Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amsar waɗannan tambayoyi daga bakin Shuraiba sai kowa ya gyaɗa kai alamar gamsuwa gami da samun nutsuwa.
Lokacin da aka shiga kasuwar sai aka tarad da takasance maƙiyaya mai faɗin gaske, tana ɗauke da gine gine cikin tsari, rumfunan masu siyan da tufafi dabam, kayan masarufi, komai dai an yi bisa tsari mai ƙayatarwa.
Kai tsaye aka durfafi rumfar wani dattijo, da ta ƙawatu da kayan alatu na hatimin sarauta, da alama shine shugaba kasuwar.
Tun daga nesa Shuraiba taga ya ƙura mata idanu ko kiftawa ba ya yi.
koda shugaban kasuwar ya yi arba da su sai ya miƙe tsaye zumbu! Ya tarbe su cikin matuƙar farin ciki yana yi masu lale marhaban da zuwa, tamkar ya sadu waɗansu yan uwanshi na jini da ya jima bai sadu da su ba.
Bayan shugaban kasuwar mai suna Sha'aran ya sauke su a bakin ƙofar rumfar, sai ya yi umarni aka kawo musu abincin kalaci aka jera a bisa wani dogon teburi, nan fa su sarki Lazwar suka shiga kimtsa cikinsu, har suna hannu baka hannu ƙwarya, domin rabon su da cin irin abincin yau wata huɗu kenan cif.
Kuma suna mamakin irin karamci da shugaban kasuwar ya nuna masu.
Shi kuwa yaro Imran da aka fara cin abincin sai ya yi bisimillah, loma bakwai ya yi sannan ya zare hannunshi ya kurɓi ruwa maƙwarwa huɗu sannan ya koma koma gefe gudal.
Al'amarin daya bawa sarkin kasuwa Sha'aran mamaki kenan, ya ƙurawa yaro Imran idanu yana so ya tuna irin mutanen da ya taɓa gani suna irin wannan dabi'a wajen cin abincin su, Shi kuwa aljani ZA'ARATUN-LAYAL, da a halin yanzu sarki Lazwar ya canja mashi siffarshu dagaaljan ya koma bil'adama, cin abincin ya yi yana santi kamar tsohon mahaukaci.
Bayan kowa ya kimtsa cikinshi ya dawo hayyacinshi, sai sarki Lazwar ya zira hannunshi a aljihun rigarshi domin ya ɗauko dinare domin ya biya kuɗin bincin da suka ci, da kuma kuɗin hayar gidan da za'a ba su.
Amma sai kawai ya ga shugaban ya dube sa fuskar sa cike da annuri ya ce "ya ku waɗannan baƙi masu daraja ku yi sani cewa, ganin ku da nayi ya sanya jikina ya ba ni cewa ku mutanen ƙwarai ne. Yanzu ina buƙatar ku gabatar min da sunayen ku.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama kowa, sarki Lazwar ya shiga gabatar da sunayen su ɗaya-bayan-ɗaya,
Amma koda yazo kan yarinya Shuraiba sai sarkin kasuwar ya dakatar dashi ya ce "ba sai ka gabatar mini da ita ba.
Al'amarin da ya bawa kowa mamaki kenan, har Shuraiba ta ce a cikin ranta shin me shugaban kasuwar ya sani game da ni. Kuma me ya sanya yake ƙura min idanu tun da muka shigo kasuwar?
Ina dalilin rashin karɓar haƙƙin aikin shi daga gare mu.
Amsar tambayoyin da yarinya Shuraiba ta kasa bawa kanta kenan.
Shugaba sha'aran na gama faɗin hakan sai ya ƙwallawa wata budurwa kira.
Budurwar ta bayyana a gare shi sanye da tufafi masu yalwa, tun daga ƙasa har sama, kuma fuskarta rufe da rawani mai ɗauke da wani hatimin sarauta idanuwanta kaɗai ake gani,
ta zube ƙasa ta kwashi gaisuwa cikin girmamawa, sannan ta buɗi baki cikin wata irin lallausar murya mai daɗi tamkar sarewa ta ce ''ga ni ya shugabana me ake da buƙata?
Shugaba Sha'aran ya dube ta ya ce "ya ke khadijat ki yi sani cewa bakomai nake buƙata a gare ki ba, sai domin ki yiwa waɗannan baƙi jagora izuwa unguwar Madinatul-dinar, masaukin manyan baƙi, ina so ki ba su dukkan abin da suke bukata na kulawa".
Koda jin wannan umarni sai B
Budurwa khadijat ta mayar da duban ta ga su sarki Lazwar tana ƙare masu kallo ɗaya-bayan-ɗaya.
Ya yin da ta haɗa idanu da yaro Imran sai taji zuciyar ta buga ƙarfi kuma tsikar jikin ta ta tashi, kamar yadda ya faru gare ta shi ma haka yaro Imran ya ji wannan yanayi a tare da shi, amma saboda kada wani ya fahimci abin da ke faruwa sai khadijat ta kawar da idanuwanta a kan shi, a ɓangaren bawa Shamsal kuwa, tun sa'adda da ya kalli idanuwan budurwa khadijat sai ya ji hantar cikinshi ta kaɗa da ƙarfi, sannan wani abu ya ɗar su a zuciyarshi da ya kasa gane ko mene ne.
Ita kuwa gimbiya Mashlira cikin idanun khadijat kawai ta kalla taji kishi ya kama ta, domin koda cewar fuskar khadijat a rufe take da rawani idanuwanta kaɗai ake gani, ta tabbatar cewa ta shafe ta a kyawun sura ne sa ba kusa ba.
Tabbas idan masoyin ta sarki Lazwar ya yi arba da ita zahiri zai iya karkata zuciyarshi izuwa gare ta.
Khadijat ta miƙe tsaye ta shige gaba, tana mai yafito su sarki da hannunta, tana mai yi masu nuni da su biyo bayan ta.
Ba tare da gardamar komai ba, suka mara mata baya har suka ƙule a cikin kasuwar, duk inda suka gifta sai jama'a su bi su da kallo, haka suka wanzu suna ratsa saƙo da lungu na unguwanni, har suka iso wani ƙasaitaccen gida.
Kai tsaye khadijat ta durfafi kofar gidan ta na isa dakarun dake gadi suka wangame makekiyar kofar shiga gidan suna masu risinawa a gare ta cikin girmamawa.
Khadijah ta kunna kai izuwa cikin gidan, su sarki lazwar na biye da ita cike da matuƙar mamakin yadda masaukin ya kasance.
Kowanne su ɗaki aka ba shi daban mai ɗauke da gado, kushin da kewayen wanka da sauran kayan more rayuwa.
Kuma khadijat ta shaida masu cewa duk mai buƙatar wani abu ya sanar da ita har izuwa lokacin da zasu tafi.
kasancewar a wannan lokaci duhun dare ya fara kawo kai, sai khadijat ta yi umarni aka kunna dukkanin fitulun dake gidan.
A lokacin da dare ya tsala sai sarki Lazwar ya shiga izuwa masaukin kowanne ya bayyana masa cewa, dole ne su kasance cikin shiri, domin a kowannnen lokaci za a iya kawo masu harin bazato, kuma ba su da tabbacin cewa sarki kasuwa Sha'aran ba shi da wata mummunar manufa akan su, kuma a gobe da duku-dukun safiya za su shiga cikin garin domin gudanar da abin da ke tafe da su.
A can masaukin yaro Imran kuwa bayan gabatar da kalacen dare, sai ya shiga izuwa kewayen ya ɗaura alwala ya dawo izuwa turakarshi ya shiga gabatar da Sallah isha'i yana cikin hakanne ya ji an turo kofar shigowa, sai da ya idar ya yi addu'a sannan ya juya domin ya ga kowane ne ya shigo ɗin.
Koda ya yi arba da wanda ya shigo ɗin sai ya yi turus!, Ba wani ya gani ba face khadijat hadima ga Sarkin kasuwa Sha'aran, tana durƙushe a gefan shi na hagu ta yi zama irin na sallah.
Cikin matuƙar mamaki Imran ya du be ta cikin girmamawa ya ce "ya ke hidima Khadijat shin ina dalilin shigowarki wannan masauki nawa a dai-dai wannan lokaci bakya tsoron sauran abokan tafiya za su zargi wani abu?
Sannan jikina ya bani cewa kina kwaikwayon yadda nake gudanar da ibadar Ubangiji na.
Shin baka tunanin hakan zai jefa rayuwarki da tawa a cikin haɗari ba?
Ko da jin waɗannan tambayoyi sai khadijat ta yi murmushi mai taushi, sannan ta dubi Imran cikin murya mai daɗin saurare ta ce
"ya kai wannan yaro ka yi sani cewa tun sa'adda nayi arba da kai a lokacin da ku ka sauka a rumfar mai gidana, naji ka burgeni sosai a zuciyata tamkar ina tare ɗan uwa na jini, kuma lokacin da ku ke cin abincin na lura cewa duk dabi'un cin abincin naka ya bambanta da nasu, wato naka irin na ma'abota addinin Musulunci ne, tun daga lokacin na ji cewa na samu ɗan uwa.
Bisa wannan dalili ne ya sanya na biyo ka izuwa masaukin ka domin na bika sallah. Fiye da shekaru goma sha biyu kenan tun sa'adda an fito neman ɗan uwa na, wanda shi ne kaɗai ya rage mini da a duniya rabon da a ce na samu jam'in sallah sai a yau,
Tabbas ina cikin matuƙar farin cikin da ba zai musaltu ba. Haƙiƙa da zaka zauna a tare da ni da ka ɗebe mani kewar mahaifina da na rasa.
Tsawon shekarun da na shafe ina aiki tare da Sarkin kasuwa Sha'aran ban taɓa bayyana addini na a gare shi, saboda gudun matsala, domin duk wanda aka samu yana gudanar da wani addini saɓanin na birnin Istanbul hukuncin kisa ne a ƙanshin shi.
Bisa wannan dalili ne ya sanya kai ma nake baka shawara da ka guji bayyana hakan, har ku kammala abin da ke tafe daku zuwa wannan birni";
Koda jin amsar waɗannan tambayoyi sai yaro Imran ya cika da matuƙar farin ciki yaji ya yi matuƙar shaƙuwa da hadima khadijat, kuma mamaki ya kama shi bisa jin cewa ta fito neman ɗan uwanta ne.
Shin khadijat ita ce 'yar uwar shi da ya fito nema ?
Amma ta ya zai iya gasgata hakan bayan cewa koda yaushe fuskarta a rufe take da rawani.
Amsar tambayoyin da Imran ya kasa bawa kanshi kenan.
Khadijat ta katse shirun da wanzu a tsakaninsu ta hanyar buɗar baki ta ce "ya kai ɗan uwa na idan ba za ka damu ba, ina neman alfarma a gare ka da ka amince min kullum na dunga zuwa wajen ka muna yin fira gami da ɗebe kewa
Koda jin wannan batu sai Imran ya ce "na yi maki wannan alfarma ya ke yar uwanta".
Wannan shi ne abin da ya faru a masaukin yaro Imran ma'abocin addinin Musulunci.
A can masaukin sarki Lazwar kuwa, fira ce ta kare tsakanin Lazwar da gimbiya Mashlira, a inda Mashlira ta ci gaba da ba shi labarin abin da ya faru tsakanin matsafi Sahibul-ukub da mutanen birnin akan dalilin da ya sanya halittar su ta koma ta maridai inda ta ci gaba da cewa.
Lokacin da rundunar matsafi Sahibul-ukub suka afkawa birnin Madinatul-Adfal sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar muni ban tsoro da ban al'ajabi.
Nan fa su ma mayaƙan birnin suka dinga tuttuɗowa daga kowacce kusurwa ana yin KARON BATTA.
Nan fa sassan jikkunan bil'adama ya dinga shawagi a sama suna zubo ƙas, hankakan mutuwa ya yi dirar mikiya a wajen ya wanzu yana kai komo wajen ɗaukar rayuka.
JINI DA ƘASA suka haɗu waje guda, ihun da kururuwar mazaje gami da haniniyar dawakai ta cika dodon kunne.
A wannan lokaci mahaifina sarki Zammar ya shiga izuwa cikin gidan sarautar yana shirin yaƙi, jim kaɗan sai ga shi ya fito izuwa filin daga kawai sai ya afka cikin abokan gaba ya hau su da sara da suka.
Yazamana cewa duk inda ya sanya a gaba sai dai ka ga dakarun matsafi Sahibul-ukub na zubewa ƙasa matattu tamkar yana sassabe a gonar auduga.
Sa'adda matsafi sahibul-ukub ya ga irin muguwar ɓarnar da mahaifina ke yi mashi, sai ya ruga izuwa inda ya ke ya tare shi suka kacame da azababban yaƙi mai matukar muni daban tsoro.
Ana fara wannan arbu ne mahaifina ya fara gane cewa tabbas shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin kuwa duk sa'adda matsafi Sahibul-ukub ya kai mashi hari da takobinshi idan ya kare harin, sai kaga ƙarfin saran ya cilla mahaifina sama ya yi ƙundumbala ya kife a ƙasa, amma saboda juriya da mafi irin ta GWARAZAN JIYA sai ya miƙe tsaye zumbur, ya ci-gaba da mayar da martani
A wasu lokutan kuwa idan ya kai mashi harin ya kauce, sai ka ga duk abin da takobin
Sahibul-ukub ta sauka a kanshi ya kama da wuta, kafin cikar rabin sa'a Sahibul-ukub ya galabaitar da mahaifina ya faɗi ƙasa magashiyan ya na amai na jini ta baki da hanci.
Wannan shi ne abin da ya faru a masaukin gimmbiya Mashlira 'yar sarkin maridai da Sarki lazwar.
Kamar yadda ya wakana a masaukin gimbiya Mashlira da sarki Lazwar haka al'amarin yakasance a masaukin yarinya Shuraiba da aljani ZA'ARATUN-LAYAL
A inda Za'aratun-layal ya ci gaba da bawa yarinya Shuraiba hikayar sarauniya Abidat ta birnin Sin.

Babi na goma

Lokacin da wannan zakanya ta ruga izuwa inda suhaimat da jaririyar ta ke kwance, koda taga halin da take ciki sai ta ruga izuwa bakin wata ƙorama ta guntso ruwa a baki ta dawo izuwa inda take ta fesa mata ruwan a fuska.
Faruwar hakan keda wuya sai suhaimat ta ja dogon numfashi gami da sauke nannauyar ajiyar zuciya, idanuwanta suka buɗe tarwai ta wartsake daga suman da tayi kawai sai ta miƙe zaune.
Ya yin da tayi arba da zakanyar sai ta razana ainun ta ja da baya tana mai ɗaukar jaririyar ta ta ƙanƙame ta a ƙirji.
Koda ganin halin da suhaimat ta shiga sai zakanyar ta juya ta ruga izuwa cikin wannan kogon dutse dake dajin.
Cikin matukar farin ciki suhaimat ta mike tsaye taje bakin wannan ƙorama ta yi wa jaririyarta wanka, ita ma ta tsafta ce kazantar da ke jikin ta, sannan ta dawo izuwa ƙarƙashin wata bishiya ta zauna ta shiga sharar da jaririyar tana mai shafa gashin kanta, zuciyar ta cike da matuƙar farin ciki maral misaltawa.
Kuma ta shiga tambayar kanta a cikin ranta tana cewa,
dhin wane ne ya kashe waɗannan dabaru? Ko kuwa wannan zakanya ce?
Amsar tambayar da ta kasa bawa kanta kenen,tana cikin wannan hali ne zakanyar ta dawo gare ta bakin ta rike da waɗansu tarin ganyayyaki ta a jiye a gaban ta,
Bisa mamaki a wannan karon sai Suhaimat taji ko kaɗan ba ta tsora ta da ganin zakanyar ba, bata re da fargabar komai ba ta ta duba abin da ta kawo ɗin. Ai kuwa sai taga a she nau'ikan kayan marmari ne dangin su ayaba da inibi, kawai sai ta shiga kimtsa cikinta har sai da ta ci ta ƙoshi, sannan ta fasa kwakwa ta shanye ruwan cikinta.
Zakanyar na tsaye na tsaye a gefe guda tamkar mai jiran umarni, a sannanne Suhaimat ta lura cewa jikin zakanyar akwai jini, take ta fahimci cewa ita ce ta kashe waɗannan dakaru domin ta ceci rayuwar ta da jaririyar ta.
Lokacin da aljani ZA'ARATUN-LAYAL ya zo dai-dai nan a hikiyar sarauniya Abidat ta birnin Sin da yake bawa yarinya Shuraiba sai ya tsuke bakinshi ya yi shiru.
Al'amarin da ya sanya yarinya Shuraiba ta dube shi cikin alamun tsananin damuwa ta ce "ya kai masanin HIKAYAR DUNIYA shin mene ne yasanya zaka katse min wannan daddaɗan labari? Tabbas ina so naji wace irin rayuwa Suhaimat da jaririyar ta za su yi a nan gaba, kuma menene dalilin da ya baro da ita daga birnin su?
Shin ma mene ne ya sanya dakarun ke farautar Suhaimat?
Koda jin waɗannan tambayoyi sai aljani ZA'ARATUN-LAYAL ya bushe da dariya ya dubi yarinya Shuraiba ya ce "ya ke Shuraiba shin baki gani ba ne har alfijir ya keto safiya ta yi".
Koda jin wannan batu daga bakin Za'aratun-layal sai Shuraiba ta cika da mamaki, ai kuwa sai ta miƙe tsaye ta domin ta fara shiri kamar yadda sarki Lazwar ya yi masu bayani.
Wannan shi ne abin da ya faru a masaukin yarinya Shuraiba.
Kamar yadda ya wakana a masaukin Shuraiba haka al'amarin ya kasance a masaukin darki Lazwar da gimbiya mashlira.
A inda Mashlira ta katse labarin bawa sarki Lazwar na matsafi Sahibul-ukub da mahaifin ta sarki Zammar.
Saboda ganin ketowar alfijir a sararin samaniya.
A ɓangaren masaukin yaro Imran kuwa, ya yin da ya ga alfijir ya gabato sai ya ɗaura alwala ya shiga gabatar da nafita, bayan nan kuma sai gudanar da sallar asuba, q lokacin da hadima khadijat ta bisa a baya a matsayin mamu.
Lokacin da rana da fito ne ta yi haske sai khadijat ta yi umarni aka kaiwa kowannnen su bahon ruwan wanka, bayan kowa ya tsaftace jikinshi ya yi kalaci, sai aka ɗunguma izuwa cikin gari domin gudanar da abin da aka zo nema.
Wannan shi ne abin da ya faru da su sarki Lazwar a lokacin da aka kai su izuwa masauki.

Babi na sha ɗaya

Lokacin da amarya Munirat ta ci gaba da tafiya a cikin gidan sarautar birnin Darul-usur bayan ta kuɓuta daga sharrin magajin gari Yasiran.
Sai ta cigaba da tafiya a cikin gidan sarautar tana ratsa ƙofofi da dakaru iri daban-daban, zuciyarta cike da matuƙar farin ciki maral musaltuwa.
Ta na cikin wannan hali sai wannan tsuntsu ya sake bayyana a gare ta a sama cikin iska
Tsuntsun ya riƙiɗa izuwa wani kyakkyawan aljani mai kyawun sura, aljanin ya na ɗauke da sura irin ta bil'adama, sai dai yana ɗauke da fuka-fukai.
Aljanin ya dubi Munirat ya ce "ya ke Munirat ki yi sani cewa da farko dai suna na Lailatul-azhar kuma ni hidimi ne ga sarkin musulmin aljanun duniya baƙaƙen fata.
Ubangiji ya bayyana wa sarkin mu halin da ki ke ciki dama sauran mutanen birnin ku na irin baƙin zaluncin da magajin gari Yasiran ke yi maku, sannan kuma ya turo ni ne domin na kawo ƙarshen mulkin zaluncin shi baƙi ɗaya.
Ki yi sani cewa kalaman da ki ka karanta a jikin fuka-fukaina har kika tsira daga sharrin magajin gari, ba wasu kalmomin ba face KALMAR SHAHADA wacce duk wanda ya furtata ta da tabbatar wa a zuciyarshi to ya yi imani da Ubangijin gaskiya da ya halicci komai da komai.
Idan har kin bayar da gaskiya da Ubangijin ɗaya daya baki nasara akan magajin gari to tabbas zamu samu nasarar ganin bayanshi.
Koda jin wannan batu daga bakin aljani Lailatul-azhar sai amarya Munirat ta cika da matukar farin ciki maras musaltuwa, ta dube shi ta ce "ina so yanzu ka shigar da ni addinin ka".
Ba tare da wani ɓata Lailatul-azhar ya karanta mata KALMAR SHAHADA.
Nan fa ya zamana cewa kafin mako guda fiye da mutanen birnin sun karɓi addinin musulunci a hannun amarya Munirat.
Magajin gari Yasiran kuwa sai ya kamu da wata irin rashin lafiya, sakamakon wannan wuta da ta ƙona jikinshi,
Nan fa aka rasa wanda zai gaje shi a kan karagar mulkin shi.
'Yan Majalisar suna ganin cewa tabbas yanzu hawa karagar mulkin Yasiran ana iya kiran shi da SARAUTAR MUTUWA. Domin su ganin a ko da yaushe magajin gari zai iya samun lafiya, ko kuma sarki Lazwar ya dawo daga tafiyar da ya yi.
Saboda ba zai yiwu a zauna haka babu shugabanci bisa dole jama'ar gari suka ɗora amarya Munirat a matsayin sarauniyar su.
Nan fa jama'a suka fara samun yanci, farin ciki gami da walwala sakamakon hasken musulmi da bayyana a gare su,
Al'amarin Shuraiba kuwa Lokacin da ta cigaba da tafiya a cikin birnin Istanbul domin nemo mahaifiyarta sai ta wanzu tana tafiya babu sassauci, tana cikin wannan hali ne sai ta hango wajen waɗansu almajirai ke zaune suna bara a kasuwar, kawai sai ta matsa izuwa daf da inda suke ta shiga yin nazarin su.
Abu na farko da ya faɗo mata a rai shine shin yanzu ina kike da tabbacin mahaifiyarki take, ki na ganin cewa mahaifiyarki zata kasance daga cikin waɗannan almajirai dake yin bara? An ya kuwa sarki Ladiyas bai mayar da mahaifiyar ki matar shi ba?
Amsar tambayoyin da ta kasa bawa kanta kenen.
kawai sai ta ɗauki mayafi ta ɗaure fuskarta da rawani, kana ta ɗauki wani ƙoƙo ta ajiye a gaban ta, sannan ta shiga izuwa cikin su ta saje da su tamkar ba ita ba.
Zaman ta ke da wuya sai wata dattijuwar almijira dake kusa da ita ta du be ta ta ce "ya ke wannan yarinya shin ke kuwa me kika rasa a rayuwar ki da za ki fito bara, baƙya duba wa ki ga cewa ke yarinya mai karancin shekaru".
Koda jin wannan batu daga bakin dattijuwar sai Shuraiba ta cika da matuƙar mamaki ta dube ta ta ce "ya ke wannan dattijuwa ki yi sani cewa bakomai ba ne ya sanya ni aikata wannan bara ba sai domin na samu abin da zanyi kalaci. Mahaifina ya mutu tun ina da shekara bakwai a duniya, mahaifiyata ce take a raye ina neman ta ruwa a jallo, domin ita ce kaɗai ta rage min a duniya.
Koda jin amsar wannan tambaya sai dattijuwar ta bushe da yar karamar dariya ta dube ta ta ce "tabbas yaro yaro ne kuma duk wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi, na san cewa akwai muhimmin al'amari daya sanya ki zuwa wannan waje domin, ban taɓa ganin ki ba tun da nake fitowa wannan bara tawa".
Koda jin wannan batu daga bakin dattijuwar sai Shuraiba ta yi dariya ta ce "tabbas da akwai buƙatar hakan da na nema a wajen wani tun kafin na iso wannan waje, amma tambayar da zan yi maki wace matsalar dake tattare da wannan waje?
Dattijuwar ta yi dariya ta ce ''ya ke wannan yarinya ki yi sani cewa bakomai yawan dinaren da mutum zai samu na sadakar da za a bashi, sai dakarun sarki Ladiyas sun zo sun karɓi haraji, da ƙyar za ka samu ka tsira da kaso ɗaya cikin goma. Idan kuwa aka yi rashin sa'a baka samu sadaka ba, to fa sai sarki ya sanya an kai mutum aikin horo a gidan sarauta domin ka yi aiki adadin wannan dinare da baka biya harajin ba";
Da jin wannan batu daga bakin almajirar sai yarinya Shuraiba ta ji ta ƙara tsanar sarki Ladiyas fiye da komai a rayuwar ta. Sannan ta dubi almajirar cikin alamun matuƙar tausayin ta ce "tabbas sarki Ladiyas ya cika azzalumi kuma maras tausayi, yanzu a ce almajirai ma sai sun biya haraji,
Koda jin wannan batu sai mamaki almajirar har ta buɗi baki da nufin ta ce wani abu sai a ka hango dakarun sarki Ladiyas sun shigo kasuwar a bisa dawakai su kamanin ɗari biyu shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannayensu ɗauke da waɗansu murtuka-murtukan kulake.
Nan fa kasuwar ta hargitse jama'a suka dunga kwashe kayayyakin su suna buɗa wa dakarun hanya, domin idan har suka iso mutum bai kwashe ba take za su bi ta kan kayan da dawakan su su tattake.


Please Login or Register in order to submit comment