Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamata acan kuma kaje masa ziyarar bazata saika gaskata abinda nace maka".

Kai Abba ya d'aga mata bai nuna wata alamar maganar data fad'a akan Taj d'in ta dameshi ba yace "oh haba wai da gaske? Hum to naji" yana fad'in haka ya rufe laptop d'in gabansa tare da mi'kewa ya shiga bedroom cizon yatsa Hajiya Jamila tai kamar zata fasa ihun takaici ganin tarkonta bai kama komai ba itama mikewar ta har zata bi bayansa sai kuma ta fasa tana jan tsaki cikin ba'kin ciki ta fice a fusace a ranta ta gama aiyana zatai tashin hankali a Mahat kwanan nan.🤔 TOFA ASHE ZAMU SHA KALLO HAJJAJU JAMILA KINA WUTA💥🔥 INA BINKI DA FETUR.

Tana komawa part d'inta ta soma kai koma cikin tunanin ta Ina zata fara me zatai wacce hanyar zata 6ulla tayi nasara¿ kasa nutsuwa tayi balle ta iya barci har asuba tana zaga d'akinta ta juya nan ta juya can Babu alamar jin barci a idonta domin abinda yake gabanta ya Kori mata komai da take ji a ranta washe gari ma saboda jin haushin maganar da sukai da Abba da dare bata le'ka part d'insa ba har yai wanka ya shirya ya tafi office bata kula iskarsa ba Shima kuma dama da 6acin ranta ya kwana yana nadamar auren mace irinta wacce bazata bar zaman lafiya ya zaga ahli ba.

Bayan sunyi breakfast kowa ya koma part d'insa babu kowa a parlor Al'ameen Mahat ya shigo yana zama akan daya daga cikin d'uma-d'uman kujerun da sukaiwa parlon zobe tare da d'auko wayarsa yana sake danna kiran Fadilah wacce take d'aki tana zubda hawaye tunda yace mata zai zo gurin ta yau ya kasa fahimtar bata sonsa balle ya rabu da ita.

Fitowar Hajiya Jamila kenan ganin daya daga cikin zaratan samarin da ake ji dasu a Mahat zaune kuma tasan abinda ya kawo shi bazai wuce gurin Fadilah yazo ba yasa gabanta ya fad'i da sauri ta juya har tana cin mugun tuntu'be ta fad'i kasa amma a guje ta mi'ke tana shiga part d'inta ta bud'e wata kofa ganin budurwa zaune tana kwalliya yasa tace.

"Faridah me kike har yanzu baki gama kwalliyar ba gashi aikin da nake so kimi yaron fa ya shigo haba faridah karki dora min hawan jini man kinsan fa saboda haka na tambayi Alhaji ki baro gurin Hajiya Dijah ki dawo inda nake tunda ya amince zai rikeki kamar yadda ya ri'ke yar uwarki Siyama".

(Faridah ma 'yar gidan Hajiya Jamila ce qanwar Siyama ce ubansu daya).

D'agowa Faridah tau tana karasa gyara d'aurin kwali ta sake kallon mirror kafin ta dau handbag d'inta da gyale ta juyo tana kallon Hajiya Jamila dake faman binta da kallo ganin yadda tayi kyau dariya faridah tai tana sakin murmushi tace.

"Sorry Mama ai kinsan dole na tsaya na tsara kwalliya yadda ganin farko zai burkice ya susuce a kaina tunda kince ba sonshi takeba ita Fadilan ni kuma zan nuna mata tayi kuskure a lokacin dazan jawo shi jikina na nuna masa so da qauna wacce kowa zai firgita humm Mama tunda kika nuna min photonsa fa na kasa samun nutsuwa na daina barci mai dad'i kullum sai tunani taya zanyi sake dashi ki kwantar da hankalin ki wannan gayen kamar na aureshi ne an gama" ta kasara maganar tana kashewa Hajiya Jamila ido.

Sauke ajiyar zuciya Hajiya Jamila tayi cikin farin ciki tana cewa "ok shikenan yar albarka jeki maza kafin shegiyar Fadilan ta fito naso ace kece kika samu Taj Mahat ko kuma ace kamar yadda kike da tsiwa haka Siyama take hum dana more wallahi na zama billionaire amma hakan ma ba komai tafiya sannu sannu kwana nesa muje zuwa Nan gaba hatta matashin kai da kud'i zanyi🤔".

Dariya faridah tai tana fita a d'akin ta bar Hajiya Jamila sai sambatu take tana hasko yadda kwanan nan zata jike da kud'i idan har burinta ya cika ta kashe Abba Taj ya auri Siyama Al'ameen Mahat ya auri Faridah tabd'ijan akwai gwangwazo wallahi bazata zauna a Nigeria ba yankin yurof zata koma ta kafa sabuwar rayuwa da qasaitacciyar daula.

Takalmi me qara wanda kana tafiya anajinsa Faridah ta sauko tana takawa qas qas cikin son d'aukar hankalin Al'ameen Mahat ta fito tana bud'e dukkan girman idonta a kansa domin ta rud'e gaskiya a fili yafi kyau akan a photo tab itakam tayi tsuntuwa karasowa tayi har lokacin yana zaune shi kad'ai a parlor Fadilah ta'ki fitowa duk ransa ya 'baci yanata kiran wayarta ta'ki d'agawa.

Zaman Faridah tayi a kujerar dake opposite d'in tasa tana qureshi da kallo gaskiya ya matukar had'uwa fad'a 6atawa d'ora qafa d'aya kan d'aya tai cikin salo da qashe murya tace.

"Barka da kwana Al'ameen Mahat ya kake"?.

Da mamaki Al'ameen ya d'ago yana kallon ta ita kuma wannan wacce ita daga Ina taya tasan sunansa? Mahat tana da girma ba duka yasan kowa da kowa ba duk da shi ba mazauni bane yau yana wannan qasa gobe yana wancan qasan saidai yasan 'yan matan Mahat basa irin wannan kwalliyar a fuskarsu koda ana biki ne qa'idarsu ce ita kuma wannan abun nata yayi yawa yasan dai ba'a nan take ba maybe bakuwa ce ya fad'a a ransa tare da d'an ta'be baki ko inda take bai sake kallo ba burinsa Fadilah ta fito suyi sallama maybe a yau zai bar Nigeria zuwa Bercelona (Spain) Al'ameen Mahat soja ne kaf girman Mahat d'aga Tajuddeen Mahat sai shi a yawan dukiya da shahara......

"Al'ameen ina magana ka shareni¿ Kodan ba sani nakayi ba? ko baka gaisawa da ba'kuwar fuska haka ne"?.

Faridah tai maganar tana sake kallon sa har lokacin yayi Mata banza kamar babu mutum a gurin cije lips tai takaicin shariyar dayai mata ya fara kamata taci gaba.

"Haba Al'ameen Mahat koba komai ya kamata ka min magana ina mace na aje ajina na kulaka amma kai kuma ka share ni why"?.

Wani irin kallo yayi mata batare da ya motsa koda lips d'insa ba, kan bala'i wani irin takaici ne ya rufe ta ji take kamar ta tashi ta rufeshi da duka tsabar ba'kin ciki bud'e baki tai zatai magana aka bud'o kofa a tare suka kalli wurin Fadilah ce ta fito sanye da farar abayat idanuwanta sunyi ja alamar kuka tai kallo d'aya taiwa duk su biyun kafin ta d'auke kai tana nufar hanyar ficewa daga parlon muryar Al'ameen Mahat ta dakatar da ita.

"Fadilah Ina zakije bayan kinsan gurin ki nazo tun d'azu ke nake jira kuma dan raini shine zaki wani zo ki fita"?.

Ko sauraron sa batai ba taci gaba da tafiya kai ya jinjina yana cewa "Fadilah Wallahi tallahi na rantse da Allah idan kika kuskura kika fita a palon nan ranki inyai dubu saiya 'baci".

Tsayawa Fadilah tai cak guri d'aya kamar an dasata tare da juyowa tana kallon sa ganin ya taso ya nufo inda take yasa ta dur'kusa a gurin tana d'ora hannu aka ta fashe da kuka ta rasa meyasa take masifar jin tsoron Al'ameen Mahat Saboda soja ne shi kuma ya'ki ganewa ya rabu da ita wallahi ko kad'an bata son kusancinta dashi meyasa bazai kyaleta ba ta tabbata indai ta bari ya aureta bazata iya zama dashi ba..........

Karasawa yai har inda take cikin tsawa yace "Fadilah d'ago min kanki kuma ki share wannan hawayen banzar dake zuba ban fad'a miki kada ki bari na sake ganin zubar hawaye a idonki ba are you out of your sense kinsan wanne irin hali da gararin da zuciyata take shiga idan na ganki a haka wannan yanayin naki yana mummunan 'bata min rai ki rufa min baki kafin nayi bol dake anan wurin"?.

Tsit Fadilah tai ta kasa motsin kirki sai kame jikinta take kuma har lokacin tana dur'kushe, tsaki Al'ameen Mahat yaja da qarfi yana cewa "tashi ki 6ace min da gani zanyi maganinki komai yazo qarshe" yana rufe baki ta mi'ke da gudu tana toshe bakinta dan kar yaji sautin azababban kukan daya taso mata da gudu ta juyo zuwa part d'insu, da kallo ya bita tare dayin qwafa yana fita a parlon mi'kewa Faridah tai cike da takaici ta shige part d'in Mama domin ta sanar mata basuyi nasara ba su sake shiri tun a falor suka had'u Hajiya Jamila na ganinta ta mi'ke daga zaunen da take tana cewa.

"Tofa yaya? Yaya? Ya na ganki babu fara'a"?.

Wulli da handbag d'inta Faridah tai tare da yage daurin kwalin ma ta jefar tana huci tace.

"Wallahi mama bazan yarda harni zai wulakanta".

"Me yayi miki"?.

"Wai tsabar cin mutumci ina ta masa magana ya shareni sannan tsinanniyar Fadilan ta fito a gabana yake ce mata wani wai tasan irin gagarin da zuciyarsa take shiga idan yaga zubar hawayen ta".

Tsaki Hajiya Jamila tai tana cewa "oh akan wannan kike damuwa barmin komai a hannu na ai yauce ranar had'uwar ku ta farko kada ranki ya 6aci nayi miki alkawari saikin auri Al'ameen Mahat kamar yadda nayiwa Siyama alkawarin auren Tajuddeen Mahat kuma bazan fasa ba bazan janye kudurina ba koda zan tafi tsirara ne saina cika burina'' Hajiya Jamila ta karasa maganar tana dun'kule hannu kamar me shirin dambe tare da sakin murmushi ita kad'ai a ranta tana jin dad'i inta tuna gaba akwai shanawa.

Da gudu Fadilah ta shiga parlon d'insu kusan karo tai da Momy wacce take kokarin fitowa da sauri Momy ta bata hanya ta wuce a firgice domin ta kawo qarfi tana zuwa ta zube akan gado tana sakin kukan da take ri'kewa Momy da tabi bayanta ganin abinda take yi yasa ta tsaya tare da ri'ke murfin kofa tana girgiza kai cikin takaicin shirmen da Fadilan keyi tace.

"Fadilah wannan wanne irin shashanci ne? Wai meye laifin Al'ameen Mahat meye abun 'ki a gurin sa Fadilah anya kina da hankali kuwa yaron nan iya so da gata ya nuna miki kulawa amma kullum ke burinki idan yazo gurin ki kisanya masa damuwa? To bari kiji abun naki ya isa haka bazan cigaba ta zama kina min shashanci ba nice na haifeki kuma na isa dake dan haka kafin ki kaini bango ki tsaya kiyi tunani idan kuma kin qi bari Abbanku ya dawo zan fad'a masa komai saiya d'auki mataki haba wacce hauka kike yi haka kina kallo yan mata sunfi karfin qirge a Mahat amma duka ya sharesu saike yake so ke kuma miyasa zaki saka masa da kiyayya haba Fadilah dan Allah kisa nutsuwa".

Ita dai Fadilah kuka kawai take ta kasa cewa komai ganin haka yasa Momy tace "shikenan idan kin gama kuka ki sameni a kitchen ina jiranki".

Cikin shashshe'ka Fadilah tace "Momy dan Allah idan Abba ya dawo ki tambaye shi zan tafi gurin Hajiya".

Wani kallo Momy tai mata jin ta inda ta 6ullo maganar da ake mata dabam itama wacce take yi dabam kai Momy ta jinjina tana cewa "ai basai ya dawo ba zaki iya tafiya ko yanzu ne kofa a bud'e take waya hanaki ina kina da mota¿ Allah ya tsare hanya" Momy tana kaiwa nan ta bud'e kofa ta fice tashi zaune Fadilah tai tana goge fuskarta tare da mi'kewa ta nufi wardrobe ta fara tattara kayan ta tana sasu cikin trolley saida ta gama ta zuge zip saidai me tasan idan ta fita yanzu tsegumin 'yan matan Mahat ma ya isheta bari ta jira magriba kafin Abban su ya dawo ta samu ta fece d'an Batta idan Al'ameen Mahat ya tafi Bercelona saita dawo dan matukar yana Mahat bazata samu nutsuwa ba.

Kai tsaye bayan fitar Al'ameen Mahat gidansu ya koma ransa a had'e da'kyar yayi sallama zai wuce part d'insa Ummi ta dakatar dashi "Al'ameen daga ina? Meya faru naganka a haka dawo nan"?.

Tsayawa yai yana juyowa ganin harda nahaifansa a falon harya dawo daga gurin aiki yasa ya sauke numfashi yana kokarin daidaita yanayin fuskarsa ya dawo ya zauna tare da gaida dashi amsawa yai yana dubansa sosai yace "Al'ameen wani abu ne ya faru naga ka shigo cikin fushi daga Ina kake"?.

D'an shiru yai zuwa wani lokaci yana son muryarsa ta daidaita kafin yace "naje gidan su Tajuddeen ne".

Kafin Alhaji Musa yayi magana ummi tace ''gurin Fadilah? Shiru Al'ameen yayi ummii taci gaba "wai dan Allah Al'ameen miyasa dole sai ita duk yawan yan matan Mahat yarinyar bata sonka ko ana so dole ne? ka ha'kura man ka nemi wata a gani na zaifi wannan shirmen da 6ata lokacinka akan wacce bata damu dakai ba".

Da sauri Al'ameen ya girgiza kai har yana dafe saitin zuciyarsa jin abinda take cewa wanda yaji saukar abun kamar za'a zare xuciyarsa daga jikinsa ne yace "nooo ummi dan Allah ki daina cewa na rabu da ita ina sonta yarinyar nan itace numfashi na idan nayi wasa da ita tamkar nayi wasa da rayuwata ne taya zan iya rabuwa da ita bayan whole world d'ina ce".

Kai ummi ta jinjina tana ri'ke baki tace "to ikon Allah sai kallo tabd'ijan Al'ameen wato sonta har yayi xurfi a zuciyarka kamar haka? Amma tunda tace batayi ka kyaleta man".

Gyara zama yai kamar Fadilan tana gurin yace "Wallahi ummi bata isa ba saina aureta wannan alkawari nane dan ubanta harni zan zauna tana juyawa".

Zaro ido ummi tai tana kallon Al'ameen da mamaki yayin da Alhaji Musa yayi murmushi yana cewa "wato Al'ameen isa da mallaka ko? Biyan bashi da d'an kishiya harda wani dan ubanta bata isa ba hum to ai nine uban nata dan ni kenan tunda daughter na tace bata so an wuce gurin xanje na samu Alhaji Aliyun zamuyi magana baza'a takurawa yarinya ba indai bata so dole a ha'kura".

Jin maganar da Alhaji Musa keyi yasa hankali tashe Al'ameen Mahat ke kallonsa cikin fargaba ya sani matukar sukai magana tasa ta qare Fadilah ce numfashin sa dole ya tari al'amarin tun kafin mahaifin nasa yaje gurin Abban su fadilan, mi'kewa yayi bai sake cewa komai ba ya shiga part d'insa ya fara shirya kaya domin insha Allahu idan bai tafi Bercelona yauba zai tafi gobe.

🔥Hum yanzu aka fara🔥
YÚSRÃH MÛSÃ ABUBAKAR 💋 ce.

Fans bari kuji ta yadda akai wannan qayataccen guri ya samo asalin sunan sa MAHAT.

MAHAT👇
M-Mühämmäd
A-Älïyü
H-Hämëëm
A-Äl'ämëëñ
T-Täjüddëëñ
M+A+H+A+T_____=MAHAT KYAKKYAWAN MATASA BIYAR KENAN 'YAN KWARAI JAJURTATTU KUMA KAFAFFU MASU KWARJINI DA AJI WADANDA SUKA DAUDAKA AKA SANSU AKE SONSU YAN MATA KE RUBIBINSU😉😆 ZARATA NI'IMTATTU JARUMAI NA GASKE..
Mutum biyu sunyi aure Aliyu Mahat da Hamim Mahat.

MÃHÃT HÕUSÍÑG ÉSTÃTÉ🌃🏙️
Babbar daulace wacce aka qawata da kwalliya taban mamaki aka kashen ma'kudan kud'ad'e masu matukar yawa wajen samar da ita da katuwar katanga mai tsananin tsayi da tsaro da akwai manyan gate sunkai biyar duka na shiga da fita ne daga estate d'in saboda girmanshi family ne masu yawa a cikin sa 6angare 6angare kakanni iyaye da 'ya'ya yawa da girman mahat zaikai gidaje ashirin a ciki kuma dukka yan uwan juna ne babu bare saidai idan ba'ko akai.

Ta yadda yaci sunan Mahat kuwa wadannan gwarazan matasan biyar suka samar da sunan ta hanyar jajircewarsu da popular da sukai a ko'ina an sansu kuma anayi dasu kowanne matashi akwai bangaren aikin da yake wanda tanan yayi suna ya sanu sunfi kowa qwazo su biyar d'in duk da Mahat cike take dam da matasan samari da yan mata amma wadannan din sune jagorori an dauki harafin farko na sunayensu aka had'e guri d'aya suka samar da Mahat Muhammad Aliyu Hamim Al'ameen Tajuddeen.

Sannan mafi yawa basu cika fita waje suyi aure ba domin akwai zu'ka zu'kan 'yan mata na kece raina a Mahat kyawawa masu aji da d'aukar hankali wadanda za'a kirasu na gaban jirgi 🛬 na gaban mota kuma asalin kakanninsu shuwa arab ne na haqiqa.

Amma duk da yawan gidan familyn kala kala ne wasu sunfi wasu kusanci kamar Tajuddeen da Daddyn Aryam sun had'u ne ta kakanni da kakan Taj da kakan Dad d'in Aryam suke 'yan uwan Taj da Dad suka zama abokan wasa Taj yana matsayin qanin Dad ya tashi Uncle a gurin Aryam ba uba ba kodan ubanne amma ubale😀 domin kunsan uba shine wanda aure ya haramta dashi kamar qanin uba uwa daya uba d'aya Taj kuwa kakanu kadai suka had'a da Dad amma akwai ala'kar aure tsakanin Aryam da Taj💃kuma a Mahat dangantaka-dangantaka ne wani sunfi kusa da wasu kamar Tajuddeen Mahat da Hafizinah Mahat da Aryam Mahat sunfi zama dangin juna sosai akan da sauran sune iyayensu suka fi had'a jini kakansu dai ya rasu amma kaka macen sunanta Hajiya Aisha takwarar Amrat ce tana can a d'an Batta sunyi mata katon gida sakamakon bayan rasuwar mijinta cewa tai bazata iya zaman cikin Mahat ba shiyasa ta koma d'an Batta kuma sukam kansu a had'e yake had'in gwiwa sukai suka samar da dan'kareran gida guda d'aya mai part uku kowa ya shiga d'aya Abban Taj Daddyn Hadizah Daddyn Aryam.
Wannan shine kad'an daga cikin abinda Mahat ta 'kunsa muje zuwa.

Dare nayi Al'ameen ya fita a gidansu ya shiga gurin Abba yayi sa'a yana falonsa shi kadai bayan ya zauna ya gaishe dashi sannan yayi masa bayanin komai abinda ya faru tsakanin sada Fadilah ran Abba ya 'baci sosai ya tsani yaga mutum na sonka kana wulakanta shi amma zaiyi maganin abun badai shine ya haifi Fadilah ba hummm kallon Al'ameen Mahat yai yana cewa.

"Kana jina Aminullahi kayi hakuri abinda ya faru ban sani bane amma da duk ba'a xo wannan matakin ba karka damu yanzu yaushe zaka tafi"?.

Cikin d'an jin sanyi sanyi Al'ameen yace "Abba gobe ne da yau zan tafi amma sakamakon bata ara min lokaci munyi magana ba yasa na fasa sai gobe".

Kai Abba ya d'aga yana cewa "Ok Ina so ka d'aga tafiyar xuwa satin sama tunda kace dama lokaci baiyi ba saboda abinda Fadilah tayi maka kake son barin Mahat ina son zanyi wani abu wanda babu zato zai faru".

Kai Al'ameen Mahat ya d'aga yana cewa "to Abba zan d'aga tafiyar zan Kira abokina Ammar na sanar dashi domin shi tun tuni yaje ni suke jira".

"Ok babu damuwa Al'ameen zan nemeka zamuyi magana jeka" mi'kewa Al'ameen Mahat yayi cikin jin dad'i yana cewa "na gode Abba Saida safe".

"Ok Al'ameen mu kwana lafiya".

Al'ameen ya matukar jin dad'in yadda Abba ya fahimce shi ba kamar mahaifin saba da yake kokarin dakatar dashi alhali Fadilah tana neman kashesa da ransa bashi da buri sama da aurenta dukka abinda ya mallaka ace ya bayar saboda ita ya fansheta ko ta soshi zai bada gabadayan sa Fadilah ce rayuwarsa.

MUHAMMAD MAHAT
Matashin d'an wasan qwallon kafa sannanne kuma qwararre.
Abeedah da Beenafah suna palor a zaune ya fito fuska a had'e ganin yanayin sa yasa kowa ta nutsu dan sun san kwanan zancen akan haka yanxu abu kad'an xasuyi yaci ubansu ya kora da ruwan faro zama yayi kusa da mum d'insa yana gaida ita dubansa Hajiya Aisha tai da murmushi tace.

"Yadai Mohan kodai zancen jiya ne baiyi maka dad'i ba? Kafi kowa sanin halin Daddynku akan abinda yai niyya baya fasawa dan haka kayi hakuri kaifa namiji ne kuma an sanku da qarfin zuciya ka kwantar da hankalin ka, ko maza ma basu isa ba balle mace me zatai maka dahar zaka sawa kanka damuwa"?.

Tunda hajiya Aisha ta fara magana sai yanxu ya d'ago ya kalleta yana cewa "mum kinsan nifa bana qaunar mutum me mugun surutu kuma dai kinsan halin Zainab nidai gaskiya mum ai min exchange nifa bana son auren ma gabadaya".

Kallonsa sosai Hajiya Aisha keyi kamar zatai dariya sai kuma ta maze tana cewa "ok to ai sai a fasa tunda baka son mace me surutu akwai kurame masu yawa Nima nasan wata yar by pass d'in mu sunanta Batulah zanyi magana da Dad d'inku kaga sai a aura ma maka ita ka huta da surutu ko"?.

Qara had'e fuska yai yana cewa "wacce irin kurma kuma mum"?.

"Kurma dai wacce ka sani".

"No mum nidai bazan iya ba pls ki taimakeni".

"A'a Mohan nikam bazan taimake kaba domin maganar gaskiya ina so kayi aure".

Jin abinda ta fad'a yasa ya qara d'aure fuska zai mike ta mayar dashi tana cewa "wai duk fushi na miye ne? To abar maganar kaje ka gaishe da mamanta kafin ka tafi nasan tunda ka dawo bakaje gidan ba meyasa wacce irin soyayya ce wannan"?.

Qin magana yayi yawani narke mata kamar yaro mi'kewa tai tana ri'ke da hannunsa suka isa dinning da kanta tayi serving d'insa abinda yake so sannan ta ri'ka bashi kuma yana zuba mata zance har saida ya koshi kafin ya mike ya koma part d'in shi yayi brush yazo ya Mata sallama ya fita.

Basu da nisa da gidansu Zainab din albarkacinsa ummanta zaije itama budurwa ce amma ba irin su Samrah wadanda suka jibge ba bazata fi shekara ashirin da daya zuwa da biyu shi kad'ai yana tafe yana fatan Allah yasa bata gidan yana shiga harabar gidan gurin parking motoci ya fara kalla ganin babu motarta yasa ya sauke ajiyar zuciya yana karasa shiga gidan,, a fuskarta ya fara sauke idonsa tana zaune qanin Afeef yana gabanta tana masa assignment jin sallama yasa ta d'ago ganin wanda batai tsamani ba da mamaki ta fara binsa da kallo harya zauna batace komai ba sai ido take binsa dashi d'an tsaki yaja yana kallon qaninta yace.

"Afeef Ina umma"?.

Amsa Afeef ya bashi yana mi'kewa zaibar gurin yace "taje anguwa".

"Ok d'auko min ruwa a fridge".

To Afeef yace yana juyawa Zainab ta dakatar dashi "Afeef jeka zan d'auko masa" jin abinda tace yasa Afeef yayi wucewarsa, mi'kewa tai tana bud'e fridge d'in ta dauko tare da cup ta kawo masa ta zuba ta bashi sannan ta wuce kitchen ta d'ebo masa snacks da donut ta had'o masa harda drinks ta kawa babu abinda ya kalla a ciki balle yaci iya ruwan farko d'in nan yasha, tana zaune a kujerar dake facing din tasa ta zuba masa ido yana d'agowa yaga kallonsa take wata uwar harara ya sakar mata yana cewa.

"Wato ke har yanzu baki iya gaisuwa ba ko"?.

Farrr tai da ido tana cewa "na iya man amma kaine fa kazo gurina bani naje gurin kaba kaga dole kaine zaka fara gaisar dani".

Cike da jin haushi yace "a haka kike so ki zama matar aure bayan baki san komai ba sai shirme ace har yanzu baki iya magana ba banza kawai".

Murgud'a baki tai cike da tsiwa tace "eh ban iya ba ai saika koya min inace Kaine zaka auresni"?.

Shiru Mohan yai yana kallon yadda take wani jijjiga saican yayi murmushi da shi kad'ai yasan abinda yake nufi kafin ya ta'be baki yana mayar da hankalinsa kan waya kallonsa Zainab tai tana cewa.

"Ka fad'a karta kashe ka dan ina son sanin wannan murmushin naka na meye meyake nufi"?.

Batare daya d'ago ba yace "naso ace yau ke mata tace kika fad'i wannan maganar wallahi yau dasai kin raina kanki saina nuna miki abinda murmushi na yake nufi kuma jikinki ya fad'a miki daga ranar ko kara na aje bazaki qetara baballe nayi magana ki musa ni".

Kau dakai Zainab tai tana d'an ta'be baki tana cewa "Allah ya kaimu lokacin saurin me kake zan zama matar taka ai wai dan kana namiji kake tunanin zanji shakkar ka to ai ni banida tsoro idan ana neman rago na ajin farko idan aka sameka an gama nayi maka farin sani".

Tunda ta fara magana ya zuba mata ido da mamaki yana kallon ta kan bala'i wai shi wannan yar yarinyar take cewa rago, rago fa? Tamke gira yai yana cewe "ni kike fad'awa duk abinda yazo bakin ki? Hum kisa Allah a ranki zan amsa miki sunan a yanxu amma ki tsoraci ranar had'uwa ta dake sai kinyi nadamar kirana rago da kikai".

Kallonsa Zainab tai gabanta na fad'uwa a rude itafa ta manta ma da waye shi Wanda ada idan taji sallamarsa ta ri'ka 6uya kenan a susuce jikinta yad'au rawa dan sai yanzu taga wautarta taya wanda zata aura bayan batasan ya yake ba zata ambace shi da rago Ko waye tasan zai nuna Mata kalarsa ranar daya kamata a hannunsa.

Kallonsa tayi ganin yadda ya d'aure fuska yasa tace "dan Allah ya Mohan kayi hakuri wallahi su6utar baki nayi bazan qara ba".

Ko kula iskarta baiyi ba yaci gaba da abinda yake cikin phone nashi jin tayi shiru yasa ya kalleta idonta ya cika fal da hawaye murmushi yayi yana jinjina kai yace ''oh tun yanzu kika fara kuka? Kar dai ki qarar da hawayenki kafin ranar tazo dan ko kukan jini zaki bazan kyale kiba kina min kallon rago ba ranar zaki kuka da kururuwa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment