Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan,

Tunda ya iso yake bin tsarin garin da kallo,shi ba kowa ya sani ba balle ya ce zai nufi gidan wani ya sauka,gashi yamma ta fara yi domin be yi iso wan wuri ba sabida tsaye tsayen da ya ringa yi a hanya,

Ganin be da option in da ya wuce ya nemi hotel ya kama,domin ya samu gurin kwana,Dan tsaki yayi tare da cewa tsiyan ka zo guri baka san kowa ba ke nan wlhy duk sai ka bi ka zama wani bako,

A ZARANDA HOTEL,ya yada zango inda ya shiga tare da biyan kudin dakin kwana uku, dole ya dan tsaya Na kwanakin kafin ya samar wa kansa,mahallin da zai zauna,domin Sam be kaunar zaman hotel,

A reception ya tsaya tare da biyan kudin daki Na kwana uku,aka ba shi key in dakin sannan masu aikin hotel suka dauko jakar kayan shi tare da nufar dakin Na shi da shi,

Godia yayi musu bayan sun aje sannan suka wuce,dakin ya bi da kallo,wow daki ne me kyau kamar mutum yana gida, domin komai akwai a ciki,gado kujera harda fridge,

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya fada kan gadon,oh my god am damn tired wlhy,ya kare yana shafe goshi,so yake ya dan huta kafin ya samu yayi wanka ya sanya wani abu a cikin nashi ko zai samu gajiyar jikin shi ya bar shi,

Ringing in da wayar sa ke yi ne ya sanya ya bude idanun shi a hankali tare da janyo wayan domin ya San ba kowa bane ila Mama,

Saidai ganin bakuwar no ne ya sanya shi mamaki,har ya yanke be dauka ba,sai da aka kuma kira sannan ya dauka,

Hello brother ya ji muryan ta ya doki kunnan sa,a hankali yace shit ba dai yarinyar nan ba,

Haba Brother yanzu kana ji Na ka share ni,ta kare cike da shagwaba,gashin kan shi ya shafa sannan ya ce Amrah yaushe kika shigo Nigeria and ina Maman ki,

Hmmm ai Yaya Nayi fushi kana tafiya Ashe jirgin mu yana landing I wanted giving you a surprise ya sanya ban sanar da ku zan zo ba,saidai am not lucky Ashe ka tafi Bauchi ta kare a shagwabe,

Hmm Amrah Na tafi ban ma Dade da isowa ba ya amsa ta da kyar, ayya sorry brother Na Na san ba Wanda ka sani a Bauchi you will be so very lonely ko dai in zo ne,

Idanu ya zaro a kasan makoshi yace what,a fili kuma sai cewa yayi kee Amrah are you okay kuwa,an ce miki ko ina ne irin Manchester ehyeee taya za ki biyo ni Bauchi,

Hey common sweetheart nima dai wasa nake maka,ko kace Na zo am not coming ta kare tana dariya,

Tsaki yayi a hankali domin shi fa haukan wannan yarinyar ke hada ta da shi sam bata da kan gado,


Ina Mama shine abun da ya tambaye ta Jin tana son kamo wata shirmen nata daban,

Ga ta nan kusa da ni in bata,idanu ya zaro Jin wai mama Na gefen ta take wannan haukan sam rayuwar turai be yi ba wlhy,hello are you lost again ta tambaya tana fari da ido kamar yana ganin ta,

Bata shine abun da kawai ya ce da ita,ba musu kuwa ta mika wa mama wayan,

Sallama ya fara mata sannan ya gaida ta,ta amsa cike da kauna sannan ta tambaye shi ya hanya ya sauka lfy,wlhy Alhamdulillah mama saidai gajiya gaskia Bauchi da nisa,dan murmushi tayi sannan tace ai ka dade baka yi tafiya bane Babana ya sanya kake ganin nisan Na shi har haka,

Gaskia kam baki ji jiki Na ba wlhy mama kamar an mun duka,dariya ta Dan yi sannan tace haba dai son to waye zai buge ka din,shima dariyan ya dan yi sannan yace Ashe Amraah ta zo?

Eh wlhy kana fita ko 30 mints baka yi ba sai ga shigowar ta,basu ma dade da dawowa da Haanaan daga Havilla sun je shan ice cream ba,

Nan take yayi kicin kicin da fuska yace haba mama nawa Angel take da za a wani kaita shan ice cream in mura ya kama ta fa,gaskia a ce da ita kar ta kuma fitar mun da yarinya wani wai yawon shan ice cream,ya kare da iya kar gaskiar sa,

Baki mama ta bude tana mamaki irin wannan rashin kunya ta Nameer,sannan tace zan iya bata sai ka fada mata da kan ka,uban da ya fi kowa son yar sa,

Ayya Mama Na ga dai har yanzu Haanan baby ce ko 3 years fa bata yi ba,ai ice cream is not good for her health at all,ya kare a marairaice,

Hmmm son ke nan,ni kam a huta gajiya sai mun yi magana later hajiya Salma na kira na,da haka ta mika wa Amraah wayan tata,

Jin abun tace ne ya sanya shi kashe wayar da sauri domin Allah ya gani bayi da energy in tsayawa Jin abubuwan da wancan wawiyar yarinyar za ta ce masa,

Toilet ya fada kai tsaye bayan yayi placing order in abincin da zai ci,wanka yayi da ruwan zafi ya gasa jikin shi sosai yanda wahalan za ta warware sannan ya fito,

Shafa ya gama yi tare da combing in gashin shi, sannan ya sanya light ash in jallabiya a jikin shi,yana fesa turare yayi daidai da knocking in kofar dakin shi,

Ko da ya bude Waiter ne dauke da abincin da yayi order karba yayi tare da musu godia sannan ya koma daki,

A nutse ya zauna bayan yayi bismillah ya soma cin abincin shi cikin kwanciyar hankali, wow Ashe dai mutan Bauchi an iya abinci ya kare yana murmushi shi kadan sa,

Saida ya cinye abincin tas, yayi realizing ashe dai yana dauke da yunwa a cikin sa,a nan cikin dakin Na shi ya gabatar da Sallan Magrib da isha'i sabida rashin sanin masallaci da ke kusa,

Around 9 ya gama komai tare da hayewa kan gado ya janyo laptop in shi tare da kunna wani American movie ya shiga kallo,ganin idanun shi Na ya ji ne ya sanya shi rufe laptop in tare da yin Azkar in bacci ya ja blanket sai bacci,

.........Senator

Shigowan shi ke nan a matukar gajiye cikin part in shi domin ba karamin gajiya yayi a meeting in party da suka yi yau ba,babban rigan jikin shi ya cire tare da mikawa Saa'eed yana cewa kai wlhy am really tired,

Sannu yallabai ko dai sai an hada ma da tausa ne yau,aa Saa'eed in nayi wanka da ruwan dumi ma zan ji daidai,da haka suka kara sa shigowa cikin parlor in shi,

Ido waje da matukar mamaki yake kallon shi,Afzal ya kira sunan shi a Dan tsorace domin ba karamin mamakin ganin shi yayi ba Sam be dauka zai dawo Nigeria yau ba beside jiya jiyan nan suka yi waya ya sanya a tura masa kudi kan ba nan kusa zai dawo ba,

Cike da tsantsan farinciki Afzal ya taso tare da fadawa jikin SEN yana cewa Dad ya ka ga surprise ina?

Fito da shi yayi daga cikin jikin shi yace Why are you back Afzal?

Kallon Saa'eed Afzal yayi sannan yace Mal can you leave us alone,sorry sir shine abunda yace da sauri tare da ficewa daga part in yana mamakin me ya kawo Afzal gidan kuma,

Afzal why are you back, ina ce I told u not to come back until I'm done with things over here,

Fuskan yara Afzal yayi tare da narai narai da idanu kamar me shirin yin kuka yace but Daddy I have missed you ne,and kai ka ki bari Na in dawo,Na gaji da zama ni kadai a can USA and beside I thought you are done with things over here ne ai tunda kai da kan ka kace da ni I shouldn't panic za ka yi taking control in komai da komai, ya kare yana zumburo baki,

Yeah Na sani but am not done working out things yet,bara ka gane ba Afzaal abubuwa sun cabe da yawa wlhy,SEN ya kare tare da zama yana dafe goshin shi,

A kusa da shi ya zauna sannan ya dafa hannun shi cikin soft voice yace yeah Dad Na san you are doing all your best so relax pls don't be over stressing your self out,

Numfashi kawai SEN ya sauke ba tare da yace komai ba,domin shi kadai ya San irin halin da yake ciki a yanzu,

Duk shiru suka yi for so mints kafin can Afzaal yayi breaking shirun da tambayan,How is Nadeeya doing?

I hope she's coping well?

Hmmm Afzaal ke nan Nadeeya is not in a good shape at the moment, but Doc Bashir is trying his best,

Can we go and see her right now pls?

Aa Afzaal dare ya Riga da yayi yanzu, and ka ga yau ka dawo daga USA am sure akwai gajiya a jikin ka,and ni kai Na a gajiye nake ka dai bari gobe da safe sai mu je ka duba ta,bayi da yanda ya iya toh kawai ya ce da Sen sannan SEN ya wuce dakin shi domin watsa ruwa,

.........Doc Nameer

Tunda yayi asuba be koma bacci ba,wanka yayi bayan ya kammala Azkar in shi sannan ya fito ya shirya cikin black trouser and white shit Wanda ba karamin karban shi suka yi ba,

Breakfast in da yayi order ya zauna ya ci cikin kwanciyar hankali, sannan ya tattara duk wani abun bukatun sa ya dau car key in shi tare da rufo dakin ya sauko kasa da key in,

A reception in ya aje musu key,sannan yace da su ya fita sai ya dawo,Allah kiyaye suka mishi sannan ya fada motar shi,da taimakon Map location da yayi setting a wayan shi ya iso Asibitin da aka mishi transfer, inda yayi parking a inda ake parking motoci,bayan an nuna mishi fanin da yake wato fanin Psychiatric,

Shiru kawai yayi a cikin motan yana me kare wa building in asibitin kallo tare da mutanan da kai kawo a cikin asibitin, yayi kusan mintuna yana zaune shi fargaban fitowa ma yake ji,

Like ka je gurin da baka San kowa ba and ba wanda ya sanka ya fi komai ban haushi,be ma san ta ina zai fara ba ko wa zai fara samu ma oho, yayi kusan 10 mints a cikin motan yana ta nazari kafin can yayi shahada yana me buda kofar motan,bakin shi dauke da adduar ubangiji ya sanya ya fara a saa, Allah ya bashi ikon da zai amfanar da mutane daga ilimin da yayi masa,Allah ya Hana ni zalintar kowa kuma ka tsare kowa daga zalinta ta,shine addu'oin da yake bakin shi yayin da ya fito daga cikin motan...


Ina matukar godia da irin so da kaunar da kuke nuna mun,Allah ubangiji ya bar mu tare,

A cigaba da sharing and commenting pls,

Ina yi wa kowa fatan Alkhairi❤️🙏🏻.
[6/21, 8:37 PM] My Best Best ❤️: 😭😔UBANA NE KO KISHIYA TA💔💔

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEY BEE)

.......

My what's app group link

https://chat.whatsapp.com/JYJvskgTzZICC4ksRfiMlK

In har kin San ba sharhi bane zai kawo ki toh don Allah kar ki shiga, haka zalika maza don Allah kar suyi joining domin group in mata ne zallah🙏🏻,

Ga masu son a tallata musu hajojin su,contact me via:

08100046388

..........
Page nine

**********

Cike da takun nutsuwa fuskan shi Na kallon kasa har ya shigo cikin clinic in hannun shi dauke da takardu,

Mutane daban daban ke kai kawo,Wanda yawanci nurses ne da kuma doctors sai workers, sai kuma tsirarun masu jinya da suke sanye da uniform a jikin su,don du samu su sha iskan safiya tare da hasken ranar hantsi,

Da ido yake bin su da kallo abun tausayi ganin haukan da suke yi tuburan,adduar samun lafiya yake wa ko wannan su,

Hey Mr Handsome in da ya ji an ambata ne ya sanya shi ja ya tsaya cak,domin tabbas ya san da shi ake yi,and duk Wanda ya kira shi da wannan sunan most be one of his old school friends and mate,

Da mamaki ya juyo domin ganin waye haka,a tsaye ya ganshi yana zuba masa murmushi,

Shi din ma murmushin ya maiyar masa tare da bin shi da kallon mamaki,tabbas ya gane shi, course mate in shi ne Wanda zai iya ce wa ma suna mutunci ba laifi domin har auran shi ya zo, canza wayar da ya yi ne ya sanya shi losing in contact in shi,

Doc Habeeb long time no see,Nameer ya ce yana mika mashi hannu,

Ka bari kawai mr Handsome I have been trying your no for a long period of time bana samun ka,har Na zo Na hakura,

Ayya wlhy Habeeb line ina ne ya samu matsala Na canza sabo,sai kuma nayi losing contact in ka,how have you been,wai me ma ya kawo ka Bauchi,

Dariya doc Habeeb ya sanya sannan ya ce see you ai kai zan wa wannan tambayan domin Bauchi kam ai garin mu ne,and wlhy a nan Na samu aiki,so ka ga am working here kai fa me kake yi a Bauchi,

Hmmm bari kawai Habeeb ni ba Na manta ba Ashe kai Dan Bauchi ne wlhy transfer aka mun daga 44 xuwa nan hospital in jiya shigowa ta ma,

Ayya toh ubangiji ya sa da abunda ya tare,where is madam ko ka bar ta a can masaukin ka,am very sure yanzu kam kuna da babies ko,

Jin abunda ya fadi ne ya sanya annurin fuskan Doc Nameer daukewa cak,lura da hakan ne ya sanya Habeeb cewa am sorry friend ko Na fadi abunda be dace bane,

Aa sam baka fadi abunda be dace ba ya daure ya ce,sannan ya kara da Alhamdulillah we are blessed with a little beautiful daughter, saidai unfortunately Noor ta koma ga me sama gurin haihuwar angel,

Allahu Akbar am so sorry for your lost friend,Habeeb ya ce yana girgiza kai,domin ba karamin mamakin mutuwar Tata yayi ba,and ya tausaya wa Nameer in domin shi kanshi sheda ne da irin kaunar da ke tsakanin Nameer da Margayiya,

Ubangiji ya mata rahma ya jikan ta sannan ya raya bayan ta,Ameen ya Allah Habeeb thank u so much,

Haba babu komai Mr handsome, so ina angel in take,wlhy Na baro ta Kaduna a gurin mama jiya da zan taho,

Allah sarki Allah ya raya ta bisa sunnah sannan yayi mata Albarka ya kuma baka mata ta kwarai Wanda za ta maye maka gurbin noor ta kuma rike Haanaan da amana,murmushi kawai Nameer yayi domin shi yana ji a jikin shi har ya koma ga Allahn sa bare kuma Kara soyayya ba balle har a kai ga batun aure,

A fili kuwa cewa yayi me hali baya fasa halin shi Habeeb har yanzu dai surutun Na nan,na biye ka sai mu kwana kana mun zuba,

Dariya Habeeb in yayi sannan yace ga ka kai kuma miskili ba baka kaunar surutu ko kadan saisa Sam bara ka iya zaman gida Na ba ashe domin daga ni har Madam da little boy in mu surutu gare mu,

Wait Habeeb wai kana nufin kayi aure,dariya ya dan yi sannan yace getting to 2 years ke nan da aure Na har Allah ya kawo karuwa mun samu baby boy,

Kai Masha Allah ubangiji ya raya shi da imani Allah ya kade fitina a zaman ku,ameen ya Allah doc Nameer ashe dai za mu Kara haduwa ikon Allah sai gashi guri daya za mu Na aiki,kai it was so nice seeing you again,

Smile Nameer yayi yace it was nice seeing too,ni dai yanzu nuna mun office in senior Doc in da ke gurin nan nayi reporting don Na samu mu fara aikin da kake murna an hada mu guri daya,

Dariya Habeeb yayi sannan yace bara ka gane bane,wlhy,Nameer haduwa da Wanda ka sani tun before dadi gare shi,mu je in gwada ma office in shi,sunan shi doctor Bashir sai kayi a hankali don mutumin Dan banza ne,

Kai kawai Nameer ya girgiza domin in dai surutu ne da gulma Habeeb to ya iya shi kamar wata mace,

Har bakin office in doctor Bashir Ubaidullah ya rako shi sannan yace da shi in kun gama da shi ma hadu a new office in ka ko nawa,da ki kawai ya amsa shi sannan yayi knocking in kofar bakin shi dauke da sallama,

A zaune ya tarar da Doc Bashir bayan yace da shi ya shigo,seat ya nuna mishi alamun ya zauan,bayan ya zauna in ne,yake tambayan shi daga ina,

Nan Nameer yayi masa bayani kan daga kaduna aka mishi transfer nan,

Saida ya kare masa kallo sannan yace ina takardun naka,

Akan table ya aje masa,sannan Bashir ya shiga dubawa a gadarance,ganin komai ya cika ne ya sanya shi dagowa yace well doc Nameer Abdallah Na ga takardun ka,komai normal ka koma gida daga gobe za ka fara aiki,

Da mamaki Nameer ke kallon shi why zai ce ya koma sai gobe ya dawo bayan shi ya dauka ya zai fara aiki,sai sa ma yayi sammakon sassafe,

Yana kokarin magana ne ya ji an bango kofan,a zuciye Bashir yace wannan wani irin Jaki ne haka zai bugowa mutum kofar office, ganin Nurse Kareematu ce tsaye tana watsa mishi kallon banza domin ta ji me ya ce wato ni ce jakar shine kalman da ta furta tana hararan shi,

Dariya ya dan yi sannan yace dadi Na da ke saurin fushi wallahi ai ban San ke bane,tsaki ta ja sannan tace wai ka je kayi baki,

Da mamaki ya maimaita kallman baki kuma ni kuma suka ce suna nema,

Ji wani tambayan iskanci Bashir in ba kai suke nema ba meyasa zan zo Na fada ma,SEN da wani matashi,

Jin sunan da ta ambata ya sanya da sauri Mike wa sannan yace haba Kareema why baki fada mun since ba kika sa zan bata masa lokaci ya kare yana gyara zaman lap coat in shi,

Nameer ya kalla sannan yace I got important issues a gaba Na so see u tomorrow kawai,ah Doc kace sabuwar hannu muka yi,Kareematu tace tana me bin shi da wani irin mayen kallo,

Jin abunda ta fadi ne ya sanya Nameer mikewa tare da watsa mata wani irin wulakantattcen kallo sannan ya bar office in,cike da mamakin wani SEN ne ya zo cikin asibitin nasu,

Doctor Bashir kuwa yanda kuka san zai yi wa SEN sujjada tsaban dukawa yana gaida shi,fuska sake SEN ya amsa shi tare da tambayan ya aiki,domin ba karamin murna yayi ba da jiya ya kira shi a waya ya sanar da shi plan in su Na ta working out,

Afzaal ya gaida wanda ya amsa shi cike da isa da gadara kamar Dan sarki,sannan suka nufi Isolated room inda aka killace Nadeeya,

Tun daga waje suke jiyo ihu da dariyar ta da alamun surutu take da kanta take irin wannan mugun dariyan,

Saida ya rubuta pin code in sannan kofar ta bude suka samu suka shiga kofar ta rufe,

A dantamalin kasan tiles suka same ta tayi zaman yan daukan karatu gashin kanta ya sauko sun rufe mata har fuska,Wanda su take irgawa wai don ta ga yawan,su sai ta kai quarter in counting in Sai ta manta shine abun yake bata dariya,

Da ido Afzaal yake bin ta da kallo domin ya kasa yarda wai Nadeeya ce wannan zaune a kasa hakan nan da sunan tayi hauka,

Kusa da ita SEN ya zo tare da taba shoulder in ta yana fadin princes look who is here to see you,

Juyowa tayi a razane don Jin an yi mata magana saidai Sam bata gane me yace ba,karaf idanun ta suka sauka a kan fuskan Afzaal,

Wata iriyan ihu ta sanya me mugun Kara Wanda saida kusan rabi yan cikin clinic in saida suka ji a ciki kuwa har da Nameer Wanda ke Dan zagawa don ganin ya tsarin gurin yake kafin zuwa gobe ya fara aiki,

Kamar Wanda aka tsikara ta mike da sauri har tana harde kafa tana kusan faduwa,flower vase in jikin gadon ta ta dauka kafin kowa yayi auni ta kwada wa Afzaal a goshi Wanda nan ya fashe kalban kuma ta yanka mishi fatan goshi nan take jini ya balle masa,

Wata iriyan Kara ya sake sakamakon azaban zafin da yake ji da kuma yanda jini ke zuba masa yake yi,baki bude Doc da Sen ke bin ta da kallo domin tunda ta fara haukan nata bata taba duka Ko attempting in ji wa kowa ciwo ba in ba kanta ba,

Kafin sukai ga mamakin ya sake su tayi wata super in Albarka tare da fitowa akan Afzaal Wanda saida ya kai kasa,

Wuyan rigan shi ta cukumo Wanda ya baci da jini,idanun ta Na fidda hawaye tana ihu ta hau cizon shi tana Marin shi ta ko ta ina a fuskan shi,

Ihu yake domin ba karya ba karamin azaba yake sha ba,domin in ta kama fatan yanda ka san ta samu fatan rago ko kaza yanda take ja ga shi zafin Marukan nata yake ji har cikin brain in shi,

Ihu yake yana fadi Daddy help me pls zata kashe ni,ina Nadeeya bata ma San yana yi ba duka take mishi ta ko ta ina kamar Wanda Allah ya aiko ta,tana kuma kan ihu tana surutan da ni kai Na ban San me take fadi ba,

Ganin tana kokarin kashe shi da duka ne ya sanya doc Bashir danna wani red button Wanda yayi alarming in nurses su taho da sauri akwai matsala,

Ai ko cikin sauri sai ga su Sister Kareematu da kyar aka samu aka banbare ta daga kan Afzaal tana ihu tana cizon nurses in tana fadin su bar ta sai ta kashe wannan dan iskan mara tsoron Allah,a bar ta ta ga bayan shi,domin barin irin wannan mugayen shi da Sen a doran kasa masifa ne domin Jinin su ya Riga da ya halatta,shine irin ihun kukan da take yi,da kyar da sidin goshi aka tsikara mata aluran bacci tare da kwantar da ita,tare da sanya mata chain a hands inta,ganin tayi bacci ne ya sanya Doctor Bashir cewa Kareematu ta ja Afzaal a je a gyara masa ciwuwukan shi,in an gama ya same su a office in shi,

Hannun SEN ya ja tare da fitowa da shi daga dakin har suka iso office in shi jikin SEN a mace yake da abunda Nadeeya ta aika ta,

Zaunar da shi Bashir yayi tare da ibo mishi ruwa me sanyi a cup daga dispenser ya mika wa SEN,yallabai ga ruwa ka samu ka sha,

Kofan SEN ya buge cike da tsantsan bacin rai Wanda yayi sanadiyar tarwatsewan cup in,

In sha ruwan me Bashir ruwan uwar ka kake son Na sha ya kare tare da wanke fuskan doctor Bashir da Mari,(Sen irin mutanan nan ne da Sam basu Iya controlling anger in su ba,in ran su ya baci in ba duka suka yi ba basa Jin anger in zai fita ko in ce irin masu saurin hannun nan ne),

Da hannu biyu Bashir ya dafe kumatun shi domin ba karya Marin ya shige shi,

Cikin zafin rai SEN yace Amman wlhy Bashir ban taba ganin Dan iska da ya raina mun wayo ba irin ka,Dan uban ka kace da ni Nadeeya tayi hauka ita kanta bata san waye ita ba balle ta san su waye a kan ta ya kare yana tsare shi da ido,

Ba karamin baci ran Doc yayi ba Amman haka ya daure yace ranka ya Dade kayi hakuri,wai hakurin uwar me zan yi kana nufin 50 mil in da ka karba a banza ne ko me?

Aa sam SEN ba haka bane, wlhy Na rantse ma da girman Allah a halin da ake cikin nan Nadeeya is not in her normal senses, tabbas ta yi nisa a hauka sabida injections In da nake bata,

In har ta haukace a taya ta gane Afzaal har tayi attacking in shi tana neman kashe shi,za ka fada mun gaskia ko sai Na sa an daure mun kai domin wlhy babu Wanda ya isa ya ci kudi Na ya kwana lfy Dan uban shi ba a yi shi ba,

Zufan goshin shi Doc ya goge yana Jin radadi a kan kumatun shi har yanzu kafin yace,

Ranka ya Dade maganar gaskia wlhy Nadeeya ta samu tabin kwakwalwa a yanzu haka,saidai one thing da nayi observing shine,har yanzu zuciyar ta ta kasa manta abunda kayi mata Wanda kila yana da hadi da wannan yaro da kuka zo tare,domin tun da muke da ita ko yatsan wani bata taba kamawa ba,

Tayu mun tsayar da aikin brain in ta mun kuma sanya shi kamuwa da tabuwa sabida aluran da muke bata amman abubuwan da ke heart in ta fa,ranka ya Dade daga gani akwai abunda kuka mata kai da Azaal Wanda ta kasa manta shi har yayi motsa ciwon nata har

Please Login or Register in order to submit comment