Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da gudu sabida gudun abunda SEN zai masa,saidai is to late yayi hakan,

Shi ko SEN karasa shigowa dakin yayi yana me hango Nadeeya a kwance lah bacci take yi ne ya tambaya yana nufan yanda take,

Da sauri Bashir yace eh ta samu bacci ashe mu je kar a tashe ta in ya so sai ku dawo ko jibi ne ku ganta tunda dai ai kun ga tana cikin koshin lfy,normally ba mu cika barin ana yawan ganin majin yatan mu ba,

Wani irin harara sen ya jefa masa sannan yace a yaushe kuka fara wannan tsarin iskancin, da rawan baki yace jiya cikin dare,ko kula shi be yi ba ya durgusa a gaban Nadeeya din da ya gani idon ta bude kamar ma hawaye take yi,

Kabiru ka ga Ashe ma idon ta biyu tana Jin mu,kanta ya shafa sannan yace hello princess, he was expecting ya ga ta janye hannun nashi kamar yanda ta saba ko ya ji tana jifan shi da mugayen maganganu saidai tsit ya ji ta,

Da matukar mamaki ya mike tare da kallon Bashir sannan yace why is she not talking, me ke damun ta kuma, Na ga yau ko ihun da ta saba da fashe fashe bata yi lafiya kuwa,

Nan take Bashir ya hau inda inda fadi yake hmmm ammmm ahhhhh daman,tassss SEN ya wanke shi da Mari sannan yace daman in uwar ka ka fada mun uban me kayi wa yarinya ta bata mun magana,

Cike da radadi tare da rudewa yace yallabai Na rantse da girman Allah dazun nan Na shigo Na gan ta haka bata magana ko motsi ma bata yi,ya kare yana kare fuskan shi da hannu biyu biyu,

Ai Jin haka ya sanya wata irin jiri kwasan senator sai ga shi yuuuuuu yayi baya zai zube a kasa,da sauri suka taro shi Kabiru yana fadin take it easy Aboki na in sha Allah babu abunda zai samu Nadeeyar mu.....

Manage this please aiki ya mun yawa wlhy,

Bi sa complain in da Na samu Na in Kara 2 more pages kafin Ramadan ya sanya ni yin typing yau, saura yanzu 3 more pages in sha Allah,

Bani kuma da bakin gode muku, masoya Na Wanda Na sani da Wanda ban san su ba,saidai nace Allah ya saka da Alkhairi da kaunar da kuke nuna mun,nima ina kaunar ku fisabillah,

Ina wa kowa fatan Alkhairi,

Sai kina gobe in Allah ya kaimu.
[6/21, 8:37 PM] My Best Best โค๏ธ: ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜”UBANA NE KO KISHIYA TA๐Ÿ’”๐Ÿ’”

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEYBEE)

.......

My group link

https://chat.whatsapp.com/JYJvskgTzZICC4ksRfiMlK

In har kin san ba karanta book ina and comment zai shigo da ke ba,to pls kar ma ki shigo, haka zalika maza should stay far away from my group pls๐Ÿ™๐Ÿป,

Ga masu bukatar a tallata musu hajojin su contact me via:

08100046388

............
Page eighteen

************

Ruwa Alh Kabiru ya shafa wa SEN a fuskan shi Wanda ya dawo da shi daga duniyar sumar da ya fada,wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya bude idanu a hankali,

Doc bashir ya gani tsaye a kan shi wanda kallo daya za ka masa ka fahimci yana cikin tsaka me wuya,

Ai da sauri ya mike tare da cukumo wuyar rigar Bashir sannan cikin ihu ya hau masa fada,Dan uban ka me kai wa yarinya ta eheyeee bara ka yi magana ba,ya dauke shi da Mari me zafi,

Kumatu Bashir ya dafe sannan ya shiga rantse rantse kan cewa wlhy shi ba abunda yayi wa Nadeeya,

Wani Marin SEN ya dauke shi da shi a Karo Na uku sannan yace har ni zan yarda da ba abunda kayi mata,nawa suka baka ka maida mun ya haka,toh wai miye ma ka mata ne,wato duk kudin da nake baka be ishe ka ba saida makiya suka Kara maka ka maida mun yarinya haka,haukatar da ita kawai nace kayi wawa ba wai ka nakasa mun rayuwar yarinya ba ya kare ya me tada jijiyoyin wuya,

Doc bashir baki ya mutu banda girgiza kai babu abun da yake yi,idanun shi har ya ciko da kwalla ya rasa da wani kalma zai wanke kan shi a gurin SEN,

Shigowan sister Kareematu ne ya sanya shi saurin nufan ta,fadi yake yauwa Kareematu Na gode wa Allah da ya kawo ki don Allah sanar da su babu abunda nayi wa Nadeeya,

Da kallon wulakanci ta bishi sannan tace ai daman Bashir saida Na fada maka aluran da kake bata sun fara yi mata yawa,Amman kaki ji karshe ka hada harda shock treatment kake mata,taya daman yarinya bara ta zama haka ba,

Ai bata hada bakin ta ba ta ji saukan mari me dankaran zafi Wanda saida ya sanya ta zaro idanu, sabida radadi,

Na shiga uku miye nayi da za ka mare ni haka ranka ya Dade,

Uwar ki kika yi matsiya ciya wato da hadin bakin ki aka kusa kashe mun yarinya, Na rantse da Allah SEN ni babu ruwa Na gashi nan shima saida Na Hana shi yace da ni babu ruwa Na ta kare tana nuna Doc bashir da ya zazzaro ido sabida tsoro,

Cukumo shi SEN tayi tare da Kara wanke shi da Mari Wanda saida ya sanya Kara,yanzu Bashir Ashe kai Dan iska ne ban sani ba miye nayi maka da har za ka sanya wa yarinya ta shock treatment,

Na rantse da girman Allah ba zan bar ku ba,daga kai har wannan shegiyar ya kare yana nuna Kareematu a gidan yari za ku karasa wahalalliyar rayuwan ku,shegu yan iska marasa mutunci, Kabiru kira mun police su zo suyi gaba da mugayen mutanan nan kafin bakin ciki ya sanya Na kashe su da hannaye Na,

Nan take cikin Kareematu ya duuri ruwa ita fa ta zo ne domin ta sanya Bashir a damuwa da matsala sai gashi ta samu rabon Mari harda za a kama su to akan me,

Kamar hadin baki sai ga su sun zube a gaban SEN suna hada shi da girman Allah kan yayi hakuri kar a hada su da hukuma,wlhy tallahi babu hannun su a wannan abunda ya farun,

Ba karamin kai ruwa Rana aka yi ba kafin aka samu SEN ya ce ya hakura bare kai gurin yan sanda ba Amman fa ya zama dole a dawo mishi da magana da kuma tafiyar yarinyar shi,domin bare yu ya basu yarinya da muryan ta da kafafun ta sannan yanzu a dawo da ita vegetable ba Sam bashi yuwa,

Haka dai suka yi ta bashi baki harda Alh Kabiru a masu bada bakin,sannan ya dan sauko daga masifar da yake yi,

Haba Alh Kabiru Na basu yarinya da lafiyar ta sannan yanzu ace ta dawo haka wlhy dole suna da masaniya,don haka Na basu Dan kankanin lokaci ko su dawo mun da yarinya ta daidai ko kuma Na kashe su da hannu Na,wuce mu tafi domin Na cigaba da tsayuwa ina iya aikata abunda be dace ba ya kare yana gallawa bashir da Kareematu mugun kallo sannan Alh Kabiru ya biyo bayan shi zuciyar shi cike da mamakin karfin hali irin Na SEN,

Suna shiga mota kuwa SEN ya kwashe da wata irin dariyar samun Nasara sannan ya zubo kirari da yar banci wa odugwu sannan ya kalli Alh Kabiru da ya zuba mishi idanu,yace ya aka yi ne mutumina,

Hmm Wlhy tallahi RILWANU tsoro ka koma bani,ban taba ganin makirin mutum ne fuska hudu ba irin ka,wlhy ko mace nan ta gan ka ta bar ka gurin tuggu,kwalba uwar sharri,ina tsoron ka wlhy,

Dariya SEN yayi sannna yace haba dai Kabiru kai da ka kwanta da Maman matar ka ka baiwa odugwu Jinin ta ban ji tsoron ka ba sai don ni da nayi wannan dan karamin drama in,

Tsaki Kabiru yayi sannan yace kai magana bata wuce maka maganar kwanciya da suruka ta nake maka ko ta draman da kai wa Bashir, sanin kan ka ne fa kai ne silan ciwon yarinyar nan Amman ka bude idanu ka nuna Sam baka da masaniya,kamar ma sune suka aikata,duk ka sanya su a guilty conscience,wlhy Sam baka da imani SEN,

Har in ana maganar imani za ka sanya baki,ko ka mance yar ka yar 3 years da kai raping ka kashe da hannun ka,sai dan dan wannan abunda nayi kake ce mun banda imani,

Don't forget duk abun nan muna yi ne don securing future in mu,and wlhy da asiri Na ya tono Na gwammaci ko ma miye ne nayi,but I have to protect my dignity shine kawai abunda Na sani,and so kake Na nuna nasan komai a gaban doc in look ina cikin mood in farinciki don Allah kar ka bata mun rai,beside Kabiru in mugunta ne har Na isa in kai ka abunda kayi ai ko zan mutu Na dawo ban isa nayi kwatankwacin su ba,

Aboki Na ke nan yau kuma tone tonan asiri ne ya tashi ke nan,Dan dariya yayi sannan yace komai kayi ba komai bane in har za ka samu kudi,go chase the bag,kar ka matsa wa kan ka legal or illegal ne in har za ka yi kudin shike nan,

Ah toh nima abunda Na gani ke nan,kai ne kake son fito mun da wata tsirfa tun farko da bata san komai ba ai da yanzu muna zaman mu lafiya ko,sannan kasan am damn lucky Nadeeya ta San asiri Na Amman odugwu ya mun Alfarma Na bar ta a raye har yanzu,ka ga ko dole nayi ko me zan yi Na ganin bakin ta yayi tsit gudun tonuwar asiri,

Haka ne kam wlhy SEN baka da dama ko kadan,am very sure Bashir be isa bacci ba yau,dariya SEN yayi sannan yace siyasa ke nan mutumi na dole ka koyi dabaru nan ne zaka mori zaman duniyar,mu karasa gida domin a gajiye nake wlhy,Kabiru be sake cewa komai ba har suka iso gidan SEN, inda suka hadu da Alhaji Salis nan aka zauna SEN ke labarta mishi abunda ya faru yana kuka,ba karamin tausayi ya bai wa Alh Salis ba,nan ya shiga zubo tsinuwa da addu'ar samun lfy wa Nadeeyar,


***********Doc Bashir

Kadan ya rage be rufe Kareematu da duka ba domin ba karamin haushin ta ya jj ba,banda rawan kai uban me ya kawo ta office in shi har da sanar wa SEN wai yana bata shocking,

Kallon ta yayi cike da bakin ciki sannan yace kin kyauta Kareematu Amman ki sani wlhy sai Na rama abunda kika mun tunda ke bakin ki sam be iya yin shiru, banza karuwa kawai,

Dariya ta sheke da shi sannan tace karuwai dai yanda nake karuwa haka kake karuwan Na miji,acewar ka banza ka mara ko,toh wlhy ka kiyaye ni, sannan da kake cewa sai ka Rama sharri nayi maka,Na gani duk abunda ke faruwa shine na fada,ni ban ce sai na rama ba akan ka an mare ni sai kai ne me hannun daukan fansa to bismillah,sakarai kawai wlhy in ka kuma kula ni ma sai nayi maka rashin mutunci, da haka ta sanya kai za ta fita,ko me ya tuna sai kuma ya bi bayan ta yana haba my Kareematy ai ba a Jin kan mu tsaya mu sasanta ko kallon yanda yake bata yi ba tayi gaba abun ta,


**************Doc Nameer

Gama wayan shi ke nan da mama yana sheda mata yayi missing in su yana son shigowa Kd this weekend in sha Allah, agogon hannun shi ya kalla ya ga goma har ya wuce,so yake ya shirya ya tafi gurin Nadeeya Amman sam yau baya Jin karfi a jikin shi,haka kawai kuma wani gefe Na zuciyar shi ke azaxxalar sa akan ya je ya duba ta din kamar tana cikin wani matsala haka yake ji a cikin ranshi ,saidai he is very tired yau be jin xai iya zuwa duba ta, alulan bacci ya dauro sannan ya kwanta bayan yayi adduan bacci tare da yaki ce tunanin Nadeeya a cikin zuciyar shi,

Saidai sam baccin ta kasa daukan shi ya kuma kasa daina tunanin Nadeeya,

Tsaki ya ja tare da mikewa jallabiya ya zura sannan ya dauko car key in shi tare da fitowa,

Saida ya biya Saje ya siyo mata ice cream da Shawarma sannan ya dauko hanyan asibitin,kamar kullum dan cin hanci da ya saba bai wa securities in ta bada tare da shigewa a bun shi,

Dakin nata ya nufa kai tsaye,yana adduar Allah sa bata yi bacci ba don kila ta gaji da jiran shi tayi bacci abunta,be taba sanin ya shaku da yarinyar ba sai yau da yace bare zo ganin ta ba har wai ya kasa bacci saida ya fito,

Da sallama ya shiga cikin dakin yana me Jin mamakin ganin komai tsaf kamar naughty girl in shi bata wuni a dakin ba yau,shirun da ya ji ya sanya shi tunanin kila baccin tayi,

Sleeping beauty har an yi bacci ke nan yace tare da nufo kan gadon nata,kwalbar da kafar shi ba buge ne ya sanya shi tsayawa tsak,tare da tsungunawa don ganin kwalbar miye haka, is not suitable ana barin kwalabe a dakin me jinya jinyan ma Na hauka,in ta ji wa kanta ciwo ba,idanu ya zaro tare da kare wa kwalban kallo,daidai lokacin aka bude dakin tare da shigowa,

Idanu Doc bashir ya tsaro cike da mamaki sannan yace kwal uba uban me kake nema ana dakin cikin daran Nan......


Remaining 2 pages in sha Allah sai kuma in Allah ya sa mun kai bayan sallah,

Ina yi wa kowa fatan Alkhairi,


Sai kuma gobe in sha Allah
[6/21, 8:37 PM] My Best Best โค๏ธ: ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜”UBANA NE KO KISHIYA TA๐Ÿ’”๐Ÿ’”

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEYBEE)

.........
MY group link

https://chat.whatsapp.com/JYJvskgTzZICC4ksRfiMlK

In har kin san ba karanta book ina da comment bane zai kawo ki to don Allah kar ki shigo, haka zalika maza should stay far away from this house domin gidan mata ne zallah๐Ÿ™๐Ÿป,

Ga masu son a tallata musu hajojin su should contact me via:

08100046388

ALHAMDULILLAH,A NAN ZA MU DAKATA DA LITTAFIN NAN HAR SAI ME KOWA ME KOMAI YA KAIMU BAYAN SALLAH,INA MIKA GODIA TA GA DUMBIN MASOYA NA WANDA NA SAN SU DA WANDA BAN SAN SU BA,INA GODIA DA IRIN KAUNAR DA KUKE NUNA WA LITTAFINA,UBANGIJI YA SAKA WA KOWA DA ALKHAIRI SANNAN YA SANYA MU FARA RAMADAN A SA'A,ALLAH YA SANYA WANNAN RAMADAN IN YA ZAMO SILAN SHIRYUWAN MU BAKI DAYA,UBANGIJI YA SA MU DACE SANNAN YA SANYA MUNA DAGA CIKIN BAYIN KWARAI DA ZA A YANTA DAGA WUTA ZUWA ALJANNAH,

SAI MU KASANCE MASU AIKATA ALKHAIRI DUK KANKANTAN SHI DOMIN DUK ABUNDA KAYI LADA NE A WANNAN WATAN,CIYAR DA MARA SA KARFI BABBAN LADA NE,ALLAH UBANGIJI YA BAMU IKON AIKATA AIKIN ALKHAIRI SANNAN YA RABA MU DA SABA MISHI A WANNAN KWANA 30 DIN,

DUK WANDA NAYI WA LAIFI YA YAFE NI SANNAN NA YAFI KOWA,DOMIN YANA DA KYAU KA FARA AZUMI BABU KOWA DA KA RIKE A CIKIN RANKA,UBANGIJI YA MANA ALBARKA BAKI DAYA SANNAN YA AMSHI IBADODIN MU YA KUMA YAFE MANA KURA KURAN MU๐Ÿ™๐Ÿป,

............
Page twenty

***********

Da ido Nameer ya bi doc Bashir da kallo,daman yayi expecting ganin shi a daidai wannan lokacin, domin yana iya hango tsantsan tsoro da ya darsa masa a cikin zuciyar shi,

Cike da muryan shakiyanci yace ah Doc bashir kai da kan ka ai da aikawa ma kayi Na zo sai na zo ai,

Lebe Bashir ya dan ciza sannan ya yayi kwafa a cikin ranshi kafin ya sanya fuskan tausayi yace a a Nameer gwara dai Na zo da kai na din, ya kare yana isowa kusa da shi,

Kallon shi kawai Nameer ke yi yanda duk ya bi ya rude kamar ki ce da shi kitt ya ruga da gudu,

Haba Nameer a rayuwar nan me na tsare maka da ka tsane ni har haka kake son ganin baya Na,

Da mamaki Nameer ke kallon Bashir in kafin yace Allah raba ni da ganin bayan wani bawa naka,doc Bashir hakikanin gaskia ban tsane ka ba hasalima miye hadi Na da kai da zan tsane ka babu abunda kayi mun,banda yau da Na kama ka da rashin gaskia,and sannan kai kanka kasan abunda kake ai be kyautu ba ko tsoro baka ji wannan alurai da kake bawa yarinyar nan ya jefa ta cikin wani hali haba kar mu zama marasa imani mana akan abun duniya da a nan gidan duniyar za mu bar shi,

Bashir ji yake kamar ya rufe Nameer da duka domin sam shi wannan waazin da yake masa ba shiga kunnan shi suke ba,amman wai me neman sulhu sai yace,

Eh Doc Nameer duk Na ji me kace kuma Na karbi laifi na,nayi kuskure yanzu dai nawa zan baka don ka samu ka sanya wa bakin ka zip,domin maganar nan in har ta fita to wlhy akwai matsala,

Wani dariya Nameer ya kwashe da shi sannan yace daman nayi expecting haka,wato dai mara kunya ko a ina yake baya boyuwa,wai ce maka aka yi kowa ne me son zuciya irin ka,kana tunanin akwai kudin da zai siyi lafiyar yarinyar nan,to bari ka ji in baka sani ba Alhamdulillah I lack nothing a rayuwa ta ina da kawaa da zuci abunda ka rasa ni abun wani be taba tsole mun ido ba kan gaskia ta nake kuma aiki Na nake yi, don haka za ka iya barin mun office ka koma naka ka jira zuwan yan sanda,

Cikin Bashir ne ya kulle yayi danasani cewa zai bashi cin hanci ai ha ci ya gane ba kowa ke da son zuciya ba gashi garin ya gyara ya bata komai,

Amman dake tsohon Dan duniya ne sai cewa yayi,wai Nameer so kake kace da ni baka da son abun duniya,kar ka manta kudi sune maganin zaman duniya,beside miye halakan ka da yarinyar nan ne da ka dage sai ka ga tonuwar asiri Na,

Kai Nameer ya girgiza sannan yayi yar murmushi tabbas ina da babban halaka da ita domin yar uwa ta ce a musulince and humanity came first akan komai,da kake maganar son kudi babu Wanda zai ce baya so,saidai da Na ci kudin da zai hana ni kwanciyar kabari gwara Na mutu da talauci wlhy,

Ni ga alaman sam baka gane wa don Allah ka fitar mun daga office yanzu ba kuma sai anjima ba zan kira mahaifin yarinyar nan Na sanar da shi komai,bare yu ya baka amanar yar sa ba sannan ka zo kana cin amana,

Ganin fa yaron nan ya dage da gaske yake yi in har ya bar shi zai iya tona masa asiri ya sanya shi zuwa tare da zubewa a gaban Nameer in ya kama kafafunshi duk biyu,

Na roke ka da girman Allah ka rufa mun asiri kai ba mugu bane haramun ne saka sharri da sharri,kayi hakuri ka taimake ni kar ka sanar wa kowa koami,wlhy nayi kuskusre na kuma amsa laifi na,

Da mamaki Nameer ke bin shi da kallo yana kokarin jan kafar shi,doc Nameer in ka fada wa yan sanda wlhy a yari zan kare rayuwa ta shike nan tawa ta kare,ina da mata ina da yara da suka dogara da ni in har bana nan rayuwar su za ta daidaice,

Daidaice doc Bashir rayuwar Nadeeya da ka daidaitar fa,wannan hakki har ina za ka kai shi yarinya da hankalin ta ka dage sai ka hauka ta ita kuma fa me za ka ce akan wannan,

Cikin kuka Bashir yace wlhh nayi nadama Nameer Na yi danasani Na biye wa son zuciya Na aikata cuta wa baiwar Allahn da bata san komai ba,Amman tona mun asiri won't solve anything, kar ka manta ance duk Wanda ya rufa asirin wani Allah zai rufa nashi,

Bashir in har na rufa ma asiri rayuwar Nadeeya fa in bar ka ka cigaba da cutar da ita,kana tunanin Allah zai bar Ni ne ina ganin ana aikata zalunci akan ido na and Na gaza yin komai akai,me zan ce masa,

Wlhy in har ka rufa mun asiri nayi maka Alkawari zan zamo mutumin kirki ba zan Kara cutar kowa ba,I will be a change man,and Nadeeya what about her,

Nameer I promise you daga yau bazan kara mata injection ba,ka ga ni da kai sai mu hada force gurin neman maganin da xai yi curing in ta,ya kare yana cigaba da bashi hakuri,

Shiru Nameer yayi yana tunanin Anya ya yarda da shi kuwa,but why not kowa yana laifi and mutum in da aka fi so shine wanda zai gane laifin shi har ya zo neman afuwa, Allah da kanshi muna masa laifi ya yafe to shi waye da ba zai ba wa doc bashir second chance ba,

Cikin sanyin murya yace stop crying and begging me like a little boy,tashi I won't tell anyone anything,

Da sauri doc bashir ya dago yace are u serious, yeah I am miye riba Na in Na tona Na asiri,beside ni ba wa ni kai wa laifi ba,ita ya kamata ka nemi gafaran ta tunda har ka gane laifin ka and ka shirya canjawa Allah yafe mu baki daya,

But I want u to know one thing in har yaudara ta kake yi wlh bara tayi mana kyau ba daga ni har kai,

Da sauri Bashir yace you won't regret this I promise u,Na gode sosai doc Nameer Allah ya yi maka albarka, and am so sorry da irin abubuwan da nayi maka a baya,

Murmushi Nameer yayi sannan yace haba babu komai ai ya wuce,yanzu dai mu fuskanci yanda za mu warkar da baiwar Allahn nan,

To ba damuwa za muyi magana ai bari Na koma office ina Na gode fa, ya kare kamar zai kwanta wa Nameer a kasa,shi dai da ido yake bin shi yana mamakin yanda zuciyar mutun zai bushe sabida son abun duniya ya iya cutar da Dan uwan shi,no wonder mana ya Hana kowa zuwa kusa da ita,shege Ashe be kulla gaskia ba,dariya ya dan yi sannan yace Allah ka shirya mana zuriaar mu,

Doc Bashir kuwa cike da bacin rai da tsantsan tsanar Nameer ya dawo office in shi,Alhamdulillah ya samu yayi wa yaron wayo,Amman ba shakka sai ya muzanta Nameer a cikin asibitin nan yanda ya tozar ta shi sai ya Rama wlhyy, shegen yaro karami da shi sai kwarjinin bala'i,yanzu ya zama dole ya canza takun shi, domin yi wa Nadeeya alurai yanzu ma ya fara, (ni ko nace ba shakka ba ka samu be hada ka da hukuma ba,ai kace komai ma),


**************

Haka nan rayuwa ta cigaba da tafiya ba karamin taka tsan doc Bashir ke yi around Nameer ba,domin nuna mishi yayi eh fa da gasken gasken ya shiryu sannan ya canja,domin tun Randa abun ya faru ya bude wa doc Nameer kofa kan ze iya zuwa ganin Nadeeya duk sanda yake so,and ya nuna mishi ya daina bata injections in nan,he is even researching irin treatment in da zai yi curing in ta gaba daya,

Randa doc Nameer ya ga condition in Nadeeya sai da ta kusa mata kuka,shi sam ya ras why yake daukan damuwar yarinyar nan too personal ne,he wish da yana daa hali da ya warkar da ita, abun ya mata yawa ga hauka,ga rashin magana da rashin motsa jiki tana nan kwance kamar kayan wanki,sam shi be taba ganin irin case in Nadeeya ba,domin banda ido babu abunda take iya motsawa a jikin ta,

Nadeeya Na cikin halin da dole mutum ya tausaya mata,bata hmmm bare uhmm uhmm,saidai tayi ta bin mutum da idanu, at least in haukan ne kawai ai da sauki kana tafiya kana maganar ka,amman a halin da take ciki sai an daga sai an kwantar, banda hawaye ba abunda ke fita a idanun ta kullum kallo daya za ka mata ka gane she is in deep pain,

SEN gurin ta yake wuni in be da abun yi yayi ta kuka yana mata addu'ar samun sauki ke nan,in abun nashi kuma ya motsa ya gasa doc Bashir da zagi kan shi ya jefa yar shi cikin halin da take ciki,saida Alhaji Salis ya dage masa da nasihar karban kaddara kafin aka samu salama,


************ Doc bashir

Around Magrib yana kokarin hada kan komatsan shi ya je hotel in da suka yi da Kareematu za su hadu ya ji an shigo cikin office in nashi kai tsaye ba tare da neman izini ba,(Allah ka tsare mu da aikata zina domin shi zina kama rai Gare shi daga zaran ka fara to wlhy bari wahala yake maka,duk tsiyan da Kareematu tai wa Bashir ba shi ya Hana shi bin ga ya saukar da kai ba domin he is already addicted to her),

Dagowa

Please Login or Register in order to submit comment