Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaban shine yayi mugun faduwa Jinin da yagani sosai a wajan, har yanxu tana a yarda ya barta sai ajiyar zuciya ta ke saukewa,gaba d’ayanta ya dauketa ya nufi toilet da ita,tana jinsa ta kara runtse idanuwanta, be tsaya da ita ko ina ba sai cikin jacuzzi, wani irin razanannan kara ta saki tare da yunkurawa zata tashi, saurin mayar da ita yayi cikin ruwan, yanxun ma wani saban kuka ta fashe dashi tana tureshi,ganin dagaske kokawar mikewa take yayi saurin danneta cikin ruwan, yarfa hannayenta kawai take tana kuka ta kasa magana ma sabida yanda take jin ruwan zafin na ratsata, har cikin kwakwalwarsa yakejin kukanta, jiyake dama shine ciwon yake jikinsa, me kwatarsa a wajanta kuma sai Allah, ya dade yana gasa mata ciwon kafun yayi mata wankan da kansa ganin da kyar take motsa jikinta,a cikin white bathrobe ya sa mata kafin ya fito da ita daga toilet din, amaimakon ya maidata kan gadon sai ya zaunar da ita akan sofa, da kanshi ya d’auke bedsheet din da ya baci,ya canza wani kafun ya Mayar da ita kan gadon,haryanxu taki yarta ta bude idanuwanta,ganin yanda jikinta yake da zafin zazzabine yashashi kashe ac yasa mata heater kafun ya koma toilet din, ba dadewa ya dawo inda take, kokarin tabata yayi da mugun zabura ta firgita harta fama ciwonta,murya a shake ta furta “ni karka tabani, daman kace bakasona,kamayar dani wajan ammey na”,zuciyar king ce ta dan harba,yasan tabbas sai yasha daru da ita, kokarin kara tabata yayi takarasakar masa wani saban kukan,kallanta yayi for second kafun ya fice daga dakin, tana ganin fitarsa tayi kokarin zuwa kulla kofar amma takasa tashi, bacci ta soma ji amma sabida tsora takiyin bacci data fara gyangyadi zata farka a za bure a haka harwani wahalallan bacci ya dauketa me tattare da gajiya.duk abunda take yana kallanta tacikin camera din dayayi setting a wayarsa yanxu ganin tayi bacci ne yasashi nufar inda take a hankali ya gyara mata kwanciyar gudun karta tashi,so yake ya dubata ko yaji mata ciwo amma yana tsoro da ya taba cinyarta zata ya mutsa fuska ganin hakan ne yasashi kashe mata deem light kafun ya tayar da sallah, sosai yayi nafila yana yiwa Allah Godiya , shikadai yasan farin cikin da yashiga yau ,lokaci zuwa lokaci yana sakin murmushin da kafun aganshi za a dade, yana idar da sallan shima magani kawai yasha sabida zazzabin dake jikinsa, simple Riga Mara nauyin ya saka mata a hankali kafun ya rungumeta tsam tsam a jikinsa kamar za a kwace masa ita,yana kwanciya wani daddadan bacci ya daukeshi da ya dade beyi irinsa ba.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

BUNKURE

Liyafa ta cigaba ,sosai su Dije suke sharholiyarsu yanxu, ba ma bintalon ba yanxu hatta Dije yawanta take zuwa ita da kawarta da tayi yanxu kullum sune hanyar zuwa wajan bokaye, da sunji kina cikin yar matsala zasu rakaki wajan malami da sunan temako, yanxu kwata kwata bintalo bata gidan , ta debe kayanta ta koma wajan hajiyarta da zama acewarta kudi da gata zata samarwa kanta,hakan da tayi kuwa ko a jikin Dije dan itama harkar gabanta take yanxu, hatta su kaka ta bawa Dije ta sa an asirce mata su gabaki d’aya gidan komai sai abunda tace akeyi hatta abinci idan Angama dafawa sai ansanar da ita sannan zata zubawa kowa da kansa. Su kaka ta bawa an fara ganin rayuwa dan Dije babu Wanda take dagawa kafa a cikinsu. Yanxu zaune take hannunta dauke da wani fasasshen mudubi sai faman shafa powder take yayinda kawarta take zaune tana charting, sai faman kas kas kas cingum din bakinta yake , tanayi tana tabe baki kafun ta kalli Dije ,”Dije baby yakamata kiyi sauri fa kinsan alhazawan yanxu basa jira in ba so kike muyi a Saran kudin da zamu dan samu ba “, washe bakinta Dije tayi “yi hakuri kawar alkairi wai Nima yau ina kara saka hodarne yanda alhazawan suka ganni zasu kara rudewa”tana kai zancanta ta ajje Mirror din tare da mikewa sanye cikin yar a tanfarta da mayafin da ta yafa kamar yanda yan mata ke yafawa . Ba bata lokaci suka fito tsakar gida ganin yanda gidan yayi kaca kaca ne yasata fara kwalla kiran sunan mutanan gidan , da daddai da daddai suka fara fitowa , maida kallonta tayi kan kaka tabawa kafun ta balla mata harara “ saunawa zance muke banaso nazo naga waje yayi datti amma sabida ku kunnnan ku na dabbobine bakwajin magana , Kema tabawa dan yanxu baza a sanya din ba, wallahi kishiga taitayinki, yanxu ina Sauri kafun na dawo inaso naga ko ina kal kal sannan na bar magi guda uku aje ayi Miya , kada ku kuskura a tava sai nazo komia dadewa da Zanyi kuwa”,hakuri suka fara bata duk da yanda ta zazzagesu basu jiba sai faman hakuri suke bata, wani banzan tsaki taja tana binsu da matsiyacin ko kafin su bar gidan , kawarta hajjo aunty kuwa sai faman dariya take a cikin zuciyarta.


➰➰➰➰➰➰➰➰➰

YOLA

Gabaki d’aya gidan ya rikice tun batan taheer kowa yashiga rudani sabida lokacin sadaukar dashi wajan bokan tsafi yayi, ko ina na gidan sai da aka bincika amma ba a ganshi ba, tsoro da firgicine ya kama ko wannan su musamman yanda suka fara zargin ko akwai me musu zagwan kasa, tun lokacin da aka sanarwa abar kauna batan taheer ta fara musu bala’in da ya girgizasu take a wajan tasa a ka yan ka mata samari biyar amma duk dahakan be yi mata ba , sako da lungu anduba a Garin YOLA da kewayanta amma ba a same saba, hatta kogan tsafin nasu ya kasa nuna masu inda yake, duk cikin su babu me kwanciyar hankali musamman wata 2 da bokanyarsu ta basu in ba haka ba za ‘a dau fansar rashin akan ahalinsu, wannan kalamai na bokanya ya razanasu,cikin rawar jiki suka sa aka fara musu bincike duk inda yake a kamosa a kashe shi .

➰➰➰➰➰➰
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

WASHE GARI

har makara yaso yayi da karya iya farkawa, yana motsawa itama ta fashe masa da kuka “ya salam” ya furta cikin kasan zuciyar sa,hannunta ya taba tayi saurin tune hannunsa tare da yunkurawa zata tashi, zafi taji sosia a kasanta da ya fi na jiya, wani saban kukan ta fashe masa dashi tana yarfa hannunta,”am sorry “ ya furta mata a hankali, wani kululun ba’kin cikine ya tokare mata makoshi “wai sorry “, bata kulashiba sai ma kokarin mikewar da ta sake kokarin yi a wannan karan fama ciwan tayi da yasata saurin rintse idanuwanta tana Jan baya, hannunta ya kama tayi saurin fusgewa bata san lokacin data bishi da wani kallo ba idanuwanta duk sun kunbura, ya bude baki zai yi magana yaji saukar muryata a dishe,”kamayar dani wajan ammey, bana sanka “, da Sauri ya kalleta yana jin yanda zuciyarsa ke harbawa da sauri sauri” please karki wahalar dani haka mana “, ya fada a zuciyar sa a fili kuwa dan peck yyi mata kafun ya furta “am so sorry wife”, sharesa tayi kamar bata jisaba sai ma wani saban kukan da ta fara raira masa kamar wacce ake wa wahayi, da sauri ya nufi toilet, be dade a ciki ba ya fito tare da daukanta kamar baby duk yanda take bugun kirjinsa ,direct cikin jakuzzi ya saka ta a hankali,kara ta saki da ta fi jiya tare da zabura da sauri ta mike cikin ruwan yayi saurin dawo da ita , batasan lokacin da wani karfi yazo mata ba ta soma kokawa dashi, ganin da gaske take ya sashi riketa da hannu daya , kuka ta fashe masa Dashi idanuwanta a kulle”daman kace baka sona ,shiyasa kakeso ka kashe ni, Nima bana sanka kamayar dani wajan oumma ta, oumma kinga yanaso yakashe miki ni tun ban kara ganin ki ba”tausayinta ne ya kamashi sosai ganin yanda take furta baya santa kuma bazata zauna dashi ba, Daidai kunnanta ya rada mata “am sorry “ kafun yacire tausayin sa a gefe ya gasata sosai duk yanda take kokarin gocewa, tare sukai wankan ynxu ma shiyayi mata , so yake ta kallesa amma takiyin haka sai ma daure fuskarta da tayi, simple Riga kawai yasaka mata wacce bazata takura mata ba, yazo zai mikar da ita ta boye hannun ,”zan iya da kaina”tana fadun hakan ta mike tsaye,duk da zafin da takeji in tayi tafiya amma taki bari ya temaka mata taku Hudu tayi tana kokarin faduwa ya rikewa kafun ya daga ta zuwa inda sallayar take,yana kula da yanda take tafiya, ga sallah ma da kyar take yi ,tanayi tana kuka, tana idar da sallah ta wanta a wajan ,da Sauri ya karasa Wajan ta bayan ya idar da sallah, ta bata yake so yayi Amma yana tsoran rigimarta, yanxu ma hannu yasa zai tabata ta fara masa masifa , bai taba sanin ta iya masifa ba sai yau, abun sai yaso bashi dariya da tausayi alokaci d’aya , tana masifan tana hawaye kuma taki yarda ta kallesa, be kulata ba ya daga ta gabaki dayanta ya mayar kan gadon ganin ta bazata iya tafiya ba. Be kuma ce mata komai ba ya fita daga dakin, kallan kofar tayi da manyan idanuwanta kafun ta d’auke tana share hawayenta,shigowarsa da tray a hannunsa ne ya ta d’auke idanuwanta daga kan kofar, da kanshi yayi serving dinta, ya kai bakinta tayi saurin dauke ba “bana ci” kawai tace masa zata koma , rike hannun yayi yanajin yanda kansa ke Sara masa kafun ya furta “Am so sorry please , kimu ko wana hukunci amma please kici abincin kisha magani “, kin kulashi tayi, yayi lallashin taki ji saida ya koma mata sak king dinsa ya hade rai kafun ta soma cin break fast din ,da kansa yake bata ganin yanda ya hade ransa kamar bashi ba . Tana kammala cin abincin mgani ya bata nan ma saida suka sha daru da ita kafun ta sha maganin, yana zaune a wajan bacci ya dauketa, ajiyar zuciya ya sauke kadan ganin bacci ya dauketa kafun ya dakko abubuwan bukatarsa,rigar jikinta yayi sama da ita ,sosai gabansa ya fadi ganin yanda ya ji mata ciwo , cikin kwarewa ya soma yi mata dinki, sai faman ya mutse fuska take ita kadai,kallan mitsitsin bakin ya kalla kafun ya lumshe idanuwansa “she’s killing me”,ya furta a fili, shima na bukatar hutawa shiyasa ba abunda ya tsaya yi Yakima gefenta ya kwanta yana rungumota.

Basu suka farka ba sai 11:00, shima kukan tahee ne ya tayar dashi, wani gashin ya sake mata sai faman shagwaba take masa gabaki d’aya ta birkita sa da salon ta ,ba abunda yake ce mata sai “sai am sorry , I love you “, rigima sosai take masa amma duk da haka sorry yake ce mata . Azahar nayi ya kawo mata wani lunch din shima da kansa yke bata abinci da gyar ya samu ya lallasheta taci nan ma magani ya bata, dukda ta fara jin radadin ya ragu Ba kamar dazu ba, yana ganin wani bacci ya kuma Dauketa shaf shaf ya shirya ya fita fuskarsa sai faman shiining take ,shi kadai yake sakin murmushi musamman idan ya tuno abunda ya Wakana a tsakaninsu. Ga baki daya ranar Beje ko ina ba yana tare da tahee da sai faman rigima take, masa akan ita bazata zauna a wajansaba,kanshi ba karamun daukan zafi yayi ba.


💖💖💖THE TALENT TROUPE 💖💖💖
Mss Lee 💖
07041879581

Book 1

Page 57

Tana idar da sallar isha’i tasaka rigimar bazata kara kwana a dakin ba sai dai ya mayar da ita wajan ammey,yasan abunda take cewa ba mai yuwa bane dan bazai taba yadda ba shima , a hankali ya kama hannunta da take kokarin kwacewa fuskarta a hade ta ki yadda ta kallesa,”am sorry please,ki canzamun wani punishment din amma banda wannan please, I can’t “,kuka ta fashe masa dashi”ai daman ka fadamun bakasona shiyasa kayi kokarin kashe nii, ni dai Allah ka mayar dani”,kwantaccen gashin kansa ya dan shafa kansa har ya fara yi masa ciwo, shi kadan yasan yanda kukanta ke cakarsa har cikin zuciyarsa, har yanzu zazzabinsa be tafiva shima,”look at me”, ya furta a hankali,kin kallansa tayi sai ma kara kawar da kan da tayi, gyada kansa yayi kafun ya taba button din rigarsa “ok shikenan kamar Kari kikeso bari muyi round two”,ba karasa zancan saba tayi saurin rike hannunsa da yake kokarin cire rigar jikinsa,hawaye har sun fara cika mata ido,yanda tayin ne ya so bashi dariya amma ya danne gudun karya kara janyowa kansa wani saban rigimar,a fili kuwa dan tabile bakin sa yayi kadan yana d’auke idanuwansa shima ,marairaice masa fuska tayi ashagwabe ta furta “kace mun fa bazaka kara ba”,be kalletaba ya cigaba da kokarin cirewa “toh yanxu na fasa tunta bakyajin magana “, da sauri ta girgiza masa kai” Allah inajin magana , tsoro nakeji “, yanda ta karasa dinne ya bashi tausayi, kara rike hannunta yayi kafun ya goge mata hawayenta “idan wannan hawayen suka kara sauka toh zanshanye kayana”,da sauri ta goge hawayen nata,”ya ciwonki fa”, kawar da kanta tayi kafun tace masa “Ni lapiya ta kalau”, Tohm shikenan zamu iyayin wani kenan” cewar king ,ynxu ma kanta ta girgiza masa “Allah ban warke ba wajan da zafi,kuma kace mun ka dena fa”, rungumota yayi a jikinsa “ am really sorry zawj, nayi leafi Amin afuwa, kinji, am so sorry “a hankali ta gyada masa kai”banaso ka dena mun kaji”, murmushi ne ya subuce masa a fuska Ba tare da ya amsa mata ba sai dan shafa mata bayanta da yake.”zaki iya tafiya”, kanta ta daga masa alamar eh, mikewa yayi shi yana miko mata hannu “let’s eat something kar ki wanta haka”, a shagwabe ta turo masa bakinta “uhm uhm bana jin yunwa “, lumshe idanuwansa yayi kafun ya kalli bakin nata “ you’re making me to ad more “, ai be kai karshen zancen nasaba ta rufe bakinta ruf,dariya ta so bashi amma ya Waske, taku ta somayi a hankali duk da zafin ya ragu makamar dazu ba, duk yana kallan yanda take tafiyar , da te makonsa suka karasa falon, da kanshi ya ja mata kujera kafun ya soma serving dinta, kadan taci tace ta koshi, be kyaletaba saida ya tabbatar ta koshi sosai kafun su koma ya bata magani.
wajan wanciyama sai da yasha rigimar bazata kwana a dakin ba, saida yace mata ba abunda zai mata sannan ta yadda ya kwanta a gefenta amma taki yarda ya tabata, shima din be tabata har saida yaga tayi bacci kafun ya rungumeta a jikinsa yana kashe gabaki d’aya dum light din.

➰➰➰➰➰➰➰

Zaune su amrah suke a falon Ammeey gabaki d’aya yan matan su ke su 5, ihsan, sumayya, firdausi,amrah da basma , kowa yana sabgar gabansa, su ihsan suna zaune kan carfet din Ammeey lokacin ta tafi part din data, suna shan fruit jifa jifa suna hira, amrah na kwance kan 3 sitter , basma kuma na zaune kan 1 sitter kafa daya kan daya yayinda take latsa babbar wayarta sai faman ya tsine take, cikin da rigar da sumayya take dannewa ta dan kallesu kafun ta kashewa su firdausi ido d’aya da dan karfi ta soma magana “ Nifa yau banga sis tahee ba, ko da mukaje part din ta kinga yaya king yace mana bacci take ,Anya kuwa su yaya bari dai nayi shiru,” kyalkyalewa da dariya sukayi jin iskancin da sumayya take wa su amrah dan sunsan halinta , itama firdausi dariyar take dannewa” uhm ke dai bari , a yan kwanakin nan da muke zuwa part din ai kinga baya hade mana rai kamar da yanxu fa har gaisuwar mu yake amsawa amma da dane ai bamu isaba,” wata dariyar suka kuma saki , ihsan sai satar kallansu basma take da suka cika fam , daga karshema basma mikewa tayi tare da barin part din ba tare da ta tanka musu ba, amrah kuwa harara ta dunga sakar musu, tayi alkawari kuwa sai ta haddasa musu wutar da bazasu iya kashewa ba,tunanin abunda zata musu take kafun ta dan saki murmushin mugunta tana barin wajan ba tare da tace musu uffan ba suma . Suna ganin ta bar wajan suka tafa gabaki dayan su , ihsance ta soma magana “wallahi bamu da mutumci, kun iya tsiya, ku kalli yanda fuskar su tayi kamar wanda aka fadawa mummunan abu”, itama firdausi dora tayi “ rabu da yan iska wai su soyayya , in banda ma iskanci irin nasu su kalli kamar yaya king suce wai sai sun aureshi ko da bala’I ai suma sun kwasowa dala da ganmu”, dan murmushi sumayya ta saki” Aah feedy, so sone fa, Kema kinsani duk Wanda ya kalli zubin yaya king ,ko baya sansa sai yaji wani abu aransa ,musamman idan aka samu marasa tsoran Allah, ko ni kunsani naso yaya king kamar raina tun bansan Menene so ba, har zuwan amrah muka fara samun sabani akan shi, amma yanxu na hakura dashi har abada Sabida yayi mana nisa nesa ba kusa ba , ku duba ku gani fa wa ya taba kawowa zai auri sister , duk da irin abunda mukayi mata bata kullacemuba lokacin da mukaje mata, gaskiya masu irin halin sister kadan ne”, jinjina kai sukayi gabaki d’ayansu kufun ihsan ta furta “ Allah sarki AKHII Allah ya jikanka da rahma, har na tuna lokacin da idan yaya king zai hukunta mu zai hana sa , ko uktiii ta hanashi, ban taba sani yana jin maganar su ba sai lokacin da mukai masa lefi akhiii moha ya bashi hakuri shi da ukhti, sai gashi kuwa beyi mana komai ba , da Yaya kabeer ne ko yaya haroon ina tunanin rugu rugu za suyi mana , duk da suma suna tsoran yaya king sosai kamar sunga mala’ika “,gabaki dayan su saida suka shiga jimamin mutuwar akhiiii kafun kuma su fara bada labarin laifikan da suke yake tema kar su da Wanda king yake Zanesu ukhti ke cecensa.” Ku naji fa Ance sun kusa dawowa suma duk da sun makale a turai sunki dawowa gida ,amma naji ance boss yace su dawo nan da one week kafun ransu ya baci” dariya suka sani kin yanda feedy ta kira king da boss, “itama ukhti fa taji anacewa zatazo tunda batazo bikin yaya king ba , ni har na matsu tazo dan nasan dole ko yayane sai anyi mana dinner indai taso kuma yaya king nasan zai amince ko sabo da ita ne”, gabaki dayan su kuwa jin hakan sai suka fara tsara yanda abun zai kasance duk da basu da tabbacin hakan, sunayi suna dariyar kansu musamman in suka tuno yanda king zai ci ubansu.


➰➰➰➰➰
➰➰➰➰➰➰➰

PART DIN DADA

Ga baki d’aya manyan iyaye ne zaune a falon dada , shiru ko wannansu yayi yana sauraran dada, saida ta kai aya kafun abeey cikin girmamawa ta amsa mata” dada Insha Allahu nan da sati d’aya zasu dawo kamar yanda kikai magana akai, sauran yaran ma insha Allahu zasuyi Auran lokaci ne kawai beyi ba”sallallami dada ta saki” zayeedu,lokaci ne kace beyi bafa , ko dai Bakuyi niyar aurar dazu yanxu ba, Ance zankada zankadan yaya haka babu aure , da alokacin mune ai sai ace baki akai musu , mu duk wacce tayi girman haka ai bazata auru ba, ni dai nagaji inasan ganin jikokina suna zagayeni, Allah ya ji kanka mahamuda Allah ya gafarta maka nasan da kana raye da tuni na fara ganin yan jikokina”, tana kai karshen zancenta ta fara goge hawayen da suke kokarin fitowa, gabaki d’aya sai da tasa jikin kowa na falon yayi sanyi musamman Wanda ta anbata da kowa bazai taba mantashi ba a cikin rayuwar sa, lallashinta suka fara gabi dayansu,kowa yana tofa albarkacin bakinsa. Allah sarki ummey tun lokacin da aka anbato moha jikinta yayi sanyi , addua ta fara masa cikin zuciyar ta , tana kokarin dannewa, amma duk yanda taso boyewan sai da abeey ya ganota, yayi shiru ne kawai bece komai ba dan shima abun yana taba masa zuciya har yanxu.sai da aka gama tattauna na tsawan lokaci kafun mahma ta kalli dada ,toh dada kingama anbato kowa zaiyi aure bamuji naki ba,wani babban salati kaka ta dauka tana kallan mahma da kananan idanuwanta “yanxu auta da yake kin mayar dani kakarkii ni zaki kalla kice na kara aure , toh Allah ya shiryeki dan nasan yanxu ina bude baki masu yan uwa zasu tarar miki” murmushi kowa ya saki dan kowa yasan da su uncle saleem yake , dukda haka kuwa sai da ya tanka,”wannan haqqun ne dada duk Wanda ya taba auta zamu shigar masa “, dan ta bile baki dada tayi tana mikewa tsaye “ daga kai har itan sai na Hana na ci muku mutunci sai naga me shigar muku, ni kunga tafiya ta bacci zanje nayi ma” gabaki dayansu seda fase sukai mata har ta bar part din kafin su dan tattauna gabaki dayan su, ana gamawa kuma kowa ya ya wuce part din da zashi.

➰➰➰➰➰➰
➰➰➰➰➰➰➰
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

Yau ya kasance Friday kamar kullum kiran sallah azubane ya tashesa, yanxun ma hakan ce ta faru a hankali ya bude fararan idanuwansa da suka kara yin haske dasu gwanin sha’awa, kallan yanda take rungume a jikinsa yayi, yana san mikewa amma bayasan tashinta, gudun kar lokacin sallah ya wuce shi yashi raba jikinta da nashi kadan yana gara mata kwanciyar tata, Dan ya mutsa fuskarta tayi bakinta ature,”stubborn , kina baccin ma bazaki hakura ba”.

Wanka yayi jikin brown din jallabiya da ta kara haska kalar fatar jikinsa , gashin kansa a kwance kamar na larabawa ya nadawa rawanin irin nadin larabawa, duk da fuskarsa ba a sake take ba amma wani irin annuri da annashuwane akan fuskartasa da ya kara wa fuskar tsa kwarjini da haiba, gabaki d’aya kamshin turarensa ma imperial majesty ya cika ko ina, hatta tahee dake kwance lafe kan gadon tana shakar kamshin turaren har cikin ranta.tun motsa warsa ta farko ta farka itama amma taki motsawa , yanxu ma tunanin yanda zata tashi take yi , fatanta d’aya Allah karyace yau ma a dakin zaiyi sallah. Yana kallan motsinta tun dazu yasan ta farka , karasawa yayi inda take kafun ya sunkuyo kadan yayi pecking kumatunta, ai kuwa da sauri ta ware idanuwanta akansa , dan Jan hancinta yayi kadan kafun ya furta “morning “,ya karasa yana tayata mikewa zaune, a hankali ta zuro kafafuwanta kafun ta mike tsaye, tana mikewa kuma ai ta koma tana rintse idanuwanta, ganin hakan yasashi saurin kamata” let’s me help you “, girgiza masa kai tayi,”zan iya, gashican ana kiran sallah kar jam’i ya wuce ka”,ta karasa tana kara mikewa kafun ta soma tafiya a hankali duk da yanda take kokarin daidaita tafiyarta,kallan kafar yayi kafun ya furta “ I have to check it again”, yana ganin shigewarta toilet din ya bar dakin bayan dan jotting din da ya bar mata a cikin wat small paper da wayarta a gefe. A toilet kuwa daurewa tahee tayi ta gasa jikinta sosai kamar yanda taga yayi mata kafun tayi wanka da alwala, sosai taji dadin jikinta kuwa, wani pink material mara nauyi ta saka a jikinta tare da feshe ilahirin jikinta da daddad’an imperial majesty me shegen kamshi, a hankali take yin komai , har ta idar da sallah tayi karatunta kafun , a hankali ta sake mikewa ta koma kan gadon, yar paper din data ganine yafi Jan hankalinta,tana daga gawa taga wani hadaddan handwriting me shegen kyau” take care of your self , I love you “, shine abunda ke jikin paper , bata san lokacin da ta fara murmushi ba ita kadai, rike paper tayi a hannunta kafun ta kwanta baccin da take ji na fusgarta, tun tana Hana kanta bacci har yazo ya dauketa gabaki d’aya .


****Yana shigowa ya tarar da ita kwance lullube da bargo ga kamshin turaransa da ya cika dakin sosai, doso inda take yayi yana kara jin kamshin turaran na kara karfi alamar Itace ta saka , yana sunkuyowa kuwa ga daki hancinsa, kwanciyarta ya gyara mata kafun yayi mata peck a goshinta. A maimakon ya koma bacci system dinsa ya dauka ya fara operating, ya dade akai kafun ya je ya dakko coffe dinsa

Please Login or Register in order to submit comment