Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a India"

"Yanzu ita Fatiman haka zaka barta har shekara ɗaya?"

Ya ɗan yi shiru.

"To, Allah ya kaiku lafiya ya dawo mana da kai lafiya"
Naseer ya amsa da Amin.

Ranan da zai wuce Kano saboda a nan za su shiga jirgi haka ya rungumi Fatima da ke ta masa kuka.
"Ki yi haƙuri Faty na. Daga yanzu dole ne ki fara sabawa da tafiyata, ko na dawo yanayin aikinmu zai dinga saka ni yawan tafiye-tafiye. Duk lokacin dana tafi ki dinga min addu'a kin ji"
Ta gyaɗa kai tana sake maƙale shi.
"Kin ga, kalleni"

Ta ɗaga ido ta kalle shi.
"Ke da kike ta kuka yanzu bayan na bar miki ajiya jiya da dare"
Ta yi saurin rufe fiskarta tana dariya.

"Ki yi addu'a Allah yasa wannan karan mun samu Baby, kin ga idan na dawo kawai sai dai na zo na tarar da mai sunan Malam yana wasa a ƙofar ɗakin Iya"

Ta sake rufe fiskarta tana jin daɗi.

Haka dai aka rabu ba dan ana so ba.

Naseer Zaki ya tafi India dan yin course na shekara ɗaya a Indian Military Academy da ke Dehradun a ƙasar India. Ya bar mutanen gida da kewarsa.

Tafiyarsa da wata ɗaya Fatima ta fara laulayin ciki. Tunda Iya ta lura da yawan baccin da ta ke ta fara zargin ciki gareta.

A hankali Fatima ta cigaba da renon cikinta kullum tana cikin kewar Naseer ga shi ko saƙo baya aiko musu ba kamar lokacin da yake Kaduna ba da yake aiko musu wasiƙa duk ƙarshen wata, kuma da anyi wata huɗu ya kan dawo gida hutu.

Wannan karan Iya ta sa ido sosai akan Fatima. Lokacin da cikin ya cika wata biyar ma ta fara hanata aiki tsoronta kar a sake rasa cikin irin na wancan karan.
Cikin ikon Allah kuwa a ranan goma ga watan March na shekarar 2001 Fatima ta haifi ɗanta namiji kyakykyawa a Asibiti.
Ba ƙaramin kulawa ta ke samu a wajen Iya da ƙannen Naseer ba.
Ranan suna aka sawa yaro sunan Malam kamar yadda Naseer ya faɗa mata. Muhammad suna kiransa da Al'amin, ita kuma Iya na kiransa da Malam.


***


Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900


Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41
[27/11, 2:51 pm] Azizat Hamza Writer: *GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)


Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat



Page 009





Hussaina ta fito daga banɗaki ɗauke da fitila jikinta na ɓari saboda jinin da ta gani ɗazu da suka dawo daga Islamiyya ya ƙi tsayawa.

"Hussaina kawo fitilan mana, zan raba miya ne"
Hauwa'u da ke tsaye a tsurkukun kitchen ɗinsu ta faɗa. Iya da Fatima sun je barka ita aka bari da abincin dare amma saboda shegen son kallo bata fara girkin ba sai bayan magariba. Wata Amarya aka kawo kusa da gidansu Anty Fauziyya tana da kayan kallo a ɗakinta.
Wani lokaci kafin ta biya wajen ɗaki idan akwai wuta sai ta shiga wajenta ta ɗan yi kallo. Yau ma wani cassette ta saka musu na India shi ya ɗauke mata ido ta manta da girkin da za ta yi.

Hussaina ta miƙa wa Hau'wa'u fitila ta shige ɗakin Iya tana tunanin wa za ta faɗawa maganar jinin nan. Iya? ko Anty Fatima? ko kuma Hauwa'u?.

"Lafiyanki?" Hassana ta tambaya lokacin da ta shigo kiran Hussainar ta fito su ci tuwo ta sameta duƙunƙune akan gadon Iya.

"Na komai, ki je ki ci ba yanzu zan ci ba"

"Wallahi idan ba ki fito ba sai na cinye naman ki"

Hassana ta fice a ɗakin tana sa wa a ranta idan Hussaina bata fito ba duka naman cikin miyar za ta tsame ta barta da gayan tuwo. Kwana biyu suna samun nama nasha-nasha a miya. Wata Akuyar Iya ce ta kasa shine aka yanka shekaranjiya tun daga ranan kuma suke watanda da nama.

Tana zama kuwa za ta fara cin tuwon ta tsinkayi sallamar Iya da Fatima.

"Iya sannu da dawowa"

Iya ta cire hijabinta ta fara ninkewa ta ce " ina Hussaina?"

"Na kirata ta ce wai in je in fara ci"

Fatima ta shige ɗakinta ta kunce goyonta ta saukar da Al'amin.

"Me ya sameki?" Iya ta tambaya bayan ta shigo ta ga Hussaina kwance akan gado.

"Cikina ke ciwo"

"Shine kika kwanta. Maza tashi Hassana ta raka ki kije kemis a baki magani"

Ta ɗan tashi zaune ta ce "har da jini"

Iya bata tambayeta komai ba ta fita ta ɗauko fitilan da ke gaban Hassana da ke kai faman tauna ƙashi ta zo ta buɗe akwatinta tana neman zani. Gida biyar ta yanka zanin ta miƙa wa Hussaina tana mata bayanin yadda za ta naɗe ƙunzugun.

Dukkansu akan tabarma ana cin abinci suka ji sallamar yaro daga zaure.

"Wai Iya Abu ta zo"

Gaba ɗaya suka sake baki.

"Iya Abu ko Hauwa'u?" Hassana ta faɗa dan Hauwa'u ce ke da samari.

"Iya Abu aka ce"

Iya Abu dai bata ce komai ba. Wa zai zo nemanta da dare haka. Babu namijin da ya ke zuwa wajenta sai Basiru ƙanin mijinta wanda shima sai da dalili ya ke zuwa kuma shi babu shamaki da shigarsa gidan, sallama zai yi daga zaure idan aka amsa ya ƙariso cikin gidan.

Hauwa'u ce ta zari gyale ta fita dan ta duba waye ya ke neman Iya.

Cikin hasken farin wata ta gane shi. Malam Dogo mai nama ne.
Suka gaisa sai wani murmushi ya ke yana sosa ƙeya. Ko da ta shiga gida ta gayawa Iya Malam Dogo ke nemanta sai abin ya sake ɗaurewa Iya kai.

"To Iya ki je ki ji me ya kawo shi mana"

"Ke!"

Hassana ta yi dariya ƙasa-ƙasa

Ko ƙarisa cin tuwon bata yi ba Iya ta ɗauraye hannu ta sa hijabi ta fita.
Mamakin zuwan mutumin da sunansa kawai ta sani bata san kamanninsa ba.

Sallama ta masa ta haɗa da tambayar lafiya?.

Malam Dogo ya wani lanƙwasa kai yana tambayarta ya aka ji da hidimar yara.

Daga yanda suke tsaye ko wajen zama bai samu ba Iya ta katse shi daga dogon hiran da yake shirin ɓarowa.

"Me ya kawo ka, Malam Dogo"

"Dama dai nace" yai shiru yana karantar fiskarta cikin hasken farin wata. Ɗazu da yamma yana rumfarsa ya ga wucewarsu ita da surkuwarta. Ya tambaya ake tabbatar masa matar marigayi Malam Muhammadu ce shine ya wanko ƙafa ko za a dace duk dama dai lokacin da yai auren farko tana da cikin Naseer, an yi aurensa da sati guda aka haifi yaron.
To sai me?.
Ko zata girme shi ma ai ba zai wuce da shekaru uku zuwa biyar ba. Ai Annabi ma ya auri wacce ta girme shi. Dan haka sunna zai ɗabbakar.

"Malama Zainabu" ya cigaba da maganarsa. "Kin san dai dama haka Allah yake lamarinsa, idan wani ya tafi sai wani ya maye gurbin wani. Kuma dama zaman duniya ita kanta cuɗeni-in-cuɗeka ne. Ina so ki bani dama na taya ki riƙe marayun da ke hannun ki"

Iya Abu ta fusata. Wani irin magana ne wannan. Yau shekara uku da rasuwan Malam babu wanda ya taɓa tunkaranta da maganar banza irin wannan sai yau.
Amma dai mutuwar miji tonon asiri ne.
Da tsofai tsofai ɗinta wani aure za ta sake yi yanzu.

"Ka ga Malam Dogo..."

"Sunana Sama'ila"

"Koma dai menene sunan naka ina so in baka shawara, kada ka ƙara zuwa gidan nan da zance irin wannan..."
Tana maganar da iya ƙarfin muryarta.

"To Malama Zainabu idan ba..."

Sallamar Baffa Basiru ya katse shi.

Iya Abu ta juya ta shige ciki ko yaranta bata tsaya biyewa tambayarta da suke ba ta shige ɗakinta ta rufo ƙofa ta samu gefen gado ta zauna ta fara hawaye.
Mutuwar Malam ne ya dawo mata sabuwa wai yau saboda Malam na cikin ƙasa har wani namiji zai iya zuwa wai zance wajenta.

Ko da Baffa ya ce a mata magana ta fito su gaisa ƙin fitowa ta yi.

Abu kamar haɗin baki sai ga shi bayan Malam Dogo kusan mutane biyu sun sake zuwa nemanta ciki har da abokin Malam ƙut da ƙut. Dukkansu babu wanda ta bawa fiska, ta riga ta gama aure a duniya. Yo ma da manya-manyan yaranta wani aure za ta kuma yi.

Lokacin da Baffa Basiru ya ga zawarawa sun fara zuwa neman Iya Abu sai shima zuciyarsa ta raya masa ai shi ya fi cancanta ya auri Abu ba wani bare ba.
Daga nan ya fara canja salonsa sai ya siyo cefane ya aiko musu, safe da dare sai ya zo duba su.
Iya Abu ta lura da take-takensa amma ta yi biris kamar bata san me yake nufi ba.
Rashin namiji a gidan ma babu daɗi. Da Nasirunta na gida babu wanda zai iya zuwa ya tunkareta da wani zancen aure.

Sai da aka ɗau wata biyu da zuwan Malam Dogo sannan Baffa Basiru shima ya fito ya faɗawa Iya Abu manufarsa. Ai kuwa ta masa tatas dan har gara ace bare ya nemeta, amma Basiru ƙanin mijinta ai wannan cin amana ne na ƙarshe.

Haka dai zawarawa suka ƙarishi zuwansu suka haƙura babu wanda Iya Abu ta amsa tayinsa.
Shi kuwa Baffa Basiru har Chinade ya je yai wa yayyenta magana amma ta ƙi bashi haɗin kai. Da ya ga fa ba zai yiwu ba sai ya janye ƙafarsa ɗan alkhairin da ya ke yi musu ya dena.

Cikin yaranta dama babu wanda ya goyi bayan Iya ta sake aure. Hadiza ce ma ta nuna kaman tana ra'ayin Iya ta sake aure saboda kaɗaici. Ai kuwa ranan da ta yiwa Iya maganar tofin Ala-tsine ne kawai bai fito daga bakin Iya ba saboda yadda ta ƙyamaci abin. Tun daga lokacin kuma kowa yayi shiru.


Tafiyar Naseer India da shekara ɗaya da wata uku suka dawo.
Watarana Iya ta yi dambu ana tsakar gida ana ci Indo ta zo daga Kano suka ji hayaniya daga waje.
Ai tun da aka shigo aka ce Naseer ya iso gari yaran suka cire hannu a abinci suka zuga waje har da Indo ma da 'yarta a hannu.

Iya dai na zaune sai hamdala ta ke a ranta. Fatima ta tashi ta shige ɗaki tana ta murmushi.

Wannan karan har kumatu yayi kamar ma dai ba karatu ya tafi ba dan yayi haske ya ɗan yi jiki. Ƙila kuwa ƙasar da ya je ne ta karɓe shi.
Kamar yadda ya faɗa lokacin da ya shigo gidan Iya ya gani zaune akan tabarma sai kuma yaronsa da ke ta ƙoƙarin rarrafe. Ko ba a faɗa ba ya sani wannan yaron ɗansa ne. Balle kuma tun a waje Hassana da Hussaina sun gulmata masa.
[27/11, 2:51 pm] Azizat Hamza Writer: *GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)


Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat



Page 010




***

Kaka Medugu na ƙofar gida yana shan giyarsa ta gargajiya elders ɗin church suka iso.
Bayan an gaisa sai suka wuce ciki.
Ya girgiza kai yana ƙara jin shigar giyar cikin jininsa. Ko da elders suka fara zuwa wajen Tabitha saboda ta dena zuwa church bai saka baki a maganar ba. Ko ɗansa bai tambaya dalilin da yasa matarsa ta dena zuwa church ba. Shi dai ya sani babu wanda ya isa ya sauya masa ra'ayi akan aƙidarsa. Wai mutum ya yasar da abinda ya sani iyaye da kakanni ya rungumi wani abu saboda da wasu jajayen fata suka shigo da shi.

Kyauta ce ta fara faɗa masa Mama ta ce ba za su sake zuwa church ba ranan wata sunday da ta je ta ɗauko sunday dress ɗinta Mamanta ta ƙi saka mata.
Akwai gidaje dayawa a Gulak da suke da addini biyu a gida ɗaya irin nasu. Shi yasa duk da ƙarancin shekarun Kyauta ta san cewa Babanta musulmi ne Mamanta kuma kirista ce. Ran Sunday sukan je church da Mama shi kuma Baba idan yana nan yana koya mata yadda ake sallah. Amma Kyauta ta fi son zuwa church saboda za su yi rawa su yi waƙa kuma tana sa kaya mai kyau ga shi idan sun dawo Mama ta kan dafa musu sunday rice mai daɗi. Kusan fiye da rabin 'yan ajinsu kirista ne hakan ya ƙara saka mata sha'awar son zuwa coci.

Ko da Kyauta ta faɗawa Kaka Medugu Mama ta ce ba za ta sake zuwa church ba ce mata yayi idan ta ƙara girma za ta iya zuwa duk inda ta ke so.

Kaka Medugu yana son Kyauta sosai. In dai ta dawo daga makaranta haka zata zauna a rumfarsa yana bata labarai ko kuma ta riƙa taya shi daka ganyayyaki da saiwowi.
Tana da basira sosai dan duk abinda ya gwada mata sau ɗaya to ta riƙe kenan.

Ba elders ke zuwa wajen Tabitha ba har da 'yan'uwanta wanda a danginsu na kusa ita kaɗaice ke auren Musulmi.

Abu dai ya ci tura ba a samu yadda ake so ba.
John-Yahaya bai taɓa tursasawa matarsa karɓar addinin da yake yi ba. Shekaru sama da goma da ya zama musulmi babu rana ɗaya da ya cewa matarsa ta shiga addininsa. Yana ƙoƙarin kyautata mata kamar yadda ya saba kuma bai taɓa nuna mata banbancin addininsu matsala ne a wajen 'ya'yansu ba. Kafin Sɗang ya tafi boarding school yana sallah sosai sannan duk lokacin da aka tashi hidimar kirsimeti ko new year ko easter ya kan bi Mamansu su je church a yi hidimar tare da shi.

Ko lokacin da Tabitha ta zaɓi ta dena zuwa church ɗin John Yahaya bai san dalili ba. Sai da aka yi sati uku bata zuwa ya tambayeta ko lafiya ta ce lafiya ƙalau.
Lokacin da elders suka fara sintiri a gidansa bai ce ƙala ba. Kamar yadda aka koya masa ba a tursasa mutum shiga addini. Duk sonsa da Tabitha ta karɓi musulunci ba zai iya yi mata dole ba. A duk lokacin da ya samu dama yana ƙoƙarin karantar da ita abin da ya sani na addininsa.
Bai sani ba ko irin abubuwan da yake faɗa mata ne yai tasiri a zuciyarta, bai sani ba ko kuma rigimar da suka yi da matan zumunta na church ɗinsu ne ya fara canja mata ra'ayi. Amma dai wani abu ya taɓa matarsa hankalinta ya fara karkata zuwa addinin da ya ke yi.

Ko bayan dena zuwa church ɗin Tabitha sai da aka shafe sama da shekara Tabitha na yiwa John Yahaya tambayoyi game da musulunci, abinda bai sani ba sai yace mata zai tambayo.
Rana ɗaya ta gamsu da zaɓinta ta cewa John Yahaya tana son zama musulma.
Wannan ya fi komai daɗi a wajen John Yahaya. Ko bayan ta musulunta Tabitha ake kiranta amma Fatima ta zaɓa a matsayin sunanta na musulunci.
Iyayen Tabitha sun yi fushi da ita sosai. Dan an ɗau lokaci ma basa mata magana ko ta je gaishe su haka zata dawo. A hankali dai suka huce suka rungumi 'yarsu.
Dama a Gulak zaman lafiya ake tsakanin mabiya addinan biyu. An riga ma an shiga cikin juna ne dan da wuya mutum kirista ya ce babu musulmi a danginsa ko kuma musulmi ya bugi ƙirji yace babu kirista a danginsa. Su 'yan'uwa ne dan haka addini bai raba zumunci da alaƙar da ke tsakaninsu ba.
Har wa yau idan ana bikin sallah mabiya addinin kirista za su taru su taya 'yan'uwansu musulmai murna su shiga hidimar sallah a ci a sha a yi murna duka tare. Haka ma musulman idan ana bikin kirsimeti za su shiga a yi biki da su, su kai wa 'yan'uwansu kirista ziyara su ci shinkafa, su ci chin-chin ayi wasa da dariya.

Sai da Kyauta ta shiga Primary five Fatima Tabitha ta fara ciwon ciki.
Suka je Asibiti aka ce musu appendix ne aka ce sai an cire. Bayan an cire appendix ɗin still ciwo ya sake dawowa daga Asibitin Madagali aka tura su Yola ganin babban likita. Bayan sun yi ta test-test, sun sha sintiri aka ce musu wai cancer ce ta kama bakin mahaifarta.

Kaka Medugu ya ce su haƙura da maganin Asibiti ga na gida nan, John Yahaya ya ce bai yarda ba.
Basu da kuɗin aiki da aka ce za a yi mata, ga magungunan da aka rubuta da tsada.
John Yahaya ya shiga neman yadda za a yi ya samu kuɗin aiki. Ya sai da biyu daga cikin gonakansa aka haɗa kuɗin suka je aka mata aiki.

Ta samu lafiya na watanni kaɗan bayan aikin. Shekara ɗaya da aikin ciwo ya sake dawowa, da suka koma Asibiti aka ce musu wai cancer'r ce ta dawo ashe ta riga ta shiga cikin mahaifarta. Aka ce musu sai dai a cire mahaifar gaba ɗaya.
Wannan karan Tabitha ta hana John Yahaya siyar da kadarorinsa akan ciwonta. Ta ce su gwada maganin gida kawai...


***


"Baba, yaushe Sɗang zai dawo?"

John Yahaya ya cigaba da kaftu ba tareda ya amsa wa 'yar tasa ba. Ta yi tambayar ya fi a irga tun daga zuwansu gonan kuma ya faɗa mata shima bai sani ba. Amma daga ta ɗan yi aiki ta gaji sai ta sake maimaita tambayar.

Jiya Sɗang ya tafi Madagali, ya je rubuta jarrabawar Jamb.

Sai da John Yahaya ya kai ƙarshen kunya sannan ya ɗaga fartanyarsa sama. Jiki da jini, yanzu girma ya sa ba ya iya irin aikin da ya ke yi a baya.

"Ngwatam, kawo min ruwa"

Kyauta da tuni ta yashe a ƙasa tana hutawarta ta ɗauki jarkar ruwansu ta tsiyaya ruwa a ƙofi ta kaiwa Babanta.
John Yahaya ya kalli 'yar tasa bayan ya miƙa mata kofin. Kyauta ta fara zama budurwa. Ance ya sake aure bayan mutuwar Tabitha amma bai ji a ransa zai iya sake wani auren ba.
Tabitha ta mutu ta bar shi da kewanta. Baya tunanin zai taɓa samun mace kamar Tabitha.

Lokacin da suka dawo daga gona Kyauta ta shiga kitchen ta ɗumama musu tuwo.
Lokacin da ta zauna ta fara ci Kaka Medugu ya ƙwala mata kira da sunan da ya fi kiranta da shi "Męnagkur"
"Na'am Kaka" ta tashi ta shiga ɗakin Kaka. Tukunyar maganinsa ya ce ta ɗauka ta je ta ɗumama masa zai sha. Ta ko ɗauki tukunyar ƙasar wanda tun tasowarta a gidan take ganin Kaka na dafa magani a ciki. Kaka Medugu ya sha faɗa mata tukunyar ya girmi Babanta ma dan tun kafin a haifi Babanta ya ke amfani da shi.

Ta shiga kitchen ta sauke ruwan wankar da ta ɗaura a wuta ta ɗaura tukunyar maganin.

Baba ya fito daga ɗaki ya ga ƙuda na bin abincin da Kyauta ta bari buɗe ya ƙwala mata kira "Kyauta"

Kafin ta zo ya nemi wani marufin tukunya da ya gani a gefe ya rufe mata abincin.
Ta fito daga cikin kitchen Babanta ya fara mata faɗa akan barin abinci da ta yi a buɗe. Ta ce masa yanzu ta shiga kitchen fa.
Bayan Kyauta ta ci abinci ta tattare kwanuka ta wanke sannan ta shiga wanka. Tana fitowa da ta yi sallar Azahar ta ɗebo wake ta fara tsincewa.

Tun kafin Mamanta ta rasu ta riga ta saba da aikin gida. Lokacin da ake sintirin zuwa Asibiti ita ke tashi ta yi wanke wanke da shara sannan ta yiwa Kaka ɗumame kafin ta wuce Makaranta. Idan ta dawo haka za ta ɗaura abincin rana. Idan yayanta Sɗang yana gida shi da ita suke raba aikin gidan.
Lokacin da Mamanta ta rasu ta rubuta jarrabawar common entrance har ta ci Special School, Mubi, amma saboda rasuwar ta ce ba zata je ba duk da kuwa Babanta ya so ta tafi. Da ta dage ba za ta je ba sai aka saka ta a Government Day Secondary School, Gulak...
[27/11, 2:51 pm] Azizat Hamza Writer: *GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)


Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat



Page 011




"Three, two, one, Action"

Director na faɗin Action sabuwar jarumar ta fara magana tana farfari da ido cikin camera. Wannan farfari da yanga-yanga da take yawan yi shi ya sa mutane ke sonta.

Jaruma Munira Bawa da ake kira da MoBaby tun a film ɗinta na farko da ta kira kanta da MoBaby tana tsaka da ɗaukar shirin film ɗinta na bakwai kenan a cikin wata uku.

Jarumar ta shigo masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood da sa'a dan kuwa tun a film ɗinta na farko da ta yi da jarumi Ali Nuhu mai suna MUNIRA tauraruwarta ta fara haskawa a duniyar film.
Sai ga shi tun daga film ɗin Munira Directoci da yawa suka fara rige-rigen saka Munira Bawa a film ɗinsu.

Munira Bawa 'yar Asalin jahar Kano ce amma tashin Lagos. Wannan yasa ko lokacin da ta shigo Kannywood ta zama daban a cikin sauran jarumai mata.
Na farko kasancewar ta yi Sakandare mai kyau a can Lagos sai ya kasance tana ɗan jin turanci, dan ko a film ɗinta na farko Munira ɗan turancin da ta ke sakewa lokaci zuwa lokaci shi yasa mutane suka ji suna sonta. Haka nan directors ke ganin tana da wata dama da wasu jaruman basu da shi.
Na biyu kasancewarta tashin Kudu sai ya kasance babu irin kayan da bata iya sakawa.
Ko da producer bai ware kuɗin kaya ba za ta sako ƙananan kaya ta saka gashin wig ta fito a film tana ƙwalisa babu ruwanta.

A shekarar 2002 da 'yan Izala ke ta wa'azi suna ƙorafe-ƙorafe akan masana'antar film ɗin ba kowacce jaruma ba ce ke iya saka irin kayan da Munira MoBaby ke sakawa.

Daraja ta uku da ta ɗaga MoBaby tun shigarta film industry shine iya rawarta. Ta taso tun tana yarinya take son kallace-kallacen fina-finan India wanda yai tasiri a rayuwarta ya saka mata sha'awar shiga film tun ma bata kammala sakandare ba.
Idan tana kallon films ɗin Indiyawa ba abinda ta ke kwaikwayo sai yadda matansu ke rawa suna kwarkwasa.
Lokacin da ta fara film mutane suka ga yadda take rawa sai aka fara dangantata da Madhuri dixit ɗin Kannywood saboda iya rawarta, wasu kuma su ce mata Aishwariya Rai. Manyan mutane da suka taso suna kallon fina finan Indiyawa na 80's kuma suke dangantata da jaruma Hema Malini.

Kafin MoBaby ta yi film goma har sunanta ya shahara ya fara fin na tsofin jaruman da ta zo ta tarar a masana'antar.

Ba zaka ce MoBaby tana da kyau na shiga rai ba amma tsantsan iya kwalliya da kwarkwasa shi yake jawo hankalin mutane gareta su ke ganin tana da tsananin kyau. Bata cika shekara bama a masana'antar ta ɗan fara shafa mai dan ta ƙarawa fatarta haske duk dama ita ɗin ba baƙa ba ce, tana da hasken fatar da a turanci ake cewa caramel skin.

Jarumi Ali Nuhu da ke tashe a duniyar film ɗin Hausa shi ya kawo MoBaby cikin masana'antar. Mijin yayarta da Ali Nuhu abokai ne na ƙut da ƙut. Wani zuwanta hutu daga Lagos zuwa Kano lokacin tana SS2 ta haɗu da Ali Nuhu a gidan. Tun daga lokacin ta sanar da shi tana sha'awar shiga film ya ce mata ta bari ta kammala karatunta tukunna. Ai kuwa tana gama zana jarrabawar WAEC ta niƙo garinta ta taho Kano ta bar iyayenta a can Lagos.
Duk da mahaifinta ya so ta cigaba da karatu ita kam ta shafawa fiskarta toka akan film za ta yi ba karatu ba, koda zata cigaba da karatu sai a gaba.
Gashi yanzu ta ji daɗin yadda tauraruwarta ke haskawa ta ajiye maganar karatu ta kama sana'ar film haiƙan.



***

*2003, Ekiti State*



Cikin shigarsa ta khakin sojoji ya fito daga ɗaki ya kalli ƙaramin falonsa wayam babu komai a saman center table da ke falon. Yau ma haka zai fita ba tareda ya yi breakfast ba. Gaskiya dole ne ya je ya taho da Fatima. Zaman gauro da yake a wannan garin ya ishe shi.
Ya shiga kitchen ya duba flask ɗin ruwan zafi ko tea ne ya haɗa ya sha kafin ya fita amma babu ruwan zafin a ciki. Yai tsaki ya fito daga kitchen ɗin ya ɗau brief case ɗinsa da keys ya fito.

Second Lieutenant N. M. Zaki kenan, soja ma'abocin tsayi da kaurin jiki.
Yana fitowa ya haɗu da maƙocinsa Christopher ya fito riƙe da ƙaramin kwando da aka saka masa kular abinci. Wannan ya sake tunzura Naseer ya ji cewa dole ne wannan karan ya taho da Fatima ko tana so ko bata so.
Dama tunda aka tura shi garin Ekiti da ya nuna yana so ya taho da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment