Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata ba. Ga shi dai ta rasa mahaifiyarta amma babu wanda ya ke kula da ita. Halima ce mata ta biyu a gidan, saboda tsananin haƙurinta ya sa tsangwamar kishiyoyi bai hanata zaman aure ba. Ko shi Mijinsu Umaru yana jinjina mutuwarta dan ta fi sauran matan haƙuri da yi masa biyayya.

Iya Abu ta zanta da Umaru akan tana so ta riƙe Fatima a wajenta. Umaru ya ce shi bai yarda a je a saka 'yarsa a boko ba idan ba rasuwar da aka yi bama yana so kafin kaka'a ya aurar da ita. Daga jin haka Iya tace idan ya amince tana so ta haɗa zumunci ɗanta Nasiru zai auri Fatima. Da wannan batu Umaru ya amince ta tafi da Fatima.

Da zata dawo gida ta taho da Fatima. Malam yayi na'am da zaman Fatima tareda su amma maganar aure tsakanin Nasiru da Fatiman sai ya nuna kaman Iya ta yi gaggawa kar a zo Naseer ya dawo ya ce bai yarda ba.
Iya ta ce ai kuwa bai isa ba.


Ranan da aka kawo musu wasiƙar da Naseer ya turo tareda kuɗi sun yi farin ciki sosai. Hadiza ce ta karanta musu wasiƙar Iya ta riƙe wasiƙar tana shafawa tana jin daɗi a ranta wai wannan daga hannun Nasirunta ya fito.
Kuɗin da ya turo ya zo musu a lokacin da abubuwa suka ɗan ja baya.

"Dama ana biyansu kuɗi ne? Hadiza ba a Makaranta ya ke ba. Ko dai yaƙi aka tura su?" hankalinta ya ɗan tashi kada fa yaƙi aka tura su ake biyansu kuɗin aikin da suka je yi.

"Kai Iya, ya ce fa ana biyansu alawus na ɗalibai duk wata"

"Ayyo"...


***


Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900


Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41
[27/11, 2:51 pm] Azizat Hamza Writer: *GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)


Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat



Page 006


***

Lokacin da Naseer ya taho hutu gida bayan watanni kar ka ga murna a wajen iyaye da ƙannensa. Haka aka dinga zuwa gaishe shi har yayyensa da suka yi aure sun zo gida. Indo ce dai da take Kano yanzu bata samu zuwa ba, wata ɗaya kafin zuwansa gida mijinta ya koma Kano dan ya samu aikin kamfani a can.

Naseer ya rame ya yi baƙi amma kuma jikinsa ya mummurɗe saboda training da suke yawan yi.

Sai da ya ɗan kwana biyu tukunna Iya ta same shi da maganar Fatima da kuma alƙawarin da ta yiwa mahaifinta. Naseer ya ce bai yarda ba shi ba zai yi aure ba sai ya gama makaranta. Ita kuma Fatima makaranta ya kamata a sata ba aure ba. Iya ta bar zancen a haka amma idan ya gama makarantar ba shi da mata sai Fatima.

Kafin ya koma makaranta sai da ya saka Fatima a makarantar je ka- ka dawo. JSS one aka saka ta dan tunda ta gama Primary bata cigaba ba.

Zuwa lokaci kaɗan ta sake jiki tana karatu abinta dama Babanta ne ya hanata cigaba da karatu amma Mamanta na son ta yi karatu.

Wani hutu da Naseer ya sake zuwa lokacin yana shekaransa na biyu a NDA ya tarar ana rikici da Hadiza. Ta gama Sakandare ta ce karatu zata cigaba Iya kuma ta ce bata yarda ba. Shi Malam dai ya ce ba zai yiwa 'yarsa auren dole ba duk da manemin nata kaman ɗa yake a wajensa.

"Yaya ni fa karatu zan yi. Baba da ya ke cewa idan na yi aure sai na cigaba shi fa Salisun cewa ya yi ba zai barni na yi karatu ba. A barni na yi karatuna a gida"

"Ka gaya mata karatu dai ba a gidan nan ba. Kina mace wanda kika yi bai ishe ki ba. Uban me za ki yi da bokon?"

Iya ta faɗa tana ɓantarar goro. Ita da Hadiza sun zamo kamar mage da ɓera a gidan kowa ba ya sarara wa kowa.

Naseer ya tsaya ya rasa ma ta ina zai fara yiwa Iya bayani. A wannan zamani karatu shine gatan mace.
Ya san me zai yi. Idan ya samu Malam ya masa bayani har ya fahimci mahimmanci cigaba da karatun 'ya mace shi zai iya canja ra'ayin Iya.

Malam dama akwai sauƙin kai. Kuma shi dake yana fita ya san yadda duniyar ke caccanjawa, yanzu yara mata har karatun gaba da Sakandare suke. Sai dai da ya ke anfi danganta hakan da 'ya'yan masu wadata shi yasa yake ganin kamar gara Hadiza ta yi auren idan ya so idan da rabon yin karatun sai ta yi a ɗakinta.

Kafin Naseer ya koma makaranta sai da ya tabbatar ya shawo kan iyayensa.
Iya dai taron dangi aka mata, uba da ɗa sun tsaya mata a wuya, ga itama Hadizar shegen naci kamar yayanta Naseer.
A layinsu kaf sa'annin Hadizan daga wanda suka yi aure sai wanda aka saka musu rana amma wai Nasiru ya dage da wannan bokon. Nasiru namiji ne idan ya yi boko mai zurfi babu matsala amma ita ɗiya mace ai rufin asirinta shine ta kasance a ɗakin mijinta.
Ga shi ana cewa matan da suka yi karatu mai zurfi basa yiwa miji biyayya.

Shekara biyu Naseer ya roƙawa Hadiza ko ta gama karatu ko bata gama ba bayan shekara biyu za ta yi aure.
Kafin ya koma Kaduna kuwa sai da ya tabbatar ya sama mata gurbin karatu a College of Education, Azare inda za ta karanci English.
Farin ciki a gun Hadiza ba zai misaltu ba. Tun daga lokacin ta sake jin ƙaunar ɗan'uwanta tana kuma ganin girmansa.

Iya dai har Hadiza ta tare a Hostel bata saki jiki da ita ba. Amma fa a hakan da za ta tafi sai da ta ƙulla mata kayan yaji da ƙanzo da bushashshen zogale da garin kunu.

Hadiza da ta tare a hostel ta buɗe bagco bag da Iya ta bata sai ta sa dariya. Iya dai akwai fushi, amma hakan baya hanata nuna soyayyarta ga 'ya'yanta.
Insha Allahu kuwa ba zata zubarwa iyayenta da mutunci ba. Abin da suke gudun ba zai taɓa faruwa ba. Karatu ta zo yi, karatu za ta yi tsakani da Allah. Ba za ta taɓa watsar da karatun da aka musu da tarbiyyar gidansu ba...


***

*1998, Azare*



"Malam ba za ka sha kunun ba?"

Malam ya girgiza kai yana sauke numfashi a hankali. Daga zazzaɓi da ya ɗan ji sauƙi ya fita kasuwa sai ya yanki jiki ya faɗi. Kwana biyar kenan baya fita, sun je Asibiti an kwantar da shi kwana biyu suka sallamo shi.
An ce wai jininsa ne ya hau.

"Zainabu"

"Na'am Malam"

Hannunta ɗaya ya kamo yace " ba abinda zan ce miki sai dai Allah ya haɗa mu a Aljannah"

"Malam..."

"Nagode Zainabu. Nagode da kulawarki gareni"

"Malam tsakaninmu ai babu godiya"

Ya ɗan yi murmushi.

"Idan Allah yayi ba zan ga Nasiru ba ki ce masa na yafe masa duniya da lahira sannan ina masa wasiyya da ya kula da mahaifiyarsa da ƙannensa"

"Malam ka dena irin wannan maganar, babu abinda zai same ka. Nasiru zai zo ya sameka da lafiyarka"...


Duk da an aikawa Naseer wasiƙa ya zo gida mahaifinsa ba lafiya bai samu zuwan ba saboda an kusa hutu. Wannan ya fi komai baƙantawa Iya rai akan irin makarantar da yake.
Naseer bai zo gida ba sai bayan kwana goma shashida da rasuwan Malam.

Tun daga hanya da aka fara masa ya haƙuri jikinsa yai sanyi. Ya shigo gida gwiwa a sace. Iya na nan kamar kullum tana zaune a ƙofar ɗakinta da rediyonta a hannu tana sauraron labaran yammaci. Tana ganinsa ta tashi ta shige ɗaki.

Naseer ya shigo ɗakin ya tsugunna gabanta.

"Iya, Baba..." muryarsa ta yi nauyi. Yana so yayi kukan amma babu hawayen kuma babu halin kukan. An riga an musu horon da hawayensu ba ya kusa.

"ɗan gidan Jiji bai aika maka da wasiƙa ba?"

"Iya...na samu wasiƙar kwana goma da suka wuce, na nemi damar tahowa gida ba a barni ba"

Ta tura fiskarta gefe ta ce " ka dai san yanzu kai ne Babban gidan"

"Allah ya jiƙan Baba ya masa rahama" ya faɗa da raunatacciyar murya

Iya ta amsa da Amin.

Sai da ya shiga ɗaki ya fara naushin gini yana ƙoƙarin rage raɗaɗin da zuciyarsa ke masa. Yau dai ɗaya ya ji a ransa ina ma shi ba soja bane ya yi kuka son ransa. Ga shi hutun ƙarshe da zai koma makaranta bai samu yayi sallama da Malam ba saboda ya tafi gaisuwar ta'aziya a can wani ƙauye Dunkurmi ta wajajen Misau.

Kafin ya koma makaranta Iya ta sake kawo masa maganar auren Fatima wacce a yanzu take cika shekara goma shabakwai, kuma ta kammala aji uku na sakandare.

Ga kuma maganar Hadiza itama. Duk dama dai yanzu wani Likita ke nemanta maganarta da ɗan'uwanta ya banje. Tun kafin Malam ya rasu Dr Anas ya zo neman izinin hira da Hadiza wacce suka haɗu lokacin da ya raka ƙanwarsa makarantarsu Hadizan. Da ke dai Hadiza ta nuna tana ra'ayinsa sai Malam ya ce a bari idan Naseer ya dawo sai ya turo.

Shima Naseer ɗin ya ji daɗin zaɓin Hadiza. Duk da dai Dr Anas ɗin yana da mata da yara biyu amma kasancewar ya yarda zai bari ta kammala karatunta sai hakan yai wa Naseer daɗi, ko ba komai dai ta samu mijin da ya ke da burin inganta rayuwarta.

Kafin ya tafin kuwa aka zo neman aurenta. Baffa ƙanin Malam ya bada ita aka saka lokacin biki farkon shekarar 1999.

Auren Naseer da Fatima ma dai babu fashi dan Iya ta nuna iya abinda zai mata kenan ya wanke fushin da take masa na ƙin zuwansa gida lokacin jinyar Malam. Tuni su Baffa suka je can Chinade suka nemawa Naseer auren Fatima a wajen mahaifinta. Lokacin da aka je tambayar Naseer ya riga ya koma makaranta amma da yardarsa aka je tambayar. Shi ma ɗin an saka bikinsa dai dai dana Hadiza...


***

Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900


Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41
[27/11, 2:51 pm] Azizat Hamza Writer: *GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)


Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat



Page 007



*1999*

* Gulak, Madagali, Adamawa State*



Tun da safe John-Yahaya ke sintiri a tsakar gida saboda matarsa da ke labour. An kira Matron Mary ta zo ta duba ta ce lokacin haihuwa bai yi ba.
Kuma tun da Asubahi ta fara labour. Ba zai iya tuna haihuwar Sɗang ba saboda shekaru goma kenan da haihuwar sai dai kamar Tabitha ba ta juma irin haka ba.
Lokacin haihuwar Paul da dare ne kusan ƙarfe bakwai aka kira Matron ta zo ta karɓi haihuwar. Kafin ƙarfe goma na dare har ta tafi.
Haihuwarta na biyu kuwa da safe ya tafi gona da ya dawo da yamma ya samu an haifi Sɗang.
To daga haihuwar Sɗang sai da aka shekara goma kafin Tabitha ta samu wani cikin. Har sun cire rai da sake samun haihuwa sai ga ciki da rana tsaka.

John Yahaya Medugu mutumin ƙauyen Gulak ne da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Madagali a jahar Adamawa.
Mahaifinsa da kowa ke kira Kaka Medugu asalin ɗan ƙabilar Marghi ne ciki da bai. Kaka Medugu tsohon mafarauci ne da ya yi tashe a zamaninsa. Sai dai yadda iyayensa basu karɓi addinin Kiristanci daga hannun 'yan missionary ba haka shima Kaka Medugu ya taso a mabiyin addinin gargajiya. Sai dai fa 'ya'yansa uku da Allah ya bashi duka mabiya addinin Yesu ne. Hakan ya faru saboda matar da ya aura ta karɓi addinin a farko farkon aurensu, sai dai duk yadda ta yi da Kaka Medugu bai karɓi addininta ba, amma kuma duk wani hidima na coci yana bada gudummawarsa. Hakanan idan matarsa na bikin Kirsimeti shima yana tayata murnan haihuwar Yesu Almasihu.

Gulak ƙauye ne da ya haɗa mabiya addinai uku, akwai Kiristoci waɗanda su suka fi yawa, sai kuma Musulmai waɗanda basu kai yawan kiristocin ba. Yawanci cuɗeɗeniyar Fulani ne ya shigo da musulunci ƙauyen. Akwai kuma mabiya addinin gargajiya wanda har yanzu suke riƙe da abubuwan da Kaka da Kakanninsu suka gada musu.
Sai dai shigowar Kiristanci da Musulunci yasa mabiya addinin ƙarfajiyan suka yi ƙaranci, yara da jikoki masu tasowa watsar da wannan addinin suke suna rungumar sabon addini da ya zamo silar haske a gare su.

Kaka Medugu yana ɗaya daga cikin tsoffin da ke ƙauyen wanda aka shaida cewa tasirin Kiristanci Ko Musulunci a ƙauyen bai sauya ra'ayinsu daga tubalin da suka taso ba.
Shi mutum ne mai daraja a idon mutane saboda matarsa ɗaya kaman auren zobe, duk da kuwa mabiya addinin gargajiya suna tara mata a gida. Shi matarsa ɗaya ce har ta mutu shekaru shabiyar da suka wuce, kuma bayanta bai sake wani auren ba.

Har yanzu yana taɓa farauta amma saboda jinyar da ke ƙafarsa ba kasafai ya ke fita ba, kusan yanzu noma ne ya ke son ƙwace sana'ar farauta da ya ke yi tun zamanin samartakansa.

Yaran Kaka Medugu biyu mata ne, sai ɗaya namiji wanda matarsa ta saka masa suna John amma sunansa na yare Adarju ne kuma har gobe Adarju Kaka Medugu ke kiran John.

John Malamin Primary school ne kuma manomi. Yayarsa Martha tana aure a Sukur ita kuma ƙanwarsa Dorcas tana aure a Maɗagali.

John mutum ne mai sauƙin kai da girmama mutane. Akwai shi da riƙo da addini sosai. Duk inda ya shiga a ƙauyen da kekensa sai dai ka ji ana ta Teacher John, Teacher John.

Shekara shahuɗu da suka wuce ya auri matarsa Tabitha. Haihuwar farko ta haifa masa ɗa namiji aka saka masa suna Paul. Amma ko rarrafe bai fara ba ya rasu. A wannan lokacin ne kuma zuwansa Yola wani aikin sa kai ya dawo ƙauyensu da sha'awar musulunci.
A hanyar tafiyarsu Yola aka musu fashi aka ƙwace musu komai. Wani da suka haɗu a motar ya taimaka masa bayan sun sauka ya kai shi shagonsa ya bashi kuɗi ya ce yai kuɗin motar komawa. Wannan abu ya daki ran John. Bayan sun gama abinda za su yi a Yola sai ya koma wajen mutumin nan Alhaji Abubakar dan ya masa godiya da ya je sai ya tarar Alhajin yana kulle shago zai je sallah.
Tun daga nan da ya koma Gulak ya ke bibiyar musulman ƙauyensu yana musu tambayoyi akan musulunci. Sai da aka kai kusan wata huɗu da dawowarsa daga Yola kafin ya karɓi kalmar shahada a wajen Alhaji Abubakar a can Yola.

Bayan matarsa ta sake haihuwa sai ya saka wa ɗansa suna Abubakar suna kiransa da Sɗang.
Daga lokacin da John ya musulunta ya ke amfani da John-Yahaya Medugu a matsayin official sunansa.

Matarsa bata musulunta ba, kuma hakan bai hana zaman lafiya tsakaninsu ba. Shi kam mahaifinsa Kaka Medugu da suke zaune tare da musulunci da kiristanci duk ɗaya ne a wajensa, dukka addinan biyu sun samo asali ne daga turawa da larabawa, basu da haɗi da abubuwan da iyaye da kakanninsu suka gada musu...


Tabitha bata samu haihuwa a gida ba. Tana labour tun safe har rana duk ta galabaita amma haihuwar ya ƙi zuwa, wannan ya sa John Yahaya ya je ya nemo motar a-kori-kura aka wuce da Tabitha Asibiti a can Madagali.
Haihuwa har tsakar dare kafin Tabitha ta haihu da ƙyar dan har ana maganar aiki za a mata washegari. Sai da aka riƙe su a Asibitin kwana biyu kafin aka sallamesu. Suka dawo gida da kyakykyawar jaririyarsu mai manyan idanu kamar na Kaka Medugu.

"Kyauta. Kyauta ce daga Allah" John Yahaya ya faɗa yana shafa kumatun yarinyar.
Ranan suna kuwa aka saka mata suna *KYAUTA-NGWATAM* (Ngwatam- gimbiya/Princess).

Kamar yadda Kaka Medugu ya saba idan aka yi haihuwa zai yi 'yan surkullensa dan ya san irin rayuwar da yaron da aka haifa zai yi. Wannan haihuwar ma sai da yayi abinsa.

Watarana Sɗang yana wasa da Kyauta a tsakar gida kusa da ƙofar Kaka Medugu ya kallesu ya ce "ka yi wasa da ita sosai kafin ku rabu"

John Yahaya da ke gefe yana wanke kekensa ya ce "Baba ka dena wannan magana"

Kaka Medugu ya kurɓi giyarsa dake cikin ƙwarya ya ce " Adarju na gaya maka Kyauta za ta yi nisa da gida"

John Yahaya yai shiru ya tsurawa 'yarsa idanu, can kuma ya girgiza kai ya cigaba da wankinsa.
Duk da dai addininsa ya hana shi yarda da canfe-canfe da duba, amma wasu lokutan Kaka Medugu ya kan faɗi wasu abubuwan kuma ka ga abin ya zo ya faru. Wannan yasa masa shakku a ransa.

Lokacin da Kaka Medugu ya faɗa masa sakamakon bincikensa cewa yai wai 'yarsa Kyauta za ta yi nisa da gida, sannan ita da yayanta Sɗang za su jima basu ga juna ba hankalinsa ya ɗan tashi. Ko Tabitha bai gayawa ba dan kar hankalinta ya tashi. Kullum dai yana addu'ar Allah ya tsare masa Kyauta, ya kula masa da ita har girmanta...


***

Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900


Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41
[27/11, 2:51 pm] Azizat Hamza Writer: *GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)


Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat



Page 008


*1999*

*Azare, Bauchi state*


Asabar ta uku a watan January'n shekarar 1999 aka shaida auren Naseer Muhammad Zaki da Amaryarsa Fatima Umaru Chinade. Sai kuma auren Hadiza Muhammad Zaki da kuma Angonta Dr Anas Saleh Liman. A garin Zaki aka ɗaura duka auren kafin aka taho Azare aka yi wunin biki.

Kar ka ga yadda Iya Abu ke shiga tana fita saboda tsantsan farin ciki. Gashi kowa ya zo ya ga kayan arziƙin da mijin Hadiza ya mata sai yace ai Hadiza ta yi ƙashin arziki. Waɗanda suka je jere gidanta suka dawo da santin kyaun gidan.
Duk cikin 'ya'yan Iya da aka aurar Hadiza ce mijinta ya ke da kuɗi.

Hauwa'u da Aminatu da suke ajin ƙarshe a Sakandare suka fara faɗin ai suma makarantar za su yi tunda Hadiza ma a makaranta ta haɗu da mijinta. Duk cikin samarinsu babu wani mai aikin kirki, abunka da kishi da ake samu tsakanin 'yan'uwa tuni suka fara hasashen yadda nasu bikin zai kasance idan suma suka auri mazaje masu kuɗi.
Gara ma Aminatu dama tana da ƙoƙari sosai kuma tana son karatun tun asali, amma Hauwa'u kam ganin ido ya sa take son yin karatun na dole. Lokacin da take Primary sau biyu ana mata repeat shi yasa ma ta dawo ajinsu ɗaya da ƙanwarta Aminatu. Har yanzun ma karatun sai a hankali, ita tana ɓangaren Commercial ita kuma Aminatu tana yin Science.

Naseer ɗakin Malam ya gyara aka saka Amarya Fatima a ciki. Sati ɗaya da bikin ya koma makaranta saboda hutun ƙarshen shekara da aka basu ya ƙare. Yana ajin ƙarshe yanzu dan haka sune manyan makaranta.

Da ya koma makaranta abokinsa Faruƙ Lawanti ya rinƙa tsokalarsa yana kiransa da angon sati ɗaya.
Hutun ƙarshen semester da ya koma gida ya samu Fatima na laulayin ciki.

Ƙannensa biyu sun zana WAEC ya zauna da su akan me suke su yi, aure ko karatu?. Yanzu kam Iya Abu ta dena ƙin karatun 'ya'ya mata, Hadizarta yanzu koyarwa ta ke a wata makarantar Sakandare tana ɗaukan albashi. Albashinta na farko ma sai da ta siya wa Iya zani.
Dan haka lokacin da Hauwa'u da Aminatu suka zaɓi cigaba da karatu bata ɗaga hankalinta ba, sai dai kuma tana tausayin Naseer saboda duk ɗawainiyar akansa ya ke.

Baffan Basiru da Malam ya masa duk wani gata lokacin da yake da rai sai ga shi a bayan ransa ya share iyalinsa. Ga gida ga gida amma baya iya taimaka musu da komai, idan aka yi magana sai ya ce ai Nasiru yana karɓan albashin sojoji. Ya manta cewa filin da ya gina gidansa akai ma Malam ne ya bashi kyauta lokacin da abubuwa suke da kyau. Zumuncin a baki ya ke dan Baffa ta kansa kawai ya ke, kwanan ma ya ƙaro Amarya matansa suka cika uku.

Iya Abu dai babu ruwanta da halin ko in kula da ƙanin mijinta ya ke da su. Har yanzu tana yin kasuwancinta na cikin gida ga kiwo da ta fara da kuɗin gado da aka bata, kuma Alhamdulillah kiwon tumaki da kajin gida sun ƙarɓeta.
Idan abu ya fi ƙarfinta to sai dai ta nema a wajen ɗanta. Ko 'ya'yanta mata ba ta tambayarsu komai.

Kafin ya koma makaranta Naseer ya biya wa Hauwa'u da Aminatu kuɗin zana jarrabawar JAMB dan so ya ke su tafi jami'a.

Bayan tafiyarsa da wata ɗaya aka aiko masa da Fatima ta yi ɓari. Cikinta bai cika wata shida ba ta haifo shi ba rai.
Abin ya masa zafi saboda ya saka buri akan haihuwar, to amma haka Allah ya so.

A kwana a tashi sai ga shi Allah ya kawo su Naseer sun kammala karatunsu a NDA. Naseer ya samu degree a ɓangaren Psychology shi kuma Faruƙ Lawanti ya gama a Political Science.
Wannan karan Naseer ke tsokalar Faruƙ yana tuna masa kukan da yayi ta yi farkon zuwansu Makarantar yana cewa shi ya gaji guduwa zai yi.

Ranan da za su gama iyayen Faruƙ sun zo kuma bisa tursasawar Faruƙ bayan an gama hidima a makaranta suka wuce gidansu Faruƙ ɗin a cikin gari inda mahaifinsa ya shirya musu dinner gama NDA. Ganin yadda mahaifin Faruƙ ke alfahari da ɗansa ya sa shi tunanin ina ma Malam yana raye shima yayi alfahari da abinda ya zama.
A gidansu Faruƙ Naseer ya kwana sai washegari ya kama hanyar Azare.

Tun daga sallama Hassana da Hussaina da ke wanki a tsakar gida suka danno da gudu suka rungume shi suna ihun murna.
Iya da ke ɗaki tana kwance saboda zazzaɓi da ya rufeta ta taso jin ihun yaran.
Daga bakin ƙofa Iya ta tsaya tana kallon Nasirunta yadda ya zamo wani murɗaɗɗen namiji.

"Ku sake ni na gaishe da Iya"

Tsugunnawa ya yi a gabanta ya ce " Iya mun dawo, a sa mana Albarka"

"Yanzu shikenan ka dawo gaba ɗaya kenan?"

Ya girgiza kai ya ce "zan sake tafiya amma shekara ɗaya ne wannan"

Da guntun hawaye a idanunta ta ce "Allah ya maka Albarka, Nasiru"
Ya amsa da Amin.
Sai da suka ɗan zanta kafin ya shiga wajen matarsa wacce ta kasa fitowa saboda kunya.

Matseta ya yi a jikinsa yana faɗin " mun same ku lafiya, Faty na"
Ta ɓoye fiskarta jikinsa tana murmushi. Ta yi kewarsa sosai.

Kwana biyu da dawowarsa ya kama ziyarar 'yan'uwa, tun bikinsa bai ga yayyensa ba. Kowacce sai da ya je gidanta, Indo da ke can Kano ne bai samu zuwa mata ba. Hadiza ta haifi ɗanta namiji har ya fara zama.

Bayan ya sarara kuma ya koma lamarin ƙannensa. Aminatu bata samu English da Chemistry a WAEC ba wannan yasa BUK suka hanata admission. Ita kuma Hauwa'u kwata-kwata ma ba abunda ta samu sai credit biyu a Hausa da Islamic.

Naseer ya nema wa Aminatu admission a School of Health Technology da ke Ningi kuma aka ci sa'a ta samu. Ita kuma Hauwa'u yayi ƙoƙarin sama mata COE Azare amma abin bai yiwu ba, dole dai sai ta sake zana paper. Daga haka ya ce ta zaɓi sana'ar da take so ta ce masa ɗinki. Ya je ya biya mata kuɗin form a shagun wata mata 'yar Igala da ta iya ɗinki sosai, ta fara zuwa shagon tana koyan ɗinki.

Bai jima da dawowa ba ya fara shirye-shiryen zuwa training na shekara ɗaya a India. Faruƙ ne ya taimaka masa wajen samun international passport ɗinsa da wuri. Lokacin tafiyar Faruƙ ya riga shi tafiya su kuma sai a batch na biyu suka samu tafiya.
Lokacin da Visarsa ta fito ya sanar da Iya duk sai ta ɓata rai. Kwana biyu da yake gida tana jin daɗin ganinsa yanzu idan ya tafi zai bar Fatima da kaɗaici.

"Iya ba yaƙi zan je ba fa. Training za mu je na shekara ɗaya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment