Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hanan ya daki jikin kujerar gaba ta motar ta rike hancin cikin tsananin fishi tana fad'in "Haba malam yaya kake shirin fasa min hancina ne?
Aliyu bai kula taba yaci gaba da tukin sa, Hanan tayi tsaki cikin takaici ta fara mita, shi dai bai ce matq k'ala ba har suka isa gida.
A gidan Alh. Musa ya dawo daga sallar magariba yana tsaye yana kallon fulawowin gidan Hanan da Aliyu suka shugo, yabi motar da kallo dai-dai lokacin da Hanan ta fito daga bayan mitar, mamaki ya bayyana akan fuskar Alh. Musa ganin ta fito daga bayan mota, kwata-kwata Hanan bata kula da tahowar mahaifinta ba sai da tajiyo muryar sa cikin tsawa ya kwala mata kira.
"Hanan! Hanan! Ta juya a gigice ta kalli inda mahaifinta yake da tashin hankali, yanda ya kira sunan ta shine sbin daya bata tsoro domin ba irin muryar yake kiranta bace, zata iya cewa tunda take ma mahaifin nata bai ta6a kiranta da wannan muryar ba
1 · Like · React · Reply · Report · 15 January 2017
Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:43] Zeinab Andiya Fox : (40)
Ta tsaya inda take ta kasa motsawa har ya iso ya tadda ta kafin tayi k'ok'arin yin Magana ya d'suketa da mari, sai-dai lokacin da Aliyu ya fito daga motar ya bud'e baki cikin tsananin mamaki, domin ya manta lokacin da mahaifin Hanan ya dake ta a gaban sa ya gani da idon sa.
Hanan ta dafe kunci cikin tsananin damuwa da kuka da rashin sanin meta aikata data cancanci mari, saita jiyo muryar mahaifinnata yana fad'in.
"Ashe ni ban isa na gaya miki magana kiji ba Hanan, ta yaya zan ce ki hau gaban mota amman ki koma baya don kin raina ni?
Hanan ta dafe kunci hawaye na zubo mata zuciyar ta na tuk'uk'i kamar zata fasa kirjinta ta fito, Aliyu ya tsaya tsuru cikin tsananin fargabar abin da zai faru, Slh. Musa yaci gaba da fad'a.kamar zai rufe ta da duka, abin da yaja hankalin Haj. Bilkisu ta fito daga cikin gidan da ssuri, mamaki ya k'ra cika fuskar ta sanda ta hango Hanan tsaye tana kuka Ahj. Musa na zuba fad'a, ta karasa kusa dasu cikin gaggawa tana kallon su daya bayan daya kamar bak'in ido a gurin ta tafara Mana.
"Lafiya Alahaji, meya faru?
Alh. Musa ya juya gareta da k'rfin haushi yana ci gaba da fad'a "Ashe ni ban isa na sanya Hanan tabi ba, Aliyu zai kai ta unguwa nace ta shiga gaban.mota ta zauna tun da ba direban ta bane ba a gaba nata shiga amman dazasu dawo ta koma baya ta zauna saboda ta rainani."
Ran Haj. Bilki ya baci har ta kasa 6oyewa tace "Yanzu hawan ta bayam mitar shine laifin data aikata data cancanci mari, wai kuwa kana cikin hayyacin ka Alhaji? Ya kamata ka dinga k'ok'arin banbance tsakanin aya da tsakuwa."
Aliyu ya fara k'ak'arin barin gurin domin bai son a gaban sa iyayan d'akin sa suna sa'insa, Haj. Bilkisu ta bishi da harara kamar idon ta zai fad'i k'asa, Alh. Musa kuwa.mamaki ne ya kamashj cikin k'arfin 6acin rai yaci gaba da Magana.
"Ashe ban isa nayiwq d'iya ta hukunci ba Bilki? Tunda kin zama kece mai sanin dai-dai da dai-dai ba gaya mini abin daya kamata nayi, na kula duk abinda yarinyar nan ke aikatawa tana samun d'surin gindi da gurinki ne, sai dai kisani wallahi bazan lamunci haka ba na gaya miki.
Haj. Bilki tayi kwafa cikin takaici ta kama hannun Hanan dake ci gaba da kuka sukayi cikin gida da gaggawa, Alh. Musa yabisu da kallo baki a bud'e kamar zai fasa ihu, yayi kwafa ya nufi cikin gidan kai tsaye shi ma.
A d'akin Haj. Bilki suka yada zango, Hanan ta zauna a bakin gado taci gaba da kuka tamkar ranta zai rabu da gangar jikin ta, takaicinta d'aya bai wuce irin yanda mahaifin ta ya mareta akan wani banza kuma a gaban sa ba, da ace akan wani laifi da ban ya dake ta abin bazai dame ta kamar haka ba.
[8/1 01:43] Zeinab Andiya Fox : Haj. Bilki ta dafa kafad'ar ta cikin rarrashi tana Magana "Kiyi hak'uri Hanan ki sanya a ranki shi ba kowa bane, kece komai, domin kece d'iyar.maigida, dole watarana zai tafi ya barki da mahaifin ki da gidan ku, domin na tabbatar bai isa yaci gaba da ruyawa damu har abada cikin wannan mugun halin nasa ba."
Hanan ta daga ido ta kalli Haj. Bilki cikin kuka ta fara Magana " Momy wanene Aliyu ne cikin rayuwar Daddy, menene had'in mu d shi?
Anya kuwa zai iya zamtowa almajiri kawai, ko dai akwai wani abu da Daddy yake boye miki da ba kisani ba akan Aliyu, inaji a jikina kamar d'an sane bai son bayyanawa saboda wani dalili, domin irin soyayyar da yake masa d'a kawai akeyiwa ita."
Haj. Bilki tayi murmushi mai ciwo tana kad'a kai "Ko d'aya Hanan kar ki sanya tinanin komai a ranki, Aliyu ba komai bane, illah wulakantaccen almajiri mara galihu wanda aka tsinta a k'ofar gidan nan, ya d'ora soyayyar sa akan yaron ne sakamakon kamarsa da d'ansa da ya mutu." Ta gyars zama takaici ya bayyana akan fuskarta.
"Kafin ni na sha gaya miki mahaifin ki ya ari Hafsa wacce ta kasance uwar 'ya'yansa uku, Abdul-jabbar shine babban d'ansa, sai k'annansa mata guda biyu, an sanya miki sunan dayq daga matan ne, asalin mahaifiyarsu mutuniyar garin yola ce, da suka hadu da Alhaji lokacin yana jami'a, sunyi aure sun haifi 'ya'ya uku.
Watarana ita da yaranta suka yi shirin tafiya biki garin Yala, yaso kaisu da kansa amman wani aiki ya hanashi tafiya ya kaisu har tasha suka hau mota, cikin yammar ranar ya sami labarin hatsarin motar su, babu wanda ya rayu cikin mitar sai k'aramar 'yar da take goyo, itama bayan kwana biyu ta rasu, tun daga wannan lokacin bai k'ara samun nutsuwar sa ba tsahon shekara guda sai da Allah ya had'a dani watarana yaje gaida mahaifina domin kamar yaron sane lokacin da suka yi aiki, tun ran da na fara had'uwa da shi ya bayyana mini matarsa da ta rasu da labarinta da irin son daya ke yiwa matar, da farko nayi k'ok'arin hakuri da shi amman son danake masa da kuma gano kishi nake da matacciya ya sanya na hak'ura na yadda na aure shi, duk randa rana ta fito har ta fad'i baiyi maganar matarsa da 'ya'yan sa ba to ranar lallai ya kwana ba shi da lafiya, sai da yaga raina yana 6aci sannan ya fara rage maganar su, amman maganar yaran musammman abdul bai dai nata ba har zuwa ranar da yatsinci Aliyu, ban taba ganin Abdul ba amman nafi tsanar sa akan auran don haka tun randa naga Aliyu naji ban k'aunar sa, na kuma tabbatar miki da sai na d'auki mataki akansa wallahi bazan yadda ina gidan mijina da uban 'ya'yana wani bare almajiri yaxo ya fini ba, ki bar ni dashi kawai." Hanan tayi kwafa tana goge fuska cikin k'ok'arin ganin ta daina kukan datake yi, amman tsanar Aliyu da k'iyayyarsa ta kuma cika ranta har tana jin bata ta6a tsanar wani abu kamar shi ba a rayuwar ta .
1 · Like · React · Reply · Report · 15 January 2017
Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:44] Zeinab Andiya Fox : (41)
A 6angaran Aliyu yayi ta k'allawa da kwancewa, ya tabbatar Alh. Musa yana k'aunarsa amman k'iyayyar da iyalinsa ke masa tana neman sanya shi ya sare, yana jin kamar yabar gidan, sai dai idan ya tafi ina zai je, gurin wa za shj, bai san ina za shi ba, a yanzu kuma yake ganin dacewar zaman gidan, domin yana gab da kammala karatun sa na sakandire shekarunsa ashirin da d'aya amman yanayin rayuwar da yake ciki bai jin wanda yake da shekaru d'ari ya kai shi samun abin da yake nema a rayuwa, karatu shine abin da ya rage masa, don haka zai yi hak'uri har ya kai ga nasara, Hamza ya shigo da gudu ya fad'a kan cinyar Aliyu, abin da ya jayo masa kwanciyar hankali har ya manta da abin da ya faru da shi.
TAFIYA MABU'DIN ILIMI
Kusan kwana uku gidan yana cikin rud'u da damuwa, Aliyu yayi k'ok'arin janye kansa da shiga cikin gidan, duk da akwai abinci sa daya kamata ace ya d'auka a cikin gidan, amman gudun abin da zaije yazo ya tattar ya hak'ura da shigar, sai dai bai bari Baffansa ya fahimci hakan ba, musu aikin gidan kaf babu wanda ya isa ya mik'o masa abinci saboda tsoron bacin ran Hajiya da 'yar ta, hakan ya sanya sai dai ya fita waje ya diya a boye yaci kasancwar Baffansa yana bashi kud'in kashewa da yake Tarawa.
Bayyanar takardar k'aro karatun Hanan shine abin da ya sauk'ak'a mata 6acin ran da take ciki tsahon kwanaki uku, ita kanta Haj. Bilkisu tayi mutuk'ar farin ciki har Alhaji Musa ya sami dariyar ta a ranar, kusan wani akayi ana shagali a gidan na farin cikin samun karatun Hanan uni6ersty of Birmingham inda ta sami karatu 6angaren (Business & Social Science) wannan abin yayi mutukar faranta ranta, cikin k'ank'anin lokaci aka kammala shirye-shiryen tafiyar ta, Alh. Musa yayi mata dukkan abinda take bukata hakan ya wanke laifin da ya aikata mata cikin zuciyar ta, daran dazata tafi ya sanya ta a d'aki ya fara yi mata nasiha mai shiga jiki.
"Hanan ke 'yatace danake k'auna fuye da kowa a wannan duniya"
Ta d'aga kai ta kalleshi da jin dad'in abin daya ambata, har saida ta kasa shuru ta furta.
[8/1 01:44] Zeinab Andiya Fox : "Daddy fiye da kowa kace fa har da Aliyu kenan?
Mammaki ya kamashi shi ya gyara zama yana murmushi a cikin ransa yasan har da kururuciya ke damun Hanan domin duka shekarunta basu wuce sha bakwai ba, sannan ga wauta irin ta 'yar fari ga kuma shagwa6a da gata da ta samu dags hannun mahaifiyar ta, koda yake shi kansa yana nuna mata k'auna tun tana k'aramarta, ya k'ara gyara zama ya shafi ha6arsa sannan ya fara Magana.
"Bari na gaya miki wata Magana Hanan a duniya babu abin da 'Dan Adam yafiso fiye da abinda ya haifa, su kansu iyayen mu suna sanmu fiye da son da muke musu wannan wata d'abi'ace ta 'Dan Adam, don haka ki sanya a ranki bazan so kowa ba fiye dake ba har abada, idan zanso wani soyayya irin taki sai dai idan yana da matsayi ne irin naki, ma'ana shima d'anane na cikina, amman soyayyar ki bazan yadda ta ta6a irin tarbiyyar danake son yi miki ba, Aliyu bawan Allah ne daya tashi babu iyayen sa bai san kowa ba, daga malamin sa sai mu, sannan yana k'ok'arin guurin ganin yayi mini dukkan abin da 'Da yake yiwa ubansa, hakan ya sanya na rike shi nima a matsayin 'Dana, idan har kika yadda Aliyu d'an uwanki ne wanda addini ya had'a ku sannan zama ya had'aku zaki zauna lafiya dani, sa6anin hakan ne kawai ke sanya ni samun.matsala dake, amman Aliyu baifi kiba Hanan ke 'yatace tacikina."
'Dad'i ya kara kamata cikin farin ciki tace "Nagode Daddy, naji d'ad'in wannan magana."
Alh. Musa yayi murmushi yace "Babu damuwa Hanan, abin danake buk'ata gareki shine kirik'e mutuncinki da rayuwarki, zan barki ki tafi k'asar nan karatu ne kawai don na yadda tarbiyyar ki, ban ta6a kamaki da wani aibin kaico ba tun daga k'uruciyar ki har zuwa yanzu, don Allah kici gaba da kasancewa akan yanda na sanki, karki sauya daga yanda na zoto diyata, kici gaba da rike mutuncin ki, zaki zauna a gidan abokina Ambasada Isa Babura wanda yake zaune acan da iyalansa, kiyi k'ok'arin d'aukar sa a matsayin mahaifin ki, hakan zai sanya ki sami abinda kike buk'ata, nana da sati uku idan Allah yakai mu, mun sami komai na tafiya nida Aliyu zamu tafi mukaiki...
Ta d'aga kai da mamakin jin an ambaci sunan Aliyu, amman hankalin mahaifinta bai kai kanta ba yaci gaba da bayaninsa, don haka ta maida kanta k'asa cikin k'aunk'uni a ranta.
A d'akin Haj. Bilkisu ta kama dire-dire irin na shagwa6a66un tana turo baki gaba, da mita akan tafiyar da aka ce za'a yi tare da Aliyu, Haj. Bilki ta k'uta cikin takici ta kad'a kai tana rantsuwa.
"Na rantse da Allah baza a yi tafiyar nan da shi ba, me Alhaji ya maida mune, ki barni da shi kawai."
Da magariba Aliyu ya shigo d'aukar abinci suka cikaro da Hajiya a Falo ya durkusa cikin ladabi yana gaisheta, ta kalle shi sama da k'asa a ranta tana fad'in.
1 · Like · React · Reply · Report · 15 January 2017
Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:44] Zeinab Andiya Fox : (42)
"Munafiki da wannan kasiye zuciyar mijina, amman ni baza yi tasiri a akai na ba."
Cikin gataali ta fara yi masa Magana dai-dai lokacin da ya mik'e domin ya kula bazata amsa gaisuwar sa ba, abin daya sanya shi fasa tashi ya tafi.
"Kaji labarin tafiyar Hanan k'sar Ingila karatu kuwa?
Aliyu daga kai yana fad'in 'naji Hajiya, Allah ya sanya taje a sa'a ta dawo da abin da ake fata."
Amin idan ma ba har ranka haka kake nufi ba, Magana nakeso muyj dakai, naji Alhaji yana son tafiyar da kai, inason kayi k'ok'arin janye kan ka daga tafiyar, domin Hanan bata buk'utar kabita kwata-kwata."
Mamaki da tsoro suka cika ransa, Allah ya sani yana k'aunar ace yau gashi a jirgi zaije k'asar waje, sai dai bai buk'atar duk abin da zai zama.matsala ga iyayan rik'onsa, don haka cikin sanyin murya ya fara Magana "Insha Allah zanyi k'ok'arin ganin na kaucewa hakan." Ya bata amsa cikin ladabi.
Tayi murmushi "™Na ji dad'in hakan." Ta wuce inda ta nufa shima ya nufi kicin kai tsaye.
Da daddare Alh. Musa suna zaune a falo shi da Hanan da Haj. Biki ya aika Hamza ya kira masa Sliyu, Aliyu ya shigo ya durk'usa ya gaida Haj. Bilki da Alhaji, Alahani Musa yayi murmushi yana kallon sa ya fara Magana.
"Ka taba zuwa k'asar waje kuwa Sliyu?
Aliyu yayi murmushi kansa a k'asa yana fad'in " Munje mana Baffa."
K'asar wajen? Haj. Bilkisu ta tambaya cikin mamaki.
"Eh ina nufin Nijir d gana da muka taba zuwa da Baffa ba. " ya bata amsa cikin sauri.
Alh. Musa ya fashe da dariya yana kad'a kai, Hanan kuwa baki ta ta6e cikin tsaki k'asa-k'asa.
"Lallai kaje k'asar waje Aliyu, to ba wannan k'asar wajen nake nufi ba ina.nufin yankin k'asashan turawa, nan bada jimawa ba idan Allah ya kaimu zamuje kai Hanan makaranta, gobe da safe zakaje ayi maka Passport sai a ssmar maka 6isa, na sanya a fara yi mini k'ok'ari don ganin an same su da wuri."
Hanan ta k'ara turo baki gaba cikin takaici, Aliyu ya kalli Alhaj yana murmushi "Baffa ka manta muna gab da fara jarabawar NECO, nana da sati uku zamu fara." Lokaci guda yanayin guskar Alh. Musa ya sauya zuwa damuwa, yayin dana Hanan da Haj. Bilkisu ya koma murmushi da jindad'in maganar Aliyu.
Alh. Musa yayi ajjyar zuciya cikin damuwa "Amman ban ji dad'in hakan ba, kodayake babu damuwa, akwai gaba sai a tafi dakai."
Wannan abin da Aliyu ya aimata ya faranta ran haj. Bilkisu har ta sauke kad'an daga dubin tsanar datake masa a cikin ranta.
[8/1 01:44] Zeinab Andiya Fox : An shirya tafiya, Hanan ta sami dukkan abin da take buk'ata na tafiya, sun rabu da mahaifiyarta cikin farin ciki, Aliyu ya kwashe su a mota zuwa air port, Hanan duk da bataso hakan ba dolenta ta hau gaban Motar, Alhajin da k'annanta suka hau baya, suna tafe suna ta hira tsakanin Alhaji da Aliyu da Hamza basu damu da itaba, ita kuwa sai cika take tana batsewa a ranta tana ganin sakewar da Aliyu ya samu tayj masa yawa a gidansu, har ya fita shak'uwa da k'annanta daya kamata ace tafi kowa shak'uwa dasu.
Sun isa filin jirgin cikin farin ciki yaran suka fara k'ok'arin yin rigima akan sai sun bi baban su, Aliyu ya fara rarrashin su da zai kaisu su hau lilo da mota da babur a gidan wasan yara, sannan zai musu shoping, da wannan ya samu ya shawo kansu, Alh. Musa ya kalli Aliyu yana murmushi yace.
"Aliyu ka kula da gidan da yaran, duk abin da Hajiyar take buk'ata ayi mata, Allah yayi maka albarka "
Cikin jin dad'i Aliyu ya amsa da amin, Alhaji musa ya fara shafa kan yaran, Hannan na tsaye tana kallon su, Aliyu yabita da kallo, a cikin ransa bai son irin mu'amalar dasukeyi ta rashin yiwa juna magana, Allah ya sani yana son ya dinga yi mata magana sai dai yanayin data d'auke shi ya sanya yake k'ok'arin kame kansa, don gudun wulak'anci ko kuma ya janyowa kansa damuwa, amman dai yaga rashin dacewar kinyiata sallama musamman a yanzu dazata bar garin, don haka cikin k'ok'arin rangwanta muryarsa yayi mata.magana.
"A dawo lafiya Hanan allah ya sanya a sami abin da a kaje nema cikin sa'a."
Kallon da Alh. Musa yayi mata ne ya sanya tayi k'ok'arin amsawa da Amin amman ciki-cikki, Slh. Musa yafara k'ok'arin tafiya, Hanan tabi bayansa cikin gaggawa, Hamza da yake shine mai wayo ya marairaice zai fara kuka Aliyu ya sungume shi daman Umar yana hannunsa d'aya cikin sauri yana fad'in.
"Lalala zan fasa zuwa Park d'in Hamza na."
Nan da nana Hamza yayi shuru cikin murna da jin dad'i Aliyu yabisu Alh. Musa da kallo sai yake jin wani abu game da tafiyar Hanan, shi dai bazai kira abin kewa ba domin babu wata shak'uwa dama a tsakanin su, amman kuma yasan ko babu komai su kan kalli juna ko daga nesane, yana zaton halin dazata samuu kanta da irin rayuwar dazatayi acan yake jimami, ttsahon lokaci yana kallonsu har suka k'ulewa ganinsa, ta6a kirjinsa da Hamza yayi yana fad'in.
"Yaya sweet". Shine abin da ya farkar dashi suka bar gurin cikin gaggawa, saida ya biya dasu inda ya ambata d'in sannan ya wuce dasu gida cike da tsaraba.
Hamza yana murna cikin gwaranci yake baiwa Momin su labarin inda Aliyu ya kaisu da nuna mata abubuwan daya sai musu.
A fili ta6e baki kawai tayk bata ce musu komai ba, amman cimin ranta cewa take "Meye abin burgewa kud'in uban kune, kome yayi muku ai bai buge ba.
1 · Like · React · Reply · Report · 15 January 2017
Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:46] Zeinab Andiya Fox : (43)
A 6angaren Aliyu sai ya tsinci kansa cikin damuwa da halin da Hanan zata iya shiga domin yana daga cikin wad'an da suka bayar da shawarar tafiyar tata, duk da bai san itace d'in zata bada farko, haka ya wuni suku har dare, sai dai a k'asan ransa yayi alk'awarin sanya Hanan cikin addu'ar sa taje tayi karatu ta dawo lafiya ba tare da wani abu ya ta6a tarbiyyar ta ba.
ILIMI GINSHIK'IN RAYUWA.
Aliyu ya sanya a ransa ba shi da wani gata ko galihu daya wuce ya nemi karatu, don haka ya dage yake yi d'in, kasancewar sa mai hazak'a da tsananinn kwazo, don haka da lokacin jarabawar WAEC ya yi ya dage da tsananin karatu, cikin ikon Allah kuwa sai gashi ya sami abin da yakeso, don haka ya zana jarabawar shiga jami'a wato (JAMB) cikin ikon Allah itama ya haye ta ya sami gurbin karatu a jami'ar Bayaro, Alh. Musa yayi mutuk'ar murna da wanna abin, sai ya zamto kamar yafi Aliyun ma farin ciki, a son samu Aliyu so yake ya karanci harkar kimiyya da fasaha kamar Likita ko mai had'a magunguna (Medicine) ko Pharmacy) ko wani abu daya shafi wannan harkar domin shine 6angaren daya karanta tun a sakandire, amman maganar da Alh. Musa ya furta ta shafe komai a ransa, domin ba yan ya nuna masa Makin daya samu na jarabawa sai ya kalleshi cikin farin ciki yace.
"ALIYU nasan kafi sha'awar karatun daya shafi harkar kimiyya da fasaha, amman ni nafi son kayi karatun dazai amfane ni, domin ni d'an kasuwa ne, kuma kainake kallo a matsayin babban d'ana da zai iya tallafa mini, don haka nake maka sha'awar karantar abin daya fi shafar harkar kasuwan ci."
Wannan kalamai na Alhaji Musa sune suka sauyawa Aliyu k'udirinsa, yaji yafi son yin abin da Baffan nasa zaiyi alfahari da shi, don haka sai ya d'suki 6angaren Business Administration ya fara karanta, hakan kuwa yayiwa Alh. Musa dad'i jwarai da gaske, ya malkawa Aliyu mota da sunan tashi ta kan shi, wannan abin ya tayar da hankalin Haj. Bilkisu har tagaza 6oyewar ta furtawa mai gidan, amsar daya bata shine kawai tayi hak'uri Aliyu ya riga ya zama d'ansu, domin bai san kowa ba sai su, ko malamin su sai yayi shekara bai sanya shi a idon sa ba, amman su suna tare da shi, idan basu kyautata masa ba mai ya kamata suyi masa.
Lokacin dayake maganar kallon sa kawai takeyi ta kasa furta komai, ba wai don bata da abin da zata futa d'in ba sai dan sanin kota furta maganar ba zata amfanar da ita komai ba, don haka ta hak'ura kawai, amman cikin ranta yana mata suya, ta rasa yanda zata iya raba mijin ta da Aliyu, hatta 'ya'yan ta gaza rabasu, don haka zuba ido shine kawai abin daya kamace ta.
Domin tayi iyakacin yin ta, ta sami shawarwarin da k'anwarta ta gwada amman kamar tana k'ara iza wutar abin ne.
Tunda Aliyu ya fara karatun sa bai ta6a samun matsala ta fad'uwar jarabawa wato carry o6er ko kuma yajin aiki ba, hakan ya sanya karatun ya tafiyar masa yanda ya kamata, sannan kuma Allah ya sanya ya sami aboki wanda ya zamto tamkar amininsa da suke tare, had'uwar su ta sanya ya k'ara samun cigaba cikin rayuwarsa.
[8/1 01:46] Zeinab Andiya Fox : Alh. Musa yana yawan zuwa duba Hanan wani lokaci ma har da.mahaifiyar ta suke zuwa, amman duk sanda Alh. Musa ya buk'aci tafiya da Aliyu sai ya kawo wani uzurin da zai hana tafiyar da shi, domin bai son abin da zai shiga tsakaninsa da Haj. Bilki.
Cikin wannan lokacin tinanin mahaifarsa da danginsa ya tsananta cikin ransa, bai san ina suke bai san waye shi ba, bai san ta ina zai samo su ba, kullum koda yaushe idan yaje gaida Malaminsu ya farayi masa maganar sai yace sunan Garin su kawai yake rike Garin Sam6auna bayan nan bai san komai akan shi ba, amman daga k'arshi ya yanke shawarar fara neman wanda ya san ko da sunan garin nasu ne.
Wani hutu da sukayi na zango karatu na biyu wanda daga shi zasu shiga aji uku ya yanke shawarar tafiya garin da malamin daya d'auko su yazauna har ya rasu, bai sanar w da mahaifin saba domin yana ganin kamar zai iya hanashi tafiyar, don haka ya shirya ya tafi a motarsa, kasacewar tafiyar ta wuni guda ce da yake k'suyukan Zariya ne.
Ya isa garin cikin sa'a yaci karo da 'Dan Malam Habu, tashin farko ya sanar dashi mahaifinsa yazo nema duk da ace ya rasu dajimawa, yazo ko zai sami wani karin bayani akansa.
Mal. Zakari shine ya gaji malaminsa gurin kiyar da almajirai, saidai shi baya tafiya d'auko almajirai kamar yanda Malamin sa yakeyi, kasancewqr zamani ya k'ara sauyawa sai dai iyayan yara sukawo masa.
Bayan gaisuwa da suka yi, Aliyu ya bayyana masa dalilin daya sanya yazo garin yana son jin a ina garinsu yake, wacce jaha ce sannan wacce local go6ernment ce, Malam Zakari ya kada kai yana fad'in.
"Bawan Allah wallahi bazan san ina bane, tabbas nasan Malamina yana d'auko almajirai lokacin da yana raye daga mabanbantan garuruwa da sunan su kawai nakeji a baki ban san su, kamar nima kawo masa ni akayi, sannan mutane irinka da suna yawai t zuwa tambaya ta musamman wanda ya bayar dasu g wasu malaman, amman bana sani, tabbas mutuwa tayi masa gaggawa bai sanar dayara da yawa ainihin su waye suba, wanda kaima yanzu ka zamto daga cikinsu, saidai kaci gaba da binkice har Allah ya sanya ka dace."
1 · Like · React · Reply · Report · 15 January 2017
Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:46] Zeinab Andiya Fox : (44) aliyu yayi shuru tsahon lokaci kansa yana k'asa yana tinani, zai tina wasu abubuwa na garin su irin mutanan garin da irin yanda suke magana, amman ba zai iya tina hanyar ba, ba zai iya tina ta ina ake shiga garin ba, hawaye ya gangaro masa mai ciwo, gashi nan da uwa da uba da dangi amman ya kasance tamkar maraya. Mal. Zakari ya k'ura masa ido cikin tausayawa

1 Comments On DA BAN SANSHI BA Book 1
avatar
fatima-1-5-8

4 months ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment