Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka sake ɗunguma aka ci gaba da tafiya.
Ana fara wannan tafiya ne sai fira ta ɓarke tsakanin yarinya Shuraiba da aljani Za'aratun-layal,
A inda Shuraiba ta dubi Za'aratun-layal tayi gyaran murya ta ce " ya kai wannan dattijon aljani wai kuwa idan ba za ka damu ba nayi maka wata tambaya mana.
Ko da jin wannan batu sai Za'aratun-layal ya ce " faɗi tambayar ki ya ke Shuraiba
Shuraiba ta ce "wai kuwa a yanzu a cikin jinsin ku na aljanu akwai wanda yafi ka yawan shekaru?
Koda jin wannan tambaya sai Za'aratun-layal ya bushe da dariya har da kyakyatawa ya ce "a halin yanzu ni ne ɗan auta a cikin jinsin mu na aljanu a ƙalla zan kai shekaru dubu ɗari uku da haihuwa'' .
Cikin matuƙar mamaki shuraiba ta ce "ai kuwa in dai haka ne jinsin aljanu sun fi kowa daɗewa a duniya.
Za'aratun-layal ya ce "kwarai kuwa zancen ki dutse".
Shuraiba ta ce "amma kuwa mai yasa kuke yiwa bil'adama bauta alhalin kunfi su sanin halin da duniya ke ciki
Za'aratun-layal ya ce "Tabbas ke yarinya ce ba ki san komai game da halin duniya ba amma bari na ba ki hikayar sarauniya ABIDAT ta birnin Sin wata ƙila ki shaida batu na.
Za'aratun-layal ya yi gyaran murya sannan ya fara da cewa

Babi na uku

Wata mace 'yar kimanin shekaru ashirin da uku ɗauke tsohon ciki a jikinta sanye da tufafi kayan fata riga da wando.
Zaune take a bisa kan wani ingarman doki baƙi, tafiya take a cikin wani irin daji mai tattare da sarƙaƙiya, kwazazzabai gami da duwatsu.
Kallo ɗaya za ka yiwa matar ka fahimci cewa tana cikin mawuyacin hali.
Kaico! Tana cikin wannan hali ne sai ta ji alamun naƙuda sun bijiro mata, kawai sai ta ja linzamin dokin ta tsaya cak sannan ta kama ta sauko ƙasa kawai sai ta taka da ƙyar ta durfafi kofar wani kogon dutse.
Kafin ta isa sai kawai ta yanke jiki ta faɗi ƙasa, a cikin wannan hali ne naƙuda ta kamata ta haife abin da ke cikin ta .
Cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa ta ɗauki abin da ta haifa domin ta ga mene ne, ai kuwa sai ta ga wata santaleliyar yarinya ce kyakkyawa ta gaban kwatance,
duk da cewar tana cikin wannan hali na laulayi bata san sa'adda hawayen farin ciki suka kwaranyo daga idanuwanta ba, a dai-dai wannan lokaci ne kukan jaririyar ya cika dajin baki ɗaya, cikin hanzari ta ɗauki wani ice mai kaifi ta yanke cibiyar jaririyar.
Tana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai ta hango waɗansu dakaru sun durfafo inda take a bisa dawakai.
Kafin tayi wani yunƙuri ɗaya daga cikin dakarun ya ɗame kibiyarshi ya harbe ta a gadon bayanta, saboda tsananin zafi da raɗaɗin da ta ji bata san sa'adda ta kurma wawan ihu ba ta sulale ƙasa sumammiya jaririyar da shiga tsala kuka.
Har badakaren ya sake yin shiri a karo na biyu da nufin ya sake harbin matar.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga wata murgujejiyar zakanya ta yi fitar burgu daga cikin wannan kogon dutse dake dajin, ta dako wawan tsalle ta daki badakaren a kirji.
Saboda matuƙar ƙarfin bangazar sai da badakaren da dokin shi su ka yi sama tamkar an janye su da ƙungiya, sannan daga bisani suka faɗo ƙasa matattu ko shurawa ba su yi ba.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin zakanyar da mayaƙan.
daga can sai zakanyar ta yi gurnani gami da hargagi sannan ta dako wawan tsalle izuwa kan mayaƙan.
Ko da ganin hakan sai dakarun su ka ɗaga makamansu suka yi ihu da kururuwa mai firgitarwa suka yi ɗauki kanta aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar muni, ban tsoro da ban al'ajabi.
Wohoho! Haƙiƙa yaƙi shi ne matattarar dukkan bala'i da musiba, kuma idan gwani ya haɗu da gwani JURIYA DA BAJINTA suka game waje guda, dole ne artabu ya zamo abin tsoro.
Nanfa zakanyar ta wanzu tana hallaka dakarun, ya zamana cewa duk inda ta sanya gaba sai dai ka ga dakaru na zubewa ƙasa matattu, a inda za ka ga ta mako badakare faga kan dokinshi ta bishi ta turmushe.
A duk sa'adda dakarun su ka kaiwa zakanyar hari sai ka ga ta wurƙila haɗe da zame wa ta kaucewa saran, kafin badakare ya sake daga takobinshi zakanyar ta dako tsalle sama ta sanya faratanta ta tsire mashi idanu ruwan cikin ya tsiyaye, take zai sulale ƙasa daga kan dokinshi yana mai kurma wawan ihu.
Kai wasu lokutan idan ta daki badakaren a wuya sai ka ji wuyanshi ya ƙara ya karye ya yi ƙara jikake ruƙus!! Ƙas! Ya faɗi kasa matacce ko shurawa bai yi ba.
Haƙiƙa waɗannan dakaru suna ganin tashin hankalin da ba su taɓa ganin irin shi ba.domin kafin cikar rabin sa'a zakanyar ta kashe fiye da rabin su.
Nanfa ƙarar karafniyar ƙarafa da ihun mazaje, haniniyar dawakai haɗe da gurnanin zakanyar ya cika dajin baki ɗaya, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda dawakai ke yin turmutsutsu, kofatunsu na kartar ƙasa.
Wohoho! tabbas masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce wuya ko da magani babu daɗi, kuma wuya mai sa dole.
Hakan ce ta faru ga sauran dakarun, domin koda su ka ga cewa a kowanne lokaci za su iya baƙuntar barzahu sai suka cika wandunansu da iska domin GUDUN TSIRA da rayuka,
sai zakanyar ta dunga ƙure masu gudu tana make su suna faɗuwa ƙasa matattu. Kafin wani lokaci ta zubar da gawarwakin su a ƙasa.
Kawai sai ta juya ta durfafi inda wannan mata da jaririyar ke kwance a ƙasa tana fitar da wani irin gurnani.


Babi na huɗu


Lokacin da aljani da aljani Za'aratun-layal ya zo dai-dai nan a hikiyar sarauniya Abidat ta birnin Sin sai ya ja bakinshi ya yi shiru.
Cikin alamun matuƙar damuwa Shuraiba ta dube shi ta ce "haba ya masanin HIKAYAR DUNIYA mene ne ya sanya za ka yanke ba ni wannan labari mai matuƙar daɗi gami tsantsar tausayi, haƙiƙa na matsu naji a wane hali wannan mata da jaririyarta su ke ciki?
Kuma wace ce wannan zakanya da ta ceci rayuwar su? Shin mahaifiyar jaririyar ta na raye ko kuwa ta mutu sakamakon harbin kibiya da wannan badakare ya yi mata a gadon baya".
Ko da jin wannan batu sai Za'aratun-layal ya cewa da Shuraiba ''shin baki lura da inda muka iso ba ne? Leka izuwa kasa ki gani".
Da jin hakan sai ta sunkuya da kanta ƙasa aikuwa sai ta hangi wani irin baƙin daji mai matuƙar kwarjini da ban tsoro.
Sarki Lazwar ya dubi aljani Za'aratun-layal ya ce ''shin me ka fahimta da wannan daji dake gaban mu?
Za'aratun-layal ya yi shiru kamar mai tunanin wani abu sannan ya ce " ya shugabana wannan daji dake gaban mu yana ɗauke da tsananin sanyi don haka dole ne kowannen ku ya sanya suturun kariya, sannan kuma dukkanin daji da ya kasance yana tattare da irin yanayin to dole ne a samu miyagun halittu masu shan jinin bil'adama da cin naman su, sai inda kizo ke saƙar shi ne bani da tabbacin waɗanne irin halittu ne.
Ko da jin wannan batu daga bakin Za'aratun-layal sai kowa yasha jinin jikinshi.
Cikin hanzari sarki Lazwar ya zira hannunshi a aljihun rigarshi ya ɗauko madubin tsafin shi da nufin gudanar da bincike, amma sai aljani Za'aratun-layal ya yi wuf da dakatar da shi ya ce ''ya shugabana ka yi sani cewa amfani da sihirin tsafi a irin wannan tafiya abu ne mai matuƙar haɗarin gaske domin baka da tabbacin cewa wanda za ka yi binciken bai fi ka karfin sihiri ba. Sannan shin ka manta cewa kowa a gidanshi sarki ne,
mafita ɗaya ce a gare mu kowanne ku yakasance cikin shiri tun da gashi yanzu la'asar ta riske mu, ba zamu ɗauki wani tsawon lokaci ba duhun magariba zai gaba ce a dajin kenan dole yaɗa zango cikin dajin dole ne domin mu kwana mu huce gajiyar dake tare da mu.
Da jin wannan batu sai kowa ya shiga sanyawa kanshi rigunan sanyi tun daga ƙasa har sama kuma kowa ya gyara riƙon makamin shi.
Za'aratun-layal ya yi ƙasa-ƙasa ta fuka-fukanshi sannu a hankali har aka sauka a bisa turba .
Sa'adda kowa ya yi arba da dajin sai tsoro ya kara kama shi.
Shi dai wannan daji yakasance gaba ɗayan shi yana ɗauke da waɗansu irin dogayen bishiyu masu rassa masu matuƙar kaifin tsiya masu tattare da sarƙaƙiya, babu wani waje da mutum zai ajiye kafarshi face ya taka dusar ƙanƙara ce, Babu abin da zai ƙara firgita mutum kuma ya jefa tsoro a zuciyarshi sai jin shiru da ya wanzu a dajin tamkar babu wani abu mai rai a cikin shi, kai hatta irin tsuntsaye haka a saman bishiyoyin babu su.
Nan fa aka fara tafiya a cikin ɗar ɗar domin shirin ko ta kwana, amma bisa mamaki sai ga shi an shafe tsawon rabin sa'a ba tare da an jiyo motsin wani abu mai cutarwa ba.
Al'amarin da ya sanya kowa ya fara sakin jikinshi kenan, ana cikin wannan tafiya ne tsinin reshen wata bishiya ya yanki bawa zafiyar a cinyarshi jini ya zuba a ƙasa.
Kawai sai a ka ji gaba ɗaya dajin ya kaure da wani irin gurnani mai ban tsoro ba shiri kowa ya tushe kunnuwanshi domin ƙarar na iya kurumtar da mutum.
Abin da su sarki Lazwar ba su sani ba shi ne zubar jini a dajin shine alamun da halittun ke gane cewa bil'adama ya shigo dajin.
Kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu irin zaratan muradai na fitowa daga kowacce kusurwa a dajin.
Muridan sun kasance masu matuƙar tsawo tamkar bishiyar kuka. Jikkunansu a mummurɗe suke tamkar duwatsu suna da rafkeken kai mai ɗauke da idanu ƙwaya ɗaya jal! Wanda ya kasance jajur tamkar garwashin wuta, fuskokin su munana ne babu kyawun gani, duk sa'adda su ka wangame bakunansu sai ka ga cewa wani irin yawun mai yauƙi na dalala, a hannayen su kuwa suna ɗauke da waɗansu irin masifaffun makamai na yaƙi da idanu basu taɓa gani ba, a ƙalla adadin muridan ya kai dubu uku da ɗoriya.
Lokacin da muridan suka kammala yiwa su sarki Lazwar ƙawanya, sai aka fara kallon-kallo tsakanin ɓangarorin biyu,tsawon daƙiƙa arba'in ana cikin wannan hali sai daga bisani ne muridan su ka yi wata kururuwa mai firgita dandazon mayaƙa a filin daga, su ka yi ɗauki izuwa kan su,
Koda ganin hakan sai su sarki Lazwar su ka yi kururuwa suka ruga izuwa kan muridan.
Ana haɗuwa aka yi muguwar KARON BATTA
Wohoho! Haƙiƙa tashin hankali ba'a sa mai rana, kuma ita wutar bala'i kafin ta zo ne ake guje mata, amma idan tazo kawai miƙa wuya ake yi a tare ta ko dai a mutu ko a yi rai.
Kaico! ana fara wannan arbu ne su sarki Lazwar suka fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin muridan sun zame masu tamkar GOBARAR ANNOBA.
Duk sa'adda ɗaya daga cikin ya kai wa su sarki Lazwar hari da makaminshi, idan su ka goce saran ya sauka akan bishiya sai ka ga ta rabe gida biyu ta faɗi ƙasa rikica za ta danne su.
Kafin ka ce me tuni muridan sun hallaka fiye da dakaru gami da kuyangi fiye da guda dubu.
Al'amarin da ya yi matuƙar figita su sarki Lazwar kenen, babban abin da ya fi dugunzuma hankalin su shi ne yadda muridan suka kasance masu matukar zafin nama, tamkar jikkunan su na amfani da wata na'ura dake sarrafa su.
Shi kan shi aljani Za'aratun-layal duk irin matuƙar karfin damtsen shi sai da ya zamana muridan sun zamto mashi ciwon idanu.
A ɓangaren yarinya shuraiba kuwa ana cikin wannan yaƙi ne wani daga cikin muridan ya kawo mata wani wawan sara da gatarinshi da nufin tsinke mata wuya,
Cikin wani irin baƙin zafin nama ta zille wa saran gatarin muridan ya shige cikin ƙarƙashin ƙasa.
Kafin muridin ya zare gatarin na shi Shuraiba ta ɗame bakanta ta harbe shi da kibiya a idon shi guda, take ya fashe jini ya dunga kwarara tamkar an buɗe kan fanfo, nan fa muridin ya faɗi kasa yana mai kwarara ihu yana birgima zuwa wani lokaci ya sheƙa barzahu komai na jikin shi ya dai na motsi.
Ko da yarinya Shuraiba ta ga wannan nasara da ta samu sai ta cika da matuƙar farin ciki, kuma a sannanne ta fahimci cewa ruhikan muridan suna cikin wannan idanu na su guda ɗaya dake tsakiyar goshin su.
Kawai sai ta ci gaba da ta harbin muridan a idanun su cikin matuƙar ƙware wa da zafin nama.
Wohoho! Gaskiyar masu iya magana da suka ce kyan ɗa ya gaji ubanshi, kuma ita sadaukantaka gadon a ke yi ba wai a kasuwa ake siyarwa ba.
Haƙiƙa babu wadda zai yi arba da yarinya Shuraiba a cikin wannan hali face ya jinjina mata.
A ɓangaren sarki Lazwar, sarkin yaƙi da su bawa Kuwait kuwa, sa'adda suka ga yadda yarinya Shuraiba ta gano lagon muridan har ta na samun nasarar hallaka su sai suka yi koyi da ita.
Ya zamana cewa suna daka tsalle sama suna hawa kan muridan suna amfani da takubban su suna soke masu idanu.
Aljani Za'aratun-layal kuwa hannunshi ya dunƙule ya shiga naushin muridan a idanuwansu. Duk wanda ya gabza wa naushin sai dai ka ga ya faɗi kasa matacce.
Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan kiɗa ya canja dole ne rawa ta canza. Nan fa muridan suka fara gane kuren su suna yin muguwar hallaka a banza, komai hassadar mutum idan ya ga yadda sarki Lazwar ke ragargazar muridan dole ne ya jinjina mashi ya tabbatar da cewa tabbas Lazwar ya cika GWARZON DUNIYA kuma SARKIN SADAUKAI.
Saboda yadda yake kashe muridan tamkar yana sassabe a gonar auduga.
Lokacin da aka shafe sa'a ana wannan arbu sai ya zamana cewa duhun dare ya fara kawo kai, nan take tsananin sanyin dake dajin ya daɗa ƙaruwa.
Nan fa su sarki lazwar suka shiga cikin wani tashin hankali, kuma tsawon lokacin da aka shafe ana wannan gumurzu bai huce muridan guda ɗari kacal ba aka hallaka ba.
Koda ganin halin da ake ciki sai sarki Lazwar ya karanto waɗansu dalasiman tsafi domin samun mafita.
Kaico! Hakikya rashin sani yafi dare duhu, inda a ce sarki Lazwar ya san abin da zai biyo baya da bai yi gangancin karanta dalasiman tsafi ba, domin kuwa faruwar keda wuya sai wata irin iska ta musamman ta mamaye dajin baki ɗaya wacce ta sanya sanyin ya kara tsanan ta. kawai sai ya ga jama'ar ya yanke jiki suna faɗuwa ƙasa sumammu.
Ko da ya waiga bayan shi domin ya ga a wane hali
yarinya Shuraiba ke ciki.
Kawai sai ya ga wayam babu ita babu alamar ta, kafin ya mayar da duban shi zuwa ga su sarkin yaƙi sai kawai ji ya yi an gabza mashi wani wawan naushi a fuska take hankalin shi ya gushe ya dai na gane kanshi.
Su sarki Lazwar ba su tsinci kansu a ko ina ba sai a cikin wani ɗakin duhu, wanda saboda matuƙar duhun shi mutum ko tafin hannayenshi ba ya iya gani, a bisa cikin wani irin ƙaton keji da aka yi shi da zallar waɗansu irin itace masu ƙwarin gaske.
Jim kaɗan da farkawar su sai kawai su ka ga ɗakin ya gauraye da wani irin haske mai ban mamaki.
Sai a sannanne sarki Lazwar ya gane cewa kowannen su an sanya shi a keji na daban ba tare da an gama shi da ɗan uwanshi ba, hatta aljani Za'aratun-layal na shi kejin daban, amma duk an daɗɗaure shi da waɗansu irin sarƙoƙi na baƙin ƙarfe.
Sa'adda kowannen su ya sake buɗe idanuwan shi tarwai ya ga babu yarinya Shuraiba da gaba ɗaya sauran tawaga, sai hankulan su suka dugunzuma ainun, kuma aka shiga firgici, aka fara tunanin shin ko yarinya Shuraiba da tawaga sun rasa rayukansu ne.
Shi kanshi aljani Za'aratun-layal da bai kasance bil'adama ba sai ya ji a ran shi yana matuƙar kewar Shuraiba tamkar da ma sun daɗe da shaƙuwa da juna.
Tsawon lokacin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne sai su kaji karar buɗe sakatun kofar ɗakin.
Jim kaɗan sai Kofar ta buɗe sai ga waɗansu irin zaratan dakarun muridan su bakwai sun shigo cikin ɗakin.
Kallo ɗaya su sarki Lazwar su ka yiwa dakarun suka sunƙuiyar da kawunan su ƙasa, saboda matukar kwarjinin da munin siffar su.
Dakarun su ka durfafi inda su sarki lazwar suke, su na isa gare su suka ɗauki kejin da suke ciki su ka ɗora a bisa kafaɗunsu, wanda aljani Za'aratun-layal ke ciki kuwa dakaru biyu suka ɗauka, kawai sai su ka fice daga cikin ɗakin, suka durfafi wata hanya ta musamman su ka shiga izuwa cikin gari.
Nan fa su sarki lazwar suka cika da matuƙar mamaki da al'ajabi suka kama kalle-kalle da dube dube-dube, tamkar ɗan ƙauye ya shiga birni, shi dai gaba ɗaya birnin muridan an gina gidajen shi da waɗansu irin manyan duwatsun wuta masu kwarin gaske, masu matukar tsawo da faɗi.
Ko da jama'ar birnin su ka yi arba da su Lazwar sai suka cika da matuƙar murna, su ka suka shiga tanɗe bakunansu gami dalalar da yawu, saboda matuƙar kwadayin yau za su kalaci da naman bil'adama.
Tafiyar daƙiƙa talatin kacal! aka yi aka iso fadar birnin.
Fadar ta kasance tanƙamemiya mai matuƙar tsawo da faɗi, kuma gininta anyi shi ne da irin waɗannan duwatsu masu ƙyalli, sannan an ƙawata ta da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya har dama abin da idanu ba su taɓa gani ba.
A wannan lokaci fadar ta cika maƙil da jama'a maza da mata yara da manya, babu masaka tsinke, bisa wata ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'an ta ta da zallar ƙarfen jauhari, aka yi mata feshi da koren ruwan yaƙut.
Wani irin shirgegen mutum ne wanda yafi gaba ɗaya muridan girma kwarjini da cika idanu zaune bisa wata ƙasaitacciyar karaga. yana sanye cikin wata irin ƙasaitacciyar shiga irin ta su ta manyan sarakai, sanye da wata alƙyabba da aka yi mata ado da gashin ɗawisu kanshu sanye da wani KAMBUN SARAUTA na zinare.
Zaune a gefen hannunshi na dama, wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa ce ta gaban kwatance.
Budurwar tana da dara-daran idanuwa farare ƙal! Masu haske tamkar tacacciyar madarar shanu, ɗigon cikin su ya kasance siɗik mai kwarjini, girar saman su baƙa ce siɗik tayi luf-luf, hancinta dogo ne mai ban sha'awa, a ƙasan shi an tsaga wani ɗan madaidaicin baki da labbanshi suka kasance jajur, wuyanta dogo mai kyau tamkar na barewa, kirjinta kuwa ya yi tudu a cike yake kuma a tsaye ƙyam! Bai ranƙwafa ba tamkar nunanniyar gwanda, cikinta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, ƙugunta daga gaba ya tsuke daga baya kuma ya yi tudu tamkar idan aka ɗora tuffa za ta zauna, 'yan yatsun hannayenta da kafafuwanta sun kasance zara-zara masu ɗaukar hankali.
Wohoho haƙiƙa Allah wannan budurwa ta cika kyakkyawa ta kece raini, babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi tozali da wannan kyakkyawar halitta face ya ɗimauce, kuma ya kamu da matukar kaunar ta a zuciyarshi.
Ba wata ba ce face gimbiya Mashlira 'ya ga sarki muridan Kushuful-mannar
Sarki Kushuful-mannar ya auri mahaifiyarta ne a cikin waɗansu a yarin larabawa da aka riba to a matsayin fursunonin yaƙi, bisa binciken da sarki Kushuful-mannar ya yi bisa halarar tsafin shi ya gano cewa 'yar shi Mashlira ce silar dauƙaƙar shi a duniya da ci-gaban zuri'arshi a doran ƙasa, bisa wannan dalili ne ya sanya ya ke matuƙar kaunar ta fiye da komai a rayuwarshi.
Tun kafin dakarun da suke ɗauke da su sarki Lazwar su iso inda karagar mulki take gimbiya Mashlira ta ƙurawa Lazwar idanu ko ƙiftawa ba ta yi, a karon farko a rayuwar ta ta ji wani abu ya ɗarsu a zuciyarta.
Shi kuwa sarki Lazwar koda ya ga irin kallon da budurwar ke yi mashi sai ya ji zuciyarsa ta buga da karfi tsoro ya kama shi jikin shi ya kama ƙyarma, abu na farko da jefa shi cikin wannan hali shi ne, a iya tsawon rayuwarshi tun da yake bai taɓa gani ko jin labarin 'ya mace mai matuƙar kyawun ta ba.
Abu na biyu kuwa shine lokacin da da ya haɗa idanu da ita sai ya ji cewa a duk faɗin duniya babu wata budurwa da yake ƙauna tamkar ta.
Yanzu ta ya ya zuciyarshi za ta kamu da soyayyar wata 'ya mace bayan cewa ba zai taɓa kusantar mace ba da niyar aure ba face ya karya sihirin dake jikinshi.
Wai shin wane tabbaci ya ke da shi cewa waɗannan muridan za su bar shi a raye,
Sa'adda sarki Lazwar ya zo nan azancen shi sai hankalinshi ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe.
Lokacin da ya rage sauran kamar taku goma tsakanin su da karagar mulki sai dakarun su ka zube ƙasa, su ka kwashi gaisuwa cikin girmamawa bayan sun ajiye kejin da su Lazwar ke ciki.
Sarki kushuful-mannar ya shin-shina su sarki Lazwar yana mai tanɗe baki tamkar wadda zai ci naman ɗawisu.
Sannan ya busar da iskar dake hancinshi wani irin tiririn baƙin hayaƙi ya fita daga ƙofofin hancinshi.
Kawai sai ya yi wa ɗaya daga cikin dakarun wata inkiya ta wutsiyar idanu. kawai sai badakaren ya buɗe kejin da bawa zailan ke ciki ya ɗauko shi ya kwantar da shi akan wani zagayayyen tudu, sannan ya ɗauko wata zabgegiyar takobi ya ɗaga sama ya datse wuyan bawa Zailan kuma ya shiga daddatsa naman shi.
Koda ganin yadda aka yiwa bawa Zailan sai su sarki Lazwar su ka kamu da matuƙar tausayin shi har ƙwalla ta cika masu idanu.
Badakaren na kammala daddatsa naman sai ya watsawa jama'ar dake fadar.
Tun kafin ya kai ƙasa jama'a sun wawashe sun cinye suna ihun murna da kururuwa mai tayar da hankali.
Badakaren ya sake sanya hannuwanshi a kan kejin da sarki Lazwar ke ciki ya buɗe sakatun, ya zira hannun sa ya ɗauko shi ya ɗora shi a bisa wannan tudu, a karo na biyu ya sake ɗaga takobin domin ya datse wuyan sarki lazwar.
Kafin takobin ta datse wuyan Lazwar sai gimbiya Mashlira ta dakawa badakaren tsawa sannan ta dubi mahaifinta ta ce "ya abbana ina neman wata alfarma a gare ka da abar mani waɗanan fursunoni zuwa gobe, domin nima ina so na ga na hallaka su da hannaye na domin ɗaukar fansar kisan da su ka yiwa dakarun mu shin ko ka manta ne cewa fiye da shekaru ashirin hakan bai taɓa faruwa ba.
Koda jin wannan batu sai sarki zammar ya yi murmushi mai taushi ga 'yarshi Mashlira ya ce "nayi miki wannan alfarma ya muradin zuciyata ai girma da matsayin ki ya huce haka, gaba ɗaya jama'ar wannan birni da abin da ke cikinsu mallakin ki ne".
Ko da gama faɗin hakan sai ya yi wa badakaren inkiya a karo na biyu kawai sai badakaren ya mayar da takobinshi cikin kuben ta.


Please Login or Register in order to submit comment