Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana da sha'awar k'ara aure ba, yaje gidan sa ya gaida shine ya sanar da shi.mutuwar matar sa a take anan ya bashi damar auren d'iyarsa Bilkisu, lokacin da mahaifinta ya bayyana mata Alh. Musa ya sami karbuwa a gurin Haj. Bilkisu
[8/1 01:40] Zeinab Andiya Fox : Karancewar yana da abin hannunsa kuma burin mahaifiyar su bai wuce ganin 'ya'yanta sun auri mai kud'i ba domin sun zamto farare irin ta sadakar yalla, bayan ya zauna da iata tsahon shekaru bai sami kaso hamsin daga cikin halin matarsa dari da ta tarasu ba, hakan bai sanya yayi sha'awar k'ara aure ba domin baya cikin tsarin sa, duk da dangin sa suna ganin ya kamata ace ya k'ara aure domin shi mutum ne mai wadata sannan kuma matar tasa ba haihuwa take yi akai-akai ba kamar yanda suke fad'a, amman yak'i yadda da hakan, haj. Bilki tasan idan ta matsa da yawa zai iya tura ta gidan su ko da bai sake ta ba, wanda hakan na nufin cikar burin dangin mijin nata na k'ara auran sa, shi ya sanya ta yadda a fili zata aikata abin da ya sanyata, amman a k'asan ran ta ta amince zata yi ta wulak'anta alu har yaji gidan ya fita daga ransa ya gudu don kansa, domin bata k'aunar kowa ya ra6eta balle kuma ace wani almajiri, tun bayan rasuwar mahaifiyar mijinta tak'ara mik'e kafa cikin gidan bata fatan kowa ya ra6e ta daga ita sai
2 · Like · React · Reply · Report · 14 January 2017
Abubakar Sadeeq replied · 1 reply
Zeinab Abdoul-karim
Idan ya tadda su suna ci, ranar daya fara gayyatarsa cin abinci a cikin su ran Haj. Bilkisu ya 6aci a aganinta yaya zasuci abinci da almajira sai da Alhaji Musa ya nuna mata Alu yana da tsafta, amman bata saurare shi ba ta karkad'e hannuwanta ta tashi, gani haka ya sanya Hanan m ta fara yunk'urin tashi Amman Alhaji Musa ya doka mata tsawa yarinyar ta koma ta zauna jikinta yana rawa kasancewar bai saba yi mata haka ba, wannan ya harxuk'a Haji. Bilkisu ta tsaya cikin bacin rai bata san itama zai koma kanta ba, ya koma kanta da fad'a tamkar zai kai mata duka, tayi k'ok'arin maida martani amman bai bata dama ba, haka tanaji tana gani Alu ya zauna Alh. Musa ya zuba masa abincin ya fara ci, ta kalli d'iyarta Hannan dake zaune amman ta kasa cinabincin saboda kyan-kyamin Alu datake yi, duk da yaron ya kasance cikin tsafta amman su basu ganin hakan, domin tsanar a cikin ransu take, tayi tsaki ta shige d'akinta a fusace.
Tun daga wannan ranar kowacce safiya idan ya iso gidan da shi ake cin abinci safe, Haj. Bilkisu tayi k'ok'arin nuna matsayin ta na matar gida ta yiwa mijin nata bore amman ya nuna mata bata isaba, yana ganin Aliyu kamar d'an sa jininsa Abdul da ya rasu, don haka itama ta sanya hakan a ranta ta yadda Aliyu nasu ne har abada, ta hak'ura d'in tana yin hakan amman idan rana tayi ya iso gidan ta kanyi kamar ta shak'e shi ya mutu ta huta, bata bashi irin abincin dasu ci sai dai ta bashi wani kala daban, Hanan kuwa bata k'aunar ko kusa da ita ya matsa ta dinga ja da baya tana toshe hancinta, hakan yana cutar da shi amman babu yanda ya iya dole ya hak'ura tun da yana samun abincin da zai ci.
Amman watarana daya fuskanci bazai iya jurar wulak'ancin ba ya sanya ya janye k'afarsa har tsahon kwanaki biyu, domin an shekara babu wani sauyi sai k'aruwa da abin yake yi kullum, sai dai Alh. Musa bai bar fishin nashi yayi nisa ba yaje har makarantar su yayi masa fad'a gami da gargad'in shi da kar ya k'ara k'in zuwa, duk abinda akai yi masa ya sanar dashi wannan ya sanya ya hak'ura ya kasance cikin rayuwar gaba Kura baya Sayaki.
RAYUWA JUYI-JUYI.
Alu ya wayi gari ya zamto yaro mai mutok'sr gata a gurin Alh. Musa yana wayo yana k'ara fahimtar irin k'sunar da maigidan yake yi masa dakuma irin yanda matar gidan da d'iyar ta suka tsane shi, amman haka bai dame shi ba domin komai Alhaji Musa yana yj masa kamar d'an sa,
1 · Like · React · Reply · Report · 14 January 2017
Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:40] Zeinab Andiya Fox : (36)
Yana zuwa makarantar su karatu ne kawai, amman kayan sawar sa da dukkan abin da zaici Alh. Musa ne yake yi masa, a hankali ma sai ya fara kwana a gidan Alh. Musa ya bashi d'aki, wannan ya k'ara kusanta shi da Alhajin duk wani abu da d'an gida zaiyi Aliyu ne yake yi, domin Alhaji yace sunan sa Aliyu ba Alu ba, a hankali tinanin Alhaji ya fara fad'ad'a ga sanya Aliyu a makarantar boko domin malamin su ya yadda dashi a wannan karon har ya sallama masa dukkan lamuramsa musamman da yake Alh. Musa mutumne mai ihsani yana yawan yiwa Malam Sadau kyauta, har ya wajabtawa kansa bashi kud'i duk karshen satin musulunci wato ranar Juma'a wannan ya sanya Malam Sadau d'iin k'ara sakakancewa da Lamarinsa.
Tinanin Alhaji ya fara ne lokacin da ya tadda Alu ya la6e yana kallon Mai yiwa Hanan lesson yana yi mata shi kuma Alu d'in yana saurara, da kansa ya fuskanci lallai yaron yana sha'awar abin, don haka ya shawarci malamin su akan zai sanya shi a boko idan yaso sai ya dinga zuwa karatun yamma, malamin yayi maraba da wannan sha'awara, amman a 6angaren Haj. Bilkisu taji abin banbarakwai amman batace komai ba, domin tasan ko ta tanka ba wani tasiri zatai yi ba, amman a 6angaren Hanan sanda taji baban ta zai sanya Aliyu a makaratar su abin ya k'ona mata rai, domin a hankali tsanar Aliyu ke k'ara karfi cikin ranta musamman da mahaifiyarta ke k'ara nuna mata irin yanda yaron ya shige cikin rayuwarsa, amman lokacin da aka kai shi makarantar taga ankai shi aji d'aya taji dad'i sosai, domin a lokacin tana aji hud'u ne ita, Alh. Yaso su k'ara masa aji fiye da haka domin lokacin shekarunsa shad'aya suka ce wannan ajin shine dai-dai da karatunsa indai karatun akeso yayi, wannan ya farsnta ran Hanan tadawo gida tana dariya cikin farinciki gami da sanar da mahaifiyarta abin da ya faru, har tana fad'in "Momy idan kika ganshi a aji sai kinyi dariya domin yafi kowa girma, wai primary 1"
Haj. Bilkisu ta dinfa dariya, har Sliyu ya shigo cikin gidan suna yi masa dariya da tsokanarsa, bai ta6a damuwa ba, domin yakan danganta abubuwan da suke masa da wanda yayyan sa da suku uba d'aya da kuma matar Babansa keyi masa, sai dai da yawan lokata musamman idan ya sanya abinci mai dad'i a gabansa zaici sai ya dinga tino Innarsa, shekaru kusan uku da wani abu kenan rabon sa da ita bai san a halin datake ciki ba, kota rayu ko ta mutu bai sani ba, bubu wanda zai bashi wani labari akan yanda rayuwar iyayan sa da 'yan'uwansa tak'are.
[8/1 01:41] Zeinab Andiya Fox : SHWKARA KWANA
Kamar yaune Aliyu ya fara shiga cikin rayiwar gidan Alh. Musa sai gashi har shekaru sunja, a wannan lokacin Hannan ta kammala makarantar sakandire school yayin da Aliyu yake aji Hud'u n makarantar sakandire da yake yasami tsallaken aji d'aya.
A kuma cikin shekaraun Haj. Bilkisu ta k'ara haihuwar yara buiyu dukkan su maza, d'aya shekarar sa biyu d'ayan kuma watanninsa shida, haihuwar da tazo musu cikin bazata da mamaki, a wannan lokacin kuma sun sauya gida daga wancan sun koma sabon gida, domin arzikin Alh. Musa ya k'ara ha6ska, ya zamto shahararran d'an kwangila yanzu, aikin da ya fara bayan ya ajiye aikin gwabnati, to yanzu kwangilar tashi ta ha6ska da gwabnatuci yake yi ya gina babban kamfanin kwangilar.
'Dakin Aliyu daban ne cikin gidan domin Alhaji ya gina masa katon d'ski a 6angaren yaran gidan wanda a turance ake kira boys k'uarters, wannan ma yana daga cikin abin da ya k'arawa Alu bsk'in jini a gurin Haj. Bilkisu amman bai ta6a kallon hakan a wani abu na gazawa ba, domin yanzu ya yadda ba shi da kowa sai su, kasancewar Malamin su daya kawosu bai dawo ba sai labarin rasuwar su akaji, shi kuma Malam Sadau bai san asalin garin su ba bayan sunan garin, saii dai duk da sun bar unguwar bai daina zuwa makarantar d'aukar karatu ba.
A 6angaran Hanan kuwa ko kallo ma Alu bai ishita ba a yanzu balle ta kula shi, idan har Magana ta had'su sai wacce ta kasance ta dole ce, yaran gida Hamza da Umar suna mutukar k'sunar Aliyu domin kusan a hannunsa suke rayuwa, duk da Haj. Bilkisu bata k'auna amman bubu yanda ta iya domin yaran sun tashi da k'aunar Maza a jininsu kamar yanda wasu yaran keyi, ita kuma batason raino koda yaushe suna hannun masu aiki, da wannan damar Aliyu ya samu ya shak'u dasu, hakan ya sanya tana ji tana gani ta dinga kyale su ga Aliyu.
Hakan ya haifar musu da shak'uwa fiye da takowa, idan basu tare da Aliyu to tabbas yana makaranta ne ko kuma yana bacci, domin Hamza ma har bacci suke tare, tunda tare da masu aiki yake kwana, wannan ya sanya dhak'uwarsu ta kuma ksruwa, hakan yana faranta ran Alh. Musa dpmin Aliyu ya zamto kamar d'ansa na fari daya rada cikin rayuwar sa, tun Haj. Bilki tana ganin zata iya ganin Bayan Aliyu har ta hak'ura tasare.
1 · Like · React · Reply · Report · 14 January 2017
Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:41] Zeinab Andiya Fox : (37)
A wanan shekarar Alh. Musa ya samarwa Hanan gurbin karokaro karatu a k'asar waje a jami'ar Birmingham ( Birmingham City Uni6ersity)
Wacce ke k'asar Ingila zata karanci digirinta na farko akan Business & Social Science, da fari Alh. Musa bai son karatun Hanan a k'asar waje amman saboda dagewar da mahaifiyarta tayi akan hakan, a cewarta wai dukkan 'ya'yan danginta da k'awayanta a k'asashen waje suke karatu, Alh. Musa yaso tirjewa amman wata hira dasu kayi da Aliyu, fomin ya zamto abokin hirarsa ya sanya ya sami kafin gwiwar daya zamto dalilin amincewarsa.
Suna tafe cikin mota sun dawo daga siyayya, Aliyu yana jan shi a mota yana zaune daga gefensa domin kusan shekara d'aya kenan da Aliyu ya iya mota ya zamto yana tuk'a Alhaji
Wani lokacin, da xuwa dukkan wasu buk'atu na gidan idan direba baya nana.
Aliyu yana tuk'in a hankali domin bai son gudu idan yana tare da Baffan nasa, Alh. Musa ya kalleshi cikin nutsuwa yana fad'in.
"Aliyu ka taba jin labarin yaran da sukw karatu a kasashen waje?
Aliyu ya d'an kalli Alhaji ya daga kai yana fad'in "Na sha jin labarin su Baffa."
Alh. Musa yayi murmushi sannan yaci gaba da Magana "Mekaji game dasu." Hankalin Aliyu yana kan titi yaci gaba da bayani" Akwai abokaina da muke karatu dadu suna maganar 'ya'uwan su dasuke karatu a k'asashen waje, suna cewa karatu can yafi na nan kyau da nagarta da kuma kula, sannan ba'a fiye fad'awa jarabawa acan ba."
Alh. Musa ya kad'a kai cikin jin dad'i "Bayan wannan babu wata illa dakaji suna fad'a kan kasancewa acan?
Aliyu ya kad'a kai alamar A'a ya d'ora da cewar "Ban jiba Baffa."
Alh. Musa yayi murmushi cikin jin d'adi "Hanan da mahaifiyar tane suka dage akan suna son Hanan d'in ta fita k'asar waje yin karatu, cikin rai na ban buk'atar hakan domin ina gudun abubuwa da zasu iya faruwa ga tarbiyyar ta, sai dai maganganun daka fad'a yanzu sun k'ara mini kwarin gwaiwa har naji zan iya yadda ta tafi d'in."
[8/1 01:41] Zeinab Andiya Fox : Gaban Aliyu ya ysnke ya fad'i domin da yasan akan Hanan ne da bai bayar da wannan shidar ba, shi labarin da ya sani akan mazane ba mataba, idan har akan mata ne bai san komai ba, sai dai bashi da damar da zai k'ara yin wani bayani bayan nan, amman cikin zuciyar sa baiji dad'in hakan ba, domin yasan Hannan yarinya ce mai rawar kai tsiya, fitar ta k'asar waje xsi iy haifar da komai a rayuwar ta, amman zai iya haifar da komai a rayuwar ta, smman zai yi k'okarin taya mahaifinta da addu'ar samun nutsuwar ta har k'arshen rayuwarsa wannan alk'awari ne ya d'aukarwa kansa.
Sun isa gida suka ci karo da Hannan ta fito cikin shigar k'ananan kaya taci kwalliya akwai alamun unguwa zata je da karamar jaka a hannunta irin ta 'yan mata, tun daga cikin mota Alh. Musa ya hango ta, yayi murmushi cikin farin ciki dai-dai lokacin da suka tsaya da motar Alh. Musa ya fito daga motar yana murmushi ya nufeta.
Hanan ina xuwa haka? Hanan tayi murmushi "daddy zan fita gidan Birthdah d'in Fadila ne, na kuma fito direba ya fita."
Dai-dai lokacin Aliyu ya fito daga cikin motar bai tsaya ga hirar dasu keyi ba, domin bashi da muhalli a cikin ta musamman daya kasance hirar da Hannan ne, idan yayi k'ok'arin tsoma kansa za ta iya gaya masa abin da zai jima yana sauya a ransa, don haka ya zagae su zai wuce dai-dai lokacin da kunnensa ya jiyo masa sautin Alh. Musa yana fad'in.
"Kinyi sa'a ga Aliyu nan sai ya sauke ki."
Ya kalli Aliyu dake k'ok'arin nufar shashinsa ya kwala masa kira, Aliyu ya waigo gami da amsawa sannan ya jiyo.
Hanan ta had'e fuska tana fad'in "Daddy nima zan iya tafiya dakai nafa."
Slh. Musa ya kada kai yana murmushi da fad'in "Kai san ban son hawan titi, bayan haka ma hannun ki bai fad'aba, sai nan da shekaru biyar xan iya sakar miki mota"
Ta waro ido cikin furgici tana fad'in "Daddy shkara biyar." Ta buga k'afa irin na shagwababbun yara tana ci gaba da Magana "Haba Daddy na riga shi fa koyan mota, sannan na fishi sanin abubuwan da suka shafi mota, amman shi an bashi famar ya tuka ni kuma ace wani bazan tuk'a ba".
Aliyu ya kalleta yana murmushin takaici bai san me ya sanya Hanan bata son ambaton sunan saba, koda yake ya kula yana daga cikin rainin da tayi masa, shi kuwa Alh. Musa fashewa yayi da dariya cikin mamaki yana fad'in.
[10/25, 8:30 PM] H Inna🧕🏼: Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:42] Zeinab Andiya Fox : (38)
"Hanan kinsan shekaru nawa Aliyu ya bsk? Bayan haka ma shi namiji ne ke kuma macece yaya zaki had'a kanki dashi?
"Au namiji yafi mace kena Daddy? Ta urgawa mahaifinta tambayar data k'ara sanya shi dariya, shi kuma Aliyu ya baza kunne don jin amsar da Slhajin zai bats.
"Nsmiji yafi mace juriya da himma, sannan kuma shi shugaba ne akan komai." Ya bata amsa.
Ta tabe baki tana kad'a kai tace "Daddy wasu matan fa sunfi maza ilimi da k'ok'ari, ko baka san haka ba?
Maganarta ta doki kirjin Alyu har saida ya kalleta, wacce bata kallon ko kusa da inda yake ma, kasancewar bai isaba a gurin ta, Alh. Musa ya kuma fashewa da dariya "Hanan kenan yanzu dai muna Magana akan yanayin halitta ne, idan kin dawo sai mu d'ora domin yanzu nagaji."
"Amman Daddy ka bari kawai zan jira direba."
"Aliyu ne zai kaiki." Slh. Musa ya fad'a yana had'e fuska, alamar dole ta yadda da abinda ya fad'a.
Ta turo baki gaba kamar zata fasa kuka, Allah ya sani bata son duk abin da zai had'a ta da Aliyu, amman tasan tunda Daddy d'in ta yace haka bata da damar d'aga abin, don haka ta nufi motar kawai ta kama murfin motar na baya da nufin bud'ewa.
"Yaya zaki shiga baya ki koma gaba ki zauna, ko kin manta Aliyu ne ba direba ba?
Alh. Musa ya sanar da ita sanda take k'ok'srin shiga gidam baya.
Ta waigo ta kalle shi da mamakin jin abin da yace, a zuciyar ta cewa take yi waye Aliyu, me yafi direba dashi, amman a fili saita kasa cewa komai ta tsaya tana kallon Mahaifin nata, Alh. Musa ya k'ara maimaita abin da yace "ki koma gaba ki zauna nace ko Hanan."
Hanan ta kama k'ofar gaban motar ta shiga tana k'unk'uni, Alh. Musa ya juya ya kalli Aliyu dake tsaye yana sauraran su.
"Aliyu ku tafi mana, sai dai kaci gaba da hak'uri da halin mutuniyar taka."
Aliyu yayi murmushi yana fad'in "Babu damuwa Baffa".
Ya nufi motar ya bude ya fara k'ok'arin shiga, Alh. Musa ya kad'a kai yana murmushi ya nufi cikin gidan.
Aliyu ya tayar da motar ya nufi hsnyar fita, sai dai tsakin da Hanan keja ke k'ona masa rai, Allah yasani yana da wsta irin zuciya daba komai yake jurewa ba musamman tsaki, tun yana yaro baya son tsaki kasancewar mahaifiyar sa ta sha gaya masa tsaki alama ce ta raini da wulakanci, amman daya tuna waye shi sai ya fara kokarin tausar zuciyar sa.
[8/1 01:42] Zeinab Andiya Fox : Hanan data ke zaune tana kumbura kamar zata fashe ta maida kanta tana kallon wundo cikin bacin rai, can ta bud'e jakar ta tadauko wayarta tafara danne-danne a cikin wayar.
Aliyu bai kallon ko 6angaren datake, sai dai yana tafiya ne batare daya san inda zasu je ba, ita bata ce g inda zasu ba shima bai tambayeta ba har suka yi tafiya mai nisa bisa titi, kowa na shak'ar kamshin sa, Aliyu yayi rawul ya koma d'aya hannu yaci gaba da tafiya dayaga babu sarki sai Allah sai ya sanya hannu ya kunna rediyon dske jikin motar, Hanan ta k'ara k'ufula ta sanya hannu ta kashe tediyon sannan ta kalleshi ranta a bace tana magans
"Kai ba zaka iya tambayar mutane inda zasu bane?
Aliyu ya waigo ya kalle ta yayi dan yak'e gami da fad'in "Oh Sorry! Na manta."
Yanayin yadda yayi maganar ya k'ara k'ular da ita taji kamar ta wanka masa mari, amman sai ta kau da kanta gefe rana huci cikin ranta.
Ina zamu je ne?" Muryar Aliyu ta daki dodon kunnenta.
Ba tare da ta kalle shi ba tace " Lamid'o Crsent layin Mai yari, House No. 10."
Ya kad'a kai yana murmushi "Mun baro hanyar ma a baya kenan." Ya k'ara yin rawun ya juya d'aya hannun, bata k'ara ce masa komai ba taci gaba da chatting d'in da take yi, shi kuma yaci gaba da tuk'i yana son ya k'ara kunna rediyon amman baya son k'ara junyowa kan sho Magana, bai ce mata k'ala ba har saida ya isa k'ofar gidan yaja ya tsaya ya kalleta bata kula da sun iso ba.
"Mun iso, koba nan bane ba?
Yayi mata Magana cikin kaushin murya, Ta daga kai da sauri ta kalli k'ofar gidan, msmakin yanda ya gano gurin ya cika ta, lokuta da dama takan yi mamakin basira irin ta Aliyu amman takan bar abin a zuciyar ta bata gaya masa ba, domin bata son ya gano shi wani ne, a yanda yayk tsammanin haka ya faru ta bud'e k'ofar ta fice batare datace masa komai ba, yabita da kallo yana murmushi, shekarun Hanan da k'uruciyar ta kaf duna tafin hannunsa shi ya sanya idan tana wani abin saita dinga badhi dariya, koda yake halayan ta kusan kaso tamanin suna nan basu ssuya ba, sai dai wasu data aro ta kara akan wad'an can bayan data fuskanci ta zama Budurawa
[10/25, 8:56 PM] H Inna🧕🏼: Motoci ne kala-kala a k'ofar gidan, 'yan mata wad'an da basu wuce tsarar Hanan d'in ba suna ta fitowa daga cikin su, Ya k'urawa Hanan ido sanda yaga ta nufi wata yarinya da da bata wuce shekarun ta ba suka yi tsalle suka rugume juna da farin ciki.
"Haba k'awata daga barin school shike nana zumunci ya watse ko waya bakya kira?"
Hanan ke fad'in haka, wacce Hanan ta kira da k'awarta tace.
"Bari ke dai k'awata nuna kammala school na wuce Singapore ashe alredy Daddy na ya riga ya mini registration bai gaya mini ba sai yayi suprise d'i na."
Hanan t waro ido cikin jin dad'i tana fad'in "Gaskiya na taya ki murna, Allah ya sanya mu a danshin ki kawata." Suka tafa suka yi hanyar cikin gidan kai tsaye, Aliyu yabi su da kallo wani abu yana fad'o masa a zuciya.
Me yasanya su mahaifansu basu yadda su rayu dasu suna nuna masu irin yanda iyayan wad'an nan yaran ke nuna musu k'auna dakulawa ba? Koda iyayan su basu da k'ud'i ya kamata suga k'auna irin wacce irin t wad'an nan yaran ke samu ga mahaifansu ko kwatankwacin ta.
Abin da yake cikin zuciyar su duk dare ya fara nuk'urk'usarsa, tinanin mahaifiyar sa ya fad'o masa, bai fiya tina mahaifinsa ba sai anyi wani abu irin na mahaifa amman mahaifiyar sa dakkan dare sai ya tina ta, wani lokaci har kuka yake yi, bai san ina ne garin su ba, bai san ta inda zai bi ya tafi garinsu ba, Malamin daya kawo su tunda suna yara malam Habu tun da ya tafi bai dawo ba, sai labari sukaji yarasu, abokin sa Rabe tini ya kauce hanya yabar makaranta ya fantsama yawon duniya, an ta6a gaya masa an ganshi a legas a irin gidajan katakwayan nan dake kan ruwa, malamin su da suka girma a gurin sa bai san kowa nasa ba, idan ya tambaye shi wani abu game da labarin sai yace bai san komai ba, ya dai san sunan garin su San6auna bayan nan bai san komai game da shi ba, shima ya san sunan k'auyen su shine kawai abinda ya rike, sai dai a wacce jaha ko wanne gari ko k'aramar hukuma k'auyen yake bai sani ba, domin sai da ya girma yasan ashe akwai gari da karamar hukuma da jaha ma, sau da yawa idan ya kwanta bacci yana ganin mahaifiyarsa kwance cikin farin yadi wanda hakan ke tabbatar masa da lallai ta rasu, wannan ke kashe masa gwaiwa ga sha'awar neman k'auyensu, domin yakance koyaje mezai yi? Wazai gani? Baban sa bai damu dashi, don haka koya ganshi ma ba wani farin ciki zaiji ba, mahaifiyar shi itace abar daya keson gani, sai dai jikin sa yana bashi ba zai k'ara ganin ta a wannan duniyar ba har abada sai dai a k'iyama, hawaye masu d'umi suka dinga wanke idonsa, ashe haka duniya take wasu su haifeka wasu su zamto iyayan da zasu d'auki nauyin rayuwar ka har ka girma, bayan kana da uwa da uba, ya jima cikin tinani bai Ankara ba harsu Hanan suka kammala fatin suka fara fitowa daga gida.
[8/1 01:43] Zeinab Andiya Fox : Karar motocin da suka fara tashi ne suka farkar da shi daga dogon tinanin daya keyi, sai ya fahimci ashe dare har ya fara shga, duk ya had'a gumi yayi sharkaf, ya fito daga cikin mitar rik'e da hankici yana goge fuskarsa.
Hanan ta nufo shi da k'awar ta da suka shga cikin gidan da wasu 'yan mata guda biyu da suke biya da ita suna hira cikin jin dad'i har suka iso kusa da shi.
Hanan ta kalli Aliyu bata yi Magana ba, kawayan nata suka fara k'ok'arin gaida Aliyu.
"Ina wani..." Hanan ta zunguri ta kusa da ita da hannunta tana fad'in "Da allah menene haka?".
Suka kalleta da sauri cikin mamaki, k'awarta Fadila tace "Ba brother din ki bane ba Hanan?
Hanan tayi tsaki "Babu abinda ya had'a ni da shi."
'Daya k'awar tata tace "k'arya kike wallahi, kuna mutukar kama brother d'inki ne."
Hanan ta kalli Aliyu wanda yake k'ok'arin shiga mota tayi tsaki tace "Alamajirin gidan mune fa".
Suka kalleta da mamakin jin abinda tace, yayin da maganar tadaki zuciyar Aliyu, baya jin haushin don Hanna ta kira shi a matsayin almajiri, amman yana jin takaicin yanda take son aibata shi a ko'ina suka je, amman sai yayi kamar bai ji abin da tace ba yafara k'ok'arin yin ribas da mitar.
Fadila tace "Amman bai yi kama da almajiri ba, kalleshi fa had'ad'd'an gaye, daga ganinsa kuma yana da ilimi."
Abin daya k'ara 6ata ran Hanan taja dogon tsaki tana fad'in "Sai kuma kuyi, tunda baku yadda ba shike nan."
Dai-dai lokacin Aliyu ya iso gabanta ya tsaya da motar yana mata horn, tayi tsaki ta nufi motar da sauri, amman.maimakon ta zauna a gaba kamar yanda suka zo sai ta nufi k'ofar baya ta bud'e tana dagawa k'awayen nata hannu alamar su kalla su gani, k'awayan nata suka dinga bud'e ido da.mamakin ganin abinda ta aikata, Aliyu yayi shuru kamar bazai tayar da motar ba, kamar yace mata ta koma gaba ta zauna, amman sai ya dake ya tada motar ya fice da gudu.
Gabad'aya suka bisu da kallo da tsananin mamaki, hancin

1 Comments On DA BAN SANSHI BA Book 1
avatar
fatima-1-5-8

4 months ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment