Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sarki Lazwar a lokacin da su sarkin yaƙi Darusu suka ɗauke shi a cikin halin suma.
Al'amarin abokan tafiyar sarki Lazwar sarkin yaƙi da bawa Shamsal kuwa, koda ficewar su daga masaukin sai sarkin yaƙi ya dubi bawa Shamsal ya ce dashi "wai kuwa me ka fahimta game da hadima khadijat akankallon da naga tana yi maka?
Koda jin wannan tambaya sai Shamsal ya yi shiru kamar mai tunanin wani abu, daga can sai ya ɗago da kanshu ya dubi sarkin yaƙi ya ce "ya sarkin yaƙi ka yi sani cewa haƙiƙa ban fahimci wani abu ba game da kallon da khadijat ke yi min ba,
sai dai a lokacin da muka haɗa idanu na ji zuciyata ta buga da ƙarfi".
Da jin wannan batu sai sarkin yaƙi ya yi murmushi ya ce "ai kuwa dukkanin ku kun faɗa tarkon so ne ba ku sani ba, lallai nan da wani lokaci za ku cigaba da kasance a kogin SOYAYYA, amma wani hanzari ba gudu ba kai a yanayin da kake kallon khadijat kana ganin cewa halin talauci ne ya sanya ta yin aikatau a ƙarƙashin sarkin kasuwa Sha'aran?
Jiki na ba ni cewa tabbas akwai wani ɓoyayyen al'amari a tare da ita.
Ko da jin wannan batu daga bakin sarkin yaƙi sai bawa Shamsal ya yi shiru karo na biyu sannan ya dube shi ya ce "tabbas maganar ka akwai ƙamshin gaskiya a ciki, domin a lokacin da muka sauka a rumfa su muna cin abinci na ga kallon da khadijat ke yiwa yaro Imran ya zarta misali. Bisa nazari da nayi haƙiƙa kallo ne mai ɗauke da tsantsar tausayi irin na 'yan uwa na jini. Amma dai ko ma dai mene ne komai zai bayyana domin masu iya magana na cewa, komai nisan jifa ƙasa zata faɗo, kuma a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe.
Sarkin yaƙi ya ce "tabbas zancen ka dutse ya abokina";
Daga wannan furuci ne kowannen su ya yi shiru.
Wannan shi ne abin da ya faru da tsakanin sarkin yaƙi da bawa shamsal a masaukin su.

Al'amrin yarinya Shuraiba kuwa lokacin da gimbiya Lamrat ta ɗauke ta a cikin keken dokin ta suka durfafi hanyar da zata sada su da gidan sarauta, sai ya zamana cewa duk inda suka gifta a cikin birnin Istanbul sai dai ka ga jama'a na faɗuwa ƙasa suna gaisuwa tamkar za su yi mata sujjada.
Haka dai aka cigaba da wannan tafiya har aka iso ƙofar gidan sarauta aka kunna kai izuwa ciki.
Bisa wani ƙasaitacce ɓangare da yafi ko ina ƙawatuwa a gidan sarautar, keken dokin ya sauke su gimbiya Lamrat, kai tsaye ta kutsa kai izuwa ciki, hannun riƙe da na yarinya shuraiba dakaru na take mata baya, ɓangaren cike yake da kuyangi, barori, hadimai da bayi suna ta kai komo suna ta hidima.
Nan fa ya zamana cewa yarinya Shuraiba ta zamto cikakkiyar 'yar ƙauye, ta kama kalle-kalle da dube-dube tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni.



Wata kyakkyawar budurwa daga cikin kuyangi ta rugo izuwa wajen su ta zube kasa ta kwashi gaisuwa ga Gimbiya Sannan ya dago da kanta sama ta ɓuɗi baki cikin ladabi da girmama tace" ya shugabata shin me kike da bukata?

Gimbiya lamrat tace " yake lazura abinda nake bukata shi ne ki tafi da wannan yarinya a tsaftace mata jikin ta a can za mata tufafi masu tsada,

Sannan a haɗa mana abincin da abin sha tare,kuma a kawo ta izuwa turaka ta.

Ko da jin wannan batu daga bakin gimbiya lamrat sai kuyanga lazura ta risina tace " An gama ya shugabata.

Tana gama faɗin hakan sai ta mike tsaye ta kama hannun yarinya shuraiba ta shige da izuwa wani bangare daban.

Sannan gimbiya lamrat ta shige izuwa turakar ta dakaru masu tsaron lafiyar na biye da ita.

Wannan shi ne abin da ya faru da yarinya shuraiba da gimbiya lamrat matar sarki Ladiyas.



***



Al'amarin yaro Imran kuwa, lokacin da ya isa izuwa masaukin su sai ya shige kai tsaye izuwa dakin sa ya shiga kewaye ya watsa ruwa kuma ya ɗaura alwala.
Sannan ya shimfida darduma ya tayar da Sallar Magariba bayan ya idar ne yayi godiya ga Allah,
Bayan wasu yan dakiku sai yaji an kwankwasa kofar dakin
Koda ya tashi yaje ya buɗe sai yaga ashe Hadima khadijat dauke da abin kalaci da taceccen ruwan sha,

Bayan ta ajiye masa abincin sai ta samu waje ta zauna a kusa dashi tsakanin su taku ɗaya

Khadijah ta dubi yaro Imran tace" Na samu wani labari dake yawo a gari akan abin da yafaru tsakanin ka da matsafi shamrul

Tabbas idan hakan ya tabbata dola ne mu kasance cikin shirin ko ta kwana domin a kowa ne lokaci dakarun farmaki zasu dunga kawo mana ziyara Domin ganin bayan ka,

Koda jin wannan batu daga bakin khadijat sai yaro Imran ya jinjina al'amarin a cikin ransa

Sannan ya dubi khadijat yace " Tabbas maganar ki gaskiya ce ya yar uwanta

Tabbas Ubangiji yana tare damu, yanzu bari nayi kalaci sai ki dawo mu gabatar da sallar isha'i

Da jin hakan sai Hadima khadijat ta mike tsaye ta juya ta fice daga ɗakin tana mai waigen Imran.

Wannan shi ne abin da ya faru da Yaro Imran lokacin da ya isa masaukin su.



***

Lokacin da dare ya tsala sai sarkin yaƙi Darusu ya ɗauki sarki lazwar ya gurfanar dashi a gaban

Mai girma sarki ladiyas a lokacin da ya ke zaune a cikin wata ƙasaitacciyar turaka,

Kai tsaya wa musalta tsaruwa da kawatuwar turakar zai iya zamowa kauyanci sai dai abinda idanu suka gani kawai,

Domin komai kasaitar Basarake da attajiri idan ya tsinci kansa a cikin wannan turaka, dola ne bagidaje kuma cikekken ɗan kauye,

Bisa wata ƙasaitacciyar kejera wani mutum zaune a kai.

Mutumin yakasance mai kirar sadaukai ya tara kwanji, kyakyawa ne nagaban kwatance kuma ma, abocin kwarjini da Haiba

Sanye yake da tufafi riga da wando irin na Hamshakan sarakai,kallo ɗaya zaka yi masa ka fahimci cewa yakasance GWARZON DUNIYA mai karfi na Allah ya isa,

Ba wani ba ne wannan mutum ba face sarki Ladiyas ibn fairuz

A wannan lokaci sarki lazwar na zaune yana kallon wani bangare na lambun shaƙatawar sa ta tagar turakar sa.

Yana cin kayan marmari dake ajiye akan faranti na zinare bisa wani madaidaicin teburi na azurfa.

Koda jin bayyanar sarkin yaƙi Darusu sai sarki ladiyas yayi ajiye wata tuffa dake hannun sa ya juya yana mai fuskantar su Sarkin yaki

Ladiyas ya karewa sarki lazwar kallo a lokacin da suke durkushe kasa bisa gwiwoyinsu kuma sun sunkuyar da kansu shi da Sarkin yaki

Lokacin da sarki lazwar yaji sa durkushe aka agaban sarki ladiyas sai baƙin ciki da takaici suka mamaye zuciyarsa yaji kamar ya kwalla ihu, wai yau ace shi ne yake durkushe a kasa agaban wani sarki saboda kawai neman biyan bukata,

A matsayin sa na hamshaqin sarki, amma babu yadda ya iya.

Tsawon dakika goma sannan daga bisani sarki ladiyas ya budi baki cikin wata irin kakkausar murya mai tattare da jarumtaka ya budi baki yace" yakai dirkar birnina alamu sun nuna mini cewa lallai zai wannan jarumi zai iya kasance daya cikin masu tsaron lafiyata amma sai dai bazai yiwu na amince da hakan ba face ya shiga izuwa dakin duhu kuma ya samu nasarar cin jarabawar

Lallai ne gobe da safe ka gabatar mini dashi a fada,

Koda jin wannan umarni daga bakin sarki ladiyas sai sarkin yaƙi darusi ya rusina cikin ladabi yace" An gama ya shugabana,

Yana gama faɗin hakan ya tashi tsaye ya juya ya fice daga turakar

Sarki ladiyas yayi koyi dashi yana mai bin bayan sa da sauri suka fice daga turakar suka durfafi wani bangare na daban.

Wannan shi ne abin da ya faru da Sarki lazwar a lokacin da aka gabar dashi a gaban mai girma ladiyas a lokacin da ya cinye gasar gwarzo.



****

Al'amarin yarinya shuraiba kuwa, lokacin da kuyangi suka kammala yayi mata wanka da ado kuma suka ciyar da ita daddadan abinci,

Sai barci mai nauyi ya dauke ta.

Bata farka ba sai da dare ya tsala, a wannan lokaci gimbiya na zaune a kusa da ita bisa kan gadon da take kwance,

Sa'adda gimbiya taga shuraiba ta farka daga barci sai ta sanya hannayen ta biyu ta sheta tsaye taja hannun ta izuwa bisa wata ƙasaitacciyar kujera da a gaban ta aka ajiye wani teburin azurfa mai ɗauke da nau'ikan abinci Abin sha da tanɗe-tanɗe,

Cikin matukar farin ciki gimbiya ta shiga ɗibar abinci da abin sha tana bawa shuraiba a baki,

Cikin matukar farin ciki,

Man take shuraiba taji kamar mahaifiyar tace ke ciyar da ita abin,

Ita kuw a gimbiya tsananin farin cikin dake zuciyar ta bazai musaltu ba,

Bisa ganin cewa yau ita ce ke ciyar da yar ta da hannun ta wacce ta rasa ta shekaru masu yawa.

Bayan gimbiya ta kammala bawa shuraiba abinci kuma ita ma ta kintsa cikin ta,

Sai shuraiba ta shiga bawa gimbiya labarin rayuwar ta tun lokacin da Sarki Ladiyas ya raba ta da mahaifiyar ta ya mayar da ita baiwar da har sa'adda ita da mahaifin ta suka koma rayuwar daji,

Har kawo lokacin da ta haɗu dasu sarki lazwar tun daga farko har karshe ta zayyanewa gimbiya,

Sa'adda gimbiya taji wannan labari da ga bakin yarinya shuraiba bata san sa'adda ta rungume ta ba tana mai fashewa da matsanancin kuka

Su duka biyun suna masu rusa kukan tausayi sai daga bisa ne gimbiya ta janye jikin ta daga na yarinya shuraiba suna masu fuskantar juna.

Kawai sai gimbiya ta sanya hannunta tayaye mayafin dake kanta fuskar ta bayyana a fili ƙarara,

Sa'adda yarinya shuraiba tayi arba da fuskar gimbiya bata san sa'adda ta sake rungume ta ba a karo na biyu tana mai fashe da kukan murna,

Ba komai ne ya sanya ta hakan ba sai domin arba da tayi da fuskar mahaifiyar ta lamrat

tana mai cewa ashe zan sake ganin ki ya ummi na ashe daman kina raye?

Dakyar gimbiya lamrat ta lallashi yarinya shuraiba tayi shiru ta share mata hawaye,

Bayan ta samu nutsuwa ne sai ta dube ta cikin annashiwa da farin ciki tace"ya ƴata kuma farin zuciya ta Hakika ina raye ban mutuwa a kowa ce rana idan dare yayi sai nayi kukan bakin ciki tare da rokon abin bauta akan ya kare mini ke kuma ya kawo mini lokacin da zan ɗauki fansa akan BAKIN AZZALUMI da ya lalata rayuwar mu wato sarki ladiyas,

Sai gashi abin bauta ya dawo mini dake cikin koshin lafiya, ina so tsaka nina dake mubar sirrin dake tsakanin mu har izuwa lokacin da zamu dauki fansa kada ki kuskura wani ya gane cewa ke ƴata ce

Saboda hakan ne ma ya sanya na boye miki fuska ta a lokacin da muka hadu a kasawu,

Domin matsawar wani ya gane hakan har sarki ya sani shi kenan dukkan shirin ya watse,

Sa'adda gimbiya jalila tazo dai dai nan azancenta sai Yarinya shuraiba ta cika da matuƙar farin ciki maral musaltuwa,

Tana mai cewa tabbas na aminta da ke ummi na kuma zamu dauki fansa akan sarki ladiyas,

Wannan shi ne abin da ya wakana tsananin yarinya shuraiba da mahaifiyar ta gimbiya jalila.



****

Al'amarin yaro Imran kuwa tun sa,adda yayi bankwana da hadima Khadijat bayan ya kammala bata labarin abin da ya faru tsakanin sa da matsafi shamrul a cikin kasuwa sai ya shiga kimtsa cikin sa bayan ya kammala ne

Hadima Khadijat ta dawo suka gabatar da sallar Isha'i

Bayan kammala wa ne ya kwanta domin ya huce gajiyar dake tattare dashi

Wannan shi ne ya faru da yaro Imran



***

Kashe gari tunda duku dukun safiya fadar sarki ladiyas ta cika ta batse da jama'a maza da mata yara da manya,

Domin a yau ne aka samu labarin cewa sarki ladiyas zai yi umarni a sanya sarki lazwar a cikin dakin duhu domin ya samu nasarar tsallake matakin gasa na karshe wanda zai bashi damar kasance ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyar sarki.

Bayan jama'a sun hallara kuma Sarki ladiyas ya hakimce a bisa karagar sa cikin ado na kece raini sai aka hango Sarkin yaƙi darusi ya shigo izuwa fadar tare da waɗansu dakaru da sarki lazwar ɗaure a cikin sarƙa.

Sa'adda jama'a sukayi arba da sarki lazwar sai fadar ta kaure da shewa da ihu,

Sai da Sarkin yaƙi ya gabatar da sarki lazwar sannan fadar tayi shiru tamkar mutuwa ta kawo ziyara,

Sarkin yaƙi ya fuskanci mutane bayan yayi gyaran murya sai ya budi baki yace,

Yaku jama'ar wannan fada kuyi sani cewa ba komai ne ya sanya muka taraku anan ba sai domin a yau ne mai girma ladiyas ya bayar da umarnin asaka jarumi lazwar izuwa dakin duhu Domin yayi gwagwarmaya da miyagun halittun da suke ciki kuma idan ya samu nasarar tsallake matakin zai zamo daya cikin masu tsaron lafiyar mai martaba sarki.

Sa,adda Sarkin yaƙi darusi ya zo dai dai nan azancen sa sai fadar ta sake kaurewa da shewa a karo na biyu,

Sai daga bisani ne Sarkin yaƙi darusi ya umarci wadansu dakaru mutum hamsin suka wangame wata makekiyar kofar dake jikin bangon fadar take wani makeken daki ya bayyana mai dauke da waɗansu nau'ikan halittu dangin kuraye da zakuna da mucizai,

Cikin hanzari waɗansu dakarun na daban suka dauki sarki lazwar suka jefa shi izuwa cikin dakin sannan suka sanya wani katon kwaɗo suka kulle kofar ɗakin,

Sa'adda gimbiya mashlira dake sanye da kayan dakaru dake tsaye a bayan Sarkin yaƙi darusi cikin ɓadda kama taga an sanya masoyint Sarki lazwar a cikin dakin duhu sai takaici da bakin ciki suka mamaye zuciyarsa taji kamar ta kwalla kara,

Amma sai ta danne zuciyar ta saboda tasan cewa badan komai masoyin nata ya shiga wannan hali ba sai domin kawai ya sadu da baiwa sharifa da zata taimaka masa wajen mallako abubuwan da zasu warkar dashi daga sihirin da abokin gabar sa yayi masa, sai kawai ta shiga yi masa fatan samun nasara,

Amma har yanzu hankalin ta a tashe yake sosai,

Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin sarki lazwar da halittun kuraye biyu zakoki biyu sai waɗansu rin mucizai masu kawuna biyar

Duk da kasancewar sarki lazwar GWARZON MAYAKI kuma Namijin Duniya sai da hankalinsa ya dugunzuma domin iya tsawon rayuwarsa bai taba gani ko jin labarin halittu masu kwarjini daban tsoron su ba,

Tsawon dakika hamsin halittun na zagaye Sarkin lazwar sai daga bisani ne kawai suka yi gurnani suka yi ɗauki izuwa kansa suna kai masa cizo da faratansu da yakushi da hannayen su, mucizan na kai masa sara gami da furzar da dafi daga bakunan su cikin wani irin bakin zafin nama daya huce hankali.

Shi kuwa Sarki lazwar ya wanzu ya na zillewa tare da gocewa hare-haren halittun cikin zafin nama JURIYA DA BAJINTA,

Sai da Sa'a ɗaya da rabi ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi batare da ɗaya daga cikin su ya samu nasara ba,

A dai-dai wannan lokaci ne halittun suka fara galabaitar da Sarki lazwar yazamana cewa baya mayar da martani sai dai kokarin kare kansa,

Ana cikin wannan yakin wani daga cikin zakunan ya yakushi sarki lazwar a cinyar ta hagu take inda ya yakushe sa ya yayi masa mugun rauni, sarki lazwar ya kurma wawan ihu sakamakon tsananin zafi da zugin da yaji a dai dai lokacin da jini ya kwaranya daga cinyar sa.

Kafin ya sake yin wani yunkuri wani mucijin ya kaf tamasa wawan sara a gadon bayan sa,

Saboda tsananin azaba sai da sarki lazwar ya a kife a kasa yana nishin wahala.

Nan fa zakunan da kurayen su ka afka masa da cizo da ya kushi yazama mana cewa duk jikin sa na zubar da jini,

Nan fa masoyan Sarki lazwar suka cika da matuƙar farin ciki har waɗansu na zubar da hawayen takaici bisa ganin halin da jarumin su ke ciki,

Shi kuwa Sarki ladiyas dake hakimce bisa karagar Mulkin sa sai ya shiga ɓaɓɓaka dariyar mugunta har da kya kyatawa nanfa sauran yan majalisa da fadawa suka taya shi

Al'amarin da ya sanya zuciyar gimbiya mashlira ta karaya kenan har kwalla ta cika mata idanu bisa ganin halin da masoyin ta ke ciki amma saboda tsoron kada wani ya gane halin da take ciki asirinta ya tuno a gane cewa ba ita ce badakaren sai tayi sauri ta goge hawaye dake kan fuskar ta, dai dai lokacin ta hango bawa shamsal da Sarkin yaƙi a cikin jama'ar gari suka zubar da hawayen takaici bisa ganin halin da shugaban su ya tsinci kansa a ciki,

Wanda a koda yaushe zai iya rasa rayuwar sa,

Lokacin da sarki lazwar ya tsinci kansa a tsakanin RAYUWA DA HALAKA,

Kuma ya tabbatar dacewa hakika a koda yaushe zai iya rasa rayuwar sai kawai yafara amfani da zallar karfin sihirin tsafin sa sai yazamana cewa tamkar ta azzara miyagun halittun yake ci domin duk sun kusan yage tufafin dake jikinsa,

Ko ina jini na zuba jiri ya fara ɗaukar sa yana gani dishi dishi,

Kwatsam sai yaro Imran ya faɗo masa arai zuciyar sa na raya masa cewa kawai ka nemi taimakon Ubangijin yaro Imran tun da dukkanin wata dubara ta kwace maka ,

Kasan masu magana na cewa wanda ya faɗa Teku ko KAIFIN TAKOBI aka mika masa sai ya kama domin ya tsira

Tun da a halin yanzu ba wanda zai gane cewa ka nemi taimakon Ubangijin Imran,

Sa'adda sarki lazwar yazo dai dai nan a tunanin sa sai kawai ya kabbara Yana mai ambaton sunan Allah a cikin ransa batare da bayyana wani waje,

A dai-dai Wannan lokaci ne wani ɗaya daga cikin zakokin ya wangame bakin sa da nufin ya cinye yan yatsun sa na hannu,

Kwatsam bazato babu tsammani sai akaga Sarki lazwar ya kurma wawan ihu cikin wani zafin nama da karfi na ban al'ajabi ya kama wuyan zaki da hannayen sa biyu ya murɗe masa wuya ta karfin tsiya take wuyan zakin yayi kara ya karye jikake rukus! Ƙas ya sheka barzahu ko shurawa bai yi ba.

Sai kawai Sarki lazwar ya mike tsaye zumbir aka sake wani sabon kallon kallo tsakanin sa da sauran halittun.

Nan take fadar ta ruɗe da shewa masoyan Sarki lazwar suka cika da farin cikin bisa ganin gwaninsu ya mike tsaye.

Shi kuwa Sarki ladiyas sai fuskar ta murtuke domin a iya tsawon shekaru da aka shafe ana gwada jaruman ba,a taɓa samun wanda ya kashe dabba ɗaya daga cikin halittun ba.

Daga sai dukkan halittun suka afkawa Sarki lazwar a ka sake ruguntsume wa da azababban yaƙi mai matukar nuni da ban tsoro.

A wannan karon sai yazamana cewa duk wanda sarki lazwar ya gabza wa nashi a cikin halin sai kaga yayi sama tamkar an janye sa da ƙungiya sannan ya faɗo ƙasa tim.

Saboda na ci da zafin nama irin kuraye, zakoki da mucizai sai mike tsaye zumbur su sake afka masa da dukkanin karfin su,

Kafin cikar rabin Sa'a Sarki lazwar ya kashe gaba ɗaya halittun ya jefar da gawarwakin su a ƙasa,

Nanfa filin fadar ya kaure da shewa da jinjina jama'a suna ta mamakin wannan jarumtaka ta sarki lazwar

Domin a tarihin gasar shi ne mutum na farko da ya taba kashe miyagun dabbobin baki ɗaya.

Ita kanta gimbiya mashlira yar Sarkin muridai dake sanye da tufafin dakaru cikin ɓaddakama bata san sa'adda murmushin farin ciki ya suɓuce mata ba

Al'amarin da ya sanya zuciyar Sarki ladiyas ta cigaban da tafarfasa tamkar zata kone kenan

Koda ganin samun wannan nasara da sarki lazwar ya samu sai sarkin yaƙi Darusi ya umurci waɗannan dabaru mutum Hamsin suka je suka buɗe Kofar ɗakin duhu aka fito da sarki lazwar likitoci suka shiga basa taimakon gaggawa domin tsayar da jinin dake zuba a jikin sa tare sanya masa magani akan raunukan sa.

Ana cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai aka hango waɗansu dakaru mutum arba'in shirye cikin gagarumar shigar yaƙi sun tuso ƙeyar yaro Imran da Hadima Khadijat an ɗaure hannayen su da ƙafafuwan su da sasari na baƙin ƙarfe a gefe.

A gefe guda kuma matsafi shamrul ne tare da waɗansu daga cikin malaman addinin su sanye da tufafi irin na bauta.

Lokacin da ya zamana tazarar dake tsakanin su da karagar mulki bai huce taku goma ba sai matsafi shamrul da sauran bokaye suka zube kasa bisa gwiwoyin su suka kwashi gaisuwa ga sarki ladiyas.

Suna masu sunkuyar da kawunan su kasa,

Sai da suka jima a haka sannan daga bisani matsafi shamrul ya dago da kansa sama ya buɗi baki cikin ladabi da girmamawa cikin wata irin kakkausar murya mai kama da kukan jaki yace

" Ya shugabana hakika abinda bauta ya bada umurnin a yanka waɗannan mutane biyu mace da namiji da suka shigo mana da wani sabon addini mai suna musulunci wanda suka nema su ja hankalin mutane wannan kasa a kai

Domin su bijirewa bauta masa wanda a dalilin hakan zai janyo mana musiba da annoba da zata haifar da suɓucewar mulkin ka,

Sa'adda da Sarki ladiyas yaji wannan batu daga bakin matsafi shamrul sai zuciyar ta kama tafarfasa tamkar zata kone yaji ya tsani Hadima Khadijat da yaro Imran,l.

Kawai sai ya dubi Hadima Khadijat da fuskar ta ke rufe da rawani yace" yake baiwa sharifat hakika kin yaudare ni kin ci amanata da kika zo da wani sabon addini a wannan birni nawa

Kuma binciken da na gudanar da na gudanar bisa halarar tsafi na ya tabbatar mini da cewa kin daɗe kina bauta wani Ubangijin aboye tun sa'adda da kike zaune a cikin gidan sarauta kafin na umarce ki

Ki koma yiwa Sarkin kasuwa Hidima domin ki boyayyen sirrin dake cikin dukiyar da domin na samu nasarar ganin bayansa

Hakika a yau zan yanke miki hukunci dai dai da laifin da kika aikata a gareni,

Sa'adda da mai girma ladiyas yazo nan a zancen sa sai sarki lazwar dake gefe guda likitoci na duba lafiyar sa ya cika da tsananin mamaki bisa jin sarki ladiyas ya faɗa na kiran Hadima Khadijat da suna Baiwa sharifat

Shin dama Hadima Khadijat ita ce Baiwa sharifat da ya fito farautar nema?

Tabbas tsugunne bata kare ba wai an saci ɗan ɓarawo,

Hakika dola ne yayi sabon gumurzu domin ceton rayuwar Hadima Khadijat,

Sarkin yaƙi, Bawa shamsal da aljani Za'aratul-layal dake cikin siffar bil'adama tare da gimbiya mashlira dake sanye da tufafin dakaru cikin ɓaddakama matukar mamaki ne bisa jin ashe Hadima Khadijat ita ce Baiwa sharifat,

Wannan fa shi ne masu iya magana ke cewa wai " Rashin sani kaza ta kwana akan dami"

Ashe sarki lazwar na tare da wanda yake nema bai sani ba har ya shigar da kansa cikin azabar sarki ladiyas,

A ɓangaren jama'a kuwa sa'adda da suka samu labarin cewa Yaron nan da yiwa matsafi shamrul tambaya akan addinin su za,a yanke masa hukuncin kisa,

Sai jama'a suka yi cincirindo a fadar suka dunga tuttuɗowa zuwa fadar domin su gane wa idanun su,

Domin a yau ne zasu tantance shin tsakanin Ubangijin wannan yaro Imran da matsafi shamrul wane ne na gaskiya?

Sarki ladiyas na kammala wannan batu sai Sarki ladiyas ya koma kan karagar mulkin sa ya hakimce,

Kawai sai wani garjejen kato ya ɗauki yaro Imran ya dora a jikin wani zagayayyan tudu a fadar sannan ya koma gefe guda yaja ya tsaya

Sarki ladiyas ya yi wa sarkin yaƙi Darusi inkiya ta wutsiyar idanu dake nuna basa umarni

Cikin dakewar zuciya gami da zafin nama Sarkin yaƙi Darusi ya zare wata sharbebiyar adda a gadon bayan sa ya durfafi inda yaro Imran yake domin ya datse wuyan sa

Yayin da sarki ladiyas,matsafi shamrul da fadawa suka bushe da dariyar mugunta har da kyakyatawa.

Jama'a kuwa sai da yawan su sai suka fara zubar da hawayen takaici da bakin ciki

Yayin da Sarkin yaƙi ya isa sai ya daga addar tasa ya ɗora akan waya yaro Imran

Kwatsam bazato babu tsammani sai akaga wata kyakkyawar halitta ta keto daga saman fadar ɗauke da waɗansu mutane guda biyu.

Ba wani bane wannan halitta da mutanen biyun ba face aljani Hadimul-khairi ɗauke da gimbiya lamrat matar sarki ladiyas da yarta yarinya shuraiba,

Kafin KAIFIN TAKOBIn Sarkin yaƙi darusi ta yanka wuyan aljani Hadimul-khairi ya ɗauko wata farar kwalba mai ɗauke da wani koren ruwa ya watsa inda yaro Imran da Hadima Khadijat suke,

Take sarƙoƙin dake ɗaure a jikin su da addar dake wuyan yaro Imran suna narke suka zagwanye suka zama ruwa,

Cikin matukar firgici Sarkin yaƙi, sarki ladiyas,da sauran jama'ar suka daga

Please Login or Register in order to submit comment