Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai tsaye daga gurin Aunty Hauwa data fito part d'in su Tajuddeen ta wuce gurin Momy mahaifiyarsa tayi sa'a tana parlor a zaune yar aiki tana d'an daddanna mata kafafunta da sallama ta shiga tana dur'kusawa a kasan carpet cikin tsananin ladabin kamun kafa dason ta gano tana da matsala tace.

"Aunty Hajiya ina Ina kwana"?.

Ta karasa maganar muryarta na rawa kamar zata fashe da kuka murmushi Momy tayi tana kallon ta da fara'a tace "lafiya lau Samirah 'yar albarka kullum sai kinzo kin gaida ni gaskiya ina jin dad'i kinfi 'yan uwanki yan matan Mahat kirki kinfi su Salma suma duk basa zuwa min ziyara sai nayi kusan wata ban gansu ba ga Iklimah kobata nan ne itakam kusan wata biyu ma ban sata a idona ba"?.

'Dagowa Samrah tai tana cewa "tana nan Hajiya babu inda taje dama Iklimah ai bata da mutunci yarinyar nan mumafa da suka fiki kusa dasu bata shiga gurin mu tafi zuwa gidansu yaya Khaleel ko ki ganta tare da bros Rufa'i dai haka suna zaga estate din nan inaga sonshi ma take Hajiya dan akwai ta da ruwan ido".

Tunda Samrah ta fara magana Momy ke kallonta tana murmushi harta gama sannan tace "ayya ai idan taso aure tayi gaskiya Samirah auren shine darajar 'ya mace miyasa koda yaushe nakewa Fadilah fad'a dan ubanta ta tsayar da miji ta'ki Al'ameen nefa ke sonta amma sai yawo take masa da hankali ta'ki sauraronsa sam na rasa miyasa"?.

A abinda Mommy tace yasa a susuce Samrah ta d'ago har tana 'kwaruwa tace "Aunty hajiya wanne Al'ameen d'in"?.

Amsa Mommy ta bata da "Al'ameen dai wanda kika sani Al'ameen Mahat" ta karasa maganar tana yiwa yar aikin nuni da cewa ya isa haka taje ta huta itama.

Numfashi mai d'umi Samrah ta fitar jin sa'ar ta zatai aure ta barta kuma wai Al'ameen? Al'ameen Mahat fa? Kai anya zata yarda ta auri Al'ameen tana kallo bayan ita ga yayanta ya'ki ya saurareta ma balle wata maganar arziki ta had'a su ...........

Katse mata tunani mum tai da cewa "Samirah maza kije kitchen ki taya Batul zatai min tuwon alkama dan Allah ki kula sosai kada tayi min shirme domin Tajuddeen yana matukar so kinji"? To Samrah tace tana mi'kewa cikin mazari tai hanyar kitchen da murna domin jin Taj Mahat abinda yafi so kenan gashi itace zatayi Allah yasa idan ya dawo sai yaci ya yaba Mumy tace itace tayi ko idan tayi sa'a ya sota gashi dama bataso ta koma gida yanxu yadda bataje school din nan ba idan Aliyu Mahat ya dawo gida Umma ta fad'a masa saiya kusan hallakata tasan halinsa sarai shiyasa duk dokar daya kafa mata take bi a zauna lafiya kar taje tana zaune lafiya wata rana tayi laifin dazai mayar da ita nakasasshiya a banza ta'ki auruwa.

Sosai ta zage a kitchen ta yiwa mum tuwon alkaman mai kyau yadda ta bu'kata tayi mata miyan da isasshiyar ganda da nau'ikan spiece iri dabam dabam masu dad'in kamshi dasa girki yayi kyau a idon d'an'danonsa cui a baki saida ta gama komai sannan ta fito tana goge zufa lokacin karfe d'aya da rabi na rana har Amrat ta taso daga school ita da Fauzan tana zaune kusa da Mom suna zance zatakai sa'ar Aryam dan itama yarinya ce saidai Fauzan shi ta biyo zai kai shekara sha takwas.

Zama Samrah tai tana mayar da numfashi ta kalli Amrat wacce ke zubawa mum surutu kamar yayyafi tace "Amrat kun dawo daga school yanxu school bus ta sau'ke ku"?.

Kai ta d'aga mata tana cewa "eh aunty Samrah yanzu na dawo".

"Ok su Irfan sun shiga gida sannan ya Aliyu ya dawo ko kinga Dad d'inmu su Salma da Nabilah sun shigo ne"?.

Kai Amrat ta girgiza "eh Irfan tare muka dawo amma Uncle Aliyu ban ganshi ba aunty Salma da Aunty Nabilah sun shiga gidansu".

Kai Samrah ta jinjina tana cewa "amma amma Siyama fa ta shigo gidane ita da Nailah sannan Maryam ma ta tafi school duk kin gansu".

Nanma kai Amrat ta girgiza tana cewa "a'a ban gansu ba saidai ko sun dawo yanxu ban sani ba".

Mi'kewa Samrah tai tana kallon Mum tace "na tafi Aunty Hajiya sai anjima kar yaya Aliyu Mahat ya dawo bana gida dama kad'an yake jira yanxu nayi masa kuskure tun akan zancen Shadat bai ha'kura ba tunda nace bana sonsa yake jin haushina yake fakona ya samu yar wata kofar dazai jibgeni saboda dashi".

Kai Mum ta d'aga "ok Samrah nagode Allah ya rufa asiri amma ki d'auki tuwon man ki tafi dashi".

Zaro ido tai tana cewa "ai Aunty zasu gane banje school ba balle akwai Siyama kila har taje ta gulmatawa Umma bari naje zan dawo da dare sai nayi dinner anan".

"Ok to shikenan ba damuwa saina ganki" ta fad'a tana cewa Amrat "ki tashi kije ki cire uniform mana kina kallo d'an uwanki kuna shigowa ya wuce" to Amrat tace tana d'aukar school bag🎒 d'inta ta shige part d'insu.

Fita Samrah tai sai kalle kalle take alamar rashin gaskiya ganin dai kamar Aliyun bai dawo ba yasa tayi sauri taiwuf tana bude kofar gate din gidansu ta shige da gudu kusan kwaro sukai da Siyama wacce ta fito daga gidan nasu rataye da handbag👜 d'inta tasha glass an murza daurin kwali wani irin kallo taiwa Samrah d'in tana cewa.

"Samrah yau ina kika je ban ganki a school ba"?.

Had'e rai Samrah tai tana kau dakai tace "ban gane baki ganni ba kamar ya"?.

"Kamar yadda na fad'a miki har block dinku naje na tambayi qawar ki Diana tace min yau kince bazaje school ba, humm kin manta warning din Aliyu Mahat kenan kome"?.

Wani kallo Samrah taiwa Siyama jin abinda take cewa kafin taja tsaki tana wucewa tace "ban sani ba" da kallo Siyama ta bita tana jinjina kai sannan tayi qwafa tana cewa "Samrah kina wasa dani harnice zaki cewa wai baki sani ba woww yarinya zan sanar dake kuma zaki gani" tana fad'in haka ta bud'e gate ta fice.

Da'kyar Samrah ta shiga parlon su a sanyaye tayi sallama ganin kallon da Umma keyi mata yasa batai marmarin zama a gunba tayi hanya part d'inta cike da fargabaar wanne kalar sharri Siyama tazo ta 'kulla mata a gurin Umma Dan tunda taga babu fara'a a fuskarta yasa tasan yaufa sai sauranta tana shirin bud'e kofa ta shiga taji muryar Umma tace.

"Samirah yau a ina kika tsaya bakije school ba har Siyama tabi block block bata ganki ba"?.

Runtse ido Samrah tai cike da takaicin Siyaman muryarta na rawa tace "amm Umma ita ce tazo tace miki banje school ba yau"?.

"Eh itace kuma zatai miki qarya ne dan ta tsane ki gidan ubanwa kika je Samrah"?.

Juyowa Samrah tai kamar zata fasa ihun damuwa tana kallon Umma wacce zallar 'bacin rai ne kwance a fuskarta wani yawun tsoron abinda zai faru yau ta had'iye bakinta na motsi tana son magana kuma ta rasa me zatace.............

"Samirah zaki fad'a min inda kika je ta ruwan sanyi tun muna ni dake ko zaki bari sai Aliyu ya dawo ya tambaye ki"?.

Jin abinda Umma tace yasa a firgice Samrah ta bud'e baki muryarta na rawa tace "Umma Siyama qarya take min kinsan halin sharrin ta fa batun yauba bata da aiki sai sa ido da gulma".

Kai Umma ta jinjina tana cewa "ok yayi kyau Samirah tunda bazaki bani amsar tambayata kin raina ni saboda kinga ki taroni a tsayi kafad'arki tazo daidai da tawa jeki ai Aliyun zai dawo gidan zan had'aki dashi tunda shi namiji ne kina tsoronsa kuma baki rainashi ba zaki fad'a masa gidan uban wanda kika tafi".

Hawaye ne ya zubowa Samrah ganin yadda Siyama tazo ta had'a mata masifa a gida duk jikinta rawa yake sosai take tsoron Aliyu Mahat domin dama bai dad'e ba da yimata wani irin ba'kin duka akan wani saurayi a cikin Mahat d'in sunansa Shadat yana sonta ita kuma ta'ki anyi juyin duniya tace wallahi bazata aureshi ba tunda bata sonshi ba iya shi kad'ai ba matasa da yawa sun sonta itama kuma gabadaya hankalinta baya kansu ta tattare dukkan nutsuwa da soyayyaarta akan Tajuddeen Mahat wanda shikuma a nasa 'bangaren babu abinda ya tsana a duniya kamar yaji mace ta furta masa kalmar SO💓 abun yana 'kona masa rai shiyasa sam yake matukar jin haushin ta.....................

"Samirah 'bace min da gani anan".

Zabura Samrah tai jin Umma ta daka mata tsawa saboda tsaiwar datai kawai batai magana ba da sauri ta tattaro hankalinta tana cewa.

"Dan Allah Umma kiyi hakuri wallahi banje ko'ina b.............

Hannu Umma ta d'aga mata "ke kinga ki rufa min baki bana son jin komai ki barnan kafin na taso kanki badai kin nuna ban isa dake ba? ban isa na miki tambaya ki bani amsa ba saboda ga 'karamar dangarki mai dad'in tsallaka ko yayi miki kyau".

Kuka Samrah ta saki ba'kin ciki ya gama cika mata zuciya tace "Umma kiyi hakuri na fita daga nan d'azu saina shiga gurin Aunty Hauwa muna zance da ita shine nayi late a tafiya school ni kuma saboda ina tsoron dawowa gida ki tambaye ni shiyasa na tafi gidan Aunty Fatima (Mum Taj) na taya ta aiki amma wallahi ko fita daga cikin Mahat banyi ba".

Kai Umma ta jinjina "yayi kyau jeki ai dama nasan can d'in kikaje kawai dai na sake tambayar kine domin Ahmad lokacin da Hauwan tai kiransa yaje yakai Aryam school yana gida sannan bayan ya dawo yazo ya fad'a min a gidan ya sameki kina kuka kuma yaga fitar Tajuddeen daga gidan wato Samira bazaki yagewa kanki son wannan yaron bako saikin kamu da ciwon zuciya sanin kanki ne Tajuddeen ya fita dabam da sauran babu mace a gabansa kin sani ba tun yanzu ba amma tsabar rashin hankali ki tsaya ki saurari samari kin 'ki dame Aliyu yafi Tajuddeen 'yan watanni yabashi kece fa kika biyo Aliyu kalleki gand'and'an dake kamar tsauni Aliyu dayake namiji ma yayi aure amma ke kin tsaya hauka to Samira shawara zan baki kije kiyi tunani a cikin kanki ki samarwa zuciyarki salama idan ba hakaba nan gaba duk halin da kika shiga Tajuddeen wallahi babu ruwana na gama iya yina".

Umma ta karasa maganar tana jan tsaki shiru Samrah tai tana jan ajiyar zuciya bata sake magana ba da'kyar ta d'aga kafafunta da sukai nauyi ta fara tafiya zuwa part d'inta yayin da Umma ta bita da kallon takaici itakadai sai magana take.

"Haba da Allah yarinya sai shegen taurin kan tsiya kamar iya Tajuddeen ne matashi a Mahat aiko zuwa gidansu da kike xuwa gurin mahaifiyar sa Fatiman kowa yasan kamun qafa kike zuwa tsabar rashin ta qarji bari Abbanku ya dawo gaskiya bazan iya ba nagaji zance na cire hannuna daga cikin lamarin ki na bar musu shida Aliyu sai susan ya zasuyi mtswww".

Yawu mai d'aci Samrah ta had'iye cike da fargaba amma bata iya cewa Umman komai ba a hankali ta bud'e kofa cikin sanyin jiki ta shige tabar umma a falo sai fad'a take kamar da mutum a gurin bayan ita.

Tajuddeen bai dawo gida da wuri ba sai dare dan haka daya shigo Mahat part d'in Aunty Hauwa ya zarce sakamakon yace mata zai koma kar taga shiru amma ko zama baiyi ba kawai chocolate din daya sayowa Aryam ya bata itakam sannan ma hartayi barci ganin yana shirin fita yasa Aunty Hauwa tace.

"Am Tajuddeen ka tsaya kayi dinner d'in mana ba kace yau anan zakai ba"?.

Kai ya d'aga "eh Aunty Hauwa nace amma yanzu wanka nake bu'kata yau nayi aiki sosai gabadaya a gajiye nake bani na tafi dashi".

Mi'kewa Aunty Hauwa tai tana had'a masa kayan abincin cikin basket ta bashi tana cewa "kayi sa'a shagwa'bab'biyar taka tun d'azu tayi barci tunda ta dawo a school sai damuna take wai har yanzu Uncle bai dawo ba ita chocolate d'inta kuma fa wallahi wacce Ahmad ya sai mata harda sauran ta tadawo amma tsabar rigima wai taka take so da'kyar na lalla'ba ta tayi barci".

Murmushi Taj yai yana kallon Aunty Hauwa kafin yace "aita kyauta da take son kayan Uncle din'ta Ahmad yayanta ne uncle kuwa ubane kinga laifinta ne humm saima gaba zakusha kallo gatan da zanyiwa wannan yarinyar ko kaina bazan yiwa shiba da ace zanyi aure d'auke ta zanyi ta koma gida na saidai ta ri'ka zuwa muku yawo"?.

Dariya Aunty Hauwa tai tana zaro ido tace "to Allah ya kaimu lokacin ya bamu aron rai musha kallon da kake fad'a aure kuma Taj ai ya zama dole"?.

Da sauri yace "noo Aunty Hauwa bai zama dole ba"?.

"Au haba" ta tambaye da surprise a fuskarta.

Kai ya d'aga mata bil hakki tsakanin sa da Allah da abinda yake ji cikin zuciyarshi yace "yes Aunty Hauwa I have confirmed it bazan yi aure ba a haka zan kare rayuwata nifa mace indai tace tana sona to gaskiya a duniya dai babu wanda na tsana sama da ita Aunty Hauwa ke kanki saida ce magana ma banaso budurwa ta cika mini yanxu zata fusata ni, bari na tafi sai gobe zan shigo da wuri saboda baby Aryam insha Allah zan tafi dare yana yimin"?.

"Ok Tajuddeen muna godiya saida safe".

Fita Tajuddeen yai yana tafiya zuwa part d'insu ya kusa isa daidai Mery da Nabilah sun fito daga bangaren su Hafizah suka gaida dashi amsawa yai yana mamakin anya yaran nan suna da hankali duk da a tsare suke kuma a cikin gida ba layi ba amma Mahat nada girma yanxun gidan ubanwa zasuje duka tsara kwalliya haka hummm shiga parlor yai da sallama Mum ita da Amrat suna zaune dan haka yasa ya dakata yana zama shima suka gaisa kallon basket d'in Mum tai tana cewa.

"Deen daga Ina haka"?.

"Part d'in Aunty Hauwa".

"Ok aina d'auka ko yau kayi fushi da namu abincin ne shiyasa ka sayo a restaurant" ta karasa maganar cikin tsokana domin tasan babu abinda ya tsana kamar cin abinci a waje duk inda yaje saiya dawo gida yake cin abinci 'ka'idarsa ce kai ya girgiza.

"No Momy abincin waje fa haba a'a nace mata zanyi dinner a gurin tane kuma aiki ya hanani dawowa shine ta bani na taho dashi".

"Oh kuma kaga anan tuwon alkama yau mukai mai kyau ga daddad'ar miya".

"Ku kai"?.

Ya fad'a yana kallon Momy dake 6oye dariyarta tace "eh mukai me kagani wato da 'yar aiki ko? Ai Samrah ce tazo gidan sukai tare ina nan wallahi suka gama komai kuma masha Allah yayi dad'i".

Jin abinda Momy tace yasa bai sake cewa komai ba ya mi'ke zaiyi gaba Mum data bishi da kallo tana girgiza kai tace.

"Deen yaushe kace zakai tafiyar nan"?.

"Next week insha Allah".

"Ok Allah ya kaimu".

Amin yace yana shigewa part d'insa cike da mamaki baiyi tunanin d'anyan kan Samrah har yakai haka ba wato yanzu ta inda ta 6ullo kenan xuwa gurin Momy saboda neman hanyar samun gurin zam humm lallai ta kama gaibu amma yana daidai da zamaninta.

Misalin qarfe sha d'aya na dare Siyama tana d'aki da waya a hannunta sai chatting take da qawaye tana dariya Mama ta bud'o kofa tana shigowa tare da zama tana kallon ta tace.

"Tashi kibar wannan haukan zamuyi magana dake mai muhimmanci".

Tashi zaune Siyama tayi tana aje wayar tare da mayar da hankalinta kan Maman tace "Mama lafiya"?.

Kaita d'aga mata tana sakeyin kasa da murya tace "inafa lafiya kina sane da cewa Tajuddeen zai bar kasar nan next zuwa Russia ko kinsan da maganar tafiyar"?.

Kai Siyama ta d'aga "eh Mama na sani wani abu ne ya faru"?.

"A'a ko d'aya babu abinda ya faru kawai inaso zaku tafi tare ne dake kin gane"?.

Zaro ido Siyama tai "Mama tare dani kuma me zanyo acan''?.

Gyara zama Mama tai tana cewa "kinsan ne Siyama nifa ina duba miki duk wani abu dazai kawo miki cigaba a rayuwarki ne kin gane kina kallo yadda yan matan Mahat ke rubibi akansa kowa so take ta sota kigafa wani mahaukacin tafkeken gida daya gina wanda akaf Mahat babu irinsa ka kud'i daya zauna masa eye kisamu ki samu kusanci dashi sosai kija hankalinsa shiyasa zan had'a tafiyarku tare zancewa Dad d'insu kema a tafi dake ki karo karatun acan nasan zai yarda saboda Alhaji akwai tausayin maraya da kukana zanje dan yafi yarda da wuri.

(Siyama agola ce da ita Mami ta auri Daddyn Tajuddeen tun tana karama akazo da ita gidan mahaifin ta ya rasu).

Kai Siyama ta d'aga tana murmushi tace "kuma fa Mama sai yanxu na gane kinsan idan muka tafi acan ya kamata nayi duk abinda ya dace domin babu mai takura min ko mai mun shishshigi kamar Samrah Hafizah Nabilah Maryam da sauransu kinsan duk suna sonshi".

Qwafa Mama tai tana cewa ''barni da tsinannu suna so su 6ata min mafarki na domin idan na samu kika aureshi da kin haifi d'a d'aya zamu kashe shi kinsan dalilin bari sai kin haihun? Saboda idan baki haihu ba iya tumuni za'a baki sauran dukiyar iyayansa ne zaku ri'ke amma idan kin haihu duka dukiya gurin mu zatayo tunda yana d'a shizai gaje dukiyarsa dan Allah Siyama ki jajirce a Russia kada ki tsaya sakalci ko wasa ki tabbata kinyi abinda tafiyarki take nufi ki janye ra'ayin sa wanda kuna dawowa sai zance aure Kinga zai dad'e inaso kiyi amfani da kwakwalwarki ki gigita kawunan yan matan gidan nan suga kun dawo Tajuddeen yana nuna miki wata iriyar soyayya wacce zatasa suyi suman ba'kin ciki ki samu da cutar hawan jini da ciwon zuciya😳.

Dariya Siyama tai tana cewa "insha Allahu Mama bazan baki kunya ba nayi miki alkawarin zan dawo zuciyar Taj Mahat cike da sona zan baiwa kowacce shegiyar budurwa a Mahat mamaki sannan nayi musu zarce".

Kai Mama ta d'aga ''yauwa yar albarka haka nake son ji kinga yanzu lokaci yana ja karfe sha biyu da rabi bari na tafi zuwa gobe saimu karasa maganar tunda weekend ne babu inda zakije amma ban sani ko idan nayi sa'a a gobe Alhaji yace kizo kije kiyi passport sai ki zama cikin shiri kinji ko"?.

"Ok shikenan Mama ina saurara".

Mi'kewa Mama tai tana fita a d'akin yayin da Siyama ta mi'ke tana sauka a gadon taje jikin window tana bud'e labule kawai ta zubawa waje ido sansanyar iskar mai dad'i tana ratsata sai murmushi take tuna wai zasu samu ke'bewa ta lokaci mai tsawo ita da Tajuddeen aiko wannan damar data samu bazatai wasa da ita ba.

Washe gari kamar yadda Taj Mahat ya fad'a tun safe yana part din Aunty Hauwa suna ta hira sai kusan qarfe d'aya ya d'auki Aryam da Amrat a mota ya kaisu suka sha ice-cream🍦 da guraren wasa iri iri dama duk weekend yakan yi musu haka dan faranta musu da sasu nishad'i a matsayinsu na 'yan yara👭 bai dawo dasu gida ba sai jikin magriba.

A ranar suka gama magana da Daddy akan tafiyarsa zaije ne gurin wani babban company da Daddyn ya bud'e acan akwai aiyukan dazai kuma zaiyi kara karatu na shekara uku kafin nan ya dawo saidai da yaji tafiyar wai harda Siyama ransa ya 6aci har zaicewa Daddy ya fasa sai kuma ya share jin Mami ce mai koro bayanin wai Siyaman karin karatun itama zataje tana dawowa kuma zata fara aiki a Taj Mahat special hospital kai ya jinjina kawai ya bar komai a ransa dan ya rantse da Allah ko Mahat zata kama da wuta tsabar hayaniya bazai amince Siyama ya d'auke ta wani doctor a hospital d'insa hum'um abin da bazai yuwu bane.

Bayan sati d'aya suka tafi a ranar hankalin Samrah ya tashi jin harda Siyama aka tafi gani take kamar ta rasa Taj Mahat har abada tayi kuka ta shiga damuwa haka ta hana kanta sukuni ta daina zuwa ko'ina kullum tana gida a bedroom zaune ta zuba tagumi da hannu bibbiyu tayi shiru ga hawaye yana zuba.

Haka 6angaren Hafizah ma dasu Nabilah kowa dai a cikin yan matan ya shiga rud'u yayin da Mama take cike da farin ciki ita kuma gani take a yanzun kamar har Siyama ta auri Taj irin hutun nan ya d'auketa suka tafi kuma abinda ta kunsa a ranta shine idan har ta samu Siyama ta auri Taj Mahat shikenan zata raba soyayyar dake tsakaninsa da mahaifansa zai tsanesu ya sharesu ya manta dasu a cikin rayuwarsa karshe zata kashe Daddy domin ta samu a raba gado tunda bata haihu dashi ba shiyasa tacewa Siyama ta lura sosai tasa ido akan duk abinda Tajuddeen zaiyi acan taga yawan dukiyar Daddy ta Russia domin dama da manufar le'ken asiri ta bishi bawai karatu ba Mami tasa a ranta idan ta cika burinta zata tattara yanata yanata tabar Mahat taje tasai gida ta zuba tsaro zuwa wani lokaci Shima Taj din su hallaka shi su yashe dukiyar wannan shine next target d'inta shiyasa tun daga yanzu ta samu babban littafi take rubuta duk abinda zai faru a gaba dan kada ta manta wani🤔.

TAB'DIJAN DANQARI ASHE YANZU AKA FARA MUJE ZUWA MAI HANKALI YAHAU KURA🐆🐅.

Tunda sukaje Taj yake aikinsa abinda ya kaishi wato kula da campanyn Daddy sannan yana karin karasunsa school d'aya suke da Siyama amma ba gida d'aya suke ita macece shi namiji ne sannan ba maharramarsa bace dan haka koda wasa baya amincewa ta shiga masa gida ba school idan ma bukata take dashi saidai tayi kiransa a waya ta fad'a masa gajiya tayi da shariyar abun ya kaita bango ta Kira Mami a waya da kukanta take fad'a mata saita kwantar mata da hankali cewa ta rabu dashi jinkai na yanzu ne daga lokacin da zatasa a karya asirin reshe zai juye da mujiya Taj Mahat zai raina kansa a hannunsu zasu gargarashi su juyashi yadda ransu yake so dan hakane Siyaman ta d'an d'auke hankalinta daga kansa har ta kama mu'amala da wasu samarin banzan a 6oye batare da sanin Taj ba domin sun nuna Mata zallar kud'i ganin abinda take so kenan Mami ta riga ta bud'e mata ido dason kud'in komai zatace kud'i duk motsinta kud'i sosai Siyama samari ke kashe mata kud'i harda turawa saidai a inda gizo yake sa'kar dan bu'katar kansu ne kowanne a cikin su ukun ba wanda bai nunata cewa jikinta yakewa ba amma ganin sun cika mata account da daloli yasa kawai ta manta wacece ita macece mai kima da daraja wacce sai an biya sadaki tabar karatu tabar layin kwarai ta fad'a harkar banza, gashi abinda Mami ta jawo mata sadaka batai maganin masifa ba.

NIGERIA 🇳🇬
Samrah tana bedroom a zaune idonta a rufe hawaye yana zuba jin an bud'o kofa yasa da sauri ta kifa kanta cikin wayancewa ta goge hawayen fuskarta tana daidaita kanta ganin wacce ta shigo yasa ta d'an saki murmushin dole tana cewa.

"Diana ki karaso man ya kika tsaya anan"?.

"Karasowa Diana tai tana zama cike da mamaki ta kasa dauke idonta akan Samran ganin yadda ta rame ta lalace tayi ba'ki kafin ta jinjina kai tana cewa.

"Samrah meke damunki ya haka me kike wannan kina kallon kanki mirror kuwa"?.

Sauke numfashi Samrah tai tana kokarin hana hawayen da suka taho fitowa muryarta cikin tsananin damuwar rashin sanin mafita tace "to ya zanyi Diana me zance kina ganin dai abinda ke faru a Mahat dama nace miki na'ki yarda na auri Shadat akan Taj Mahat to yanzu maganar da nake miki Shadat Mahat yayi aure ya auri wata cousin d'ina Batula Rufa'i Mahat yace Iklimah Mahat zai aura kuma kinga Hadizah Mahat itama tayi aure maganar da nake miki yanxu Al'ameen Mahat ne yake son Fadilah qanwar Tajuddeen Mahat nifa banida kowa bani da komai duk sa'anni na sunyi aure sun barni Taj Mahat ya'ki ya saurare ni Daddy da Umma sunce ba ruwansu ya Aliyu Mahat har fasa min jiki yayi saboda wannan al'amarin Diana ki bani shawara yanxu ya zanyi zuciyata gaf take da tarwatsewa a halin yanxu Taj Mahat yana Russia sun tafi tare da Siyama suna can wa yasan irin gwallin da zatai masa ya kamu da sonta ina kallo su dawo suyi aure wallahi bazan iya rayuwa ba Diana ni kaina bansan wanne irin so tanewa Taj Mahat ba dan Allah Diana kiyi wani abu" Samrah ta karasa maganar tana fashewa da kuka.

Shiru Diana tai cikin nazari tana kallon qawar tata cike da tausayawa domin gaskiya ta fad'a gararin soyayya kuma soyayyar ma mara amma ba wacce kake so ake sonka ba..................

Katse mata tunani Samrah tai ta hanyar girgiza

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment