Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah komai zai zo ya wuce,maganar Nadeeya kuma yau Zan Kara Sanya yan sanda suna checking duk wani shige da ficen motoci sannan Zan Sanya ayi sanarwa duk Wanda ya same ta Zan bashi kyautan makudan kudade,da yardar Odugwu nan take zaki ga an same ta,

Idanu ta watsa mishi tare da fadan Waye wani Odugwu,Abul bait da hankalin Ka kuwa,wani irin sakarci ne hka,

Da sauri yace hajiya Odugwu Yana nufin shugaba ne ina nufin Allah ke nan,

Bana son iskanci fa wani hauka ke nan Allah za Ka wani kira Shi Odugwu wlhy ka na kiyaye halcen Ka Kar Ka je fa kanka a wuta da kanka,ta kare cike da fada,hakuri ya bata sannan ta mike tace ni kam Zan koma ubangiji ya shige mana gaba,

Haba hajiya ko ruwa fa Baki sha ba,ina azumi Abul bait daman Jin Shirun ne ya sanya ni cewa Zan zo tunda Kai ka gagara zuwa,

Nan ma hakuri ya bata sannan yace da ita Yana zuwa,daki ya nufa kudi ya Ibo masu yawa sannan ya fito yayi daidai da fitowan Afzaal da gajeran wando,

Kai ko ba Afzaal ba,eh hajiya ni din ne Ina kwana ya kare Yana Sosa keya,

Abul bait uban me yaron nan ke yi cikin gidan nan na gani Yana da gida KO ba haka bane,

Eh hajiya daman sabida laluran da ta sami Nadeeya ne ya sanya Shi dawowa nan domin Zama Shi kadai in babu daadi,

Harara hajiya ta jefa mishi sannan tace yaron goye ne Shi,yanzu hka ya dace inda yake yawo daga Shi sai guntun wando,wannan AI iskanci ne,nan ko ta hau Sababi,

Shi dai Sen hakuri ya yi ta bata da kyar ya samu ya lalabata tayi shiru suka fito tana kuma mishi nisiha Kan ya ji tsoron Allah a duk abunda ya Sanya gaba,sannan in ya samu lokaci ya ci ya zo ya gaida kawunnan Shi tunda Shi komai sai an fada ma ka,

Hakuri ya kuma bata tare da Mika Mata kudadan hajiya gashi ayi tsaraba tunda kin ki kwana,

Mota ta shige sannan tace rike kudin ma Abul bait Wanda Ka aiko wancan satin ma ko ficika ban taba ba,ni dai ina kuma maka nasiha da Ka ji tsoron Allah a duk inda kake,murtala ja Mota mu tafi,a haka suka fice daga gidan aka bar Sen tsaye da kudi a hannu duk jiki a sanyaye,toh ko dai hajiya ta san abunda yake aikata wa ne,in ko haka ne da ya shiga uku,wani zuciyar ce tace da ta sani hajiya bara ta iya shiru ba sai ta tare Ka da maganar,sai dai in ta Fara zargi na,AI ko ya Zama dole ya canza taku domin ko giyar wake yake sha bare so hajiya ko wani ya San asirin Shi ba,ajiyar zuciya ya sauke tare da komawa cikin gidan.



Asaalamu alaikum

Ina fatan anyi jumma lfy ubangiji ya kara mana lafiya da Zaman Lafiya Allah kuma ya amsa mana ibadun mu da adduo'in muπŸ™πŸ»
[6/21, 8:37 PM] My Best Best ❀️: πŸ˜­πŸ˜” UBANA NE KO KISHIYA TA πŸ’”πŸ’”

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEYBEE)

........

My what's app group link

https://chat.whatsapp.com/FKZuWu1yj7VJ9L6izLqLhA

In har kin San ba karanta book ina da commenting bane zai kawo ki toh kiyi Zaman ki ba sai kin Shigo ba, haka zalika Maza should stay away from my group domin na Mata ne xallah πŸ™πŸ»,

Ga masu son a tallata musu hajojin su should contact me via:

08100046388

.........
Page twenty-two

*********

Doc Nameer*******

Tsaye yake a bakin kofar dakin Mama, Yana me jiran umarnin shigowar Shi,

Shigo Babana mun Gama wankan tace da Shi,da dan karfi yanda zai ji abunda tace,

Cikin sallama ya Shigo cikin dakin,a kwance ya tarar da Nadeeya sanye cikin sky blue dogon Riga ban da kamshi babu abunda take yi,idanu ya lumshe yana me kara gode wa Allah da ya bashi Mama a matsayin Mahaifiyar shi,

A kujeran dakin ya ja ya zauan sannan ya ce sannan da kokari Mama ta ubangiji ya Saka miki da gidan Aljannah,

Murmushi tayi sanann tace Ameen Baba na Bana fatan yanda kake kyautata mun kake tattalin rayuwa ta da farinciki na,a ce ka nuna abunda kake so na Gaza yi maka,ko na Gaza Kula maka da shi,ta kare tana murmushi,

Shima murmushin yayi domin sam be gane inda zancen nata ya nufa ba,

Zama ta gyara sanann tace ni kam Babana jikin yarinyar nan Anya kuwa ma tsaya na asibiti kawai,

Shi din ma Zama ya gyara sanann yace wlhy mama Nima abun yana Bani mamaki,yanda kika ce tana yawan firgici cikin dare kamar me yin miyakun mafarkai,

Haka kawai fa Mama na gan ta ranar tsaka ta Zama haka,ko yatsa bata iya moving,ya kare cike da jimami,

Numfashi mama ta sauke sannan tace wannan lamari nata da daure Kai Babana babu komai Amman muyi ta fada wa Allah in sha Allah zai amsa ya bata lafiya,

Ameen ya rabil Alameen mama tah Bari na je 44 gurin Mujaheed tun shekaran jiya yake ta Kira nasan ya na can yana Mita na dawo ban neme Shi ba,kuna bukatar wani Abu ne,

Murmushi tayi tana me matsa kafan Nadeeya da ke bacci tace ubangiji ya kiyaye ya tsare Babana Bama bukatar komai,saidai in kana dawowa Ka biya ta Islamic chemist Ka karbo mana pure honey da man Habbatus Sauda,na gurina ya kare,

In sha Allah zan taho da su iya kan Shi kuke bukata??

Eh iya kan Shi ne Shi din ma ita nake baiwa tunda Manzon Allah da kanshi yace kuna shan Habbatus Sauda da Zuma domin yana magance ko wace irin cuta da ke jikin Ku banda mutuwa,

Haka ne kam Mama ubangiji ya Kara mana lafiya da nisan kwana me amfani Bari na je sai na dawo,

Toh ubangiji ya tsare,da haka ya samu ya fito daga dakin da kyar ya samu Zaliha ta Raba Shi da Hanan domin rikici ta Sanya Kan sai ta bishi,

Kai tsaye 44 ya nufa inda Saida ya tsaya aka gaggaisa da mutanan arziki sanann ya nufi office in Mujaheed,

A Bude ya samu kofar so shiga yayi Kai tsaye tare da sallama inda ya samu babu kowa a office in,guri ya samu ya zauna Yana me kare wa office in kallo,

Rayuwa ke nan kamar be yi rayuwa a hospital in nan ba,shigowar Mujaheed ne ya katse mishi tunanin da ya dan fada,

Mikewa yayi fuskan Shi cike da annuri Ashe dai nayi missing in Ka my gee ya kare Yana Mika mishi hannu,

Harara Mujaheed ya watsa mishi kamar wani mace kafin yace dallah Malam zo Ka fice mun a office,

AI wlhy Nameer Ka gwada mun matsayi na ace sabida Allah yau kusan week da zuwan Ka Amman sai yau muke haduwa,haba daga zuwa Bauchi shine har Ka Hadu da abokan da suka Fini ko??toh wlhy Ka sani Shi dai tuwo sunan Shi tuwo ba a canza masa suna ni din nan dai nine Aminin Ka na tun yarinta duk Wanda za kayi Baya na suke eheee,

Nameer kasa rike dariyar da yayi ganin inda Majaheed ya rufe Ido yake surfa mishi masifa,

Nan ko Mujaheed ya kuma kulewa,harara ya kuma buga mishi sannan ya juya,ni baran bar maka office in bare yu Ka Sanya ni gaba kana mun dariya ba instead Ka Bani hakuri kayi mun laifi,amman Ka zauna kana mun dariya kamar Ka samu mahaukaci,

Kasa kasa Nameer yace miye maraba Likitan mahaukata kam AI shima ya zautun,

Dadin abun kaima zautatcen ne Ashe ya kare tare da bugun kafadun Shi,nan duk suka kwashe da dariya,

Zama suka yi bayan sun yi musabaha sannan aka shiga gaisawa,

Mutumina gaskia Bauchi ta karbe Ka fa,Ka ga yanda kayi fresh Ka Kara kyau kuwa har Dan kiba fa na ga Ka Kara mun,

Kallon kanshi Nameer yayi sanann yace a hakan wai,domin Shi a tunanin Shi ma Rama yayi ko don pressure irin ta Sen da ya sanya musu,

Eh wlhy Masha Allah kayi kyan gani kamar wani Sabon ango ko dai ko dai,kayi gamo da kyakkyawar Diya a garin Bauchi dake Kula mana da Kai ne,daman matan Bauchi an canfa kyawawa ne akwai su kuwa da iya tatali da iya Kula da saurayi ko miji,

Dariya Nameer ya Sanya sannan yace AI ko sanin Hali ya Sanya na taho maka da number in wata me kawo mana tallan masa a hospital,ganin yanda kake ta son karawa Maman Afreen kanwa,

Allah ya sauwaka wlhh Ka ma cuce ni AI ko class ina ya zuba duk aji na na kare da me kawo tallan masa ya kare Yana checking Kan Shi in,

Dariya Nameer ya sanya sanna yace yanzu fa Ka Gama cewa matan Bauchi akwai iya Kula da rike Maza,Kai ina ruwan Ka da kyan ta in da za ta Kula da Kai AI lafiya Lau,

Be Kai ga bashi Amsa ba wayan Nameer tayi Kara,ganin Habeeb ke Kira Saida kunya ya kama Shi don zai iya cewa tunda ya dawo be Kira Shi ko sau daya ba sai Shi Habeeb in ke ta Kira,

Dauka yayi tare da sallama,amsawa Habeeb in yayi sanan yace wlhy Doc Handsome zumuncin Ka kadan ne,AI ko ba dan komai ba mana magana akai akai mu samu mu ji ya jikin Nadeeya domin Muhibba sam bata da kwanciyar hankali kullum tambayar ta ya me jiki,

Murmushi Nameer yayi sannan yace don Allah kayi hakuri ban kyauta ba Kan wlhy abubuwa ne suka hade mun Amman a baiwa sister na hakuri a kuma ce da ita jiki Yana ta kyau Alhamdulilah,

Toh Masha Allah ya mutan gidan duka su mama hope dai duk kuna lafiya ko,

Wlhh lafiya kalau Alhamdulilah ya baby boy,da kuma aiki,

Dan dariya ya Sanya sannan yace ba Ka gudu Ka bar Baya da Kura ba,Kai Ka ga yanda garin Bauchi ya burkice da jamian tsaro ,ko wani lugun da sako suna gurin bincike Ake na inalilahi,

Dan dariya Nameer ya sanya sanan yace su yi ta yi,kashe kudi ne wlhy be ishe su ba kila da kudin ma aje Shi yayi campaign in Shi da Shi,domin wanann Jabiru kana ganin Shi idon Shi idon kudi,karba zai yi ta yi gurin Sen,

Kai dai Bari AI yanzu kam abun ma ya bar hannun Shi sun shiga court na ji tun last Monday yanzu haka an dage shariar suna gidan yari an bada tsaron su sai nan da 2 weeks za a koma a cigaba da case,Zan so mu samu mu je mu ga idanun mutanan Ka ya kare da dariyar mugunta,


Allah ya shirya ka Habeeb wlhy,yanzu kama sun ne abun dariya ko me,

AI dole nayi Dariya Nameer duk Wanda ya sai kwando daman ya san za ta zubda mishi ruwa,ba dai su son abun duniya da kwandayi ba wlhy kadan ma suka gani,ni AI Zan so a yanke wa ko wannan su hukuncin ko da 3 years in prison ne with hard labour kila su shige hankalin su in sun fito,


Dariya Nameer ya sanya sannan yace amman wlhy Kai kam akwai mugu ,

Ba wani mugunta abunda Ka shuka Shi zaka girba in ji bahaushe,yanzu dai yaushe za Ka dawo in ban da abun court in nan Bashir is busy AI da yanzu ayoyin zargi sun dawo kanka,

Hmmm haka ne kam yanzu dai ina gurin Mujaheed ne Bari na koma gida I will call u,

Okay Ka gaida Mujaheed in da haka suka yi sallama ya kashe wayar Shi,abun har yanzu dariya yake bashi,irin wannan Ka amshi laifin da ba Ka ma san a yaushe Ka aikata Shi ba,Amman kana paying price haka,

(One thing in life shine Ka ji tsoron Allah Ka ji tsoron shiga ko daukan hakkin bayin Allah, mugunta kyeta son zuciya ubangiji Ka Raba mu da Shi,zalunci babbar musiba ce,Ka zalunci Dan uwan ka ya daga hannu yace be yafe ba Allah ya Isa and Ka dauki hakan ba a bakin komai ba,Kai kasan isan Allah kuwa,Ka kuwa san ta inda wanann Allah ya isan zai fada maka kuwa??kila Kan dukiyar Ka kila lafiyar Ka,kila kan ranka babu ta inda bata faduwa, saisa no matter how try your possible best Ka ga Ka zauna Ka kuma rabu da kowa lafiya,Manzon Allah SAW yace Ka zo da ko wani irin laifi ranar kiyama yayi alkwarin tsaya maka Amman Banda shirka,Sata,da kuma laifi tsakanin bawa da bawa,domin wannan tsakanin Ka da Dan uwan ka ne in ya ji ya yafe fine and good, ubangiji Ka Raba mu da zulantar Kan mu da Yan uwan mu,ya kuma Sanya mu fi karfin zukatan mu domin da Ka cutar gwara Kai an cutar da Kai,Allah kayi mana me kyau duniya da kiyama🀲🏻)

Kashe wayar Shi ke nan ya mike tare da zuba su a aljuhu ganin fuskan Aminin nashi cike yake da tambayoyi Wanda he is not ready ya amsa su,

Amman Sarai kasan dai ina son muyi magana Ka wani mike,

Agogon hannun Shi ya kalla sannan yace sorry friend I have to go mama ta aike ni but don't worry zuwa gobe in sha Allah zan dawo mayi duk maganar da kake son yi,bye bye a gaida Afreen da haka ya fice daga office in ya bar Mujaheed Baki Bude brain in Shi cike fal da tambayoyi Wanda babu me bashi amsoshin su sai Nameer in,

Nameer ko,be tsaya ko ina ba sai Islamic chemist in Zuma da Habbatus Sauda in ya siyo da yawa ya biya aka bashi sanann ya biya ya siyo musu ice cream kafin ya dawo gida,

Mama ya tarar ta Sanya Khadija a gaba tana yi Mata fada Wanda harda zagi,abunda zai ce rabon da ya ji har ya mance,

Da sallama ya Shigo dakin tare da neman guri Kusa da ita ya zauna tare da riko hannayen ta Mama me ya faru waya bata Miki Rai har haka,

Cike da fushi take fadin haba Babana yanzu ace kamar khadija ce za ta zamo me bakin Hali ta fita zakka cikin yara na,tun ranar da Ka kawo yarinyar nan cikin gidan nan Naga alaman ran ta be so ba,sai wasu irin halaye take yi ta matsa mun lalle sai na Fadi Mata daga ina take,ba dama in ce ta taya ni Kula da yarinyar nan sai tayi Mata yar ko oho ko kuma ta hau Mita,

Yanzu Dan ubanta ita ta fi karfin Allah ya Mata irin wannan jarabawar ce ko ma fiye da haka,and ya Zama dole sai Ka san mutum a rayuwa kafin Ka ji tausayin Shi ko Ka taimaka mishi,

Gida dai nawa ne and Babana Dana ne na ciki na KO Kuda KO kuliya kana da right in kawowa Ka aje cikin gidan nan tunda na mahaifin Ka ne,Akan me za ta Saka yarinya a gaba toh an ki sanar da ke daga ina take akwai abunda zai Kara Miki ne in kin sani??

Ya Isa Mama don Allah kiyi hakuri dole ta so sani Kin san duniyar yanzu ba tsaro,na san tana yin hakan ne for our well being,

Wani well being Kai mance mugun hali irin na khadija kake wlhh, toh ni dai ka fada Mata babu ruwan ta,in har bara ta iya taya ni Kula da Amanar da Ka Bani ba toh let her stay away Kar na kuma Jin tayi wasu kananun maganganu in ba haka ba ranta zai yi munanniyar Baci,ta kare tana mikewa,

Numfashi Nameer ya sauke domin Sarai ya san halin kanwar tashi za ta aikata fiye da hakan ma in dai Khadija ce,

Nan ya shiga yi Mata nasiha tare da Mata bayanin taimakon Nadeeya yayi,ta dai ji amamn ita har yanzu so take ta san miye dalilin da zai Sanya Shi dauko ta all the way from wani gari zuwa Kd,


2 weeks later*******

Yau ta kama Monday ko wani maaikaci haba haba yake ya samu ya Isa gurin aikin Shi da wuri,


Nameer ya dawo bakin aikin Shi tun bayan kwana uku da suka yi waya da Habeeb inda ya bar Nadeeya can Kd karkashin kulawar Mama, khadija ma ta koma gidan ta domin Allah yayi ta da wata irin zuciyar banza Sam bara Ka ce yarinyar mama bace,gidan ya rage daga mama sai Zaliha sai little,Saida ya bar musu duk wani abunda za su bukata kafin ya taho ya cigaba da aikin Shi cike da kwanciyar hankali like babu abunda ya sani,

Babu yanda Habeeb be yi ba Kan su shirya su tafi court ganin yanda za a karasa wai ance zuwa da Kai ya fi sako amman sam Doc Nameer yace Yana da abun yi da ya fi wannan mahimmanci Shi dai ya je in ya dawo ya bashi labari,

Da haka ko Doc Habeeb ya shirya ya tafi high court,

Kasancewar rashin zuwan alkali da wuri Shi ya dan yi delaying in su domin har an taho da su doc Bashir,an Shigo da su cikin court room,

Dariya ce ta kusa subucewa Doc Habeeb yayin da yayi arba da doc Bashir da Kareematu,yanda kasan an babbaka gallon a fuskan su,wani irin Baki muni da kwanjamewar da suka yi,Kar Zaituna ta samu labari daman can ba auki gare ta ba,

Shigowar alkali ne ya daidai ta surutu da hayaniyar da ke cikin court in duk aka Mike domin nuna girma wa alkali inda saida ya zauna sanann kowa ya nemi gurun Zaman Shi,nan ko aka shiga karanto cases har aka zo Kan su doc Bashir,

Nan aka Kara fiddo su inda aka nemi lawyern me Kara da Wanda Ake Kara su fito,

Ba sai na ja Ku da dogon surutu ba nan dai aka shiga gabatar da shariar su inda sam su doc Bashir sun ki karba laifin su acewar su babu Abunda suka yi,


Asaalamu alaikum

Ina fatan kuna lafiya

Ayi mun afuwa 2 days in nan ayuka ne suka Dan mun yawa,GA ciwon Kai da ya sako ni gaba πŸ™πŸ»,

Na so in yi ya fi haka amman Allah be so ba,so bare with me pls

In sha Allah sai zuwa gobe in me kowa me komai ya so,


Ina yi wa kowa fatan Alkhairi πŸ™πŸ»
[6/21, 8:37 PM] My Best Best ❀️: πŸ˜­πŸ˜”UBANA NE KO KISHIYA TA πŸ’”πŸ’”

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEYBEE)

......

My what's app group link

https://chat.whatsapp.com/FKZuWu1yj7VJ9L6izLqLhA

In har kin San ba karanta book ina da comment bane zai kawo ki toh yi Zaman ki don Allah ba sai kinyi joining ba,haka zalika Maza should stay away from my group domin na Mata ne xallah πŸ™πŸ»,

Ga masu son a tallata musu hajojin su should contact me via:

08100046388

Alhamdulilah ya rabil Alameen 🀲🏻❀️Allah na gode da Ka nuna mun zagayo war haihuwa ta ina me Rai da lafiya, Happy birthday to my humble self ubangiji Ka mun albarka ni da zuriah tah,Allah Ka kare ni daga dukkan sharri, sannan ya Karo mun shekaru masu Albarka 🀲🏻,I am a year older today ,y"all should say a prayer for me da bakunan Ku masu Albarka πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ

.........
Page thirty_one

**********

Tafiyar hours ne suka iso da doc Nameer cikin garin Kaduna,a matukar gajiye ya dauki hanyar gidan hajiya,

Numfashi ya Shaka sai ya ji wani irin sanyi a ranshi komai dadin wani gari garin Ku ya fi,ji yake kamar be da wani sauran damuwa cikin duniyar nan,a nutse yake driving bayi da burin da ya wuce ya ganshi rungume da little in Shi,

Da haka ya karaso gidan yayi horn aka Bude mishi gate,Wanda be sanar da hajiya ya iso ba,ganin motar kanwar Shi Khadija ne ya bashi mamaki toh yaushe ta zo jiya suka yi waya da hajiya har ya kashe bata yi Mai tadin khadija ta zo ba,Baki ya tabe sannan yayi parking tare da fitowa,

Sai a lokacin ya ji zuciyar Shi ta Fara bugawa be gane yayi hauka ba sai yanzu,toh me zai Fara ce da Mama game da Nadeeya Akan miya sa ma ya dauko ta ba tare da yayi shawara da uwar Shi ba abunda tun Yana karami be taba yi ba shine yanke hukunci ba tare da ya sanar da mama ba,duk abunda zai yi sai ta sani ta bashi kuma go ahead,toh ko ya fice ya kaita hotel ne wani xuciyar ta Fadi mishi,

Da sauri ya girgiza Kai tare da aro jarumta kawai ya fito tare da rufe motar ya nufi cikin gidan,fuskar Shi dauke da murmushi,

Bakin Shi dauke da sallama ya shiga parlor in hajiyar,

Da gudu Hanaan ta yo inda yake tana dariya tare da Bude hannaye tana Fadi tana tashi duk a zumman oyayo,

Fuskar Shi dauke da murmushi domin ganin ta kawai ya Sanya Shi farin ciki,be dauka hka yayi missing in tilon diyar ta Shi ba sai da ya rungume ta a kirjin Shi,

Cikin gwarance tace papa,tana dariya tare da tsalle a jikin shi,

Kanta da ya sha kitso ya shafo tare da amsa ta da ya aka yi my angel,kallon Shi take kamar tana fahimtar abunda yake Fadi,

Ah Babana har Ka iso,mama tace tana murmushi,har ga Allah tana tsananin Jin kaunar Dan nata Nameer a ranta,yaron akwai Shiga Rai and tana matukar tausayin Shi,ko don Rashin matar Shi da yayi,

Aje Hanan yayi Wanda take kokarin Sanya mishi kuka,

Ka ji yar nema da can da be nan ya kike yi don neman ta yau shine za ki mana kuka,Maza yi mun shiru,

Kai kawai ya girgiza don in yace zai yi magana mama haushin Shi za ta ji,an wuni lafiya mama ta,

Lafiya kalau Babana Ka iso lafiya,ya hanya,ya kuma aiki,

Wlhy Alhamdulilah mama na same Ku lafiya,wlhy duk Alhamdulilah tashi mu shiga Khadija ma na ciki dazu da safe suka zo,

Mikewa yayi tare da riko yar hannun angel suka karasa shiga cikin parlor,

Kujera ya samu ya zauna tare da sauke ajiyar zuciya wato ba karamin gajiya ya kwaso ba,

Daddyn Hanaan Ashe da rabon mu Hadu,khadija ta Fadi tare da fitowa daga dakin hajiya,

Juyowa yayi fuskan Shi da murmushi yace ah mutanan Abuja yaushe a gari,wlhy yaya dazu muka zo ya aje ni ya koma,ina ta missing in Ku ne nace Bari dai na leko,

Murmushi yayi sannan yace toh sannnu da zuwa ina baby,bacci tace da Shi daga haka be kuma ce Mata komai ba,ita din ma haka ta juya tare da shigewa daki,

Ruwa da lemo yar aiki mama ta Sanya ta kawo mishi, sanna ta kawo mishi tuwon shinkafa miyar taushe ta sha Naman rago kifi da kayan Hadi,

Murmushi yayi Yana Kara Jin dadin samun mahaifiya irin maman Shi,

Fitowa tayi ta ga ko warmers in be Bude ba,kallon Shi tayi da mamaki bayan ta zauna sannan tace Baba na lafiya kuwa,

A hankali ya dago tare da cewa me kika gani mama,yo gani nai AI Baka taba komai ba,Kai da Ka Ibo gajiya AI Ka samu Ka ci Ka koshi,ko dai sai Ka watsa ruwa ne gajiyar ta fi sakin Ka,

Ni ban ma ga bakon da kace da ni za Ku zo tare ba,ko dai ya fasa biyo Ka ne,domin har na sanya an gyara mishi dakin Baki,

Sai a lokacin ya tuna da ya rufe yar mutane a mota ita kadai,da hanzari ya mike tare da kokarin yin waje,

Hannun Shi mama ta riko sannan ta janyo Shi ya koma ya zauna,idanu ta tsare Shi da su,Kai Baba na lafiya kake kuwa??

Shiru yayi domin har ga Allah be ma san ta inda zai Fara yi Mata bayani ba,be san ta ya za ta dauki maganar ba,

Kayi shiru ina maka magana,da alamu dai akwai abunda kake son fada Amman Ka kasa,yaushe muka Fara boye boye tsakanin mu Baba na wani abun ne ya faru na kalli gaba daya Baka da kuzari,

Jarumta ya aro tare da riko hannaye ta cikin taushin murya yace hajiya mama nayi Miki laifi ki ya yafe ni sabida Allah,

Kallon Shi ta dan yi na mintuna kafin ta nisa tace me kuma Ka aikata mun da har kake neman yafiya ta,

Mikewa yayi tare da saukowa ya zauna Kusa da kafafun ta kamar wani yaro karami tare da kama hannun ta,

Cikin sanyi murya yace mama ban ma san ta ina zan Fara Miki Baya ni ba,saidai ya Zama dole in sanar da ke domin Bani da Wanda ya wuce mun ke,you are the only one da nake da,and I don't know taya za ki dauki maganar I don't even know ko abunda nayi daidai ne ya dace ko be dace

Please Login or Register in order to submit comment