai yayi kwanan ba'kin ciki ta qara da cewa.

"Ai Alhaji ba iya nan Taj Mahat ya tsaya ba, a halin yanzu maganar da nake maka ba komai yake a Russia ba sai 6arnatar maka da dukiya da kula kulen abokai na banza da kashewa 'yan mata kud'i gabadaya ya lalata maka companyn ka ya Kori qwararrun ma'aikata ya zuba sabi wanda basu San ciwon kansu ba, basusan komai ba Alhaji ya kamata ka dakatar dashi kafin ya rusa maka dukiya".

Tofa anzo wajen duk abinda Abba yake yana aiki da kwakwalwar sa da kuma tunanin sa jin wannan tsinannan jawabin da Mama ta kora masa yasa ya mata wani irin mitsiyacin kallo oh wato ya fahimci inda ta dosa ai bata iya qaryar bama taya zai yarda da wannan zancen yafi kowa sanin waye Tajuddeen a rayuwa domin shi ya haifeshi a gabansa ya girma shine ya bashi tarbiyya ko a mafarki Taj Mahat bazai ta'ba aikata haka ba.......

Ganin kallon da Abba yake Mata yasa ta d'an fara Sosa jiki tana cewa "Alhaji gaskiya na fad'a maka Taj Mahat baya aikin daya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment