Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sameta a kwance inda ya barta ya haura gadon ya yaye mata bargon yakai hanu zai tasheta kawai sai yaji zazzabi a jikinta salati ya saki yace “meye kuma ya kawo zazzabin bloody naga a hankali nayi miki"




Kama hanunsa tayi ta miqe zaune ta dubi agogo cikin qarfin halinta tace “kwana biyu kenan da nake fama da zazzabin kawai daurewa nakeyi qarfe nawa ne daurin auran naka ne" tsuke fuska yayi yace mata “ba wannan ne a gabana ba so nake naji meye yake damunki" ajiyar zuciya tayi ta lumshe idonta yayi murmushi ya dauki wayarsa ya kira Dr Saleem yace “gamunan zuwa da Hearty zaka dubamin ita Ina zargin kamar nayi ajiya fah" bai jira abinda zaice ba ya kashe wayar ya dauki hijjab dinta yasa mata suka fito daqyar tasha tea saboda tashin zuciyar da takeji yana riqe da hanun Shurafah da take koyon tafiya suna fita sukaci karo da Aunty Zarah da Sa'ud da Sarah sukayi tsalle suka rungume juna su ukun Aunty Zarah kam wani mugun kallo take watsawa Hameed saboda tafi kowa sanin halin ballagazancin matar dazai auro tace.



“Aa ango ya naganka a gida unguwa tanacan ta dauki harami zaa daura auran Salamatu da Sallau sallamamme asararre" sosa kansa yayi ya dauke wata siririyar qwalla a idonsa yace “wlh ni nama manta saida bloody ta tunamin kuma sai naji jikinta da zafi shine zamuje a dubamin ita" sakin Sa'ud da Sarah tayi tace “kuyi hqr Ina zuwa yanzu aunty ku shiga ganinan" juyawa tayi tabi bayansa ya bude mata motar ta shiga shima ya shiga yaja suka fita a bakin get taga motar qawarta ta makaranta Saudat Alfah takuwa riqeshi tana dariya tace “Abu Shurafah kaga Saudat Alfah ma da nake bakalbr jiya itama tazo" kallonta yayi da rinannun idanunsa ya kawar dakai yace “yanzu saboda zanyi aurene ake taruwa haka a gdana Umaimah wadannan duk nasan zugamin ke zasuyi don Allah kada ki biye musu duk abinda zasu fada miki qaryace nine kawai zan fada miki gsky" jikinta ne yayi sanyi ta dago ta dubeshi tace “wai da gaske yau zaa daura maka aure da Salma Abu Shurafah?"







*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[1/28, 8:44 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *G.U*















Dagowa yayi da sauri ya kalleta hawayen da yake qoqarin hadiyewa suka zubo masa yace “nima jin abin nake kamar tatsunniyar tsoffi bloody waini Hameed Adam Hameed Shuwa zaa sake daurawa aure da wata watanma wai Salma Umaimah wannan abin da ciwo Allah Kaine ka halliceni ka halicci Salma Allah indai da nufin cutar dani da matata jinina takeson shigowa gdana Allah kayimin maganinta Allah kafimu sanin abinda ke boye game da wannan masifaffen auren Allah ka kawomin dauki Allah idan na tuna da yau zaa dauramin aure da wannan baiwa taka Allah zuciyata zafi takeyi bloody ciwon zuciyata neman tashi yakeyi"



Cikin kuka da baqin kishi da tausayin kanta ta daure daqyar bisa taimakon addu'ar da takeyi a zuciyarta tace “kayi hqr" iyakar kalmar data iya furta masa kenan yayi parking a asibitin ya kashe motar ya ruqo hanunta qamqam a cikin nasa jikinsa na wata irin rawa yace “a... akwai matsala Umaimah dauki wayata ki bude ki kiramin Dr Saleem Umaimah yi sauri zuciyata zata tarwats....”



Yana fadin haka yana qara qanqameta qirjinsa yana bugawa da qarfi, cikin Kaduwa da tashin hankali ta lalubo number Dr Saleem din ta kirashi bugu daya ya daga ta kara a kunnenta yace “hello ango mijin amarya amma Umaimah nake nufi..." Da sauri ta katseshi da cewa “na shiga ukuna Dr bloody mutuwa zaiyi zuciyarsa ke masa ciwo..." a firgice yace “what? Umaimah kuna Ina?" Cikin kuka tace “muna cikin asibitinku ya kawoni a dubani kuma shima yace zuciyarsa tarwatsewa zatayi jikinsa sai rawa yakeyi" da sauri ya kashe wayar ya fito kafin yazo tuni Hameed ya gama fita daga hayyacinsa amma duk da haka tana maqale a jikinsa yaqi sakinta sai kuka takeyi tana jijjigashi tana danna masa masa qirjinsa saboda tasani tun tana qarama idan ciwonsa ya tashi haka takeyi masa.




Qarasowar Dr ne yasata ta zare jikinta daga nasa daqyar daidai lkcn kuma wayarsa ta shiga ring batabi takan wayar ba sai taimakawa Dr Saleem data shigayi suka fitar dashi aka dorashi a kujerar tura marasa lfy suka nufi heart attack word da gudu takebin masu turashi din saboda suma gudun sukeyi suna shiga suka nufi emergency din word din suka kwantar dashi suka fara bashi taimakon gaggawa daqyar Dr Saleem ya lallabata sukaje itama ya dubata ya tabbatar mata tana da shigar cikin sati biyu da kwana biyu tayi farin ciki amma damuwar da take ciki ta danne farin cikin ta fitowa tayi ta zauna a reception tayi tagumi daidai lkcn Daddy ya shigo asibitin lkcn 11:30am yayi parking ya shiga word din da sauri hango Umaiman ne yasashi nufarta da sauri yace “mamana meye ya kawo tashin ciwon nan wlh ina kwance a gda Alh Jamilu ya kirani yake fadamin an taru gurin daurin aure shida zai karbi abinsa baizo ba so shine naketa kiran wayarsa najita a kashe na fito na nufo gdan naku don nasani yanda yake dumin wannan qaddararren auren lfy bazata hanashi fitowa ba Ina zuwa Zarah take sanar dani kun tafi asibiti so shine na Kira Dr yake fadamin ke ya raqo a dubaki saboda yana zargin kinada shigar ciki kuma sai ciwonsa ya tashi meye yayi dalilin hakan?"



Miqewa tayi ta shige jikinsa ya rungumeta sosai ta saki wani marayan kuka tace “Daddy na tabbatar da bloody bayason Salma Daddy bayason auran Salma kuyi masa sauqi wlh qaddararmu ce Salma ni dashi Daddy ya sanar dani komai ya fadamin yanajin tsanar Salma a cikin jininsa amma kuma yakasa bijiirewa auran ta baya tunata idan baya tare da ita sai ta kirashi kota nemeshi kuma idan ta kirashi baya iya bijirewa umarninta Daddy ba fushi zakuyi da Bloody ba addu'arku yake buqata wlh Daddy baya cikin hayyacinsa kagafa yanzu kawai mgnrta nayi masa ciwonsa ya tashi wannan wacce irin masifa ce Daddy me Salma take nufi damu? Meyasa ta nace sai ta shigo cikinmu ta rusa mana farin cikinmu?”



Ajiyar Daddy yayi me qarfi ya sanya hanunsa ya dagota ya fara share Mata hawayenta yace “akwai manufar wannan shedaniyar yarinyar akansa koma dai menene yau dai an daura aure Umaimah tun lkcn da Hameed yayi min mgnr auran yarinyar nan na nuna rashin amincewata amma naga ya dage nasan tabbas akwai matsala so nayi qoqarin tursasashi amma yaqi Umaimah an tsaface mini da an sanya masa ya daina jin tsorona dagani har mahaifiyarku yama daina zuwa inda muke saboda zamu fada masa gsky Hajiya tace jiya ta kirashi tace ya sakeki saboda bazaki zauna da muguwar yarinyar nan ba da Sunanta yayi tambari ta fitar da mace a gdanta kota hanyar saki kota haukata kota kashe abune me sauqi a gurinta amma yaqi yace tayi masa uzuri ku hakan bazai faru daku ba saboda kun fahimci juna kuma kin bashi hadin kai shine ta kumayi masa rantsuwa akan saiya sauwaqe miki bazai kasheki da baqin cikinsa a banza ba Umaimah bayan qiyayyar Salma da ciwon auranta dakecin zuciyarsa harda wadannan kalaman na Hajiyanku addu'a kawai ya kamata muyiwa Hameed saboda kansa na cikin tukunya baya cikin hayyacinsa nasa ma da sauqi saboda qarfin kariyar farko da kuka samu daga kakanku musamman ke da kike mace da abin sai yaci uban haka ki qara hqr Umaimah mijinki yana sonki da izinin Allah komai zaizo qarshe bada dadewa ba”




Da wadannan kalaman ya rinqa kwantar Mata da hankali har yasamu yaga ta nutsu sannan ya zaunar da ita ya shiga ciki yaji dadin ganin jikin Hameed din bai tsananta sosai ba har yadan dawo hayyacinsa yana shiga ya zuba masa ido saida ya qarasa gabansa ya kamo hanunsa yace “sannu babana kuma ango Allah ya sanya alkhairi" kallon Daddy yayi da sauri yace “an daura ne?" Murmushin takaici Daddy yayi yace “to me zaa jira tunda kabada komai Allah dai ya tayaka ruqo ya baka ikon kwatanta adalci babu wata nasiha da zanyi maka tunda kai ba baqon riqe mace biyu bane amma wannan takun yana da bambamci da takun zaman Sadiya da Umaimah dole ka sanya ido a gidanka tunda ka nace hadasu zakayi Hameed kada naji kada na gani wlh har idan kakai hqrn Umaimah qarshe wlh babu ruwana zan cire hanuna daga lamarinka da ita gabadaya na zuba muku ido saboda itama yace kuma tanada yanci"



Numfashi ya sauke me wahala yace “ina take Daddy cikine da ita ko?" Kawar dakai yayi yace “tana waje bansani ba saboda bamu samu ganawa da likitan ba amma dai bata cikin nutsuwarta akwai damuwa sosai a tattare da ita Hameed ina qara jaddada maka girman amanar dake hannunka ba iya mata kawai take a gurinka ba qanwa ce kuma yace sannan amanar Allah ce" yana gama mgnr ya juya ya fita tana ganinsa ta miqe tayi gurinsa tace “ya tashi Daddy?" Murmushi yayi yana jinjina girman qaunar dake tsakanin yayan nasa yama rasa tsakaninsu waye yafi qaunar wani.
Jinjina mata kai yayi ta nufi dakin da sauri tana shiga ta nufi gadon baiji shigowarta ba saboda duniyar tunanin daya lula saida yaji ta rungumeshi ta karkatar da kanta daidai fuskarsa gabanta ya fadi sosai ganin hawaye a idonsa tasa harshenta ta lashe tace “nayiwa mijina kuma dan'uwana alqawarin zan bashi matsala ta kowanne bangare ba” matsata yayi s jikinsa yace “na gde bloody I love you so much” shigowar Dr Saleem da Daddy ne yasata miqewa a kunyace ta koma gefe ta zauna sukayi murmushi dukkansu Dr Saleem ya dubesu yace.




“Ya kamata ku cirewa kanku damuwa ku karbi duk abinda ya fado rayuwarku a matsayin qaddara Hameed rayuwarka tana cikin barazanar katsewa indai bazaka daina sanya muguwar damuwa a zuciyarka ba kasan matsalarka yakama komai ka rinqa maidashi abin wasa sannan matarka tana buqatar kulawa saboda nagani blood pressure dinta ya hau sosai sannan ga jaririn ciki komai zai iya faruwa saboda haka kuyi taka tsantsan dukkanku kunada matsalar da batason damuwa" hakanan sukayi sallama dashi suka tafi bayan ya dorashi akan magungunan da yakesha idan irin wannan matsalar ta taso.



Itace take driving din yana zaune a gefe Daddy kuwa gda ya wucce suna tafe kamar kurame babu wanda ya iya cewa da wani komai suna shiga get din gdan gaban yayi wata muguwar faduwa saboda ganin dayan bangaren cike da mutane ana shiga da kaya da qarfi taci wani uban birki ta juyo ta kalleshi shima ita din ya kalla da sauri yace “ Innanillahi wa innah ilaihir raji'un bloody kinga har sun kawo kayanta wayyoh nikam na shiga ukuna wannan wacce irin qaddara ce" wani matsiyacin kallo ta watsa masa ta bude motar da sauri zata fita yayi saurin riqo hanunta yace “kiyi cooling mind dinki bloody kada su gane rauninki suje su fada mata don Allah na fada mata cewa matata halin nana Fadimatu (R.A) ne da ita inasonki kema kinasona kuma kinason farin cikina kina tayani son duk abinda na kawo Umaimah dole ne kishi kuma halal ne nima bazanso ace baki kishina ba amma kiyi qoqarin danneshi ki barshi iyakar ni kada mubada qofar da zaa samu a shigo mana da baraka cikin gdanmu don Allah wlh nafiki kishin kaina Umaimah ji nake kamar na kashe kaina jinake dama na mutu na dawo duniya a wani bani ba mai tarin qaddarori marasa dadi Umaimah dama mu mutu kowa ya huta tunda mun kasa samun farin ciki a duniya qila mu samu a lahira......









*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*







[1/28, 2:03 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *G.U*














Kuka ta saka masa ta qanqameshi shima hawayen yake yana buga bayanta alamun rarrashi daqyar suka iya saita kansu ya sanya harshensa ya share mata hawayen ya bude motar ya riqota a jikinsa bai damu da yawan mutanen dake gdan ba kuma bai amsa gaisuwar da dangin Salma suketa yi masa ba yaja matarsa suka shige part dinta yana shiga yayi turus ganin Hajiya a zaune a parlourn da Aunty Jameelah da Zarah ga qawayen nata guda uku qanqameta yayi a jikinsa cikin rawar murya yace “shi... shikenan Hajiya tazo ta rabani da rayuwata Hajiya Umaimah rayuwa tace kada kice zaki rabamu wlh alhakin kisana zai rataya a wuyanki saboda inason matata Hajiya cikine da ita kada ki rabamu ki tausayawa yayan mu wlh mutuwa zanyi idan babu Umaimah a cikin gdana"




Miqewa Hajiya tayi tana zagaya parlourn tace “Zarah shiga ki hado mata kayanta ai ba wannan ne karon farko da mace take haihuwa a gda ba wlh Hameed bazan bar yar qanwata ta salwanta saboda kai ba kaidai na sallama ka tunda kai ka daukowa kanka kara da kiyashi dama ai hausawa sun fada jaye-jaye ke sanya jidali wlh baka fara kuka ba Hameed indai Salma ce gakanan gata ko kasheka zatayi babu abinda ya shafi Zulaiha amma Umaimah kam saika barta ko itace ke busa maka numfashi....”



Fuzgo hannun Umaimah tayi da qarfi shi kuma ya riqeta qam a qirjinsa yace “wlh Hajiya ko zaki tsinemin bazan rabu da matata ba saidai ki kasheni" tsayawa tayi sororo tana kallonsa yayi qasa da gwiwarsa ya durqushe yana wani irin kuka me ban tausayi jikinsa yana rawa yace “meyasa kullum tausayinki ya qare akan Umaimah Hajiya ni bakya tausayina meyasa bakwa yiwa rayuwata uzuri bayan bani na tsarota haka ba kuma ban isa na canzata ba meyasa kullum burinki nayi miki biyayya ni na cutu Hajiya ya kikeso nayi ya kikeso na kasance gwauro babu Umaimah ina Hajiya bazai yuwu ba bazan iya biyayyar dazan cutar da kaina ba..."




Sake jan jiki yayi kusa da Hajiya yace “Hajiya wlh aurena da Salma qaddara ce wlh tallahi billahillazi La'ilaha illah huwa Hajiya banajin ko digon soyayyar wata mace a raina bayan yar'uwata kuma matata Umaimah Hajiya na tsani ko tafiya ta tasomin wacce zata nisantani da kwanciya a jikin matata Umaimah Hajiya babu macen da nake samun nutsuwa da ita kuma nasa a raina zan samu bayan Umaimah Hajiya babu macen da zata iya dauke lalurar rayuwata bayan Umaimah saboda ita kadaice take sona domin Allah kuma ita kadaice take gamsar dani"



Yanda yake mgnr yana kuka muryarsa na daukewa ne yayi bala'in tsorata Umaimah ta fashe da kuka ta qanqameshi tace “Hajiya badon halinmu ba kiyi hqr wlh Hajiya inason mijina kuma baa kaina aka fara kishiya ba Hajiya shikenan idan kin rabani dashi haka zan rayu bazanyi wani auren ba idan har kin yarda zakita kallo na bazaki sake auradda ni ba to na amince ki rabamu idan kuwa kinsan zaki qara auraddani to kiyi hqr ki barni na rayu da dan'uwana Hajiya bansan waye zan aura ba meye halinsa matansa nawa idan bashida mata inada tabbacin wataran bazai min kishiya ba banida shi saboda haka Hajiya ki tayamu da addu'a Allah ya bamu ikon cinye jarabawarmu"




Ba qaramin sanyi kalamansu sukasa jikin Hajiya yayi ba ta dubesu a sanyaye ta tsugunna ta kama hanun Umaimah hawaye ya kwace mata tace “mar'atussaliha baki cancanci suna Umaimah ba duk da itama asalin mai sunan sahabiya ce kuma baiwar Allah amma naso ace sunanki Fadimatu saboda halayyarki tayi kama data Nana Fadima itace macen da har kullum take fifita farin cikin mijinta fiye da nata Umaimah da ace a zamanin annabi Muhammad (S.A.W) mukazo inada tabbacin kina cikin khulafa'ul rashidun ko kuma kina daya daga cikin matan da annabi ya dafa kawunansu yasa musu albarka kuma ya roqa musu albarkar ubangiji duniyarsu da lahirar su tabbas ina alfahari da samun ya a gareni kuma Ina alfahari da kasancewarki suruka a gareni Umaimah dama ace inada wani dan bayan Hameed wlh rayuwarki bata dace da azzalumin mutum irin Hameed ba da kullum baya sanin haqqin kowa sai nashi tabbas mgnrki gsky ce addu'a zan tayaki da ita Allah ya kareki da sharri da makirci irin na jinin Hajiya Talatu kishiya juji shidai daya debo da zafi ya qare a bakinsa"




Miqewa tayi ta taka zuwa tsakiyar parlourn ta tsaya ta sake share hawaye ta juyo tace “bazan maka mugun fata a cikin aurenka ba kuma zan tayaka da addu'a tunda kaima nawane ban isa na canza maka suna ba amma ka sani auranka da Salma babu wani alkhairi saboda haka bacci ba naku bane ku daure ku rinqa tashin tsakar dare kuna salatulduha sannan ku rinqa azumi da yawan karatun qur'ani hakan zai zame muku kariya daga sharrin shaidan da sihiri ko wanne iri ne duk da kaidai ka riga ka shiga hanu wlh na sani kuma na yarda auranka da Salma aikin sihiri ne"



Tana gama fadar haka ta fice daga parlourn suka kalli juna ita dashi taga yanda yake kwararar da hawaye masu dumi zuciyarsa tana wani fat² tayi saurin rungumeshi tace “ina tare dakai mijina a kowanne hali ina fatan kazama kaine mijina a jannatul-ma'awah" miqewa yayi ya dagata cak bai damu da yawan mutanen da suke gurin ba ya haura sama da gudunsa saboda bayason surutu.
Duk wanda ke gurin saida ya zubar musu da hawaye Saudat Alfah tayi ajiyar zuciya tace “bantaba ganin soyayya me ratsa zuciya daban tausayi irinta Umaimah da mijinta ba wlh ko soyayyar Aunty Murjanatun mu da Muhammad mijinta batakai wannan soyayyar dadin kallo da burgewa ba tabbas Umaimah yar aljannah ce kamar yanda Hajiya ta fada saboda dukkanmu na tabbata babu wadda zata iya yiwa mijinta wannan sadaukarwar qaunar akan kishiya kishiyar ma wacce take barazana ga rayuwarta da lafiyarta da mijin ma gaba daya dole mu jinjinawa Umaimah Umaimah na sallama miki kinyi nisan da bazamu tadda ke ba"




Sukuwa suna haurawa ya direta a gado ya fara romance dinta ta riqeshi da sauri tace “bloody muna da baqi fah a gdannan ka sani" lumshe idonsa yayi yaci gaba da matsata kamar lemon tsami yana cire mata kayan jikinta yana cewa wlh ko a gabansu zan iya turmusheki Hearty inajinki a duk wani bangare na jikina bloody soyayyar jini daban take da kowacce soyayya a duniya baayi kamarki a duniyata ba kuma ba zaayiba kece farko kece qarshe Umaimah ni da ke abu dayane zuciyarmu daya jininmu daya komai namu dayane Umaimah"



Da wadannan kalaman suka fara tsotse kansu suna shafe²nsu wanda Allah ya sani Umaimah badon dadi takeyi ba tanayi ne kawai donta faranta masa saboda ta lura yayi nisa sosai saida ta tabbatar ta gamsar dashi suka shiga sukayi wanka sukayi sallar azahar ya tayata ta shirya tsaf cikin wata atamfar Super Holland ja tayi kyau matuqa duk da ramar da tayi shima ya shirya cikin wani blue din yadi dake jikin atamfar tata da blue saiya zamana kamar anko sukayi nan fa suka bata lkc wajen yin hotuna sune har parlour ana suba selfie sudai su Aunty Jameelah da Aunty Zarah da Sa'ud da sauran mutane sai suka zama yan kallo a gdan suna sha'awar soyayyar ma'auratan.




Bayan sun gama haukan selfie dinsu suka zube a parlourn suna dariya dariyar tasu saida tasa kowa ma dariya harga Allah shidai ya manta da mutane a parlourn saida yaji sunyi dariya ya shafa kai cike da kunya yace “inajin yunwa bloody" miqewa tayi ta shiga kitchen ta zubo masa abincin da su Aunty Zarah suka girka ba kunya ya noqe kafada yace “muje na tayaki muyi namu ni duk abincin daba hanunki ne ya girka ba ba dadi yakeyi min ba"








*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[1/28, 8:26 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *G.U*


















Bata iya yimasa musu ba ta miqe suka shiga kitchen din basuyi wani abu me wahala ba jallop din taliya ce sukayi ta zuba masa takai masa sama ta hada masa lemukansa da komai takai masa ya zauna zaman cin abincin itakuma ta sace jikinta ta koma parlour sukaci gaba da hira da baqinta dauriya kawai takeyi tana yaqe saboda bataso tabada qofar da zaa fahimci rauninta amma zuciyarta cike take da fargaban zuwan Salma gdan yau hakanan dai suka yini har dare sannan duka suka watse suka tafi suka barta saida ta rakasu har inda suka aje motarsu sannan ta dawo ta kwanta a parlourn tana tunanin wadanna irin mutane ne dangin Salma da bazasu iya zuwa inda take ba saidai idan ta fito su rinqa binta da kallo kalma wata Mata ta tuna lkcn data rakasu Aunty Jameelan bayan sun tafi ta juyo zata dawo sukayi karo da ita ta fito daga bayan dakinta taja baya da sauri kawai sai taga matar tayi murmushi tace “Umaimah kike ko?"



Daga kai tayi da alamun mamaki tace “eh lfy?" Sake fadada fara'arta tayi tace “aa to lfyr kenan dangin kishiya kam ai bakya tambayi lfy a gurinsu ba koda yake meye ma na bata bakina abuda saura qiris" wannan kalamai sune sukeyi mata yawo a zuciyarta “saura qirin meyene to saura qiris din?" Tambaya ce da bata da amsa saboda haka tayi luf a kujerar tanata zuba hailala da salatin annabi har akayi sallar insha ta tashi ta shiga dakin qasa tayi sallah ta haura saman harta nufi dakinta sai kuma ta juya ta shiga dakinsa ta bude ta shiga yana kwance da Shurafah rungume a qirjinsa idanunsa a bude suke ya zubawa pop din dakin ido har ta qarasa kusa dashi ta zauna baiji ba saida ta tabashi sannan ya dawo hayyacinsa ya sauke idanunsa akanta tare da sauke ajiyar zuciya tayi murmushi tace.




“Kowanne ango a daren da zaa kawo masa amaryarsa baya samun zama balle ya kwanta harsai yaga an shigo da ita gdansa amma kai gaka a kwance banga kana shirin zuwa ka daukota ba yakamata ka tashi kayi wanka ka fara shirin tarar amaryarka nasan tanacan tana daukin zuwanta gareka da tarin alkhairanta da kyautukanta masu muhimmancin da ko labarinsu bazanji ba" tana mgnr tana sake sauke idanunta a kansa yanda taga idanunsa sun kada sunyi jawur ne yasata tabbatar da cewa kuka yayi kawar da kanta tayi ta miqe ta shiga bathroom ta hada masa ruwan wanka ta dawo ta janye Shurafah dake jikinsa ta ja hanunsa ya bita kamar raqumi da akala suka shiga bathroom din ta rufe ta matso gabansa tace.




“Zakayi da kanka ko nayi maka na qarshe?" Dubanta yayi da sauri tayi saurin yin murmushi ta lakace masa hanci tace “ina nufin zuwa ranar da amarya zata sake bani aronka tunda yanzu itace take riqe da kambun ka sarautar tatac....” rufe mata baki yayi da sauri yace “banida wata sarauniya a fadata bayan ke bloody wlh bazan iya yiwa kaina komai ba duk jikina a sanyaye yake" hadiye wani yawu tayi me ciwo ta fara balle bottle din rigarsa ta cireta ta zare masa wandon tajashi har komin wankan ya shiga ta rinqa diban ruwan a hanunta tana zuba masa a sumarsa saida ta jiqata ta dauko shampoo ta matsa ta wanke masa ita tsaf ta sake daukan shaver tayi masa shaving na qasa da sama har qashin qirjinsa saida ta rage masa kasancewar yanada suma sosai a jikinsa kuma tunda ya kwanta jinya bai rageta ba garama na qasan shine take tunanin ya rage bayan yaji sauqi dagowa tayi ta shafa gefen fuskarsa kawai sai taji hawaye ne yakebin kuncinsa batayi masa mgn ba saboda tana cewa zatayi masa mgn itama kukan zatayi hqrnta ya fara qarewa wai ita Umaimah itace take gyara mijinta saboda wata ajiyar zuciya taja da qarfi wadda tasashi bude idonsa ya zubasu a nata yanajin zuciyarsa kamar ana hura masa wuta ya janyota cikin bath din ya matseta a qirjinsa yace.



“kinajin abinda nakeji a qirjina kuwa bloody bana sanin sanda hawayennan yake zubomin duk dauriyata na kasa daurewa nisa dake wlh Umaimah ajiye mace sama da daya bai kamace ni ba saboda bazan taba kwatanta adalci akan wata mace ba indai inada ke Umaimah..." Rufe masa baki tayi tace ya isa bloody don Allah ka daina banaso abinda ya faru ya riga ya faru kuma koma mene kaine ka jawo mana da bakaje kakai kanka gurin Salma ba da bata ganka harkun fara soyayya ba” dagowa yayi da sauri bakinsa yana rawa yace “wal....” daga masa hanu tayi da sauri jikinta na rawa tana neman rikice masa tace “ya isa haka banason jin komai a game da matarka Abu Shurafah ka tashi ka shirya ka tafi gurinta tanacan tana

Please Login or Register in order to submit comment