Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magana ta yarda da Musan kawai a sha biki ta huta da maganar mutane.
Wani lokaci idan Naseer yai magana sai ta ga kamar Malam ne ke maganar.

"Auren zumunci ai akwai daɗi, Nasiru. Ga shi kai ma ka yi har da Albarkar 'ya'ya biyu"

Miƙewa ya yi ya ɗan karkata hularsa ya ce " Aminatu ba za ta auri wanda bai yi karatu ba"
Daga haka Iya ta haɗiye sauran bayanin.
Dama ta san ta inda Naseer zai ɓullo mata kenan. Amma yadda Musa makaniken mota ɗan yayarta da suke 'ya'yan Baffanu ya dage da zuwa yana lallaɓata yasa ta ke sha'awar haɗa auren zumunci.

Ta yi shiru da maganar ta bi bayansa tana masa addu'ar Allah ya kare shi.
Naseer shine babban gida dan haka maganarsa dutse ce a gidan.
Ga shi dai shi ɗaya tilo ta haifa amma kuma ya zamto mata tamkar maza goma.
Ko cikin dangi ana alfahari da sojanta.
Shi ne ya ɗaga darajan gidan nasu. Daga Azare, Zaki har Chinade babu tamkar ɗanta Nasiru.


***

Tunda Faruƙ ya bayyana masa cewa daga Lagos zai taho Abuja Naseer ya canja aƙalar tafiyarsa. maimakon Kaduna Kano ya wuce zai duba yayarsa Indo da ke can sai kuma ya hau jirgi ya wuce Abuja daga nan.

A gidan Indo ya samu tarba mai kyau.
Mijin Indo yana da rufin asiri dai dai gwargwado sannan mutum ne da ya ke son Iyalinsa. Duk cikin 'yan'uwansa mata banda Hadiza babu wacce ta yi sa'ar miji kaman Indo. Halilu yana son Indo ba kaɗan ba. Ga shi za su kai shekara goma shabiyar da aure amma har yanzu ita ɗaya ce a wajensa. Kuma ko a taɗi baya ji ana maganar wai Indo da mijinta sun samu matsala.
Saɓanin sauran da idan matsala ta tashi shi ake kira.
Wannan yasa ya ke ganin ashe abun ba daga karatu bane, daga zuciya da ɗabi'ar mutum ne.
Halilu dai bai yi boko ba amma yana son matarsa sosai kuma yana riƙe da ita da amana. Har yau Mijin Indo bai taɓa kiransa dan neman taimako ba.
Saɓanin sauran da suke bibiyarsa akan ya taimaka musu. Mijin Hauwa'u kam ma ba zai iya misalta matacciyar zuciyarsa ba. Zai samu lokaci dai ya je Bauchin nan ya masa magana. Kullum cikin kukan babu ya ke da 'yan ƙarairayi da zai sa a taimaka masa.

Yana cin abinci a falon Indo Mukhtar babban ɗan Indo ya shigo gidan sanye da uniform ɗin makaranta. Yana ganinsa sai ya sa dariya ya ƙariso gabansa ya ƙame jiki ya buga ƙafarsa ya sara masa yace" Shun Sir"

"To ƙaramin soja, yi hankali kar ka buge masa kofin ruwa" Indo ta faɗa

"Mukhtar ne ya girma haka"

Yaron ya fara dariya yana sosa gashin bakinsa da ya fara tohowa.

Indo tace " ka san yaushe rabonka da shi kuwa. Abba ai ya zama saurayi"

Sai da yaron ya shige ciki ta ke cewa ai shima Mukhtar ɗin wai soja ya ke son zama. Naseer ya ce hakan na da kyau.

Lura ta yi da yadda ya ke cin abincin kamar hankalinsa na wani waje ta ce "Baban Al'amin na ga alama zaman kaɗaici ya fara taɓa ka"

"Uhm"

Ta yi murmushi " au baka ma ji ni ba. Na ce gaskiya ya kamata ka yi aure ko mu haɗu mu maka auren dole"

"Za ku zauna da ita kenan"

"To ai ba mu ga alamar kana da niyya ba"

"Kar ku damu zan yi aure"

"Allah ya sa. Tun bara kake cewa za ka yi"

Ko da ya gama cin abincin bai wani jima ba Sallah kawai ya yi ya musu sallama ya wuce airport dan jirginsa ƙarfe biyar da rabi na yamma ne...


***

Waya ta ke tana ta faɗa lokacin da ta ke fitowa daga cikin gidanta.
"Shi Sani Kings ɗin ne ya sakata a film ɗin? Me yasa baka faɗa min tun da wuri ba..... kai matsa min a waje"
Ta kashe wayar tana jan tsaki.
Munira MoBaby kenan da take waya da manajan ta.
Tauraronta yayi tashe daga shekarar 2002 da ta shiga film zuwa 2006 amma shekarar 2007 ya zo mata da canje-canje dan kuwa sabbin jarumai kyawawa wanda basu kaita shekaru bane suka shigo masana'antar. Wannan yasa wasu daraktocin ke rububin saka su a film.
Babu wacce ta tsaya mata a wuya irin wata sabuwar jaruma da kusan film uku kenan da take biɗa amma an bi gefe an je an sakata.
Jarumar da ke ƙoƙarin karawa da ita ita ce Zarah Beauty. Shekarunta shatakwas kuma tashin Egypt ce. Mamanta Balarabiyar Egypt, Babanta ɗan Nigeria wannan yasa ta ke da ruwa biyu.
Ita kanta MoBaby sai dai baƙin ciki amma ta san Zarah kyakykyawa ce.

Ta san yadda industry'n nasu ya ke. Da zaran ka fara tara shekaru kuma aka samu sabbin kyawawan fiska za a fara ja baya da kai.
Ga shi farkon shekaran nan da ta buɗe kamfanin film ɗinta na MoBaby Movies Production 'yan hassada suka fara wareta gefe. Film ɗinta da ta fitar a ƙarƙashin kamfanin mai suna *ni naka ne* ya samu lambar yabo saboda waƙoƙin da suke cikin film ɗin sun haɗu ga kuma sabon jarumin da ta saka shima ya haska film ɗin.

"Hajiya mu tafi ne?" Direbanta ya tambaya.

"Asabe ta saka min akwati a mota?"

"Ta saka Hajiya"

"To mu wuce"

Ya buɗe mata ƙofar baya ta shiga ta hakimce tana danne dannen waya.





***

Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900


Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41
[27/11, 2:52 pm] Azizat Hamza Writer: *GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)


Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat



Page 015



Hannunsa ɗauke da jarida yana karatu abokiyar zaman nasa ta zauna a gefensa. Saboda shi ke zaune jikin window bai damu ya ɗaga ido ya kalli wacce ta zauna a gefensa ba. Yana sanye ne da riga shirt baƙa da kuma baƙin wando, idanunsa ɓoye cikin baƙin glass.
Fitinannen ƙanshin da ke fitowa daga gefensa ya hana hancinsa sukuni.
Ya ɗan sauke jaridar kaɗan ya kalli gefensa ta wutsiyar ido.

Kaman bata san da mutum a gefenta ba sai tauna chewing gum take tana latsa wayar iphone ɗinta.
Bai san lokacin da ya juyar da gabaɗaya fiskarsa yana kallonta ba. Sai a lokacin ta juyo suka haɗa ido. Wani murmushi ta masa tareda kashe masa idanu. Wannan ya sake rikita nitsuwarsa. Gyaɗa mata kai ya yi ya ɗaga jaridar hannunsa ya cigaba da karatu duk da kuwa har lokacin hankalinsa na kan budurwar da ke gefensa.

Mamaki ne ƙarara ya bayyana a fiskar MoBaby ganin mutumin da ke gefenta bai nuna alamar ya santa ba. Ta saba idan ta shiga waje ba sai ta bayyana kanta ba ake ganeta saboda a cikin shekaru biyar ta zamo top Kannywood actress. Idan za ka lissafo jarumai uku mata masu tashe a Kannywood industry ba ka saka sunanta a ciki ba to lissafin bai zama dai dai ba.

Har Nollywood film ta yi guda uku duk da kuwa a can Nollywood ɗin ba wai an bata role mai ƙarfi bane.
Har jirgi ya tashi mutumin da ke gefenta bai ce mata ƙala ba. Bai ma kalli inda ta ke ba.
Wannan abun mamaki ne babba a wajen MoBaby. Ita jaruma, star, ace ta zauna kusa da namiji kuma ko sannu bai ce ba balle yayi ƙoƙarin karɓar numbarta.
Kasa nitsuwa ta yi. Dan babu yadda za a yi ace kyaunta bai ja hankalin wannan mutumin ba. Babu namijin da zai ganta ba tareda zuciyarsa ta motsa ba.

"Jaridar Daily trust ne?" Ta tambaya tana riƙe jaridar.

Bai yi magana ba sai kawai gira da ya ɗaga mata.
Kutumai! Waye wannan?. Kai ƙaryarsa ya ce bata masa ba. Ko dai baya kallon fina-finai ne?
Amma ai ko a social media ta yi ƙaurin suna babu yadda za a yi ace ba ganeta ba.

"I'm Munira, popularly known as MoBaby" ta faɗa tana wani fari ido. Wannan fari da idon dai shine sirrinta na jan hankalin mazaje.

Sai da ya ɗan yi shiru na 'yan sakanni kafin ya iya buɗe bakinsa ya ce "Captain Zaki"

"Ashe kai soja ne" ta faɗa tana murmushi. Ta taɓa soyayya da wani soja kuma ta san sun iya kula matansu.

"Da alama Captain ba ma'abocin kallon fina finai bane?"

"No" ya faɗa a taƙaice.

"Shi yasa baka gane ni ba"

Tana jira ya tambayeta ko ita ɗin jaruma ce amma bai ce komai ba.
Kai Captain Zaki akwai miskilanci.

"I'm an actress"

"Nice"

Har jirginsu ya sauka a Abuja Captain Zaki bai tambayeta numbarta ba. Da kuwa ya tambaya ɗin za ta bashi dan ya burgeta.
Ba dan kada ta zubar da ajinta ba da ta tambaye shi numbarsa. Amma ko a hakan dai sai ta sa an binciko mata shi.


*

"Mutumina yau fa sai ka zaɓa ko ka ƙi ko ka so"
Faruƙ Lawanti kenan ke faɗawa Naseer dai dai lokacin da suka fito daga mota za su shiga hall ɗin da ake dinner abokinsu.
Babu ƙarya ga kyawawan 'yanmata nan masu aji a cikin hall ɗin amma babu wacce ta ɗau hankalinsa.
Suna cikin waɗanda aka saka a high table saboda sune manyan abokan Ango.

Tunda Naseer ya kafa kansa a waya babu abinda ya ke sai bincikar shafin Munira MoBaby a facebook.
So ya ke ya gama aminta a ransa cewa zai nemeta kafin ya mata magana.
Ya jima bai ji mace ta shiga ransa farat ɗaya ba irin yadda MoBaby ta shiga ransa. Babu ƙarya kyawunta na ɗaya daga cikin dalilan da suka kwaɗaita masa rayuwa da ita.
To wani soja ne baya son mace mai kyau?.
Shi Naseer Zaki baya neman abu ya rasa. Wannan ya sa bai yi gaggawar yi mata magana lokacin da suka haɗu a jirgi ba.

" ka ga wannan actress ɗin yadda take rawa, me ma sunanta?" Faruƙ Lawanti ya taɓa shi.
Ɗagowar da zai yi ya dubi inda Faruƙ ke nuna masa ya ci karo da yarinyar da tun daren jiya take ransa.
Munira ce.
Wani abokinsu da suke table ɗaya ya ce " na ji ance MoBaby 'yar'uwar Amaryar ce"

"Kai yarinyar nan akwai shape" suka haɗu suka saka dariya.
Kaman sukar mashi haka wani tsinin kishi ya soki zuciyar Naseer.
Ya kalli inda ta ke a lokacin ya furtawa ransa sai ya auri Munira. Munira tasa ce.

Kiran wata ƙanwar Ango ya yi ya miƙa mata ƙaramar takarda ya ce ta bawa Munira.
Yana gani yarinyar ta je table ɗin da Munira da ƙawayenta suke zaune dan an gama rawan abinci ake ci ta kai mata takardar.

Munira ta karɓi takardar ta buɗe ta karanta kamar haka.

* ki sani baki dace da kowa ba sai Captain Zaki. Dan haka ki adana mini kanki* a ƙasa sai ya rubuta numbarsa.

Tana karanta takardar wani murmushi ya suɓuto mata. Ta gane sunan. Wannan dai sojan da yai ta ja mata aji a cikin jirgi. Tarkonta ya kama shi kenan. Dama waye ba zai faɗa tarkon MoBaby ba.

Ta ɗaga ido tana neman inda ya ke amma bata gani ba. Yarinyar da ta kawo mata takardar kuwa ta bar wajen.
Ta yi murmushi. Tana son namiji mai isa da izza.
"Wato da shi na dace" ta faɗa ta yi 'yar dariya.


***

Da gaske Captain Naseer Zaki ke neman Munira MoBaby. Sai dai matsalar tasu guda ɗaya ce. MoBaby ta ce ba za ta ajiye aikin film ba. Shi kuma ya ce sharaɗinsa ɗaya sai dai ta bar film.
Wannan yasa soyayyarsu ta kwaɓe tun ba a je ko'ina ba.
Tabbas Naseer Zaki ya shiga ranta amma kuma idan ta ajiye film a lokacin da tauraronta ke ƙoƙarin disashewa saboda Zarah Beauty ai anyi ba a yi ba kenan.

Bayan rabuwarsu da Naseer wani Alhaji ta haɗu da shi wanda ya ke zuba mata maƙudan kuɗaɗe. Wannan yasa lokacin da ta tashi fitar da wani sabon film ɗinta mai suna *CAPTAIN SADEEQ* ta kashe kuɗi sosai akan film ɗin, har ƙasar waje sai da aka je aka yi shooting wasu scenes. Ta sako wasu jaruman Nollywood a ciki abin sai ya zamo wani sabon salo a duniyar Kannywood dan kuwa har asalin barikin sojoji sai da aka nuna a film ɗin.
Film ɗin CAPTAIN SADEEQ ya ƙarbu sosai kuma ya sake fitar da sunan Munira MoBaby a duniya.
Har ƙarshen shekarar 2007 babu film ɗin Hausa da yake tashe irin film ɗin Captain Sadeeq. Ta samu awards da yawa.

Ranan da aka sake film ɗin sai da ta kira Captain Zaki ta faɗa masa. Bai ce komai ba sai Allah ya bada sa'a. Wannan ya ƙona mata rai.
Bata taɓa saurayin da ya ke da jan aji irin Naseer Zaki ba. Yadda ya ke nuna yana sonta a lokaci guda kuma ya ke nuna bai wani damu da ita ba shi ya ke birkita mata tunani.
Shi ba kamar sauran mazan bane da suke rawar jiki a kanta.
Kuma duk ƙoƙarinta na son yakice shi a zuciyarta ta kasa.
Naseer Zaki akwai shiga rai.

Tunda fina-finanta kamfaninta suka fara kawo kuɗi ta yi ƙoƙarin neman yadda za a yi ta disashe tauraron Zarah Beauty gabaɗaya.
Akwai jaruma Salma da ta ke aiki a ƙarƙashin kamfaninta amma kuma sunanta bai yi tashe ba kamar yadda sunan Zarah Beauty yayi tashe.

Hayar mutane ta yi ta sa aka fara binciko mata sirrikan Zarah Beauty. Ta sani yadda yarinyar ta yi tashin ƙasar waje ba za ta rasa wani sirrin da za a iya bankaɗowa a haskawa mutane su fara jin haushinta ba.

Cikin sati biyu ta samu labarin ai Zarah Beauty na shaye-shaye. Ai dalilin dawowarta Nigeria ma saboda anyi anyi ta dena ta ƙi ne mahaifinta ya dawo da ita Nigeria ko zata nitsu a nan kuma ta haɗu da wani director da ya ga kyaunta ya mata tayin shiga film.

Lokacin da aka yaɗa hotunan Zarah Beauty a shafukan facebook tana club tana shan ƙwaya da wasu abokan ƙwayanta sai mutane suka yiwa Zarah Beauty caaa.

Aka shiga zaginta ana aibatata.
Kafin kace me tuni abokanan sana'arta suka shiga kusheta suna Allah wadarai da abin ta ke.
Zarah Beauty ta yi ƙoƙarin kare kanta da faɗin tsohon hoto ne wannan, yanzu ta dena shaye-shaye, amma babu wanda ya saurareta.
Fina-finan da aka ce za ta yi duk aka cireta a cikinsu. Aka shiga juya mata baya.
Wannan yasa dole ta gudu ta bar Nigeria ta koma Egypt.
MoBaby da ta ji labarin Zarah Beauty ta bar Nigeria sai ta yi murmushin nasara..




***


Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900


Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment