Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yayansa hudu Nihal Maliha Shurafah da Shuraif Maliha itace me wayo tunda a qallah yanzu ta doshi shekara takwas itace take cewa uban nasu “Uncle naga Aunty tana fushi dakai kuma kun dawo gdannan dukkanku kuma jiya naga wani yazo gurin Aunty ta fita suna hira har suna dariya" tashin hankali wata uwar zabura da yayi ya fara qwalawa Hajiya kira Hajiya ta fito daga kitchen tana cewa “waikai wanne irin mutum ne kaine diba nan duk yayanka ne amma kaqi hankali ubanme zaka bani kake dokamin kira haka?"




Duban Hajiya yayi da idonsa da suka canza kala saboda bala'in yace “wato Hajiya yarinyar nan har kin barta ta fara kawo mana qartin banza gdannan ko to wlh bazai yuwu ba karyata zanyi na balla banza kuma naci uban duk wanda ya qara zuwa gdannan da sunan yazo gurinta haba Hajiya wannan ai cin fuska ne da wulaqanci ansan dai ina gdannan koma meke faruwa zanji baba megadi yasha fadamin yaga wani ya tuqota ya kawota gda ko yacemin yaga wani yazo gurinta to nida kashedi ne nayi muku wlh Allah hauka zanyi a gdannan ga duk wanda ya qara zuwa yayimin sallama da mata shima megadin bari naje wlh ya qara barin wani dan iskan ya shigo gdannan a bakin aikin sa”



Yana gama fadamin haka ya fice fuuuu kamar zai kifa riqe haba Hajiya tayi tace “wata sabuwa inji dan caca to uwarka zatayi maka a gdan da zakace baza azo gurinta ba zakuwa kaci kan uwarka wlh Hameed dani kake zance kama godewa Allah Umaimah najin kunyarka ni bantaba ganin yarinya me yakanar Umaimah ba ko baqo tayi da zarar taga yamma tayi zata sallameshi idan nace meyasa tace babu komai bayan nasan saboda Kaine"
Yana fita kuwa yayi katari Dr Sulaiman ya kawota daga mkrnta malaminsu ne tunda ya qyalla yaganta ya dauki so da kulawar duniya ya dora mata da farko Shuraif yakeja a jikinsa saidaga baya daya bincika yaji sun rabu da mijinta sannan ya fara fito mata da ainihin buqatarsa gareta da farko taqi sai daga baya Saudat ta rinqa tausarta tana fada mata shima kyakkyawa ne gashi fari gashi da gani babu tambaya naira ta zauna masa to daqyar dai ya samu ta saki jiki dashi suka fara gudanar da soyayyarsu amma qasan zuciyarta danqare dason dan'uwanta wanda bazata iya gogeshi a mind dinta ba don tasha kiran Dr Sulaiman da Hameed saidai yayi murmushi kawai yace “ sweet Allah yasa kisoni koda rabin son da kike yiwa Hameed ne sweet wlh inasonki fiye da tunaninki na fada miki bantaba soyayya ba saboda tsoron mata nakeji sai a kanki"



To yauma zancen da yake mata kenan tayi dariya ta lakace masa hanci tace “sai kuma ka fara da bazawara me yara biyu....” dora hanunsa yayi a saman lips dinta ya kashe mata ido yace “banason ji idan yayanki goma inasonki kuma zan rayu dake zan baki soyayya madara kuma nasani nima zaki soni irin son da kikeyiwa abu Shurafah koma fiy...." Aslm alaikum sukaji anyi musu sallama gabanta yayi mugun faduwa da sauri Sulaiman ya dubeshi yayi murmushi tare da shafa sumarsa ta fullanin asali yace “amin wslm" ya miqa masa hanu amma sai ya noqe ya kalleta da jajayen idanunsa ka cafketa da qarfi yace “dama abinda kikeyi a makarantar kenan idan kinje irin wadannan yan iskan kike kulawa to karatun ma kin daina" yana fadin haka ya figeta ya cillata parlour ya juyo shidai Sulaiman yana tsaye cike da mamaki “dama wannan shine yayannata da take cewa dashi tanajin tsoron yazo gda kada yagansa?" Ya tambayi kansa kafin ya samo amsa yaji muryarsa yana cewa “kada ka qara biyomin qanwa gda wlh zan daureka harsai igiya tayi rara" wuccewa yayi Sulaiman yayi saurin binsa yace “kayi hqr Yaya wlh bada wasa nake ba auran Umaimah zanyi....”









*UMMUH HAIRAN CE...*✍🏻
[1/31, 5:48 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *GU*






























Wani abune yaji ya caki zuciyarsa ya juyo da sauri yace “aure kuma wa zaka aura habadai wlh tun lkc be qure maka ba ka kama gabanka Umaimah ba matarka bace nayi mata miji" tsayawa Sulaiman yayi sororo har Hameed ya shige parlourn yana zuwa ya fara dukan dakin na Umaimah yana cewa “aure fah yace Umaimah aure? Wlh qarya yakeyi ya aureki" Daddy dake zaune ya miqe ya haye sama.
Ita kuwa tanajinsa taqi budewa muryar Hajiya taji tanayi masa mgnr ya juya ya fara sababi yana cewa ai duk ke kika daure mata gindin tacimin mutunci harni wani zai tara yacemin wai auren matata zaiyi wlh bazai yuwu ba kasheni kukeso kuyi" Hajiya ce ta haushi da bala'in da yafi nasa dole yayi qus sai zafin zuciya da sharar hawaye da yakeyi.




Tana zaune a dakin wayarta tayi qara tana dagawa taga Dr sunan da tayi saved din number Sulaiman da ita ta daga tace “ina fatan ranka bai baci da abinda bloody yayi maka ba" gabansa ne ya fadi yace “ bloody kuma wifey Hameed fah kenan?"
Ajiyar zuciya tayi tace “hakane shine mijina na farko shine Abu Shurafah Dr qaddara ce ta rabani dashi nasani yana Sona kuma yana kishina so wannan dalilin yasa nake boyeka gareshi saboda nasani bloody baya da juriya akan duk abinda ya shafeni nasan baqin kishinsa kuma nasan matsalarsa yanada matsalar heart attack shiyasa banason abinda zai taba lfyrsa ko banza yayana ne shine ya riqeni tun bayan mutuwar iyayena kuma uban yayana ne....”




Numfashi yaja me qarfi yace “ya isa Umaimah pls ya isa haka don Allah ki gabatar dani a gdanku wlh da gaske nakeyi inason yin aure nagaji da kadaici sweet inason nima naga yayana abokaina daga me yaya biyu sai me uku nima yakamata ace yanzu inada iyalina wlh ko bakya sona zan hqr na rayu dake sweet please” murmushi tayi tace “to yanzu ya kakeso ayi Dr?” numfashi ya sauke yace “ki bani dama na shigo gdanku na gabatar da kaina iyayena suzo ayi mgnr aurenmu Allah ni idan son samuna ayi bikinmu da wuri saboda a matse nake sosai inason naji abinda akeji"




Ta bude baki zatayi mgn taji Hajiya na cewa “Baby kizo Daddynku yana kiranki" amsawa tayi da to ta miqe tace “afwan D.S zanje Daddy yana kirana" amsawa yayi da “babu matsala amma don Allah ki duba buqatata Ummuh Shurafah" ajiye wayar tayi ta dauki mayafinta ta yafa ta fito saida gabanta ya fadi ganinsa kwance a parlourn ta raba ta gefensa zata wucce ya riqo hanunta ta juyo da sauri ta zuba idonta cikin nasa ya miqe zaune ko riga babu a jikinsa ya janyota da qarfi ta fada jikinsa ya matseta a qirjinsa yana goga mata gashin qirjinsa yace “kasheni kikeson kiyi ko Umaimah saboda kinga inasonki shine har kika dauko wani banza kika kawosh..." Daga masa hanu tayi ta janye jikinta daga nasa ta hade rai sosai tace “banaso kada ka qara zagarmin mijin da zan aura Hameed duk yanda nake mutunta ka da baka haqqinka a matsayinka na yayana hakan baiyi maka ba saika shiga rayuwata to gaskiya banas....” bai barta ta ida fadi ba ya dora lips dinsa saman nata ya riqe qugunta sosai yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya qoqarin qwacewa take yaqi bata dama neman zura hanunsa yakeyi a rigarta ta qanqame jikinta ta saki kuka daidai lkcn Hajiya da Daddy suka sauko daga saman turus suka tsaya Hajiya tayi saurin rintse idonta ganin yanda suke kokawa bilhaqqi yana neman balle bottle din rigarta Daddy ne ya daka masa wata uwar tsawa hakanne yasashi dakatawa da abin da yake shirin aikatawa ya hada kansa da kujerar yana mayar da numfashi ita kuma ta miqe da gudu tana kuka ta qanqame Hajiya wani takaici ya cika zuciyar Hajiya tace.




“Kin fara biye masa ko to wlh baku isa ku cusa mana baqin cikin da kuka qunsa mana a baya ba saboda haka Daddy yau dai ka ganshi da idonka wannan shaidanin yaron ko Umaimah bata bashi hadin kai ba ana kwana ana tashi saiya yaudareta balle itama qwaryar sama ce ke dukan ta qasa haline yazo daya harijan banza da wofi to wlh ki fito da miji kiyi aure duk kwartancinsa ai baya biki gdan mijinki ba ko” kuka takeyi sosai tace “wlh Hajiya ba gurinsa nazo ba Kiran da kikace Daddy yanayi min shine ya fito dani shi kuma ya tsayar dani” Daddy ne ya kamo hanunta yace “waye yazo gurinki dazu?" “malami nane Daddy” “meye ya kawoshi ance ba zuwansa na farko kenan ba ko?" Dagakai tayi tace “eh zuwansa na uku kenan wai aurena yakeson yi" murmushi yayi yace “alhmdllh anzo gurin to ke ya kika gani kina son sa?"



Kallon Hameed tayi daya dago kansa da sauri ya zuba idonsa akanta yanason yaji me zatace sake maimaita tambayar Daddy yayi yana kallon Hameed din cikin in...ina tace “aa.. eh Daddy" murmushi yayi yace “amsa daya nakeso ki bani eh ko aa” kawar da kanta tayi da sauri tace “eh Daddy” tana fadin haka ta kwasa da gudu ta fada dakinta shima miqewa yayi da sauri yace “haba Daddy meye hakan wanne irin tanasonshi yanzu aura masa ita zakayi Daddy kada kuyimin haka ku bakwa kishina ne wlh duk ranar da kuka daurawa Umaimah aure da wani nama mutu na gama na kwanta da ita wani ya kwanta da ita..."



Bige masa baki Hajiya tayi tace “to ai matsalar tace tanasonshi saboda haka ka shafawa kanka lfy ka nemi mata ka aura ka huta da kwana kai daya kana fama da azumi kullum" Daddy ne yace “idan kin shiga kice da ita nace ta turomin shi gobe inason ganinsa" amsawa tayi da “karkaji komai Daddy Sulaiman mutumin kirki ne kullum yazo gurinta saiya aikomin da gaisuwa yanzu Umaimah zatayi aure me yanci" maganganun iyayen nasa mugun caccakar zuciyarsa sukeyi yaja qafa daqyar ya shige dakinsa ya fada saman gadon zuciyarsa na tafasa ya miqe da sauri ya dauki magungunansa yasha ya koma ya dauki wayarsa ya kira number Umaimah amma sai yaji user busy ya sake kira haka a qarshe dole ya hqr ya qyaleta.





A ranar da Daddy yace yanason ganin Sulaiman washe gari yazo suka zauna da Daddy sukayi mgn bai fada Mata yanda sukayi ba washegari Hajiya ta aiketa gdan Aunty Zarah a ranar magabatan Sulaiman sukazo gdansu suka kawo kudin aurenta dubu dari biyu da hamsin aka tsayar da lkcn biki wata daya masu zuwa washegari dake juma'a Hajiya ta cire Shuraif daga nono itadai batayi mgn ba kuma bata tambaya ba sai bayan kwana biyu Sulaiman yake tsegumta mata cewa an kawo kudin aurensu har anci kwanaki uku.
Batayi wani farin ciki ba sukayi sallama ta ajiye wayar hakanan Hajiya ta rinqa gyarata ta kowanne bangare gyaran jiki gyaran sama da qasa babu inda Hajiya bata yiwa gyara irin nasu na shuwa ba.



Shi kuwa Hameed tun ranar da aka kawo kudin auren Umaimah yake wani mugun zazzabi da ciwon qirji fushi yakeyi da Daddy sosai musamman da Daddy yace shine zai karbi waliccin auren Umaimah......







*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/1, 8:18 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_GU_*















Haka kwanaki sukayita tafiya rayuwa taqiwa masoyan dadi duk yanda Umaimah takeso ta watsar da lamarin Hameed ta kasa jinsa takeyi a cikin jininta ciwon da yakeyi yafi komai daga mata hankali musamman a yan kwanakin nan da abin nasa yaci tura ranar daya rage saura sati daya bikin Umaimah dangin Sulaiman suka kawo lefenta ya zuba mata kaya sosai babu harkar qaranta komai na budurwa yakeyi Mata rawar kafa yake sosai akan auran amma abu daya da yake sanyaya masa jiki yanda amaryar tasa bata nuna masa farin cikin.




A wannan ranar kuma Hameed jikinsa yayi tsanani sosai Daddy ne ya matsa masa sukaje asibitin aka bashi gado hankalin Umaimah kwata² baya jikinta dauriya kawai takeyi bisa tursasawar Hajiya da take qarfin halin itama ake hidimar bikin itadai Umaimah ko lalle batayi ba saboda duk dakiyarta lkcn da suka fita domin zuwa gdan kwalliya ranar dinner ta roqi Saudat da Sa'ud akan su taimaka su rakata ta dubo jikin bloody dinta da farko qi sukayi Saida sukaga yanda hankalinta ya tashi sannan suka yarda sunayin parking ta bude murfin ta nufi dakin da yake da sauri cikin saa kuwa babu kowa ta tsaya ta zuba masa ido yanda duk aka daure masa qirjinsa da na'urori shine yafi komai daga mata hankali gashi kwance kamar gawa sai idanunsa da suke motsi kawai yana ganinta ya fara qoqarin miqewa tayi saurin matsawa jikinsa ta dora kanta a saitin fuskarsa ta qanqameshi ta saki kuka a haka su Sa'ud suka shigo suka tarar dasu tana kuka shi kuwa bama zai iya kukan ba sai zafin zuciya kawai daqyar ya motsa bakinsa yace.




“Shi..shikenan na rasaki Umaimah na roqeki kada ki manta dani a addu'ar ki idan bazan taba yafewa duk wanda ya rabani dakeba Umaimah nasani kema saboda babu yanda zakiyi ne zaki auri wani amma ki riqe kuma kisa a ranki watarana zaki dawo gareni Umaimah don Allah idan kinje kada ki bari ya tabamin ke idan na tuna abinnan zuciyata neman tarwatsewa take bansan meyasa naqi mutuwa ba....”



Rufe masa baki tayi tana girgiza masa kai tace “bazaka mutu ba Hameed zaka miqe kaci gaba da rayuwa kayi hqr haka Allah ya tsara mana...” ji tayi an janyeta tana juyowa taga Sulaiman ne suka shigo da mahaifinsa da Daddy kuka ta saka me sauti ta fada jikinsa ta qanqameshi tana kuka tace “kayi hqr dani a yanda nake D.S wlh inason sabawa zuciyata dakai amma na kas..." Rufe mata baki yayi yayi murmushi me ciwo yace “kiyi hqr ki daina kukannan banaso inasonki zanyi hqr dake a duk yanda kika zomin kuma zan riqeki amana da zuciya daya nayi alqawarin saina goge miki duk wani namiji dake zuciyarki nazama nikadai ne nake mulkinta"





Yana fadin haka yaja hanunta suka fice ya sata a motarsa Saudat Alfah da Sa'ud suka biyosu ya zage sai goge mata hawaye yakeyi duk da yanda yakejin kishinta a ransa amma ya kasa nuna Mata saboda yasan nunawar qarin shigarta damuwa ne Sa'ud ce ta leqo tace “ango kabamu aron amaryar taka yamma tayi kwalliya zamu" kallonta yayi yace “kuyi gaba zamu biyoku" hakan kuwa akayi shine yakaita har gurin kwalliyar Saida ya shigar da ita har ciki ya sumbaci hanunta yace “ki kulamin da kanki iya yau na baki amanar kanki daga gobene"




Qasa tayi da kanta tana murmushi yayi murmushi yace “yanzu hankalina ya kwanta matata tayimin murmushinta me tsada" juyawa yayi ya fita yana daga Mata hannu ta bishi da kallo tana masa murmushi shima yanayi mata kiss ya jefo mata ta kumayin dariya har haqoranta suka bayyana.




Hakanan akayi musu kwalliyar suka fito suka tafi gda suna zuwa gda motocin daukar amare sukazo 6:30pm suka isa gurin dinner ba tare suka taho ba amma tare suka shiga anatayi musu tafi da ihu suka isa gurin da aka tanada dominsu suka zauna daqyar yasata ta tashi suka shiga filin rawar lkcn da M.C din ya kirasu suka dan taka kadan kai ranar Umaimah taga rashin kunya a gure D.S ko kunyar mahaifiyarsa bayaji da Hajiya da suke gurin kamota yakeyi tako ina suna hotuna itadai hawaye kawai takeyi da ta rasa na meye farin ciki ko baqin ciki basu tashi ba sai sha biyu suna zuwa gda wanka kawai tayi ta kwanta tana kwanciya D.S ya kirata yana fada mata wai yau bazai iya bacci ba duk ta tayar masa da hankali ji yake kamar ya janyo gobe itadai murmushi kawai tayi masa sukaci gaba da hirarsu waishi ya matsu yaji abinda akeji.




Washe gari qarfe goma daidai na safe aka daura auran Dr Sulaiman kabir Yola da Umaimah Ahmad Hameed Shuwa farin ciki gurin Sulaiman baa cewa komai ita kuwa da aka sanar da ita an daura auran kamar yanda Hameed ya suma haka itama ta yanke jiki ta fadi hankalin gdan biki ba qaramin tashi yayi ba shidai Daddy baa gama bikin dashi ba ya dauki dansa suka wucce India ita kuwa amarya Umaimah lbr yana zuwarwa Sulaiman babu kunya ya shigo cikin gdan har dakinta ya shiga ya kuwa yi saa babu kowa ya mayar da qofar ya kulle ta bude idonta a hankali da suka kumbura saboda kuka zama yayi a kusa da ita ya dagota jikinsa yace “ni bantaba ganin aure irin namu ba sweet Ina cikin farin ciki ke kina baqin ciki yakamata ki yarda da qaddara ba duka abinda zuciya takeso take samu ba ki qaddara dama Hameed ba shine mijin da zaki qarasa rayuwa dashi ba wlh Umaimah inasonki kuma zanyi miki komai donki yarda da hakan babu saki a tsarin aurena dake aurene na mutu ka raba”






*UMMUH HAIRAN CE...* ✍🏻
[2/1, 1:44 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_GU_*





























Kuka takeyi sosai tana shigewa jikinsa shima yana qara matseta yanajin ninkin sonta da tausayinta ya yarda so halitta ne duk kyansa da kwarjininsa amma Umaimah kuka takeyi saboda an daura aurenta dashi wasu hawaye masu zaffi suka zubo masa suka diga a dokin wuyanta yace “kiyi hqr Sweet da zan iya halatta miki Hameed dana halatta miki shi saboda nasani shine burinki" saurin dago da kanta tayi tace “wlh ba hakanne yake sani kuka ba tunanin halin da yake ciki shine yafi dagamin hankali D.S aman jini fah yakeyi..."




Rufe mata baki yayi da nasa ya lumshe idonsa a hankali yanajin wani farin ciki na mamayar zuciyarsa yau da Umaimansa zai kwana a hankali ya janye bakinsa daga nata yace “zamu hadu anjima kiyi hqr ki cire komai a ranki ki barwa Allah ikonsa zan tayaki da addu'a Allah ya sassauta miki son mijin daba naki ba kiso mijinki me qaunarki” murmushi yayi mata ya daga Mata hannu yace “mu hadu a matakin qarshe" ya juya ya fice da sauri batasan sanda tayi murmushi ba sanyi Halin Sulaiman yana burgeta a hankali ta daga hanunta tace “Allah ka cusamin son mijina Allah kabani ikon yimasa biyayya Allah kada ka jarabceni da jarabta irin ta gdan Uncle Hameed"




Haka ta yini a kwance tana juyi Saudat Alfah da Sa'ud da Sarah sune suka zama amarorin bikin suna tausayin Umaimah suna tausayawa Sulaiman da irin rawar qafar da yakeyi akan Umaimah dashi aka zage akayi aikin shirya gdan bai iya barin masu decorations din su kadai ba abokansa sai tsiya sukeyi masa wai ba sabon ba wasu suna cewa dashi wai Allah yasa ba auran kisan wuta tayi dashi ba da haka har magrib tayi aunty Jameela Zarah da Hajiya da Hajiya Kaka sune suka sanyata a gaba suna yi mata nasiha akan ta riqe mijinta amana kada ta cutar dashi domin shi da zuciya daya yake sonta kuma ya yarda zai rayu da ita duk da kasancewarsa saurayi sannan yan'uwansa basu nuna mata wani hali na tur ba mahaifiyar mijinta kamar ta goyata tanata godewa Allah daya nuna mata lkcn auran dan nata sama da shekara talatin da uku amma ko zancen budurwa akayi masa sai ya kama fushi da mutane yau gashi shima yayi mata saidai fatan zaman lfy.




Sosai Hajiya tayi mata nasiha me shiga jiki tare da fitowa ta fada mata bazata taba yafe mataba idan tayi qoqarin kashe aurenta saboda Hameed ta sake fada Mata maganganun da mutane sukeyi akan cewa auren kisan wuta tayi amma D.S ya toshe kunnensa yace yaji ya gani.
Haka yan daukar amarya sukazo tana kuka mecin zuciya wai yau ita Umaimah zaa dauka akai gdan wani a sunan mata? Tana tuna haka ta sake rushewa da kuka hakanan uwar mijinta ta ruqota a jikinta tanata bata hqr da sanya mata albarka Hajiya Sa'adatu mahaifiyar Sulaiman cewa tayi dakanta zata daukowa danta amaryarsa aikuwa haka ta sanyata a mota ta kwantar da ita a jikinta tace “kiyi hqr Umaimatu wlh na tayaki murna kin samu miji saidai fatan dorewar zaman lfy bawai yabon kai ba bakuma dan Sulaiman dana bane nasani zakiyi hamdala kiyiwa Allah gdy yayi miki sauyi na alkhairi na jima Ina fadawa Allah yayiwa junior zabi na qwarai kuma na yarda yayi masa”




Da wadannan kalaman motocin sukayi parking sauran mutanen suka firfito suna ta guda gabanta ya sake faduwa Hajiya Sa'adatu ta kama hanunta Aunty Zarah ta kama dayan suka nufi gdan wata waqa me sanyin sauti yana tashi sunan Umaimah ne da Sulaiman yake tashi a cikin waqar haka suka ratsa har cikin parlourn saida Hajiya Sa'adatu tace “kiyi addu'a kafin ki zauna a bakin gadonki cikin aminci" saida tayi addu'ar sannan ta zauna Hajiya Sa'adatu tayi murmushi tace “alhmdllh yau ubana ya angwance Allah na gde maka Allah yasa bani na dauki jikoki na" murmushi Aunty Zarah da Aunty Jameelah sukayi suka amsa da “amin" sannan suka fara zamewa suna guduwa ya rage gdan daga ita sai Sa'ud da Sarah Saudat Alfah mijinta yazo sun tafi tashi sukayi suka fara gyara mata gdan saida suka gama tsaf sannan suka koma haushi da takaici ya cika Sa'ud tace.




“Nifa kukannan ya isheni Umaimah wlh ko lahira aka kaiki yau yakamata ace kin hqr da kukannan mijinki yana sonki kuma kece kika kawoshi kikace kinaso saboda haka kiyi hqr ki karbeshi kiyi masa duk abinda ya dace" Sarah ce ta cafe zancen da cewa “manta da yar banza anjima kadan lbrn zakiji ya canza..." Bugun qofar ne yasasu yin shiru suka juya da sauri bude qofar yayi ya shigo da sallamarsa ya sauke idonsa akan ya sauke ajiyar zuciya yace.




“Kuyi hqr na katseku ko bari na baku guri" saurin amshewa Sarah tayi da cewa “aa Yallabai ai kayi mana kara ma muma tafiya zamuyi gdajenmu kaima ka huta" murmushi yayi yace “ok kuzo ku gaisa da baqi a waje yana mgnr yana matsawa kusa da ita hanunsa yasa ya bude fuskarta yana murmushi yace “masha Allah wannan rana da girma take" kamo hanunta yayi ya miqar da ita yajata ya hadata da jikinsa suka fita ihu mutanen dake parlourn suka dauka yayi dariya ya zaunar da ita sukayi ya zaunar da ita a saman kujera sukayi raharsu sukayi musu sallama suka tafi tare suka tafi dasu Sa'ud ya rakasu ya dawo ya kulle qofar parlourn ya qarasa ya dagota yana sauke ajiyar zuciya ya riqo hanunta suka nufi dakin yana maqale da ita a jikinsa yace “banyi tunanin zuwan wannan ranar kwana kusa ba Sweet wlh yau Ina cikin farin ciki wanda bazan iya misaltashi ba muje muyi alwala muyi sallah mu godewa buwayi gagara misali"






*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/1, 7:30 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_GU_*





















Tare sukayi alwalar suka fito ya shimfida musu sallaya sukayi sallar gdy ga Allah rakaa biyu yayi musu addu'a sosai sannan ya dauko kayan daya shigo dasu ya baje a flat ya zuba mata lemo a cup ya dage saitaci haka sukaci abincin yana kallonta yana mata murmushin qarfafa gwiwa suna gamawa ya tashi ya debe kayan ya fita dasu ya dawo lkcn ta tashi ta shiga bathroom tayi brush ya cire kayansa ya rage dagashi sai boxes nd singlet gabanta ya fadi sosai ya matso kusa da ita ya ruqo weast dinta yanajin sha'awar kasancewa da ita ya dora kansa a wuyanta yana lasar gefen kuncinta yace “ina sha'awar raya daren nan amma kamar kin gaji ko?"



Wata irin faduwar gaba taji ta lumshe idonta yayi ajiyar zuciya yace “bazan takura miki ba kuma bazan miki dole ba amma nasan zaki tausayawa tuzurun da sai yau Allah ya azurtashi da mata" yana fadin haka ya fara zare mata kayan jikinta ya ta rintse idonta Hameed ne kawai yake fado mata a ranta daga ita sai pant da bra ya sanya hanunsa ya kashe switch din dakin ya kunna lamp ya dagata cak ya dorata a gadon idanunta a rintse ya balle bra din ya dora tattasan hanunsa da wani salo me shiga jiki yace “ahhhh!” sake rintse idonta tayi ya rinqa matsa nononta da murza nipples dinta a hankali ya jima yana murzawa kafin yakai bakinsa ya kama ya fara tsotsa yana tura hanunsa cikin gashinta yana lumshe ido tare da busa mata iskar numfashinsa breast dinta cikakku sunyi mugun tafiya da imanin D.S sosai salonsa yake shiga jikin Umaimah a da dabara da wayonsa har ya cusa mata feeling din abun ya

Please Login or Register in order to submit comment