Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜”UBANA NE KO KISHIYA NA๐Ÿ’”๐Ÿ’”

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEY BEE)

Gargadi........

Wannan littafin mallaki Na ne kuma bana yi shi don cin zarafin wani ko wata bane hasalima duk wanda ya ga ko ta ga labarin yayi daidai da tsarin rayuwar ta ko makamancin hakan to ina me bada hakuri,

Sannan ban yarda wani ko wata su juya mun labari Na ko su canza ba tare da neman izini Na,

Da sunan Allah me rahma me Jin kai,Allah yanda Na fara rubuta labarin nan lafiya Ubangiji ka sa Na gama shi lafiya,

..............
Page one

**********Bauchin Yakubu

GRA

Karan hayaniyan mutane tare da bugun gate in wani tangamemen gida ne yayi alarming securities in gidan kan bakin da me gidan ke expecting tun safe sun iso,

Sunday ne ya mike tare da kallon mal Iro yace Iro I think they are here already make I do quick and open this gate before oga change am for me,dariya mal Iro yayi tare da bantaran goron sa domin shi Sam ba gane wanga turanci na Sunday yake yi ba,normal turanci ma ya ya kare da shi balle wata broken,

Shi ko Sunday cikin sauri ya tashi tare da nufan black gate in saida ya bude kofar ya leka ganin dandazon yan jarida ne ga sanya shi saurin bude gate in gaisuwa suka yi exchanging bayan sun shigo cikin premises in gidan,

Masha Allah Na fadi sakamakon karewa gidan kallo da nayi,wata gida ne Wanda ya amsa sunan sa gida babban duplex building ne wanda aka kawata wajen gidan da flowers kaloli daban daban,kallo daya za ka yi wa gidan ka san mamallakin sa ba karamin attajiri bane domin duk layin zan iya cewa gidan Sen RILWANU AUDU WAZIRI .... Ya fi Na kowanne kyau,

Sa'eed ne ya fito daga cikin main house in gidan sanye da black and white uniform, shine mafi kusanci da Senator Rilwan,

Cikin fara'a ya karasa gurin yan jarida domin an riga an San da zuwan su,sun zo ne domin tattaunawa da Sen RILWANU AUDU WAZIRI wanda aka tsayar a partyn su domin yin Takaran Gwamnan jahar Bauchi,ganin zabe ya karato ne ya sanya ya hada zaman shi da kanshi domin bayyanar da wasu raayoyin shi tare da amsa wasu yan tambayoyi da suke ta son masa,

Ba karamin lucky da dadi yan jaridan da suka samu zuwa suka yi ba domin sun San ko banza bara su koma hannu Na dukan cinya ba domin Sen RILWANU an san shi da halin kyauta da son jamaa ka'ida ne duk wani Wanda ya zo ganin shi to baya zuwan banza,

Iso Sa'eed yayi musu zuwa ga wani babban Hall dake cikin gidan Wanda an yi shi ne daman domin taro,

Hall ne babba me kyau dauke da kujeru da Dan karamin tables Wanda ke dauke da snacks and drinks a kai,

Bismillah have a seat Sa'eed yace yana murmushi su din ma murmushin suka yi tare da fara kokarin zama,baran sanar da Sen zuwan ku kafin nan ku fara shan ruwa,

Ya wancin gurin ba karamin dadi suka ji ba domin ka je inda za a karbe ka a mutunta ka har a baka abun makulashe ma wani abu ne,nan suka hau Dan ciye ciye da dan shaye shaye kun san mutanan mu ba a ganin bati a bari lol....

Kusan 15 mints da fitan Sa'eed suka fara Jin alamun tafiya tare da magananganun mutane Wanda ya tabbatar musu gwamman goben su ne ke tafe,da sauri suka yi arranging kansu tare da kokarin setting cameras in su domin kowa so yake ya fara daukan sa a hoto,

Kofar aka bude Wanda securities in sa ne kusan su biyar a gaba sanye da irin same kayan da ke jikin Sa'eed sai wasu biyar in a baya sai kuma wasu mutane su uku a tsakiya ko wannan su ya hade cikin dakkakiyar shadda sai kyalli kawai suke zuba wa da kamshi,

Da sauri yan jaridan suka Mike suka fara daukan su a hato,daya daga cikin mutanan ke kirarin Senator Rilwan sai kayi gwamman mu Na gobe insha Allah sai ka mulki jahar Bauchi...

Wanda ake kira da Senator RILWANU AUDU WAZIRI Na bi da kallo,masha Allah na furta sakamakon ganin babban mutum me kamala sanye yake cikin farar shadda Wanda ta ji aiki da brown zare ta ko xauna masa damas a jiki duk da shi din ba ramamme bane ba kuma za a kira shi da kato can ba,

Brown hula takalmi tare da links ne a jikin sa,saidai duk gayun nan da ya ci yayi lacking Abu daya shine murmushi,

A cikin yan jaridun ne daya ya kalli daya yace Salman ya haka yau kamar abunda ke damun Sen domin daga fitowan sa jikin shi a sanyaye and ka dubi fuskan shi ko digon faraa babu bayan kuma shi mutum ne me yawan faraa,

Hmm Tahir manta kawai ni kaina jiki Na yayi sanyi domin tun duban farko da nayi masa na gano damuwa lulube a fuskan sa,ni dai ko ma miye ke damun shi Allah ya sa kar yayi affecting Alkhairin da zai mana,

Daya daga cikin yan jaridan ne ya tashi tare da mika gaisuwa bayan Alhaji Rilwan ya zauna tare da manyan Aminan sa guda biyu,Alhaji Salis da Alhaji Kabiru,

Nan suka shiga masa tambayoyi akan zaben da ke tahowa ya yake ganin abun zai kasance tunda yana da abokan hamaiya dukda ma shi din mutum ne me Alkhairi hannun sa a bude yake ya sanya mutane ke kaunar sa sosai,

Mikewa yayi sai a lokacin Na ga yayi murmushi farko dai da sunan Allah ya fara sannan ya mika godiya sai kuma ya fara jawabin sa kamar haka......

Hakika farin jini da soyayyan da ya samu a gurin mutane daga Allah ne domin in za a tuna sanda ya fito neman senator haka nan mutane suka yi ta kauna shi,ya gode wa Allah da irin daukaka da nasarorin da ya samu a rayuwar sa sannan ya Na mika godia ga dumbin jamaar garin Bauchi bisa yadda da kaunar da suke nuna masa kuma in sha Allah muddum ya zama Gwamma to zai yi mulki bisa tsoron Allah zai kaunaci talakawan sa zai.nan dai yayi ta jero irin cigaban da zai kawo wa garin Bauchi,

Nan ko aka sanya tafi ana fadin sai kayi Gwamma in sha Allah uban marayu kuma gatan Bauchi,

Dan gurban ruwa yayi sannna ya cigaba da jero jawaban sa ,yanda Hall in yayi tsit baka Jin muryan kowa sai nashi,

Kamar daga sama suka ji an banko kofar Hall in kafin securities su kai ga sanin waye har ta shigo,

Sanye take da ash in dogon rigan material kanta ko dankwali babu dogon bakin suman kanta ya kwanto har kafadun ta,kafafunta ko slippers babu,da gudu ta hayo kan stage in,

Kallon Sen Salis yayi yace Alhaji kamar Princess nake gani lafiyan ta kuwa??

Wata kallan gumi ne ya tsattsafo wa Sen a fuskan shi wanda ya sanya bayan hannun sa ya goge ji yayi wani irin balain ciwon ciki da zafi ya durnuke shi lokaci daya duk da uban AC's in da ke cikin Hall in,

Tafi ta shiga yi hannuwa bibiyu tana yi tana fadin wow wow nice one, so tsayawa kuka yi don kuma baku da aikin yi irin sa yana cika ku da maganganun karya da yaudara ku kuma kuna saurara kuna cewa sai yayi sai yayi me.ta kare cikin murya me karfi idanun ta jajjawur hawaye Na zuba,

Wannan mutumin ne wai har kuka tsayar matsayin Dan Takaran ku wai wannan mugu mara mutuncin mutumin Wanda babu ko dikon tsoron Allah a tattare da shi kuke so yayi mulkin jahar Bauchi inalilahi wa ina ilaihi raju'un da kuwa masifa da bala'i ta afku a garin nan,

Cikin sauri Alhaji Kabiru ya tashi yace keeee NADIYA kina da hankali kuwa wani irin shashanci da iskancin banza ke damun ki ko dai kin yi shaye shaye ne in to hauka kike to kiyi maza ki dawo hankalin ki uban ki mahaifi kike jefa da irin wanna kalmomin,

Cikin sauri ta katse shi da ka dakata mun karamin Dan iska ai ba da kai nake ba sarai Na san waye shi, Dan juyi tayi tare da nuna SEN in tace wai ko ba the greatest SEN RILWANU AUDU WAZIRI ba the most richest man in Bauchi ko ba shi ba,Wanda a idanun duniya yake Na Allah amman a badini fa,Allah Ubangiji ya tsine maka Daddy ya Allah Na roke ka,ka hada shi da masifan duniyaa da ba lahira babu masifa kamar kasancewa yar ka da nayi I regret being Ur daughter you are indeed a disgrace to all fathers around the world da yardar Allah bara ka taba samun mulkin jahar Bauchi ba yanda ka tarwatsa mun farinciki Na Allah ya tarwatsa naka I hate you so beyond word,

Da sauri Sen ya runtse idanun sa Wanda hawaye suka taru a ciki,

Alhaji salis ne yayi alama da hannu wa Sa'eed su fita da ita mana domin ganin yan jaridan attentions in su duka Na kanta,da sauri suka nufe ta,don't touch me wawaye jakuna kun saida wa imanin ku da lahiran ku ga wannan mugu Azalumin mutum,ta nuna Sen,

Kama ta suka yi da karfi tana tirjewa tana kuka tana aunawa Sen zagi tare da dibe masa Albarka zagin sa take ta uwa ta uba tana kiran sa da mugayen sunaye Wanda duk Wanda ke gurin sai da jikin su yayi sanyi,


Ku tashi ku bashi guri dumin associating da irin wannan wlhy kan jawo talauci da kassanci ni dai shawara Na baku shine kalman NADIYA Na karshe kafin su Sa'eed suka fidda ta,

Wato yanda ka san anyi ruwa an dauke haka cak jikin kowa ya koma a cikin Hall in baka Jin komai sai sheshekan SEN RILWANU AUDU WAZIRI wanda ya kifa fusakan shi bisa tafukan hannun shi yana kuka,

Ba shi kadai ba jikin gaba daya yan jaridun yayi laasar domin wannan ba karamin abun girgiza da alajabi bane,ace 'Ya daya dilo a gurin Sen RILWANU ne ta fito ko Dan kwali babu tayi masa irin wannan mugun diban Albarkan kan kowa ya kulle,

Da kyar daya daga cikin yan jaridan ya mike tare da cewa yallabai ko za ka iya mana karin bayani game da abun da Hajiya NADIYA ta gama fadi,

Mikewa yayi ya kalli Dan jaridan idanun shi yayi jawur har ya bude baki kawai ya girgiza kai tare da Saurin fice wa daga Hall in domin ya cigaba da zama zai iya fashe wa da kuka bin shi suka yi suna yallabai yallabai ina ko sauraran su be yi ba,ya fice cikin sauri yana baza babban Riga Adduar shi daya Allah sa ba a dauka abunda Nadiya ta fadi ba in ko an yi hakan shike nan tashi ta kare magauta sun yi nasara a Kansa,


Duk yanda suka so su ji wani abu daga bakin Aminan sa kala basu ce musu ba domin har yanzu cikin shock suke,Sa'eed ne yanda ta musu jagora suka shigo haka yayi musu suka fice daga gidan zuciyar kowa da abunda ke sakawa game da abunda ya faru duk yanda aka yi akwai boyayyan alamari a kasa ammann babu me basu wannan amsoshin sai shi kan shi SEN in ........


Toh fa wannna alamari da daure kai yake ace ya ce ke jifan uban ta mahaifi da irin wannan kalomin..

Ku biyo ni a sannun cikin wannan tafiya me cike da sarkakiya ,Na San ko wannan ku zai cika da tambayoyi Wanda Na tanadi amsoshin shi tsaf,๐Ÿ˜

Ga masu son a tallata musu hajojin su za su iya tuntuba ta ta wannan layin:
08100046388.
๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜”UBANA NE KO KISHIYA NA๐Ÿ’”๐Ÿ’”

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEY BEE)

I Dedicated this whole book to you my dearest ummu Mansur (uwar daki na๐Ÿฅนโค๏ธ),I love you so beyond words ........

My What's app group

https://chat.whatsapp.com/JYJvskgTzZICC4ksRfiMlK
..............
Page two

***************

Falmata!! Falmata ihun kiran sunan ta Sen ke yi daga ganin yanayin sa kasan yana cike da tsantsan bacin rai,

Jiki Na bari Na ga wata yar dattijiwa ta fito tana goge sauran ruwan dake hannun ta a jikin zanin da ke jikin ta alamun daga kitchen ta fito,

Gaban Sen ta zo tare da zubewa jikin ta Na rawa domin ko be fada ba ta san yau ta kade,

Kallon ta yayi Na yan seconds sannan ya ja tsaki ya watsar,cikin bacin rai da hargagi kamar ba shi ne mutumin ya gama magana cikin tattausan murya a gaban yan media dazu ba,

Da yatsar sa manuniya ya nuna ta sannan yace Ashe Falmata baki da mutunci ban sani ba,jikin ta Na rawa tace tuba nake uban gida Na wlhh tallahi ban san lokacin da uwar daki Na ta mike ba zato Na duk tana bacci Na shiga kitchen domin samar ma abun da za ka ci in kun gama taro sai kawai shigowar ta Na gani da su Sa'eed,

Dallah rufe wa mutane baki yar iskar mata kawai one task kawai Na baki shine lura da princess tunda Na sanar da ke ina da taro yau Amman kin shiga wai kitchen dafa abinci ai ko kin dafa abincin karshe ke nan domin yau din nan zaki bar gidan nan ya kare kamar zai duke ta,

Nan take ta hau kuka tana rokon shi Allah Annabi kar ya daga ta daga gurin neman Halal inta shekaru kusan nawa tana masa aiki yayi hakuri yayi over looking mistake in nan da tayi wlhy ta dauka NADIYA bacci take har yanzu duba da kwanan ta biyu tana bacci bata farka ba so bata dauka za ta tashi yanzu ba,

Alhaji Salis ne yace ya isa haka Sen is of no use ka tsaya kana venting anger in ka akan wannan worthless matar,let's go and face our problem ya fada calmly,

Tirjewa SEN ya ke yi while Salis Na jan shi domin barin gurin don ya ga alaman ranshi yayi kololuwa gurin baci,

Da kyar dai ya samu suka bar gurin bayan Salis ya ce da Falmata dake ta faman rokon SEN ta tashi ta koma kitchen ta cigaba da aikin ta,

Har sun kai ga shiga part in shi ya hango Sa'eed,kamar Wanda aka tsikara yace Salis kira mun wancan useless boy in, daga gurin Alhaji salis yayi wa Sa'eed magana kan ya zo SEN Na son ganin shi,

Da sauri kuwa ya karaso yanda suke tsaya cike da girmamawa ya dan rusuna yace Allah ya ja da ran ka gwamman mu Na gobe,

Gwamnan uwar ka SEN yace cikin tsantsan bacin rai bayan ya wanke Sa'eed da wata zazzafan Mari,da sauri ya dafe kuncin shi don ba karya Marin ta shige shi,

Don uban ka Sa'eed me kuke yi har NADIYA ta samu damar shigowa cikin press confirence ina,nace uban me kuke yi ,

Kan shi Na kasa yace yallabai wlhh ba laifi Na bane laifin Muktar ne tunda su na bari a waje ni kan ba ina tare da kai a ciki ba,

Cikin bacin rai SEN yace Salis ka duba ka ji wannan wawan yaro yake fada mun waye chief security ina ba kai bane ya ci ace duk kai za ka kula da komai wlhy in har wani abu ya samu kujera ta wlhy tallahi gaba dayan ku baran raga muku ba shashashu kawai Wanda basu San yanda ke musu ciwo ba,

Jan hannun shi Salis yayi yace don Allah RILWANU stop all this is not that necessary ta ho mu shiga ka samu ka sha ko ruwan sanyi ne,

Bayi da option sai bin bayan Alhaji salis in Wanda ke matsayin Aminin shi kuma mataimakin shi domin shi ya tsayar as deputy governor in shi,ko ba don komai ba ya ci ya jiga makoshin Na shi don ba karamin bushewa yayi ba,

A tangameman parlor in shi da ya gaji da tsaruwa suka ya da zango,fridge ya bude tare da dauko bottle water me sanyi ya zuba masa a glass cup tare da mika masa have a sip yace da shi calmly,

Ba musu Sen ya karbi cup in ruwan tare da nufan bakin shi sa cup in Sai kuma ya tsaya kallon Salis yayi yace Salis wat will happen in har shegun yan jaridun nan sun yi recording scene in da princess ta gama yi,

Numfashi Salis ya ja tare da zama kusa da shi yace kai I don't think za suyi shooting because gaba dayan mu are shocked am sure harda su ina za su samu daman dauka, Allah sa ba Wanda ya dauka domin in har an dauka yadawa za suyi a duniya and muddum aka yada shike nan makauta sun samu nasara akan mu,

Da yardar Allah bare ma faru that way ba just be faithful my friend,dan shiru suka yi duka kafin yace yanzu ina ita princess in,

Cup in hand in shi ya aje tare da furzar da iska yace an mata alauran bacci,

Gyara zama salis yayi sannan yace wai ni kam me ke damun NADIYA ne lfyan ta kuwa ni dai sani Na da ita bata da wata cuta da ya shafi brain inta balle nace shine ya tashi mata,

Ajiyar zuciya SEN ya sauke sannan yace wlhy Salis karan shigowar waya ce ta katse mishi abun da yayi niyan fada,tare da zaro wayar tasa daga aljihu,

Ganin Wanda ke kiran sa saida gaban shi ya fadi ba kowa bane illa shugaban party in su,Na shiga uku shine kalman da ya fadi be ma San ya fada ba,dafa shoulders in shi Salis yayi yace ka dauka komai zai tafi daidai,

Dauka yayi jiki ba kwari,gaishe shi yayi inda yayi sauran tsayar da shi ta hanyar cewa SEN RILWANU shin ka shiga social media kuwa yau,idanu ya runtse yana fatan ba dai video in abunda NADIYA tayi masa ke trending ba,

Cikin sarkewaan murya yace aa ranka ya Dade ban shiga ba wa niiii abuunnn ne ya faruuuu ya fada da kyar,

Lalle RILWANU au baka ma San me ke faruwa ba ko to gaba daya kafofin sadarwa Na duniya kama daga kan Twitter Facebook YouTube Instagram video in ka ne kawai yake trending wani irin shirme ne haka ace a dauki yarinya ka tana maka zagin tsamen nama a gaban media Inalilahi,Anya ba muyi zaben tumin dare ba kuwa za ka jawo bacin sunan party in mu daman can kai ba mutumin kirki bane wai,

Cikin tashin hankali yace yallabai kar ka ce haka wlhy tallahi nima yanda kake cike da mamaki haka nake Sam ba haka princess take ba duk Wanda ya sanni yasan akwai kyakkyawan soyayya da kauna tare da shakuwa tsani na da tilon yarinya ta,wannan definitely sa hannun magauta ne an ga nasara da daukaka Na tattare da ni,but don Allah sir kayi hakuri a kuma bai wa yan party hakuri in sha Allah I got this I can control it duk me nema Na da sharri Na fi karfin shi,

Hmm shike nan gaskia try your best ka wanke kanka domin wlhy banda maganar ka babu abunda ake yi a media kowa da irin abunda yake fadi son ranshi ka ga kuma kujeran gwamma ba karamin kujera bane,

Hakuri ya bashi tare da bashi assurance zai kawo karshen matsalan gobe in sha Allah,suka yi sallama tare da kashe wayan,

Wata irin wawan jifa yayi da wayar ta bugi bango nan take kuwa ta tarwatse,cikin ihu yace damn it meyasa haka zai faru da ni why za a yi using NADIYA ta domin bata mun siyasa ta why my baby ,rike shi Salisu yayi yace calm down in sha Allah za muyi coming over this,

Shiru yayi yana ta Dan nazari kusan Na mintuna sannan ya mike yace Salisu thank u so much you can take za ka iya tafiya,kace da Kabiru ina son ganin shi in ka fita,okay Ranka ya Dade a huta lfy Allah ya kyauta Na gama yace tare da barin parlor in cike da mamakin me ke damun Nadiyar har haka,

A hanyar fita daga gidan ya hadu da Kabirun sanar da shi yayi ya je part in Senator yana son ganin shi,da toh ya amsa suka yi saying good bye in su don shi Salisu gida zai koma,

Shi ko Kabiru kai tsaye part in Senator ya nufa inda ya tarar da shi ya kasa zaune ya kasa tsaye,

Dafa shi yayi yace SEN take it easy sanin kan ka ne dai over thinking baya solving problems, cikin murya me rauni yace Kabiru ya kake son nayi dazun nan shugaba party ya kira ni har yana ce mun sun yi Dana sanin tsaida ni zaa iya kwace ma kujera na a tsaida wani,

Calm down ba wanda ya isa ya kwace ma kujera yan gari ai suna bayan ka,wani irin baya Kabiru bayan an samu Dan iskan da ya yada video in nan yanzu haka shike trending a duniya,

Whattttttt Kabiru yace yana zaro idanu shegu tsiyan yan jarida ke nan munafurci Amman ba komai we got this in control zauna ka ji yanda za aka yi,

Nan ko SEN ya zauna shima Kabirun zama yayi suka shiga tattaunawa game da yanda za a yi,sai ga SEN har yana dariya suna tafawa da Kabirun ganin sun kawo karshen matsalan nan,Kabiru be bar gidan SEN ba sai dab Magriba akan gobe yana so ya kara gayyato masa yan jaridun zai Kara tattaunawa da su a haka suka rabu

Please Login or Register in order to submit comment