Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kansu sama cikin matukar al'ajabi da mamaki,

Yaro Imran,Hadima Khadijat, Sarki lazwar, Sarkin yaƙi, Bawa shamsal, gimbiya mashlira da aljani Za'aratul-layal, kuwa sai suka cika da matukar farin ciki maral musaltuwa,

Aljani Hadimul-khairi ya a sauka a turba bisa ƙafafuwan sa.

Nan fa aka shiga kallon- kallo tsakanin sarki ladiyas,da uwar gidan gimbiya lamrat,

Matsafi shamrul da yaro Imran da Hadima Khadijat, Sarkin yaƙi Darusi da sarki lazwar,

Cikin matukar ɓacin rai mai girma ladiyas ya dubi uwar gidansa lamrat yace" ya uwar gida na shin ina dalilin wannan zuwa naki a cikin wannan yanayi?

Koda jin wannan batu daga bakin Sarki ladiyas sai gimbiya lamrat ta tari numfashin sa tana mai daka masa tsawa,

Ta dube sa cikin matukar fushi tace"kai tsohon azzalumi kuma la'ananne kayi sani cewa a yau ne zan ɗauka fansar jinin mai gidana daka hallaka nida yata mashlira,

Ka sani cewa tsahon shekarun da ka shuɗe kana azabtar da jama'ar burnin Istanbul kana yiwa mutane BAKIN ZALUNCI,

Kuma ina so kayi sani cewa Ni da yata mashlira tuni mun karɓi addinin yaro Imran,

A halin yanzu ni ba uwar gidan ka ba ce face abokiyar gabar ka,

Sa'adda mai girma ladiyas yaji wannan batu daga bakin gimbiya lamrat sai zuciyar sa takama tafarfasa tamkar zata kone ya dakawa lmarat tsawa a lokacin da idanun suka kaɗa suka yi jawur cikin kakkausar murya mai tattare da tsananin fushi yace" Kaicon ki yake lamrat hakika kin tafka babban kuskure da har kika yi gangancin haɗa kai da makiya na domin farautar rai na,

A yau ne zan hukunta ki da hukuncin da laifi mafi muni da ke yarka yarinya shuraiba,

Sa'adda sarki ladiyas yazo nan azancen sa sai ya mike tsaye zumbur daga kan karagar mulkin sa ya cire alkyabbar sa take wata irin gagarumar shigar yaƙi mai matukar firgici da ban tsoro ta bayyana a jikin sa,

Kawai sai ya dako wawan tsalle daga inda yake tsaye yana saman ya daga hannunsa sama wata irin sharbebiyar takobin sihiri ta bayyana a hannun sa ya dira a daf da inda gimbiya lamarat take

Koda ganin hakan sai yarinya shuraiba tayi wuf ta zare kwari da bakan ta tayi shirin ko ta kwana

Sarki lazwar kuwa duk jikin sa akwai manyan raunuka Amma sai yayi wuf ya kwaci wata takobi a hannun wani badakare ya falfala da gudu izuwa kan sarkin yaƙi Darusi

Hadima Khadijat da yaro Imran kuwa sai suka yi ɗauki izuwa kan matsafi shamrul suna masu kwala kabbara,

Bawa shamsal Sarkin yaƙi kuwa sai suka tari dakarun dake fadar,

Shi kuwa aljani za'aratul- layal sai yayi girgiza take siffar sa ta canza daga ta bil'adama zuwa ta aljani kawai sai ya marawa mai gidan sa sarki lazwar baya .

A sannan ne gimbiya mashlira dake sanye da tufafi irin na dakaru ta bude fuskar ta ta bayyana a fili nan fa kowa ya cika da mamaki kawai sai tayi koyi da aljani za'aratul-layal ta kaiwa masoyin ta sarkin lazwar ɗauki,

Lokaci guda ɓangarorin biyar suka afkawa juna da azababban yaƙi,

Wohoho kaico! Hakika guguwar annoba idan ta taso babu mai maganin ta face Allah, kuma Hakika inda babu kasa nan ake gardamar kokawa,

Domin KARON MAZA sai JARUMAN DUNIYA da suka ciri tuta a GUMURZUN SHEKARA DUBU, waɗanda komai TSANANI DA UKUBA a filin DANDAZON MAYAKA baya sa ka su gudu.

Hakika komai dakewar zuciyar mutum idan yaga yadda fadar ta yamutse da gumurzu dole ne ya ɗimauce ya fita daga hayyacin sa domin dola ne artabun ya zamo tashin hankali,

Nan fa jama'ar fadar suka ɗimauce suka kama guje- guje da ifice-ifice domin tsira da rayukan su

Ɓangarorin biyar suka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare-hare Cikin wani irin baƙin zafin nama JURIYA DA BAJINTA tamakar jikkunan su basu kasance na jini da tsoka ba

Hakika duk wanda bai fita filin yaƙi ba to bai ga karshen tashin hankali ba,

Kuma tabbas wanda bai san yaƙi ba shi ne yake fatan zuwan sa,

Ana fara wannan ɗauki ba daɗi ne gimbiya lamrat, yarinya shuraiba da Aljani Hadimul- kahiri suka fara gane cewa tabbas shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin kuwa tsananin zafin naman sarki ladiyas ya nunka nasu sai arba'in,



Nanfa yazamana cewa mutum uku sun kasa galaba akan ɗaya ya zame musu alaƙaƙai

Duk sanda suka kai masa hari da makaman su idan ya kare da tasa takobin sai kaga makaman su sun dakushe shi kuwa ko gezau bai yi na,

Idan kuwa ladiyas yakai musu hari idan suka goce sai yazamana cewa duk abinda takobin ta saransai yayi bindiga ya tarwatse koda kuwa gini ne

Matsafi shamrul, yaro Imran da Hadima Khadijat kuwa tuni labari yasha Bambam,

Domin kuwa sun hana tsafi shamrul sakat har sai ya zamana cewa ya daina amfani da makami ya dawo yaƙar su da karfin sihirin tsafi,



Domin wani lokacin idan Imran da Khadijah suka sareshi ta takobin su sai su ga wajen raunin ya koma ya haɗe sumul,

Wasu lokutan ma sai ya rikiɗa ya zama haske

Sarki lazwar, gimbiya mashlira, Aljani Za'aratul-layal kuwa sun wanzu suna masu kaiwa sarkin yaƙi Darusi hare -hare cikin gwanintar yaki tamkar zasu cinye sa ɗanye,

Amma bisa mamaki sai ya zame musu kadangaren bakin Tulu suka kasa samun nasarar koda lakutar jikin sa, duk kuwa da cewar karfin mutum biyu ne da aljani ɗaya akan mutum guda,

A ɓangaren Bawa shamsal da Sarkin yaƙi ku wa sun wanzu suna ragargazar dakarun dake fadar duk inda suka sanya gaba sai kaga dakarun na zubewa kasa matattu,



Nan fa karar karafniyar karafa, ihun mazaje hade da hargowar aljanu gami da ifice-ificen jama'a ya cika dodon kunne.

Kura ta turnuƙe fadar baki ɗaya tamkar haɗari zai gangamo a kece da ruwan sama.
Lokacin da aka ruguntsume da azababban yaƙi tsakanin manyan sarakuna biyu, aljanu biyu,gami da jarumai shida sai yakin ya zamo tashin hankali gami da ban tsoro ga yan kallo

Sai da aka shafe tsawon sa,a biyu ana wannan ɗauki babu daɗi tsakanin jaruman batare da ɗayan su ya samu nasarar hallaka ɗaya ba

Abangaren sarki ladiyas kuwa ya zame wa su gimbiya lamrat ANNOBA ƊARI



Domin kuwa duk da cewar aljani Hadimul-kahiri na amafni da addu'o,i domin su halaka sarki ladiyas amma sai hakan ya gagara domin sai sun datse wuyan sa suna tunanin ya mutu

Sai kawai suga wani ruhun ya keto daga cikin karkashin kasa ya sake shiga jikin sa,

Sai kuma a ɗora wani gumurzun nan fa yazamana cewa su Hadimul-kahiri sun kashe fiye ruhika arba'in na sarki ladiyas

Al'amarin daya sanya kenan su duka ukun suka samu miyagun raunuka a jikin su Musamman yarinya shuraiba

Haƙiƙa sarki ladiyas bakaramin hatsabiba ne domin yayi nisa a halarar tsafi wanda cimma masa abu ne mai matukar wahala.

A dai dai wannan lokaci ne Yaro Imran da Hadima Khadijat suka samu nasarar hallaka matsafi shamrul ta hanyar amfani da takubban su suka caka masa akan ƙawon zuciyar sa,

Yayin da suka hango su yarinya shuraiba kuma suka ga irin mugun halin da suke ciki sai suka kai musu ɗauki

Nan fa yazamana cewa labari ya canza domin a wannan karon sai ya zamana tasirin sihirin dake tare da sarki ladiyas ya fara karyewa,

Domin duk sa'adda Hadima Khadijat da yaro Imran suka kai masa hari da makaman su duk inda suka sara sai suga sun tasiri akan sa



Bisa taimakon Ubangijin halitta dakyar da siɗin goshi suka samu nasarar hallaka sarki ladiyas

Ta hanyar sare masa hannayensu sa da ƙafafuwan sa,suka jefar da gawar sa akasa

In da ace mutum ya na wannan waje a lokacin da sarki ladiyas da matsafi shamrul suka yi mutuwar wulakanci dola ne yayi farin ciki maral musaltuwa bisa ganin yadda Allah s,w,t ya kawo karshen azzalumai

A daidai wannan lokaci ne su gimbiya mashlira Aljani Za'aratul-layal da Sarki lazwar suka samu nasarar hallaka Sarkin yaƙi Darusi,

Sa,adda sauran jama'a da dakarun fadar da ke gwabza yaƙi da su Bawa shamsal suka yi arba da gawar sarki ladiyas sai dukkanin su suka durkusa kasa bisa gwiwoyin su sukayi mubaya'a,

Suna masu cewa hakika mun bayar da gaskiya da Ubangijin yaro imran

Cikin hanzari waɗansu likitoci suka shigo fadar ɗauke da kayan aiki

Suka shiga. Duba Lafiya yarinya shuraiba, gimbiya lamrat,da sarki lazwar,

Sannan yaro Imran ya ruga izuwa inda Hadima Khadijat take suka rungume juna cikin matukar farin ciki maral musaltuwa bisa sake saduwa da juna da suka tsawon shekaru

Daga bisani yaro Imran ya janye jikinsa daga na yar uwar sa Hadima Khadijat,

Ya juya ya fuskanci jama'a sannan ya buɗi baki yace_ Hakika na tabbatar da cewa a halin yanzu zukatan ku sun gamsu cewa babu abin bauta da gaskiya sai Allah mai kowa mai komai

Bautar gumaka da matsafa karya ce, Babu wani Allah sai Allah ɗaya

Saboda haka yanzu batare da wani ɓata lokaci ba yaro Imran ya faɗi kalmar shahada,

Take dubban ɗaruruwan jama'ar dake fadar suka maimaita,

Sautin muryoyin su ya cika fadar kuma ya amsa kuwwa izuwa cikin birnin baki ɗaya

Bisa mamaki sai Yaro Imran da Hadima Khadijat suka ji

Sarki lazwar da Sarkin yaƙin sa da bawa shamsal tare gimbiya mashlira sun amsa kalamar shahadar,

Nan fa suka cika da al'ajabi,

Sarki lazwar ya tako da ƙafafuwan sa izuwa inda imran da Khadijat suke

Ya duba Khadijat cikin girmamawa yace " yake sharifat Hakika rashin sani ya sani na tafi neman ki a can nesa alhalin kina kusa dani,

Yanzu gashi na karɓi addinin Musulunci shin ina makomar tafiya ta izuwa nemo abubuwan da zasu warkar dani daga sihirin da abokin gaba ta sarki Durwazu yayi mini,

Na karɓi Addinin Musulunci ne domin yadda da Ubangijin ku a zuciya



Nan take sarki lazwar ya shiga basu labarin yadda ya nemi taimakon Ubangijin halitta a lokacin da marigayi Sarki ladiyas ya sanya shi a cikin ɗakin duhu, a lokacin da yaga mutuwa muraran



Sa'adda sarki lazwar yazo nan azancen sa sai Hadima Khadijat da yaro Imran da sauran jama'a suka cika da matukar mamaki



Hadima sharifat tace" Yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa ai shi addinin Musulunci yana shafe komai saboda haka a halin yanzu sihirin da sarki Durwazu abokin gabar ka yayi maka ya karye



Babu bukatar sai na taimaka maka wajen mallako abubuwan da zasu warkar dakai daga sihirin.



Domin su ma abubuwan da za'a mallako dukkanin su na tsafi ne



A halin yanzu zaka iya kusantar kowa ce irin ya mace kuma har ka samu Haihuwa ka yarda Ubangijin musulunci kawai a koda yaushe



Koda jin wannan batu daga bakin Hadima Khadijat wato Baiwa sharifat sai sarki lazwar ya cika da tsananin farin ciki wanda bai taɓa yin kamar sa ba



Daga wannan ne aka ɗunguma izuwa gidan sarauta domin kowa ya huce gajiyar dake tattare dashi



A cikin wannan dare ne Hirar soyayya ta ɓarke tsakanin sarki lazwar da gimbiya mashlira yar shugaban muridai,



Yaro Imran da yarinya shuraiba, Hadima Khadijat wato Baiwa sharifat da Bawa shamsal



Kuma a wannan dare ne akayi shelar Naɗin sarautar yaro Imran da wazirinsa Bawa shamsal



Tun kafin wayewar gari Ciki da wajen Birnin Istanbul ya cika ya batse da jama'a baƙin sarakuna daga Kowa ce nahiya da yan kasuwa



Tun lokacin da alfijir ya keto bayan an gabatar da sallar asuba sai jama'a suka yi tsinke a fadar maza da mata yara da manya



Sarakuna da manyan baƙi an ware masu wajen zaman su daban,



Haka ma na talakawa komai dai an yisa bisa tsari



Sarkin fadar birnin Istanbul wani dattijo ya tashi ya gabatar da jawabin maraba ga mahalar ta taro



Sannan ma'ajin sarautar ya gabato da Kayan sarauta da suka haɗar da alkyabba,rawani,kwagiri,takalmi, da sauaran su



Sarkin fada Huzaifa ya ɗauki kayan ya shiga sanya wa yaro Imran a jikin sa bayan ya kammala ne sai ya umarci yaro Imran yaje ya zauna bisa karagar mulki ya hakimce, nan fa tsananin kyawun surar Imran ya fito ƙarara yarinya shuraiba kuwa sai ta dunga satar kallon sa tana yi masa kallo mai nuna alamun tsantsar so da kauna.



Nan take jama'ar fadar suka yi mubaya'a a gare shi



Daga nan kuma sai akaga shiga shagalin ɗaurin aure mutum shida sarki Imran da yarinya shuraiba Hadima Khadijat da Bawa shamsal,sarki lazwar da gimbiya mashlira.



A wannan rana anyi gagarumin shagalin da ba'a taba yin kamar sa ba tsawon kafuwar birnin Istanbul



Bayan an kammala ciye-ciye da tanɗe-tande,

Kowa ya cika cikinsa sai sarakunan da suka halarar bikin naɗin sarautar suka dunga zuwa,gaban sarki Imran suna karbar KALMAR SHAHADA tare da jama'ar su

Hakika farin ciki ya cika zuciyar kowa,

Bayan tarewar angwaye uku sarki Imran, shamsal da sarki lazwar,

Sai sarki Imran ya umarci Aljani Hadimul-kahiri ya ɗauki sarki lazwar da amaryar sa gimbiya mashlira da Sarkin yaki haɗe da aljani Za'aratul-layal domin ya kai su izuwa birnin zawatul-ifdal,



Sai da aka fara biyawa ta birnin su gimbiya mashlira aka musuluntar da Sarkin muridai da Mutanen sa kuma aka karya sihirin tsafin da aka yi musu suka dawo ainahin siffar su irin ta bil'adama suka daina cin naman bil'adama bisa taimakon Ubangijin halitta

An yi shagalin farin cikin dawowar yar Sarkin muridai gimbiya mashlira,

Sai da aka shafe mako ɗaya sannan aka sake ɗungumawa aka durfafi birnin zawatul-ifdal,

Amma sai aka bar Sarkin yaƙi imhal domin ya cigaba da bayar da ilimin addini ga jama'ar birnin,kuma Sarkin muridai ya naɗashi wazirinsa,

Lokacin da aka isa Birnin zawatul-ifdal sai Sarki lazwar ya cika da farin ciki bisa jin labarin abinda ya faru da magajin gari yaseeran da Amarya luwairat wacce a halin yanzu ita ce ke rike da karagar mulkin kasar.

Bayan ta musultar da jama'ar birnin ta hanyar wannan aljani da ya taimake ta ta tsira da fyaɗen da magajin gari ya nufi yayi mata.

bayan ya kashe angwanta.

Jama'a sunyi farin cikin dawowar sarki lazwar, batare da damuwa ba aka sake ɗaura auren Amarya luwairat da sarki lazwar

Sarki lazwar ya tare da amaren sa biyu luwairat da gimbiya mashlira,

Bayan an yan ta aljani Za'aratul-layal sai sai aljani Hadimul-kahiri ya koma izuwa birnin Istanbul

Sannu sannu bayan mako ashirin sai aka wayi gari matan sarki lazwar luwairat da mashlira suna ɗauke da juna biyu

Farin ciki a wajen sarki lazwar kuwa kamar ya zaunu

Tun daga wannan rana HASKEN MUSULUNCI

Ya mamaye duniya baki ɗaya zaman lafiya ya wanzu tsafi, zalunci, bautar gumaka suka rushe baki ɗaya.



Ƙarshe

Alhamdulillah



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment