Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

adduar tsawan ran da nadungayi yau ta cika burina ya cika naganin Auran tahanuni, tunda Allah ya dauke ran mahmuda, Allah ka basu zaman lapiya me dorewa” ta karasa zancanta tana goge hawayanta, wani dan madaidaicin box dada ta dakko tare da daurawa tahee a tafukan hannunta”wannan kyauta ce na baki sabida yanda kike sani farin ciki tahura ta karki ji komai duk lokacin da ya bata miki rai ki sanar dani zanyi maganinsa” kuka tahee ta fashe dashi me rasa zuciya ko magana ta kasa yi,a hankali sautin kukanta ke tashi kadan kadan, daga wajan dada wajan ummey aka nufa dake share hawayan farinciki yau Allah ya nuna mata bikin d’anta da take mararin gani har cikin zuciyarta , itama nasihar tayi musu kafun ta bawa tahee kyautar diamonds set tundaga kan sarka , dan kunne , zobe da abun hannu bayanshi kuma ta bata kyautar manyan Lamborghini sababbin yayi gudu biyu ,guda gabaki d’aya aka saka afalon dukda dayawa mutanan wajan ba haka suka soba , da aka zo kan ammey kuwa kuka ta fashe dashi daya taba ran kowa ga tahee da take kuka kasa kasa itama , da kyar aka samu tayi shiru itama nasiha tayi musu kafun tayi musu kyautar diamond itama da babban mall dinta dake Lagos, kowa yaji dadin yanda ta hadasu musamman yanda ta raini king amatsayin d’anta tun yana karami,gabaki d’aya iyayan falon kowa kyautar da daga gold sai kyautar motoci da company da take samu , wannan abu shi ya kara bakatawa amrah da basma rai kowa yana ganin da ace babu tahee da shine zai samu wannan kyautar. Part din abeey aka suka nufa mahma na take musu baya, yanda ya gansu ba karamun farinciki yasa shiba daya kasa boyuwa akan fuskarsa, shima sosai yayi musu nasiha ne ratsa jiki akan zaman aure, yana kammala yi musu kuma ya basu kyaututttuka masu girman gaske , d’aya daga cikin jirgin NAHYAN sukutum ya mallakawa tahee,wani saban kuka tahee tasaka masu, kama hannunta mahma tayi batare da ta bari tace komai ba ta nufa da ita dakin da su ummey suke ciki daga ummey sea small mom, anyi anyi da ammey tazo taki zuwa acewarta sune iyayanta ai, sosai suka zaunar da ita sukai mata nasiha me ratsa jijiyoyin jiki da tsoka ko wannansu saida ya rungumeta tare da lallashinta kafun abar mahma ita kadai sai amzy da aka kara kira , wani wanka suka sata ta sake yi kafun su shirya ta cikin Wani Dan ubansun lace meshegen kyau red colour , shigarta ta ynxu harta taka wanda aka yi mata dazu kyau da haduwa, wani abu amzy ta bata Tasha kafun akara kyarata, suna kama gyarata kuwa aka dakko wata lapaya red itama aka nada mata a jiki( oh oh oh ni miss lee, ni kaina saida kyawun ta ya tafi dani).


A bangaran king kuwa Suna fita abeey ya rungumeshi , yana sauke a jiyar zuciya ba “addua ta daya kullum naga auranka tun bayan rasuwar Mohammad, amma Allah baiyi ba sai yanxu , na rokeka ba danni badan na isa da kai ba , ka kula da maraicin yarinyar nan , tana bukatar kulawa ta musamman ko dan irin kaddarar rayuwar da ta fuskanci kanta a ciki, idan kamun hakan ka gama yi mun komai arayuwata, Allah yayi maka albarka yanda ka faranta mun Allah ya baka masu faranta maka kaima “, lumshe idanuwansa king yayi yanajin kalaman mahaifinsa har cikin zuciyarsa,har yanxu yana tuna kalaman nan” akhie , idan Allah yasa ban ga auranka ba inaso ka zama da happiness man , ranar auranka,duk matar da aka zaba maka ka karbeta hannu biyu kasota kamar yanda kake san mu”, kara lumshe idanuwansa yayi tuno Wannan kalaman daka wajan mutumin da har yau bazai taba mantawa dashi ba, besan lokacin da bakinsa ya furta “I promise you , I will always be what you wanted me to be”, kara rungumeshi abeey yayi tsam a jikinsa kafun ya raba jikinsu, dan Allah abeey king yayi “abeey ni baka bani kyautar jirgin ba ‘ai”, dan bugunshi abeey yayi “ Wanda kake dasu ya isheka, maza tashi kabar mun daki”, wani gajeran murmushi king ya saki da ya fito da zallan kyawun da Allah yayi masa ,ban taba ganin wanda ko be yi murmushi ba yana kyau balantana ya gwada koda motsa lips dinsa ne, sallama yayi wa abeey kafun ya bar part din, koda suka hadu da sha’aban sai faman tsiya yake masa, saida ya dawo masa asalin king dinsa kafin ya kyalesa.


✨✨✨✨

Karfe 8:20 pm mahma da small mom suka dauki tahee zuwa dakinta na aure bayan nasihohin da jan hankalin da akai mata,kasa mikewa tahee tayi daga zaunan da take sai faman kukar da take Durza da ya haifar mata da zazzabi, mikar da ita small mom tayi kafun su nufi motar da aka bude musu, ba ayarda kowa ya bisuba,suna zuwa Daidai part din akasa tahee ta fitowa da kafar dama bakin ta dauke da bismilla,har suka shigo part din komai sai sun sa tayi bismilla cike da addua suka shiga part din, basu tsaya a falo ba suka hau step da ita, wani door suka bude Babban falo ne meshegen kyau a wajan, shima basu tsaya a wajan ba kai tsaye daya daga cikin bedrooms din aka kaita, ba bata lokaci su mahma suka sata yin wani saban wanka, tare da shirya ta, saida suka zo tafiya ne tasakar musu wani saban kukan , jikinta sai faman rawa yake sabida zazzabin da ya kamata,da kyar suka samu sukayi mata dabara suka gudu. Ganin saura ita kai yasa ta kara fashewa da wani saban kukan.

Kallan yanda take faman kuka yayi kafun ya karaso cikin dakin bakinsa dauke da sallama , kan gadon ya karasa tare da dagowa, jin an dagata yasa tayi saurin bude idanuwanta , kallan Wanda ya dagatan tayi kafun ta kara sunkuyar da kan nata tana fashewa da wani saban kukan, rungumeta yayi a jikinsa yana sauraran yanda take kukan,bayanta ya dan shafa kafun ya furta “it’s ok don’t cry”, a tsaye ya cigaba da shafa bayanta har saida ta daina kukan ta dawo ajiyar zuciya .

Zaunar da ita yayi akan gadon kafin ya fita daga dakin ba dade wa ya dawo hannunsa dauke da karamun tray,farfesun kayan cikin dake cikin plate din ya mika mata , girgiza masa kai tayi alamun bata jin yuwa, shima dan girgiza mata kan yayi ganin tana kokarin yi masa musu yasa ya hade ransa , da sauri ta fara shan farfesun,daman yunwa take ji , be kyaleta ba saida Tasha fresh milk din da ya zuba mata, tana kammalawa ya bata magunguna Tasha , tana turo bakinta tashanye magun gunan,”we’re friends ai yanxu ko”, dan kanta ta daga masa kadan har yanxu taki yarda ta kallesa”ok since we’re friends , ai zaki te makamun ko” yanxu ma kanta daga masa, murmushin iya kan labba ya saki kafun ya mike “je kiyi alwala, turo masa bakinta tayi kafun ta furta “ni nayi salla” Nima nayi ai , ya bata amsa ganin zata kara magana ya katseta “banasan musu go and do what I asked you “
Tana shiga toilet ya ciro mata hijab shima ya fita , futowarta daga toilet din ta tarar da hijab din da ya fito mata dashi, sawa tayi Daidai lokacin da yashigo dakin,sallah ya ja su raka ‘a biyu , ya dade yana addua kafun ya dora tafukan hannunsa akanta yana addua, duk tanbayar da yayi mata game da addininta sosai take bashi amsa, suna kammala adduar ta kara turo bakinta, kallanta yayi kafun ya furta “na fita ko” da sauri ta daga masa kai, be ce mata komai ba kuwa yace mata saida safe ,kafun ya bar dakin. Wani ajiyar zuciya ta sauke , wardrobe ta bude ganin babu kayanta aciki sai wata karamar trolley , tana bude wasu kayan bacci ne a ciki dakyar ta iya daukan guda daya a ciki ta saka , tana sakawa ita kansa saida taji kunyar kayan da sauri ta haye kan gadon tana lulluba sabida sanyin da ya ratsa mata sassan jiki, da Kyar bacci barawo ya saceta tanayi tana farkawa gudun karya shigo dakin kafun bacci ya nauyi ya dauke ta sosai.

Karfe 2am ya shigo dakin ganin ta takure waje daya ne yashi karasawa gaban kan,a gefenta ya kwanta a hankali gudun kar ta tashi daga baccin da take yi kamar a takure, goshinta ya taba yaji har yanxu zafin jikin ta be sauka ba, janyota yayi gabaki dayanta ya dora akan kirjinsa, wani ajiyar zuciya ta sauke me karfi da yasashi kallanta kadan, kara rungumeshi taji ajikinta kamar wacce akace za’a kwace mata shi, lullube jikinsu yayi da bargon yana jin yanda zafin jikinta ke ratsa sa,kallan innocent face dinta dake bacci cikin kwanciyar hankali yayi kafun ya furta “ stubborn girl na kusa yin maganinki “, yana kara rungumeta a jikinsa, ba dadewa shima bacci ya daukesa, baccin da zai iya cewa tun tsawan wasu shekarun baya beyi baccin da begaji dayinsaba kamar na yau.

Kiran sallar asuba na farko ne ya farkar dashi, a hankali ya fara mutsu mutsu da idanuwansa kafun ya bude su gabaki d’aya akan kyakkyawar fuskarta ,zubawa fuskar idanuwansa yayi Kafun ya gyara mata kwanciyarta yana barin dakin. Kusan mintuna 30 da fitarsa itama ta soma mutsu mutsu kafun ta bude idanuwan gabaki d’aya, adduar tashi daga bacci tayi a bayyane ganin babu kowa a dakin yasa ta sakin ajiyar zuciya , Wanka tayi cikin simple doguwar Riga kafun ta tayar da sallar asuba , tana idarwa karatun alkurani ta yi , ta dauki kusan good 2 hours tana karatun har saida gari ya fara haske tukunna.

Turo kofar dakin da akaine yasa ta Mayar da kallanta bakin kofar, zuba masa ido tayi ganin shirgarsa ta yau sak balarabensa , jallabiya ce a jikinsa white colour sai abun nadin larabawa red colour , harya karaso wajan bata sani ba sabida yanda ta zuba masa ido , sai da ya hura mata iska kadan kafun ta sauke ajiyar zuciya, cikin kunya ta sunkuyar da kanta,kafun ta furta “ina kwana”, ba amsa mata ba sai kallanta da yayi, kara maimaita gaisuwar tata tayi ,ynxu ma be kulata ba , sun kuyar da Kai tayi kasa ya daga da kanta, bakinsu ya hade waje d’aya kusan mintuna daya kafun ya zare bakinsa “ bakyajin magana kenan ko”girgiza masa kai tayi alamun Aah , waje ya samu ya zauna , dan turo masa bakinta tayi kadan “ina kwana “, har yanxu be amsa gaisuwar tata va, sai ma a wayarsa da ya dauka , tunowa da wacce take hannunta yasa taje ta dakko ta , binta da ido kawai yayi kafun ya dauke kansa, cikin girmamawa ta miko masa wayar be amsa ba sannan be kalletaba,”ga Wanka “ ta furta a sanyaye, kallanta yayi “Menene nawa “ wayanka ta basa amsa ,”it’s your” ya furta , da wani irin shock ta kallesa, batasan lokacin data rungumeshi ba,hannu d’aya yasaka ya tallabota gudun karta fadi” dady dagaske ta wace”, gira kawai ya dage mata,kara rungumeshi tayi lokaci d’aya wani kukan ya kara wace mata, dagasken gasken yanxu kukan take me taba zuciya , very tight king ya rungumeta a kunne ya rada mata “it’s ok” kafun ya dago da ita , kallan yanda hawayen suke zuba afuskarta yayi kafun ya harareta kadan”so kuke su mahma suzo suce miki na miki wani abun kenan ko”, girgixa masa kai tayi tana goge hawayan nata “nagode sosai Allah ya kara budi”ya ji dadin adduar da tayi masa sosai cikin zuciyarsa ya amsa da amin, a fili kuwa dan tabile baki yayi “we’re friends ai no need” jinjina masa kai tayi zata mike yakara gyara mata zama akan cinyarsa,yanda ake anfani da yawar ya nuna mata komai already daman anyi settling komai na cikin wayar, murmushin fuskarta kasa boyuwa yayi sosai ta nuna jin dadinta,ganin karfe takwas ta kallesa “dady me kake so kaci” Kai tsaye ya bata amsa da “you”,wara idanuwanta tayi “toh ni taya za a da fani” bece mata komai ba yakama hannunta suka fito falon sai ynxu ta ke kallan yanda komai na dakin yake a canje,janta yayi har wajan dining ganin abunci ajjjere ne tayi serving dinsa tare da kunun aya, kince yayi saida tasa hannu ta fara basa a baki, duk loma d’aya in yayi baya sakamar mata hannun sai ya tsotseshi,abun har kunya ya fara bata, sai da tayi feeding dinshi kafun shima yasoma bata dan dole take karba,suna kammala ci falo suka zauna tana zaune kan cinyarsa kallan gashin kansa take so take ta taba amma ta kasa, kamar yasan me take tunanin ya dauki hannun nata guda daya ya dora a saman kansa,murmushi ta saki tana kara tura hannayenta cikin gashin kansa me tsananin taushi da laushi, suna zaune ahakan sukaji an turo kofar da dan karfi, zaro idanuwa tayi waje tana kokarin sauka amma ya kara riketa ajikinsa sosai yana bin amrah da tashigo masa part kai tsaye da wani rin birkitaccen kallo daya firgitata, hatta karamin ture din hannunta saida ya fadi kasa tsabar firgita.


💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

Mss Lee 💖
💖💖GIDAN AUNTY💖💖
( a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee 💖

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

PAID BOOK

MAI BUKATAR COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 07041879581.

BOOK 1📕

Page 53 _ 54💖

Da wani irin rikitaccen kallo ya bita dashi , hannunsa daya yasa ya rike kugun tahee da ta kasa motsi, a mugun fusace ya furta “are you mad “, jikin amrah rawa ya fara ganin yanda ya fusata , cikin rawar baki ta furta “dan Allah kayi hakuri yaya king, ca akai na kawo muku”, guntun tsaki king yaja yana dauke kansa daga kanta, wasu zafafan hawayene suka sakko mata,” clean that trash now”da sauri ta gyada masa tana furta “toh toh”, tattare kayan tayi waje daya Allah ya temaketa ma abun be bare ba dan a kulle yake sosai a cikin wata yar roba, tunda ya rike mata kugu ta kasa motsi sai ma shakuwar data kamata, mikewa tayi niyar yi ya kalleta, ganin haryanxu fuskarsa a hade take yasa ta furta “ru..ruwa zansha “, jinjina mata kai yayi yana kara rike kugun nata kafun ya kalli amrah da tayi nadamar zuwa wajan ya fi a irga,”jeki kawo ruwa yanxu”,da sauri amrah ta ajje tray din hannunta ta nufa fridge a tunaninta king ne zaisha harda daurayo cup dan ta bakantawa , sai taga sabanin hakan ,ruwan kawai ya karba ya balle murfin tare da kaishin saitin bakin tahee, a hankali take shan ruwan sai da ta sha sosai kafun ta dauke kanta,”baki iya gaisuwa ba “ ya furtawa amrah dake duke a kasa, da sauri ta furta “kayi hakuri , yaya king ina kwana”be amsa mata ba har tsawan mintuna biyu da ya shude kafun ya sake cewa “ni kadai kika gani “ da Sauri ta kara girgiza kai tana hadiye kukan da yake kokarin zuwan mata “ au… aun.. aunty ina kwana” dan kallanta tahee tayi kafun ta dauke kanta itama “lapiya Lou “ kawai tace mata,wani kululun bakin ciki ne ya kama amrah tana dannewa ne kawai dan ba yanda zatayi, cikin rawar murya ta furta “yaya king sai anjima, aunty sai anjima” mai gayyar ko motsawa beyi ba balantana tasa ran zai amsa ,kasa kasa take kallan tahee dan tasan tabbas da batayi mata sallama ba saukar mari zataji a kumatunta,Zata tafi ya tsayar da ita “wait”, yna nuna mata dinning “clean it up and ki gyara wajan”magana tahe tayi kokarin yi itama ya bita da kallansa , shiru tayi kawai tana sun kuyar da Kai,goge hawayan da suka zubo mata amrah tayi , shekara biyar kenan tunda tazo gidan bata ko daukan tsintsiya amma yau sai gashi tana bautawa wacce tafi tsana a duniya , kanta kawai take gyadawa, sai data wanke komai sannan ta gyara dinning su king na zaune a falo, kamar munafuka ta karaso inda suke tana satar kallan king “nagama” bece da ita komai ba sai dauka tahee da yayi kamar baby ya hau kan steps da ita.zubewa amrah tayi a Wajan tana sakin saban kukan da ya tsaya mata a makoshi”ni king zai wulakanta agaban wannan kaskantacciyar” birgima ta somayi akasa kamar wata yarinya jin Alamun kamar takun tafiya yasa tayi saurin barin part din bakin ciki da ta kaici fal ranta.

Be sauke taba sai akan gadon dakin da suka kwana, kallan ta yayi kafun ya furta “me kikeso “,juyawa tayi kamar me tunani kafun tace “kayan sa wata nake nema”, hannunsa ya miko mata ba musu ta saka nata. Fitowa sukai daga cikin dakin sai bin ko ina take da kallo ganin duk ancanza komai data sani, steps suka fara takawa a hankali,kafun ya daga ta gabaki d’ayan ta ya karasa hawa steps din da ita, bata san lokacin da bakinta ya furta wow ba tana zaro idanuwanta, yanda komai yake a tsarane ya fi burgeta ,kamar ba akasar Nigeria ba ahaka wajan ya kawatu ina kawatuwa ta yanda ko baki bazai iya fusalta kyan wajan ba,”yayi miki kyau” yanxu ma gyada masa kanta tayi, bece mata komai ba ya jata cikin white room dinsa, nan ma sakin bakintayi tana kallan dakin musamman yanda dogayen labulen suke kawanye da dakin, remote ya ya danna take a wajan tabulen ya fara bude kansa,kara zaro idanuwanta tayi kafun ta karasa wajan balcony din, ganin yanda wajan shan iskar yake da shegen kyau shima komai nashi fari ne ,kamar karta motsa a Wajan jin yanda iska ke kadata,kallan glass din da yayi wa Wajan kwawanya tayi kafun ta dan Kai hannu kamar zata tava sai kuma cikin sauri ta dauke hannunta, jiyowar da zatayi ne sukai karo dashi,sunkuyar da kanta kasa tayi cikin jin kunya sam ta manta yana wajan,hannunta daya ya kama tare da dorawa kan glass din , cikin sauri ta zame jikinta daga nasa, bece mata komai ba ya kama hannunta suka nufi wata kofa dake cikin bedroom din, babu komai a ciki sai glass na kayan sawa shake a wajan masu shegen kyau hatta fitilar wajan ta banbanta da sauran,yana dannan wani bottom gabaki d’aya wardrobe din suka bude kayansa ne shake a wajan masu matukar tsada , daga ciki kuma akwai wasu kayan matan suma masu kyau, komai na cikin Wajan na mace da namiji ne hatta kayan sawar, gefe daya ma wasu takalma ne masu shegen kyau na mace sai kuma ta kalmansa masu shegen yawa suma , komai na bukata a kwai a dakin dan lissafa su bata lokaci ne , shima dakin sosai ya mata kyau amma ganin kayan mata a cikine yasa jikin ta yin sanyi daman ta san ba santa yake ba, wasu kayan sawa ya nufa doguwar abayace purple me shegen kyau , storn din jiki sai walwali suke dauka ,kayan ya mika mata kawai tare da ficewa daga cikin dakin, kallan kayan tayi kamar bazata saba sai kuma ta saka ,kallan yanda kayan yayi mata cif cif tayi kamar an aunata musamman in tayi motsi sai storn din suma sunyi motsi dakara , gashin kanta ta gyara kafun tayi rolling din mayafi, sosai farar fatarta tafito cikin abayar da ta saka , duk da tsananin kyan da tayi murnarta koma ciki tayi dan tasan baya bawa zaiyi ba dan baya santa. Kokarin cire wa ta farayi ya shigo cikin dakin sanye da kana nan kaya farare tas dasu, gashin kansa sai faman shining suke , bin jikinta yayi da kallo kafun ya karaso inda ta ke, dago da fuskarta yayi batare da yace komai ba ya soma bata wani hot kiss a kan labba, “Kinyi kyau”ya furta ta yanda bazata jiba tagadai ya dan motsa bakinsa.
Kama hannunta yayi da kanshi ya fara nuna mata ko ina na cikin part din musamman wajan kucciyar sa da sukaje, wani irin farinciki da shauki ne ya kamata , duk maganar da zatayi itama kucciyar sai ta kwaikwayeta,bata san lokacin da ta ke dariya ba , be hanata ba saida ta gaji dan kanta kafun ya kaita dakin gym dinsa, nan sai bin wajan take da kallo kamar a mafarki, wajan swimming fool dinsa ya kaita ,kinshiga tayi wai batasan fadawa ruwa, murmushi kawai yayi ya kama hannunta da gyar tahee ta shiga wajan tana makale a bayansa take bun ko ina da kallo, gabaki daya 3rd floor da 2nd floor sai da suka zagashi, ita kadai sai faman sakin murmushi take. Tare suka sakko down stairs hannunsu sarke da na juna, kallanta yayi kafun ya rada mata “ am going out now “, cikin dan jin kunya ta furta “A dawo lapiya ,Allah ya bada abinda aka je nema”lumshe idanuwansa yayi sabida yanda yaji dadin adduar,gefen fuskarsa ya nuna mata alamar ta sumbaceshi, dan ware idanuwanta tayi akansa, shima kwaikwayr yanda tayi yayi ,kafun ya kara nuna mata , girgiza masa kai tayi alamun bazata iya ba, gyada Mata Kai yayi kamar ya hakura sai kuma ya janyota jikinsa”tunda bazaki iya ba , ni I can do it”, kokarin kwace kanta tayi ya kara matseta ta yanda bazata iya kwacewa ba,knocking din kofar akai tayi saurin kallansa ,”ana knocking” , hakan yayi ai sai su kalli yanda zanyi miki kiss din ai,dan turo masa baki tayi tare da marairaicewa, “dan Allah ka sakeni “, lumshe mata idanu yayi,”dan Allah “ ta kara karye masa murya a shagwabe , yanda tayi sai ya burgeshi kamar karta dena,wani knocking din aka sakeyi, batare da ya ankara ba ta sumbaceshi a kumatu, kasa motsiyayi sabida yanda kiss din tazo masa a bazata, da mugun sauri ta kwace kanta tagudu upstairs tana dariya kasa kasa. Kwafa kawai yayi yana bin stair case din da kallo kafun ya bude door din, zaki ne tsaye a bakin door din , yana ganin king cikin girmamawa ya gaishe shi kafin ya mika masa wasu file , jinjina masa kai king yayi yana karban files din amaimakon ya koma ciki sai ya fita shima .


**** kan gadon ta ta fada tana sakin dariya kasa kasa, ita kadai tasan yan da take san bawan Allahn nan dan ya galadima ta komai arayuwa, ya kula da ita alokacin da take bukatar kulawa, ya zauna da ita alokacin da bata san wacece ita ba, indai ba butuluce itaba be kamata ta butulce masa ba , Ada tayi alkawari bazata taba nuna masa tana sansaba ,yanxun ma Hakane amma tayi alkawarin kula dashi iya iyawarta. Wani murmushine ya subuce mata musamman yanda ta hango face dinshi dazu bayn ta gudu, so take taje ta gaishe dasu ammey amma tasan hakan ba me yuwa bace kuma bata da number ammeyn balantana ta kira ta, wayar da ya bata ta dakko tana kare mata kallo, babbar wayace meshegen tsada dukda bazata iya kiyasta kudin taba. Snap tashiga ita kadai ta dinga daukar selfie, da Wanda tayi tana murmushi da Wanda take turo bakinta,da ka karshe ma gyalan tacire gashinn kanta y zubo, sosai tayi snap din ta, duk ciki babu na banza dan bakaramun kyau hotunan sukayi ba. Shaf shaf ta kara tsaf tace dakin , ta fito ta kara gyra floor 2 duk da yanda ya kasance kalkal dashi. Kamar ta gyara masa saman sai kuma taji tsoran hawa , hakura tayi da gyarawar Daidai zata sakko down stair ta hango wata yar karamar white farar takarda,dan karamin tsaki ta saki a fili ta furta “Allah ya shiryeni “ tana daukar paper har zata saka a trash bin dan karami dake wajan sai ta fasa tare da bude ta , Rubutun da tagani ne yasata jefar da takardar zuciyrta na tsananin bugu, kara kallan paper din tayi da kyau tana karanta ta , bata gasgata abunda yake ciki ba ta dan goge idanuwanta , d same kallarce a jiki” KILL YOUR HUSBAND” shine dai still a jikin paper din sai wani dan karamin zare ja da ya fado, a matukar rude taja baya in bata manta ba ta taba ganin zaren wata

Please Login or Register in order to submit comment