Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fashewa da kuka yana fad'in. "Ni ba zani ba baffa! Don allah ka barni, nibani son zuwa baffa! Sumaye ta d'uke kanta daga 6angaran da Alu yake tayi gurin mal. Beld'o kai tsaye ta durk'usa cikin girmamawa ta mik'a masa k'ullin kayan. Tun da ta fito lanto ke kallon ta da 6acin rai kamar ta rufe ta da duka, amman ta gaza furta komai, fuskar malam ta fad'ad'a da farin ciki ya mika hannu ya amshi buhun yana fad'in. Kin gani ko? Na sanar dake baza ta sa6a umarni na ba, nine mijin sumaye ninasan halin ta." Lanto tayi tsaki gami da yin hanyar d'kin ta da gaggawa, sumaye ta yunk'ura ta mike da kyar, lokacin da malam yayi kan Alu wanda keci gaba da kuka yana ja da baya. "Kayi hak'uri baffa, ka barni gurin Innata don allah! Kalaman da Alu ke furtawa kenan cikin tsananin kuka yana kuma ci gaba da ja da baya. Wani abu mai ciwo ya soki zuciyar mal. Beldo har yaji dama ya sani
[8/1 01:22] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Bai sanar da tafiyar alu gaban lanto ba, tabbas da ya janye ta ya sauya lokaci ba wannan ba, amman ina babu wata dabara yanzu dole sai ya tafi, ya nufi yaron dake ja da baya yana fad'in. Haba maisango na, ilimi abin nema ne, dukkan 'yan uwan ka suna can neman sa, shi na ke fatan ka samo, zaka dawo ka zauna da inna ka gaji da ganin ta a lokacin da ka zama abin alfahari watarana." Alu ya ci gaba daja da baya yana kallon innar sa yana kada kai, sumaye tana kallon shi hawaye na k'ok'arin zubo mata tana karewa, har zuwa sanda hawaye ya su6uce ya zubo, wannan shine abu na karshe da alu ya gani ga mahaifiyar sa wanda ya bashi damar juyawa yayi hanyar fita da gudu, mal. Beld'o ya bishi da sauri yana kwala masa kira. "Alu? Mai sango! Yaron bai juyo ba yayi waje da gudu, mal. Beld'o ya rufa masa baya cikin gaggawa, sumaye taja baya cikin rawar jiki ta jingina da katangar gidan ta kasa tana nish sama-sama, shi ke nan ta shiga uku, an raba ta da abinda ke sanya ta farin ciki, wannan itace ranar da take kokawa kanta da[8/1 01:23] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (12) rayuwarta, mai ya sanya al'umar su suka zabi raba uwa da d'an tane, mai ya sanya ba'a tambayar ra'ayin mahaifiya akan komai, shin itab ta da hak'k'i akan d'an tane, wacce irin rayuwa ce wannan, lallai tana ji a jikin ta wannnan ce ranar rabuwar su, wannan ce ranar da aka raba ta da d'an ta tana ji a jikin ta sun rabu kenan har abada, tana jin baza ta k'ara ganin sa ba, domin tana baiwa kanta mutuwa, idan da hali ace ta mutu yafi komai dad'i a gareta yanzu, domin tana rayuwa saboda Alu ne, kasancewar bata da kowa a wannan duniya, mahaifiyar ta tana haihuwarta ta fad'i ta mutu, a gurin kakar ta ta girma ta gurin uwa nonon ta tasha tarayu, tun daga wannan lokacin mahaifinta bai k'ara sumun lafiya ba, mutane da dama sun yi zaton samun lafiyar ya dangata ga k'ara aure ne, don haka aka matsa masa har ya k'ara auran, amman bai k'ara samun lafiya ba har zuwa sanda ya rasu shima, lokacin tana da shekaru biyu a duniya, hakan ya sanya bazata d'orar da komai na gatan iyaye ba, sai dai ta tashi abar k'auna gurin
[8/1 01:24] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Kakar ta, ta jiyar da ita dukkan dad'i, kwatsam tana shekarun 'yan matancin ta shabiyu itama kakar ta ta rasu, wannan ya fidda mata k'aunar komai na duniya, domin rik'on ta ya koma hannun kawun ta wanda matarsa ta kasance mara imani da tausayawa, hakan ya sanya da malam beld'o ya fito neman auran ta bata nuna k'in amincewa ba, domin tasan hakan ne gatan ta, duk da mutane da dama na ganin zaman gidan kawunta yafi rayuwar gidan mal. Beld'o amman a ganin ta hakan itace mafitar rayuwarta, anyi auran ta dashi, auran da bata ta6a d'orar da jin dad'in sa ba, domin ta sha wuya a cikin sa gurin abokiyar zamanta, kai tsaye ba zata ce mal. Beld'o yana azabatar da itaba, sai dai bubu wata kulawa ko wani abun tarairaiya cikin rayuwar gidan sa, a haka taci gaba da zama tana haihuwar abinda ke mutuwa, wanda jama'a da dama ke d'ora alhakin mutuwar 'ya'yan nata akan abokiyar zamanta, sai dai bata ta6a yadda da hakan ba, har zuwa lokacin da allah ya zaunar mata da Alu wanda dukkan fatan ta da rayuwarta dogara akan sa,[8/1 01:24] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (13) kuma yau gashi an raba su, tana ji ajikin ta irin rayuwar datayi ta maraici irinta d'anta ma zai yi. Lanto ta lek'o daga cikin d'akin ta, ta rik'e ha6a tana kallon sumaye wacce ke haki kamar zata sume a tsaye tana tana fad'in lkon allah? Wato idan kana raye zaka ga abubuwan mamaki, d'an guda daya tal da aka d'auka shine kike neman halaka rayuwar ki, allah yabani hakuri ni da aka kwashi 'ya'ya na har uku ban san inda suke ba tsahon shekaru, ban kuma ta6a damuwa ba saike mai guda daya, lallai kina da aiki. Tayi hanyar girken akuyoyi tana cigaba da dariya da shewa farin ciki ya cika zuciyar ta. Sumaye tabi ta da kallo, tana son tafiya amman k'arfarta ta kasa motsawa daga gurin, ta fara karanto addu'ar dake karantawa ko da yaushe wato fatiha da kulhuwallahu bata san adadin da takaranta ba, sai ta fara jin sauki da sanyi cikin ran ta k'afar tata ta saki a hankali ta yunk'uri ta nufi cikin dakin ta, amman har lokacin cikin ta da marar ta a d'aure suke tamau. Abin dake ranta bai wuce yaya aka kare da ALU da
[8/1 01:24] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Baffan sa ba, tasan halin mal. Beld'o babu abin da zai sanya ya sauya nufin sa, mutum ne shi mai magana daya, dukkan abin da zai faru bai girgiza shi kwata-kwata, a ranta taci gaba da yin addu'a ga kanta da kuma d'anta. A can waje tun da Alu ya zuba da gudu mal. Beld'o ya rufa masa baya, sai dai yana fita yaci karo da wani kato gungumen dutse ya fad'i k'asa kwance allah ya sanya bai ji mummunan ciwowa ba sai buguwar da babban yatsan k'afarsa yayi ya fara jini, mal. Beld'o ya iso gurin da gaggawa ya daga hannu a fusace ya wanka masa mari, yaron ya fashe da kuka sosai cikin fusata ya fara fad'a. "Kaga ja'irin yaro, ina binka kana gudu. Ya k'ara daga hannu da nufin k'ara marin sa, sai dai hango ciwon dake kafarsa ya sanyayar masa da gwiwa da sauri ya kamo kafar yana fad'in. Kai maisango kaga yanda kayi wa kan ka illah ko? Ya kamo kafar yaron da tausayawa, sai ya mufi ciyayin dake zube a gurin ya sanya hanun ya fisgo su ya mutsike a hannusa ya diga ruwan akan ciwon, kamar daukewar ruwan sama sai ga jinin ya[8/1 01:25] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (14) tsaya tsaf, alu har lnkacin yana ci gaba da kuka. Mal. Beld'o ya dafa kansa cikin lallashi bayan ya tsugunna a gabansa yana fad'i" daina kuka kaji maisangona, kasan ban son ganin kukan ka, wannan karatu da zaka tafi shne kawai gatan ka, idankaje can zaka gane abin dana ke son d'ora ka akai, watarana zaka zama babban mutum mai ilimin da zaka yi amfani da shi ba akan ka kad'ai ba har ga al'umma ma baki d'aya. Alu yayi shuru yana sauraran mahaifinsa, hak'ik'a maganar mahaifin sa ta shige shi, amman kuma abin dake ransa shine halin da innar sa ke ciki, don haka ya kasa hak'uri har sai da ya furta. "Baffa innata fa? Waye zai dinga d'ebo mata ruwa a rafi? Waye zai dinga iza mata wuta, waye zai dinga yo mata ice? Mamaki da tausayin yaron ya shige shi, wato duk gudu da yake yi shi ba yana yin don za'a dauke sg daga garin su zua wani gari bane kamar yanda sauran yara keyi, shi yana gudune saboda halin da zai bar mahaifiyar sa achki, ya k'ara dafa kan shi. Kar ka damu dukkan abinda kake mata zan sanya salame ta
[8/1 01:26] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Dinga yi mata kaji ko? Alu ya kurawa mahaifinsa ido kamar yana shakku akan abin da ya fad'a, mal. Beld'o yaci gaba da magana "kayi karatun da zan yi alfahari da kai maisango na, innarka tana nan a hannun ubangiji babu abin da zai same ta. Amman baffa kana ganin Salame zata d'ebowa Innata ruwa? Alu ya tambaya cikin fargaba. "Me zai hana ta zuwa Alu? Ai ni zan sanya ta, idan kuma batyi ba kasan bana wasa gurin bugun mutun ko? Alu ya d'ga kai alamar eh, mal. Beld'o yayi murmushi gami da fad'in yauwa yarona ta shi mu tafi maza kada mai tafiya daku ya tafi ya barka. Ya kama hannun yaron, Alu ya mike yana digisa k'afar suka nufi can wajan gidan mai gari, akwai yara da yawa wad'an daza'a tafi dasu can binni akwai na garin su da wanda aka kawo da mak'otan garin da kuma k'auyukan dake nesa da garin, wasu daga ciki yaraN suna cikin murna da jin dad'i wasu kuma suna kuka kamar Alu, mal. Beld'o ya isa gurin mai gari ya zauna, bayayan ya zaunar da Alu cikin sauran yaran, yaran da suka kasance abokan Alu suka fara
[10/25, 3:44 PM] H InnaπŸ§•πŸΌ: [8/1 01:26] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (15) fara tsokanar shi ganin yana kuka, kasancewar yana da zuciya ya sanya bai kula su ba, domin innar shi ta hana shi fad'a, saboda idan ya fara fad'a bai iya iya hak'uri sai ya jiwa mutum ciwo hakan ya sanya innarsa ke kwabar sa dayi masa nasiha akan yin fad'an shi ya sanya yakan daure kafin ya kula mutum suyi fad'a. Kusan awanni uku aka kwashe kafin a kammala hada yaran, sannan aka fara kokarin tafiya dasu, mal. Beld'o ya kamo hannun alu ya jashi gefe ya dafa kanshi yana magana cikin kwantar da hankali. "Kiyi karatu da yawa kaji Alu Maisango, kar ka yadda ka bi yaran banza kaji ko? Alu ya daga kai alamar to, amman har lokacin yana ajiyar zuciya, yaran suka yi bankwana da iyayan su da dangin su suka d'auki hanyar tafiya, domin sai sun yi tafiya zuwa babban kauyen dake bakin hanya wacce tafiyace ta kusan kilomita biyar sannan zasu sami dotar shanu da zata shigar dasu binni, wasu na kuka wasu na murna suka dauki hanyar tafiya. Alu yana tafe yana waigen garin su wanda shi kad'ai ya sani cikin abin da ya
[8/1 01:26] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Shafi rayuwarsa wato garin sam6una sai sunan baban sada innarsa, har suka kule mal. Beld'o yana daga masa hannu, yaron yana yin kuka amman irin na zuciyar nan sai ajiyar zuciyar da yake hakan ne kawai zai tabbatar maka da lallai kuka yake yi har suka bacewa ganin kowa suka nausa cikin jeji, suka dai na waigawa. Kasancewar sun saba tafiyar ya sanya ba su gajiya ba har suka iso ainihin babban garin nasu, motar amalanke tana jiransu aka watsa su cikin motar aka fara tafiya, Alu yana ta kallon garin su sai da motar ta tashi sannan ya fashe da kuka, ya had'a kai da gwiwa yana kuka, shike nan bazai k'ara ganin Innar sa ba, bai san inda za'a kai shi ba. Abokinsa Idi ya dafa shi yana kuka k'asa-k'asa shima kadaina kuka Alu, Inna tace mini acan akwai shimkafa da abubuwa masu dad'i, zamu dinga ganin talbijin irin ta gidan maigari a ko'ina, zamu dinga shan ruwan sanyi muci abinci mai dad'i, sannan tace mini sau uku suke garki acan ba irin garin muba. Dukkan bayanin da Idi yake yi bubu wanda ya shiga zuciyar Alu,[8/1 01:27] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (16) domin ba abubuwan da za'a taddane a ran sa ba tinanina halin da Innar sa ke ciki ne a ransa, amman ya rage kukun ya juya ya kalli Idi yana fadin. "Idi Innar ka tace maka zamu k'ara sumun wata Innar acan ne? Idi yayi shiru da rashin sanin amsar da zai baiwa abokin nasa, tabbas ko sun sami komai ba zasu sami uwa acan ba, don haka ya kad'a kai alamar a'a, Alu ya goge idon sa yana ci gaba da magana. Saboda bazan ga inna ta acan ba shi ya sanya nake kuka idi. Jikin idi yayi sanya ya jingina da karfen motar, Alu ya waiga ya k'urawa garin su ido wanda suke k'ara yin nisa, tun suna iya shaida garuwaruwan dake mak'ota dana su saboda zuwa biki ko aiken da ake musu har suka dai na shaida komai domin sun shiga cikin tskiyar daji, wasu sun yi bacci, wasu kuma idon su biyu, Alu yana daga cikin wadan da basu ko rufe idon su ba, domin yana ganin da ya rufe idon sa zai ganshi a wani gari, tinanin halin da Innar sa ke ciki a yanzu shine abin dake damunsa, Allah ya sanya ma ya d'ebo mata ruwa da safe a rafi ya cika mata
[8/1 01:27] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Dukkan mazubin ruwanta, sannan yayi mata kara wanda ta tura shi k'ark'ashin gadon ta, yayi murmushi da jin dadi cikin ransa, ko da salame beta debo mata ruwa ba zata kwana biyu tana amfani da wanda ya d'ebo mata. Sai gab da magariba suka fara isa cikin gine-genen binni, basu da suke ido biyu ba hatta masu bacci ma sai da suka farka, domin jin yanda sauran 'yan'uwa suke ihu da shewar ganin manyan gine-gine abin da basu taoa gani ba, su yara ne k'anana da yawan su basu ta6a zuwa binni ba, iyakacin su babban garin dake kewaye dasu wanda babu ginin bene ko daya a cikinsa, banbancin sa da garin su ginin bulo ne kawai, domin suna gine-gine da bululluka sa6anin k'auyen su wanda da bulon k'asa kawai suke yin gini. Sai da magariba suka isa cikin garin kano kano wanda nan ne inda yaji malamin nasu yana sanar dasu zai ajiye wasu, sai dai abin da ya bashi mamaki bai wuce ganin an fara sauke wasu daga cikin su a wasu makarantun ba, sai yaji malam Habu d'in na yana fad'in da kad'an zai tafi zai bar sauran nan, [8/1 01:28] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (17) domin shi can wajan zariya zaiyi, a can makarantar su take, cikin wad'an da aka sauke harda abokin sa Idi hankalinsa ya tashi kwarai da gaske sanda yaga an sauke Idi a wata makaranta, ya kalli mal. Habu cikin rud'ani yana fad'i. Malam don allah ka barni anan nima, ka barni tare Idi. Mal. Habu yayi masa dakuwa yana fad'in kaci gidan ku, kaine zaka sanar dani abin da ya dace nayi, kalli ya wan ku, ya yazan iya barinku guri d'aya, ni kaina bazan iya rike ku duka ba balle shi da zai mini alfarma. Haka aka wuce dasu yana hangen idi yana hawaye, dukkan abubuwan burgewa na binni da suka fara sanya su farin ciki yanzu sun daina burge shi yanzu kwata-kwata. Tafiyar su kayi tsakanin inda aka suke idi da inda suka kara tsayawa bubu nisa, ANSAMU MATSALAR SHAFI. Malamin ya kallesu da kulawa ya shafa kansu yana fad'in masha allah, kar ka damu malam habu zamu rik'esu kamar yanda ka bayar dasu za'a kula da karatun su insha allahu, ubangiji yataya mu rik'o. malam habu ya kad'a kai da gamsuwa yana fad'in amin summa amin.
[8/1 01:28] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Sannan ya sanya hannu cikim aljihunsa ya mik'awa malamin, ya kalli su alu yana murmush. To yara ayi kartu sosai, idan lokacin saduwar ku da iyayan ku yayi zanzo na d'auke ku kowa ma kai shi ya gansu, baku da kowa anan sai wannan bawan allah. Ya nuna mal. Sadau da hannusa muza mu wuce sai allah ya k'addara saduwar mu kuma malam. Rabe ne ya iya amsawa da amin alu kam bin sa yayi da kallo idon sa na zubda hawaye yana rumgume da buhun kayan sa, har mal. Habu ya jiya ya fara tafiya ya nufi motar dake tafe dasu kai tsaye ya shige, mal. Saudau ya kalle su. "Yaya sunayen ku yake ne? Rabe ne ya fara fad'ar sunan sa sai alu shima ya fad'i nasa, ya girza kai da gamsuwa, yana fad'in to daga yau nine baban ku kuma babar ku, dukkan abin da ya dame ku ni zaku gayawa, zaku kai kayanku waccan rumfar ku sami guri ku ajiye ta, annan zaku dinga kwana, tun da asuba ake fara karatu idan gari yayi haske sai ku fita ku samarwa kanku abin da zaku karaya, wajan k'arfe goma na safe zaku fara zama karatu sai k'arfe d'aya zaku fita bara
[8/1 01:29] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (18)

Nan ma zaku samu abinci rana karfe hud'u za'a k'ara zama a makaranta sai karfe shida za'a tashi, bayam karfe tara na dare za'a kara zama sai karfe goma shad'aya za'a tashi idan ba'ayi ruwa ba kenan, idan kuma anyi ruwa ba'a karatun dare, duk karshen sati kowa zai kawowa malam kudin laraba, watarana kuma za'a tafi gona ta can bayan gari ayi noma, ai daman kun iya noma ko?
Gabadaya suka amsa da eh yayi murmushi daidai lokacin da aka fara kiraye-kirayen sallahr magariba " yauwa maza ku tafi ku ajiye kayan naku ku d'auro alwala ku wuce masalaci kuyi sallah.
Ya wuce da sauri ya fara tafiya suka bishi da kallo Rabe ya fara tafiya "Zomu tafi mana. Rabe ya fara tafiya Alu yayi tsaye kamar bazai motsa ba sai kuma ya fara tafiya yabi bayan Rabe, har suka isa cikin rumfar, Rumface da aka rufe saman ta da kwano sannan aka zagaye ta da katakwaye, amman guraren da yawa sun cinye don haka aka toshe suda tsummokaran kayan almajiran, akwai akwatina zube da buhunan da gana must go a gurin, k'aton guri ne da kusan mutum hamsin zasu iya kwanciya,
[8/1 01:29] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Akwai wasu almajiran wad'an da basu tafi masallaci ba, akwai tarin alluna a gurin da yawa, Idi da Alu suka k'arasa suka tsaya suna karewa gurin kallo, yaran da suke cikin gurin suka bisu da kallo, wani k'olo ya iso zai shigo ya tsaya yana kallon su sai ya kaiwa k'eyar Alu duka yana fad'in " kuwuce mana kuyisami guri ku zauna.
Alu yayj taga-taga kamar zai fad'i amma bai fad'in ba, Rabe ya wuce da sauri ya sami guri ya zauna, Alu ya isa ya zauna a kusa da shi, abu na farko dake damun su shine yunwa gashi ance zuwa zasu yi su nemo abincin dazasu ci, suka tsaya suna kallon kowa yana harkarsa, wani daga cikin almajiran wanda bai wuce shekarun su ba ya k'arasa ya zauna a kusa dasu yana fad'in.
Sannun ku, yanzu aka kawo ku? Suka daga masa kai alamar eh, yayi murmushi yana fad'in "sunana Isa kuna jin yunwa ko? D sauri suka k'ara daga masa kai alamar eh, azaton su abinci zai ce musu gashi amman sai suka ga ya k'ara murmushi yaci gaba d magana. Sanda aka kawoni nima haka naji yunwa kamar zanmutu gashi bansan kowa ba,[8/1 01:29] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (19)
Kuma bani da ko kwabo haka na kwana da yunwa ban san daga zuwan mutum zai fara bara ba, nayi tsammanin wanine zaizo yabani, idanzaku bara ku taso mu tafi.
Alu yayi jagale yana kallon yaron, Rabe ya mike da sauri yana fad'in "Taso muje.
Suka mik'e da sauri, Alu ya kalli kayan Rabe sannan ya kallesu.
"Kayan kaka kuma fa? Ya tambayi Rabe "meza'ayi d kayansa, kaima ka aniye naka anan babu wanda zai d'aukar maka, baka ga kayan mu anan gurin a ajiye ba muma. Yaron ya bashi amsa ya nufi wani gurin wani buhu ya bud'e ya d'auko roba k'ok'on bara ya kifa akansa, ya kalle su "ku taho mu tafi.
"Amman bamu da kwano famu. Rabe ya sanar dashi. Kuzo muje mu samo a can sai ku dinga yi da barar kwano idan muka shiga gida." Suka kad'a kai suka bishj a baya, har lokacin Alu ya kasa sakin jikin sa, tinanin Innar sa yana dumun sa a ransa, yana jin dama ya sani daya tsaya sunyi sallama bai falla da gudu ba, ya taho bai yi sallama da ita ba.
Jama'a suna ta sallah su kuma suna yawon bara, tun da suka fara tafiya garin ya fara had'ewa da hadari aka fara iska, Isa ya kallesu yana fad'in.
[8/1 01:30] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Kunga hadari ya had'o gashi ba'a samun abincin a irim wannan lokacin da sauri, nizan dinga shiga idan na shiga gidan faruko kai sai kashga na biyu kai kuma ka shiga na uku. Yan magana yana nuna su, suka amsa masa da daga kai alamar to, haka d'in suka fara yi sai dai bai fi gida uku suka shiga ba aka fara ruwa, isa yafito daga gidan da yake da gudu yana fad'in ku tuho mu koma kada ruwa yayi mana duka. Ya fara gudu suka rufa masa baya suna gudu, suna gudu ruwa yana k'aruwa, har suka isa rumfar su suka shige, abin da ya basu mamaki bai wuce ganin rumfar ta cika da mutane ba, kowa yana neman gurin kwanciya, ga ruwa yana shugowa ta gefe da gefen rumfar, Alu da abokansa suka fara k'ok'arin neman gurin daza su raba su kwanta, sai dai abin ya faskara domin duk inda suka raba sai a hankad'e su, daga k'arshe Rabe da Isa suka sami gurin suka ra6a amman Alu bai samu gurin kwanciya ba sai can karshen bakin kofar ya samu ya rabe amman gurin bai isheshi kwanciya ba sai zama yayi, rabin k'afafunsa ruwa na fesowa suna jikewa
[8/1 01:30] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (20) haka ya zauna shuru yana karewa daran ubangiji kallo. Acan kasan zuciyarsa tinanin innarsa yake yi, kota kammala abincin dare, ko ta sami wanda ya iza mata wuta, ko a wane halitake yanzu, wannan shine abin da ya sanye bai jin dukan ruwan dake sauka a rabin jikinsa, har zuwa sanda bacci ya d'auke shi. Ya waye gari asuba tayi an fara tash cikin gaggawa kamar masu shirin zuwa lahira, wasu na nufar gidaje barar ruwa domin basu da ruwan sai sun bara tukun, wasu kuma na tsugunnawa gaban ruwan da ya taru cikin dare suna alwala da wanke bakuna su, shi kam ba zai iya amfani da ruwan k'asan ba, ga shi kuma bashi da robar dazai barato haka ya zauna shuru har aka fara karatun asuba, babu sallah balle wanke baki shima ya shiga sahun karatun, sai dai yunwa ta sanya shi bai fahimtar dukkan karatun da ake masa, ga kuma tinanin innarsa, wannan itace rayuwar da mahaifinsa ke sanar da shi zaiyi mai dad'i a binni, shi dai baiga wani abin dad'i cikin wannan rayuwa bayan bak'ar wahala ba, yana zaune yana karatu yana kuka,
[8/1 01:30] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Yana jin kamar ya gudu ya koma gurin innarsa wacce bai san halin datake ciki ba a yanzu, amman yasan babu hali yin hakan domin bai san inda zai bi ya sadu da garin suba. AKWANA A TASH... Wata guda ya k'are ga Alu, dukkan yanda yaso ya saba da wannan rayuwar ya kasa, idan akwai abin dake wahalar da rayuwarsa bai wuce rashin abin da zai ci ba, da yake damuna ce mutane masu gidajan kan su ma suna fama gurin samun abin dazasu sanya a bakin salatin su balle almajirai, sai dai ya fara sabawa da rayuwar wahala da kwarzaba manyansu da jama'ar gari, ya fara fahimtar karatun sosai, ya fahimci dalilin da yasanya mahaifinsa ya dage ya taho, wato idan mutum yana jin matukar yunwa yafi dagewa yayi karatu, amman a wani 6angaren yana ganin kamar bashi da gata. yau an wayi gari cikin mamakon ruwa daya hana kowa fita, hatta kasuwa a ranar ba'a cita cikin dadin rai ba, domin mutane da dama sun yi zaman su cikin gidajan

1 Comments On DA BAN SANSHI BA Book 1
avatar
fatima-1-5-8

4 months ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment