Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita ta fara masa ƙorafin idan ta tafi za a bar Iya Abu cikin kaɗaici sai ya haƙura. Shima dai rashin sanin yanayin garin ya sa bai takura mata akan dole sai sun taho tare ba.

Kamar yadda yai niyya da ya samu sarari ya je gida ya ce da Iya zai taho da Fatima. Bata hana shi ba amma tace ya bari a yi bikin Hauwa'u tukunna tunda bikin ya yi kusa. Da haka dai ya haƙura ya sake dawowa babu matarsa.

Ƙarshen shekara da ya je bikin ƙanwarsa Hauwa'u ya taho da matarsa da ɗansa.
Ita kam Hauwa'u bokon dai bai yiwu ba dan samarin da take tarawa ma ba zasu barta ta yi karatun ba. Tun data sake zana paper bata ci ba ta watsar da maganar karatun ta rungumi ɗinki. Alhamdulillah lokacin da Ogarta ta mata freedom ta ƙware sosai a iya ɗinki.
Naseer ya kashe mata kuɗi sosai a bikinta ya kuma siya mata keken ɗinki akan idan ta je can gidan mijinta a Bauchi sai ta fara sana'ar ɗinki a can.

Ita kuwa Aminatu bayan ta gama Health Tech Ningi sai ta sake samun gurbin karatu a BUK ita ko maganar aure bata yi ta sa a ranta sai ta cimma burinta na zama ƙwarriyar Likita.

Koda Naseer ya taho da Fatima Ekiti gaba ɗaya zaman barrack yai mata banbaraƙwai. Ta fara kewar su Iya saboda kaɗaici.
Ita dama tun can ba mai son hayaniya ba ce, ga shi barrack ɗin yawanci Yarabawa sun fi yawa.
In dai Naseer ya fita to tana gida ita da ɗanta tana kallo ko karatun novels wanda ta taho da su tun daga Azare.
Cikin matan maƙotansu wata Bahaushiya bakatsiniya ce Maman Iklimah kawai su ke ɗan magana, ita ma ba sosai ba.

Abinka da aikin Soja ko wata shida bata kai ba a garin aka sake yiwa Naseer transfer zuwa Ondo. Haka suka sake ɗunguma suka wuce barrack ɗin Akure.
Da suka je ta fara ji ina ma a Azaren kawai ya barta ya ke zuwa mata duk sanda ya samu dama. Har ta ɗan fara sabawa da mutanen Ekiti kuma sai ga shi sun dawo Akure.

Lokacin da Naseer ya samu ƙarin rank zuwa matsayin First Lieutenant sai aka sake tura shi jihar Calabar. Wannan karan kam sai da Fatima ta koma Azare ta ga 'yan'uwa sannan wani zuwansa hutu ya ɗauketa suka wuce Calabar. Ita dai wannan tashi-tashin da suke ya fi komai bata wahala. Sai ta ɗan fara sabawa da waje sai a sake tura shi wani wajen.
To ya za ta yi. Ita fa ke auran Soja.
Hatta Al'amin abin sai da ya shafe shi. An sa shi makaranta a Akure ya ɗan fara kama karatu aka sake tisa ƙeyarsa zuwa wata makarantar a nan Calabar...


*ko kun hango abinda na hango?*
*ga Munira MoBaby ga Kyauta Ngwatam🤔*




***

Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900


Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41
[27/11, 2:51 pm] Azizat Hamza Writer: *GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)


Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat



Page 012


Da rana tsaka Iya Abu ta tsinkayi sallamar Mariya, ganinta janye da akwatuna biye da yaranta uku ta san ba lafiya ba.
Bata tambayeta dalilin zuwan nata ba sai da Mariyan ta gama jera akwatunanta a ɗaki ta shiga kitchen ta dafawa yaranta taliyar murji suka haɗu suka ci.

"Me ya haɗa ki da Baban su Farida?"

"Cewa yayi ya sake ni"

Iya ta ja numfashi ta ce "Allah ya kyauta".

Lokacin da Naseer ya bugo waya Iya ta ke gaya masa Mariya ta dawo gida mijin ya sake ta. Naseer ya ce idan ya zo zai zauna da mijin.

Wannan zuwan da Naseer yayi gida ya tarar da abubuwa da dama ga maganar Mariya wacce da ya samu zama da Mariyan ya ji bayani daga wajenta ya kuma kira mijin suka yi magana sai ya ga gara kawai rabuwar saboda auren akwai cutarwa. Ya ma ga ƙoƙarin zaman Mariya da mijin iya waɗannan shekaru. Wai ace kusan shekara biyu kenan kusan ita kaɗai ke ciyar da kanta. Sai ta yi sana'a ta samu kuɗi ma ya karɓe kuɗin da bashin da babu ranan biya. Yanzun ma aure ya rungumo kuma ya san ba zai iya riƙe su su biyu ba ya ce ya saketa.

Ta ya ma namiji zai auri mace ya riƙa muzguna mata?.
Mata da suke da rauni.
Mata abun tausayawa ne fa.
Nauyi ne ya ƙaru masa dan kuwa mijin Mariya ba shi da niyyar ɗaukan buƙatun yaransu uku. Itama kanta Mariyar da ta gama idda zai bata jari ta fara wani abun.
Wannan zuwan nasa yasa aka fara gyaran gidansu, niyyarsa idan aka kammala gyaran sai ya maida hakalinsa kan nasa ginin, inda ya sai filin aka masa foundation ma babu nisa da gidan Iyayensa.

"Iya za a turamu aiki Delta, sai a saka mu a Addu'a"

"Ni kam aikin Sojan nan, Nasiru, Toh! Allah dai ya tsare, amma zuciyata bata so. Yau kuna nan gobe kuna can. Da ka tafi hankalina kwata-kwata baya kwanciya har sai ka zo gida"

"Iya addu'a kawai za ki cigaba da yi mana"

"Yanzu da Fatiman za ka wuce can?"

"Ba zai yiwu na tafi da ita ba."

"To ka kawota gida mana"

"Al'amin yana makaranta. Itama akwai makarantar koyon girki da take yi"

"To, Allah ya kaika lafiya ya dawo mana da kai lafiya. Allah yasa a je a yi aikin a sa'a a dawo a sa'a"

Naseer ya amsa da Amin...


***

*2004, Lokoja, Kogi State*


Babu abinda ke ɗaga hankalin matar soja irin a tura su aikin kwantar da tarzoma. Watanni biyu kenan da tafiyar Naseer Delta. Watan farko yana ɗan bugowa idan ya samu dama amma yanzu kusan sati uku kenan Fatima bata ji ɗuriyar mijinta ba.

"Ki riƙa mini addu'a Faty na. Bana son ƙi riƙa kuka kin ji. Ke fa matar soja ce dan haka kema kin zama soja" ya cire hularsa ya saka mata sannan ya ɗaga hannu ya sara mata. Tintsirewa ta yi da dariya ganin yadda ya wani ƙame ya haɗe fiska kamar ita ɗin soja ce. Hawayen da suke fitowa ya sa hannu ya goge mata. Ta ƙanƙame shi sosai tana sauke numfashi bata san yaushe za ta sake samun damar riƙe shi irin haka ba.

Watanni biyu kenan da suka wuce.

Fatima ta sa bayan hannunta ta goge hawayen da ya zubo mata.
"Allah ya tsare min kai Baban Al'amin".
Sai da ta miƙe za ta shiga kitchen ta ji wayarta na ringing.
Ta jawo wayar akan gado ta duba, sunan Iya ta gani.

"Assalamu Alaikum"

"Iya ta ɗauka" ta tsinkayi muryan Hassana sannan ta ji Iyan na cewa ta bata wayar. Fatima ta yi murmushin surukartata. Har yanzu dai bata iya bugo waya da kanta ba. Idan aka buga dai tana iya amsawa.
"Hussaina ta ce wannan koren zan riƙa dannawa idan na ji wayar na ƙara" wani lokaci da Fatiman ta je gida farko farkon lokacin da aka siya wa Iya waya ta ke faɗa mata.

"Iya, Ina wuni"

Ko amsawa ba ta yi ba tace "Fatima har yanzu Nasiru bai bugo ba?"

Fatima ta sauke ajiyar zuciya. Har ta gaji da faɗawa Iya cewa matsalar network ke hana Naseer kira.

"Iya wayarsa ce ta samu matsala kuma ƙauyen da suke ba service"

"Allah dai ya tsare shi a duk inda yake. Wannan aiki na su kullum kana cikin fargaba"

"Lah! Ya kusa dawowa fa. Wata uku ya ce kawai za su yi"

Lokacin da wata uku suka cika da tafiyar su Naseer ko ita Fatiman ta karaya dan yanzu kam ta fara tsorata da lamarin, dan kusan wata biyu shiru bata ji daga gare shi ba.
Zaman gidan ya isheta. Ta riga ta gama training ɗin da take na koyon girke-girke. Dama cewa yayi idan ta gama zai bata jari ta fara sana'ar yin cakes da sauran Pastries.

Wani lokaci ta kan shiga flat ɗin maƙociyarsu da ke mata kitso ko zata ji wani bayani daga nata mijin tunda shi yana nan amma kullum zancen ɗaya ne. Ba a ji daga mutanen Delta ba.

Wani lokaci idan tunanin ko dai mijinta ya mutu ne ya zo mata sai ta wuni kuka.
Watarana ma da Al'amin ya isheta da tambayar ina Abba kawai sai ta fashe masa da kuka. Sai aka koma shi Al'amin ɗin ke bata haƙuri. "Ummi ki bar kuka, ki bar kuka Ummi" duk da dai bai san kukan me ta ke yi ba amma ya sa hannunsa yana share mata hawaye yana cewa ta bar kuka. Fatima ta jawo shi ta rungume shi.

Ranan da Naseer ya bugo tana wanke kayan Al'amin a ta baya ta ji ringing ɗin wayarta daga falo. Da gudu ta shiga dan yanzu da ta ji wayarta na ringing da gudu ta ke ɗaukar wayar ko za ta dace da kiran Naseer.
Wata number ke kira ta ɗauka cike da fatan Baban Al'amin ne.

"Faty na"

"Baban Al'amin kai ne?" Ta fashe da kuka.

"Nine Fatima"

"Alhamdulillahi. Alhadulillahi" ta ke ta maimaitawa dan jin muryansa kaɗai ya wadatar. Cewa yana raye tsawon watanni huɗu da bata ji muryansa ba ya isa ta yi raka'a biyu dan nuna godiyarta ga Allah.

Duk maganan da ya ke mata ta kasa furta masa komai sai ma sake maƙale wayar a kunnenta ta danne da hannu biyu tana jin daɗin muryan nasa, muryan da dashewarsa bai hanata jin tasirinsa a jikinta ba.

Tunda ya ce mata cikin satin za su dawo ta fara washe baki tana nanata " Allah Baban Al'amin?, Allah za ku dawo cikin satin nan?"

Kamar kar wayar ya ƙare amma ce mata yai yana so ya je ya bada report zai kirata zuwa dare.

Suna gama wayan zama ta yi akan tile ta dafe ƙirjinta hawayen farin ciki na zubo mata.
Ba ta fata a sake turasu irin wannan aiki. Daga za su yi wata uku sai da suka yi wata biyar da sati ɗaya.

Sai da ta tattare nitsuwarta kafin ta kira Iya. Aminatu ce ta ɗauki wayar ta ce Iya tana sallah.

"Anty Amina Yaya ya kirani. Yanzu muka yi magana"

Daga ɓangaren Aminatun ta ce Alhamdulillahi.

Jin maganar Nasiru ake daga Sallama Iya ta miƙa hannu a bata wayar. Tana jin bayanin Fatiman ta saka kabbara. Kullum da addu'ar dawowarsa lafiya take kwana take tashi. Ba zata iya irga sau nawa ta ke yin sadaka saboda Allah ya kare mata shi ba. Kwanaki can ɗan Taure ta yanka ta yi sadaka da naman dan can ƙasan zuciyarta tana ganin kaman sadakan ƙosan da ta ke duk jummu'ah yayi kaɗan.

Suna gama wayar Iya ta fito tsakar gida ta fara kiran 'yan biyu su je su auno gero a store su jiƙa. Gobe da safe za ta yi kunu da ƙosan sadaka.
Allah ya warware mata babban matsalarta. Yanzu saura ta maida ƙarfinta wajen yiwa Aminatu addu'a.
Ga shi ko Mariya da ta zo ta yi zawarci ko shekara bata cika ba ta sake aure. Amma Aminatu har yanzu babu mashinshini. Ta kammala karatun Likitanci tana bautar ƙasa a babban Asibitin FMC da ke Azare amma maganar aure shiru. Bama wanda yake zuwan ne balle a sa rai. Kuma a yadda take lura da Aminatun ba damuwa ta yi da rashin auren nata ba.
Ita akan Aminatu har ta fara tsoron karatun 'yan biyu ga shi take takensu suma bokon suke son yi.
Kamar yadda Iya ta yi sadaka a Azare a ɓangaren Fatima ma sadakar ta sa aka mata. Tun a ranan ta fara gyare-gyaren gida.
Washegari ma sun sake waya da Naseer inda Naseer ke ce mata ta shirya ta wuce Azare Azare zai fara zuwa sai su dawo Lokojan tare.

Kwana shida da bugo wayarsa ta farko ya iso Azare. Shigowar dare ya yi suna zazzaune a tsakiyar gida yai sallama. Wannan karan Fatima ko kunyar surkuwarta bata ji ba da ita aka tashi ana rige-rigen rungumar Naseer.

Tun a daren ta lura da yadda ya faɗa ya ƙara baƙi, fararen idanunsa sun rikiɗa sun koma ja...
[27/11, 2:52 pm] Azizat Hamza Writer: *GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)


Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat



Page 013

Abu na farko da Fatima ta fara lura da shi game da mijinta tun dawowarsu shine rashin samun bacci.
Kwata-kwata baya iya bacci. Da ya rufe ido ko minti ishirin ba zai ka ba sai ya zabura ya tashi.
Ko kuma sai yana cikin bacci sai ya fara magana da ƙarfi yana bada command kaman yana filin daga.

Shirunsa shi ya sake kashe mata jiki ta tabbatar ba lafiya ba. Duk da dai ba wai dama can yana da yawar magana ba amma kuma yanzu idan yana gida idan ba ita ta masa magana ba haka zai yi shiru ya yi ta kallonta.

Ranan da ya je ya duba wani abokinsa da suka dawo tare wanda ya ke Asibitin mahaukata ɗaki ya shiga ya yita dukan gini.

"Baban Al'amin!"

Da ƙyar ta iya riƙe shi tana bashi haƙuri. Hannunsa sai jini ya ke.

"Kamal ya haukace Fatima. Kamal ya haukace"

"Ka yi haƙuri. Zai samu lafiya" ta rungume shi tana lallaɓashi kamar ƙaramin yaro.

Komai ya canja sanda Naseer ya dawo daga Delta. Ya koma mata wani sabon mutum ba mutumin da ta aura a farkon shekarar 1999 ba.

Ranan suna bacci da ke ana sanyi ta tashi fitsari sai ta ga bargon data rufa musu ya zame. Ta jawo bargon zata rufa masa ta ji an damƙo ta.

"Ba..ban... Al'... ni ce" ta faɗa da ƙyar

Sai da ya ƙyafta ido sannan yai saurin sake mata wuya yana faɗin "Fatima, ki yi haƙuri ban san ke bace"

"Baban Al'amin ya kamata ka ga likita. Tunda ka dawo kake wasu abubuwa da suke bani tsoro"

Jawota yayi jikinsa ya ce " ki yi haƙuri. Gajiya ce kawai"

Washegari numbar abokinsa da ta san yana jin maganarsa ta kira ta faɗa masa abun da yake faruwa.

Lokacin da Faruk Lawanti ya kira Naseer suka gaisa shi kansa yanayin yadda Naseer ɗin ke amsa masa ya tabbatar masa Naseer ba ƙalau ya ke ba.
Sun saba da sun yi waya da juna Naseer ya ke tsokalarsa da *Anty Faruƙ* shaƙiyancin da ya ke masa kenan tun lokacin da ya ajiye aikin soja ya faɗa harkar siyasa.

"Mutumina kana buƙatar ganin Likita. Kada ka cuci kanka, ba gazawa ba ce soja ya je rehabilitation. You need it, iyalinka suna buƙatar lafiyarka"

"Ƙalau na ke Lawanti"

"Na sani Zaki. Na san ƙalau kake. Amma dole ne ka je ka ga Likita saboda kwanciyar hankalin Iyalinka"

Naseer yai shiru yana sauke numfashi. Akwai abubuwan da ya gani da ba zai iya faɗansu ba. Akwai abubuwan da suka faru a sanadinsa. Akwai rayukan da suka tafi ba za su sake dawowa ba.

"It's okay to cry, Zaki" abinda likitansa ya fara faɗa masa kenan lokacin da Naseer ya ke ta ajiyar zuciya saboda abubuwan da ya tuno da suka haɗu suka taru masa a maƙoƙoro.

"Ka yi kuka, za ka samu sauƙi. Kuka ba gazawa ba ce. It's a sign of strength"

Shi kansa a zama na biyu da likitan nasa da ya bari hawaye suka zubo masa sai ya ji wani sanyi a ransa. Sai ya ji kamar an sauke masa wani dutse mai nauyi a kansa.
Kukansa na farko kenan tun da ya shiga aikin soja kuma yana fata ya zamo na ƙarshe.


Fatima ta ji daɗin canjin da suka biyo bayan wata ɗaya da Naseer ya fara ganin Likita. Ya fara samun bacci, ya dena zabura.
Sai dai wani abu ya tafi da Naseer ɗinta mai sakin fiska wannan Naseer ɗin idan ta ga haƙoransa to magana ya ke.
Wani lokaci da gangan ta ke wani abun ko zai yi dariya amma sai dai ya motsa baki kawai.
Ko lokacin da ta gano tana da ciki ta faɗa masa ba ta ga ya yi dariya ko murmushi ba.
Alhamdulillah ya faɗa ya fara tambayarta ina bata jin wani ciwo.

Shi kansa Al'amin ya fuskanci canjin mahaifin nasa. Dan yanzu wai yai ta masa wasa suna dariya irin na da babu shi.
Yanzu kam Fatima gani take Naseer ɗinta ya tafi, wannan Soja ne ya dawo a madadinsa.

Ko a can Azare suma sun ga canjin nasa.
Iya har tambayar Fatima ta ke ko Naseer yana sake mata fiska a gida.
Fatima ta yi murmushi ta ce yana yi.

Lokacin da cikin Fatima ya shiga wata bakwai aka tura Naseer course ɗin wata shida a China.

"Baban Al'amin wannan karan ma zaka dawo ka tarar Baby ta fara tafiya"

Naseer ya shafa cikinta yace " Baby kar ki yi fushi da Daddy kin ji ko"
Fatima ta saka dariya.

Da dare tana taya shi haɗa kaya ta ce "Baban Al'amin ni kam sai nake ganin kamar wannan karanma zamu juma bamu haɗu ba"

"Ki dena faɗin haka. Wannan karam karatu ne Fatima ba aiki ba. Da mun gama zan dawo Insha Allah."
Ya dafa kafaɗarta ya manna mata kiss a goshi ya ce " ki yi haƙuri za ki haihu bana kusa"

"Al'amin ma ai sai da ya fara rarrafe ka zo ka ganshi"

"Ki ƙara min haƙuri, kin ji" ya sake mata peck a goshi.

"Ni kam Baban Al'amin ka min dariya mana kafin ka tafi. Ka san yaushe rabon na ga ka yi dariya kuwa"

Murmushin gefen baki ya mata yana shafa kumatunta. Shi kansa ya rasa me ya ke hana shi yin dariyan. Ko ya yi yunƙurin yi sai dai kawai ya iya yin murmushi.

"Ai ban ga haƙoranka ba"
Buɗe mata bakin yayi kamar mai tallen MacClean.
Fatima ta saka dariya.

Washegari kuwa har mota ta raka shi da guntun hawayenta.

"Baban Al'amin"
Sai da ya juyo ta faɗa jikinsa ta ƙanƙame shi. Yau kam kunyar tata a ɗaki ta baro shi kafin su fito. Sojan da zai kai shi airport ya juya fuskarsa yana murmushi saboda shi ga shi gauro ne har yanzu bai yi aure ba.

Wata ɗaya da tafiyan Naseer da aka yi hutun makarantan su Al'amin Fatima ta tattara musu kayansu suka wuce Azare. Ta faɗa wa Naseer wannan karan a Azare za ta zauna har sai ya dawo. Idan an koma makaranta za ta saka Al'amin a makaranta a nan Azare ɗin.
A gidan Iya ta zauna duk da an kammala ginin gidan Naseer sai dai ba a zuba kaya a ciki ba tafiyarsa course ya hana shi saka furnitures a gidan ya bar shi akan sai ya dawo sai a saka kafin su tare.

Wannan karam kan ba a kwana biyu uku Naseer bai kira gida ba, idan ya jima ne yai sati.


*July, 2005. Azare*


Ranan wata laraba da yamma Fatima ta fara naƙuda. Iya da Hussaina suka kaita Asibiti.
Haihuwar bai zo ba sai ƙarfe ɗayan dare.
Wacce ta karɓi haihuwar ce ta ja Dr Aminatu da ta shigo gefe tana mata bayanin abinda ya ke faruwa. Bleeding Fatima ta ke sosai.
Dr Aminatu ta je ta yi magana da Likitan da ke kan duty suka shiga dubata.

Ba a sallamesu a Asibitin ba sai da ta yi kwana huɗu bayan an ƙara mata jini. A ranan da suka koma gida kwana ɗaya kuma jikin ya sake dawowa, sai ta yi ta jin hajijiya.
Dr Aminatu ta ce su koma Asibitin a sake dubata. Suna Asibitin har aka yi suna. Yarinyar ta ci sunan Fatima Zahra. Sunan da Naseer ya zaɓa mata kenan. Dama ya ce idan mace ce to Fatima ce idan kuma namiji aka samu to zai ci sunan abokinsa.
Ba a yi taron suna ba saboda mai jego har yanzu tana Asibiti.
Kwana biyar da sunan 'yar har ana shirin sallamarsu Fatima ta rasu.
Mutuwar ta girgiza su ba kaɗan ba.
Ana ta kiran wayan Naseer amma ba ta shiga.
Sai ran sadakan uku da ya kira ake gaya masa rasuwan.
Shiru yayi lokacin da Yayarsa Bintu ke faɗa masa rasuwar.
Ya yi kusan minti biyu yana ajiyar zuciya kafin ya iya cewa " Allah ya mata rahama"

Ko da aka bawa Iya wayar kasa magana ta yi. Da ƙyar ta iya cewa "Nasiru, Fatima lokaci yayi. Allah ya gafarta mata"
Ya amsa da Amin.
Kamar yadda bai ga rasuwan Malam ba haka nan Fatima ta tafi ta bar shi ba tareda sun yi bankwana ba...
[27/11, 2:52 pm] Azizat Hamza Writer: *GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)


Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat



Page 014


*2007, Azare Bauchi state*


"Yanzu haka zaka cigaba da zama babu aure. Nasiru ka yiwa kanka adalci kuwa?"

Naseer ya ɗaga ido ya kalli Iya sai dai bai iya ce mata komai ba. Shekaru biyu kenan da rasuwan Fatima. Kuma ko yaushe ya samu damar zuwa gida sai Iya ta saka shi a gaba da maganar aure.

Ba wai baya son auren bane. Sai dai har yanzu ya kasa samun nitsuwar da zai tsaya ya nemi wata mace. Zaɓa masa Fatima aka yi kuma ya riƙeta da hannu bibbiyu, bai taɓa nadamar haka ba saboda Fatima mace ce ta gari. Duk da ba auren soyayya suka yi ba, a zaman aurensu akwai zaman lafiya da farin ciki.

Wannan karan yana so ya zaɓo matar da zai aura da kansa ne, sai dai har yanzu bai ga wacce ta dace da shi ba.
Iya ta masa tayin 'yanmata kusan uku yana ƙi, yayyensa mata ma ba a barsu a baya ba, kowa da wacce take biɗar ya aura.
Akwai wata cousin ɗin abokinsa Faruƙ Lawanti da ta nace masa ita ma, amma bai tunanin zai iya aurenta dan bata kwanta masa ba.

Yana buƙatar mace a tare da shi. Yana buƙatar 'ya'yansa Al'amin da Zahra su koma hannunsa da zama.
Akwai kaɗaici idan ya dawo daga office ya shiga gida ya ji wayam babu ɗuriyar mutum a cikin gidansa.
Yana da niyyar shekaran nan ba zai ƙare ba zai yi aure.
Ko ina matarsa take zai samota ba sai an nemo masa ita ba.

Kamar yadda ya saba zuwa ya yi kwana biyu a Azare wannan karan ma kwana biyun yayi ya shirya komawa bakin aikinsa a Maiduguri amma kafin nan zai halarci bikin wani abokinsu a Abuja. Tare da Lawanti za su wuce dan dukkansu a NDA Kaduna suka haɗu.
Kaduna zai fara wucewa ya haɗu da Lawanti su wuce Abuja.

"Maganar Aminatu baka ce komai ba"

Iya ta masa maganar lokacin da ya shigo ɗakinta sallama.

Sun yi magana da Aminatu. Itama tana son auren amma abun ne ya gagara, duk masu zuwa sai su dinga ja baya da tsoron wai tunda aikin Asibiti take ba zata samu daman zaman gida ba, masu aikin Asibiti basa hutu safe har dare kullum suna aiki.
Ya kan faɗa mata cewa za ta samu mijin da zai sota ya kuma aminta ɗari bisa ɗari da irin aikin da take. Kar ta ɗaga hankalinta.
Ita kuma Iya kullum ƙorafinta Aminatu ta doshi shekaru talatin babu aure.
Da ke a lissafinta na dikake gani take shekarun Aminatun da yawa tunda ba wai ta kama ainihin shekarar haihuwarta bane (date of birth).
Sai dai Naseer da ya san lissafin shekarun ya san shi kansa yanzu ne ya shiga shekara talatin ɗin, amma a lissafin Iya ganin ya kai arba'in ta ke. Ta manta cewa auren wuri yayi.

"Aure lokaci ne" ya bata amsa "Kamar yadda Allah ya baiwa sauran 'yan'uwanta mazajen aure itama Allah zai bata nata mijin. Ki dena ɗaga mata hankali, ki cigaba da yi mata addu'a kuma ki sa mata albarka a aikin da take. Wannan kawai shine iya abinda za ki iya yi mata"

Yana alfahari da ƙanwarsa Aminatu. Ita ce ta ciri tuta ta yi karatu mai tsayi bayan shi. Da ke Allah ma ya taimaketa dukkan karatun da ta yi cikin sa'a ta yi, babu wani tangarɗa ko kaɗan.
Akwai Alfanun karatun 'ya mace. Ita kanta Hadiza ma da ta yi NCE farkon shekara da ya zo gida take ce masa ta samu admission a ATBU da ke Bauchi za ta jona degree kuma mijin ya barta ta cigaba da karatunta.

"To ga nan Musan gidan Inna Ladi yana so ya aureta ta ƙi shi. Ka ga auren ne bata so"

"Amina ba za ta auri Musa ba" Naseer ya faɗa da wani izza wanda ke nuna maganarsa ta tsaya kenan.
Iya ta hangame baki. Dama so take ta lallaɓa shi ko zai yiwa Aminatu

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment