Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Shuraiba aljani Za'aratun-layal a ƙarshe.
Lokacin da kowa ya wartsake ya dawo cikin hayyacin shi, suka arba da wannan kyakkyawan yaro da hadimin shi suna gudanar da Sallah,
sai kowa ya yi turus! Cike da matuƙar mamaki gami da al'ajabi.
Abu na farko daya bawa ko mamaki shi ne yadda yaron ke gudanar da ibadar cikin tsafta da tsari mai ban sha'awa, sannan ya aka yi su ka tsira da rayuwar su? Kuma ina aljani Durusul-fannar ya ke?
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kan su kenen, kawai sai suka zuba idanu suna kallo, har ya kammala ibadar sannan ya juya ya fuskanci su sarki Lazwar ya ce "ya ku waɗannan mutane ku yi sani cewa ban ceto rayuwar ku domin ku saka min da wani abuba, face kawai saboda Ubangiji na ya bayyana mini ku a cikin mafarki na. Kuma ta silar ku ne zan samu nasarar gano 'yar uwata da ta ɓace, kimanin shekaru bakwai.
Bisa wannan dalili ne ya sanya na ce ci rayuwar ku bisa taimakon Ubangijina, duk da cewa ta mai bautar Allah maɗaukakin sarki, ku kuma kun kasance kuna bauta wa gumaka".
Sa'adda su ka ji wannan batu daga bakin yaron sai kowa ya sake cika da matuƙar mamaki da al'ajabi.
Ita kuwa yarinya Shuraiba sai ta ƙura wa yaron idanu, gami da yi mashi wani irin kallo da ita kan ta bata san dalilin yin shi ba, tana mai cewa a ranta.
Shin wai dama akwai wani Ubangiji da ya halicci mutane bayan allolin mu?
Amma addinin wannan yaro yana tattare da tsafta da kayatarwa,
Nan take ta ji tana matuƙar ƙaunar yaron a cikin ranta tamkar ta daɗe da shaƙuwa da shi.
Sarki Lazwar ya buɗi baki ya ce ''ya kai wannan yaro mai ban al'ajabi shin mene ne sunan ka da labarin ka?
Ko da jin waɗannan tambayoyi sai yaron ya yi murmushi da ya ƙara wa fuskarshi kyawu ya ce "Ni suna na Imran ibn Nadir na fito daga ƙasar Yemen ne neman 'yar uwata wacce na rasa ta sakamakon farmakin bazato da aka kawo birninmu, ita ce kaɗai ta rage mini a cikin jinina, sannan babban burina shine kuma na yaɗa addini na gaskiya a doran ƙasa, game da tambayar ka kuwa mene ne labari na wannan hikaya ce mai tsawo yanzu babu lokacin yin shi sai dai a nan gaba".
Ko da jin amsar wannan tambaya sai sarki Lazwar ya juya ya dubi sarkin yaƙin shi yana mai yi mashi raɗa a kunne ya ce "ya dirkar birnina shin yanzu kana ganin zamu amince da yaro Imran mu yi wannan tafiya tare da shi alhalin ya kasance mabiyin addinin Musulunci, kuma sanin kanka ne cewa iyayenmu da kakanninmu mun mutu ne bisa ƙiyayyar wannan addini.
Sannan ka san babu yadda za'a yi sirrikan tsafi na su yi tasiri a wannan tafiya matsawar yaro Imran zai karanta abin da ya shafi addinin su,
Abu ɗaya ma da nake tsoro ya kasance shi ne a koda yaushe zan iya rasa sirrikan tsafi na.
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai sarkin yaƙi kara bakinshi dai-dai kunnen sarki cikin ladabi ya ce "ya shugabana tabbatas zancen ka dutse ne, sai dai wani hanzari ba gudu ba, baka ganin cewa dukkanin abokan tafiyar mu sun faɗa tarko da yawa amma sirrikan tsafin ka ba su tseratar damu ba. Yanzu da wannan yaro bai ceci rayuwar mu ba da yanzu kuma wani labarin ake yi daban ba wannan ba.
Ni dai shawara ta shine ka ga dai Imran yaro ne ƙarami babu ta yadda za ayi ya canja tunanin ɗayan mu mu shiga addinin shi, kawai zamu yi amfani da shi ne, domin cimma buƙatar mu daga baya sai mu yi watsi da shi".
Da jin wannan shawara ta sarkin yaƙi sai sarki Lazwar ya bushe da 'yar karamar dariyar mugunta ya dafa kafaɗunshi ya ce "an gaishe ka namijin duniya shi yasa dai-dai da sa'a ɗaya bana son a ce na rabu da kai saboda irin wannan al'amari,
Ko da gama wannan shawara sai sarki Lazwar ya dubi yaro Imran ya ce "ya kai wannan Imran ma'abocin taimako haƙiƙa mun amince mu yi wannan tafiya tare, sai dai bisa sharaɗi guda, sharaɗin kuwa shi ne iya tsawon wannan tafiya da zamu yi har ka sadu da 'yar uwarka, ba za ka tilasta ɗayan mu cewa sai ya yi imani da Ubangijin ka ba";
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai yaro Imran ya yi lallausar murmushi a gare su ya ce "ka kwantar da hankalin ka ya kai wannan sarki mai daraja ai addini ba a tilasta mutum ya shige shi face idan ya yi niyya da kan shi,
Da jin wannan batu daga bakin Imran sai kowa ya gyɗa kai alamar gamsuwa, yaro Imran ya mayar da duban shi zuwa ga aljanin shi ya ce "ya kai Hadimul-khair ina mai umartar ka ka shiga izuwa cikin wannan daji ka samo mana abin da zamu yi kalaci gami da ruwan sha.
Aljani Hadimul-khair ya risina ga yaro Imran ya ce "an gama ya shugaba na. Yana gama faɗin hakan ya kaɗa fuka-fukanshi ya nausa izuwa cikin dajin,
Jim kaɗan bayan shuɗewar waɗansu 'yan daƙiƙu sai Hadimul-khair ya dawo ɗauke da waɗansu nunannnun kayan marmari da suka haɗar da tuffa, gwanda, ayaba, lemu gami da ibini.
Ya ajiye a gaban Imran,shi kuma Imran ya yi umari kowa ya ɗebi wanda zai ishe shi, sannan kowa ya shiga kimtsa cikinshi, ita kuwa damisar yarinya Shuraiba sai ta kama kiwon a wajen tana kama kwari da kananan dabba tana lamushe su.
Bayan an kammala ne
an samu nutsuwa sai aka
ɗunguma a ka ci-gaba da tafiya, inda aljani Za'aratun-layal ya ɗauki sarki Lazwar, sarkin yaƙi, bawa Shamsal da gimbiya Mashlira, amma sai yarinya Shuraiba ta ki yarda ta hau kan shi, inda ta nemi alfarma a wajen naaro Imran da ya amince mata ta hau bisa kan aljanin sa tare damisa Faizur.
Al'amarin da ya yi matuƙar fusata sarki Lazwar kenan ya buɗe baki da nufin ya hana yarinya Shuraiba hawa kan aljani Hadimul-khair, amma sai sarkin yaƙi ya dakatar da shi yana mai yi masa raɗa a kunne ya ce "haba ya shugabana kar ka manta cewa Shuraiba tana da matuƙar muhimmanci a wannan tafiya tamu, domin ita ce ta san sirrin birnin Istanbul dama shi kanshi sarkin birnin, kar tun yanzu ka ɓata kiɗan da rawa, har Shuraiba ta fahimci cewa kana ɓoye mata wani abu game da yaro Imran har ta yi ƙoƙarin shaƙuwa da shi ta fahimci addinin shi.
Idan kuwa har hakan ta faru to kuwa zamu rasa su baki ɗaya wato Imran da Shuraiba.
Ko da jin wannan batu daga bakin sarkin yaƙi sai jikin sarki Lazwar ya yi sanyi ya koma ya zauna aka cigaba da tafiya.

Babi na bakwai

A can birnin Zawatul-ifdar kuwa, jama'a kuwa sun fara yabawa aya zaƙin ta, domin magajin gari Yasiran yana yi masu MULKIN ZALUNCI da ya zarce na sarki lazwar.
Domin ɗan ƙankanin laifi mutum zai aikata sai a yanke mashi hukuncin kisa ko zaman gidan kaso, yiwa 'ya'ya mata fyaɗe, ƙwace gami da fashi da makami ya yawaita a birnin Zawatul-ifdar.
Duk wanda ya yi sabon aure to ba zai tare da matarshi face an kai ta ga magajin gari Yasiran ya tara da ita sannan zai karɓi amaryar shi kashe gari.
Yan kasuwa aka matsa masu da karɓar haraji, nan fa ya zamana cewa hatta 'yan majalisar birnin sun fara ƙosawa da mulkin zaluncin Yasiran, suka shiga tunanin hanyar da za su kawar da shi daga kan karagar mulki, duk da cewar a halin yanzu sun fi matuƙar tsoron shi fiye da sarki Lazwar.
Wata rana da hantsi lokacin zaman fada an cika maƙil da jama'a babu masaka tsinke, duk inda mutum ya duba kawunan bil'adama ne rututu tamakar dandazon kiyasai, ana jiran fitowar magajin gari Yasiran.
Ana cikin wannan hali kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ji fadar ta kaure da wata irin mahaukaciyar dariya mai ban tsoro, daga can sai aka ga Yasiran ya bayyana tsulum! A fadar tamkar an jefo shi daga sama, hannunshi na dama riƙe da wata sharɓeɓiyar takobi, na hagun kuwa riƙe da wani mashi an tsire kan wani mutum a jikin shi jini na zuba.
Sa'adda jama'a su kayi arba da kan, sai suka ɗimauce 'yan majalisa kuwa sai jikkunansu suka kama ƙyarma saboda matuƙar tsoro, ba komai ne sanya su ƙyarma face bisa arna da kan sarkin fada, wato ɗaya daga cikin yan majalisar magajin gari Yasiran ya ɗaga hannunshi sama fadar tayi tsit! Tamkar mutuwa ta kawo ziyara.
Fuskarshi a murtke ya ce "ya ku al'ummar wannan fada mai albarka ku yi sani cewa, wannan shi ne darasi ga duk wanda baya goyan bayan mulki na a wannan birnin".
Yana gama faɗin hakan sai ya yi jifa da kan sarkin fada a kas, cikin hanzari wani badakare ya shigo fadar janye da hannun wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa, tana ta rusa kuka sai ya iso da ita daf da ida karagar mulki take sannan ya risina ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa.
Sannan ya buɗi baki cikin ladabi ya ce "ga ta nan na zo da ita ya shugabana";
Yasiran ya dube shi ya ce "sai ayi hanzari akai min ita turakata".
Badakaren ya miƙe tsaye ya fice da budurwar wacce ke rusa kuka tana magiyar a rabu da ita, komai rashin imanin mutum idan ya ga halin da budurwar ke ciki, dole ne ya zubar mata da hawaye saboda matuƙar tausayi, da yawa daga mutanen fadar sai da su ka zubar da ƙwalla sabo da matuƙar tausayin budurwar.
Wannan shi ne abin da ya faru a can birnin Zawatul-ifdar bayan sarki Lazwar ya ɗora magajin gari Yasiran a bisa sarautar shi ya shiga izuwa duniya.
Haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce, sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'a je ba, sai ga shi an shafe tsawon kwanaki arba'in da huɗu ana tafiya tsakanin sarki Lazwar, gimbiya Mashlira, yarinya Shuraiba, sarkin yaƙi ,bawa Shamsal aljani Za'aratun-layal tare da yaro Imran.
A iya tsawon wannan tafiya shaƙuwa mai karfi ta ƙullu tsakanin yarinya Shuraiba da yaro Imran, kuma Imran ya bayyana abubuwan mamaki gami da ƙarfin ikon Ubangiji.
Domin sau talatin da bakwai yana ceto rayuwar su sarki Lazwar bisa taimakon Ubangijin musulunci.
Bisa wannan dalili ne ya sanya Mashlira da Shuraiba suka fara kwaɗayin shiga addinin.
A ranar da kwana hamsin suka cika ne aljani Za'aratun-layal ya sauka a bisa wani daji dake kusa da birnin Istanbul, nan fa farin ciki ya kama kowa shima aljani Hadimul-khair ya sauke Imran da yarinya Shuraiba
Bayan kowa ya sauko sai aka shiga tattaunawa akan hanyar da kowa zai bi wajen shiga birnin Istanbul, inda Shuraiba ta dubi kowa sannan ta yi gyaran murya ta ce
"akwai shawarwari da zan bamu waɗanda matsawar muka kiyaye su zamu shiga cikin birnin Istanbul lafiya kuma mu fito lafiya sumul.
Da farko dole ne kowannen mu ya ƙaurace sanya tufafi masu tsadar gaske, ko wada ke nuna wata alama ta mulki .
Na biyu gujewa ƙarya da ha'inci, sannan yin biyayya ga dukkan abin da ya shafi masarauta.
Waɗannan sune shawararin da idan muka kiyaye su zamu cimma nasara.
Koda Shuraiba ta zo dai-dai nan azancen ta sai ta juya da dubi Gimbiya Mashlira ta ce "ya ke Mashlira ya zama wajibi idan zaki shiga cikin wannan birni na Istanbul ke rufe fuskarki da rawani, har zuwa lokacin da zamu kammala samun abin da muka shiga nema, domin tsananin kyawun surarki zai jawo miki matsala.
Koda yarinya Shuraiba ta zo nan a jawabin ta sai tayi bankwana da damisarta suna masu zubar da hawayen rabuwa da juna, har sai damisar ta ƙule izuwa cikin daji ta daina hangen ta.
Ko da jin wannan batu daga bakin Shuraiba sai kowa ya gyaɗa kai cikin farin ciki, kawai sai sarki Lazwar ya karanto waɗansu dalasiman tsafi ya nuna aljani Za'aratun-layal da ɗan yatsan shi na hagu, take Za'aratun-layal ya riƙiɗa izuwa wani garjejen sadauki mai kwarjini daban tsoro, sannan ya sake karanto waɗansu dalasiman tsafin take tufafin dake jikin su ya canja launi zuwa makasƙanta, babu wanda zai ga sarki Lazwar da gimbiya Mashlira a wannan hali face ya cika da mamaki bisa ganin yadda suka koma tamkar almajirai saboda tufafin dake sanye a jikkunansu.
kaico! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka biyan buƙata ya fi dogon buri. kuma ranar biyan buƙata rai da dukiya ba a bakin komai suke ba.
Kawai sai aka ɗunguma aka durfafi ƙofar birnin Istanbul gadan-gadan, shi kuwa yaro Imran sai ya matsa kusa Shuraiba ya yi mata raɗa a kunne, sannan ya dawo da duban shi ga hadimin shi ya ce dash ''ya kai Hadimul-khair ina ganin ya kamata ka kasance a ɓoye, koda ka bayyana har sai lokacin da na buƙaci hakan" koda jin hakan sai Hadimul-khair ya risina ya ce ''an gama ya shugabana, kawai sai ya ambaci sunan Allah gami da yiwa Annabi salati take ya bace bat, tamkar bai taba wanzu wa ba.
Wannan shi ne abin da ya faru da su sarki Lazwar lokacin da suka iso izuwa birnin Istanbul.


Babi na takwas


BIRNIN ZAWATUL-IFDAR

Al'amarin wannan budurwa da magajin gari yasiran ya yi umarni a kai mashi ita izuwa turakar shi kuwa, ba wata ba ce face wata sabuwar amarya, kuma an ɗauko ta ne domin ya keta mata haddi.
Lokacin da wannan badakaren ya isa da ita turakar sai ya tarar da kuyangi na ƙawata turakar da kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya, wani irin daddaɗan kamshi na tashi a ko ina.
A harabar turakar da bakin ƙofa kuwa dakaru ne birjik shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannayensu ɗauke da miyagun makamai.
Ya yin da amaryar ta tsinci kanta a ciki turakar sai ta sake fashewa matsanancin kuka mai tsuma zuciya, tsawon sa'o'i tana cikin fargaba da tsoron abin da zai faru gare ta, kuma tana tuna halin da angon ta ya ke ciki.
Haka ta kasance a cikin wannan hali har duhun dare ya fara nisa, a cikin wannan hali ne ta ji motsin shigowar magajin gari Yasiran ba, nan fa tsoro ya kara kamata ainu.
Tana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai kawai ta ga wani kyakkyawan tsuntsu yana fitar da wani sautin kuka mai daɗin saurare, yana shawagi a harabar turakar.
Cike da matuƙar kwadaituwa da son ganin tsuntsun, ta matsa izuwa tagar dake turakar ta leƙa ai kuwa sai ta ga anyi wani rubutu a jikin fuka-fukan tsuntsun da harshen Larabci
kawai sai ta furta a bakinta, faruwar hakan keda wuya, ai sai ta ji dukkan baƙin ciki gami da tsoron dake zuciyarta ya tafi, tamkar babu wani mugun abu dake shirin faruwa a gare ta.
Cikin farin ciki mara musaltuwa ta cigaba da karanta kalmomin a cikin ranta
A dai-dai wannan lokacin ta ji an turo kofar shigowa turakar, tana buɗe wa sai ga Yasiran ya bayyana, yana sanye da wani mayafi na alhariri da ya rufe daga cibiyarshi izuwa gwiwarshi.
Sa'adda amaryar ta yi arba da shi saboda matuƙar tsoro ba ta san sa'adda ta faɗi ƙasa ba, jikinta na ƙyarma tamkar mazari, shi kuwa magajin gari sai ya nufi inda take yana mai bushewa da dariyar mugunta har da ƙyaƙyatawa,
Lokacin da ya matso daf da ita sai ya kawai ya miƙa hannunshi da niyyar ya cakume ta.amma
sai ya ji wani irin tiririn zafi ya tunkaro shi tamkar an yana kusa tanderun wuta.
Al'amarin da ya yi matuƙar ba shi mamaki kenan kuma ya fusata ainun, kawai sai ya buɗe baki da nufin ya karanta waɗansu dalasiman tsafi.
Kaico! haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu, in da ace Yasiran ya san abin da zai faru da bai yi gangancin karanta dalasiman tsafin ba, domin kuwa yana cikin hakan ne wata irin gagarumar wuta ta kama a jikinshi tana ci. Nan fa magajin gari ya shiga kurma wawan ihu yana mai kai komo a cikin turakar domin ganin ya kashe wutar, amma duk sa'adda ya zuba ruwa sai wutar da ƙara ruruwa.
Ita kuwa amarya munirat koda ta ga wuta ta kama a jikinshi, sai ta ci gaba da karanta waɗannan kalmomi na larabci da taga ni a jikin fuka-fukan tsuntsun nan a cikin zuciyarta, kuma ta miƙe tsaye zumbur ta rugawa izuwa ƙofar fita daga turakar.
Bisa mamaki duk ƙofar da ta tunkara sai ta ga ta buɗe da kanta, wani abu da ya bata mamaki kuma ya ɗaure mata kai shi ne, gashi dai ƙiri-ƙiri dakaru suna kallon ta ta tsakiyar su take ratsawa, amma babu mai ɗaga mata yatsa ballantana ya ce mata uffan.
Haka dai amarya Munirat ta cigaba da tafiya a cikin gidan sarautar, zuciyarta cike da matuƙar farin ciki maral musaltuwa gami da imani da ma'abocin waɗannan kalmomi da ta karanta suka ce ci rayuwar ta. A dai-dai wannan lokaci ne dakarun dake gidan sarautar suka dunga tuttɗowa suna zare makaman su suna rugawa izuwa ɓangaren sarki, bisa jin ihu gami da kururuwar magajin gari Yasiran da suka yi.
kafin ƙiftawar idanun gidan sarautar ya hargitse da guje-gujen jama'a gami da ifice-ifice tamkar an busa ƙahon BUSAR MUTUWA.


Babi na tara

A can birnin muridai kuwa, sarki Zammar mahaifin gimbiya Mashlira ya ga dukkanin abin da ya wakana tsakanin yaro Imran da aljani Durusul-fannar.
A cikin halarar tsafin shi a lokacin da yake zaune a fadar tare da 'yan majalisar shi.
Ko da ganin hakan sai ya cika da matuƙar baƙin ciki maral-musaltuwa.
Wata rana sarki Zammar na kwance a cikin turakarshi da ta ƙawatu da kayan alatun more rayuwr duniya, sai ya yi mafarki da yarshi Mashlira tana cikin ƙoshin lafiya.
Kuma har ta gaya mashi cewa bata guje mashi domin ta ci amanar shi ba, sai domin ta shiga duniya ta samo masu maganin lalurar da ta addabe, su tun daga wannan rana Sarki Zammar ya kasance cikin matuƙar farin ciki, ya yiwa 'yarshi fatan alheri da samun nasara.
Wannan shi ne abin da yafaru acan birnin muridai.


Babi na tara

Tafiyar daƙiƙa latalin kacal aka yi aka iso ƙofar shigowa birnin Istanbul, sa'adda aka yi arba da yadda ƙofar birnin takasance sai kowa ya cika da matuƙar mamaki, katangun birnin sun kasance masu matuƙar tsawo, a sama da ƙasan ƙofar birnin miyagun dakaru ne na mutum da aljan ga su nan birjik shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannayen ɗauke da waɗansu irin masifaffun makamai
Kai koda tsuntsu ne ya zo giftawa ta wannan waje waɗannan dakaru ba zasu bar shi a raye ba, tsananin kwarjini mayaƙan ya isa ya ɗimauta duk wata halitta mai numfashi.
Idan har ƙofar birnin Istanbul takasance haka, to ya tsaron gidan sarautar birnin zai kasance kuwa?
Sarki Lazwar ne ya yi wa kanshi wannan tambaya a cikin ranshi ba tare da ya furta wani ya ji ba.
Wani narkeken sadauki mai matuƙar muni da kwarjini ya matso daf da inda su sarki Lazwar su ke ya kare masu kallo da yan mini-minin idanuwanshi jajaye tamkar garwashin wuta, cikin wata irin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce "ya ku waɗannan baƙi shin daga ina kuke, kuma mene ne ke tafe da ku izuwa birnin nafi daraja a duniya?.
Ko da jin wannan tambaya sai zuciyar sarki lazwar ta kama tafarfasa tamkar zata ƙone.
Bakomai ne ya sanya hakan ba, sai bisa jin badakaren ya ambaci birnin Istanbul da suna mafi daraja a duniya.
Amma koda ya tuna cewa shi fa a halin yanzu sunan shi bawa ba BASARAKE ba, sai ya danne zuciyarshi, ya dubi badakaren ya ce "ya kai wannan badakare ka yi sani cewa ba komai ne ke tafe damu izuwa wannan birnin na ku ba face sai domin mu gudanar da kasuwanci, kuma a halin yanzu mun fito ne daga nahiyar ƙasashe larabawan gabas.
Ko da jin amsar wannan tambaya sai badakaren ya bushe da dariya sannan daga bisani ya murtuke fuska ya ce "Zamu ba ku izinin shiga wannan birnin saboda muhimmancin abin da ke tafe da ku. Sai dai wani hanzari ba gudu ba idan muka samu ɗayan ku ya karya dokokin wannan birnin namu, to zamu ƙwace dukiyarku gami da tusa ƙeyarku izuwa gidan kaso.
Ko da jin wannan batu sai hantar cikin kowa ta kaɗa da karfi tsoro ya kama shi.
Kawai sai badakaren ya yiwa waɗansu dakaru inkiya ta wutsiyar idanu take dakarun suka shiga wangame kofar birnin, ƙofar na kammala buɗewa su sarki suka kunna kai izuwa cikin birnin zukatansu cike da matuƙar farin ciki.
Lokacin da su Sarki lazwar suka tsinci kansu a cikin birnin Istanbul sai suka kama kalle-kalle da dube-dube tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni, kuma suka cika da matuƙar mamaki gami da al'ajabi, bisa ganin yadda birnin ya kasance mai matuƙar kyawun gine-gine tamkar aljannar duniya.
Kai tsaye yarinya Shuraiba ta durfafi hanyar kasuwar birnin, amma sai sarki Lazwar ya yi caraf! ya dubi yarinya Shuraiba ya ce "ya ke Shuraiba shin mene ne dalilin da ya sanya za ki kai mu kasuwa? Bayan cewa ba kasuwanci ne ya kawo mu wannan birni ba?
Ko da jin waɗannan tambayoyi sai Shuraiba ta bushe da dariya ta ce "ai bakomai ne yasanya na kawo mu kasuwa ba sai domin kar ka manta cewa ka faɗawa dakaru masu tsaron kofar birnin Istanbul cewa kasuwanci ne ya kawo mu, tabbas dola ne a kowa ne lokaci dakarun sarki su kawo ziyarar bazato, domin binciken gaskiyar maganar abin da ka faɗa masu,
Abu na biyu kuwa shi ne a lokacin da muka shigo wannan birni 'yan fashi da makami gami da 'yan damfara sun shaida shigowar mu, a koda yaushe za su iya kawo mana farmaki domin a tsammanin su za su samu dukiya mai tarin yawa a wajen mu.
Waɗannan dalilai ne suka sanya na kawo mu kasuwa domin babu wani waje mai ɗauke da cikekken tsaro fiye da kasuwa".
Ko da jin

Please Login or Register in order to submit comment