Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma duk an aurar dasu sai wa ‘inda ba a rasa ba, cikin izgili da wulakanci suka fara amsa musu gaisuwar tasu, tare da habaice habaice kowa na fadar albarkacin bakinsa . Wata tsohuwa ce ta fito daga wani daki gashin kanta duk yayi furfura da kar take iya tafiya,”wa nake gani kamar maryama da bankadaddun ‘ya’yanta, me ya dawo daku kuma , ko da yake daman kun saba zuwa ba nosis (notice).”to Nide wallahi babu ruwa na ga dakin kucan ba Wanda yake shigarmuku sabida hajiya kilishi ta Hana, amma wallahi bazaki takurani ba,”wai ma tsaya uban me ya kawo ku wannan karan kuma “, sun ku yar da Kai oumma tayi dan kwata kwata ta kasa magana ma, taheer da taheera kuwa ko wannansu hade rai yayi, in akwai abunda suka tsana a zagar musu mahaifiya. Tabe baki kaka ta bawa tayi” oh ni ‘yasu kujimun muna furci daga tanbaya sai ki wani fara sum sum da kai sai kace wata muna fuka”.tun tsirewa mutanan gidan sukayi da dariya, yayinda ko wa ke tofa albarkacin bakinsa. Ganin abun nasu ba me karewa bane yasa oumma mikewa tare da nufar dakinta Wanda ya kasance na hajiya kilishi ne mallaka musu,dakine a ciki da falo harda d’an kewaye da aka d’anyi mashi daga waje.Balefi kusan duk cikin gidan babu inda ya kai nasu kuma kilishi ta Hana kowa kwace musu acewarta wata rana in suka zo zasu dunga zama a ciki. Shigarsu cikin ‘bangaren sai da suka d’auki tsawan lokaci suna gyaranshi dan ba karamun daud’a yayi ba, suna gamawa duk sallah sukai suka mimmi’ke ga yunwa sunaji amma ba daman cin abinci sabida sunsan ko zasu mutu mutanan gidan bazasu basu ko ruwan shaba. Haka suka zauna oumma da tahee suna daki d’aya yayinda taheer kuma yake shinfida a falo dakin. Cab cikin dare lokacin da kowa ke hutawa wani ba’kin haya’kine ke tashi kad’an kad’an kafun daga baya wannan bakin ya bace batt…, can dakinsu taheera kuwa wani abune kamar silver yake faman she’ki a jikin taheera yayin da fatarta ke d’auke da wannan silver d’in kamar na maciji, kafun wani lokaci ta rikid’e tare da dawowa katuwar macijiya, ko munti 2 batai ba jikinta ya kuma dawowa Daidai, sai nan ta kara dawowa wannan macijiyar, daidai gabanin asuba jikinta ya dawo daidai, kwata kwata babu alamaun wannan macijiyar.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰

Comment and share ✍️
GIDAN AUNTY ❤️
(A heart touching love story)

By Aysha Galadima
( mss Lee)

💖The talent troupe🔥

PAID BOOK

BOOK 1📕

Bismillahirrahmanir rahim…..

Free page 3 🦋

➰➰➰➰➰➰➰➰
Wani kayataccen daki yashiga babban gaske me shegen kyau da tsaruwa , duk da kasancewar komai na part din da glass akayishi hakan be hana tsantsan kyauwun dakin boyuwa ba sai ma kara futo da ainahin kyan da yayi.Direct inda wardrobe din dakin yake ya nufa, daga jikin wardrobe din ya danna wani abu me kamar design , take wardrobe din dakin ya rabe biyu wasu manyan elevator guda biyu ne suka bayyana,na farko yashiga inda ya danna 3, direct floor 3 ya kaishi, wani katafaran falo ne awajan komai na cikin falon white colour ne hatta da labulayen dakin, ga wasu dan ubansun 2 set sofa masu shegen kyau a wajan suma white colour , daga kasanshi kuma wani lallausan farin carpet ne me shegen laushi, daga gefe a kwai standard glass da komai na cikinsa kana iya gani, iya haduwa falon ya hadu , baka jin komai na tashi sai sanyin ac da kamshin turare , a hankalii yake taka kafarsa kamar bayasan takawa, kai tsaye center table din falon ya nufa , remotes din dake center din falon ya danna, a hankali gefe daya na labulen ya fara budewa, tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki, wani kayataccen daki ne ya bayyana komai na cikin dakin white colour din hatta furnitures din dakin , babban gado ne a dakin me girman gaske sai shimfidarsa da ya kasance white and black,, daga gefe daya wani chair ne a wajan me shegen kyau shima white colour , iya tsaruwa dakin ya tsaru, direct toilet ya nufa ya dau kusan 30 minutes aciki kafun ya fito da white din jallabiya fara kal da ita , gaban mudubin dakin ya nufa wanda yake shake da mayuka mabanbanta da turaruka masu shegen kamshi,imperial majesty kawai ya fesa a jikinsa , take dakin yacika da kamshin turarensa , ba’ajin kamshin komai sai na imperial majesty daya cika dakin. Rawanin da larabawa ke daurawa ya daura akansa,inda ya futo cak a balaraben sa,ba karamun kyau kayan sukayi wa fatar saba , iya haduwa ya hadu , daga gefan fuskar sa kwantaccen bakin kashin kansa ne ya fito sai faman kyalli yake, bakin sajan bakinsa me shegen kyau ya futo da ainahin pink lips dinsa,rawanin sai ya kara futo da kyawawan idanuwansa masu zara zaran eye lashes ,tare da bakar gashin girarsa,iya kyau yayi kyau ba karamun na wasa ba, duk wanda ya kallesa sai yaso yasake kallansa, fatabarakallahu ahsanil kalikin shine abunda nake fada kawai a raina. Yanxu ma be zauna ba, wayoyinsa kawai ya dauka tare da ficewa a dakin baki daya.direct down stairs ya nufa yanxu ma ta elevator ya nufa, a kasa ya tarar da zaki, zaki na ganinsa ya sara masa tare da saukar da idansa dan ba karamun kyau uban gidan nasa yayiba , “tabbas ubangidan sa na da kyau , kyau da ake kira kyau” duk cikin zuciyar sa yake magana , cikinsauri kuma ya bude wa king motar da ya dauko kirar mercedez benz ganin ya karaso inda yake ,basu tsaya a ko ina ba sai babban masallacin dake unguwarsu,bayan idar da sallar magriba din ma basu bar masallacin ba sai bayan sallar isha’i, duk kallan da ake masa yanaji amma ko dako wa yaga masu kallan nasa beyiba sai ma kara tsuke fuska da yayi, ana idar da sallah zaki yaja motar tare da barin unguwar baki daya.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰
Sallar asubane ya tayar da oumman nasu, tahee!! Tahee, “uhm” cewar tahee, oya a tashi lokacin sallah yayi, yanxu ma “uhm”ta karacewa kafun a hankali ta soma adduar tashi daga bacci,falo takoma tare da tashin taheer, ganin ya’ki motsawane yasa oumman mi’kewa “nasan sarai kana jina maxa ka tashi kafun ranka ya ‘baci”, murmushi yasaki tare dayin adduar tashi daga bacci, dama ya rigada ya tashi tun lokacin da oumma ta fara tashin taheera ya farka.
mimmikewa sukai tare da dauro alwala kasancewar har gidan ana jin kiran sallah yasa su bin jam’i, bayan sun idarne ko wannan su yayi adduar safe da maraice kamar yadda suka saba a kullum,”oumma ina kwana”duk suka hada baki wajan gaishe da oumman tasu, murmushi oumma ta saki”fatan ‘yan biyu na sun tashi lapiya”, “lapiya lou” suka amsa mata.suna zaune sukaji sai faman buga musu kofa ake , tashi oumma tayi tare da bude kofar , ba kowa bace face kaka tabawa , daure da daurin kirji, gaishe da ita oumma tayi, tabe baki kaka tabawa tayi “ba gaisuwarkice ta kawoni ba, maza maza ki tashi kigyara tsakar gidan nan ga wanke wanke na jiranki, sannan kisaka tanbad’ad’d’un ‘ya’yanki su d’ebo mana ruwa,dan ba hutu kuka zoyiba”. “Insha Allahu zamuyi”cewar oumma, yanxun ma tabe baki kaka tabawa tayi”ke kika sani, kar Allah yasa kiyima”tana gama fada ta bar wajan , koma wa daki oumma tayi , yanda ta barsu a haka tazo ta samesu sabanin dazu yanxu ko wanne ya yi cidin cidin da fuska dan sarai sunji me kaka tabawa kecewa, murmushi oumma ta saki “kuyi hakuri yan biyun ummansu wata rana sai labari ai”,jikinsu ne yayi sanyi jin abinda oumma tace.kamo hannunta sukayi tare da sata a tsakiyarsu,”kiyi hakuri oumma ba wai fushi mukai ba , kawai bamasan abunda kaka tabawa da mutanan gidan nan suke miki”,shafa fuskar taheer dake magana oumma tayi,”bakomai taheer komai me wucewa ne bana so kuna sa abunda da suke mana a ranku, yanxu ku tashi kudebo musu ruwan da sukace kunji, ku kula sa hanya banda rigima”, “toh oumma “duk suka amsa mata , itama wajan ta biyosu tare da fara sharan tsakar gidan.
Sun dau dogon lokaci suna d’ebo ruwan , lokacin har oumma ta kammala share tsakar gidan da ya dawo kamar bashine me tarkace ba. Tulun kayan wanke wanken suka hada ‘kuda sai faman bin kwanukan suke, sundau dogon lokaci suna wanke kwanukan , dadin su daya ma haduwa sukai su duka suka wanke dan ba karamun kwanuka aka bata ba ,gama wanke wankensu ba dadewa aka kawo markadan wake , zama tahee tayi ta buga wannan kullun, yayinda oumma ke hura jikakken ican da aka jika duk idanuwanta sunyi ja sabida yadda hayakin ya cika mata ido.

Duk wannan abun da suke mutanan gidan sai faman kai kawo suke , ba wanda yace dasu ko sannu sai ma banzan kallan da ake binsu dashi da hantara.basu suka kammala ba sai wajan karfe shadaya,ragowar guntun dumamen tuwan jiya kaka ta bawa ta mikowa oumma,” kar alashemu ace bamu baku abinci ba ko akai mu duniya” cewar kaka tabawa ,kallan tuwan da baifi cin mutum daya ba oumma tayi, batace komai ba sai ma daki da ta nufa , anan ta samesu sai faman sauke nunfashin yunwa suke ,kwallace ta tarar mata , ganin suna kokarin mikewane yasata saurin goge idanuwanta kada suga rauninta, tuwan da ke hannunta ta ajje musu, cikin sauri suka mike tare da wanko hannayensu,har sun saka hannu zasu fara ci sai suka fasa tare da zubawa oumman tasu idanu,sarai ta fahimcesu amma ko motsawa batayi ba, langwabar da kai sukayi kamar wasu yara oumma suka kira sunanta , girgiza kai kawai oumma tayi tare da mikewa tare da zama a tsakiyarsu.taheer ne ya kutsuro tuwan tare da kallan oumman tasu “oumma haa” dariya duk suka saki ganin yadda ya bude bakin nasa , cikin kulawa yasa mata tuwan, itama taheera saka mata tayi a baki, hannu oumma ta saka itama ta fara basu a baki , duk da tuwan bashi da yawa amma haka ko wannansu yasamu yaci , cikin farin ciki da kaunar junansu.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
10:20 pm motarsu ta danno kai cikin gidan , kamar ba dare ba har yanxu akwai hasken futullu da ya haska ko ina na gidan, daya daga cikin building din gidan zaki yayi parking , ya dau kusan 2 minutes zaune a cikin motar idanuwansa a lumshe kamar meyin bacci, a hankali ya zuro da kafarsa guda daya kafun a hankali ya juro da gaba dayar kafar tasa yana mikewa,cikin takunshi me kama da na izza ya fara tafiya tare da nufar kofar da zata sadashi da babban falon building din.Babban falo ne me kirgan gaske da ya cika da tsadaddun furnitures na alfarma , iya haduwa falon ya hadu ba abudna yake tashi sai daddadan kamshi da sanyin ac, ganin bata falon yasa ya juya da niyar komawa, foot steps dinta da ji ne yasashi tsayawa kafun ya juyo a hankali,murmushi ta sakar masa”son “ be amsa ba sai ma zuba mata kyawawan idanuwansa da yayi, sannu a hankali ta karaso wajan, sanye take cikin hijab hannunta dauke da tasbaha sai faman sakin murmushi take , sau da ta karaso inda yake kafun ya bude baki a hankali kamar wanda magana take wa wahala, cikin cool voice din shi me shegen dadi ya kira sunanta “Ammi,”hararar wasa ta jefa masa”sai yanxu ka tuna dani”lebensa ya motsa kamar me sanyin magana sai kuma ya fasa tare da dauke kansa, kamo hannunsa tayi tare da zaunar dashi kan daya daga cikin kujerun falon,”oya zauna ka ci abinci nasan yau kwata kwata ba abuncin kirki kaciba , na kusa yi maka aure kwanannan ko zaka shiga taitayinka”,bece komai sai hade fuska da yayi tare da kau da kansa, murmushi ta sakar masa “mai da wukar son wannan hade rai haka, nima wasa nake maka , ai samun wacce zata siyo zuciyar ka sai anshirya “a jiyar zuciyar da ko ammi dake kusa dashi bataji ba ya sauke tare da sassauto da fuskar tasa kadan . Abincin ta dakko masa da kanta tare da jerasu can center table din gabansa,zubawa tulun abincin data ajje a gabansa idanu yayi sai kace mutum goma zasu ci, bece komai ba sai idanuwansa da ya zuba mata ,sarai ta gane me yake nufi”duk suna part din dada tunda kai cin abinci cikin yan uwan naka ne bakaso”, lumshe fararan idanuwansa yayi, itama ammi bata kuma cewa komai ba sai abincin da ta zuba masa cikin hadaddan plate din da ta dakko, “oya haa” bude lumsassun idanuwansa yayi tare da kallanta, yanda tayinne yaso bashi dariya amma kwata kwata be yitanba, a hankali ya bude bakin nasa ta fara feeding din nasa , 7 spoon yayi tare da kawar da kansa,”son karkace mun kakoshi”lumshe mata ida nuwansa yayi, girgiza kai kawai ammi tayi tare da dakko masa hadaddan kunun ayar da tayi masa, sosai kuwa yasha kudin ayar bayan ya kammala shane ammi ta mike, “oya tuzuru aje a kwanta sea da safe”, bai ce mata komai ba sai mikewar da yayi , dariya amminta saki”bani na kar zoman ba rataya aka bani”inda sabo ta saba da halinsa na kinson yin magana tunda tasan halin kayanta,”Ammi sai da safe “ ya fada cikin husky voice dinsa, side hug tayi masa , Allah ya tashemu lapiya ka kwanta da wuri dan na san ka gaji, jinjina mata kai yayi alamar toh tare da ficewa.

Har yanxu zaki na waje kikam kamar bushiya , inda ya barsa anan yazo ya samesa be ce masa komai ba , shima zakim bude masa kofar mota yayi, cikin takunsa na kullum ya nufi motar, haryasa kafa zai shiga sai kuma ya daga idanuwansa tare da kallan wani building sai kuma ya lunshesu tare da shiga cikin motar, daidai part dinshi zaki yayi parking yanxun ma shine ya bude masa kofa . “Sai da safe king”hannu king ya daga masa kabar bazai ce komai ba sai kuma ya bude baki a hankali “good night”. Murmushin jin dadi zaki ya saki be bar wajan ba har saida yaga shigewar king sannan shima ya barwajan.

Direct yana shiga part din sama ya hau ta elevator , yana shiga dakin rawanin kasansa ya bayyana,kofar da zata sadashi da toilet ya nufa, ya dau mintuna a cikin toilet din kafun ya fito da wasu white pj mas masu laushi , imperial majesty ya fesa , dakin ya kara dauka da kamshin turaransa da ke kama daki,kan gadan sa ya nufa kai tsaye cikin luntsumeman gadansa, har ya kwanta sai kuma ya mike tare da dakko wasu magun guna .maganin hannunsa ya sha tare tare da bude bedside drawer. Har ya bude zai zubasu idanuwansa suka sauka kan wani hoto dan karami, daukan hotan yayi tare da zuba masa ido . Wasu matasan larabawane a jikin hoton sun rike hannun junansu, kana ganinsu kasan ba karamun kaunar junansu suke ba. Sauke ajiyar nunfashi yayi tare da mayar da magun gunan, shima hotan mayar dashi ma a daninsa yayi tare da danna wani remotes take futulun dakin suka dauke , wasu kaloli masu kyau da haske suka fara cika dakin me kama da dim lights , sannu a hankali bacci ya daukeshi.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰

Comment and share

💖The talent troupe🔥

Writers of ….✍️

Duk karfin izzata
Gidan Aunty
Sarki sameer
Jini daya
Ya fita zakka…..
💖GIDAN AUNTY💖
( A heart touching love story)


By Aysha galadima
( mss Lee)

💖The talent troupe 🔥

PAID BOOK

BOOK 1 📕

Bismillahirrahmanir rahim……

Free page 4 and 5🦋

Bugun kofar da akai da Karfine ya katsemusu hirarsu, TAHEER ne ya mike da Niyar bude kofar amma oumma ta tsayar dashi, “dawo taheer bari na bude” fita oummansu tayi suma mimmikewa sukai tare da bin bayanta. Yan gidan ne cike taf a wajan kowa sai faman zabga masu Harara suke , mazan gidan kuwa duk Wanda yaga taheera sai ya kara kallanta sai mafan satar kallanta suke sabamin matan dake harararta.

“Munafukan Allah muna furcin me kuke kullawa, bayan kunsan akwai ayyuka a gabanku, shine dan muna furci da kinibibi kuka shige daki dake da ‘ya’yan ki masu kama da tattabaru” cewar wata da tafi kowa za’kewa a cikin su. Zuba wa sarautar Allah ido taheer da taheera sukai wai sune tattabaru hmm . Hakurin da suka ji oumma na bayarwa ne yasa suka maida hankalinsu kanta ,” kuyi hakuri Dije bansan akwai ragowar aiki ba shiyasa”.
Matar da aka kira da dije ce ta Dallawa oumma harara “ kyaji da munafurcin ki, inba munafurciba ba me kuke kullawa a daki ko sallan karuwancin da kika saba kike koya musu” baki taheer ya bude daniyar yin magana amma kallan da yaga oumma tayi masane ya hanashi hakan , sun kuyar da kanshi yayi yana taunar lebensa. Wata daga cikin mutanan gidan ce ta soma magana itama “ kinsan dangin Matsiyata ba abunda suka iya sai tsiya in ba karuwanci take koya musu ba me suke yi a dakin”, nan da nan mutanan gidan suka fara musu gori da hantara , suna ci musu mutunci , kowa nagidan da abunda yake fada a kansu, kaka ta bawace kawai bata wajan . TAHEE da tunda aka fadi kalmar karuwanci idanuwanta Suka faru da ha waye ga wani irin ja da sukai, ba abunda ke mata yawa sai kalmar karuwanci ko magan ganun da mutanan gidan suke bata ji, wata gigitacciyar kara ta saki da ya firgita kowa dake wajan hatta taheer da ke kusa da ita, hannunta ya so kamawa amma ta hankadashi , daya bayan daya ta soma bin mutanan gidan da tun lokacin da ta saki ihu sukai shiru da kallo, ba Wanda ne tsure ba da irin kallan da take musu, ida nuwanta ne suka sauka a kan dije dake faman zare idanuwa , a guje tayi ganta , suna ganin hakan kowa na gidan ya Watse dan ba karamun firgitasu tayi ba daga mazan har matan. Wani murmushi taheer ya saki daman yasan za Arina, a zuciyarsa sai faman Allah shikara yake musu. Dije dake kokarin shiga daki tahee ta cafko, riko tayi mata ba na wasa ba , Innalillahi wa inna ilaihi rajiuna Dije take ta faman fadi , fuskar ta tuni ta jike da gumi sai faman zare ido take , jama’a ku kawo mun a gaji shikenan ni fatalwa ta kamani, kukai kawai Dije take majina duk ta bata mata fuska. Ita kanta oumma Dije ta bata dariya kuma ta bata tausayi dan Tasan kome zatayi yanxu TAHEE bazata hakura un tayi mata ta Karfi kuma rashin lapiyar tane zea tashi. Taheer ma dake gefe sai faman kunshe dariyarsa yayi ganin yadda Dije ke faman fadin fatalwa ta kamata. Kallan d tahee tayi mata ne ya sata kunshe bakinta “nayi shiru , Wlh nayi shiru” , tana gama fatar hakan ta rike bakinta gam hawaye na fita, Kwale idanuwan ta TAHEE tayi a kanta , take a wajan Dije ta saki futsari dariyar da taheer yake rikewane ta fito wajan dan ba karamun dariya ta basu ba. Baki TAHEE ta bude da nufin cizonta, lokaci daya kuma ta zube a wajan. Tana faduwa kuwa Dije ta arta a guje duk da kibarta a haka ta ke kudin tana tsine TAHEE a zuciyarta.
Daukarta taheer yayi shi da oumma suka nufi daki da ita,” maza dakkomun maganinta “ cewar oumma , be dade ba ya fito dauke da roba a hannunta, ruwan adduar dake ciki oumma ta iba ta dan shash shafa mata a jikinta da fuskarta, nannauyar ajiyar zuciya ta saki , nun fashinanta na Daidai ta .
Har yanxu akwai ragowar murmushi akan fuskar taheer , hararar sa oumma tayi” kasan Kai kadai ne zaka iya temakonta, me yasa baka temake taba kabarta a hannu tahee”, wani murmushin taheer ya saki” oumma kinsa konayi kokarin temakonta Nima hadawa zatai dani, ranta ya baci sosai ko nine naje wajan ba ragamun zatai ba “, jinjina Kai oumma tayi Alamar gamsuwa da maganarsa, wata ko daddiyar dari biyu ta dakko tare da mika masa” ungo maza jeka siyo mana kwaki da kyada nasan in ta tashi zata dan ji yunwa , nan yadda ka kalli kowa ba ko kace zaka musu wani abu nasan halin ka sarai, saura kace kaima zaka rama, in naji sabanin hakan ranka zai baci” jinjina mata kai yayi tare da amsa mata, dan tabbas ba hakura yayi ba amma yanxu ba yadda zeyi dadinshi daya tahee ta rama.

Kasancewar basu da nida da me ka tin ba dadewa ya dawo , har lokacin tahee bata tashi daga baccin da take ba. Ajje Garin sukai sai da ta tashi sannan suka hada, har lokacin fuskarta a hade take , ba Wanda ya kulata a cikinsu har suka kammala cin abincin, maganin dazu oumma ta mikowa tahee , tana bata rai ta karbi maganin a haka ta shanyesa.

Kiran sallar da ake ne ya sasu mikewa tare da dauro alwala, lokacin ta saki fuskarta kamar ba Itace tagama tsorata Dije ba, sallah suka kabbara tare da bin jam’i, bayan sun idan ne sukayi shafa’i da wuturi, sannan ko wannansu ya biya wa oumma haddar alqur’ani cikin natsuwa. Bayan sun kammala ne oumma ta kara musu arba’una Hadith da ahlari, sai da ta tabbatar sun gane sanna suka zauna suka fara hirarsu irin tasu sai faman tsokanar oumma suke kamar wata kakarsu. Ganin 11 tawuce ne yasa oumma ta umarcesu da suje su kwanta.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰
Karfe 2 ya farka daga baccin da ya daukesa, a hankali ya fara karanta adduar tashi daga bacci cikin daddadar muryasa, sanna ya mike kamar bayasan taka kafafuwansa. Toilet ya nufa be dade ba yafito kyakkyawar fuskarsa dauke da ruwa da Alama alwala yayi, duk da kasancewar dare ne hakan be Hana takunsa na mazantaka canzawa ba, inda shinfidaddiyar farar daddumar take ya nufa tare da kabbara sallah cikin nutsuwarsa,ya dade yana nafilfilu sannan ya fara karatun alqur’ani mai girma a hankali cikin daddadar muryarsa ne ratsa zuciya kamar karya dena .sai da ya kammala suratul bakara gaba dayanta , sannan ya fara adduoi cikin harshen larabcin da ya zauna a bakinsa, ko wace harafi na futo wa .

4:2 shine abunda agogon wayarsa ya nuna masa, lumshe fararan idanuwansa yayi da suka fara canza kala tare da mikewa, inda system dinshi yake ya nufa , ya dade yana operating a kanta , kiran da ake na sallar asuba ne ya katse masa aikin da ya fara a system din nashi, ajjeta yayi gaba daya tare da gyara zamanshi kamar Wanda bazai tashi ba sai kuma ya mike tare da nufar hangar da zata sadashi da bathroom dinsa. Be dade ba ya fito cikin wasu kananan kaya white colour masu shegen kyau, damtsen hannunsa ya fito sosai , yayinda budaddiyar rigarsa me shape din v ya futo da kirjinsa kadan , sosai kayan sukai masa kyau , yalwataccen gashin Kansa masu sheki da san tsi sun kwanta luff tare da harneda da sajan fuskarsa, sosai kayan sukai wa kakkarfar surarsa kyau , ba abunda yake tashi sai kamshim imperial majesty .

Masallaci suka nufa shida zaki bayan An idarne kamar kullum ya umarci zaki ya bawa liman kudi yayi Sadaka,kamar yadda ya umarceshin haka yayi liman sai faman addua yake masa. Direct gida suka koma bayan an idar da sallah , part din dake tsakiya zaki yayi parking , king kuma ya shiga part din. Zaune yake cikin fararan kaya , dattijon arziki kenan, uban marayu, fari shima amma ba kamar king ba, kana ganinsa kaga bafullatani dattijo. Ciki ciki king yayi sallama tare da nufar inda mutumin yake , amsa sallamar mutumin yayi tare da zuba masa kyawawan idanuwansa irin na king, kawar da Kai king yayi tare da zama a kasa wajan kafafuwan mutumin . Ya dau kusan 5 minutes zaune a wajan bece komai ba shima mutumin

Please Login or Register in order to submit comment