Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iyali suka fara yawa gashi mahaifinsa ya rasu shi ke kula da mahaifiyarsu da ƙannensa.

Wannan rufin asiri shi ya kawo su ga wannan lokaci, babu arziƙin amma akwai wadata da kwanciyar hankali.
Yanzu haka yana taɓa noma da kasuwanci kuma Alhamdulillahi ya fi ƙarfin roƙo.

Allah ya Azurta Malam Muhammadu da 'ya'ya goma. 'Ya'ya huɗu Abu ta haiho duka mata kafin aka samu namiji.
Sai da aka samu Maimuna, Aisha (Indo), Mariya, da Bintu kafin aka samu Muhammadu Naseer. Daga shi kuma aka sake haifo wasu biyar ɗin duka mata. Hadiza, Hauwa'u, Amina, da kuma 'yan biyu Hassana da Hussaina.

Yayyen Naseer duka an aurar da su. Maimuna aka fara yiwa aure tana gama makarantar Firamare. Daga baya aka haɗa Indo da Mariya aka musu aure, dama shekara ɗaya ne tazarar dake tsakaninsu.
Ita Bintu shekara biyu kenan da aka aurar da ita. Cikin 'ya'yan da aka aurar Bintu ce ba a aurar da ita da wuri ba, dan sai da ta kai shekara shashida kafin aka mata aure.
Ta gama Primary ta yi Form 1-3 kafin Malam yace bokon ya isa haka.

Hadiza da ke bin Naseer ma sai da aka shigo da maganar aurar da ita Naseer yace fau fau a barta ta kammala Sakandare tunda tana son karatu. Dama wani ɗan Baffansu ne ya fito wai yana sonta. Malam da Iya Abu kuwa dama basa iya yiwa Naseer musu saboda yadda suke son ɗan nasu. Har gara ma Malam ya kan ɗauke ido ya masa faɗa wani lokaci, amma Iya Abu sam duk abinda Nasirunta yayi dai-dai ne bata iya masa faɗa.
Kafin ta haifi Naseer, har gorin haihuwar 'ya'ya mata ake mata da aka ga ta haifi huɗu a jere duka mata. Bayan haihuwarsa kuma sauran ma matan ne dan haka shi take gani ta ji cewa yanzu babu mai mata gori. Bata haifi maza dayawa ba, amma Nasirunta ma NAMIJI ne kamar kowanne ɗa namiji...




***


Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900


Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41
[27/11, 2:51 pm] Azizat Hamza Writer: *GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)


Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat



Page 003


Lokacin da aka zo aka sanar Indo ta haihu Iya Abu na zaune a ƙofar ɗakinta tana ƙullin Omo. Malam da kansa ya shigo ya faɗa mata dan zai shigo gida bayan ya dawo daga sallar La'asar Halilu mijin Indo ya tare shi yake gaya masa haihuwar.

"Namiji aka samu" Malam ya faɗa yana ƙoƙarin zama akan tabarmar da Iya Abu ke zaune. Ciwon kai da yake fama da shi ya sa tun Azahar ya baro kasuwa.

"Allah ya raya" Iya Abu ta faɗa ƙasa-ƙasa cike da kunyar wai 'yar tata har ta riga ta haihuwa.

"Ɗazu a kasuwa Malam Umari ke faɗa mini jibi ɗansa zai dawo, kin kuwa san shima yaron na sa a can Toro yake karatu. Ina ga shima Nasirun jibi yana hanya"

"Alhamdulillahi" Iya Abu ta faɗa tana washe baki.

"Allah ya dawo da shi lafiya"

Ga Makaranta nan nan a Azare amma haka Nasiru ya tsallake ya tafi Toro. Ita dai ko kaɗan ba ta son Nasiru yayi nisa da gida. Shine fa magajin gidan gaba ɗaya. Sauran matan da ke gabanta yanzu da an kwana biyu da ɗauki ɗai-ɗai za a aurar da su su tafi gidan mazajensu. Amma Nasiru shine Babban gida.

Iya Abu ta miƙe tana goge sauran burbuɗin Omo a jikin zaninta ta ɗauki fantekar kayanta ta shiga da shi ɗaki.

Yaran suna dawowa daga Makarantar Allo da Iya ta faɗa musu Indo ta haihu suka wanke ƙafa suka tafi duba jariri. Haihuwar Indo na biyu kenan, ta farkon da ta haifeta shekara uku da suka wuce bata zo da rai ba sai kuma ɓari da ta yi sannan wannan.

Kamar baki washegari da Asubahi Iya Abu ta tashi da naƙuda. Ta daure ta cigaba da ɗan ayyukanta kafin haihuwar ta zo. Dukkan haihuwanta a gida ta yi. Ungozomar anguwarsu ake kira mata ta karɓi haihuwar. A haihuwar 'yanbiyunta da ta ɗan wahala ne ma aka kira mata wata sabuwar Amarya midwife da ke ƙasan layinsu da suke kira da Sister Fati Ita ta ƙarfi haihuwar dik da kuwa ta so Iya Abu ta yarda su je Asibiti amma ta ƙi ta dage ita ba inda za ta je.

Wasa wasa Iya Abu na tunanin haihuwa kafin hantsi sai ga shi har Azahar shiru. Zuwa la'asar da Kande Ungozoma ta zo gaba ɗaya ta galabaita. Shiru haihuwa har Magariba. An je neman Sister Fati a gida wai tana Asibiti.
Iya Abu ta galabaita ƙwarai. Da Malam ya dawo daga sallar Magariba aka ce har yanzu shiru ya ce su tafi Asibiti kawai.
Iya Abu ta ƙi fau fau. Wai 'yarta Indo ta haihu a Asibiti sannan itama ta je ta haihu a Asibiti, wannan abin kunya ne.

Sai kusan ƙarfe goma na dare da Sister Fati ta zo gidan sannan Iya Abu ta haihu. Lokacin ta gama yin laushi kusan ƙarfinta ya ƙare.
Bayan ta haihun Sister Fati ta ce ya kamata gobe da safe su je Asibiti a ƙara dubata.

Tunda aka ce mace ta haifa Iya Abu ta ji jikinta ya yi sanyi. Ta riga ta gama saka rai da haihuwar namiji sai ga shi macen ta sake haihowa.

Washegari Iya Abu ta tashi da yunƙurin fara aikace-aikacen da ta saba duk da kuwa jikinta babu wani ƙarfi.
Ta saba idan ta haihu da ƙarfinta take tashi ta cigaba da harkokinta kamar ba ita ta haihu ba.
Lokacin da ta ciko bokiti da ruwan zafi za ta shiga banɗaki sai ta yanki jiki ta faɗi...



***


*GOVERNMENT COLLEGE, TORO*


Kusan kowanni ɗalibi cikin ɗaliban da suka kammala jarrabawar ƙarshe a makarantar Government College da ke Toro murna haɗe da kewa ne cunkushe a zukatansu.
Daga an rabu yau ba a san yaushe za a sake haɗuwa ba.
Ɗalibai da dama za su yi kewar Senior Zaki saboda mutuncinsa. Ba ya ƙuntatawa juniors, amma fa idan junior yayi laifi zai sha punishment mai shiga jiki. Amma wai irin cin zali na haka kawai da seniors ke wa juniors ɗinsu senior Zaki ba ya wannan, kuma ko ya ga ana yi zai sa baki ya hana.

Tuni sun haɗa kayansu. Lokacin da aka fara kiran 'yan Azare senior Zaki ya shiga bankwana na ƙarshe da sauran abokansa da juniors ɗinsa da suka ɗauko masa kaya.
Wasu har da hawaye saboda senior Zaki daban ne a cikin dukkan seniors ɗin da suka gama. Yana da zafi sannan yana da sauƙin kai. In dai ba ka laifi to babu abinda zai haɗa ka da senior Zaki.

Senior Zaki ya shiga motar yana kewar gida, yau dai babu cin tuwon hostel sai tuwon Iyansa.
Lokacin da ɗalibai 'yan Azare suka gama shiga motar sai Direba ya hau hanya.
Ana tafiya ana taɗi. Wasu kuma na sake taya senior Zaki murnar kyaututtukan da aka ba shi. Har da masu cewa sai sun bi shi gida sun buɗe kyaututtukan kafin su wuce na su gidan.
Shi kan sai murmushi ya ke yana ayyanawa a ransa babu mai buɗe kyaututtukan da aka bashi sai Iya.

Motar ta su ta yi gudu sosai dan ana kiran sallar la'asar suka shigo Azare.

Tun daga bakin titi da Naseer ya sauka akan mashin yara suka yanyame shi suna masa oyoyo. Wasu suka ɗauki akwatinsa na ƙarfe wasu kuma suka ɗau jakar Ghana-must-go suka bi shi har cikin gida.
Yadda tsakar gidan ya ke a hargitse ya fara sanar da shi ba lafiya a gidan. Iya Abu bata barin waje da datti.

Ya juyo ya tambayi ƙaninsa Nura ɗan Baffansu da ya riƙe masa ledar tsarabar da ya siyawa su Iya a tasha.
"Ina mutanen gidan?"

"Sun tafi Asibiti"

"Waye ba lafiya?"

"Iya Abu"
Ai bai jira ƙarshen ba ya fita. Sashen Baffansa ya shiga inda Amaryar Baffansa da suke kira Umma Talatu ta sanar da shi Asibitin da aka kai Iya Abun.

Lokacin da ya isa Asibitin ya tarar ana buƙatar jini. Jinin Baba A+ ne ita kuma Iya Abu O+ ne. Wai an aika Chinade ƙannenta su taho.

Ran Naseer a ɓace ya fara yiwa Baffansa magana.
"Fisabilillahi Baffa tun safe a ce wai ana jiran sai mutanen Chinade sun zo sannan a sa mata jini"

Baffansa na ƙoƙarin bashi amsa ya share shi ya bi bayan wata Nurse yana tambayarta ina zai je a ɗauki jinin. Ya riga ya san kalar jininsa O+ ne tun a Makaranta da aka taɓa masa gwajin.

Sai da aka ɗau jinin ya fito ya samu Baba ma ya dawo. Dama zuwa yai neman kuɗi. Buhun hatsi ya kai kasuwa ya siyar a farashi mai rahusa duk dai dan ya samu kuɗin Asibiti.
Jini leda uku ake buƙata da safe da ƙyar aka samu aka sayi leda ɗaya aka saka mata shi yasa ma suka aika Chinade ɗin saboda 'yan'uwanta su zo.

"Baba" Naseer ya ƙarisa wajen yana dafa kansa saboda hajijiya da yake ji. Nurse ɗin ta ce ya tsaya ya huta amma ko minti biyar bai yi ba da aka ɗau jinin ya fito.

Baba ya riƙe shi ya zaunar da shi kan kujera.
"Sannu ko. Allah ya maka Albarka"

Zuwa Maghriba mutanen Chinade suka iso. Amma saboda an riga an saka wa Iya leda biyu sai washegari za a saka leda na ukun.
Aka haɗu ana yiwa juna sannu.
Sai a lokacin Naseer ya san cewa Iya haihuwa ta yi. Taɓ! Yai ta mamaki dan hutun ƙarshe da ya zo gida har ya tafi bai san Iya na da ciki ba.

Wasa-wasa Iya Abu sai da ta yi kwana goma a Asibiti kafin aka sallameta. Zuwa lokacin 'yar da ta haifa ta rasu ana kwana huɗu da haihuwarta. Malam ya sa wa 'yar suna Jamila.

Mutuwar jaririyar yai wa Iya ciwo. Ko da ta dawo gida sai da aka ɗau lokaci kafin ta fara dawo da walwalarta.



********




Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900


Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41
[27/11, 2:51 pm] Azizat Hamza Writer: *GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)


Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat



Page 004




"Soja dai?"

Iya Abu ta sake kifiyar da ke hannunta da take wa Hussaina kitso.

Naseer ya tsaya daga gefe riƙe da form ɗin NDA da ya je ya siyo a Kaduna. Jiya da dare da ya dawo bai samu ya yiwa Iya bayani ba amma da Asuba ya zanta da Baba wanda shima ya nuna damuwarsa kan ra'ayinsa na son zuwa Makarantar Sojoji.

"A'a ba zai yiwu ba Nasiru, bayan ka san kai ne Babban gida"

"Iya na sha faɗa muku Soja nake son zama. Wai menene a aikin Sojan nan ne"

"Ka haƙura da maganan Sojan nan. Ga karatun Likita ko Malamin makaranta duk zaka iya yi. Ɗan gidan Gajiye ba Likita aka ce zai zama ba, yana can yana karatu a Maiduguri"

"Iya gaskiya ki yi haƙuri ra'ayina kenan"

Iya ta juyo ta masa wani kallo sannan ta cigaba da kitson da take.

Naseer yayi shiru yana bin form ɗin hannunsa da kallo.

Kallo ɗaya zaka yiwa Iya ka ga tsantsan kamanninta da Naseer, sai zanen uku-uku da ke gefen goshin Iyan wanda ya fara koɗewa saboda girma kaɗai da Naseer ɗin ba shi da shi.

Iya Abu baƙar bafulatana ce. Tana da tsawo da dogon hanci da ya ƙawata matsakaicin fiskarta. Bata da jiki sam kuma jinyar da ta yi kwanan baya ya sake bushar da ita.
Naseer babu abinda ya bari na kamannin Iya sai ɗan kaurin jiki da ya ɗauko daga wajen Malam. Saɓanin Iya shi Malam yana da tsayi kuma yana da ɗan kaurin jiki. A duk cikin 'ya'yansu Hadiza ce kawai bata da tsayi amma duk sun yi gadon tsawo daga wajen iyayensu.
Shi Malam fari ne amma ba sosai ba shi yasa yaran suka rabu biyu, wasu sun ɗauko hasken fatarsa wasu kuma sun ɗauko baƙin Iya.
Asalinsu Malam ruwa biyu ne, jinin Fulani ne da jinin Bare-Bari. Ance Kakansa daga wajajen Potiskum ya taho Almajiranci garin Zaki, a nan yai aure ya haɗa dangantakar aure da Fulani. Daga nan kuma 'ya'ya da jikoki duk suka kasance mazauna garin Zaki.

Ita Iya ta ko ina ta haɗa jini da Fulani. Tana jin Fulatanci sosai dan ko lokacin da Malam ya aurota ba ta jin Hausa sosai amma saboda shi Malam ba ya jin Fulatanci da kuma zama cikin Hausawa sai ya zamana itama harshen nata ya juya zuwa Hausa dan idan ka ga tana Fulatanci to tana cikin 'yan'uwanta ne.


"ban amince da karatun Soja ba. Allah ya tsareka da aikin kasada"

"Haba Iya! Haba Iya!"

Iya ta sa hannu a ƙasa ta lalumi kifiya ta cigaba da tsaga kan Hussaina.

Wasa-wasa batun maganar zuwa makarantar Sojoji ta jawo rikici tsakanin Naseer da Iya. Shi ga shi ya je ya karɓo form ya cika amma Iya ta ce sam bata yarda ba. Idan kuma ya takura sai dai yayi gaban kansa.

Shima dai Baba ba wai yana ra'ayin zaɓin ɗan nasa bane musamman yadda ake jin jiki a mulkin Soja da ake ciki. Amma kuma baya so ya tursasa wa ɗan nasa. Tun yana ƙarami yake maimaita cewa shi kam Soja zai zama. Ga shi har yanzu abin na ransa.


"Zainabu" Malam ya kira sunan Iya lokacin da suka kaɗaice a ɗaki.

"Na'am Malam"

"Ba zan miki dole ki canja ra'ayinki ba. Amma maganar Nasiru ki sake dubawa"

"Malam shi kaɗai fa garemu. Aikin Soja akwai kasada a ciki. Mijin Nafisa watansu uku da aure da aka turasu yaƙi ko gawarsa ba a gani ba" idanunta suka cicciko da hawaye.

"Malam ka yi haƙuri mu haɗu mu hana shi wannan aikin"

Malam yayi shiru. Ya san abinda ta ke tsoro.

Shi kam har cikin ransa da Naseer da sauran 'yan'uwansa mata duk ɗaya suke a wajensa.
An sha yi masa maganar ƙarin aure saboda ya samu haihuwar 'ya'ya maza dayawa amma ya ƙi. Duk 'yan'uwansa maza babu mai mace ɗaya sai shi.

"Kin ga, mutuwa da kike gani ba a iya guje mata. Ko Nasiru ya shiga aikin Soja ko bai shiga ba idan lokacinsa ya yi bamu isa mu hana shi tafiya ba. Tunda bamu da iko akan haka kin ga kuwa ba zamu hana shi yin abinda yake so saboda kawai muna tsoron masa mutuwa ba"

"Malam..." hawaye ya hanata fito da maganarta. Malam ya matsa kusa da ita ya riƙeta yana sake bata baki.

Tunda ta auri Malam Iya Abu ba ta taɓa yi masa musu ba. Tarbiyar da aka mata kenan, yi na yi, bari na bari.
Ta sani tunda ya mata wannan maganar yana roƙo ne da ta amince da buƙatar Naseer.
Girman Malam a wajenta da kuma nasihar da ya mata ya sanya ta haƙura ta cewa Naseer ta amince.
Lokacin da ta kira Naseer ta sanar da shi ta amince tsabar murna har da faɗawa jikinta ya rungumeta ƙyam yana dariya. Abin ka da kunyar nan ta Fulani ta fara ture shi tana faɗin ya saketa amma shi ko a jikinsa, sai da ya samu nitsuwar ɗumin uwa kafin ya saketa.
Duk da yana tsananin son aikin Soja ya riga ya yiwa kansa zaɓi, in dai Iya bata amince ba to zai haƙura ya nemi wata makarantar. Sai ga shi Allah ya ji addu'arsa Iya ta amince.

Ranan da za su je jarrabawa. Iya har da sadaka tana addu'ar idan zaɓin Naseer alkhairi ne Allah ya tabbatar ya sa ya ci jarrabawar. Idan kuma ba shi bane alkhairi to Allah ya chanja masa da wata.

Bayan wata ɗaya aka manna sunan waɗanda suka ci. Sunan Nasir Muhammad Zaki ya kasance cikin ɗaliban da aka ɗauka a shekarar 1996 a makarantar Nigerian Defence Academy da ke Kaduna.
Ranan da Naseer zai tafi Iya har da ƙwalla. Ta dinga binsa da addu'a shi kuwa sai murmushi yake yana faɗin Makaranta zai je ba yaƙi ba. Ita dai Iya har yanzu tsoro ta ke dan dai kawai babu yadda ta iya ne amma maganar Sojan nan bata so.



***

*1996*

*Nigerian Defence Academy, Kaduna*



Tun daga bakin gate Sojoji suka ce su ɗauki jakukkunansu a ka su kama tsallen kwaɗo su shiga ciki.
Nasir yai murmushin gefen baki lokacin da ya hango wani ɗalibi da iyayensa suka kawo ɗazu a mota. Akwatuna biyu ne da wata ƙatuwar jaka a gefe. Ko ya za a ayi ya ɗauki waɗannan kayan oho.
Shi kam ya gode Allah da bai riƙo kaya ba. Akwatinsa na ƙarfe ta makaranta ta riga ta ji jiki dan saman akwatin duk ya mokwaɗe bata rufuwa da kyau, shi yasa bai ɗaukota ba.

Naseer yayi Bismillah ya saɓi jakar ghana-must-go da ya taho da shi daga gida a ka ya kama tsallen kwaɗo ya bi sauran ɗaliban da ke gaba suna tsalle da akwatuna a kai.

Garin kwakwi da garin ƙanzo da yaji da Iya ta haɗa masa su suka ƙarawa jakar ta sa nauyi dan ya san dai shi kam bai ɗau wasu kaya masu yawa ba. Daga 'yan kayan sawa kaɗan sai takardun Makaranta.

Ya iso dai-dai yaron nan mai akwatuna dariya ya ƙwace masa. Yaron sai zunduma kuka yake yana roƙon wani Soja da ya tsaya a kansa lallai sai ya ɗau duka kayan lokaci guda.

"Kai mai dariya zo nan" aka daka masa tsawa

Naseer ya gimtse dariyan ya tsaya da tsalle.

Shi ba wai ma yaron ne ya bashi dariya ba tunowa da yai iyayen yaron da suka kawo shi ɗazu har da yiwa wasu Sojoji magana akan a kula da ɗansu. Sojojin suka ce ba matsala su tafi za a kula da shi. Da haka suka kori duk waɗanda suka rako 'ya'yansu. Sai ga shi tun daga gate an fara nuna musu banbancin civilian da Soja.

Akwatin yaron ɗaya Sojan ya aza wa Naseer ya ce ya wuce. Shi kuma yaron aka haɗa shi da akwatinsa ɗaya da jaka. Hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarsa suka kama tsalle suka shiga cikin Makarantar Sojoji na binsu a baya suna waƙa.

Shi Naseer duk da kayansa ya fi na yaron nauyi ya fi shi sauri. Sai ya yi nisa sosai sai ya tsaya ya ɗan jira yaron wanda ya haƙura da kukan ya yi shiru. Ba shi kaɗai bane yaron babba a wajen kuma duk kukan mutum Sojojin nan babu ruwansu sai dai ka yi tsalle ka tsaya ka huta ka cigaba amma babu wanda suka yarje wa yayi tafiya a tsaye.

"Naseer Zaki" Naseer ya faɗa lokacin da yaron da ya ragewa jaka ya iso shi yana haki.

"Fa Faruƙ Lawanti" ya faɗa da ƙyar yana haki.

Naseer ya sa dariya. Shima Faruk ɗin ya saka dariyan wahalar da suka tsinci kansu a ciki.

A haka suka cigaba da tsalle har suka isa bakin Admin block. Ba ƙaramin nisa ne daga bakin gate zuwa wajen ba.

Suka nuna takardunsu da admission letter. Aka fara raba musu hostels.
Faruƙ ya riƙe hannun Naseer yana Allah Allah a haɗasu ɗaki ɗaya.


Suna tsaye Admin Officer ɗin ya kira sunaye huɗu " Zaki, Tsoho, Akande, Lawanti. Go to D Block"
Tuni suka sake rungumar kayansu suka bar wajen dan neman D Block wannan karan a ƙafa suke babu batun tsallen kwaɗo suna tafiya ƙafafuwansu duk ta yi tsami.



***



Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900


Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41
[27/11, 2:51 pm] Azizat Hamza Writer: *GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)


Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat



Page 005


***

Suna isa bakin hostel ɗin suka tarar wasu seniors ɗinsu na tsaye da bulala duk wanda zai shiga sai an masa bulala uku a baya wai WELCOME TEA kenan.
Faruƙ Lawanti kaman ya kurma ihu wato ma dai gidan wahala Babansa ya turo shi. Mahaifinsa Kwamishinan lafiya ne a Kaduna. Ba ya son zuwa NDA mahaifinsa ne ya takura masa akan makarantar da zai yi kenan.

Nasir kam ko a jikinsa. Ya sani wannan somin-taɓi ne ma akan abinda za su tarar gaba. Kuma ko kaɗan bai yi dana sanin zaɓinsa na son zama soja ba.

Ko ɗar bai yi ba lokacin da aka zuba masa bulala a baya. Yayin da Faruƙ ke ta rawar jiki.

Suna shiga ciki aka nuna wa kowa gadonsa sannan aka gwada musu yadda ake gyara gado. Ba yadda Amarya ke gyara gado ba, yadda sojoji ke gyara gado. Aka ce kullum gadon su ya zamto irin haka ko kuma dukkansu su sha punishment. Ko zama ba su yi ba bayan sun canja cikin uniform da aka basu aka buga ƙararrawar fita cin abinci.

Ba su suka dawo ɗakin ba kuwa sai can dare kusan ƙarfe shaɗaya, dan kuwa daga cin abinci suka yi sallah aka sa su gudu. Bayan nan kuma aka kira su camp fire drill inda kowannensu sai da ya tsallake wuta. Suka dinga rawa suna zagaye wutan jikinsu na ƙuna saboda zafin wutan.

"Naseer ni fa zan gudu, ba zan iya wannan wahalar ba"

Naseer ya juyo gefen Faruƙ ɗin wanda tun da ya hau gado ya ke ta nishi gaba ɗaya jikinsa yayi tsami.

"Haba kai kuwa, tun daga ranan farko. Ka yi haƙuri dai har zuwa lokacin da zamu saba"

"Ni fa ba zan iya sabawa da wannan wahalar ba"

"Za ka saba"

Ƙarfe huɗu da rabi sai ga shi an buga ƙararrawar tashi. Faruƙ ji yayi kamar ma baccin da yayi bai kai awa ɗaya ba aka tashe su.
Tuni Naseer har ya miƙe ya gyara gadonsa kamar yadda aka koya musu jiya. Yana ƙoƙarin cewa Faruƙ zai gyara masa nasa aka shigo duba su dukkansu sai suka ƙame. Faruk da wasu uku gadonsu ba a gyare yake ba sai wasu guda huɗu da suka gyara gadon amma bai yi neat irin yadda aka koya musu ba.
Dukka ɗakin kuwa sai da suka sha punishment, da wanda yayi laifi da wanda bai yi ba.

A ranan aka fara koya musu deep water swimming da yadda za su iya tsayawa cikin ƙasan ruwa na mintuna.
Lokacin da aka gama gaba ɗaya sun galabaita. Naseer ma ya ji jiki dan rabonsa da shiga ruwa tun suna yara da suke zuwa wanka a rafi.
Daga baya aka kai su aka fara koya musu yadda za su yi amfani da wuƙa su far wa abokan gaba.

Idan aka ce ana cin kwakwa a NDA to kuwa ba a yi ƙarya ba dan kuwa zuwa 'yan kwanaki da zuwan su Naseer NDA wasu da suka gaji da training da ake musu suka hau katanga suka gudu gida. Wasu kuwa cewa suka yi ba za su iya ba suka nemi a barsu su tafi. Ba dan Naseer da ya hana Faruƙ guduwa ba da tuni ya gudu dan ya riga ya gaji da wahalar makarantan.



***


Iya Abu na zaune a ɗaki tana ninke kayan wanki ta jiyo sallamar Malam a tsakar gida. Ya sako kai cikin ɗakin tana ƙoƙarin fitowa.
"Ina tare da baƙo daga Chinade, a kawo masa ruwa da abinci"

"Malam waye?"

"Amadu ne, ƙanin mijin Halima"

"Lafiya dai ko?"

"To, lafiyar dai muke fata"

A zaure suka zauna inda Malam ke tambayarsa mutanen gida. Bayan an kawo masa ruwan randa mai sanyi ya sha tukunna ya faɗi abinda ya kawo shi. Allah ya yiwa Halima matar yayarsa wacce ta ke ƙanwa wajen Iya Abu rasuwa, har anyi sadakan uku ma.

Lokacin da Malam ya faɗa wa Iya Abu sai da ta yi kuka. Halima ƙanwarta ta uku kenan, uwarsu ɗaya ubansu ɗaya.

Yadda Allah ya jarrabceta da haihuwar 'ya'ya mata ita kuma jarrabawarta tunda ta haifi Fatima yau shekara goma shahuɗu bata sake haihuwa ba. 'Ya ɗaya kamar mayya, gorin da kishiyoyinta ke mata kenan.

Da yamma bayan Amadu ya tafi Iya ta nemi izini Malam ya bar ta ta je Chinade dan ta yiwa 'yan'uwanta ta'aziya. Bayan kwana ɗaya Iya ta shirya ta tafi garinsu.

Ko da ta je gidan rasuwa yadda ta samu 'yar marigayiyar bai

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment