Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bin king da kallo” yanxu gee sabida baka da mutumci nagama ce maka nayi kewarka shine kake tanbayata mahma,toh baza’a fada ba”,dafe kai king yayi kafun ya furta “oh my god sha’aban kafara samun ciwon kai, wai mema ya kawo ka”dariyar keta Wanda aka kira da sha’aban din ya saki kafun ya furta “nazo ganin amarsune, tunda kayi aure babu goran gayyata “ gajeran tsaki king yaja kafun ya furta “I don’t have your time “yanxu ma dariya sha’aban yasaki”dole ka fadi haka mana king tunda ka angwance kalli wani kyallin amarci da kake”Naushi king ya kai masa a kirji yana kaucewa , a hankali ya furta “parrot”,daga hannu sama sha’aban yayi kafun ya furta accepted,girgiza kai king kawai yayi tare da kama hanyar part dinsa ganin ankusa yin sallar azahar,shima sha’aban part din abeey ya shiga yana furtawa king sai yazo cin abincin amarya.

➰➰➰➰➰
Yana shiga part din nasa yaga bata falo sam ya manta da zancan yace mata kada ta fito a dakin, a gogon hannunsa ya duba 1:10pm, dakin da suka kwana ya nufa kai tsaye sai alokacin ya tuno da abunda ya faru,dafe goshin sa yayi kafun ya furta “ya salam “ yana shiga cikin dakin,yana shiga dakin da plate din da ya ajje mata na abinci ya fara cin karo ,yana nan yanda ya ajjesa da alamu ma ko tabashi ba aiba, cikin dakin ya karaso yana bin dakin da kallo dan ganin ta inda zata bullo, a saman gadon dakin idanuwansa ya sauka, sosai ta takure waje daya kamar me jin sanyi, cikin sauri ya karasa kan gadon kafun ya yaye bedsheet din,da sauri ta tashi zaune a firgice da alamu bancin nata be yi wani nisaba, tana ganinsa ta kara ja baya da sauri kamar wacce taga wani abun tsoratarwar,”me ya Hana ki cin abinci “ ya furta yana binta da idanu, a hankali ta furta “na koshi dady”kamar wacce aka sa dole,karasowa kan gadon yayi kafun ya dora hannunsa kan forehead din ta,zafin da ya jine yasashi saurin kallanta,ganin tana kokarin lumshe ido,”open your eyes “da Sauri kuwa ta bude idanuwan nata har yanxu tsoran nasa be fita a ranta ba, fita yayi daga dakin ba jimawa ya dawo hannunsa dauke da wani mug me shegen kyau, tea ne a ciki mea dumi sai faman tashin kamshi yake,mika mata yayi ba tare da ya kalletanba “shanyesa duka “baki ta bude zatai magana ya bita da rikitattun idanuwansa,da sauri ta kar ba ta farasha saura kadan ta kware,saida ta kammala sha ya kyaleta ,ganin yadda take sun kuyar da kaine yasa ta bashi tausayi duk da yasan ba lefin ta bane , a gefan gadan ya zauna kafun ya janyota jikinsa yana rungumeta,kuka kawai tahee ta fashe masa dashi ,tapping din bayanta yayi a hankali kafun ya dagota “kayi hakuri dady” ta furta a marairaice ,dogon hancinta yaja yana dan dungure mata kai, dariya ta fashe dashi kafin ta kara rungumeshin.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

YOLA

bakaramun ukubar rayuwa su taheer suke fuskanta ba, gashi sau daya ake basu abinci a rana sai biredin da ake jefo musu kamar wasu kaji, mutanan cikin dakin har yan rige rigen dauka suke sabida bakar azabar da suke fuskanta. Suna kwance a inda aka killacesu a ka bude kofar dakin,kowannansu rarra kubewa yayi gudun kar a gansu, mutane biyar mutumin ranar nan ya zaro, ciki har da taheer , bugun su mutuminnan ya fara kamar Wanda aka kaiko, kafun ya samu wani d’aki me shegen duhu ya kullesu a ciki, ko wannansu ba me motsin arziki aciki shash shekar d’aya daga cikin suce ta cika musu kunne a hankali taheer ya bude idanuwansa da sukai masa nauyi kafun ya soma magana “me yasa kake kuka”kara fashewa da kukan saurayin yayi kafun ya furta “gida nake so na koma” daya daga cikin sune ya amsa masa a wahale shima “muma dukan mu muna so mu koma gida amma ba yanda zamuyi, ni so nake na samo hanyar da zan futa daga wajan nan,mutanan nan basu da imani ko kadan,bamuyi musu komai ba suke cin zalin mu,kamar yadda sukai wa sauran muma ina tunanin siyar damu zasuyi”be karasa zan can nasa ba yaji an banko kofar, saurin gimtse bakinsa yayi, wani gabjejene ya shigo dakin ,yanxu ma jibgarsu yayi cikin mugunta da rashin imani kafun ya jefo musu guess’s guda uku da pure water guda biyu ,kamar Wanda suka shekara basu ci abinci ba haka suka samu guntuwar gurasar nan sunaci ,kalaman saurayin can ne yake ta faman kai kawo a zuciyar taheer,sosai kwadayin samun mafitar ta yanda zasu gudu ya shiga ransa shima ,babu Wanda ya kara magana a cikin su sabida yadda ko wannansu yake jan nunfashin azaba.

➰➰➰➰➰➰➰➰

BUNKURE

Acikin yan kwanakin nan sosai kaka ta bawa ta rame,duk lokacin da ta kwanta bacci mafarkin su oumma kawai take, tun abun baya tamun ta har ya soma damun ta,sosai ta shiga dana sanin abunda ta dinga yi musu alokacin baya , kusan kullum kenan yanxu sai ta leka dakinsu ko zata ga sun dawo, mutanan gidan ma ko wannansu ya fara shiga taitayinsa sabida wahalar baccin da suke samu cikin tare ,da yawa daga cikin su suka nutsu .

A ban garan su Dije kuwa liyafa ce ta karu, yanxu kwata kwata bintalo bata kwana a gidan sai dai tazo da safe tayi abunda zatayi ta bar gidan , wani lokacin ma kayan ta kawai zata iya ta har gidan, har yanxu kuma babu me daga mata yatsa sabida duk ta bawa boka sunayensu . Dije kuwa ko a jikinta halin da bintalo ta jefa kanta ,tunda tana kawo mata kudi,burin ta daman ta samu kudi,yanxu har wata kawa tayi me suna hajjo aunty, hajjo aunty makirar matace ,burinta kawai ace tafi wani, sun hadu da dije ne a wani biki ,shikenan suka kulla alaka mai karfi kamar wacce suka yi shekaru da dama tare , yanxu ko wana sirri na Dije ,hajjo aunty ta san dashi, itace kuma me bata shawara,yanxu itama hajjo ta fara sawa Dije kwadayin yawo kamar yadda take,a tunaninta ai shine kadai hanyar da samun kudi kafun su tura bintalo can burniii.


🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰

LAGOS

8:30pm ya shigo cikin gidan , be nufi part din kowa ba sai na dada, babu kowa a cikin falon wani daki dake facing din na dada ya shiga,kamar yadda yayi hasashe kuwa tana kwance kan gado tana baccinta cikin kwanciyar hankali, kiss din da tayi masa a kumatu ne ya fado masa rai kafun ya kawar da zancen yana karasa shigowa cikin dakin , be jira komai ba dauketa kamar wanda ya dauki baby ya fito da ita, a maimakon ya fita daga part din dada wani corridor dake jiki ya nufa daga jikinsa wani dan adone a wajan ,adan wajan ya dan karkata kadan,take a Wajan jikin bangon ya tsaye wata kofa ta bayyana,shiga yayi ciki kafun ya kulle ta ciki, daga wajan kuwa kamar babu wata tsaga da ya taba yi a wajan, yar tafiya yayi kadan kafun ya bude daya daga cikin kofofi ukun da ke wajen, yanxun ma yar guntuwar tafiya yayi,kafun ya bude wata kofa,yana bude kofar kai tsaye bedroom din da suka kwana ne ya bayyana sai faman tashin kamshi dakin yake kamar kullum,kwantar da ita yayi kan bed din kafun ya warware mata veil din jikinta yana gyara mata kwanciyar . Sai da yayi Wanka kafun ya fito daga part din nasa , direct part din ammi ya nufa, koda ya isa part din ammi na kitchen sai faman aikace aikace suke,shigowar sa falon ne yasa ammey fito wa da yalwataccen murmushinta na kullum da ta saba, tana ganinshi ta bude masa hannayenta a hankali ya karasa wajan ta kafun yayi hugging dinta, cikin sanyayyar murya kamar bashi ba ya furta”nayi kewarki ammey “itama ammeyn cikin sanyin jiki ta furta “Nima nayi kewar ka sosai son,ya kake ya daughter na”gingina mata kai yayi kafun ya furta “all will be alright ammey,trust me zata ganeki soon” murmushi ammi ta saki tana ja masa hancinsa “ai na yadda da son dina ,shiyasa bani da wata damuwa”lumshe mata ido yayi yana budewa, kunun aya ta kawo masa tare da abinci, kunun ayan kawai ya sha sosai batare da yaci abinci ba,sun dau tsawan lokaci suna tare kafun yayi mata sai da safe.
Koda ya fita daga part din ammey part din ummey ya nufa,ko da ya shiga part din itama tana kokarin fitowa ne , ganin shine yasa ta koma,bayan gaisuwa babu wani abu da ya kara shiga tsakaninsu,Mikewa yayi da niyar tafiya yaji saukar muryan ummeyn sa”ya jikin daughter “ajiyar zuciya ya sauke kafun ya furta “Alhmdllh “,ummey bata kara cewa komai ba tsawan 2 minutes kafun ta furta ,”gobe UMAIMA zatazo” harbawa zuciyar sa taji jin umaima zata zo amma a fili babu alamun hakan a fuskarsa sai “Allah ya kawo ta lapiya “ da ya furta yana barin part din….



💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖
💖💖GIDAN AUNTY💖💖
(a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee 💖


PAID BOOK

ME BUKATAR GIDAN AUNTY COMPLETE YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 07041879581.

BOOK 1 📕

Page 41_42 💖

Karfe 11 na dare ya nufi part din dada ,lokacin ba kowa a cikin falon ko ina na wajan ya dau shiru, wani corridor ya nufa kusan tafiyar mintuna 2 kafun wasu kofofi su bayyana a wajan,kofar hagunsa yayi knocking ,kusan mintuna d’aya ba a amsa ba, kara knocking yayi nan ma shiru, juyawa yayi da niyar komawa wata kamilalliyar murya ta bashi izinin shigowa , a hankali ya tura kofar dakin ,babban falone a wajan me shegen kyau da haduwa,komai a cikin falon ya hadu iya haduwa, tsaye take cikin maroon din hijab dinta daya kara fito da kyawun fuskarta da alama sallah ta idar yanxu, murmushi ta sakar masa tana buda masa hannun,cikin takunsa na kullum ya karasa wajanta tare da rungumeta ba kowa bace face ZARMEEN wato kanwar abeey auta ga dada kuma .”mahma “ ya furta yana kallan kyakkyawar fuskarta,dungure masa kai tayi “babu wani mahma, se da ka ganni zakace mun wata mahma”, kunnuwansu ya rike “am sorry “dan tabe bakinta tayi “babu wani sorry da zan karba sai ka kawo mun daughter na ganta, tunda sai dai naji labarin auranka , ka kyauta son”, shiru yayi mata ba tare da yace mata komai ba” kama hannunsa tayi suka zauna kafun ta kallesa” yanxu son fadamun kana santa and ya kamanninta yake ” kallan aunty sa yayi na yan sakanni kalmar kana Santa na masa yawo arai “so!? Never, she’s too small for me”,ya furta cikin zuciyarsa ,kallansa aunty zarmeen tayi tana sakin murmushi” da alama dai ka fada santa da yawa tunda har ka kasa amsamun,gaskiya wannan daughter tawa ba karamun sa ‘a tayi ba and let’s go ,bari na nuna maka wani abu “ta kama hannunsa suna shiga wani daki , wasu designers din set din akwatunane acikin dakin milk colour masu shegen kyau, kallan mahma yayi alamaun karin bayani,murmushi mahma ta sakar masa “kayan legend daughter ne abeey yace a taho dasu sauran sai auntyn ka ta karaso gobe ,zauna se na bude maka” girgiza mata kai yayi “no need mahma” ta bude baki zatayi magana sha’aban yashigo dakin bakinsa dauke da sallama,tsayawa kallansu yayi kafin ya karaso cikin dakin “mahma yanxu kinga danki shine har kin fara mantawa dani” dan hararar sa tayi “ zaka shiga tsakanine “daga mata hannu yayi yana furta “toh mahma me kuke tattaunawa sannan wannan akwatunan na wanene “ budar bakin mama se cewa tayi “ka bari duk lokacin da ka kawo mun matarka kaima sai a dama dakai dan haka bamu waje “kyalkyalewa da dariya sha’aban yayi “Lalle Geee kana da farin Jini ,kowa kai yake so, basma ma sabida kai tazo gidannan Bawai gaishe da abeey ba kamar yanda ta fada, ga sauran yan matan gidan musamman wannan ne rawar kan”, wani shegen kallo king yabi sha’aban dashi kafun ya kalli mahma” good night mahma”murmushi mahma ta sakar masa “night too son”,kama hanyar fita yayi yana hararan sha’aban,cikin daga murya ya furta “ina gaishe da amarya”,Jan kunnansa mahma tayi,sai da ta bari king ya fita kafin ta furta “ka fita idona sha’aban”ouch ya furta yana kama hannun mahma din” mahma amma ba kya ganin king zai saki yarinyar nan d zaran ta dawo sense dinta,ko da ace yana santa mahma toh shi haryanzu ya kasa gane hakan,ya kamata kiyi wani abu akai”shiru tayi kamar me nasani kafun ta gyada masa kai “zan fara zuba masa ido tukunna” amma mahma basma fa kinsan ba dan kowa tazo gidan nan ba sai shi,gashi yana da mata”,gyada masa kai mahma tayi ,”wannan ba matsalata bane ,idan yace yana ra’ayin auranta fine, Inyace bayaso ai babu Wanda ya isa ya masa Auran dole ko” jinjina mata kai yayi alamar gamsuwa kafun su ci gaba da wata sabuwar hirar.

****tunda ya bar part din mahma zantukanta suke dawo masa ,”so!?? Din da tace shine abunda ya fi tsaya masa arai ga kayan lefe da suke shirin yi batare da sanin saba,yanxu shi yazaiyi ,dole yasan mafita tunkan abu ya kwabe masa Musamman idan small mom tazo gobe ,”ya Allah “ ya furta cikin ransa. Koda ya koma part dinsa be shiga dakin da take ba sabida hukuncin da ya Yankewa zuciyarsa dole ya nesan teta.hakan ce kuwa ta faru be shiga dakinta ba sai wani dakin sirrinsa da ya shiga , babu komai aciki sai na’urorin computers cike a wajan, d’aya daga cikin computers din ya nufa , a ciki ya hango yadda take bacci cikin kwanciyar hankali,abunda ya faru tun bayar fitansa ya duba, mamakine ya kara kamasa ya fuskanci duk lokacin da ya fita zai tarar an gyara ko ina , a tunaninsa masu aikine sai yau ya kara tabbatar da zarginsa , a nutse take yin sallarta,bayan ta idar karatun alkurani tayi cikin kira’a me dadi da natsuwa.mamakinsa be kare ba sai lokacin da ya ga ta gyara ko ina ,”Anya yarinyar nan ba aljana bace”. Kashe komai na wajan yayi tare da fita, lifter ya hau ya karasa 3rd floor dinsa , ko ina kamshin ac ne ke tashi kamar ba a amfani dashi, system dinsa ya dauka ,itama sosai yayi aiki akanta ya dade yana aiki akan system din har wajan karfe 3 na dare, har ya kwanta da niyar yin bacci kalaman mahma ya kara fado masa ransa “kana santa!?”, dogon tsaki yaja yana kokarin kawar da zancen amma ya ki barin sa , mikewa yayi tare da sakkowa dakin da take , har yanxu baccin ta take cikin kwanciyar hankali. Fuskarta ya zubawa idanuwansa, so innocent take baccinta kamar bata da damuwa, dan siririn gashinta da ya rufe mata ido ya sa dan yatsansa ya gyara mata kafun ya kara kallan kyakkyawan fuskarta,lips dinta da yayi ja sosai shine yafi daukan hankalinsa,daidaita fuskarsa yayi zuwa tata,sumbatan bakin nata yake kokarin yi ,kalmar “kana santa “ shine ya fado masa rai yayi saurin janye bakinsa kafun ya mike wajan gabaki d’aya yana rintse ido. Rana ta farko a rayuwarsa da ya kwanta akan sofa, sai faman rintse ido yake ko tunanin da yake ze bar zuciyarsa, ya dade yana kwance akan sofa din nan ,ganin kansa na sara masa ne yasa shi mikewa tare da komawa kan gadon, ko kallan inda take beyi a tunaninsa ko zai samu ya rintsa,abunda zuciyarsa ke kokarin kimtsa masa yake kokarin kaucewa,ganin yana kara wa kansa zafi ne yasa ya janyota jikinsa, a tare ko wannansu ya sauke a jiyar zuciya,a hankali kafin bacci ya d’auke shi.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

YOLA

9:30pm
Lokacin wani wahalallan bacci ne ya dauki mutanan dakin , TAHEER na gefe shima yana baccin wahalar, jiya yi kamar antabasa,a zabure ya mike yana kokarin kwace kansa, biyu daga Cikin mazajen da suke tare da sune suka rikeshi gagam bayan sun yi na saran bude kofar, idanuwansa kawai suka bar masa abude baya iya komai sai bin su da yake da kallo , komai suna yi ne cikin kulawa da taka tsantsan, sabida yadda gidan yake da wahalar futa amma duk da haka suka sha da kar, kamar sun san hanyar ko ina na wajan, sai da sukayi tafiya me Nisan gaske bayan sun fito dashi, wata mota da akai parking ne suka samu na sarar boyeshi a ciki kafun su juya da niyar tafiya, rike hannunsu yayi hawaye na zuba a cikin idanuwansa,a wahale ya furta “suwanene ku,me yasa kuka te makamun “, dayan guy din na kusa dashi ne ya kallesa amaimakon ya amsa masa tanbayarsa sai ya sakar masa yalwataccen murmushi”ka kula da kanka,wannan motar zata futar dakai daga Garin nan ,da zaran kafita kada ka sake ka kara waiwayota “ yana kammala zancan sa ya juya,kara rike hannun mutumin taheer yayi,”dan Allah ku fada mu suwanene ku”, dukansu murmushi suka sakar masa kafun Wanda ya rikewa hannun ya furta “SIF”,nagefansa kuma ya furta” LOLA”,basu kara bari ya furta wani abuba ,Wanda yace lola ya fesa masa wani farin abu a fuska take a Wajan bacci ya daukesa Daidai lokacin da motar nan ta soma tafiya, motar na barin wajan mutanan nan suka rikede tare da komawa macijansu.

🫧🫧🫧🫧🫧
➰➰➰➰➰
Washe gari da wani irin ciwon kai ya tashi, da gyar yake bude idanuwansa da suka kada ,wani irin jiri jiri ne yaji yana kokarin kamasa, yana tashi itama tahee ta farka kamar wacce tasan lokacin tashinsa, a hankali ta fara karanto adduar tashi daga bacci duk a kunnansa,be kulataba har yaje ya shirya cikin wata ash din jallabiya ne shegen sanshi, kansa har yanxu da lemar ruwa alamun wanka yayi,yau ko masallaci be jeba anan cikin dakin yayi sallarsa,a haka tahee ta fito itama sai kunbura baki take ganin yaki kulata,cikin nutsuwa tahee ta kabbara sallar ta , komai cikin nutsuwa da bin ka’ida take yinsa, duk abunda take yana kallo amma haryanxu be motsa daga inda yake ba,tana idar da sallar ta soma karatun alkurani cikin wata kira’a me shegen dadi, lumshe idanuwansa yayi dan jin dadin karatun yake har cikin zuciyar sa,sosai ya kasa kunne yana sauraran karatun da take, ta dau dogon lokaci tana karatun kafun ta idar,a hankali ta nufi inda yake tare da dora kanta a saman cinyarsa,cikin sanyin murya ta furta “dady”yi yayi kamar be jitaba, ko motsawa beyi ba daga yadda yake,kara kiran sunansa tayi,amaimakon ya amsa mata se cewa yayi” baki iya gaisuwa ba”da sauri ta furta “dady ina kwana” banza yayi da ita kusan mintuna d’aya kafun ya bude rinannun idanuwansa da suka kada,kwata kwata besan dogan magana yau,”tashi ki zaune”ya furta ba tare da ya kalletaba,da sauri kuwa ta mike zaune” zan tanbayeki , ki amsa mun kawai “, be jira ta basa amsa ba ya fara tanbayarta game da karatun alquranin da ta fara karantawa , wanene ya koya mata",shiru tayi kamar me nazari kafun ta bude hannayenta biyu alamun itama bata sani, still tanbayar da yayi mata game da sallarta ,shima nan da hannunta ta nuna masa kafun ta furta “Nima ban sani ba”,tanbayoyi ya soma yi mata game da addininta, sosai kuwa take basa amsa ,shi kansa yayi mamakinta.a karo na farko daya furta “TAHEERA MOHAMMED”,be karasa kai zancen saba sabida yadda yaga tayi saurin dafe kanta,kallanta yayi kafun da kyar ya bude bakinsa “me ya faru” kanta kawai take nuna masa,shiru yayi yana binta da idanuwa tsawan mintuna daya kafun ya kara furta “taheera Mohammad “wannan karan kuka ta saka masa Sabida yadda taji kanta na mata zafi,tafukan hannayensa yasaka yana taba goshinta,babu zafi ko daya sai zufar da ta fara tsatstsafo mata,”ciwo yake miki” da sauri ta daga masa kanta, be ce mata komai ba sai mikar da ita da yayi tsaye ,direct kan bed din ya kwantar da ita, duk yadda take tsattsafo da gumi haka ta dage sai ta lulluba, be ce mata komai ba ya lullubetan,”karki bacci ina zuwa” ya furta mata a hankali,kanta kawai ta daga masa ,ya mike zai tafi kuma ta kara rike masa hannu,”dady kada ka tafi kaji”, lumshe mata eyes dinsa yayi “yanxu zan dawo” yana furta Hakan ya bar dakin , sunan da ya kira dazu take kokarin tunawa,ganin yadda kanta ya kara daukan zafine yasata rufe idanuwan nata, be jima ba ya dawo dauke da wani cup dan madaidaici, gefan fuskarta ya shafa , a firgice ta bude idanuwan ,Wanda ta ganine yasata binshi da idanuwa,mikar da ita zaune yayi kafun ya mika mata cup din hannunsa,”shanye ki ban kofin”,karban kofin tayi tare da kaishi Daidai bakinta, tana shakar kamshin sa tayi saurin janye bakinta, cikin marairaicewa tace “bana sha”kara hade ransa yayi kafin ya nuna mata cup din “kishanye kafun ran ki ya baci”kamar zatayi kuka tayi kurba d’aya ko hadiyeshi batayi ba ta fesoshi waje,sosai kuma ya batawa king farar rigar jikinsa,ta dago da niyar yi masa musu ganin yadda ya hade ransane yasata kara kafa kai cikin kofin, cikin sauri ta shanye abunda take ciki kafun ta mika masa kofin, ko minti d’aya batai ba ta mike daniyar barin wajan, hannunta na dama ya rike gagam tare da mayar da ita wajan da ta tashi,hannun ta fara kokarin kwace wa ,dayan hannun na toshe da bakinta, yana kula da ya na yinta sarai amma duk da hakan be sakar mata hannun ba sai ma janyota da yayi jikinsa,wani irin amaine yazo mata ba shiri ta fara kwarashi a jikinsa,lumshe idanuwansa yayi yana jin yadda take kwara bakikirin aman cikin fitar hayyaci,sai da ya bari ta gama kwarara aman kafun ya dagata a jikinsa gabaki dayanta ya nufi toilet da ita.

➰➰➰➰

Tunda suka watsa masa powder dinnan yake bacci cikin babbar motar da tayi kama da ta masu daukan kaya.tafiya ce me dogon zango tun suna tsayawa a hanya har suka dena ,cikin sharara gudu motar nan take tafiya har Garin Allah ya waye,har lokacin kuma taheer na cikin motar,cikin wani babban waje me cike da mutane suka tsayar da motar. Surutan mutanene ya farkar dashi,azabure ya bude idanuwansa ganin bakowa a Wajan sai tulun kaya yasashi fara rarraba idanuwansa,ga Duhun da ya toshe masa fuska baya gani, cikin fitar hayyaci ya fito daga cikin motar ba tare da kowa ya ankara dashi ba,cikin layi ya soma tafiya ,yana wuwwuce mutanan da ke babban wajan, ga tsakanin yunwar da ta haifar masa da jiri,ta fiya kawai yake baya kallan gabansa, gashi ko takalmi babu a kafarsa, Daidai wani babban titi ya soma ratsawa Kwata kwata baya ganin gabansa, motoci kuwa sai kauce masa suke, cikin sharara gudu wasu bakaken BMW suka shawo kwanar wajan ,ba tare da sun ankara dashi ba motar nan tayi sama dashi, ya fado ko motsi ba yayi, cikin sauri driver din motar ya fito,ganin baya motsine yasashi dora hannu aka ,”shikenan na zama gawa Nima”, tun kafin a tabbatar da mutuwar Wanda ya kade ya soma kuka, cikin Sauri wasu sojoji biyu suka fito daga cikin motar, cikin turanci suke tanbayar drivern yana basu amsa,a hankali aka bude bakar BMW din bayansu,da Sauri d’aya daga cikin sojan ya zo wajan kofar tare da sarawa na cikin motar, a hankali wata farar kafa ta zuro da kafarta,kafun ta fito da gangan jikin ta gabaki d’aya , fatabarakallahu ahsanin khalikin, kyakkyawa ce matar , gata fara sosai kana ganinta kaga cikakkiyar balarabiya , sanye take cikin jallabiya irin ta mata ash colour da ya rufe jikinta gabaki d’aya , a hankali ta soma ta ku sojojin nan suna take mata baya har ta karaso wajan da taheer yake a kwance,”ya salam “ta furta a hankali”kallansu tayi cikin bacin rai “me kuke jira ku sashi a car”cikin gaggawa kuwa daya daga cikin su ya dauki taheer zai sashi a motar su “on my car” ta kara firtawa,”mah” wani soja ya furta ,kallan da ta jefa masa ne yasashi sunkuyar da kai kafun ya shigar da taheer cikin motar ta,a guje suka bar wajan,Kai tsaye motocinnan basu tsaya a ko ina ba sai a cikin babban private hospital din cedarcrest hospital ltd dake sam mbakwe st ,ba bata lokaci a ka dauki taheer zuwa emergency. Wayar matar ne ya soma ringing cikin wakar

Please Login or Register in order to submit comment