Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah ga shi fav chocolates in ki ne Na kawo miki,take care of yourself ko,yanzu zan ga doctor game da case in ki ko xa a canja miki treatment ne don Na ga jikin naki sai Kara rashin dadi yake yi,

Hawaye ke zuba a idanun ta, tana ji tana gani suka fita daga dakin ba tare da sun saurari ko sun tausayawa irin rokon da take musu ba,hurgi tayi da ledan chocolates in suka zube,tana kuka tana I don't want your money or chocolates freedom ina nake so,tunda Na bika ta lallami kaki yarda SEN mark my words sai Na tona ma asiri shine ihun da tayi Wanda am very sure daga shi har doc sun ji,

Kai kawai ga girgiza ba tare da yace komai ba suka nufi office in Doc bashir,

Suna shiga ya daga hannu cikin zafin rai tare da kwada wa Doc bashir wata irin Mari me zafi da Kara,tassss kake ji,

Da sauri ya rike kumatun sa da yake ji suna masa radadi,yace Yallabai lafiya,

Cike da bacin rai SEN yace lafiya kake tambaya ta Dan uban ka,ni za kayi wa karya Bashir ni?ya nuna kansa, Na gani jiyan nan sai da Na sanya aka kawo maka 5 mil duk za to Na kayi nisa akan aikin da na baka ace one simple job ka kasa mun sai cin kudi Na kake sabida gani Dan iska me kudin banza ko,

Da sauri ya ce a a yallabai wlhy sam ba haka bane, aluran ne har yanzu basu iso ba sun dan yi wahalan samu ne,

Dallah ka mun shiru yau abu kusan sati har yanzu ace Alura ya kasa samu,kasan baka shirya ba kace we can trust you with this iyeee ya kare cikin fada,

Shi dai doc be da baki da ya wuce hakuri don hakuri ya ringa ba wa SEN yana mishi Alkawari kan in sha Allah gobe za a kawo,

Da kyar ya samu ya sauko sannan yace da shi and wlhy Bashir Na ga alaman kana da son duniya muddum Nadeeya tayi maka wani offer a cikin haukan ta ka karba sai Na ci uban ka,sai Na daure ka tas kai da zuriar ka in har Na shigo ban ga yarinya ta ba,am doing this for her on good so bana son Jin wata bad news daga gare ka shine abunda SEN yace babu wasa a tattare da shi,

In sha Allah bara a samu ba baran baka kunya ba sir ,daga haka SEN be Kara cewa komai ba ya fice daga office in,duk Wanda ya gan shi sai ya kwashi gaisuwa inda duk wanda ya gaishe shi sai ya mai kyautan kudi, saisa yake kara siye zukatan mutane,domin video in da ya sanya aka yi Na biyun ba karamin sympathy ya samu a gurin mutane ba,domin haka aka din gi zuwa masa gida jajje wasun ma da yawa be san su ba,daga masu zuwa jajje sai masu zuwa kan sun san malami me karya sanmu,sai masu zuwa kan cewa sun fara yi wa Nadeeya sauka,ba karamin tausaya masa mutane suka yi ba,wanda hakan ya kwantar wa party hankali suka bar shi ya cigaba da Takaran sa,

Da harara Doc bashir ya bi bayan SEN tare da Kara susa kumatun shi sannan yace Allah ya isa na,haka kawai ni na san miye tsakanin ku da yar taka,nasan me ka mata kana neman maida komai kaina,(ni ko nace madallah ai kadan ka gani ko ba son kudi ba ),

Tsaki ya ja tare da kiran Wanda yayi order in aluran a hannun shi,nan fa ya hau surfa mishi tijara,ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba,hakuri mutumin ke bashi kan gobe da sassafe za a kawo mishi,da haka yayi ending call in,

Kamar yanda mutumin yayi alkawari kuwa sassafe aka kira doc bashir kan ya zo ya karbi order inshi,abun da yake ta jira ke nan tun tuni,be bata time ba ya je ya karba Wanda aka sako masa a cikin box,kai tsaye hospital ya nufa don so yake yanzu yanzu ya fara mata aluran don ya ga alaman SEN zai iya cin uban shi in be yi ba,

A hanyan shi ta shiga hospital in ne ya ga isowar doc Kareematu wanda daman shi ya kira ta tun yana hanya,a tare suka yi parking sannan suka shigo,

Kareematu aluran fa sun iso Na sanya wada ya kai mun office ina kuma yau nake son Na fara mata,

Kallon shi tayi sannan tace kai doc gaskia ni ina Jin tsoro kasan fa wannan aikin na da hatsari za a iya kwace mana lasisin mu muddum asirin mu ya tonu,

Ke dallah dadi Na da ke tsoro,ga dai ki da son abun duniya Amman akwai tsoro, taya asirin mu zai tonu daga ke ne fa sai ni muka San wannan batu,

Ke din ma don ina kaunar ki da arziki ne ya sanya Na fada miki,don ko banza ai ina moruwa da ke ya kare yana kashe mata ido daya,

Ni dai gaskia Bashir ina Jin tsoro wlhy Baban ta fa babban mutum ne,in ya sani baka tunanin mu kare rayuwar mu a prison,

Oh shit Kareematu wlhy Sam baki gane wa nace miki ki saki jikin ki,aluran nan ma fa bake za ki Na mata ba ni zan nayi are u happy now,ya kare yana kallon ta

Gaskia ni kam Bashir ina Jin tsoro, Dan kakai ya girgiza sannan yace na gane matsalan ki bani account details in ki,ko da yake ma bar shi ina da shi I think,

Dan wayan shi ya daddanna sannan yace da ita,Na miki transfer in 1.5mil are u in for this or no,

Idanu ta zaro jin amount in da ya ambata,bakin ta har rawa yake tace are are you seri ous Bashir,

Dan dariya yayi sannan ya nuna mata debit alert in da aka masa,wanda take ta ji karan shigowan message,

Haba dan ihu tayi tare da rungume shi tana wlhy ya shigo Bashir kai 1.5 fa,shafo bayan ta yake yi cike da iskanci yace wannan somin tabi ne my love,in har kika bani goyan baya har mota sai Na canza miki,

Cike da murna tace wlhy har goyan jiki ma na baka Doc Bashir ina,

Shegiya kareema yaushe rabon da ki kira ni da haka,fari tayi irin Na yan bariki sannan tace ai yau a guest house in ka ma zan kwana, dariya ha kwashe da shi sannan yace to shi mijin naki fa,dallah ya tafi can ce masa zan yi night gare ni domin yanda ka faranta mun din nan sai Na jiyar da kai dadi Na musamman, (wa'iyazu billah, wannan rayuwa da muke ciki yanzu abun tsoro ne ace mata da auran su suna zina,Allah ka dada kare mana imanin mu da mutuncin mu),

A tare suka shiga dakin Nadeeya a kwance suka tarar da ita kamar me bacci,

Kan gadon Kareematu ta hau tare da shafa kan Nadeeyan sannan tace sannu maza tashi lokacin magani yayi,Nadeeya bata ko kula ta hasali ma ko ido bata dago ta kalle ta ba,

Kareematu tashi ki dauko drip in da muka shigo da shi ki daura mata domin she looks very weak and pale am sure taki sake wa ta ci abincin kirki,

Tashiwa kareematu tayi tare da dauko drip in,hannun Nadeeya ta kama tare da fara neman jijiyan ta,ko motsi Nadeeyan bata yi ba domin ita kanta tana bukatan karin ruwan,don gani take tsaban kukan da take yi ruwan jikin ta Na gab da kare wa,

Cike da nutsuwa, Kareematu ta samu ta huda Nadeeya tare da daura mata ruwan,

A hankali ruwan ya fara shiga jikin ta wanda ta lumshe idanu ,domin ji tayi kamar kanta Na juyawa,a sannu bacci yayi awun gaba da ita sakamakon aluran baccin da Kareematu tayi a cikin drip in,

Kallon Bashir tayi da ya gama hada aluran a sirinji guda biyu yana nufo Nadeeya ya sanya tace Doc anya kuwa wannan doss in basu mata yawa ba ,Na ga aluran nan duk masu karfi ne and biyu Na ga kana shirin yi mata,

Dan dariya yayi sannan yace my Kareematu ke nan,ai da uku ne ma soke dayan nayi domin zai iya zamo mata matsala nan gaba,sabida in no time nake son ya fara aiki ya sanya zan Na mata biyu daya a cikin drip while daya a jijiya,ya kare yana juye ruwan aluran a cikin drip in,

While dayan a nutse ya kama hannun ta tare da tsikara mata a jijiyan ta,yauwa kin ga an gama Na yanzu saura kuma an jima da yamma in sha Allah,

Da mamaki ta kalle shi bayan ya ja wa Nadeeya bargo tace kana nufin sau biyu za a Na mata a Rana,yes sau biyu ne hope dai kin kalli yanda Na dama aluran da yanda nayi mata don in bana nan ke za ki Na mata,

Da kai kawai ta amsa shi sannan suka baro dakin yana cewa yi sauri ki karasa abunda kike yi nima Na samu Na gama aikin gaba Na mu samu mu tafi don wlhy tun dazu da kika di ga mun Zuma a baki hankali Na ya fara barin jiki Na........


Na san akwai lots of typing errors hakan kuma ya faru ne sabida rashin edit in da ban samu nayi ba,so ana mun afuwa pls🙏🏻,

Hakikanin gaskia bani da bakin da zan gode muku yan group ina bisa irin goyan baya da kaunar da kuke nuna mun saidai nace Allah ya saka da Alkhairi ya kuma bar kauna🥹❤️,

Ina mika sakon gaisuwa da kuma godia Gare ku masoyan book in nan Wanda Na sani da Wanda ban san su ba,Allah dai ya bar zumunci,

Sai kuma gobe in Allah me komai me kawo ya so,

Ina yi wa kowa fatan Alkhairi.
😭😔UBANA NE KO KISHIYA TA💔💔

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEY BEE)

........

My what's app group link

https://chat.whatsapp.com/JYJvskgTzZICC4ksRfiMlK

Ina marhaban da duk me son shiga wannan group in saidai in har kin san ba sharhi za ki Na yi ba toh don Allah kiyi zaman ki kar ki shigo, haka zalika maza na roke ku da Allah kar kuyi joining in group in nan domin Na mata ne zallah🙏🏻,

Ga masu son a tallata musu hajojin su contact me via:

08100046388

.........
Page seven

**********

Tabbas rayuwar duniyar nan abun tsoro ce Na kuma Kara yarda in har kana raiye to kana da sauran kallo,domin lokaci daya Nadeeya ta koma abun tausayi,duk wani me imani in har ya ganta sai ya zubda mata hawayen tausayi,

Yau kusan kwana biyar ke nan doc bashir nayi mata injections in nan ba daga kafa kullum biyu safe da yamma,irin yawan doss in da yake bata ya sanya ya fara nuna effect in shi akan ta,

Domin a halin da Nadeeya ke ciki yanzu ita kanta ba gane kan ta take yi ba,haka kawai cikin dare za ta fara ihu tana tsigan gashin kanta tana kuka tana surutai,ko kuma ta mike tayi ta rawa tana tafi ita kadai,

Sai abun yayi kamar ya lafa da ya kuma mata aluran shi ke nan sai kuma ta burkice ta fara behaving abnormal,

Ba karamin dadi doc bashir ke ji ba ganin aikin sa is working domin Jinin Nadeeya Sam be da karfi ya sanya within no time injections in ya fara aiki,kila da ukun yake mata,wataran saidai ta buge kowa ta fita da gudu tsirara kan titi tayi hauka tuburan, Nadeeya brain inta ya fara samun matsala, don ita kadai sai ta dauki fiye da awa tana hira da iska,ko kuma ta tashi da gudu tayi ta zagaye dakin tana tsalle,abun dai gwanin ban tausayi,

Yana da assurance tunda har ya fara aiki haka in har ya cigaba da bata to burin su zai cika zata yi hauka Na har gaban abada bara ta taba samun lafiya ba,

........... Kaduna

Doctor Nameer ko tsaf ya hade kayan abun bukatun sa domin a gobe Sunday yake son shiga Bauchi Monday yayi reporting ya fara aiki,

Zaune suke da Mama suna Dan taba hira Haanan Na jikin shi yana mata wasa,

Hope dai ka dauki yajin da Na zuba maka a roba dai ina,Dan murmushi yayi sannna yace eh mama Na dauka,ai ko kin taimake ni domin ban San ko abincin restaurants in su Sam ba dadi,

Dariya mama ta sanya sannan tace Amman kam Babana baka da dama wai ni kam me ka maida Bauchin ne,yanda kake ganin Kaduna city ne haka ma bauchin take fa,garin Sam ba laifi ai nan muka kai yar gidan Aminiya ta hajiya Salma,

Shi dai be ce da ita komai ba domin Allah ya gani ba son zuwa garin nan yake ba,

Can kuma sai ya kalle ta yace Maama ko dai za ku shirya mu tafi tare ne,

Ai nan ma dariyan ta kuma sanya wa sannan tace yau kun ji mun Babana wai sai kace wani karamin yaro,kawai sai Na shirya mu bika gurin aiki,ni ba matar ka ba ina mahaifiyar ka,ai ka ga ranar aure yau da da matar ka ce ai ba sai ka tsaya neman shawaran ta ba,

Fuskan tausayi ya sanya sannan yace ayya Mama na yanzu don Allah bara ki Bini ba zan dai siya miki Sheraton wannan sallan a dinka miki,

Dakuwa tayi mashi da hannu sannan tace kaci gidan ku Babana to rike kayan ka in dai sai Na bika Bauchi ne kai sanin kan ka ne sarai tun kafin Na Auri Alhaji Allah ya jikan shi nake sanya kaya masu tsada,dariya ya kwashe da shi domin shi din ma ya fadi ne don Jin bakin mahaifiyar ta shi,

..........

Alhaji Abdallah Mai nasara Dan haifaffen garin Kaduna,daga shi sai kanwar shi guda daya tal me suna Hajiya Bilkisu iyayen su suka haifa,

Baban su me rufin asiri ne sannan ya yi kokarin wadata su da duk wani abun da yaro xai bukata na rayuwar yau da kullum,haka zalika mahaifiyar su mata ce jajirtatciya akan yaran ta domin sun samu tarbiya daidai gwargwado,

A haka har suka girma Abdallah ya samu gurbi a makarantar ABU inda ya hada degree in shi, dake mutum ne me son kasuwan ci sai ya fada kasuwa inda Allah ya sanya wa harkan Albarka budi sai shigo masa suke yi ta ko ta ina,

A haka ne watarana ya je garin Yola ya ci karo da matar sa kyakkyawan bafulatana in da a take ya nuna yana bidan auran ta,ba tare da bata lokaci ba aka tsaida musu Rana,domin an yi dace itan ma tana kaunar shi sannan yana da gida aiki har da abun hawan sa,

Ba tare da an ja lokaci me tsayi ba aka daura auran Abdallah da Amaryan sa Aishatu in da aka kawo ta unguwar badarawa anan cikin Kaduna,

Akwai shakuwa soyayya hakuri da kuma tsantsan biyayya a zaman Aishatu da Abdallah domin mata ce me kawaici da sanin ya kamata,ya sanya yan uwan shi suke Jin dadin zama da ita, auran su da wata bakwai lokacin ma har an samu rabo a tsakanin Allah ya dauki ran mahaifin Abdallah, Wanda ba karamin taba su yayi ba,an ci kuka kam domin sun yi babban rashi kafin suka fauwala wa ubangiji komai,

Allah ya Albarkaci Abdallah da Aishatu da samun yara uku biyu maza sai Autar su mace,

Dan su Na fari sunan shi Abubakar Sadiq Wanda a yanxu Baban Engineer ne,yana da aure harda yara uku suna xaune ne a garin Lagos,sai Na biyu Nameer,sai kuma Autar su Nana Khadija Wanda tai aure ita ma tana zaune a garin Abuja harda Dan ta Na miji guda daya,

Nameer Abdallah matashin saurayi ne me ji da jini a jika,akwai shi da cikar halitta da kwarjini tare da saukin kai,

Likitan mahaukata yake da burin karanta tun yana yaro ya sanya Baban shi biya masa kudi ya tafi Cairo don samun gurbin karatu a can,

Mutum ne me taka tsantsan da Rayuwar sa hakuri rashin magana da kuma tsananin tsoron Allah,mutum ne me yawan ibada tare da tsarkake da kuma mika alamuran sa ga Allah,ya sanya ya kasance mafi soyuwa a cikin yaran su domin shi Sam be da hayaniya ko matsala,mutum ne me balain kokari,sannan in dai abu be shafe shi ba to Sam baya sanya baki ciki,

Allah ya tsare shi baya shaye shaye balle neman mata,yana aji uku ne Allah ya hada shi da Ra'isaah Abdul Aziz,Wanda balarabiyar Egypt ce, soyayya ce me karfi tare da shakuwa ya shiga tsakanin su a kan kanin lokaci,ta zamo wani jini Na jikin shi,tunda yake be taba so ba sai akan Raa'isah Wanda yake Jin ta har cikin zuciyar sa,


A nata bangaran ma hakan take,ba tare da bata lokaci ba ta gabatar da shi wa mahaifin ta ganin kamalan sa ya sanya kai tsaye mahaifin nata yarda da batun soyayyar ta su,ganin ya kusa gama wa ya sanya aka bar bikin sai bayan ya gama karatun shi,

Cikin ikom Allah kuwa gamawan shi da wata guda aka daura masu aure wannan ranar kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha don murna haka yake ji,domin shi kan shi mamakin irin yanda yake tsananin kaunar Raa'isaah yake yi,

Hidiman biki aka yi aka gama sannan aka bashi Amaryan sa domin ya sanar da ita shi bare iya nisa da iyayen sa ba,a malali Baban shi ya Gina masa gida me kyan gaske inda nan aka sanya Amarya,

Rayuwar auran su rayuwa ce me cike da tsantsan soyayya da fahimtar da kuma tattalin juna,ko wannan su rige rigen faranta ran Dan uwan shi yake yi,duk Wanda ya ga yanda suke gudanar da Rayuwar auran su to tabbas sai yai shaawa, domin Raa'isa mata ce ta kwarai me tsaninin biyayya, babu abunda daya ke boye wa daya,Raa'isah ta zo Nigeria bata Jin ko zo a yaran Hausa Amman bata dauki wata uku ba aka fara koya mata hausa,


Watan su uku da aure Allah ya azurta ta da samun ciki,tattali kula da soyayya take samu daga gurin Nameer,

Wanda hakan yayi daidai da rasuwar Mahifin su Alhaji Abdallah me Nasara sakamakon hatsarin jirgin sama da suka samu,

Ba karamin jijiga Nameer yayi da Jin mutuwar mahaifin shi ba domin akwai shakuwa me karfi tsakanin su,sun yi kuka sun ji ba dadi Amman hak a karshe dole suka hakura suka fawala wa Allah komai suka cigaba da yi masa addua,

A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya cikin Raa'isah yana dada girma hutu Nameer ya dauka a gurin aiki domin bata cikakken kulawa,kama daga kan girki wanki,wanke wanke shara duk shi yake mata,ganin ta yi nauyi already,

Duk wani abun da zai faranta mata shi yake yi,haka zai kashe Rana daya ya zauna kawai yana yabon irin kyan da ta Kara sakamakon samun cikin nata,Wanda ita har mamaki take yi domin muni ta ga ta yi tare da kumbura Amman kullum Nameer kyau yake cewa tana masa,

Tabbas Nameer da Mama sunyi playing role me girma a rayuwar ta more especially ma lokacin cikin ta,domin duk wani kula da soyayya gata ta gani a gurin su,a haka har cikin nata ya shiga watan haihuwa,ba yanda mama bata yi da shi ba kan ya dawo da ita gurin ta zata fi kula da ita Amman Sam yace aa shi zai kula da Noor in sa,sunan da yake kiran ta da shi ke nan,

Suna zaune ranar Alhamis da safe yana matsa mata kafa yana mata hira akan in ta haihu bayan suna in sha Allah zai kai ta gida ta je ta ga family in ta,ba karamin dadi ta ji ba nan tayi ta murna tana she can't wait ta haihu,

Wannan daran haka suka raya shi cike da soyayya da shaukin juna,Wanda cikin dare naguda ya tashi mata gan ga gan ga,daukan ta yayi cak sai hospital, saida suka isa sannan ya samu ya kira mama,

Suna nan tsaye har asuba Amman Allah be yi ta sauka ba,har suna shirin shiga da ita tiyata cikin iko Na Allah sai ga kan jinjira a nan ta samu ta haife santaleliyar baby girl in ta fara me kyau da ita,in da ita kuwa Raa'isah ko shurawa bata yi ba tace ga garin ku nan rai yayi halin shi,

Ko da sakon mutuwar ta riski Nameer yankan jiki yayi ya fadi ya suma kwanan shi uku be San yanda kan shi yake ba,kafin ya farfado,

Da kyar da addua aka samu ya dawo cikin haiyacin sa domin kusan zare wa yayi,don ko kadan be yi tsakanin wai mutuwa Noor in shi za ta yi ba,ko ana gobe za ta mutu zama suka yi tare da tsara irin yanda zasu yi rayuwa tare da babyn su ashe rashin sani tafiya za tayi ba tare da ko ta san me ta haifa ba,babu ruwan Allah baya barin wani Dan wani ya ji dadi,Alhamdulillah Raa'isaah tayi mutuwar shahada,(ya Allah kar ka dauki ran mu sai kana farin ciki da mu),

Kwanan su 5 a Asibiti sannan aka sallame shi,gidan ta mama ta wuce da shi domin ganin lamarin Nameer in dai da ayoyin Allah,

A haka aka yanka wa yarinya rago tare da maida mata sunan mahaifiyar ta suna kiran ta da Haanan,Wanda Sam ba a yi taron suna ba sabida rasuwar da aka yi,


Da kyar da nasihohi aka samu Nameer ya dawo haiyacin sa domin ko kadan ya kasa jure rashin mahaifin shi da LOML a cikin shekara guda,


Tun da aka samu ya dawo hankalin shi ya kara komawa wani shiru shiru,kullum yana zaune shi kadai yana tunanin Raa'isaah,tare da daukan soyayyan duniya ya daura wa Haanan,ba ya shiri da abunda zai taba ta ko kadan,

Ba yanda ba ayi da shi akan ya kara aure ba,Anty Bilki har gida ta kawo masa tayin diyar ta Amrah kan ha aura ,Amman Sam ya nuna baya so,

Domin gani yake bare taba samun mata kamar Noor ba ta so shi tun bayi da komai Allah ne yi za ta more shi a yanzu da samu ke ta xuwa masa ba,saisa ya dagr duk wasu kudadan shi daga Maman sai Haanan yake wa spending,

Kwata kwata yaki bude zuciyar sa yau fiye da 2 years balle har ya sanya wata diya mace a ciki domin a cewar sa tun bayar rasuwar noor to be ga wata ya macen da ta yi masa ya aura ba,and da aka Dame shi yayi aure ko Dan angel in sa,shi he can take care of her alone, bare juri ganin ya auro mata tana cin uban Haanan in sa ba,ya sanya Sam be ma da raayin Kara auran,

..........Back to story

Har bakin mota Mama da Haanan suka rako shi sai kuka take tana mika masa hannu kan ya dauke ta ya tafi da ita,

Jin kukan nata yake har ranshi domin ya San Mama sam bara ta bashi Angel su tafi can uwa duniya kam,

Addu'oi sosai Na tsari da fatan saa mama tayi masa sannan suka rabu ya ja motar shi tare da barin gidan zuciyar shi Na zafi,don kukan da angel ke yi har ransa yake ji,

Sai da ya biya 44 yayi wa mujaheed sallama tare da daukan sauran abubuwan shi har mota mujaheed ya rako sa yana masa tsiya kan in ya je Bauchi pls ya duba mishi ya SEN da wannan mara ta idon yarinyar ta shi suke ciki,da toh kawai doc Nameer ya amsa shi domin shi miye hadin shi da Sen balle wata yar sa,shi da da xai je asibiti ko ina zai gan ta har ya San ya suke ciki oho, da haka ya shige motar shi tare da daukan hanyan Bauchin Yakubu,sai mu ce Allah ya kiyaye hanya Doc Nameer.....

Keep on sharing and commenting pls,

Ina matukar godia da irin kaunar da kuke nuna mun,Allah saka da Alkhairi,


Sai kuma zuwa Monday in Allah me komai me kowa ya so.
[6/21, 8:37 PM] My Best Best ❤️: 😭😔UBANA NE KO KISHIYA TA💔💔

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEY BEE)

.......

My what's app group link

https://chat.whatsapp.com/JYJvskgTzZICC4ksRfiMlK

Ina maraba da duk me son yin joining Amman in har kin San bara ki Na yin comment ba toh don Allah kar ki shiga,haka zalika don Allah maza kar su shiga,domin group in mata ne zallah kuma mafi yawan su matan aure ne🙏🏻,

Ga masu son a tallata musu hajojin su contact me via:

08100046388

..........
Page eight

*********

Tafiya good five hours ne ya shigo da doctor Nameer cikin Bauchin Yakubu,ba karamin gajiya ya taro ba domin shi ya tuko motan da Kansa,it's been a while since da yayi long journey haka

Please Login or Register in order to submit comment